yafito ya d'auki wani plastic da yake zuba ruwan zafi yayi ruwan ya d'auko ya d'auraye sannan ya nufi gun ya siyo ya ketaro ya daga titin ya shiga motar sa ya koma asibiti yana parking motar sa ta fara tsuwwa! Yana dubawa dasauri ya koma waje guda tare k'amewa wajen guda tamkar yana gabansa,
"Good morning sir."
Daganan yayi shiru yana sauraren har yagama saureren Abinda zaiji sannan ya kuma k'ara sarawa ya kashe wayar cikin damuwa ya shiga room d'in da Ammar yake ciki yana kwance
Aje plastic d'in yayi yafita ya d'auko cups da ya manta yazo ya sheka ma Ammar ruwan zafi.
"Ammar bari na d'an mik'ar da kai kasha ruwan zafin ko."
Ammar gyad'a kai yayi
Haidar pillow yasa yatada Ammar ya jingina dashi yadda zaiji dad'in zama sannan ya mik'a masa cup d'in ruwan zafi yana kurb'a a hankali
Haidar kuwa duk yanayinsa ya koma nadamuwa wayarshi ya zaro yayi wasu danne danne sannan ya maida
Tsinkar muryar Ammar yayi.
"Haidar ina ka tsince nine har naganni asibiti kuma nasan kana jos me yakawo ka lagos ne har kaganni a wannan halin.?"
Numfashi Haidar ya aje tare fad'a masa yanayin daya ganshi ciki har ya d'auko sa ya kawosa asibiti....
"Zaka iya gane wadda sukayi maka wannan abu ne Ammar?''
Girgiza kai yayi
"Haidar bazan iya gane suba saboda fuskar su akwai mask a fuskar su."
"Naji Haushin dabakaga Fuskar su ba Amma a dingi zuwa rafi zamu had'e wani gun Amma, Ammar meya fiddo dakai ne a daren?"
"Wallahi Feena ta matsa min na fito siyo mata shawarmma da ice cream shiyasa nafito''
"Wai Ammar meyasa ta maida ka sakarai ne ko ina tajaka kana binta ne wai kana koma sokalo kamar ba Amma d'in dana sani ba haba haba to ka abinda ta janyo maka badon kana da tsawon rai ba da tuni ka dade da shekawa barzahu.
Ammar kallon Haidar yayi ganin yadda yake bala'i shiru yayi ya kyalesa shigowar doctor ne ya bashi magani sannan ya fita...
''Haidar Aroman wayar ka nasan tawa ta fad'i kou."
Haidar juyowa yayi ya kallesa bai kai dafad'a masa wayar sa na hannunsa "mai zakayi da ita ne ko zaka kira Daddy kasanar dasu ne."
Zan kira Feenah nasanar da ita halin da nake ciki ne kada hankalinta ya tashi...
Cikin Fushi Haidar ya juyo ya kallesa tare da sakin wani tsaki
Wayarka na hannu na kuma bazan bayar ba ka kirata intazo tayi ne ba itace silar halin daka shiga ba
Nadauka daddy zaka kira ma kasanar dasu"
bazan fad'a musu ba gudun tashin hankalinsu ya tashi ka ganni kuma gari ba kusa ba kuma naji sauk'i fa kabani na kira office na sanar dasu to..."
Mik'a mishi wayar yayi jin office zai kira ya sanar dasu abinda ya sameshi
Bayan yagama wayar ne
Ya kalli Haidar
"Haidar ya sunan hospital d'inan da muke ciki ne?"
*"MUNEERA HOSPITAL"*
"OK"
shiru ya ratsa d'akin Maida wayar yayi ya aje
*After 10 Minutes*
___________kofar aka dinga kwan kwansawa da k'arfi Haidar cikin fushi ya d'ago saboda bugun k'ofar yayi yawa yana dubawa wani a wayar sa k'ofar ya nufa ya bud'e da k'arfi cikin tsoro taja baya...
_Wakuke zato ne?_
_Waleema naje shiyasa kugansa hakan ba yawa Amma kusha kuruminku yanzu nadawo daidai_💞
[11/3, 10:53 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??🔷_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
*47&48*
_Duk wata mai suna Zainab wannan page d'in nata ne yau, Allah jikanki yayata zainab Allah yayi miki rahama yagafarmiki ya rayamiki zuri'a dakika bari ya Albarkacesu mutuwar ki kullum sabuwa ce a zuciyarmu_😭👏🏻
"Doctor don Allah kadubamana Daddy kada murasa shi."
Shigowar Doctor Hafeex ne Fatyma tanufi shi tana wannnan magaganun ki
"Ki kwantar da hankalinki Zai samu sauki nufar shi kallon su yayi "zan samu ruwa masu sanyi ne?''
"Eh."
Dasauri Fatyma tanufi gurin Fridge ta bud'e kwalbar ruwa ta d'auko ta b'alle murfin ta mik'a ma doctor Hafeez shafa ma Dady ya fara yi abisa fuska da bisa kanshi
D'auko wani abu yayi daga cikin Briefcase d'insa daya shigo da ita yafara dannawa Dady shi A k'irji A hankali numfashin Dady yafara dawowa normal yabud'a idonsa.
"Daddy sannu."
Gyad'a mata kai yayi
Dije ma matsowa tayi "sannu Dady."
Murmushi yayi tare da gyad'a mata kai itama.
"Munyi sa'a numfashi sa yadawo normal jininsa ma ya daidaita Amma ya kamata a kiyaye b'acin ransa sosai domin irin hakane mutum yake kamuwa da bugawar zuciya lokaci d'aya sai dai akaga mutum ya mutu,ko kuma paraliyse ta kamashi wato cutar b'arin jiki.
"Insha Allah Doctor za'a kiyaye ga duk abinda Abinda kace."
"Yanzu zai samu hutu kamar na kwana uku ga wasu magugunan da zaiyi Amfani dasu insha Allah komai zai koma normal Amma kada yasaka damuwa a ransa fa."
"Insha Allah duk za'a kiyaye doctor mungode sosai."
Gyara ma Daddy kwanciyar akayi yadda zaiji dad'i Doctor Hafeez yabada magagunan yayi musu bayanin yadda zai sha su,
Bada jimawa ba bacci mai nauyi ya d'auke Daddy Mammy tagumi tayi tana kallon Mijinta tana tunanin abinda aka fad'a masa har ya shiga wannan halin goge hawayen fuskar ta tayi tare da kallon Dije da Fatyma.
"kuje ciki tunda yasamu bacci Fatyma banaji kince zakije school k'arfe 12 am ne."
"Mammy nafasa zuwa zan kira Afrah nace mata bazan sami shigowa ba
"Meyasa Fatyma bazakije ba."
"Mamy Kina ganin halin da Dady yake ciki konaje school d'in tunanin halin da yake ciki zanyi.''
"Yaji sauk'i fa fatyma.".
"Don Allah Mammy kada kice wani abu nidai Allah bazanje ba."..
"Shikenan to."
"Muje ciki Khadeeja".
D'akin Fatyma suka nufa Fatyma tana nuna da Dije dama tund'azu.
"Khadeeja meke damunki ne?"
Sunkuyar da kanta tayi
"Kaina ke min ciwo."
Sannu bari na d'auko miki magani."
Fatyma wata y'ar locker ta bud'a panadol Extra ta b'allo kwara biyu bari na d'auko miki ruwa kisha sannu."
Bada jimawa ta dawo da cup da ruwa ciki Dije runtse ido tayi ta had'iye maganin domin bata k'aunar shan magani ita ko kad'an.
"Yauwa sannu ki kwanta zuwa anjima zakiji sauki insha Allah."
"Nagode."
"Ki kwanta"
Dije nufar gadon tayi ta kwanta bata jima fatyma tana janta da magana har wani bacci mai nauyi ya d'auketa...
Fatyma kallon ta tayi ta girgiza kanta sannan ta tafi tunanin ko meyasami Dadyn ta tashi tayi ta fita domin ta kasa samun natsuwa da da zama d'akin...
_BAYAN KWANA D'AYA_
__________"Sir Sannu Allah sawwak'a ya kawo sauk'i da wuri domin nasan zamuyi missing d'inka a office kwana biyu kafin ka warware''
Murmushi yayi mata
''zainab kenan baki iyawa da office ke d'aya kenan?"
"Haba sir yazanyi da wannan tulin aiki na office ai kana matuk'ar kokari sosai fa."
"Haka Oga David yace da sukazo fa."
"Ai da tare zamu tafo dasu Aikin ne ya rik'eni kawai nace su tafo zanzo daga baya."
Ledar dake gabanta ta d'auko.
"Sir ga kayan fruit na tafo maka dasu."
"Harda d'awainiyya.."
"sir babu yawa fa."
"Thanks so much zainab."
"Sir wai ina Madam tunda naxo bangan taba."
"Taje gida ta dawo Amma yanzu zata dawo.
Alhalin Feena tunda tagama gayama Daddy magana bata jima ba tace zataje ta dawo haryanzu bata dawo ba gashi Haidar tunda shima ya fita bai sake ganinshi ba ya kira wayar shi bata shiga don ma Doctors suna yawan shigowa dubasa gashi ya kira taki picking shi tashin hankalinsa kada kada ace wani laifi yayi mata,
(Kuji man Ammar)
"Zainab bani ayaba ko Apple naci kada kice kin kawo man kayan dubiya ban ciba."
Dariya tayi ta mik'e d'aukar wani plate tayi data gani gefe d'auraye sa tayi da wani ruwa data gani cikin bucket gefen gadon da Ammar yake,
Apple d'in ta mik'a masa yaci kusan rabi mik'a mashi ayabar tayi yacinye kusan guda biyu ya cinye ta b'are masa ta uku ta mik'e ta mik'asa turo k'ofar d'akin akayi aka shigo cikin wata murya tace
"Kutumar uban nan Ammar mezan gani hakan wace y'ar iska ce kowace karuwa da zata baka Ayaba har da b'are maka dasauri ta kwab'e Ayabar daga hannun Ammar.
Cikin wani *ZAZZAFAN KISHI*(Jidda Aliyu)
Ke karuwa yar iska matsiyaci karuwan ci naki ne har sai kiboyoshi A asibiti."
*"Queen"*......
d'aga mashi hannu tayi
"Kaga malam kada naji ka tsoma bakin ka a cikin wannan lamarin in ba so kake ka had'u da Mummana b'acin raina ba wallahi.."
Ammar cikin sanyi jiki kamar wani k'aramin yaro konace d'an Feena yayi shiru k'ara juyowa tayi kan zainab zata damko wuyan rigar ta dasauri zainab ta rik'eta tare da kallon ta.
"Kada ki yarda hannun ki yakai da wuyan riga ta inko kika kuskuran hakan zan gwada miki wacece ainahin zainab wallahi."
"Wacece ke fa cen karuwa y'ar iska...".
Saukar marin dataji ne yasata kin k'arasa maganar da zatayi kallon ta tayi taga yadda take hucin "kada ki kuskura ki k'ara had'ani da kalmar karuwaci inma karuwaci nake da ubanki na fara daga shigowar ki baki jira komai zaki hau zage zage da tsinane baki duba halin da marar lafiya yake ci ko sir bai fad'aman nasan kece matar sa."
Zainab juyowa tayi ta kalli Ammar yake cikin tashin hankali wannan rigima dasuke gashin Feena ta hanasa magana
"Am sorry sir da abinda nayi ma madam d'inka ita taja Amma gaskiya bakayi dacen mata ba domin dagani bata tashi a gidan tarbiyya Am sorry sir banada hak'uri idan akayiman abu kuma bana b'oyeman magana, Allah k'ara Lafiya sai kadawo office."....
D'aukar Hand bag d'in tayi zata fita wurgo wani abu taji tana dubawa taga Applen d'in datagakawo Ammar ne da kingi Ayaba Feenah ta watso mata su.
"Ki d'auki tsiyarki kitafi da ita baya buk'ata murmushi zainab tayi
"Kinacin darajar oga ne Amma wallahi da nuna miki calour d'ina domin gaba ki kiyaye tunda wadda na kawo mawa yaci Ai kuma buk'ata ta biya..saki ta buga ta bud'e k'ofar d'akin ta fita cikin b'acin rai....
Fenna maido hankalinta tayi ga Ammar ga haushin Marin da Zainab tayi mata ga magaganun da Ta fad'a mata bata maida mata martani ba tana tsoron ta tayi magana taci uban duka
_Domin zainab irin wad'ad'an karkafafan mata ne ga jiki ga tsawo ga kuma k'arfi_
Domin Feena lokacin da Zainab tayi wurgi da Hannun ta wani azabar zafi ya ziryace ta shiyasa bata biye mata ba
"Queen kiyi hak'uri baki tsaya kika saurari ko wacece ba."
Wacece face k'aruwar ka wadda kuke shek'a aya a bayan ido na shine don kaga bani nan har ka kira ta kai ga jarrabe ka matsu ne kuma gabanka taci man mutunchi Amma babu abinda zaka iya cewa ko."
"Queen meyasa kike wad'ad'an magagune kinsan A duniya ba mace da nakeso kamar ki wallahi bazan iya kula kowacce mace A duniya da wuce ke nayi miki Alk'awarin hakan tun ba yau My Feena zainab mataimakiya tace a office babu Abinda ke tsakani da ita kiyi hak'uri naji Haushin marin da tayi miki inajin tamkar ni ta mara, Amma zan koma office zata gane ta mari kyakyawar Fuskar ki.".
Feenah kallon shi tayi
"In ma budurwar kace na gano hakan wallahi tallahi zaga fuskaci mumunan tashin hankali daga garen..."
"Bama hakan bane Queen"
Haka Ammar ya cigaba da rarrashin Feenah har ta d'an sauko daga Fushin da takeyi ta d'an zauna bakin gado.
"Queen nakiraki naji Lafiya Amma bakiyi picking why?."
"Ina hutawa ne ko bakaga lalura da nake tatttare da ita bane bana iya picking ne ina kallon kiran naka kabarni daga jiya sai dai naci cake da lemo wannan abu na cikina ya isheni da zillo wallahi danasan hakan zai bani wahala da tuni na zubar dashi...."
"Kiyi hak'uri zai daina.."
Shigowar da akayi d'akin ne yasa Feena tayi shiru tare da wani mummunar fad'uwar Gaba ganinsa cikin kakinsa ga kuma fuska murtuke babu Alamar murmushi tattare dashi ...
"Haidar sannu"....
Ko kallon inda take baiyi ba ya maida idon sa ga Ammar ya jikin naka."
Haidar Kanajin Queen nayi maka sannu da zuwa Amma bakayi mata magana wai me tayi maka kake mata wannan Abun ne gaskiya Haidar banajin dadin haka."
"Bana buk'atar sannu da zuwan ta kuma bana buk'atar amsawar wata ne shiyasa kai meyasa baka kishin kanka ne matar bata sonka bata kula dakai tunda tabar asibitin tun jiya Around 5pm bata dawo ba sai yanzu sunan mijin da take k'auna kuma take so ne."
Cikin Fad'uwar gaba Feena ta kalli Haidar ta yaya akayi yasani tunda tabar guri nan bata dawo ba sai yanzu lalai akwai aiki ja gaban ta.
"Babu ruwanka matata ce kuma hakan nakeson ta bakasan lalura data hanata zuwa ba nidai kadaina hakan na lura kwata kwata baka son na kasance da farin cikina tun ba yau ba."
Haidar kallon Ammar yayi yadda yake kumfar baki akan Feenah, Amininsa wadda basu tab'a samun sab'ani ko fad'a ba ko dayaushe k'okarin suke su kyautata ma juna duk da kowa da irin aikin sa Amma suna kula da junansu.
Amma gashi yau mace zata had'asu Anya Feena hakan tabar Ammar wata zuciya ta fad'a masa Amma yayi sauri kawar da zance daga zuciyar sa.
"Kayi hak'uri Amini naga ranka ya b'aci aiki da yakawoni lagos nagamashi yau daga nan kuma Benin nayi zamuje kwantar da wani yak'i da akeyi Allah baka lafiya Allah k'addara saduwar mu kasan yanayin aiki mu ina fatan inkaji labarin mutuwa ta zakayima Amininka Addu'a sai wata rana..."
Juyowa yayi yayi ma Feena wani kallo zai fita tsinkar murya Ammar yayi yana kiransa Amma ko juyowa baiyi yasa kai ya fita cikin b'acin rai.....
Feenah Add'ua tafarayi Allah yasama ya mutu
Kallon Ammar tayi yadda ya dafe kai tare da runtse idonsa harararsa tayi tare da maida kanta wajen wayar ta ta cigaba da chart d'inta bata damu da yanayin da yake ciki bama....
_*BAYAN WATA BIYU*_
____________
Tun lokacin da Daddy ya kira Ammar Feena ta d'auka har yayi sanadiyyar fad'uwar sa bai k'ara kokarin kira ba ya share sa ya fad'a Mammy yadda sukayi Amma ya hanata ta sanar da Aysha ko Fatyma.Mammy kuka tasaka mishi tana cewa wannan wace irin mace ce Ammar ya aura.
Dije kuwa ta saki jikin ta har gobe taki nuna damuwar ta akan wane irin zama take babu miji a kusa da ita,
Wata islamiyya da Fatyma ke zuwa tare suke zuwa,
Tak'ara gogewa farinta yak'ara fitowa tayi bul bul da ita ga kuma girki da ta kware dashi domin school Mamy tasakasu a nan bayan su itada Fatyma wadda ake zuwa Saturday &sunday ana koyan duk wani nau'in abinci a ciki dana turawa dana gargajiya,
Dije ta kware dashi,
"Naja'atu yau tsawon wata biyu tun lokacin dana kira Wannan yaron ban sake kira ba Amma yau nakirasa Amma taki shiga zan tura masa text message yazo nabashi kwana biyu banganshi sai gani da matar sa a lagos".
"Daddyn Ammar duk yadda kayi daidai ne Amma har gobe ina mamakin sauyawar Ammar."
"Kicigaba dayimasa Add'ua Naja'atu karkisa ka damuwa...."zan tura masa message d'in a yau.......✍🏻
_Kuje kusha ruwa naga kunajin kishirwa_🧐
*_AMATALLAH_*🌹
[11/3, 10:53 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??🔷_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_*45&46*_
"Am sorry."
Wane irin buga k'ofa kike sai kace wata k'aramar yarinya ko kin manta da hospital ne nan akwai patient da yanayin ciwon su baya buk'atar hayaniya ne"
"Ina sauri naga halin da My Ammar yake ciki ne"
Ashe kina sonshi har kika fiddo dashi wannan time d'in da kinsan yana iya fad'awa wani had'ari Amma kika fiddo shi saukin d'aya Ammar bai rasa rayuwar sa ba wallahi da sai nayi shari'a dake kin k'are rayuwar ki prison ko waye father d'inki A nigeria."...
"Haidar.."
Juyowa ya kallesa
"Kaga malam dakata don ta maidaka sokon miji ta yaya zata tadoka cikin dare ka fito ne,Kuma kana kwance baka lafiya shine kayi mata text massage tazo ta iske ka ko Amma matar kace ba tawa bani da iko akanta Amma daka mutu wallahi kowacece ita sai nayi shari'a da ita kawai don ta maida ka sakarai sai ka biye mata kai kanka da halaka ga abinda kajawo man kan ka nan ai.".. Ficewa yayi daga d'akin
Dasauri Feena ta nufo Ammar."kana kallon Abinda yake man da magagunun dayakeman har fad'aman yayi nina tura a kasheka kuma kanajin duk abinda yake fad'a na rasa ko wace irin tsana ce Haidar yake man haka."
"Kiyi hak'uri *MY QUEEN*
Haidar yana da sauk'i kai narasa abinda kikayi masa ne Amma zan mishi magana kinji."
"Daidai yafi don nagaji da kullum yake nuna man tsantsar tsana danake hangowa cikin idon sa kamar ya duke ni kai kuma har yanxu kaki d'aukar wani hukunci har nakirasa nace kana wacce hospital wai yaki d'aga wayar tawa to....
Had'a bakinsa yayi danata shi ya dak'atar da ita daga maganar
"Haba queen kibar maganar kinji gashi yanzu *MUNA TARE* ba"
Yamutsa fuska tayi tare da raba jikinta dana Ammar
"Yanzu ya jikin naka ne''
"Naji sauki badon Allah ya kawo haidar ba dakin rasani Queen."
"Kadaina wannan maganar please muna tare har abada bamu mai rabamu da juna.."
Murmushi yasakarmata
"Queen zan shiga toilet taimakan nashiga toilet d'in."
tabe baki tayi sannan ta taimaka ya sakko daga bisa gadon daganan ta janye jikinta da dafa bango Ammar ya shiga toilet..
Yana shiga wayar sa tafara d'auka tana ringin d'in Feenah bata kula ba k'ara kira akayi idon Feenah yakai da wayar sunan data gani ne a wayar yasata firgita dasauri suna _*MY DADY*_
tagani yana yawo b'aro b'aro a wayar dasauri ta d'auka tare da fita daga d'akin tashiga wata corner kanga wayar tayi a kunne
"Hello Dady anyini Lafiya."
Dady idon sa ya maido ga Mammy baiyi sannan ya furta
"Lafiya.."
"Ya mutanen gidan kuma."
"Lafiya ina Ammar d'in ne?"
Fennah ya mutsa Fuska tayi gashi nan kusadani yana aiki ne bazai iya picking kafad'aman abinda za'ace masa in yagama na fad'a masa."
"Kice ina son yimasa magana."
"Ok."
Feenah yitayi kamar tana magana
Can ta maida wayar a kunnen ta
"Hello Daddy yace kafad'i duk Abinda zaka fad'a na fad'a masa bai iya karb'ar Wayane aiki yake ne''
"Ki kafad'a masa ko waye keson magana dashine."
"Eh ba Dady bane Alhaji kabeer wadda ya haifi Ammar...kit...
Dady ya kashe wayar..
Feenah ganin ankashe wayar yasata sakin wata dariya
"Kad'an kenan inka kira sa mezayi maka salon wani munafurci ko me Amma bari nayi maganinka."
Contact tashiga tasa number Dady a blacklist sannan ta nufi d'akin ta iske Ammar yana dafa bango zai fito
"My Fee ina kikaje ina kiranki kizo ki taimakan ne."
"Naje waje nayi waya da Mommy ne da phone d'inka tawa babu recharge card ne."
"Ok."
Feena ta taimaka masa ya hau gadon ya kwanta maida wayar tayi ta aje ..
______ "Dadyn Ammar Lafiya meke Faruwa ina Ammar d'in bakayi masa magana ba"
Tambayoyin da Mammy ta jero ma Daddy kenan.
D'ago idanuwansa yayi wadda sukayi jawur tsananin b'acin rai dayake ciki kanshi yaji yayi masa dum! duhu yagani ya gifta masa Mamy ganin Dady tayi ya silale k'asa ya sume k'ara Mamy ta saki tare salati
"Dadyn Ammar! Dadyn Ammar!!!"
Amma babu Alamun numfashi tattare dashi
"Wayyo Allah na Dadyn Ammar don Allah katashi kadaga ka mutu..."
Dagudu Fatyma tafito daga d'akin Dije tana bayanta ganin halin da Mammy take ciki ga kuma Dady kwance
"Mammy meyasame Daddy ne."
"Fatyma maza kira Doctor Hafeez"
To Mammy cikin sauri ta koma d'aki ta d'auka wayar ta tana kyarma ta kira doctor Hafeez tana kuka cemata yayi gashinan, komawa tayi gun Daddy Sukasashi gaba suna kuka Dije tana gefe itama tana Kuka ganin Halin da Dady yake ciki kamar mattace.......
_Yawan comment yawan typing_👌🏻
_*AMATALLAH*🌹_
[11/3, 10:54 AM] 😘💕: 🔷 *_MATA KO BAIWA??🔷_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
*49&50*
_*WANNAN PAGE D'IN NAKU NE HAFSAT MUSA TRUE FANS INA MATUK'AR JIN DADI COMMENT D'INKU SOSAI DA SOSAI WALLAHI YA NUNA KUNA BIYE DANI MATUK'A*_💖💖💯
Zaune yake yana duba wani abu a lap top k'amshi tureren ta kawai yaji yasa shi shiga wani wani yanayi mai wuyar fassaruwa saukar hannuwanta yaji bisa kafad'ar shi, tare sanyayar murya ta wadda take mishi shagwab'a ko dayaushe,
"Uhumm Habibi yanzu fa time d'ina shine zakazo
kuma kana aiki ne nidai gaskiya ban yarda ba cikin shagwab'iyayar murya ta farayi masa magana lumshe idon shi yayi saboda wani yanayi da yaji yana shiga..."Hubby zokiji."
Kewayo tayi ta zauna bisa jikinsa tare da d'ora hannuwanta bisa kafad'ar shi
"Habibi kabud'a idon ka mana.'' "Bazan bud'e ba sai kin sumbaceni sannan "shikenan to Habibi na ji yayi ta d'ora leb'en bisa nashi tare da zura tongue d'inta cikin bakinsa cafke yayi tamkar yasamu lollipop ga leb'en ta masu matuk'ar taushi haba jiyayi ya surkucece gaba d'aya saboda wani salo da take masa.
"Habibi na d'ora girki bari na duba ji yayi ta mik'e da waiga yayi yana kallon bayanta gashinta ta saki har tsakiyar baya yadda take juya jikinta Ajiyar numfashi yayi tare furta " Iuv you so much Hubby I luv so much Hubby na."....
Tsaye tayi jin Ammar yana magana cikin baccin sa saurare tayi taji meyakecewa ji tayi yana Furta i Iuv u so much hobby na jefasa masa pillow tayi ganin yadda yake juye juye
"My Ammar!!! lafiyan ka kalau ko meke damunka kuma wacece Hubby da kake ta nanata ma kalmar so haka.."
tun kafin ya bud'a idon sa Feena ke jero ma Ammar Question firgice ya bud'a idon sa yafara waige waige dafe kansa
Kanaji inayi maka magana zaka shareni ko d'ago idon sa yayi wadda tuni sun ja kala cikin sanyi murya tare da sakin murmushi "Mafarki nayi *MY QUEEN* kina furtaman Loveword masu dadi"
"Amma tunda muke dakai baka tab'a kira na da Hubby sai a cikin mafarki zaka ambace ni."
"Haba My queen wane nake da ita da zan furta ma haka yawuce ke."
Tab'e baki tayi yunwa nakeji ina buk'atar kaje kayiman girkin Abinda zanci juyowa tayi tafita Ammar binta da kallo yadda cikin ta yak'ara fitowa dafe kansa ya k'ara tariyo mafarkin da yayi magana yafara
"Wacece wannan wadda nake gani a mafarkina wadda nake shiga yanayi wadda ko akan Feena banajinsa wacece wadda har yazuwa yanzu nakasa ganin Fuskar ta ne wadda nakejin ta cikin raina fiye da Feena kodai Aljana ce tunowa da yayi da Abinda Feena tasa Mik'ewa toilet yashiga ya watsa ruwa ko yaji k'arfin jikin sa
Ammar yanayin da ya gansa cikinsa jan tsaki
"Meyasa duk lokacin da zanyi mafarkin ta sai taja min wanka ne." Tsarkake jikinsa yayi tare dayin na soso da subulu yafito ya zira wata t shirt mai gajeren hannu sai there quarter d'in wando ya fito a hakince ya iske sarauniyar tasa tana kallon wani Nigeria film
"Sai yanzu My Ammar zaka fito kayiman girkin?"
Kiyi hak'uri na watsa ruwa ne?"
Tab'e bakin tayi tare da cewa "kai Kullum wanka kamar kogi da zaka mosque sallar juma'a bakayi wanka ba."
Murmushi yayi tare wucewa kitchen ya girka mata abinda take buk'ata supergetti ya dafa mata tare da miyar kifi yayi mata kamar wani kuku 👨🏻🍳 haka Ammar ya jero girkin da yayi mata bisa wani tire ya fito dasu kusa da wani d'an table ya jera mata
"My Queen angama fa."
Yamutsa fuska tayi"mene ka girka?''
Supegetti da soup d'in Kifi nayi miki Feena jawo tire tayi tare da d'aukar plate tayi ta zuba
"Bazan iya ci ba kabani a baki."
"Angama."
Haka Ammar yafara ba Feena Abinci a baki bai wuce 6 spoon ba zuwa 7 tace ta koshi haka Ammar ya tattara kayan yakai kitchen d'akinsa ya nufa don ya d'auko lap top d"insa zaiyi wani aiki kafin ranan Monday, yana shiga wayar shi tayi tsuwaa Alamun shogowar text a ciki nufar ta yayi ya bud'a *MY DADY* shiga message d'in yayi
_Ammar yau komai kake ka biyo jirgi ina buk'atar ganinka ka iso garin kano in ba haka wallahi tallahi wallahi tallahi zaka yi nadamar kin bin umurni na dazaka bi ranka zaiyi matuk'ar b'aci zaka had'u da mummuna Fushi na da baka tab'a ganinba Ammar!!_
Ammar jiyayi ya rud'e ganin wannan text d'in na Dadyn sa dasauri yafito ya iske Feena tana chart
*"MY QUEEN* Kano zani yanzu yanzu nan wata mik'ewa tayi