Share this page
zuwa gobe sai kitafi kinga yanzu marece yayi da wuya kinsamu jirgjn da zai tashi ma." "Ai shikenan." "My Ammar kaje kayi wanka abinci fa yana jiranka." Mik'ewa yayi ya fita Feena gyara kwanciya tayi bisa duguwar k'ujerar dake d'akin tayi bata nuna Alamun zata bishi ba wayar ta tacigaba da latsawa.Momy sai taga yafita yad'an jima da fita sannan Mommy ta kalleta. "Ina Fatan kingama komai ko daughter?" "Mommy nagama komai jira nake yafito daga wanka yaci abinci sannan nayi wannan hayak'in." ''Yauwa daughter." After 10minutes tare suka fito bayan yayi wanka ya zira jallabiya fara mai gajeren hannu sumar tashi luf sai kyalli take Feena k'ujera taja ta zauna tare ja ma Ammar yazauna jawo plate d'in tayi, ta k'ara ya mutsa shi d'auko spoon tayi "My Ammar yau ni zan baka Abinci da kaina." Murmushi yayi "Tam My fee." Murmushi wadda keda manufofi, d'ebo Abinci tayi ta nufi bakinsa Ammar Babu bissimallah ba neman tsari daga shaid'an , ya bud'a bakinsa Feena ta bashi abinci rik'e spoon d'in yayi my fee nima bari na baki abinci kou?'' d'ebo Abinci yayi dasauri ta rik'e sa "bana iyaci My Ammar yau babyn mu babu abindaa yake buk'ata sai Ice cream konaci zan iya Amai." Cikin tausayi ya kalle ta sannu my Fee." "Yauwa my Ammar" Lagwab'ar da kai tayi kamar da gaske Ammar jawo juice yayi wadda tuni Feenah ta aje gabansa tsiyayi a cup ya sha, tsikar jikin sa yaji ta tashi baki d'aya tana mishi yamutsa ga kanshi da yayi mishi wani dum tamkar and'ora dutsi a kanshi Feenah ta lura da yanayi da Ammar ya shiga murmushi tayi domin tasan aikin Boka dukus ne ya fara aiki tasowa tayi gabanshi "My Ammar meke damunka ne?'' "Kaina ne naji yayi min nauyi." Sannu kak'ara shan juice d'in may be kaji yayi sauki Feena d'aukar juice d'in tayi ta girgiza mishi sannan ta bashi Ammar tashi yayi domin ji yake babu abinda yake buk'ata irin ya kwanta ga magrib ta kusa Amma ina d'aki ya shiga, Feena dariya tayi "Lalai Aikin Boka dukus nayi bari naje na fad'a ma Mommy." Tashi tayi ta nufi room d'in da Mommyn tasauka. Wacece Feena? Nafeesa Taheer Bushasha shine cikaken sunan ta, Taheer Bushasha sunan mahaifin nafeesa haifafen d'an garin bauchi ne iyeyenshi sun bashi ilimin Addini dana boko inda har ya had'a digirin d'insa samun aiki yayi tsaye kullum shine bin kamfafanoni ko ya dace da aiki shine zuwa ma'ikata amma ina ba'a dace ba kullum firar shi cikin Abokai danasamu kud'i za'ayi Bushasha fa ko in yasamu aiki ko a gaban iyayen shi zai ce "Baba , inna in har nasamu kud'i zakuyi Bushasha fa za'ayi Bushasha da kud'i cikin abokai da cikin unguwa da ya zauna maganar kenan, har sunan shi ya koma Bushasha in ma bakace gidansu Bushasha baza'a gane ba K'annan shi biyu mata Zulaihat da Rukayya, Duk suna gidan aure, Yana cikin wannan burin aiki bai samu ba har ya gaji da zarya neman aiki ya hak'ura da yake kuma yana zuciyar nema ba da aikin office ya dogara ba haka yake fita yayi dako kud'in da ya samu yayo cefane ya kawo gida domin kuwa Yana tausayin su kwarai da gaske burin shi ya kyautata musu yasamu kud'i ayi Bushasha, Ana haka yasamu aikin koyarwa a secondary school salary sa da yafito zaiyi Bushasha dasu har su k'are sai da iyayensa suka dinga yi masa Fad'a Amma sai yayi Murmushi kawai yace Inna kudai Allah k'aro kawai ana hakan yana malamin makaranta soyaya ta kullu tsakaninsa da k'anwar abokin sa rahama, rahama yarinyar yace marar kunya bata ragama kowa y'ar bal'ai ce gata da son Abin duniya kawai ta Amince da Taheer da taganshi handsome kyakyawa kuma d'an gayu amma burinta yanan. Anyi aure Amarya ta tare a gidanta dake cikin gidansu taheer d'aki d'aya aka d'ibar mata bata girmama iyayenshi ko kad'an Amma gaban idon shi zata ta faran faran dasu kamar tayi musu sujjada, Amma ba yan idon shi rashin kunya kala kala mahaifiyar shi tayi niyyar yi mashi magana Amma mahaifin shi yace ta kyaleshi wata rana zai gani da ganshi. Rahama tana bak'in ciki matuk'a ganin yadda haidar ke d'awainiyya da parents d'insa wata rana ma zai iya siyo abu yace su ya siyoma su hak'ura wata ranan ya siya masu, Da yafita makaranta zata fito da dinga zabga masifa Amma ko kallon inda take inna bazatayi ba sai dai tayi murmushi ta cigaba da abinda take Wata rana tana cikin zazzaga ma inna masifa....rukayya da zulaihat suka shigo bata lura da shigowar su ba suga yadda take zazzzaga mahaifiyar su masifa ai da Allah ya had'asu suka rufe ta duka inna hak'uri take basu Amma basuji sai da sukayi mata lis har bazata iya tashi ba sannan suka ka kyale ta da jan k'afa ta koma d'aki tana rufzar kuka jin jikinta ya fad'a yasa ta d'auki mayafinta ba inda ta nufa sai gidansu, ta fad'i k'arya da gaskiya akan abinda sukayi mata,k'annen taheer, Shikam yana dawowa ya iske kannanshi suka gaisa ya nufi d'akinsa ya iske batan fitowa yayi yake tambayar su nan suka fed'e masa biri har wutsiya cikin tsananin b'acin ya kalli mahaifiyar shi haba Inna meyasa baki fad'aman abubuwan datake miki ba ashe Rahama dama rashin mutunchi ba iya ni ya tsayawa ba harda iyayena wallahi bata isa ba cikin tsananin b'acin rai ya fita ba inda yayi tsinke sai gidan su rahama... _Anan zan dakata insha Allah sai bayan sallah in Allah yakaimu zamu cigaba_ _Kowa ya ajeman nama sallahπŸ˜‹ da nawa dana Dije_ _Sai kuma na Ammar da Feenah_ _nasan sai sunfimu samun nama_🀨 Happy sallah in Advance πŸ“šβœ [11/3, 10:51 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _*27&28*_ _Alhamdullah dafatan_ _anyi sallah lfy my fans_ _Zamu d'ora daga inda muka tsaya Dije taga nama sallah tana godiya❀ Amma banga na Ammar da Feenah ba_πŸ™„ _Mekuke nufi😏_ _Dedicated to princess and Beauty_ Yana isa gidansu rahama bai shiga cikin gidan ba aiken yaro yayi ya kira ta sai taja aji sannan tafito tana yatsina ba gaisuwa bare sallama tafito ta gatsine "Lafiya ka aika kirana bancin y'an uwanka sun gama dukana sun ma tarar dangi shine kaima zaka biyoni har gidanmu toni na gaji da aurenka ai bakai kad'ai namiji ba"... "Rahama!! " dasauri ta kalleshi domin bata tab'ajin yayi mata wannan kiran ba "Rahama anfad'a miki uwa wasa ce ko a kasuwa ake zuwa ne ake sawon ta kin manta ne tsawon wata tara ina zaune cikin jikinta na hanata zama na hanata kwanciya zama dakyar zata yishi tafiya dakyar na hanata sukuni sanan azo ga nakuda ta mutu ko ta rayu duk wannan azabar nakudar takeji bayan ta haifeni sannan azo ga raino na nayi mata kashi, Fitsari a jiki nayi mata tumbud'i amma bazata damu ba tayi min wanka ta goyani a bayanta ga shayawar datake min nayi rashin lafiya hankalinta da natsuwar ta tarasa inhar ba lafiya nasamu ba bazataji dadi ba Rahama bazan iya fad'a miki iya Adadin muhimmacin da uwa take a duniya ba ke dakanki zaki san hakan kuma zaki bata matsayinta amma ke wai har kin kai matsayin da zaki wulakanta man iyaye wallahi babu macen a duniya da zan iya kallo ta wulak'anta ma iyaye inaji ina kallo ko da ko wani irin so nake mata a rayuwa ta kije na sake ki saki d'aya cikin Fushi ya juya ya barta gun rahama dafe kai tayi ta d'auka Taheer bazai iya sakin ta ba Amma gashi ya saketa ta d'auka rarrashin ta zaiyi su koma ta k'ara zuba wani mulki sai reshe ya juye da mujiya.... da kuka da gunji ta shige gida.. Taheer ko inna da baba sunyi masa fad'a akan saurin sakin da yayi ma rahama yayi saurin yanke hukunci da wuri dasai yayi mata uzuri kuskure ne zata gyara hakuri ya basu kawai yace babu yadda za'ayi ya zauna da macen da zata dinga ci ma iyayensa mutunchi bayan wata uku ne aka aiko rahama tana da shigar cikin Taheer wata uku Abokin taheer yayan Rahama hakuri yaba taherr domin kuwa bai garin komai ya faru baba da inna kuwa cewa sukayi tunda akwai wannan rabon yakamata tadawo d'akinta ta haihu sun sa yanzu tayi nadama dakyar Taheer ya Amince ya dawo da Rahama d'akin ta koma shiru tana yi ma su inna da Baba biyaya domin wata uku datayi gidansu, tasha wahala tunda suka gano laifin ta ne dukkan wani aiki ita keyinsa gashi babu wani isashen abinci tuwo ne gidan ta kuwa sai abinda takeso takeci Ana haka taheer yana koyarwa kuma yana tab'a kasuwanci saida atamfofi a cikin a kasuwa a cikin haka rahama ta haifu ta haifi mace mai kama da mahaifinta kyakyawace sosai yasa mata sunan mahaifiyar sa Nafeesa Yake cema ta Ummin shi Shekarar Nafeesa d'aya Kasuwanci atamfofi ya fara samun cigaba yana zuwa yana saro su ya kuma mallaki shagonsa na kansa har yasamu mataimaki, Bayan wani lokaci Allah mai azurta bawan shi A duk lokacin da yaso sunan taheer ya koma Alhaji taheer ya ziyarci d'akin Allah yakai iyayensa su rahama ankoma Hajiya wulakacin ya dawo sanadiyar an raba musu gida ya gina nasa yana kokarin bama Nafeesa tarbiyya zaman gidan dabaiyi nr sosai Baisan irin rayuwar da Rahama ta d'ora ta ba rahama bata son ganin laifin Nafeesa ko kad'an ta shagwab'ar da ita komai tayi daidai ne wajen ta ta taso yarinya marar tarbiya da rashin kunya, Alhaji taheer bushasha Allah ya d'aukaka shi yayi kud'i wadda yake yi irin na nigeria dana kashashen waje yazama hamshakin d'an kasuwa Rahama ta had'u da mata y'an Duniya wadda suke mallaka miji sai abinda suke so A haka Tayi wata Aminiya Hajiya ladi ita tabata shawarar mallake Alhaji taheer ba karkarda Hajiya rahama ta Amince sukaje wajen boka Dukus waiyazubllah.. boka dukus ya bata abubuwan da zatayi Amfani dasu tsafi gaskiyar mai shi daganan sai yadda Tayi dashii yarage kula da mahaifiyar shi wadda ita kad'ai ta rage masa Alllah yayi ma mahaifinsa rasuwa bada jimawa da dawowa daga aikin hajjin sa ya kwanta rashin Lafiya sai kannesa suma sunga canji Don ma Inna tana yin Addu'a domin tasa ba halin d'an ta bane hakan baya zuwa gaishe ta sai dai yayo aike Hajiya rahama dadin hakan takeji tana juya shi yadda takeso ga d'iyar ta tana yadda takeso inda tace zata cigaba da karatun ta a k'asar waje haka Dadyn ta yayi mata, komai tatafi England gida guda ya kamata ta nan fa sharholiya ta b'alle shaye shaye kala tayi Abokai maza da mata komai na bad'ala anayin sa cikin gidan Feenah bata cika shaye shaye ba sai in ranta ya b'aci bata kuma sex sai making love, barta da samari na tsiya da zuwa club kala kala tasan kowabe club a England, Tana shekarar k'arshe ne a degree d'inta ta had'u da Ammar inda yazo had'a Masters d'in sa sun had'u cikin school inda tana zaune taga giftar warshi ya wuce bin shi tayi da kallo har yab'ace mata dasauri ta kalli k'awar ta Khairi wadda itama yan nageria ce "Waye wannan Handsome guy d'in tunda nake kinsa ina tarraya daga turawa har bakaken Amma banga wadda ya tafi da tunani ba kamar wannan guy d'in waye shi?" Khairi dariya tayi Wannan shine Ammar Kabeer yana had'a master's d'insa ne yaro dan jan classa Akwai girman kai Friend d'insa d'aya duk fad'in school d'inan Haidar imran duk halin su d'aya basu kula kowa karatu suke kinga ko ba calour d'in mu bane don haka ki kyale shi ma." "Khairi kenan bakisan Halina akan abinda nasa ma raina ki zuba Eyes ki kallo wallahi sai Ammar ya soni bari kiga" Feenah mik'ewa tayi cikin shigar ta na riga da wando duk sun d'ame mata jiki ga wani yalolon gyale da d'ora bisa kafad'ar ta sai takalmata masu tsini hange tafarayi inda zata hango sa zaune da rangwad'a ta nufi gunsa. "Hy d'an samari barka da karatu jawo kujera tayi ta zauna Amma Ammar bai d'ago Fuskar shi ya kalle ta ba hankalinshi yanaga Book d'in da yake Dubawa Feenah Hannu tasa ta Amshi book d'in ''Haba kyakyawa kanajin ina maka magana zaka wani shareni.." Saukar marin dataji ne A fuska yasa ta kin k'arasa abinda zatace. ''Ke wace irin banza ce dakikiya meye had'ina dake ne tun kafin raina ya b'aci tashi kibar nan gurin idiot stupid!! " Feenah dafe kunci tayi tare da mik'ewa "Ni ka mara?" "An mareki d'in banza in baki wasa ba zaki saukar ma duka daga yanayin shigar ki baki da tarbiya bare ladabi." Feenah rike da kunci tabar gun gidan da dadyn ta yakamata wadda babu nisa tsakaninsa da school, ta nufa tana shiga bisa gado ta fad'a ko takalmin k'afar ta bata cire ba tana dinga wani nishi na b'acin rai tashi tayi Firji d'in dake kusa da ita ta bud'a bottle d'in giya ne tunda take bata tab'a sha ba sai friends d'in kwalbar kawai ta d'aga tasa ma bakin ta, daganan ta fara surutai, kala kala har khairi ta shigo ta iske ta hakan sai can bacci ya d'auketa. Ansamu kamar kimanin wata d'aya Feenah Allah ya jarreb'ace ta matuk'ar kaunar Ammar Amma kullum wulakanta da fad'a mata bakaken magaganu yake ko gaban waye, don ma Aminsa Haidar na tausar Amma Ammar yana wulakanta Feena tabi ta kod'e batada aiki sai shaye shaye, ta koma daga giya sai codien abincin ta a hakan Hajiya rahama tazo ta iske yar lelenta shalele cikin wannan halin, Feenah rusa mata kuka tayi tace inhar bata samu Ammar zata iya kashe kanta Hajiya rahama rarrashin ta yi tare da kwantar mata da hankali a takaice tare suka dawo Nigeria washe gari babu inda sukayi tsinke sai wajen boka dukus dake wani daji sosai ba tsoron Allah ba komai Hajiya rahama suka tafi tun kafin su fad'a mishi ya sanar dasu abinda ke tafe dasu cikin tsoron Feenah ta koma bayan Mahaifiyar ta lab'e boka dukus tambayar Feena yayi me takeso ayi ma Ammar cikin tsoro tace so take ya sota kamar hauka sannan ta aureshi boka dukus dariya yayi sannan yabata wani turere wadda zata shafa da Yajikamshi Shikenan sai wani kwali wadda zata shafa a ido dasun had'a ido shikenan haka hajiya rahama ta dire kud'i Feenan farin ciki kamar me ranan takoma England dama Dadyn tabai nan har tabar gidan bai nan yana Dubai a Business d'in sa TSAFI GASKIYAR MAI SHI Masu karatu a takaice tunda Ammar ya shaki kamshi turaren Feena ya had'a ido da ita shikenan ya rikece akanta yana mata wata Azababiyar soyaya ba jan aji ba komai feenah ta Amince suka fara wata mahaukaciyar soyaya itada Ammar Haidar yayi mamakin yadda Amininsa ya Amince da soyayar Feenah ba yajin maganar kowa sai ta Feenah Haka har suka kammallah karatu inda Ammar ya had'a master d'insa ita kuma Feenah Degree suka dawo gida suna manne da juna dare da rana bashi da lokaci sai na Feenah iyayensa sunyi mamakin canzawar halayarsa A haka har yadawo bayan ya dawo ne yasamu aiki a lagos inda yake aiki wani company na kera motoci inda yake inda yake A fanni b'angaren fitar da duk abinda zai shigo kuma zai fita sai da sanisa inda yake kwasar manya kudad'e suka bashi gida da mota Sai da akasha artabu sannan dadyn Ammar ya Amince da auren Feenah Ammar sai da Ammar ya kwanta rashin lafiya sannan amma sai da Ya fad'a mishi sharad'in sa ya Amince badon yaso ba saboda ya lura Feena batada tarbiya saboda yazo da ita ba kunya ba kawaici tunda ya lura da shigar ta mamy ma ba yadda suka iya haka suka Amince Amma dadyn sai da ya fad'a mishi da sharad'i Ya Amsa ne kawai don ya Amince ya auri sanyi idaniyar sa Feena.inda aka sha bidiri akayi bikin Feenah da Ammar suka d'aga sai lagos suke zuba soyaya inda yanzu Feenah keda shigar ciki na wata biyar tana yadda take so a gidan Ammar ga kuma taci Alwashin Ammar nata ne ita kad'ai. DAWOWA LABARI "Dije kinga yanzu zaku tafi gidan mijinki Alhaji Kabeer yace mijin naki yana lagos can yake aiki aiki ya rikesa shiyasa bai samu hallatar d'aurin auren ba Dije ki kasance mai biyaya kinji ko ki rike ibada kinsan aure bauta ne Karki Abinda mijinki ran shi zai b'aci ki kasance mai ladabi ga duk abinda yasakaki ki zauna da Abokiyar zamanki Lafiya inki shiga wani hali ringa Karatun Alqur ani shine mafita ki dinga Add'ua Dije Alllah yayi miki Albarka dije kin sani Farin ciki kin sani na cika Alkawari insha Allah zaki farin ciki da wannan abu komin daren dad'ewa Dije Kuka ta fashe dashi jikin innar ta ta fad'a inna itama kuka ta fashe dashi "Dije Allah yayi miki Albarka Allah yabaku zama lafiya kinji Dije." Saida Baffah ya rarrahesu sannan matar Kawu jabir ta kama Dije suka fito suka shiga mota dije tanata dirzar kuka Laure tana gefen ta itama kuka take a kunne ta ta yi magana Dije d'aga kiga Habu namiki bye bye dasauri Dije ta d'ago Fuska Habu ta gani yana d'aga mata hannu fuskar sa da hawaye da hawaye Dije tafara saki itama tana d'aga masa hannu har sukayi nisa Matar kawu Jabeer kamo Dije tayi ta d'ora a kafad'ar ta dije shashekar kuka kawai take tana tunanin yadda taga Habu suka d'aga sai kano ta dambo tumbi giwa... Rabuwar masoyana na sanya kuka ido😭 _Tofa ga dije and'aga binni ya zata k'are ita da Feenah da Ammar muje zuwa_ πŸ“šπŸ–Š [11/3, 10:51 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _Dedicated to beauty and princess_ *_29&30_* "My Ammar har kashirya ne fita ne?'' Kallon ta yayi cikin wata zazzafar k'aunar da yakeji rungume ta jikinsa yayi "Eh zan tafi muna da wasu bak'i ne kuma dole sai sun ganni sannan." Kuma Mommy kasan jirgin da zata tafi Around 8:30 zasu tashi fa kuma yau na tashi jikina ba dad'i bazan iya tuki ba ya za'ayi ne?" "My Fee duk yadda kikeso hakan zanyi indai ranki zai farantu da hakan kinsan bana son b'acin ranki." "So nake muje kaje mommy airport sai ka maido ni gida sannan sai ka wuce office d'in." Ammar kallon Feenah yayi "My Fee bakiji yadda nace ba bak'i gareni fa Around 8 kiyi hak'uri please zan turo driver mu na office ya kaiku pls my Fee." Dak'atar dashi tayi da hannu cikin b'acin rai "Kaga kayi tafiyar ka basai ka kawo man wata magana Mommyn tawa ce bazaka iya kaiwa kawuce kayi tafiyar ka office banason jin komai." dasauri Ammar ya tari Feenah dake shirin barin waje "haba My fee pls kiyi hak'uri kinji bari na kai Mommy d'in sannan na tafi." Feena kallon Ammar tayi batayi magana ba. "My Fee ki saki ranki mana ko hankalin Ammar ya kwanta." dariya tayi "shikenan Amma kason ban cika son nayi magana ba kayi man gardama." "shikenan Angama My β™• queen." "Fee ko ruwan tea ban samu ba? Kafin na fita office.?" ''Babu nima mommy ta had'a min nasha.". "Ok ina Fita office nasamu." "Ok bari naje naga Mommy ta idar da shiryawa." D'akin da Mommy ta sauka ta nufa iske Mommy tayi tana saka sark'a a wuyan ta. "My Mommy zanyi kewar ki sosai." ''My daughter karki damu bazan dinga call d'inki zan tafi ne dadynki ya kirani gobe zasu dawo shida wannan makirar matar tashi. (Alhaji taheer yak'ara aure inda d'iyar k'anwar innace ya aura ansha daru kafin anyi auren inda inna ta dage da Add'ua akayi auren inda yanzu suna yayan uku tare maza biyu mace d'aya rabi'atu matar da ya aura mace ce mai kirki da son Addini tana dage yi ma mijinta addu'a dare da rana) "Mommy ni banga Abinda Aunty rab'iatu ke maki kika tsane ta tana girmamaki fa." "Daughter kenan bazaki tab'a ganewa ba ko duk wannan duk munafurci da kissa irin nata." "Mommy ga Ammar can fa zai kaiki airport." "Ok" d'aukar hand bag d'inta tayi tare cewa "ina kika baro Ammar d'in?" Yana palour." ''Ok abinda zan fad'a miki kinga komai ya canza ne?" "Mommy nagani sosai bakiga gani ba yanzu yadda yake man da raina ya b'aci." "Shikenan baby sai munyi waya." Haka suka fito jere sai kace wasu k'awaye doguwar riga ce jikinta bak'a gyala gyalen tayi suka fito Ammar yana jingine da k'ujera yana ganin su ya mik'e." "Mommy har kin fito." "Eh Ammar zanj tafi gobe Dadyn Baby zai dawo ne." "Ok Muje." Feena kallon Ammar tayi bangane ba Ammar wazai rik'e wad'ad'anan kayane na hannu mommy ni zan rik'e ko ita kasan dai ba lafiya gareni ba babynka yana tak'ura man." Ammar cikin kyarma ya amshi Hand bag d'in Yafito. Mommy kallon y'ar ta tayi yadda ta fara zuba mulki tun yanzu. "Daughter kirage ma yi mashi hakan. Mana." "Mommy ni kad'ai nasan wahalar da Ya bani inason Ammar har cikin raina kema kinsani Mommy ina tuno abinda yayi man ne nake mishi." "Daughter kenan." Haka suka fito Feenah ta kwantar da kanta bisa kafad'ar Mommy. Ammar dama ya bud'e musu bayan mota mommy ta shiga sannan Feenah ta shiga Ammar kallon ta yayi "My fee ki dawo gaba mana." "Anan nake son zama ka rufe murfin mota muje time yana tafiya." Ammar yaji ciwo cikin ranshi yau shi aka maida driver Amma ya rasa Abinda ke damunsa bazai iya yima Feena gardama ba. Haka ya rufe murfin mota suka nufi airport. Wajen parking d'in motoci Ammar ya nufa yayi Feenah hana Mommy ta bud'e murfin motar tayi "Waka aje ne dasai bud'e mana murfin ne?'' Ammar murfin ya bud'e suka fito maidawa yayi ya rufe cikin sigar Alamun rarrashi ya kalli Feena "Please my Feena kinga na fara samun kiran daga Office kiyi hak'uri naje sai nasa driver office ya mai daki gida." Wani mugun kallon ta watsa mishi. "Wallahi babu inda zaga sai jirgin su Momy ya tashi kamaidani gida sannan in kuma office d'in ya fini Muhimmaci kawuce katafi." Juyawa tayi ta koma kusa da Momyn ta Ammar komawa yayi ya jingina da mota yana jin wani b'acin rai, Amms babu damar yayi magana domin shakkar Feenah yake sosai. A haka aka fara kiran sunan har akazo wajen Mommy, Momyn Feena k'ara bata wasu shawarwari tayi tare da fad'in sai sunyi waya a hakan suka rabu tana d'aga mata hannu Jikin Ammar ta kwanta ta shagwab'a "my Ammar nayi kewar Momyna kamar na bita mutafi tare nakeji." "Kiyi hak'uri zamuje kinji My Feena." Haka suka shiga mota "My Ammar inajin yunwa mu biya restaurant inason pizza πŸ• ne " Ammar kallon ta yayi babu yadda zaiyi domin yana matuk'ar gudun b'acin ran Feenah. Saida aka shafe 10 minutes sannan aka basu sannan ya nufo da ita gida nan ma sai da b'ata mishi lokaci bai isa office ba sai a round 9 har bak'in sun fara shirin tafiya don ma ya rarrashesu sosai sannan suka hak'ura sannan suka fara meeting d'in. β˜… β˜† A hankali ta bud'e idon ta daga baccin gajiyar da tayi domin basu iso kano ba sai cikin dare mik'a tayi tare da addu'ar tashi daga bacci kallon Laure tayi dake ta sharar baccin ta bisa gadon da suke kallon d'akin tayi tsaftace yake sai tashin k'amshi yake komai tsaf gado ne sai mirror ciki sai wadrope tashin Laure ta farayi "Laure! Laure!! " Bud'a idon ta tafarayi a can kuma ta mik'e tana mintsinar ido "Dije har safiya tayi ne?" "Eh mana bakiga har rana ma tafito fa.'' "Wallahi Dije naji dad'in bacci shiyasa kai binni akwai dadi sosai." Dije kallon ta tayi tare tab'e baki "Har dad'in binni kikeji nikam nafijin

Chapter 4 of 11