Share this page
na Amince masa da hakan yaji dad'in haka dagareni nan ya dinga yi man godiya kamar nayi masa wata babbar kyauta. Ko auren da Ammar yayi sai da yazo Alhaji kabeer yasanar dani yace kuma Alk'warin mu nan yana jira ne ki ida makarantar ki sannan ayi magana idan kije can in da rabo sai ki ida gidan mijinki kinji yadda mukayi yanzu idan na karya wannan Alk'awarin Dije wannan kallo zaiyi man kenan shiyasa na hanaki kula kowa don Alhaji kabeer baiji dadi bane da tuni anyi biki Kidaure kiyiman wannan biyayar kinji ko. don nasa bazaki watsa man k'asa a ido ba Share hawayen fuskar ta tayi "Baffah na Amince da hakan... Allah yasa Hakan yafi Alkhairi Baffah bazan baka kunya ko na watsa maka k'asa a ido.".. Baffah Murmushi yayi "Allah yayi miki Albarka kinji Dije.".... "Ameen Baffah." tashi tayi ta nufi d'aki bisa tabarma dake d'akin ta kwanta rintse idanuwan ta tayi ta tuno farkon had'uwar da Ammar har da matarshi wata rana ce ta dawo daga yo ittace da Inna ta aiketa yowa... tana ta sauri domin ita d'aya ce Laure Abokiyar ta bata jin dadi tana tafe tana y'an wakokin ta bataji k'arar mota ba bayan ta jin k'ara tayi ta cika mata kunne ga kuma mota ta nufo ta gada gadan da sauri ta saki icce ta rud'e gefe d'aya ta samu ta rakub'e Chab'o taji ya manta Fuska can kuma taji an wanke ta da mari dasauri ta bud'e idonta bisa wata farar mata ta d'ora su...... _*Hhhhhh k'ara k'ara readers wakuke tunani ta wanke ta da mari??*_ [11/3, 10:45 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _Sadaukarwa_ _Ga dukkan masoyana dake Fad'in duniya da wadda nasani da wadda ban sani_ _I ❀u All_ _*9&10*_ Inno cikin firgici ta kalli Inda Dije take babu numfashi tare da ita "Laure d'ebo ruwa a tunkuya maza maza Da Kuka laure ta shiga cikin Ta d'ebo ruwa dama gasu sunyi sanyi sosai kafin laure tadawo matan gida har sun taru cikin sauri Laure tadawo da kwanon Ruwa, Inno Amsa tayi ta fara shafa ma Dije a fuska a hankali can dije ta bud'e idon ta tashi tayi da gudu kamar zata ruga Dasauri Inno ta rike ta ."Dije yi hakuri zauna bakiga ciwo a goshin ki ba.".. Dije shafa gun ta taji ciwo ga wani zafi datakeji gun Fashewa tayi da Kuka hajjo yar tsohuwa Kusa da Dije ta matso "Sannu Kinji Dije Narasa Abinda ke damun Ammaru ko bashii gani ne ya buge ki ne.".. Laure cikin sauri tayi magana "hajjo yana gani fa ya fito daga inda suka sauka shine Dije ta fad'a mishi bata sani shine ya tunkud'ota har ta fad'i..." "Yanzu ina Ammaru.?'' "Yafita baima tsaya duba halin da take ciki ba ya fita." Hajjo Girgiza kanta tayi sannan tafara magana. "Kiyi Hakuri kinji Dije karki Fad'ama su innanki ga abinda ya faru kice fad'uwa kikayi kinji ko Dije." D'aga Kai tayi tana sharar Kuka Hajjo kama tayi suka shiga ciki wasu magaguna ta d'auko ta shafa mata gun ciwon sannan ta d'aure mata. "Kidaina Kukan Dije basan ki da hakan na rasa Abinda ke damun Ammaru nidai suzo su tattara kayansu su tafi shida matar shi wadda batada tarbiyya ko kad'an sai rashin kunya."... Haka Hajjo ta rarrashi Dije tadaina Kuka har suka fito tare da laure suka nufi gidansu Dije Inna tana zaune tana tankad'en gari taji sallamar su Dije tana d'ago Fuska taga Dije d'aure da wani bisa kai. Dasauri ta mik'e "Subhanallah!! Dije mezan gani haka meyasameki ne?" waigowa tayi wajen Laure "Laure meyasami Dijen ne naga lafiya lau kuka tafi Kasuwa meya faru da ita ne?"" Dije dai Kuka ta fashe dashi Laure ma tafara taya ta. "Kuyiman bayani kun fara Kuka.?'' "Inna fad'uwa tayi ne mun shigo gidanmu ne?" "Wajen wasan ko da guje guje ko?" Laure kallon dije tayi "Aidama nasan ni baku girma Kullum cikin guje guje kuke yanzu ga abinda yaja muku taji ciwo." ."inna munbari bazamu k'ara ba". "Allah yasa to." Zama sukayi bisa tabarma dake malele tsakar gidan Laure ta d'auko ma dije pillow ta jingina dashi.... Ajiyar Numfashi tayi Tuno abinda yafaru can baya itada Ammar sunke kanta cikin k'afar ta tana rerewa kuka shine yanzu za'a had'a ta aure dashi mutum dagashi har Matar shi suna matuk'ar kyamar yan kauye basu son mu'amula ta had'asu dashi shine yanzu za had'ata aure dashi to wace irin rayuwa zatayi gidanshi sannan wace irin rayuwa zatayi a binni ba gaban Innar ta ko Baffan ta ba??? "Dije" Dasauri tad'ago Fuskar ta ganin Innar ta k'ok'arin goge hawayen Fuskar ta ''Na'am inna." "Mikeke bakiyi Bacci ba.'' "Yanzu zan kwanta Inna?" "Dije kiyi hak'uri kinji ko kidaure ma zuciyar ki ki Amshi zab'in da Baffanki yayi miki kinji ko Add'ua zaki dinga yi yasa hakan yafi Alkhairi kinji kou karki saka damuwa hakan Allah ya k'addara miki kedai kikasance mai biyaya abinda Allah ya k'addara D'an Adam bashi musayar shi.".. "Hakane Inna insha Allah zanyi Amfani da abinda kikace kuma zan kasance mai biyaya ga duk Abinda kuka ce min" "Yauwa Dije Allah yayi miki Albarka kiyi addu'a ki kwanta ko "To Inna sai dasafe." Kwanciya tayi ji tayi Inna ta gyara mata abinda ta lulluba sannan tayi mata Add'ua taja mata k'ofa ta fita... Ahaka har bacci ya d'auke ta.. _Kunji fa yaya zata kasance ne inda dije ta shiga gidan Feena tayi Alk'awari Kuma ita kad'ai ce gun Ammar duk macen data k'okarin_ _shigowa sai dai gawa_ _Ga kuma Ammar ya tsani y'an kauye_ _Hmm akwai rikici fa kudai biyo y'ar mutanen katsinawan dikko_ _Ina muku kwauron typing inayi kad'an aradun Allah typing d'in ne yanzu banason yi kucigaba da hakuri_πŸ™πŸ» [11/3, 10:46 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *_11&12_* _Alhamdullah Allah abin godiya masoyana na nesa da na kusa ga hafsy ta dawo insha Allah kunjini shiru sosai wayar ce sai taga doctor ta hau gado muje zuwa nagode da kauna masu cigiyata da mata ko baiwa muje zuwa acigaba da gashi_ "Honey" Juyowa yayi ya kalle ta kawai Amma daka kalli idon shi kasan akwai gajiya tattare dashi. "Menene My Feena" Shagwab'e Fuska tayi tare da kwantar da kanta bisa kirjinsa tana wasa da gashin dake kwance luf a kirjin sa. "Yunwa nakeji kuma girkin ka nakeso yanzu kadafaman." Kallon ta yayi "My Feena baki tausayaman yanzu na dawo daga office fa.." "shikenan tunda ba zakayi ba basai ka kawo man wata magana bari na zauna da yunwar." Tashi tayi daga jikinsa ta koma wata k'ujera dake nesa da Ammar dafe kanshi yayi saboda ba k'aramar gajiya yayi ba yau office ga kuma yunwar da yake ji juice kawai yasha ya zauna ga kuma Feena ta sa mishi rigima wai girkin takeso kuma hankalin shi ya tashi ganin yadda ta b'ata rai tashi yayi ya nufi k'ujerar da take zaune. "Haba My fee meye na Fushi kinsan bana fushin ki fa ga kuma Babyn mu me kikeso na girka miki ne?'' Juyo Fuska tayi a yamutse "kabarshi nafasa ci." ta maida k'anta ta cigaba da kallon television. ''Haba Fee kiyi hak'uri kjnji kidaina b'ata ranki ki fad'i duk abinda kikeso yanxu na shiga kitchen na girka miki shi. "shinkafa nakeso da miyar kifi sai juice d'in cucumber."... Zaro idon shi komai ya tuna kuma yace "angama My Fee bari naje na canza kaya kou." "Ok kayi sauri fa domin babyn ka tund'azu sai yawo yake man." Nufar ta yayi dag'e rigar yayi wadda dama ko ida rufe mata cibiyar ta batayi ba yayi kissing d'in cikin. Cikin Matuk'ar farin ciki. "My fee bazaki tayani cire kayan ba kenan." "My Honey bana iyawa kaima cire kayan sai na tayaka kamar dai wani k'aramin yaro..." Maida hankalinta tayi da television tana kallon wani shiri da suke Ammar d'aki ya nufa toilet kawai ya nufa ya watsa jikin shi ruwa ko zaiji sauk'i gajiyar da yayi Yana fitowa wata t shirt yasa mai gajeren hannu tare da wando there quarter ya nufi kitchen yafara aikin da Gimbiyar shi ta saka shi.. ## "Dije yanzu kina ganin za'a rabamu shikenan Dije ki tuna da irin k'aunar da nake miki mana Dije kije kice ma Baffa baki son Wannan auren ni kikeso Dije." d'ago Fuskar ta tayi tafara zubar hawaye tafara yi mashi magana. "Haba Habu ka manta duk wani d'a na gari ya nason ya gama da iyayenshi lafiya ko manta sune silar kawo mu duniya ko kamanta babu da wadda suka fima su a duniya sune cin mu sutura mu komai na mu biyaya kuma yazama wajibi ga kowane d'a yayi.ma iyayen sa in har yanaso ya gama da duniyar lafiya Bazan tab'a magana akan wannan abin da Baffah ke niyyar yi wato had'a aure na da Ammar jikan mai gari bazan tab'a saka Baffah ya ji kunya ba akan alfarma da aka nema gunsa yaji kunya idon duniya zan amince na zauna da duk wadda Baffah ya zab'aman"... Shiru tayi saboda kukan dataji yana niyyar zo mata. "Shikenan Dije Allah ya tabbatar da Alkhairi kinji kin tunasar dani abinda na manta domin komai ya samu bawa daga Allah ne sannan komai rubbatace daga Allah tun ran gini tun ran zane Allah yasa hakan yafi alkhairi Dije kiyi biyaya da zab'in Baffah kinji ko kiyi biyyaya ga mijinki kin san dai yadda y'an binni suke suna matuk'ar k'yamar y'an kauye kamar mu dole sai kin daure kinji ko ki kuma yi hak'uri wata ranan hak'urin zai zamo riba ko wane yanayi kika tsinci kanki karki kai ma kowa kukan ki kitashi kiyi Alwallah kiyi sallah ki kaima sarkin sarakuna wadda bashi da abokin tarayyya. Mai sammai da kassai ki rokeshi zai yaye miki duk wata damuwa." "Nagode Habu da wannan nasihar taka kuma zan kasance mai Amfani da duk abinda ka fad'aman." "Karki damu dije daga zan dinga yi miki kallon k'anwa dama yau saura sati d'aya na tafi birni karatu dana bari sai anyi maganar auren sai ga wa wannan abu." Zaro zoben dake hannunsa yayi "Dije gashi ki saka Hannunki nasan wata ranan zaki tuno dani kiyi man addu'a Allah ya bani mace kamar ki Dije na tafi.".. Cikin sauri ya juya zai tafi dasauri ta mik'e ''Habu katafi fa kace." "Eh Dije.".. Cikin sauri ya kauce yabar gun Durkushewa wajen tayi tana kuka zoben da yabata na azurfa ta saka hannun ta kuka kawai take ganin kukan bai yi yasata ta mik'e ta nufi hanyar gida sai ta share hawayenta sannan tayi sallama Inna naganin yanayin ta tasan akwai damuwa. "Dije har kin dawo?" "Eh Inna gashi tace tana gaidaki." Tana bata tayi saurin shigewa d'aki wani sabon kuka taji yazo mata..... For comment only 08164042255 _*HAPSY BABY*_🌹 [11/3, 10:47 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *_13&14_* _wannan page naku kuyi yadda kukeso dashi naji dadi comment d'inku jiya_ _Jidda bin usman_ _Beauty_ _Princess_ _Ummun fadeela_ _Ramlat mahmood_ _Ummun waheed_ _Amma na beatuy da jidda kason yafi yawa fa_😜 "Shikenan yanzu an rabani da habu sai wannan d'an wulak'anci wadda ya raina mutum shi za'a had'ani dashi Anya Baffah yasan ko waye Ammar da yake k'ok'arin had'ani dashi kou.".. "Dije !" Dasauri tafara k'ok'arin goge hawayen Fuskar ta Amma ta makaro Baffah ya riga yagani hawaye dake zuba a fuskar ta "Baffa kayi hak'uri banji shigowar ka bane " daganan bata sake magana duk'ar da kanta tayi domin data kuskura ta k'ara wani furucin kuka ne zai biyo bayan hakan. "Dije me kike ma hawaye ne kuma wane tunani kika tafi har nashigo nad'an jima baki sani ba?'' "Babu komai Baffah." "Dije ban sanki da k'arya ba shine yanzu zaki farayi man Shikenan." Juyawa yayi zai bar d'akin dasauri ta taso daga gadon innar ta durkusa kusada Baffah "don Allah Baffa na kayi hak'uri zan fad'a maka abinda nake ma kuka..". "Shikenan Dije ina jinki." "Dama "inna ce ta aikeni gidan kyauta mai magani na Amso mata maganin zazzab'i shine muka had'u da Habu yayi min bankwana da nasiha akan auren da zaka had'ani da jikan maigari..." Daganan ta sunkuyar da k'anta saboda zuciyar ta dataji tana yi mata zafi.. "Dije d'ago Fuskar ta na'am Baffah." "Bakya son wannan auren da zan cika Alk'awarin dana d'auka kou Shikenan Alhaji kabeer da yazo zan fad'a masa wannann abu bazai yuyu ba". Dasauri ta d'ago Fuskar ta "A'aaa Baffah kar kace haka banaso ka kasance k'aramin mutum mai karya Alk'awari a rayuwa nayi maka Alk'awarin bazaka sake ganin d'igon hawaye na akan wannan lamarin Baffa na.".. Murmushi yayi "Allah yayi miki Albarka Dije.". "Ameen Baffa na." ## Zaune yake cikin wani palour yana duba wata jarida sanye yake da glass da gani medical glass ne mai k'ara k'arfin ido wata mata ce babba ta shigo palour hannun ta rik'e da wani bowl rufe sallama tayi sannan ta sami guri ta zauna, "Uwar gida sarautar mata." "Hmm Abban Ammar kenan." "Ko bahaka bane Mamar Ammar da Aysha da Fateema. Murmushi kawai tayi ta bud'a bowl d'in k'amshi dambun naman kaji ya gauraye palour. "Abban Ammar ga dambu nama ya kamallah fa." "Ai tun kafin kishigo inan k'amshin ya isaman hanci." Jawo bowl d'in gabanshi yayi yasa spoon ya d'ebo ya nufi bakin shi "Kai yayi dad'i sosai har gobe ina Alfahari dake a b'angaren girki shiyasa bana iya cin girkin kowa sai na matata." Dariya tayi tana matuk'ar yadda Mijinta koda yaushe tun auren su ko dayaushe cikin yaba mata yake duk shekarun dasukayi tare. Bayan ta gama ya kamallah ne kallon shi tayi. "Abban Ammar kwana biyunan ko kunyi magana da Ammar ko?'' Yanayin shi ya canza dagani yana cikin damuwa "Yau kusan wata d'aya kenan tun ranan da yace man yana aiki har yanzu bai sake kira na nima." "Abban Ammar me ammar ke nufi yana neman ya maida mu ba iyayensa ba matar shi ta fimu muhimmaci Abban Ammar kuka ne ya kufce mata. Naja'atu kiyi hak'uri kidaina kuka kinji Kou nima kaina ina mamaki da wannan sauyawar hali ta Ammar wai Ammar ke gudun mu Amma nasan abinyi gobe Insha Allah zani gidan Akan maganar Alk'awarin da mukayi da Malam ibrahim Akan auren Ammar d'in bazan dawo ba sai an d'aura aure sannan na kirashi yazo ya tafi da matar shi" "Shikenan Abban Ammar Allah yasa hakan yafi Alkhairi Amma Abban Ammar ina cikin damuwa halin da Ammar ya canza kwata kwata kamar ba'a Ammar yanzu baya sauraren maganar kowa sai ta wannan matar tashi." . ''Karki damu komai zai wuce kamar ba'ayi ba." "Allah yasa.". "Ameen naja'atu." _Tofah gafa Dije na neman shiga gidan Feena ga kuma Ammar baisan da maganar aure ba sai an d'aura sannan a sanar dashi ya kuke ganin zai karbi abu??_ For Comment only 08164042255 _*HAFSY BABY🌹*_ [11/3, 10:47 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *15&16* "Inna kawo na ida miki girkin." Kallon fuskar ta tayi taga babu Alamun damuwa tattare da ita.Amma sai tace "A'aaa Dije naga baki jin dadin jikin ki shiyasa na fito nake gi." "Inna na warware fa dama kaina keyi man ciwo kuma ya daina yi man kwata kwata yanzu man." "Shikenan Allah sawwaka ina fatan kin fidda dukkan wata damuwa dake ranki akan wannan lamarin auren Addu'a kawai zaki cigaba yi kinji dije." "Insha Allah Inna dama tunjiya da mukayi magana da Baffah nayi masa Alk'awarin bazan sake damuwa akan hakan ba komai ya faru da bawa rubbatace daga Allah." "Yauwa Dije." Inna ki koma ki zauna ni zan idar da girkin yanzu." "Aa Dije." "Allah Inna zan ida". Hakan ta rarrashi innar ta takoma bisa tabarma ita kuma ta fara iza wutar girkin da innar takeyi tana cikin sharar gidan taji sallamar Laure cikin fara'a ta d'ago Fuska. "Laure harkin dawo daga gidan yaya Hassatun?" "Eh yau dasafe na dawo nagaji nayi kewar Innar mu dake shiyasa na tafo." Can kuma ta canza Fuska "ko dayake ke kin kusan tafiya ki barni ashe Ammar zaki aura d'an gun kawu kabir?" Dije canza Fuska tayi kama Hannun laure tayi suka nufi d'aki. Zaunar da ita tayi bakin gado "Laure wallahi ko kad'an bana son auren Ammar saboda na tsaneshi sannan kuma ina tsoron tunkarar zaman a gidan sa saboda irin wulak'anci da zani fuskata kina sane da irin yadda halin sa yake sannan kuma kinsan yadda matar shi take duka suna k'yamatar mutanen kauye fa laure wace irin rayuwa zanyi laure ki fad'aman nima ban san da maganar ba sai Baffa da ya fad'aman sadda Habu ya aiko kirana sannan ya sanar dani Alk'awarin da sukayi da kawunki Laure bazan iya ba Baffa na kunya ba ko kuma ya shiga sahun mutane masu k'arya Alk'awari na Amince da wannan abu Allah ya tabbatar da Alkhairi." Murmushi tayi ma laure wadda daka kalla kasan don dole ta k'ak'aro shi Amma bai kai zuciyar ta ba Laure kallon Dije tayi "Dije nima babu abinda nake tunani kenan tunda naji maganar a wajen Inna wai zaki auri Ammar mutum da ya tsani duk wani d'an kauye gashi ke kusan karo biyu kunayi dashi duk bakiji d'adin hakan ba ina da ance zakiyi rayuwar aure dashi Dije yakike tunani kuka zata fashe dashi dayake laure irin masu saurin kukan abin kad'an zai saka su kuka dasauri Dije ta rik'eta girgiza mata kai tayi "karki kuka kinji Aminiya ta Add'ua zaki man Allah ya tabbatar da Alkhairi cikin wannan Abun nima na daina kuka saboda Kuka babu maganin dazaiyi mana sai Addu'a kinji k'awalliya romon j'aba .." da dariya ta idar da magana ta kama kafad'un laure abinda zai sa ta dariya tayi wato Amarya Amadu Amadu kai ta Amadu bada kanki a asare kije kice ma Su Hajjo ya fad'i.". da dariya ta biyo ta har waje tsakar gida suka fara zagayewa inna kallon su tayi. "Laure wai sai yaushe zaku girma ne kuna Abu kamar k'ananan yara." "Inna Dije ce ke tsokana na fa.".. Sallamar Baffa ya katse musu magana dasauri Dije ta nufin gurin Baffa "Sannu da dawowa Baffa na yau ka dawo da wuri Baffah." "Wallahi kuwa Dije zuwan Alhaji Kabir ne ya sani dawowa ne." Gaban dije ya fad'i Amma bata yarda Baffah ya gani ba sai Innar ta data lura Kauda Fuska tayi saboda tana matuk'ar tausayin Dije. "Dije bari naje sai mun had'u anjima." Baffah kiran Laure yayi d'ibar mata rogon da kilishin da yashigo dasu yayi sannan ta tafi. Maido idon shi yayi ga Inna sai dije ta koma kusa da inna ta zauna. "Alhaji kabeer yazo cikin garinan yazo har inda nake shine nace maganar bazata yiyu muyita nan yaje zan koma gida zanyi magana da yaya jabiru komai yace zuwa gobe sai anyi komai domin yace yana so ayi komai cikin hanzari." "Allah to ya kaimu Malam."... "Ameen." Baffah maido kallon shi yayi ga Dije yaga ko fuskar ta tayi wani abu Amma baiga Alamun komai ba "Dije bakice komai ba." "Baffa na aini ba abinda zance komai kayi shine daidai Baffa." "Allah miki Albarka Dije. D'auko min fura ta d'aki." "To Baffah na." Tashi tayi cikin kuzarin ta tanufi d'akin Baffah don d'auko mishi fura.... Jingine yake a hannun kujera idon sa yana rufe Amma daganinsa kasan ba bacci yake ba domin kuwa ga lap top nan gabansa tare wasu takkadu a gaban sa Amma ya kasa komai tunanin Dadyn sa yake mamy sa kusan yau kwanaki biyu da suka wuce, Fitowa tayi sanye cikin wani mini sikert na roba ya wani matse ta sai wata vest marar hannu sai d'an cikin dake jikin ta anyi parking d'in gashi da wani k'aton ribbon ga cingum sai rangwad'a take babu inda tayi masauki sai jikin sa "Honey." Bud'a lumshashun idonsa yayi ya d'ora bisa idon ta wani yar! taji domin idanuwan Ammar yana rik'ita taji ta shiga wani yanayi "My Fee.". "Honey tunanin mekake ne haka har na tsaya baka sani bane meke faruwa ne?" Wani k'aramin tsaki yaja "Kawai ina tunanin Dad ne da mamy na." Gaban ta ya fad'in nan danan ta canza Fuska "Kamar yaro zaka zauna kana tunanin wai Dady da mamy ne.". "Eh saboda nayi kewar su sosai My Fee narasa dalilin da yasa na daina damuwa da mamy da dady kwata kwata ko na niyyae kiran su kona je sai naji nakasa Amma two days ina mafarkin su ya zama dole k'arshen watan ne naje." Bai jira maganar ta kawai ya mik'e ya nufi d'akin sa domin kuwa wannan tunanin da yayi har yaji kansa na mishi zafi. Feena binsa da kallo tayi har ya shige d'aki mik'ewa tayi sannan ta saki wani murmushi daganin sa na mugunta ne "Ammar kenan kana tunanin zan barka kaje ne ko kana tunanin zan zira maka ido ne har sunyi k'ok'arin had'aka da wata Hmm Ammar kai nawa ne ni d'aya a rayuwa mamy da dadyn ka kuma suyi hak'uri da kai domin kuwa kaina Nafeesa Taheer Bushasha ne duk kau macen datayi kokarin shiga gonar ta Hmm had'a hannu tayi tare da murmushi ta shige ciki wayar ta kawai ta d'auka ta latsa wata number "Hello Momy." nafessa yana ji muryarki hakan?'' Abinka dama da yar shagwba tuni ta fara narkewa. "Momy Ammar ne naji ya fara wai tunanin zuwa gida wai kwana biyu yana tunanin dadyn sa da mamyn sa kuma Momy kinsan in yaje lamarin nan ya b'aci zasu iya had'ashi da wata fa tunda ba sona suke ba." Cikin shagwab'a ta idar da maganar. "Haba! Nafeesa kamar dai baki dani a duniya kece d'iya tal fa danake da ita inhar ban share miki hawayenki ba wazai share miki ne? ki kwantar da hankalin kiji ko yanzu marece yayi dama Dad d'inki yaje Thailand shida wannan matsiyaciyar matar tashi gobe zanyi sakko naje gun Boka dukus komai kenan zakiga sakon kinji y'ar lelena." "Yauwa Momy na shiyasa nake Alfahari dake i luv so much Momy sai anjima." Bankwana sukayi ta kashe wayar wani Murmushi tayi ta kwance bisa gado "Ammar nawa ni d'aya ni Nafeesa Taheer bushasha duk macen datayi tarraya da Mijina zan iya halakata.... _Turkashi!!! kunji batu na Nafeesa taheer bushasha hhhh akwai chakwakiya fa_πŸ€’ _Inaji comment kuji wani anjima inkuma banji ba shikenanπŸ€·πŸ»β€β™€_ For comment only 08164042255 πŸ“šπŸ–Š [11/3, 10:48 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *_17&18_* _Afuwan Afuwan masoyana dajina kwana biyu kuyi hakuri kunsan dai ba haka nake Amma insha Allah bazaku sake jina shiru ba har sai na kamallah muku mata ko baiwa._ _Dije na gaisuwa tana gaida masoyanta_❀ _Amma har yanzu banga na Ammar da Feena_πŸ˜‚πŸ€’ _Godiya ga d'umbin masoyana da yan uwa da abokan arziki da suka tayani murnar zagayowar ranan haihuwata wallahi bazan iya lissafa ku sbd yawanku nagode nagode abinda zance Allah saka muku da mafificin Alkhairi ya biya ma kowa bukatansa ta Alkhairi_ _Washe gari_ Dije tana sharar tsakar gida tana gyara gurin tumaki da awakin dake d'aure. "Dijen Baffah aiki aketa yi ne?" "Baffah na kusa kamallawa ma." Durkusa tayi har k'asa "Baffah ina kwana." "Lafiya lau." Inna ce tafito daga d'aki baffa kallon Inna yayi "Bari naje gurin yaya jabeeru kafin rana tayi." "To.Allah kiyayaye." "Baffah na Allah kiyaye." "Ameen Dije." Baffah fita yayi ya nufi gidan yaya jabeeru wadda babu Nisa tsakanin sa da gidan sa. Yana isa k'ofar gidan yaga yaron shi yafito ''Aaa mannir." "Kawu ina kwana." "Lafiya lau munnir yaya jabeeru yana ciki ko?'' "Eh kawu yanan bai kai da fita ba." "Yauwa koma kace ina magana don Allah.".. "Kawu bazaka shigo bane?''. "A'aaa muneer jeka fad'amasa dai ina waje." "Tam kawu." Baffah jingina yayi da bango yana jiran Fitowar aiken da yayi bada jimawa kuma sai ga Muneer d'in

Chapter 2 of 11