yafito "Kawu yace ga shigo." "Tom Shikenan muje."
Shiga sukayi Baffah sallama yayi yaya Jabeeru Amsa yayi yana zaune k'ark'arshin inuwa bisa tarbama
"Haba! Audu sau nawa zan fad'a in kazo ka dinga shigowa Amma sai ka tsaya daga waje kayi magana dani sai kace bak'o haba! Audu."
"Yaya kayi hak'uri Kana da iyali fa in da nashigo na tarar da iyalanka yanayi da bai dace ba fa?''
"Hakane Audu sai kadinga tsayawa daga soro." "Shikenan yaya ina kwana."
"Lafiya Lau antashi Lafiya ya wajen su halimar da dijen ne?"
"Duk suna Lafiya lau Yaya."
Shiru ne ya d'an biyo bayan sun gama gaisawa baffah gyaran murya yayi sannan ya fara magana "yaya dama Akan maganar Dije ne da gurin D'an Alhaji kabeer Ammar"
"Eh Ina sane da maganar Audu Amma naji shiru har yanzu in har bazaiyi ba menene na jira sa ne? Sai naga kamar abarshi kou?"
"Aa yaya jiya Alhaji kabeer d'in yazo har gurin da nake yace yazo ne akan maganar yana son ayi komai cikin hanzari tunda an riga anyi maganar komai yana son Kafin ya tafi ma An d'aura auren shine nace sai gobe zamu zo nayi magana dakai."
"Tam Alhamdullah dama komai sai lokaci yayi ake yinsa Audu to yanzu kamar wane rana kake gani?"
"Yaya ai duk yadda kace lafiya lau amsar ka kawai nake jira in yazo wurina ko zuwa anjima ne sai nafad'a masa."..
"Shikenan kace masa nan da mako d'aya za'a d'aura auren."
"To yaya Allah ya nuna."
"Ameen Audu Allah kajikan Baba da Inna Allah kak'ara had'a kan zuri'ar mu wadda ko bayan ranmu zamuyi Alfahari da ita."
"Ameen Yaya Ameen yaya."
Baffah bankwana yayi ma Yaya jabeer ya mik'e ya fito gidansa ya nufa inna kawai ya iske cikin gidan sallama yayi ya shiga "malam har kadawo daga gurin yaya d'in ?"
"Eh nadawo."
Tashi tayi ta d'auko shimfid'a masa tabarma kaba tayi zama yayi idonshi ya maida gare ta munyi magana da yaya jabeeru nan mako d'aya mai zuwa za'ayi komai."...
Tus!!! Sukaji fashewar tulu k'asa dasauri Baffah ya juyo Dije tsugunee
"Subhanallah Dije meyafaru ne.''
dasauri ta had'iye wani abu da yatsayama a mak'oshi Amma yakiya ya wuce daurewa tayi Baffah ban lura bane ba nayi tuntunb'e "
Badai kiji ciwo ba kou?"
"Eh Baffa banji sai d'an yatsan da yake man rad'ad'i Amma kad'an."
"Sannu kinji"
Dije tattara tulun tayi tana fakaitar Baffa da inna tana share hawayen da ambaliya a fuskar ta Amma ta makaro Inna tuni ta lura Amma ta kyale ta.
Dije tana gaba kwashe tulun da ya fashe
''Inna bari nashiga d'aki kafin ranan tayi sanyi naji kaina na min ciwo."
"To Allah sawwaka kinji magani nan rufe da kwarya sai kisha."
D'aki ta nufa durkushewa tayi waje guda
"Mako d'aya zan zama matar Mugu azzalumi wadda bai d'auki d'an kauye mutum wadda farkon had'uwa dashi mugunta ce to Matsayin me zance gidanshi mata ko baiwa?
Baffah ko bai jima ba cikin gida Alhaji kabeer yayi sallama dashi fitowa yayi rik'e da tabarma suka shimfid'a cikin wata itaciya dake k'ofar gidan "barka da zuwa."
"Lafiya lau malam audu."
Gaisawa sukayi.
"Nazo ne dama naji yadda akayi domin da maganar na kwana cikin raina."
"Karka damu Alhaji ban dade da dawowa da gurin yaya jabeer ba d'in kuma munyi magana yace nan da mako d'aya insha Allah mai zuwa."
"Yauwa Alhamdullah masha Allah dama bana so ad'auki wani lokacin data wuri na ma ana iya d'aura wa gobe Amma mako d'ayan kamar gobe Allah ya nuna mana lafiya" Ameen."...
"To sai magana ta gaba malam audu ban lura maka d'awaniyya komai karka wahalar da kanka daidai da cokali duk na d'auki d'awaniyyar komai."
"Haba Alhaji kuma.."
''Karka ida malam audu Dije ko ba yaron wajena zata aure inayi mata komai ai ban fad'i ba saboda d'iya ta ce kuma zaman arziki ke caza komai karka damu don Allah karka ce komai. Ni mai yima d'iyar komai ce a fad'in duniya ko bawani mun had'a gari d'aya fa."
Nan Alhaji kabeer ya kashe ma Baffah jiki da
kalamai har ya amince.
***
Hidima tsakanin gidan Baffah da gidan mai gari inda Mamy mahaifiyar Ammar da k'annensa Aysha da fateema duk sun iso a gidan mai gari duk suka sauka b'angare guda aka basu suna hidimar biki
Dije Fuskar bazaka kallah kace tana cikin farin ciki ba ko bak'in ciki ita kad'ai tasan yadda takeji a cikin ranta ta b'oye damuwar ta ne kawai Amma cikin ranta tashin hankali ne dank'are cikin ranta tana tunanin yadda zata tunk'ari gidan Ammar take.
''Wallahi Mamy ina farin ciki da wannan auren da yaya Ammar zaiyi nifa da bana k'aunar matar tashi ko kad'an gani na da ita d'aya Amma naji kwata kwata batayi man cikin raina ba to wai mamy duk ina yaya Ammar d'in ake wannan hidimar bai zo bane.?"
"Dadyn ku yace bazai sanar dashi komai har sai and'aura sannan zai kira shi Yazo ya tafi ta matar shi."
Fateema dake gefe tana saurarean maganar Mamy da aysha kallon su tayi "mamy wai meyasa Yaya Ammar ya canza hallayer sa ne nifa ko kiran sa nayi baya d'auka."
"Aiki ne yayi masa yawa shiyasa."
"Mamy..
"Banason jin wata magana kiyi abinda ke gabanku."
Shiru sukayi domin sunga kamar ran mammy ya b'aci
"Aunty aysha kizo muje Gidan da matar da yaya Ammar zai aura..."
"Ok tashi muje."
"Mammy sai mun dawo"
"Adawo lafiya ku gaishe ta."
Fitowa sukayi suka nufi gidan su Dije lokacin ita kuma tana wani b'angare daga cikin gidan itada su laure sai wasu k'awayen su domin gobe d'aurin aure kusan dama akwai da kara tuni gidan ya cike da dangin inna da dangin Baffah sai hidima ake.
Sallama sukayi nan fa kallo ya dawo kansu anga bakin binni tarbasu akayi cikin mutunchi nan suka gabatar da kansu na kannen angon, karramasu akayi sosai sannan aka kaisu b'angaren dasu dije suke dasauri Laure ta taso .
"Yaya Aysha."
"Laure k'awayen Amarya anan kenan"
Dije ko tanaji Laure ta Ambaci yaya Aysha tasan k'annen Ammar ne dasauri ta jawon kallabin k'anta ta rufe
"Laure ina yayar tamu."
Laure nuna musu Dije tayi tanaja Kallabin k'anta ta rufe fuskar ta.
"Dije ki bud'e Fuskar mana."
Dije kin bud'e fuskar ta tayi Fateema tashi tayi ta nufi gun datake
"Haba Amaryar yaya kunyar mu kikeji ne keda zaki shigo cikin mu ki bud'a fuskar ki mana"
"Daky'ar Dije tana bud'a Fuskar ta Aysha da fateena kuma cikin ransu yaba tsantsar kyawu suke na Dije don ma tana rayuwar k'auye da birni sai ta dinga had'a go slow. Saboda kyawunta inda ta k'ara burgesu ga kunyar dake gareta lalai yanzu yaya Ammar zaiyi aure.
Dayake wayayu nan y'an boko nan suka shige cikin k'awayen Amarya duk sun girmesu aka cigaba da shewar dasu.
Rik'e take da hannunshi ta kwantar da k'anta bisa kafad'ar shi
"Habibi ina k'aunar ka Hubby na farin cikina."
Shafar Fuskar ta yayi tare da had'a bakin shi dana ta ke haske ce a rayuwata inasonki sosai Matata abin Alfahari na ina k'aunar ki k'aunar ki da basan adadin ta ba.".
''Nagode mijina"
Shagwab'e Fuska tayi
"Ni ka goyani."
"Shikenan tashi muje."
Guje guje suka farayi cikin gida irin na masoya har sai da ya rungumeta jikinsa tare da had'a bakin shi da nata yana sinsinar gashin ta "ina kaunarki matata ni dake har abada...."
Wata k'ara tayi tare da mik'ewa firgice daga bisa gado sambatu tafarayi
"Wallahi Ammar nawa ni d'aya ba wata shegiya kinyi k'arya ko wacece ki shigo rayuwa ta ni da mijina."
Tuno yadda tagansu a mafarki tayi wurgi ta farayi daga dake kusa da ita, kamar mahaukaciya dasauri ya shigo d'akin ya tarrada da ita tana wurge wurgen kaya ..
πβ
[11/3, 10:48 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA ???π·_*
_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_*19&20*_
_Gaisuwar sada zumunchi gareki_ _rahamatullah_ _Hajiya_
_Bansanki baki sanni ba ina mik'o gaisuwa lodi lodi muna matuk'ar jin dadin novel d'inki mai take muk'addari ne Amma fa kija ma sakeena kunne in batai wasa ba zan ture ta gun Sageer nashigo saboda abinda takemana yayi yawa fa sbd ni ta gun Sageer ceπ― bawani deeniπ Ehhe nagaisheki yar uwa Allah k'ara baseera da hazak'a_
"My Fee lafiya meyafaru ne?"
d'ago Fuska tayi ta kalleshi idon ta don tsananin bala'in kishi har sun koma jajaye wani haushin sa taji mafarkin da tayi yadawo mata yadda Ammar kema wannan wadda har ta farka bataga Fuskar ko wacece ba.
Rushewa tayi da kuka ta cigaba da rikito kayan saman mirror
"Wallahi ko wacece k'aryar ki kishogo rayuwa ta da Ammar har ki had'a jikin dashi."..
Ammar ta baya ya shammaci Feena wadda ta koma tamkar zarara mahaukaciya ya riketa
"My Fee wai menene keda na barki kina bacci Amma sai kawai na jiyo k'ararki me yafaru.?"
tusa k'anta tayi cikin k'irjinsa fashewa tayi da kuka babu kaukautawa kamar an aiko mata mahaifinta ko mahaifiyar ta tarasu
"Don Allah My fee ki sanar dani abinda ke faruwa kin barni cikin rud'u da tashin hankali sanadiyyar zubar hawayenki menene?"
Zaunar da ita gefen gadon da yake yayi tare ta d'ora bisa cinyarshi ya kwantar da ita bisa kafad'ar shi aikin rarrrashin ta yafara sai da yaga tayi tana ajiyar Numfashi sannan ya maido hankalin shi gare ta.
"My Fee sanar dani ko hankali na ya kwanta kinji Baby na"
"Uhumm uhumm mafarki nayi yanzu kana.."
Murmushi yayi ya kalli Feena "yanzu Fee wannan shine kika rud'e daga mafarki ina tare da wata a mafarki shine zaki zama tamkar zarariya haba Fee mafarki ne fa."
D'ago Fuskar ta tayi ta kalle shi "My Ammar komai zaka kira ni ka kirani koda ko mahaukaciya zaka ceman na Amince indai akan ne na Amince My Ammar baka kayi mafarkin na shiyasa kake ganin bana ita iya aikata komai akan hakan."
Ammar kallon ta yayi "karki damu My Fee Ammar naki ke kad'ai kinji ko baby na mafarki ya daina rud'ar dake mafarki ba gaskiya bane." Rungumeta yayi jiki suka fita palour ya zaunar da ita "zauna ki huta naje na gyara d'akin da kika b'ata."
Gyad'a kai tayi tare da kwantar da kanta a hannu kujera tana k'ara tunanin mafarkin da tayi Ammar da wata mace.
###
_K'arfe 10 : Am_
K'ofar gidan masallaci cike da mutane motoci jere tunda daga shigowar ka wannan k'auyen zaka san ana wata hidima saboda yadda garin ya d'auki taron mutane ta ko ina sai hidima ake.
can na jiyo cikin lasifika Ana magana an d'aura auren *AMMAR KABEER DA KHADIJA ABDULLAHI* akan sadaqi naira dubu hamsi gashi ya biya nan fa aka d'auki wata sabuwar hidima
Dije tana d'akin kwance ta kundudune laure taji akanta
"Dije tashi and'aura aurenki da Ammar yanzu su Kawu suka dawo gashi can ana hidima k'ofar gidan mu."
Dije wata zabura tayi kamar ba ita ke kwance ba
''Mekikace Laure.....???"
_Iya comment d'inku iya typing_π€¨π€·π»ββ
πβ
[11/3, 10:49 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA ???π·_*
_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
Laure cikin tsoro ta kalli Dije ganin yadda ta zaro mata idanuwana ga jikin ta dake da matsanacin zafi
"And'aura aurenki nace Dije ya kike Abu kamar baki san komai ba?"
dije rushe wa tayi da kuka tare da komawa tayi ta kwanta.
"Shikenan And'aura man aure da wannan mugun Azzulumi wayyo ni dije na shiga Uku."
Wani ciwon kai ne ya dirar mata tare da wani zazzab'i mai zafi laure gani tayi Dije na karkawara nufar tayi
"Dije meke Faruwa ne?"
Batayi mata magana sai wasu hawayen dake zarya a kuncin ta.
"Bari na kira Inna."
Sauka zatayi daga bisa gadon Dije rik'e mata hannu tayi tare da girgiza mata kai cikin wata murya tana rawa tace
''A'aa lau..re kar..ki kirata..
Akwai wani magani.. Acikin waccen kwar..ya bani na sha.."
Dasauri Laure ta nufi wajen kwaryar da Dije ta nuna mata ta d'auko mata maganin ta sha
"Dije daurewa zaki don Allah kinsan yanzu taron ne zai dawo nan za' a zo a tafi dake inda aka ga kuma yanayin ki ya canza za'a iya zargin wani abu azo ana ta cece kuce ki daure don Allah yanzu kinga su Talatu da haule sun shigo."
"To Laure karki damu bara na daure suna cikin magana sukaji gud'ar wasu ayarin mata dasauri dije ta goge hawayen fuskar ta tajawo wani mayafi ta rufe fuskar ta.
Ayarin matanan nashigowa da guda duk kan Dije yana k'asa,
Wata k'anwar inna ce ta nufi gurin lauren kamo Hannun ta tayi ta d'ora mata wani zane da murjani irin na mutanen da ana saka mata nan fa aka sake d'aukar wata gud'a sannan kuma ta shiga Fesa mata wani turere a jiki nan fa guri ya sake had'ewa da wata hidima irin tasu. Amma kan dije yana k'asa jikin mayafi hawaye keta zarya a Fuskar ta.
Su aysha da fateema suna gefe suna kallon irin Al'adar tasu abin yana basu sha'awa yadda sukeyi abubuwan su,
Nan wasu dangin innar da baffah suka d'auki Dije wani d'aki aka nufa da ita wanka ne aka sata ta sillo tana fitowa aka bita da wasu turarinka masu k'amshi kitso akayi mata guda hud'u duk sun zobo a fuskar ta gudu biyu, biyu sun baya har gadon bayanta sannan aka bita da lilishe irin nasu na kauye sannna aka lullubuta aka tafo,aka d'ora bisa wata k'ujera,
Nan fa aka kace sai dangin ango sun sayi Fuska sannan za'a bud'e Fuskar Amaryar su gani aysha bud'e Hand bag d'in ta tayi ta fiddo bundle d'in y'an naira 500 ta aje kusa da Amarya nan fa aka d'au wata shewa tare da hanayiyya domin duk wata amarya indai za'a sayi fuskar ta iyakar sayen 3k inko mijin mai kud'i ne 5k yau gashi na dije an bada 50k
Basu tsinke da Al'amarin ba sai da Fateema ta aje 10k saman na Aysha nan fa daga mai 3k sai 2k daga b'angaren ango sai da aka had'ama Dije 100k wooo nan fa guri ya kacame gari ya d'auka an had'a ma tsabar kud'i har dubu d'ari nan wasu suka dinga ji inama y'ay'an su ne zasu auri Ammar lalai dije ta more ta taki sa'a da aka d'aura mata aure da Ammar wannan tsabar kud'i data samu, d'inkin balinki na wasu,
Su aysha sun yaba kyawun irina na Dije duk ta yi kwalliyar kauye ga gashin ta da ya zubu da bayan har kafardar ta inada taji binni ai zata koma kamar ba ita ba zata koma balarabiya,
Aysha da fateema phone d'in su ka fito sukai ta d'aukar photo da dije kuma ita d'aya..
A haka akayi hidima aka watse ana kowa yana yaba wasu sunajin dama su Dije ta taki sa'a irin wannan Arziki ta tak'a wasu kam cikin k'awayen dije ji suke ina ma Ammar zai gansu yace yana son su ai da gudu zasu Amince da hakan,
Zaune yake office d'in shi aiki kawai yake har kanshi ya d'au zafi gashi wasu papers ne yake ma singing yana gamawa firji ya bud'e ya d'auko juice mai sanyi tunda ya d'aga sai da yaga yakusa shan rabi sannan ya aje.
Kwanciya yayi bisa wata doguwar k'ujera gashi ya kunna Ac. bada jimawa ba bacci ya d'auke shi.
Zaune yake a wani garden bisa wata k'ujera yake ga bowl nan aje apple ne yanyanke sai ayaba ya d'auko apple zai kai baki ji yayi an rik'e masa hannu
"uhhmm uhumm ni banyardaba kaci da kanka ba ni zani baka."
Murmushi yayi yana shak'ar k'amshi tureren ta mai saka shi wani yanayi jawota yayi ta fad'o jikinshi tureren ya fara shak'a tureren ta tare da shak'ar kamshi gashin k'an ta.
had'a bakin shi da nata yayi yafara tsotsa tamkar ya samu wani sweet mai dadi saboda taushin lebben ta jiyayi zai zauce, tura hannun sa yayi a cikin rigar ta d'aukar ta yayi ya d'ora a bisa wani carpet yafara sucking breast dinta yazo zai tattara gashin da ya rufe mata fuska...
K'arar wayar buga kyaure ya tadashi daga bacci da yake dasauri ya tashi dafe kanshi yayi yana tariyo mafarkin da yayi,
"Meke damuna?Naso naga wannan ko wacece murmushi yayi saboda mafarkin yayi masa dad'i, k'ara kwankwansa k'ofar akayi
"Sir nice an aikoni ne"
"Kije ina zuwa."
"Ok sir."
Tashi yayi ya nufi toilet d'in dake office yayi wanka saboda abinda ya gani.
"Yanzu don nayi wannan Dream d'in har mafarkin har wanka zanyi tsaki yayi ya kunna shower.....
_Kuyi hak'uri da wannan naso yafi wannan yawa wallahi ina asibiti d'iyar sister aka kwantar da ita kutayamu da Addu'a Allah yabata lfy_ππ»π’
πββ€π€
[11/3, 10:50 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA ???π·_*
_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_Afuwan posting danayi kafin wannan na mance ba san number ba 21& 22 ne yanzu zamu tashi 23&24_
_*23&24*_
_Dedicated to Beauty and princess_β€
Yana gamawa yafito da Alwallar sallar Azahar da ya makara baiyi ba carpet d'in sallah ya shimfid'a yayi yana gamawa ko mintin 5 beyi ba ya mik'e bai tsaya in add'uoi ba ya mik'e bisa k'ujera ya koma yana k'ara tariyo mafarkin da yayi, wayar shi ya jawo number sakatariyar shi ya kira, bada jimawa ta shigo Amsar files d'in Hannu ta yayi ya fara abinda zaiyi dasu,
Yana cikin aiki ne wayar shi tafara k'ara yana dubawa yaga princess d'insa ce wato Feena Murmushi yayi sannan ya d'aga
''Hello My Fee.''
"Hmm My Ammar duk kewar ta isheni cikin gida gashi inajin yunwa ga bebyn ka nan ya isheni ."
"Sorry My lovely kidaure ko indomie ce ki dafa kafin na dawo mana."
"Gaskiya nidai bazan iya ba ko tashi daga bisan gadon nan."
"Kiyi hakuri yanxu hakan papers ne gabana nake singing d'insu kuma yau zan bada su kici ko cake ne da lemo ne kafin nadawo."
Kit! Yaji ta kashe wayar
Dafe kanshi yayi can kuma ya cigaba da aikin da yake Amma baki d'aya hankalin shi yayi wajen feena."
Aje wayar tayi tana ajewa gun television ta nufa music ta kunna tare da kure Volume ta k'ure ta cigaba da juyawa dama daga ita sai wata riga wadda d'ame mata jiki bata ida kawo gwiwa ba wayar ta ta hanga tana haske gurin ta nufa dasauri ta d'auka ganin Momyn ce "hello Momy ."
"My daughter zoki bud'e man ganin a waje munzo ina ta kiran wayar ki baki d'aga ba."
Wani ihu tayi tare da aje wayar ta nufi k'ofa ta bud'e rungume momyn ta yi har suka shigo ciki cikin shagwab'a ta fara magana
"momy kinyi surprised d'ina bakece man kina zuwa ba"
"Sorry daughter banyi tunanin zanzo ba bane da da furera zan aiko ta kawo miki sakon ki sai naga kawai bari na kawo miki saboda nayi miki bayani sosai shiyasa na biyo jirgi kawai
"Wayyo Momy na i luv so.much kina k'aunar farin ciki na."
"Nafeesa ke d'aya ce tilo fa da nake da ita in bansaki farin ciki ba waxan saka ne.?''
"Hakane Momy ina Dad?"
Tab'e baki tayi har yanzu basu dawo daga Thailand d'in ba shi da wannan yar iskar matar tashi ba."
"Mommy yanzu Dad yadaina kulani."
Hmm wannan makirar matar tashi shegiya tsinaniya ta ina zata yadda ya kulaki Amma na kusa Maganin ta."
"Mommy bari na kawo miki ruwa lemo yau My Ammar baiyi mana girki ba ya fita nikuma bazan iya shiga kitchen ba."
"Ta yaya ma zaki shiga kitchen da wannan nauyi jikin ki meyasa Ammar d'in bai kawo miki house girl ne? Tunda yaga abinda ke tare dake ko baki da ciki bai kamata ma komai na gidanan kiyi shi ba saboda ba baiwa na kawo mishi ba."
"Momy ninace bana son House girl ne kinsan y'an matan lagos d'inan da saye zuciyar miji fa
(Irin su jidda da salma lol) Ko mijinka bai niyyar kula su sai kiga sun rinjayeshi kuma bani keyi shi komai da ya dawo daga office."
"Aikin boka dukus yana kyau kenan.''
''Gaskiya Momy aikin shi yana kyau ai na yardashi hundred percent tunda har yayi man silar auren Ammar dole na jinjjna mishi Momy."
Boka dukus kenan jikan boka katalu uban shaid'anu ai kowace buk'ata indai kika kukan gun boka dukus ta k'are shike share mana hawaye koda yaushe
_Waiyazubullah_
"Gaskiya ne Mommy dole a jinjina mishi."
Feenah tashi tayi
"Momy kawai bari naje restaurant nayo miki take away."
"Ok Baby kiyi tuki a hankali kinga dai abinda yake tare dake."
"Ok Momy..
D'aki ta koma wani wando pencil ta d'auko blue ta d'ora wata din riga top, pink ta sa inka kalle ta bakace wa ta iya hausa balle har tasan wata kalma musulci wasu takalma masu mad'auri da tsinin su, tasa wani figigin mayafi ta d'auka ta yafa jikinta key d'in mota ta d'auka tare da bud'a wata looker ta d'auki kud'i tafito,
"Mommy bari naje na dawo."
Kallon ta tayi
"Baby sai kindawo ki kula da tuki ba banda na ganganci ina jiranki."
"Tom Mommy kissing d'inta tahi a gefen kumatu sannan ta fita, ta shiga mota.
Mommy gyara zama tayi ta k'ura television ido tana kallo remote ta d'auka ta fara canza tasha,
After 40 minutes
"Kitabbatar da kinyi wannan hayak'in kuma ya shakeshi sai kuma wannan ki tabbar kin sa mishi shi abinci da kuma juice,
Kin kayi wannan abun daughter zaki k'ara mallake Ammar fiye da tunaninki domin zai koma sarauniya shi kuma bawa zai dawo a k'arkashinki."
Wani ihu ta saki tare da rungume Mommy ta
"Wayyo Mommy naji d'ad'in haka bari na tashi na zuba mishi cikin take away d'in danayi ya kusa dawowa"
"tashi maza tou.''
Feena dasauri ta tashi ta juye abincin cikin wani.plate kulli maganin ta d'auko ta barbad'a ta motsa sannan ta aje lemon da yafisha ta d'auka ta zuba ta girgiza sannan ta d'auko ta aje a dinning table,
''Mommy nagama."
"Yauwa Baby''
''Mommy muje na kaiki d'aki huta zakiman kwana biyu ko?"
"A'aa daughter gobe zan tafi yanzu ma don nayi marece da yau zan tafi."
"Kai Mommy."
"Nafeesa kar customers suzo banan."
"Shikenan Mommy."
D'aki guda takaita mommy ganin yadda d'akin yayi kura ita tacire mayafin tashiga gyara shi.
Feena palour ta dawo tana jiran dawowar Ammar ta aiwatar da abinda takeso k'arar doorbell taji dasauri ta mik'e ta bud'e jikinsa ta fad'a ''welcome My Ammar ."
"My Fee."
Haka ta rungumasa suka shigo ciki My Ammar kaje kayi wanka Abinci yana jiranka nasan zaka dawo da yunwa."
Cikin mamaki ya bita da kallo..
ππ
_Nagode da Addo'inku taji sauki sosai nagodeβ€_
[11/3, 10:50 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA ???π·_*
_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
_*25&26*_
_Dedicated to Beauty and princess_
"My Fee abinci fa kikace yana bisa dinning table yana jira na?"
"Eh mana My Ammar Mommy ce tazo fa shine naji restaurant nayi mata take away shine nason zaka dawo da yunwa shine na shirya maka komai a dinning table,
''Thank you Luv kamar kinsan inajin yunwa Muje nafara gaida Mommy sai naje nayi wanka sai naci Abinci."
"Ok Honey bunch."
Jakar da ya shigo da ita ya aje bisa k'ujera,
Sak'ale hannunta tayi kaf'ad'ar Ammar suka nufi Room d'in, Mommy tana kwance tayi d'ai d'ai kamar irin d'akin ta bata tunani ko surukita zai iya shigowa kowane lokaci,
Feena kuwa har suka shiga bata sauke Hannunta daga kafad'ar Ammar ba, shigowar Ammar yasa Mommy mik'ewa zaune daga bisa gadon da take Ammar gaida ta yayi sannan
"Lafiya Lau Ammar mun same ku lafiya?''
"Lafiya Lau Mommy ya wajen su Daddy?"
"Lafiya lau duk yana gaisheku dafatan babu wata matsala ko?"
"Babu komai."
"To Alhamdullah nima nazo gun wata k'awata da bata da lafiya anan legos take shine Baby tace sai na kwana gobe na tafi,"
"Gaskiya Mommy gwara ki kwana