Share this page
gagareta tagumi ta buga ''yanzu Mijina ina karkashin ikon sa Allah yasa kada Daddy yace kada na bishi lagos d'i nan. Ammar samun kujera yayi ya zauna d'aukar remote yayi yana canza tasha Amma surar Dije sai yawo take masa cikin idanuwa firji ya tashi ya bud'e robar swan water ya shiga bama cikin sa wayar sa yazaro number Feena ya danno. (Ita da yakamata takirasa shi zai kirata) "Hello Queen." My Ammar nad'auka tunda kaje kano zaka manta da Queen d'inka" "Haba Queen ta yaya zan manta dake kenan zan iya mantawa da kaina Queen." "nasan ko ance kada ka kikarani ." Yanzu kinsamo house girl d'in da zata tayaki zama ne?" "Nasamo Amma ni Girkin ta bayayi man taste kamar naka yanzu ta yiman Ferfesun kifi Amma ba kamar naka ba." Karki damu Queen jibi kamar yanzu muna tare da juna zan miki girki." "Ya Alk'awarin da kayiman ina fatan baka kula ko wace mace ba My Ammar." "Queen ni nayi miki Alk'awari ta yaya zan karya miki shi karki damu babu macen da zan kula har nadawo lagos." "Ok Nagaji anjima ka kirani."d'it ta kashe wayar Ammar bin wayar yayi da kallo Murmushi yayi jin Queen d'in sa tana Lafiya kuma yayi waya da ita lafiya lau... K'ara zama yayi bisa kujera Ya tafi wani tunani tuni ya manta da Al'amarin Dije tunda yayi waya da Fenna Queen d'insa "Lah! Mammy yaya Ammar yazo." Waya fad'a miki hakan kefa kin cika shirme." Zumb'ure baki tayi "Malam Garbati ne yasanar dani yanzu." Wuce Mammy tayi dasauri ta tunkari cikin palour iske Ammar tayi yana kallo wata k'ara tasaki yaya Ammar dasauri ta nufi gunsa ta mak'alkalesa "Yaya Ammar Ashe dagaske kaine kazo.'' "Autar Mammy haryanzu baki girma ba tamkar babyn goyo kike ko." Zumb'ure baki tayi "yaya Ammar don nayi murnar zuwan ka shiyasa zakace hakan ko."mik'ewa tayi zata tatafi dasauri ya rik'ota "Sorry Auta ina Mammy ne?" "Gatanan zata shigo" Mammy ce keshigowa canza Fuska tayi ko kallon inda Ammar yake batayi zata shige ciki "Mammy bakiga ya Ammar ba?" Naganshi wani abu ne?" Cike da Mamaki Ammar da Fatyma suka bi Mammyn tasu da kallo Ammar bud'a baki yayi "Mammy ina yini mun sameku laf....." D'aga Mishi Hannu tayi ta dak'atar dashi Rik'e gaisuwar ka bana buk'ata ba ita nake jira inada y'ay'an da suke gaisheni a kullum don haka bana jiran taka." Wuce shi tayi gwiwa sake ya koma ya zauna Kallon Fatyma yayi ''Fatyma me akayi ma Mammy ne take fushi dani ne hakan?'' "Yaya nasan bai wuce jimawar da kayi baka zoba Yaya Ammar Daddy ka kusan 7Months rabon ka dakazo Dole Mammy tayi fushi Amma nasan zata sauko." "Jeki gyaraman d'akin nawa na d'an kwanta.". "To Ya kusan kullum cikin gyara yake sai nad'an kara sharewa maka bari naje." ________Mammy tana shiga d'aki zama tayi bakin gado taji dadin zuwan Ammar kenan yanajin maganar mahaifinsa haryanzu Amma dole ta nuna mashi kuskurensa a matsayin su iyayen shi. Tashi tayi ta nufi d'akin Dije don tagano yadda take,iske ta tayi kundudene Cikin Blankent tana rawan jiki taba jikin tayi taji da wani irin zafi rau! Khadeeja!! Khadeeja!! Amma babu Alamun zata Amsa dasauri mammy ta fito Fatyma fatyma.!!dasauri tafito Mammy lafiya fiddo Mota mutafi asibiti Khadeeja batada lafiya." Dasauri Fatyma zata nufi waje cin karo sukayi da Ammar "Lafiya Auta." "Khadeeja ke bata lafiya zan fiddo mota mutafi asibiti."bata jira Amsae sa ba tanufi waje Ammar kuwa shiga ciki yayi iske Mamy tayi ta tallabo khadeeja a jikinta ta d'ora ta kafad'ar ta.Bai jira mamy tayi masa magana amsar ta yayi kamar Baby doll ya nufi waje lokacin har Fatyma ta bude kofa sata yayi baya Mammy shiga tayi ta tallabota jikinta "Bani key d'in" Fatyma mik'a masa tayi ya shiga sannan ta shiga Malam garbati tuni ya bud'a gate a dagudu suka fita zuwa asibiti......✍🏻 _Ina cikin wata damuwa kutayani da Addu'a Allah yayeman don Allah_😭 _*AMATALLAH🌹*_ [11/3, 10:55 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??🔷_* _*BY AUNTY* *HAFSY*💕_ ( _*INDON KAUYE*_) _*60&61*_ _*ALHAMDULLAH MASHA ALLAH KAINE ABIN GODIYA DARE DA RANA MASOYA DA BAZARKU CE NAKE TAKA RAWA IN BABU KU BABU TAKA RAWA FARIN CIKI NA BAI BOYUWA IRIN YADDA NAGA KUNA MATUKAR K'AUNAR WANNAN LITTAFIN NAWA 👆🏻NAGODE SOSAI DA ADD'UAR KU GARENI NAJI SAUKI ALHAMDULLAH, ONE LOVE❤ MY PEOPLE*_💋 "Dad.y.".. Dady ko kallon inda Ammar yake baiyi ba ya wuce zuwa cikin d'akin "Doctor ya jikin nata" Normal Alhaji zuwa anjima da drip d'in ya k'are zamu sallame ta." Daddy kallon Dije yayi "Sannu Khadeeja." "Yauwa Daddy." Naja'atu meyafaru da ita Khadeejar ne?" "Dadyn Ammar wallahi ban san meyafaru ba mun dawo ne ina shiga d'akin naganta hakan," Daddy ajiyar numfashi yayi waiwaya yayi inda Ammar yake yaga bayanan maido idon sa yayi ga Mammy "Yaushe Ammar yazo ne?" Nadawo na iske sa a cikin gida bansan time d'in da yadawo tunda banyi wata magana dashi sai shi da fatyma kawai." Daddy aje numfashi yayi yana mamakin yadda Ammar ya Amsa kiransa ya d'auka bazai zo ba sai gashi yazo, Doctor Hafeez fita yayi daga Mammy sai Dady sai Fatyma dake kusa da gadon Dije wadda wani bacci ne mai nauyi ya d'auke ta tun shigowar Daddy d'akin bada jimawa ba, Ammar yana fitowa kuma fitowa yayi ya had'a kanshi da mota yafara maganar zuci. "Meke Faruwa ne Daddy da Mammy ke Fushi dani hakan babu inda nasamu sakakiyar fuska sai gun Fatyma to menayi musu me? wai wannan wacece da su Mammy suka rud'e da rashin lafiyar ta naso na tuna inda nason Fuskar kai ba itace ba ta yaya wannan Village girl d'in zatazo wajen su Daddy ma gaskiya ba itace ba Amma kafin nakoma zan tambayi fatyma naji wacece wannan wadda da duk Alamu su Daddy sunaji da ita hakan" Tuno lokacin da ya d'auko ta yayi da lokacin daza shiga da ita Emergency room yadda yaga gashin ta yalwatacen har a baya yadda yakasa samun natsuwa har ya rufe mata shi, da kuma lokacin da dr Hafeez keyi mata Magana k'asa k'asa kamar wani saurayi da budurwa wani dogon tsaki yaja wadda baisan lokacin da yasakeshi bs hango Dr Hafeez yayi yana tafowa wajen shi dasauri ya juya yabar wajen saboda haushin sa da yakeji. "Kai mundade muna bacci fa." Khairi kallon Feena tayi yadda tadage tana d'irkar bacci mik'a Khairi tayi babu salati babu komai kallon Agogo tayi taga har 6 tayi dundu takaima Feena dasauri ta watsar cikin muryar maye wadda bai ida sakin ta ba ta kalli Khairi. "Khairi wane Irin iskaci ne wannan ina bacci na mai nishad'i da dad'i zaki tadani kin san bana son haka fa."..tsaki taja zata koma ta kwanta wani bacci Khairi ta kalle ta inaga baki da ra'ayin cire wannan k'adagagen abin dake gabanki shiyasa zaki ce haka shikenan bari na tashi naje ni." Wani wantsar Feena tayi tare da murje idon ta." "Ohh namanta Khairi yanzu yaza'ayi ne ?'' tashi zakiyi.muje kinsan yanayi garin lagos da dare ya fara kowa zai shige gidansa in baka da gida hotel, in bahaka ayi cininka nan take ko a sassare ka nan take ko babu mai taimakon ki." "Ok bari naje na d'an watsa ruwa." Khairi kallon Feena tayi tare da sakin wata Hamma "Nifa yunwa nakeji Feena." "Ok bari nasa wannan yarinyar ta girka miki Feena d'akin da taba yarinyar data d'auko gidan Mama talatu tana shiga ta iske ta zaune tayi shiru tana ganin Feena ta mik'e domin ita har ga Allah awanni da tayi da Feena tsoron ta take, "Ke kitashi kishiga kitchen ki dafamana indomie had'e da kifin gongoni." "To Aunty." Haka Feena ta juya ta shiga d'akin ta kewaye kawai ta nufa ta watsa ruwa alwallah ta d'oro ta d'ora sallar azhar da la'asar lokaci guda yar parking sai yawa ba lada haka feena ta dungugurata ta mik'e ta nufi wadrope d'in ta wata buba ta wata shadda blue tasa kallon kanta a madubi tayi tsaki taja. "Sai yanzu da khairi ta fahimtar dani nakejin tsanar wannan ciki don Allah ji yadda ya maidani duk ya b'ata min make up da nayi wallahi dole na cire wannan cikin dake jikina." Wani yalolon mayafi pink Feena ta d'auka tasa tare saka wasu flat d'in shoes pink yar purse ta d'auko ta nufi d'akin Ammar ta d'ebo kud'i wadda zasu isheta komai ta fito ta iske Khairi bisa kujera tana sakin hamma "Khairi nagama tashi muje." Wani kallo ta watsa mata "Cikin nawa bai Amshi abinci bane zakice natashi muje kodai baki sanar da ita bane" "Kutuma kina nufi bakici indomie d'in danasa a girka miki ba tund'azu"... Feena ta bud'a baki zatayi magana saiga ta tashigo ta tire jere a hannun ta. "Uban me ya tsaidaki har tsawon wannan time d'in ne?" "Aunty kiyi hak'uri ...." Shut up b'ace min da gani badon Mijina bai nan ai bazan kawo ki gidana ba amma zuwa jibi kibar shi ai idiot get out." Jikinta yana kyarma ta aje bisa dinning table tabar gun. Haka sukaci indomie d'in suka sukayi kat suka bar komai watse suka nufi hospital d'in daza'a cire ma Feena ciki... _________________Doctor Hafeez ya shigo yaga drip d'in da akasa ma Dije ya k'are ya duba yaga komai lafiya lau takaddar sallama ya basu tare da rubuta masu wasu magani dazatayi Amfani dasu ta k'arajin karfin jikinta. Daddy godiya yayi ma Doctor Hafeez Sukayi sallama, Mammy ce ta rik'o hannun Dije suka fito harabar Asibitin Dady yayi mamakin ganin Ammar acikin mota Amma bai nuna suka nufi motar Daddy suka shiga basuyi mashi magana ba Ammar shima tada wadda yazo da ita yayi yabi bayansu da Daddy. Bayansu isa gida ne maigadi ya bud'e musu gate suka shiga Haka Mammy tasake riko hannu Khadeeja har suka isa palour ta zaunar da ita "Sannu kinji Khadeeja mekike buk'ata yanxu nashiga kitchen dakaina nayi miki." Daddy dariya yayi "Naja'atu na lura kinaji da wannan y'a taki sosai ko" "Daddyn Ammar kenan inkaji so d'aya kenan da yawa har ba adadi." Suna cikin raha ne Ammar ya shigo Mammy canxa fuska tayi Ammar gaban Dady ya durkusa ya bud'a baki zaiyi magana cikin wata murya ............ _*ҚŨŇŜĂŇ ĂбĨŇҚĂ ĎĂ MĂŘĂŘ ĹĂҒĨŶĂ бĂŇ ĎĂŴÕ ĎĂĨĎĂĨ бĂŇÊ ŜĤĨŶĂŜĂ ҚŨ ҚĂĜĂŇŜĂ ҚĂĎĂŇ ĂMMĂ ĨŇĂĜĂ ĈÕMMÊŇŤ ŜÕŜĂĨ ŽĂŇŶĨ ŴĂŇĨ PÕŜŤ ĎĨŇ ĈĨҚĨŇ ĹÕҚĂĈĨ*_🤷🏻‍♀ *_ĂMĂŤĂĹĹĂĤ_*📕✍🏻 [11/3, 10:55 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??🔷_* _*BY AUNTY* *HAFSY*💕_ ( _*INDON KAUYE*_) _*MY BEAUTY KINYI MATUK'AR KOKARI PAGE D'IN YAYI SWEET SOSAI ALLAH BAR KAUNAR TSAKANINA DAKE KINA KAUNAR MATA KO BAIWA💯 ONE LOVE DEAR*_💕💋 _Ma'u halliru (granny)_ _Na'ima gazobi_ _Zainab Abdurahaman_ _(Hausa novel)_ _Aysha bakari_ _Aunty halilos fans_ _Khadija_ _Aunty halillos fans_) _Rahama Almustapha_ _PML FANS_) Maman twins _TABITAL PULAAKU_ _Dije tana gaidaku sakonku yana zuwa gareta_💕 _*56&57*_ Ammar tuki yake Amma Mammy cikin fushi tafara magana "Wannan tukin da kake fa kada yarinyar mutane ta mutu inkasan bazaka iya tukin ba kafito kabani na tuka." "Mammy inayi gudu da yawa in aka had'u da accident fa kinga anyi biyu babu kenan." Inkana k'ara gudu kakara kada yarinya mutane ta mutu." Wace asibiti zamu nufa?" Wace asibiti kasan muna da file can cikin fad'a Mammy ta ida yima Ammara magana. "Sorry Mammy." Ammar k'ara gudun Motar yayi ganin yadda Mammy take cikin fushi ya nufi Asibitin da suke da File Ameema Hospital,tun kafin su ida shiga Fatyma takira Doctor Hafeez ta sanar dashi suna tare da marar Lafiya suna shiga gate d'in aka turo wheel chair Ammar d'aukar Dije yayi yasakata a ciki ganin kallabin ta yayi ya cire gashin kanta ya bazu bisa kafad'a wani abu yaji ya d'arsu cikin ransa da bai san ko meye dasauri ya dakatar da nurse d'in dake kokarin tura Dije fatyma ya kalla "Bani hular bisa kanki." Fatyma cirowa tayi ta mik'a masa sa ma Dije yayi tare cunkusa gashin ta ciki nurse d'in binsa da kallon mamaki sukayi suna maganar zuciya "Lalai wannan mijin nata ya cika kishi tana kwance bata numfashi sai ya b'oye gashin ta. Haka aka tura Dije aka nufi Emergency room da ita. Su mammy da fatyma kuwa kujerar doguwa dake kusada Emergency room d'in suka zauna Ammar fitowa motar ya shiga ya zauna jinsa yake a wani yanayi marar dadi rigar sa ya sunsuna lumshe idon sa yayi jin wani k'amshi turare da yake samun kansa yayi da k'ara sinsina rigar. "Meke damun na hakan ne nasan babu wata mace danake son kasancewa da ita kamar my queen,Amma zuciya ta tana karanto surar yarinya da bansan ko wacece ita ba." Tsaki ya buga tare da saurin kawar da zance daga zuciyar sa kiran Feenah ya shigo cikin wayar sa hannunsa yana kyarma ya d'auka tare kangawa a kunnen sa. "Hello Queen." Kana dai lafiya ko babu wani matsala?" Lafiya lau Queen sai duk ban lafiya sabod...." Me?"" "Baki kusadani Queen." "To tunda ka matsa sai kaje kano ba gatanan katafi ba kun had'u da Dadyn naka?" "A'aa ina Hospital ma yanzu haka nida su Mammy." Kace man kana lafiya waye hospital ne dazakace ka zauna ko Mammy ke batada lafiya ne?" Nooo..ko d'aya nakawo Mammy ganin wata k'awar ta ke bata da lafiya." (Samun kansa yayi dayi mata k'arya hakan). "Ok My Ammar ina fatan dai kana sane da Alk'awari da kayiman nakin kula kowace mace har daworka lagos wannan shine dalilin kiranka da nayi don nakara tunatar dakai domin kuwa Kai Mijin mace d'aya Kit yaji ta kashe wayar bin wayar yayi da kallo Yanajin takaichi abinda Feena take masa Amma kwata kwata ya gaza Furtawa saboda wani kwarjini datake masa gashi yana matuk'ar gudun b'acin ranta ko yayane bayason yaga yanayin Fuskar ta ya canza. _______ tashi tayi daga kwanciyar datayi zaune tsaki taja ''Meke damu na ne tun tafiyar Ammar kano naji baki d'aya yanayi na ya canza tamkar wani Al'amari na shirin faruwa dani nakasa samun natsuwa a tatttare dani nakanji gabana ya fad'uwa wani kishi yana kamani tamkar My Ammar na tare da wata mace ne wannan shine dalilin da yasa nake kiranshi kuma ya tabbatar man da babu wata mace da yake tare da ita, in akwai fa?'' Wata zuciyar ta fad'a mata hakan zumbur ta mik'e daga zaunen da ta ke "wallahi karya babu wata mace da isa ta mallaki Ammar da yawuce ni Nafeesa taheer Bushasha nice tashi ni kad'ai." Tana wannan surutun ne Wadda ta d'auko daga gidan Mama talatu ta shigo Feena wurga mata kallo tayi "Lafiya?" Cikin ta ya kama kyarma awwani da tayi da ita tsoron ta takej "dam..damm.wata ce a palour tace nayi miki magana tanason ganinki ne." "Wacece?" "Bata fad'aman ba." "Ok Muje kin isheni da wari cikin d'aki." Waje suka fita wadda tagani yasata sakin wata tsuwaw! Khairi!!" Rungume juna sukayi suna murnar ganin junan su. ___________ "Sannu Kijin Khadija hakan kikace jikin baiyi tsanani ba." Dije shiru tayi Fatyma ce ta matso kusada gadon da Dije take "sannu Khadija yanzu mekekije ne?'' "Banajin komai yanzu." Mammy mik'ewa tayi bari naje Gun doctor d'in Fatyma zauna naje gurinsa na dawo." "Tam Mammy." Mammy tana fitowa ta hango Ammar yana waige waige batayi masa magana ba zata wuce Can Ammar yaga Mammy. "Mammy." Batayi masa magana binta yayi har office d'in Doctor Hafeez yana zaune yana rubuce rubuce sallama tayi sannan ta shiga Ammar shima sallama yayi nuna ma su kujera yayi suka zauna, Doctor Hafeez aje rubuce rubucen da yake yi ya kalli Mammy. "Amm Mammy (Kamar yadda su fatyma ke kiranta haka yakirata) "Karku damu ba wani Babban Abu ne ba firgita ne tayi tayi da wani abu shiyasa ta shiga wannan halin Amma yanxu munyi nasaran daidai ta komai ta dawo normal zuwa anjima ruwan da akasa mata yakare zamu sallame ta Amma tarage damuwa a ranta." "Insha Allah Doctor Mungode." Mammy tasowa tayi tabar Ammar can gurin Doctor Hafeez ta tafo d'akin gun Dije tana tunanin abinda yasakata damuwa hakan samun kujera tayi ta zauna ta kalli Dije. "Mammy meke damunta?" "Khadeeja bayan tafiyar mu unguwa me akayi miki har ya firgita ki kika shiga wannan yanayin ne? Ko muna miki wani abu ne? Wadda bai dace ba Khadija?"... "Aaaa Mammy in nace kuna mun wani abu wadda banaso tabbas nayi muku karya kuma nayi Butulci." "To me akayi meki ne?" "Fashewa tayi da kuka" ''Khadeeja kiyi shiru kinji kinga halin da kike ciki dai kiyi shiru kinji daughter banason kukan nan." Rarrarashin Dije tayi har tayi shiru daga kukan da take, "Fatyma gashi bamu fito da waya kada Dady yazo bamuna." "Mammy nasan Garbati zai fada masa muntafo asibiti kuma nasan Daddy yasan asibitin da muke zuwa." "Doctor Hafeez yace zuwa Anjima zai sallame mu da ruwan da akasa mata yakare babu wani problem" Shiru ya ratsa d'akin turo kyauren akayi aka shigo Ammar ne shida Doctor hafeez. _______________"Khairi Kece a Lagos babu zato ba tsammani baki sanar dani ba." "Wallahi kuwa Fee yane ya lagos ya nauyi dakike ta fama dashi ne dariya ta fashe dashi wallahi Fee kin bayar damu wai ciki a jikinki kina yarinyar ki ki tsufar da kanki da wuri yanzu fa da kin haihu sai shayawar nan danan zaki rakwab'e ki koma tsufuwa Ammar d'in dakike takama dashi ya guje miki." Wani kallo Feena tayi ma Khairi. "Kidaina wannan batun babu Abinda zai ra bani da Ammar Khairi kinsan kuma nawa ne ni kad'ai kuma zan iya aikata komai saboda shi kodako kisan kai ne indai wata ta nemi shiga gona ta............ _*AMATALLAH*_🌹 [11/3, 10:55 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??_*🔷 _*BY AUNTY* *HAFSY*_ 💕 _*INDON KAUYE*_ _*64&65*_ Dije fitowa tayi d'aure da towel sai hijabin ta data saka fuskar nan ta tayi fayau siririn hancin ta ya kara fitowa sai d'an mitsilin bakinta mirror ta kalla taga yadda ta koma yini d'aya, cire Hijabin tayi domin tasamu wata abinda zata saka tana cikin shafa mai ne tasan babu mai shigowa daga Mammy sai Fatyma domin ko Daddy baya shigowa d'akin sai in wata matsala ta faru sai shigo, bata tura k'yauren d'akin kawai tayi bata kulle shi ba "Fatyma!!"..... Ida shigowa yayi baki d'aya muryar shi ta tsaya cak bisa kallon Dije da yayi cinyoyin ta yabi da kallo sannan ya dawo daga dukiyar fulani ta yaganni domin ta d'an zame towel d'in.. Dije wata mik'ewa tayi da sauri ganin wasu mayattacen ido da yazubo mata babu ko kyaftawa tana mik'ewa towel ya balle mata ai Ammar wani jan numfashi yayi ganin wasu dukiyar fulani tsaye cak! gasu kamar bollom bollom, ai wani tsalle Dije tayi jikinta yana rawa ta d'auko hijibin da take sallah har k'asa ta zira dasauri Ammar ya daidai ta wani tsaki yaja tare da d'aure Fuska ya kalli Dije. "Ina Fatyma take ne?'' Cikin kyarma murya Dije ta fara magana "tana kitchen....bata..shigo ba.." Ammar kallon k'asa ido yayi ma Dije sannan ya fita daga d'akin yanufi kitchen massalaci zaya yanason sanar da Fatyma harda wani mai d'an nauyi zata mishi saboda yunwar da yakeji. Dije yana fita dasauri ta tashi ta rufe k'ofar hadda saka key ajiyar Numfashi tayi magana tafara kamar tana tare da wani "hakanan sai ya kama shigo ma mutane d'aki babu wani neman izini duk yabi ya kalleman jiki." Tsaki taja kawai ta nufi wadrope riga da sikert tasaka sukayi mata d'as a jiki masha Allah komawa tayi bisa gado ta zauna tunda tana fashin sallah. Ammar yana fita ya iske Mammy kad'ai a cikin kitchen d'in tana k'ok'arin dama kunun gyad'a "Mammy ina Fatyma ne?'' Tashiga ciki ne zatayi sallah nima yanzu na kammallah zan shiga" Ammar kallon Kunun gyad'ar yayi "Mammy zan samu kunun nan nayi Kewar shi sosai tun a lagos babu shi kwata kwata balle nasha'' Mammy kanta na duk duke rik'e da ludayi🥄 tana motsa kunun "Meke Amfanin Matar taka da bazata iya yi maka Abinda kakeso ne? "Mammy wai bata iya kunun gyad'a ba ita" (Kunji k'arya gun Ammar) Mammy tab'e baki tayi "to wannan Khadeeja na had'a mashi yanzu zan kai mata shi ta sha" "Wai Mammy wacece wannan khadeejar da kukeji da ita tamkar tsoka d'aya a miya ni bansatba a familyn d'inku ko na Daddy." "Gobe zakaji matsayin ta ai." "To ni dai Mammy don Allah ki d'ibar mani nasha kunun zanje masallaci nadawo kinji Mammy." "Naji zan d'ibar maka." Yauwa Mammy na sai nadawo." Mammy kallo tabi Ammar dashi taga ya rame girgixa kai kawai tayi samo jug tayi ta d'ibar mishi sannan ta d'ibar Khadeeja ajeshi tayi ya d'an huce kafin ta idar da sallah sai takaimata. Fatyma ce tayo sallar tafito daga d'akin Mammy ta nufi d'akin su tura kyauren tayi tajishi kulle "Ahhh me yafaru ne Khadeeja zata rufe k'ofa ne kamar batanan." "Khadeeja! Khadeeja!!" Jitayi ta taso ta bud'e tura kyauren d'akin tayi ta shiga kallon Dije tayi ganin ta da zurmemen hijabi har k'asa ga sai wuri wuri take da ido kamar za'a sace ta. "Lafiya Khadeeja meyafaru ne?" "Babu komai Aunty Fateema." "Yaxakiceman babu komai baci gashi kinsaka k'ofa kuba gaki insaka wannan k'atuwar Hijabin kamai mai shirin zuwa wa'azi ne? Gashi idonki da tsoro kamar za'a d'auke ki ne" ''Aunty Fatyma Ya Ammar ne yashigo nemanki shine nafito daga wanka.." Fatyma tuni ta fahimci inda maganar khadeeja ta dosa yazo ya iske ta babu kaya shine ta rikece." Dariya Fatyma tayi "haba khadeeja kamar bakisan matsayin ya Ammar wajenki ba kin sani ko wanene wajenki yana da ikon ganin komai naki fa gaskiya banyadda da wannan abu ba kenan ko dakin tare a gidanki zaki bari matar nan tashi ta dinga yin abubuwa kala kala tunda tsoron sa kikeji tamkar ba mijinki ba.".. Dije kuwa shiru tayi tayi tana sauraren Fatyma gabanta keta d'ar d_'ar jin wai zata zauna da wannan matar ta Ammar Fatyma ce ta katse ta daga tunanin da take. "Inaga fa wannan zuwan da yaya Ammar yayi dake zai wuce fa lagos." Dasauri Dije ta d'ago Idon ta ta kalli Fatyma "Aunty fatyma dani zaya lagos don Allah abarni gun Mammy kada yatafi dani nidai bana zuwa." Fatyma ganin zata tada hankalin ta yasa dafa kafad'ar ta...... _Don Allah kuyi hakuri don Allah dajina kwana biyu wallahi hidima ce muke shiyasa wannan dakyar nayishi wallahi Amma xuwa gobe in nasamu wani lokaci xakujini_ _I ❤you my people_ _*AMATALLAH*💕_ [11/5, 5:23 PM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??_*🔷 _*BY AUNTY* *HAFSY*_ 💕 _*INDON KAUYE*_ _*66*_ "Ki kwantar da hankalinki Khadeeja Aure bauta ne babu inda baya kai d'iya mace karki tada hankalinki kiji Khadeeja ni ban tababatar ai dake Yaya Ammar d'in zaya ba nace hakane kawai kar kiriceman Mammy ta shigo tayiman fad'a Kinji Khadeeja ki kwantar da hankalinki." Fatyma tana cikin rarrashin Dije har ta jawo mata wata firar don ta mantar da ita sai ga Mammy ta shigo d'akin rike da jug d'in Kunun ayar da ta dama mata. "Khadeeja Amshi kunu na ki zuba kisha zuwa anjima ki zuba kisha." "To Mammy nagode.." Mammy kallon Dije tayi "Banason wannan godiyar Tsakanin uwa da y'a babu godiya kinji Khadeeja." "Mammy nima zansha kunun tundazu yawu na ke tsinkewa." Bazaki iya tashi kiyi ba sai da kiga na had'a ma daughter ko saboda kwiwar yi kikeji kun saka kunun ido keda yayanki to kije kema gayacan na d'ibar miki a kitchen kibar ma Khadeeja wannan nata ita d'aya." "To Mammy bari naje nima na d'auko nawa nasha" "Dadai yafi miki don wannan na Khadeeja ne nima bari naje na ida shiryama mijina girkin nasa Fatyma inkinfita ki mik'a ma yayanki na shi d'aki kafin ya dawo daga massalaci." "To Mammy.." ______________________"Khairi haryanxu banji wani chanji daga wannan ma maganin danasha fa banajin komai kuma Doctor d'in da yabani yace xanyi ciwon ciki ko yayane Amma tunda nadawo nasha maganin nan babu wani abu danaji." Khairi kallon Feena tayi hannun ta rike da kwalbar syrup tana sha had'eshi coke. ''Ki kwantar da hankalinki kwanta kibashi kamar kwana biyu zaibi rariya nina fiki buk'atar hakan saboda inason ki wataya kiyi life d'in mai dadi kinga ko kora da wannan kinjiki normal Amma ga Feena in cikinan bai zube ba fa? Kikayi sake har ya shiga cikin wata 7 kinji Abinda doctors ke fad'a mana zubar dashi yanada matuk'ar had'ari fa.'' Feena wani kallo ta wurga Ma khairi zai zube ma saboda yanzu bana kaunar cikinan ko kadan a tare dani khairi." "Kawata ga shawara ma in har xokiji." Feena matsawa tayi

Chapter 9 of 11