rushewa tayi da kukan Fatyma taji tausayin su matuk'ar gaske domin tasan Aminan juna ne Laure da Dije tsakiyar ta zauna tare dafasu.
"Kuyi hak'uri Ai bama mutuwa d'aya daga cikin ku yayi ba rabuwa kuma ba mutuwa bace kuna tare da juna kunji ku daina Kuka nima kada ku sani nayi Kuka Aure ne babu inda bazai kai d'iya mace ba."
rarrashin su tayi har sukayi shiru taga sun fara murmushi sannan tace
"Kuzo muje muyi dinner."
"Nak'oshi nidai."
Fatyma kallon Dije tayi
"Haba Khadeeja me kika ce da zakice kin koshi ne?"
"Allah kuwa nakoshi"
"To mekikeso tunda bazaki ci Abinci ba."
"Babu komai."
"A'aaa gaskiya ba'ayi haka bari na samo miki wani abu mai ruwa may be ki samu kici."
Fatyma mik'ewa tayi taja Hannu Laure suka fita Dady da Mamy suna bisa dinning table, Mamy kallon Fatyma tayi
"Ina khadeejar ne naganki ke da laure."
"Mamy tace man bazata ci Abinci ba ta k'oshi shine na tambaye ta metakeso tace man bakomai shine nakeso had'a mata wani abu mai ruwa ruwa nasan kewar su gwagwo take shiyasa tace bazata ci ba."
Mamy kallon Fatyma tayi
''Bata buk'atar komai.?"
"Eh Mammy."
Mammy mik'ewa tayi daga k'ujerar
"Ina zuwa Dadyn Ammar''
Dije ta had'a kanta da gwiwa tana ta sharb'ar kuka tana goge wani wasu na fitowa saboda kewar Inna da Baffah ya fara damun ranta.
Turo kyauren akayi aka shigo ta d'auka Laure bata d'ago Fuska ba muryar Mammy taji.
''My daughter khadeeja meyafaru? da zaki ce bakya cin komai ne."
Goge hawayen Fuskar tayi.
"Na k'oshi ne shiyasa."
"Haba daughter mekikace ki fad'aman dai abinda kike buk'ata ni dakaina zan shiga kitchen na girka miki komai kikeso."
Dije wasa da zobe hannun ta tayi Fuskar tana sadde k'asa
"Ji nake bana buk'atar komai ne bana iyacin komai shiyasa."..
"Shikenan bari nazo."
Dije kallon Mammy tayi har ta fita tana mamakin wannan hallayar ta y'an gidansu Ammar maganar zuci ta fara.
"Kowa nashi yana da matuk'ar kirki da mutunchi Amma shi halin shi ya sha bambam ina iri halin su gareshi."..
Maganar mammy ya katse mata zancen zucin datake.
"Amshi nan madarar ce tayi sanyi nasan zata shiga cikin ki ga kingin nan A firji zuwa anjima sai ki k'ara shan ta kinji.daughter Allah yayi miki Albarka bari naje."
"Nagode".
"Daughter babu godiya tsakani dake ki d'auke ni kamar innar kinji ko na d'auke ki y'ata kada kiji kunyar sanar dani komai kinji ko."
Dije gyad'a kai tayi.
Mammy tana fita
ta k'afa cup d'in madarar a bakin ta wani sanyi da dad'i ya ziyarci kunne ta bata san lokacin da ta shanye ta ganin cup d'in tayi Empty sannan ta aje sa hamdala tayi saboda jin cikin ta yad'an taso.
tashi tayi tanufi toilet ta watsa ma jikin ta ruwa domin ko a kauye bata kwanciya sai tayi wanka sannan.
tana fitowa kuwa atamfar data sa da safe ta maida ta d'ora wata hijabi taganni a cikin kayan da akawo mata cikin wani akwati tana zira hijab d'in ne Laure ta shigo.
"Laure har kungama cin Abinci ne.?''
"Mungama wayyo ni Laure daga yau nagama cin Abincin binni."
Dije kallon ta yi ita Abinci binni zatayi kewa ita da zatayi kewar Baffah da Innah ga Habu data rabu dashi wadda bata tab'a sa ran zata rabu dashi ba kallon zob'en da habu ya bata tayi goge hawayen Fuskar tayi kafin Laure ta lura wadda tuni tayi masauki a gaban madubi tana shafa hoda da janbaki
"Lafiyanki Laure dare ne fa kike ta d'ora hoda jambaki a fuskar ki bacci zakiyi fa"
"Eh kibarni nayi daga yau fa baxan k'arayi ba."
Dije gyad'a kai tayi
"Nidai natafi gurin su gwagwo ki kwana kina kwalliyar."
Laure murgud'a ma ma dije baki tayi ta cigaba da kwalliyar ta.
Dije sallama tayi iske Fatyma tayi cikin su gwagwo suna ta wasa da dariya samun waje tayi ta zauna d'an k'anwar inna ta d'auka tana mishi wasa iyakar ta dasu dasunyi magana tayi musu murmushi kawai ta na saka baki kad'an kad'an tana wasa da yaron hannun ta har yayi bacci ta rungumesa jikinta,
Fatyma sai da safe tayi musu ta fita suna yaba kyakyawan halayyar su kowa nasu ne Anan suka d'ora yi ma Dije nasiha akan rayuwar aure da kuma zama da mijin ta,
Dije tayi shiru tana jinsu kawai Amma zuciyar ta wani bugu kawai taji tanayi, taci burin ma yau cikin su zata kwana ma.
____________________ shigowa tayi iske sa tayi kwance yana bacci kallon sa tayi tare da zama gefen da yake k'ura masa ido tayi "Ina sonka my Ammar Amma dole na juya yadda nakeso domin ba irinmu ake ma hakan ba."
Canza Fuska tayi kamar idon sa biyu kiran sunan sa ta farayi da k'arfi
"Ammar! Ammar!! Ammar!!!"
A hankali ya bud'a idonsa ya dora ga feenah wadda tuni ta canza daga yadda ta shigo.
"My Feena meyafaru ne."
"Tund'azu sai haukan kiranka nake Amma kayi banza dani ka share ko."
Ammar kalar tausayi ya koma "kiyi hakuri queen bacci ne ya kwasheni banji bane kinsan ba yadda zanyi na kyaleki.."
"Kaga ni ba dogon zance na tambayeka ba farfesun kaza nakeso tare da ice cream domin nawa yak'are da shawarmma nakeso naci..."
Ammar zaro ido yayi tare da kallon Agogo 9:15 pm
"My Fee dare yayi fa kinsan kuma yanayin garin yadda yake da 8 tayi kowa ya shige gidan sa fa bare har na fita kiyi hak'uri...."
"Wallahi ban zan hak'ura sai naci abinda na lissafo maka inkuma bazaka siyo ba kana son b'acin raina shi kenan sai ka fad'aman dama ai nason baka kauna ta gobe zan tafiya ta gun Mamy na ka aikoman da takaddar ta tunda bakajin tausayin abinda nake tare dashi Amma kasani dana sa k'afa nabar gidan nan kada kasaran ina tare da cikin ka domin duk hanyar da zan bi na xubda shi sai nabi dama ni ba so nake ba."
"Kiyi hak'uri My feenah bazan iya rayuwa sai dake kece rayuwata ki daina Ambatar zamu rabu da juna kinji matata farin cikin ki shine nawa bari na tashi naje na siyo miki Feenah tab'e baki tayi ta kalli Ammar,
Ammar jallabiyyar sa ya d'auka tare da key d'in motar sa ya fita sai da yayi ma Feenah Kiss a gefen Fuska sannan ya fita ya shiga mota ya fita
Ya hau titi garin yayi shiru sai kace tsakiyar dare ne.
Inda zai wuce akwai y'an sanda da sojoij sai ya nuna id card d'insa sannan ya wuce Amma sai yafad'a musu dalilin da ya fito dashi a haka har yaje ya siyo ma Feenah abubuwan data lissafa masa tana so yana hanyar dawowa ne yazo wani waje mai yawan duhu ne motar sa ta tsaya cak! Ya taka burki Amma taki motsi
Fitowa yayi don ya duba ta yana cikin dubawa ne tare wayar shi da ya kunna torch light yaji motsi kamar wani abu dasauri ya juya baiga kowa ba cikin dakewa ya cigaba da gyarawa yakoma ciki ya zauna Amma shiru taki tashi, fitowa yayi ya k'ara dubawa yana cikin dubawa motsi yaji dasauri ya juya wasa k'arti yagani su 3 d'aya ya d'ora mashi bindiga a bisa kai............
_πwayyo Ammar komai zai faru dashi ne kubiyoni next page nak'asa cigaba typing saboda tausayim Ammar_
_*AMATALLAH*_πΉ
[11/3, 10:53 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA ???π·_*
_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_*39&40*_
"Kud'i ko rayuwar ka."
Ammar Add'ua ya cigaba dayi juyowa ya kallesu
"Ban fito da kud'i ba saboda dare ne yanz..
naushi yaji da bakin sa kafin ya ida
"Kafin son ka Mutu kenan da kud'in da muke buk'ata wajenka."
Ammar Add'ua kowacce tazo mishi yake cikin ranshi domin koda ATM card d'inshi bai fito kud'in da yafito dasu basu wuce 5k ba kuma yayi ma Feenah siyayya dasu N500 kawai ya rage,
Wani bugu ya sake ji a tsakiyar bayansa babu zato ko tsammani ya sake jin wani,
"Boss naga Alamun fa zai yi mana gardama."
"Kai da Bosho ku shiga motar sa kuga Abinda ke cikin ta ne kufito dashi.."
"Angama Boss."
Haka suka nufi motar Akabar Boss da Ammar, Boss ya k'afe Ammar da bindiga wadda Ammar ke kwance k'asa a sanadiyyar naushin da sukayi masa,
"Boss babu komai a motar sai wannan ledar dake ciki."
Mik'o mishi ledar yayi
"Shagali zakaje kayi meyasa baka fito da kud'i irin wannan lokacin ba ne ka fanshi Lafiyar ka da ranka bane ban zamu kyaleka hakanan ba sannan zamu tafi da motar sannan muyi maka hukunci da b'ata mana lokaci da kayi"
Ammar bud'a idonsa yayi
dayake masa matuk'ar nauyi kafin ya ida bud'esa yayi magana naushin wani k'aton abu yayi bisa tsakiyar bayansa kan ya ankare ya k'ara jin wani wani duhu ya gani ya gifta masa a ido wajen yana juya mashi fad'uwa yayi sumame Amma duk da hakan su Boss da Bosho basu kyale Ammar ba sai da yimasa lis jikinshi ko ina yana fidda jini sannan suka kyalesa tsakiyar titi,
Motar Ammar suka nufa suka shiga suna jin dadi domin motar ba k'aramar mota ce ba da anja mata fenti da number ba k'ananan kud'i zasu ba da suna mata kallon k'arama ce ashe babba ce sun sa key motar taki tashi, sai ma wata tsuwwa! da wata danja ta dinga yi nanfa suka rasa yadda zasuyi mata gashi taki mutuwa
"Boss kanajin wata tsuwwa datakeyi gashi kuma taki tashi fa."
Naushi Boss d'in yakai mata motar aikam ya danno wani danja nan ta cika musu murya dasauri suka fito Amma har suka fito bata daina tsuwwar ba.!!
Hasken mota suka hanga Bosho idonsa yakai dasauri ya juyo gun Boss cikin sauri "boss gafa wata mota nan tafe kuma ina zaton ma'aikata ne fa ciki....
"Kai wannan kamar moto d'in Ammar kou."
"Sir nima naga kamar ita ta wananan Aminin naka kou?"
Gyad'a masa kai tare da cewa "matsa sosai muga."
Kashe motar sukayi Ya fito rike da bindingar sa yar k'arama dake hannun sa gudun matsala.
"Boss Sojoji kuma rik'e da Bindingar sa yake."
Bosho muje kar mu kwana ciki bamu tsira da komai ba kuma akamamu shikenan."
dagudu suka yanki daji domin dama bindingar tasu babu bullet cikin ta suna tsorata mutane da ita su kwace dukiya gurin su,
Motsi sukaji dasauri ya waiga tare da tun karo inda motar Ammar take yana waige waige shida wadda suke tafe.
Jiyayi ya taka wani abu dasauri ya juyo Ammar ya gani kwance cikin jini babu Alamun Numfashi tare dashi dasauri ya juyo gunsa Ammar!!!
Baki d'aya dajin ya Amsa
"Ammar meyafaru dakai ne hakan wayayi maka hakan dasauri ya janyo sa jikinsa yaron sa wadda suke tare dashi kuwa.."yallab'ai muje asibiti.."
"muhusin muje muje kar narasa Aminina muje..."
Wadda aka kira da muhusin dasauri ya maida murfin motar Ammar wadda ke bud'e yayi suka nufi motar sa
"Yallabai kabani nayi tuk'in nan ka koma baya ka kwantar da hankalinka.
Baya ya koma ya kwantar da Ammar bisa jikinsh..
Wata asibiti suka nufa _*MUNNERA HOSPITAL*_
wadda akeji da ita a cikin garin lagos saboda masu hannu da shuni ke ma'aikata gwammanti ke zuwan ta suna tsayawa ya shiga daga ciki bada jimawa ya fito tare wani ma'ikacin asibitin tare da abin d'aukar marar lafiya...akasa sa Ammar ciki aka nufi Emergency room dashi shima ciki ya afka nan aka rufo kan Ammar yana tsaye ya dafe kanshi idanuwan nasa sunyi masa jawur jijiyon kansa sun tashi
Wani doctor ne ya juyo wajen sa tare da dafa kafad'ar sa yace
"Sorry My friend..........
_Waye wannan ne kuke tunani da yatada hankalinsa akan Ammar_? _ne wane hali Ammar yake ciki ne ya Feena zataji ne in taji abinda ya samu Ammar ne_
_Muhad'e next page idona ke ciwo shiyasa banyi da yawa Amma next page zaizo muku da yawa har naje muku gun....π_
_*AMATALLAH*_πΉ
_*FOR COMMENT ONLY*_ππ»
_*08084766569*_
[11/3, 10:53 AM] ππ: _*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERSπππ*_
_We dont just entertain and educate, but we also touch the heart of readers_
π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
*_41&42_*
"Sorry My Friend ka kwantar da hankalinka kabar dai ba soja nake gani ba yayi wannan rikecewar hakan"
Juyo da idanuwansa yayi wadda basu koma daidai ba sunyi ja.
"Bakasan yadda nake jinsa a raina ne ba kasan yadda muke ba shiyasa komai zan iya yi akan Ammar yanzu wane hali yake ciki ne?"
"Ka kwantar da hankalinka yanzu zamu bashi hutu kamar zuwa gobe da safe mugani yanzu duk wani taimakon da ya kamata a bashi anyi masa yanzu zaka tafi domin munada maa'ikatan da zasu kula dashi ne."
''Yanzu kana nufin natafi nabarshi shi d'aya?"
"Eh karka samu damuwa da hakan muna maa'ikatan dake duba patient sosai."
Gaban gadon da Ammar yake ya nufa yana bacci ga duk bandeji d'aure da kanshi da hannun sa har bayan sa.
"Allah ya baka lafiya Amini na Allah ya kawoni lagos sanadiyyar naga halin dakake ciki suwaye sukayi maka hakan Amini su waye suke k'okarin kashe kane."
"Yanzu bashi da bakin yi maka magana in har ba farkawa yayi ba."....
Zarya take tsakiyar d'aki waya rike da hannun ta "Ammar ya matuk'ar raina man hankali me yakeyi a waje har wannan lokacin bai kawo man abinda na buk'ata bane."
"Yana can yasamu wata a waje ya barki anan ke tunda baza ki iya biya mishi buk'atar sa ba''
Wani irin zabura tayi
"K'arya ne wallahi Ammar bazai aikata hakan ba haka ta jawo wayar shi yaki picking zuciyar ta dinga yi mata sake sake kala kala daga waccen sai waccen.
Wayar ta k'ara d'aukowa ta k'ara kira...
______yana shiga mota yaga wayar Ammar wada ya d'auko yashe bisa titi tana bada haske d'auka yayi yaga suna *MY QUEEN* yana yawo bisa screen d'in picking yayi ya ganka a kunnesa tun kafin yayi magana ya fara jin Amon muryar ta.
"Ammar wannan wane irin wulak'anci ne kasan ina buk'ace da wannan abu shine zaka tafi kayi zamanka ne har da ceman dare yayi bazaka je ba salon kuma wani iskaci da raina ni dakayi ne..."
Tsawar da aka dakata mata ne yasa bata ida zance dake bakin ta ba har ta d'auke wayar daka kunnen ta maganar wadda taji yasa maida wayar a kunne.
"Haka dama kike mashi ba shakka sanadiyyar ki ne Ammar ya fito ya had'u da wannan Abu kenan ina zargin ki may be ke kisa ayi masa wannan abu ko to wallahi Ammar ya mutu sai nayi shari'a dake yanzu yana kwance farfadowar sa kawai nake jira naji wadda ya aikata hakan garesa..."
Kit!! Ya kashe wayar saboda shi dama tun farko kwata kwata feena tun a school batayi masa har saboda rashin tarbiyyar ta da kuma wadda take tarraya dasu yayi mamakin da yadda Ammar ya rud'e akan Feenah wadda yadaga cikin wadda suka tsane ta Amma lokaci d'aya yake mata wata Azabbatar soyaya da ya mutu akanta ya rikece,
Wai kusan kowaye wannan nasan wasu sungane wasu basu gane ba, to *ALIYU HAIDAR* kenan Aminin Ammar wadda dawowar su daga karatu, yayi jarrabawa aikin soja dama shi yana matuk'ar son aikin a ranshi in da yayi nasara ya haye ga kuma wajen training ya haye, ya fito kuma babban soja saboda matsayin karatunsa da kuma takaddunsa da sukayi kyau sosai, saboda shi da Ammar basu da wannan shashanci nak'in karatu suna maida hankali sosai akan karatu,abinda yakai su shi suke Land Army ne aiki ya kawo su lagos suna takon wasu masu safaran hodar iblis ne kuma suna rayuwa a wani daji ne shine jagoran tafiya shine Babba cikinsu, ya biyo hanyar zasuje hotel d'in da aka sauke su ya had'u da Ammar...
"Hello Haidar don Allah kafad'aman wane hali Ammar yake yanzu don Allah Haidar.."
Shiru dataji yasa ta sauko wayar daga kunne ta mik'ewa tayi daga zaunen datake
"Nashiga Uku meyafaru da Ammar wane hali yake ciki ne yanzu yana ina nasan kona kira wannan mai baudad'en hali baya kulani."
Ko can Feena na shakkar Haidar saboda bataganin Fuskar rainashi ba dama Haidar irin wad'ad'an mazan ne miskilai ba kasafai ake ganin dariyar su ba,
"Wayyo ni nafeesa don Allah Ammar kada ka mutu ina sonka wallahi babu namiji dana keso kamar ka a raina ina kake ne haka ta dinga kuka tsakiyar palour wani zazzabi ya sauko mata,
_Na munafurci ba Amma ba inji ni ba inji fans Saboda ni Feenah ta hannu dama ce Lol_
_Wanene Ammar?_
_Ammar dogo ne ba sosai bai da k'iba siriri kuma ba kamar kara ba lol da kin kallesa zakiga yana yanayi da mutanen sudan ko fulani yana da yalwattaciyyar suma ba karfafa bane ga sajensa yana da manya ido masu razana y'an mata da siririn hanci ziir ga gashi yalwace a fadadan kirjinsa ba kodayaushe Zakaga dariyarsa ba sai dai murmushi afuskarshi Fans Ammar dai Handsome guy ne yana da matuk'ar kyawu masha Allah_
_Ammar shine na farko gun mahaifyar sa Mamy (naja'atu) da Dady (Kabeer)_
_Yana da kanne biyu Aysha da fatyma inda Aysha ke auren wani d'an Friend d'in Dady tana da y'ay'a biyu,Samha da_ _Yazeed_
_Fatyma kuma tana karatu a Bayero university tana 300level_
_Daddy yana da arziki Amma ba irin wannan mashahurin arziki nan ba d'an kasuwa ne sosai yana zuwa k'ashashen duniya yana saro kayayaki kamar su zanen gado dogayen riguna takalma kayan yara hadda na manya da gyaluluwa yana kawo wa Nigeria inda yana da shaguna manya manya kamar gudu hud'u ya zuba yara duk a cikin su_
_Daddy mutum ne wadda kowa nashi ne yana da matuk'ar son taimaka na kasa dashi yana da taimakon talakawa sosai da sosai iya karfin sa yadda Allah ya bashi shiyasa yake taimakon kauyensu sosai_
_Ammar iyayensu sunyi masa tarbiyya sosai ba taso yaro sangarttace ba yanada ilimin Addnin daidai gwagwardo yasan littafai da dama, yayi karatunsa daga nursery primary zuwa secondary school d'insa a private school abotar su da Haidar tun a primary school inda yana primary 5 aka kawo haidar school d' insu kuma basu da nisa wajen gidajen su daganan abotar su ta d'ore_,
_Sunyi degree d'insu a Bayero university kano inda suka had'a masters d'in su a England_
_Ammar tun yana yaro in sukaje kauye yana da kyakyanmi ya'n kauye yana mak'ale wajen Mamy baya ko shan ruwan gidan Mamy tana d'auka yarinta ce zai daina in ya girma Amma har ya fara girma ba daina ba yana kyamatar su yana d'aukar su wasu mutane dabam k'azamai ne_
_Gashi an had'asa aure_ _da dije kuma y'ar kauye ko ya zasu kaya ne zai daina kyamatar yan kauye yana ce musu k'azamai_
_Domin Ammar d'an gayu ne bayason_ _k'azanta ko kad'an ko lokacin da yake school ba kowace mace yake kulawa a_ _department d'insu ba_ _sai yaga kin waye sosai_ _sannan zaku dinga_ _gaisawa dashi_
_Ga Dije y'ar kauye yaza'a kaya ne??_
_Muje zuwa_
_Around 11:Am_
"Dije Aure bauta ne na ubangiji ki rike Auren ki ibada ne kinji ko ki kasance mai tsoron Allah ko da yaushe ki tuna da zaki mutu komai kikayi Allah zai tambayeki ki rike auren ki hannu biyu biyu Aljannar ki tana k'ark'ashin kafar mijinki
In kuma kinyi dakyau zaki gani Allah baku zaman lafiya."
Dije kuka kawai take har kanta yana mata ciwo mik'ewar Inna da gwagwo yasa ta fashewa da wani kuka wadda zai kai su kauye yazo,
Laure da gudu ta shigo rungume juna sukayi tare da fashewa da wani kuka kowa na gurin sai da yaji tausayin su......
_Koni dake dauko muku rahoto sun bani tausayi π€ayi hakuri da wannan sai nadawo daidai daga tausayin su Dije_π
_*AMATALLAH*_πΉ
[11/3, 10:53 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_*43&44*_
_Ina k'aunarki fisabillahi Billyn Abdul Allah kara baseera da hazakaπ_
"Kuyi hak'uri kunji rabuwa ba mutuwa bace kuna tare da juna."
Laure tashi tayi daga jikin Dije tana goge hawayenta suka fita harabar gidan inda Mota zata d'auke su zuwa gida su Inna da gwagwo suka shiga Laure da dije ne manne da Juna laure kallon Su gwagwo tayi
"Don Allah zan fad'ama Dije wata magana gwagwo ku jiramu."
"Laure wace irin magana ce wadda bakuyi ba sai yanzu."
"Gwagwo yanzu zamu gama."
Laure jan Hannun Dije tayi suka koma can in da baza gansu ba
"Dije Duk kan tsanani yana tare da sauki kuma duk bawan da bai had'a Allah da wani ba ya dace don haka kiyi biyayya ga Yaya Ammar duk irin abinda zai nuna miki karki nuna gazawar ki ga abun ki daure kiyi masa abinda zaki rike Add'ua domin itace takobin mumuni duk rintsi duk wuya karki sake da Add'ua insha Allah ba zaki wulakanta A duniya ba wannan tsinanar matar tasa kuwa ki cigaba da Add'ua Allah tsare ki daga kaidin ta karki saka damuwa a ranki don Allah dije kije ki shiga wani hali don Allah Aminiyata."
"Nagode Aminiya ta zanyi Amfani ga duk abinda kikace man Allah k'addara saduwar mu Laure ki gaidaman Baffah na da inna ta kice zanyi kewar su matuk'a."
Laure rike Hannun dije tayi can kuma ta saki tana tafiya tana mata bye bye dasauri Dije ta nufi Laure ta riko hannun ta wajen rikon hannun ta ne D'an hannun laure ya fad'i kasa. Dije durkusawa tayi k'asa ta d'auka zata ba Laure Amma tana d'agowa taga laure har tabar gurin damke sa tayi a hannun ta cikin sauri ta dawo gun motar su gwagwo taga har laure ta shige mota, ta fiddo kanta ta window d'in motar tana d'aga ma Dije Hannu.
Dije kasa d'aga mata tayi tayi tsaye kamar icce har motar su gwagwo ta fice daga Gate d'in Sai sannan Dije ta zube nan kasa tare da fashewa da wani matsanancin kuka
"Wayyo Baffana wayyo Inna ta wayyo Aminiya ta Laure ku dawo ku tafi dani gida don Allah kada ku barni a nan ku dawo ku tafi dani gida bana zama a nan Baffah na inna ta."
Mammy ce ta nufo gunta, mik'ar da ita tayi daga zubewar datayi k'asa tare rungume ta a jikinta kawai ta nufi cikin gida da ita sannan fatyma da Daddy suka biyo bayanta cike da tausayim Dije...
Mammy zaunar da Dije tayi bisa k'ujerar cikin palour tare da zama Kusa da ita
"Haba my daughter kamar dai baki d'auke mu iyaye ba da zaki dinga kuka kidaina damuwa Kinji Aure babu inda bai kai d'iya mace kuma insha Allah bazaki kukan rashin Inna da Baffanki ba kinji Daughter na takaina."...
Haka Mamy ta dinga rarrashin dije shima Daddy ya d'ora da nashi rarrashin gurin Dije
"Khadeeja zo mu shiga ciki na gwada miki wani abu Fatyma jan hannu Dije suka nufi d'akin ta..
Dady kallon Mammy yayi mamyn su fatyma d'auko min wayata d'aki na kira Ammar..
"To Dadyn Ammar."
D'aki ta nufa don d'auko masa wayar..
______________________ A hankali ya fara bud'a idon sa jin kansa yayi masa nauyi yaji maida idon yayi ya rufe Amma yana motsi da kafar sa,
Haidar dake zaune bisa kujera idonsa yakai da motsin da Ammar yake da sauri ya mik'e ya nufi wajen gadon,
"Ammar kafarka ne bari naje nakira doctor ya dubaka''
Dasauri Haidar ya nufi office d'in Doctor tare suka dawo duba Ammar yayi yaga babu wata matsala sai sai rauninka da jikinsa yayi kuma zuwa Anjima zasu k'ara duba gurin rauninka.
Bayani yayi ma haidar
"Yanzu ruwan zafi kawai za'a bashi yasha zai sha wani magani ne yanzu."
"Ok doctor thank you bari naje na had'o masa."
Haidar kallon Ammar yayi
"Ammar bari naje naso maka ruwan zafi kou?"
Ammar gyad'a kansa yayi tare da yimasa murmurshi
Haidar fita yayi ya shiga motar yayi ya fita baiyi nisa ba yaga gurin da ake siyar da ruwan zafi ya gani parking ya gyara