meta arasa domin naga basu dawo da su da zanji dadi nayi murna na rabu da k'aya"
K'arar waya ne ya katse abinda yake zaro ta yayi daga Aljihu sunan Daddy ya gani yana yawo a screen d'in jim yayi kamar bazai d'aga ba can ya d'aga har takusa tsinkewa
"Hello Daddy."
"Kana ina ne ina ta kiran wayar ka har zata tsinke baka d'aga ba."
''Daddy na shiga toilet ne"
"Ok ka Amshi passport d'in Khadeeja A hannun naja'atu kaje kayimata duk abinda ya kamata ayimata kaje kayi mata tunda gobe zaku tafi kaje kayi muku duk wani shirye shirye."
Kit Daddy ya kashe wayar Ammar bin wayar yayi da kallo kawai wasu hawaye yaji masu d'umi suna mishi zarya wata zuciyar tace mishi "kawai ka gudu ba dole bane ka zauna da ita idan suka nemeka suka rasa zasu hak'ura."
Wata zuciyar yaji tana fad'a masa Ammar kana son ka had'u da fushi ubangiji kuwa da zaka ki bin umurni iyayenka kana son kaga daidai a rayuwa kaje kayi abinda mahaifinka ya umurce ka."
Cikin sanyi jiki ya nufi cikin gida iske Fatyma yayi jikin Mammy kwance tana ajiyar zuciya sallama yayi mammy kasa kasa ta amsa tare da cewa ka biyo ta nan ne kasake dukan ta ne akan matar taka ko yayane ?"
"Allah ya huci zuciyar ki Mammy ba dukan ta zanyi ba wannan ma Kuskure ne bazan iya jure azagi matata gabana ba Daddy yace nazo na amshi passport ne."
Mammy bin Ammar tayi da kallo ciki tsantsar mamaki wai bazai iya juri a zagi matar shi gabanshi ba
"Bansan ko wane passport kake nufi ba mai mata wadda ya zabi matar shi akan kowa nashi."
"Bahaka bane Mammy passport d'in wadda ake kira matata.''
Mammy kallon Ammar tayi domin abinshi har fara bata tsoro."
Zage jikkar ta tayi ta d'auko passport "Fatyma d'auko min paper da biro."
"To Mammy."
Bada jimawa ba ta dawo rike da biro da paper Mammy Amsa tayi ta rubuta abun da za'a buk'ata (Mammy tayi karatu har NCE)
Mik'a ma Ammar tayi Amsa yayi kawai ya fita duba paper yayi yaga sunan Dije ne da wani abun da za'a buk'ata tsaki yaja tare da shiga motar ya nufi Ameenu kano international airport saida ya biya banki ya fiddo isasun kud'in dazasu isheshi komai sannan ya shiga airport d'in da yake ba bako bane akan shiga jirgin kuma yana da Friends sosai wajen cikin minti 20 yagama komai, jirgi zai tashi gobe zuwa lagos karfe 12 pm na gobe sannan ya fito,
"Mammy bakya gani ya Ammar kamar bashi ba Anya ba Asiri matar shi tayi masa da baiji maganar kowa sai ita kamar tsoron ta yake fa Mammy."
"Kul kar nasake wannan jin maganar bakin ki babu wani asiri son da yake mata ne yayi yawa shi yasa karki k'ara kawo haka a ranki tashi gayacan ana sallar magariba mu shiga ciki."
___________ kundedene take saboda ita kadai ciki n d'aki duk tsoro ya kamata ba Fatyma kusa bare ta dauke mata kewa ga ciki ta yana mata murd'ewa saboda haka period d'inta yake mata zai d'auke sai kadan da zai dinga d'iso mata amma anjima in zai dawo cikin ta zai ta murda mata Yadawo da yawa. tashirya dama cikin Always wadda yagana ta bata tunda ta lura tana period, A haka har bacci ya d'auke ta mai matukar nauyi.
*WASHE GARI*
*SUNDAY*
*10:am*
Duk wani shiri da yagana zatayi ma Dije tayi Dije kuwa sai kace wadda tayi shekara cikin turare domin duk inda ta wuce sai kaji tashin kamshi turare mai sanyaya zuciya ga wani had'i da ta had'ama Khadeeja wadda sai saka jikinta sheki da kyau sosai da wasu turare domin Mammy ba kananan kud'i ta ba yagana ba wajen 200k ta aje mata shiyasa take shirya ta bana wasa ba wajen karfe 10 yagana ta kira Mammy akan ta kammalah shirya Dije. mammy tace bari ta turo a d'auke ta kafin ta iso duk tayi ma Dije bayani yadda zatayi ma amfani abubuwan kawai tace mata na kamshi ne don ta lura kamar Dije batasan komai akan rayuwar aure ba Amma harda abubuwa dazasu kara rikita duk namijin da ya kusancen ta,
"Kai Khadeeja wannan k'amshi da kike fitarwa fa kamar kinyi wanka da turare fa kinji yadda motar nan ya d'auki kamshi."
"Kai Aunty fatyma."
Allah serious kamshi kike sosai mai dadin ji."
Dije sunkuyar da kai tayi tana murmushi a haka har suka iso gida,
Mammy ta jinjina ma yagana itama domin wani kamshi da Dije ke fitarwa a jikinta ga wasu ta had'osa da ita d'aki Mammy d'aki taja Dije.
Tea ta had'a mata mai kauri duk da Dije tace ma Mammy tayi Breakfast haka ta bata tea d'in tasha, sai dataga ta shanye sannan ta kalleta.
"Khadeeja a yau zaku tafi lagos karfe 12, nasan ki da hakuri don Allah ki kara da wadda kikeyi kinji ko wata rana sai labari zakiyi farin ciki wata rana komai yayi zafi maganin sa Allah kizamo mai biyaya ga mijinki in har abinda zakiyi mai kauce ma tsarin Addini ba kiyishi kinji ko Zaki ci riba gaba zakice nafada miki hakan kuma zan dinga kiranki ki kasance mai b'oye sirrin mijinki khadeeja kinga matar Ammar ta girmeki ki kasance mai bata girman mata koda yaushe banda fitina koda ta nemiki da ita karki biye mata kinji ki barta kawai."
Mammy dakewa tayi ma Dije nasiha domin idon ta tab yake da hawaye Dije fad'awa tayi jikinta ta fashe da kuka Mammy kasa daurewa tayi itama ta fashe da kuka haka Fatyma tana shigowa taga Mammy da Dije suna kuka itama dorawa tayi haka Daddy ya shigo ya iske su kamar wadda akayima mutuwa Dije da fatyma suna bisa cinyar Mammy sai rifzar kuka suke,
"Haba Naja'atu kamar wadda akayima mutuwa bafa mutuwa bace haba naja'atu kuyi hakuri kunji.
Kar nima nafara cikin zolaya ya ida maganar bai bar d'akin ba sai da ya tabbatar da sunyi shiru sannan yayi yabar d'akin, sannan fatyma da Mammy suka fara shirya kayan Dije wadda ba duka aka had'a ba Mammy ta rage wasu ciki katon trolley ta had'a mata duk wani abu da zata buk'ata.
11:30
Su mammy harda Daddy suka fito domin zuwa airport Ammar wadda yasha kyau cikin k'ananan kaya fuskar sa d'aure ko hak'orinsa baka gani haka suka shiga mota suka nufi airport su jira mintina da ya rage ya tashi,
Suna tsaye Ammar ya koma gefe d'aya sai ga wata akori kura ta tsaya kusada inda suke kara dubawa nayi hangowa nayi ashe Hafsat musa true fans ne kowace rike da jikar ta kaya wai rakiyar dije ne zasu lagos Ammar jiyayi sun ishe airport din da hayaniyya Daddy dasu Mammy dariya suke masu ganin yadda kowa ke kokarin tsayawa kusa da Dije cikin Fushi Ammar ya iso gun wata tsawa yayi musu karo da juna suka dinga yi suna yada jikar su nemansu nayi narasa su duka lol ashe duk matsorata ne.
Kiran passenger aka farayi har akazo gun su Ammar kallon Daddy yayi da Mammy "zan wuce Dady."
"Ammar batada kowa garin lagos don Allah ka kula da matar ka nabaka Amanar Khadeeja Ammar Allah kiyaye kada ka cutar da ita Mamy ce mai magana zuwa tayi ta had'a hannu Ammar da Dije "Ammar ka kula da ita kaga bata tab'a shiga jirgi ba kabita a hankali don Allah."
Ammar wani shock yaji Amma daurewa yayi yaja ta suka nufi jirgi tanayi tana waiwayan mammy da dady da Fatyma har suka ida shigewa jirgi suna shiga ya cire hannusa "bagidajiya yar kauye stupid girl tsaki yaja ya zaunar da ita da karfi kusada kujera da yazauna ba ajima ba jirgi yafara lulawa a sararin samaniya a hankali ya nufi lagosβπ»
_*AMATALLAHπ*_
[11/14, 7:47 PM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??_*π·
_*BY AUNTY* *HAFSY*_ π
_*INDON KAUYE*_
*70*
_Don Allah kutasauyaman ga typing ga Editing ga turawa a groups duk ni daya Amma wasu sukan biyoni private na tura musu wasu pages na mata ko baiwa ko kuma na dinga tura musu ta private don Allah kuyi man Afuwa ba wulakanci bane saboda wulakanci ba hali na ba ne kun sani kuma,ku tambaya a groups nasan zaku samu insha Allah sai in baku samu zaku man magana bazan ki tura muku ba Amma kutausayaman_π’
_*ILOVE YOU MY FANS*β€_
Jirgi yana fara tashi Dije daddafe k'ujera da take sama tayi domin ji tayi zata fad'o ga wani kugi dataji yanayi fashewa tayi da kuka tare fara Addu'ar duk da taxo bakin ta Ammar kallon ta yayi ganin yadda idanuwan mutane suke kallon su jawo ta yayi da karfi har kanta yana karo da k'ujera "da Allah kiyi ma mutane shiru bakyauyar banza kinja idanuwan mutane duk sun dawo kanmu wallahi Daddy ya had'oni da bala'i wai wannan xan kira wife d'ina."saka mata belt d'in yayi sannan ya zauna, jirgi yana ida tashi sai ga Dije kuka ta fashe dashi tare da sakin wata k'ara Ammar gani yayi kawai ta langwabar da kanta ta sume Ammar cikin tsoro ya jawo ta kusadashi robar ruwan dake kusadashi ya kwarara mata fuska firgice ta tashi doctors d'in cikin jirgin suka nufo gun Dije Ammar dakatar dasu yayi tare da yi musu magana da Turanchi saboda turawa ne basujin hausa ko kad'an
Ce musu yayi suje kawai ta farfad'o ba wani matsala, Dije dasauri ta mik'e ganin ta bisa kafad'ar Ammar tayi
Ammar d'an matsowa yayi "kawai kinja mutane kallo harka da bakauye mutum sai azata sato ki nayi shigar da ita a kirjin sa shiru Dije kawai tayi gabanta yana fad'uwa ga tsoron Jirgin da take ga tsoron Ammar da ke dankare da ranta ga fad'uwar gaban yadda zata tunkari lagos bata san kowa ba,a haka wani nauyayan bacci ya d'auketa a kirjin Ammar wadda ya shigar da ita Ammar saukar numfashi yaji dubawa yayi yaga bacci ne ya d'auke ta tsaki yaja tare da k'ara kallon ta yarasa dalilin da yasa kawai bai gajiya da kallon Fuskar Dije tunda ya diro kano kawai yana shawa'ar ya kalleta ziririn hancin ta da d'an mitsililn bakin ta ya kura ma ido muryar yaji ana tambayar shi akwai abinda yake buk'ata girgiza kai yayi wucewa tayi Ammar gyara ma Dije kwanciyar yayi tare da jan wani tsaki ya rintse idonsa yana tunanin wace magana zaije ma Feena akan Dije wacece ita a gareshi tuno da mafarkin da yayi da sauri ya bud'e idon sa tare da dafe kansa yana tunanin abinda zaije ma Feena dashi domin ko kiran ta ya kasa yi saboda tashin hankali.
Mammy sai da taga tashin jirgin su Ammar ajiyar zuciya ta saki wani tausayin Dije yana kwaranya mata a zuci tasan Ammar yadda ya amshi auren nan ta yaya zai rik'e dije A matsayin matar sa ta aure ne ga matar shi wadda batada ladabi ko kad'an
"Naja'atu tunanin me kike ne? Muje mana."
Ajiyar zuciya tayi Daddy Ammar ina tunanin rayuwar da Khadeeja zatayi ne hannun Ammar kana kallon yadda ya nuna bashi ra'ayin aure nan fa gashi ba kowa gareta lagos ba balle ta dinga ganin sa tanajin dadi."
"Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru kinji Kidaina wannan tunanin Ammar zai kula da ita sosai kuzo muje fatyma."
Mota suka nufa suka shiga suka tafi Mammy da fatyma zuciyoyin su cike da kewar Dije.
*MURTALA MOHAMMED INTERTIONAL AIRPORT*
*A* hankali jirgi yafara saukowa har ya sauka inda yake daidai wajensa bayan d'an wani lokaci passanger suka fara fitowa Ammar kuwa idon shi ya maido da Dije dake baccin ta har yanzu bai san ta farka bane kawai lamo tayi Dije wani rankwanshi taji a kanta zabura tayi zata mik'e kasawa tayi saboda belt d'in dake jikinta waigowa tayi taga Ammar ne yasakar mata rankwanshi a tsakiyar kanta, duk'ar da kanta k'asa tayi kawai mswtt sai ki taso muje kuma wakika aje sai d'aukar miki trolley d'in Ammar d'aukar yar kamar jikar sa yayi yayi gaba Dije da sauri taja trolley d'in tana jefa kafar ta inda taga Ammar ya saka tashi Ammar yasan zata iya k'ara bashi kunya gaban mutane tsayawa yayi tare yimata magana cikin Fushi "wallahi ina takaicin jerewa dake bare ace musan juna dake ai sai ayiman dariya "
"Kayi hakuri ya Ammar."
Wurga mata harara yayi
"Wane hak'uri ba cin an riga an cuceni za'a haddasa min tashin hankali."Fizgo ta yayi suka ida saukowa wani gefe ya koma fiddo wayar sa yayi ya danna number john driver d'in office d'insu yazo ya d'aukesa a airport hango Dije Yayi ta had'a kanta da trolley wani tunani kawai ya d'arsu cikin ransa murmushi yayi wadda tunda Daddy yasanar dashi auren sa Dije baiyi ba nufar inda Dije take yayi..........βπ»
_Wayyo Allah Me Ammar Ke shirin aikatawa da yasa shi murmushi neππ»ββ_?
_Muhad'u next page_
_Kaina ke ciwo shiyasa na dakata daganan_π€
_*AMATALLAH*π_
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels