daf da Khairi ta mik'a mata kunnen ta rad'a mata wata magana..
Ganin nayi Feena tayi dariya sun tafa da khairi sannan suka kafa cup d'in da suka had'a syrup da coke a bakin su....
_________________ Juye Juye kawai take a bisa gadon da take kwance ga baki d'aya ta nemi bacci ta rasa a idon ta tun maganar da Fatyma tayi mata wai tana ganin yaya Ammar da ita zaya lagos tashi tayi xaune ta jinginar da pillow jingin gado ta jingina dashi "Allah sarki Baffah da Inna ta ina kewar sosai duk da inajin muryar ku da Habu na Aura ina kusa daku bana rabuwa daku. Sai wannan mugun mijin Azzaluma da aka auraman."
Dasauri ta kori shaid'an domin tunanin Habu taji zatayi kallo zoben hannunta tayi tuno nasihar da Habu yayi mata tayi Kuka ta fashe dashi dasauri ta toshe bakin ta gudun kada tada Fatyma dake bacci hankalin ta ya tashi saukowa daga bisa gadon tayi ta shiga toilet Alwallah ta d'auro ta shimfida carpet d'in sallah tafara salatin ga Annabi Muhammad s.w.a tana karatun Alqur ani iya ida ta hardace cikin kanta tunda batada halin taba izif sittin tunda batada tsarki jitayi damuwar tafara raguwa daga xuciyar.
_Wai idan kina fashin sallah kice bazaki kusanta da ubangijiki kan ya sausata miki wani abu dake damunki Aaa zaki iya Alwallarki lafiya lau kinemi sausauci daga ubangijinki domin Allah mai jin rokan bayinsa ne_
_*SATURDAY*_
8: 20 am
Bud'a idonta tayi hankalinta hasken rana tagani kallon ida take kwance tayi taganta bisa carpet d'in sallah Amma an d'ora mata pillow kallon kanta tayi taga anzare mata Hijabin dake jikinta Add'uar tashi daga bacci tayi turo kyauren d'akin akayi Fatyma ce tagani
"Khadeeja harkin farka? Mammy ce dama tace na barki kiyi baccinki ki gaji yanxu ma na leko ne naga kintashi ne Breakfast ya kammalah."
"Wallahi kuwa Aunty fatyma bacci ne ya d'aukeni bansan ma nakai wannan lokacin ba, Ina kwana."
"Lafiya kalau Kahdeeja ya karfin jikin yanxu?"
"Alhamdullah."
Masha Allah yanzu jeki kimtsa sai kizo kiyi Breakfast d'in ko."
"To Aunty."
Fatyma fita daga d'akin tayi Dije mik'ewa tayi ta nufi toilet tayi wanka ta gyara jikinta tsaf sannan ta fita wasu riga da zane na Atamfa ne tasaka sunyi mata cif a jikin ta gwanin kyau turaren tasa wadda sai kamatso kusada da ita zakaji kamshin sa zira silifas ta fito Ammar yana kai dankali bakin sa yayi Arba da Dije jiyayi ya kware wani tari ya farayi nan danan idon sa yafito........
_*BATTERY LOW*_
_Hy people kuyi hakuri da dajin shiru hidama ce mukayi Amma Alhamdullah mu kamallah yanxu zandawo daidai yanzu Amma kusani da comment dinku zai bani kwarin gwiwa duk da kunayi akara sai naji dadin yi muku da yawa in naji comment ya ratsani_nakuma yi muku akan lokaci_π
_*AMATALLAH*π_
[11/7, 8:02 PM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??_*π·
_*BY AUNTY* *HAFSY*_ π
_*INDON KAUYE*_
_*My people inayinku kamar yadda kukeyi da yar katsinawan dikko sosai gaskiya mata ko baiwa yana da matukar masoya inayinku ko ina kuke a fadin duniya*_πβ€
_*67*_
Fatyma dasauri ta tsiyayi ruwa a cup ta mik'a Ammar "Sannu ya Ammar Amshi ruwa kasha tarin ya lafa''
Ammar Amsar cup d'in yayi ya kafa a bakinsa sai da ya shanye ruwan duka ya aje cup d'in Dije cikin sanyi jiki da tsoron Ammar ta ida isowa wajen durkusa tayi ta gaida Daddy ya Amsa yayi mata ya jikin ta, sannan ta nufo gun Mammy tagaida ta cikin kyarma murya ta kalli inda Ammar yake kokarin had'a haruffa sunan shi tayi "ina kwana..ya Ammar"..
Ammar dakewa yayi Amma bai d'ago bakinsa taga kawai yayi motsi tasan ya Amsa mata.
"Daughter dawo nan kusa dani kixauna ya k'arfin jikin naki?."
"Alhamdullah Mammy.''
Yanzu bakya jin komai ko kuma wani waje yana miki ciwo ?''
"A'aaaa Mammy banaji."
Masha Allah jiki yayi kyau Haka akeso."
Itadai Dije zama tayi Amma daka
kalle ta kasan A tsorace take .
"Mezaki ci ne?''
Khadeeja? Custard ko tea ne?"
"Aunty fatyma tea d'in xan sha."
Da soyayan dankali xan had'a xan hada miki ko doya da plantain ne?"
"Soyayar doya kad'ai Amma bada yawa ba."
Haka Fatyma ta had'a mata tea d'in da soyayar doya d'in ta mik'a mata d'auka tayi zata bar wajen saboda gaskiya bazata iya cin wani abu gaban Wannan mugun ba "Khadeeja ina zaki?"
Mammy xan shiga ciki ne."
"Meyasa.?"
Dije duk'ar da kanta k'asa tayi Mammy tuni ta fahimci yanayin ta da abinda take nufi,
"Shikenan jeki kiyi breakfast d'in d'aki."
"Amm Khadeeja in kin gama Breakfast d'in kizo ina nemanki a babban palour,"
"To Daddy."
Dije d'aki ta shige tafara shan tea d'in tana maganar zuci "kai gaskiya na k'agagara wannan mugun yatafi ko nasamu nasake sai wani d'aure fuska yake mugu kawai.".tanayi tana mita
Ammar kallon Mammy yayi suka had'a ido jiyayi ya koshi mik'ewa yayi zaya bar wajen yana goge baki Daddy tsayar dashi yayi "inason magana dakai a babban palour yanzu."
Ammar samun kansa yayi yaji gabansa ya yafad'i yaji Daddy yace ma waccen wadda bai san sunan ta ba itama yanason ganin ta a babban falo to *MEKE FARUWA*
"to Daddy."
Ammar babban palour ya nufa yazauna fiddo wayar shi yakira queen d'insa domin tun jiya da daddare yake danna mata kira Amma taki picking k'arshe ma yana kiran wayar yaji switch off da safe yana tashi ya kira yaji switch off yanxu ma try yayi yaji kuma ta shiga sai da ta kusa tsinke sannan yaji ta d'aga
"My queen Good morning."
Can k'asa yaji muryar ta
''My Ammar nad'auka ka manta dani ne ko an hanaka ka kirani ko."
"Queen tun jiya nake try number taki switch off ne."
"Ok na manta na kashe ta ne bana buk'atar hayaniya ne jiya shiyasa na kashe ta yaushe zaka dawo ne saboda banajin dadin girkin wannan yarinyar gaskiya in bana naka ba ga kwata kwata yanxu d'akinmu baya samun Queen"."
"Queen xuwa gobe zandawo saboda nayi kewar ki keda baby na."
Jiyayi tayi tsaki "Kaga my Ammar inada buk'atar ganinka gobe in kuma bazaka dawo shikenan kuma ina fatan har yanzu Alqawarin da kayi yanan."
"Queen bazan karya miki Alqawarin kece kad'ai matar Ammar."
"Dayafi maka zaman lafiya.
Kit takashe wayar Ammar bin wayar yayi da kallo shigowar su Mammy palour ne yasa daidaita natsuwar shi Daddy da Mammy samun waje sukayi suka zauna bada jimawa ba saiga Fatyma da Dije sun iso suma samun waje sukayi suka zauna.
Shiru ya ratsa palour can Daddy yayi gyaran murya
"To dukkan godiya ta tabbata ga Allah da yahad'a mu anan Ammar kasan dalilin da yasa kazo inason ganin ka?''
Ammar girgiza kai yayi gabansa yana fad'uwa
"A'aaa Daddy ban sani ba."
Zaka iya tuna sharad'inmu da mukayi dakai kafin auren ka da wadda kakeso ne?''
"Daddy na manta a game dame"
Daddy murmushi yayi "Ammar kenan ka manta inda nace maka kanada matar dana zaba maka ne ka kafe ga wadda kakeso na fad'a maka kuma duk lokacin sharad'i zaka auri wadda na zaba maka a matsayin mata a duk lokacin danaso muyi hakan dakai.?"
"Eh Daddy" munyi jikin shi yana kyarma domin shi tuni ya manta da zance ya d'auka Daddy ya wuce maganar."
"Yauwa daka tuna haka yau Kimanin wata biyu da ya wuce an d'aura maka aure da wadda na zab'ar maka a matsayin mata danakeso ka aura nakira kwanaki matar taka taki bari nayi magana dakai don haka ga matar ka nan khadeeja wadda yau kimanin wata biyu da d'aura maka aure da ita kuma da ita zaka tafi Lagos k'afarka kafarta zaku tafi babu wata jan magana da matar ka zaka tafi
Ammar d'ago idon sa wadda yayi ja saboda tsabar tashin hankali da rikici dayake cikin su wadda kwata kwata ban iya aunashi...........
_To my peopleπ€« kuhad'o kud'in jirgin tafiya lagos faπ wadda zashi dannar kirjin Feena Ammar yazai ya tunkari Feena da maganar_?
_Muje zuwa nasan ba haka kuka so ganin shi ba wallahi sai kunyi hakuri ba'acewa komai wallahiπ€« kudai ku cigaba da bina zamu kai inda kukeso_
_*AMATALLAH*_π
[11/10, 7:52 PM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??_*π·
_*BY AUNTY* *HAFSY*_ π
_*INDON KAUYE*_
_*68*_
_*Wasu nakirana ko sunyi man text message ko a WhatsApps nabasu complete d'in mata ko baiwa, Mata ko baiwa yanzu nake typing d'inshi bangama ba nagode masoyana*π_
"Daddy meyasa ba'asanar dani ba lokacin daka d'aura min aure sai dai naji kamar daga sama wai an d'aura min aure kimanin wata biyu da suka wuce Daddy"
"Kaine gaba damu ko mune gaba dakai kana sane da mune iyayenka? ba wasu don haka baka isa kasamu abu ba kace ka yadda za'ayi na fad'a maka tun wuri ka canza tunani"
Mammy ce take maganar cikin fad'a
Ammar sunkuyar da kansa k'asa yayi wasu hawaye masu d'umi yaji suna mishi zarya a kumatu tattare sa tsabagen tashin hankali magagunun Feena suka fara yi masa yawo a tsakiyar kai yadda take fad'a masa mik'ewa zai bai palour Daddy ya dak'atar "dawo ka zauna bamu ida maganar da nakeso dakai ba."
Jikin Ammar ba kwari ya dawo ya zauna "in har ka wulakanta Khadeeja don baka santa tamkar ni ka wulakanta saboda khadeeja y'ace a wajen saboda mahaifin ta Tamkar d'an uwa yake a wajena saboda kauyen mu d'aya dashi kuma aboki na Sosai kuma nasa hallayar sa nasan ko waye shi
shiyasa har nayi kwad'ayin had'a zuri'a
dashi nasan wata rana zakayi Alfahari da haka da kanka don haka banyarda da wulakanta Khadeeja ba yaushe zaka lagos d'in ?"
"Gobe saboda ban sanar a office ba zanxo."
"Ok kana iya tafiya kafin gobe Daddy juyowa waje Mammy "Naj'aatu sai kifara shirya yar taki kafin gobe kinji gobe zasu tafi."
"Angama Daddyn Ammar."
Ammar rai b'ace har baya ganin gabansa yatashi yabar palour yana shiga ya buga hannun sa da bango tare da fad'awa bisa gadon
"Tayaya Daddy zai min aure bansani ba ta yaya zan tunkari Queen da maganar wai Daddy ya had'ani aure da wata bagidajiya yar kauye wadda nafi tsana wai kauye Me Queen zata d'aukeni munafiki ko makaryaci ne bana son b'acin ran Queen bana son naga walwalar ta ragu a fuska wane irin matsancin tashin hankali ne zan fuskata Daddy meyasa kayi man haka wannan shine dalilin kiranka dakayi man, danasan wannan kiran ne da banxo ba garinan ba zan had'u da matsancin tashin hankali a gun Queen"
( _Kujiman Ammar kiran mahaifnsa yake cewa da yasani baizo ba Allah karemu da karewa da aiki sihiri_ )
Daddy juyowa yayi wajen Khadeeja bayan Ammar yabar palour d'in kanta na sunkuye k'asa tunda Daddy yafara magana ta sunkuyar da kanta hawaye cike da idon ta
"Khadeeja.''
D'ago fuskar ta tayi sai hawaye suka zubo "Na'am Daddy."
''Kiyi hak'uri akan hakurin da kike kinji insha Allah zaki Alfahari da aure nan ki kwantar da hankalin ki akan zaki mijinki lagos ki kasance dai mai yin biyaya ga aurenki domin ni mahaifinki ki d'auke ni tamkar Abdullahi Aure bauta ne na ubangiji kuma babu inda bashi kai d'iya mace a duniya ki kasance ko da yaushe mai biyaya ga mijinki zaki ga ribar biyaya da kikayi Khadeeja Allah miki Albarka Khadeeja kinji."
"Ameen Daddy."
"Tashi kuje Fatyma "
"To Daddy"
Fatyma kama hannu Khadeeja tayi suka nufi ciki Daddy ya maido kallon ga Mammy."
"Ku ida shirye shiryen da zakuyi kafin gobe xuwa anjima abinda babu kufita kasuwa a siyo shi."
Daddyn Ammar indai b'angaren kaya ne nasawa akwai wadda ma har yanzu bata d'inka su ba akwai kuma sabbi d'inkaku ma wadda bata sa da yawa sai dai abubuwa da ba'arasa ba."
"Shikenan zuwa anjima zan baki 150k ayi abinda za'ayi daganan sai ku shiga studio ayimata passport kinsa batadashi natafiyar ko"
"To Allah yakaimu."
Tashi kije ki k'ara kwantar mata da hankalinta Naja'atu.".....
Dije suna shiga d'akin ta fashe ma Fatyma da kuka ''don Allah Aunty Fatyma kice ma Daddy bazanbi ya Ammar lagos ba mugu ne shi da matar sa zasu iya aikata man wani abu ba sona yake zai iya komai don ya illatani Aunty fatyma kamar yadda yayiman a can baya Aunty fatyma kice ma Daddy abarni ni zan iya yi ma ya Ammar biyaya ko ina yake zan kare *MARTABAR AURE* dake bisa kaina"
Fatyma dafa Dije tayi yadda ta rikice
''Calm down Khadeeja ki natsu mana ta yaya kikasan Ya Ammar mugu ne kuma matar sa muguwa ce ina kika tab'a rayuwa dasu ina kika san su.?''
Dije tunowa tayi ko iyayenta bata sanar da irin muguntar da yayi mata a karin farkon haduwar su da yadda ya tsani yan kauye.
''Khadeeja ina saurarenki fadaman mana,a ina kikasan ya Ammar ne?''
Shigowar Mammy d'aki ne ya katse tambayar da fatyma take ma Dije.
Mammy nufar gadon da Khadeeja tayi tana kuka
"Daughter ki daina Kuka kinji ko ki kwantar da hankali kada ki tada hankali kinji ko kinason Kisaka Mammynki damuwa ne?''
Dije Girgiza kai tayi
"To kiyi shiru kidaina kuka kinji Zaki samu soyayar Ammar a hannunki ni dakai na fad'a miki hakan zaizo yana miki hawaye akan ki amince da soyayar shi karki damu da abinda yake miki wata rana zaki sha mamaki daughter na kinji Mammy kwantar da Dije tayi bisa kafad'ar ta tana rarrashin ta tare da fad'a mata wasu magaganu masu kwantar da hankali sannan tayi shiru.
"Yauwa Daughter jirani ina zuwa."
Mammy d'akin ta nufa wata loker ta bud'e da wani d'an k'aramin mabud'i wani garin magani ta d'auko sannan ta samu cup ta d'an zuba maganin kad'an madara peak ta gwangwani ta juye ta nufi d'akin su Dije
"Amshi nan Daughter maganin nan migayu ne kinji.
(Lol mammy taba Dije na wani sinadarin k'ara ni'ima ne wadda duk randa namiji ya kusance ta zai matuk'ar rikecewa akanta sauran bayani bakuji ta bakina sai in hakan ta kasance da dije)
Dije kafa kai tayi tasha wani bauri bauri taji Amma ta shanye saboda Mammy tace mata maganin miiyagune.
"Yauwa daughter.
Fatyma kushirya anjima zamu fita kasuwa."
"To Mammy."
_________Zaune take bisa dinning table suna Breakfast itada Khairi yamutsa fuska tayi tare da aje spoon da take cin Abinci tayi
"Khairi kinga har yanzu ko tsikara d'aya banji ba"
Karki damu kijira ko zuwa gobe ne kawai kisha overdose inhar bai ba kawai ki kwantar da hankalinki kiyi Amfani da shawarar da nabaki."
"Shikenan."
"Inaga A yau zan wuce Abuja fa"
Feena zaro ido tayi haba Khairi bazaki jira My Ammar ya dawo ba gobe zai dawo fa kina d'eba man kewar shi fa"
"Sorry kawata zanje Dubai ne ranan Monday kinga ko kafin monday zanyi shirye shirye tafiya."
"Amma am not Happy."
Haka ta dinga yagar abincin suna magana sama sama.
_______turo kyauren yayi a hankali ya shigo iske ta yayi zaune fuskar nan ta babu far'aa ko kadan Alamun bud'e kyaure taji d'ago fuska tayi ta ganshi maida fuskar tayi ga abinda take can yaga Dije ta billo ta wata k'ofa fuskar ta fayau sai wani kyali take cikin fusata Feena ta mik'e "My Ammar wannan wacece ne?" Shiru yayi ya kyaleta
Wata magana tak'ara cikin k'araji "ina tambayar ka wacece ne?''
"Matata ce"
Matar ka My Ammar gyad'a mata kai yayi "Amma kitsaya ki saurereni don Allah zan miki bayani Queen.."
"Dakata bakin munafiki mayaudari babu kalmar da zata fito bakin na saurereta kana zaton bana iya abinda nayi niyya ko kana zaton karyar ce nake zakasan ba'ayi ma Nafeesa Alk'awalin karya gani yayi kujerae datake sama ta d'aga ta zaro wata sharb'ebiyar wuka tayi "yanzu zan kasheka sannan na kashe matar da kake cewa taka ce'' sannan nima na kashe kaina nufo Ammar tayi da wukar da gudu Dije ta nufo gun ta tare Ammar Feena caka wuk'ar tayi ga cikin Dije jini ya fara tattara kamar famfo sharkab ta zube k'asa kallon Ammar tayi "kana ganin wasa ko nufo shi tayi da wukar ta luma masa da ciki.....
Cikin firgita Ammar ya tashi daga baccin daya d'aukesa tare da wannan mumunar mafarkin da yayi kallon d'akin dayake ciki yayi tare da kallon cikinsa ajiyar numfashi yayi tare da dafe kai yana tariyo mafarkin da yayi ajiyar zuciya kawai yake jikin sa yana wani irin kyarma tare tunanin yadda zaiyi da Feena.
________________wajen karfe 4:pm Mammy suka shirya suka fito zasu kasuwa domin Dije ta shirya cikin wata atamfa yellow mai d'igon ja ta d'ora Hijab ja tayi kyau masha Allah, suna fitowa Ammar yana zaune palour Mammy suka wuceshi Dije ce bayansu cikin sanyi jiki ta wuce Ammar tsaki yaja tare da fad'in "bagidajiya yar kauye."..Dije kawai taji abinda yace saboda su Mammy sunyi Gaba maida hawayen ta tayi kada hawayen dake niyyar zubo mata mammy ta gani.
Sun shiga kasuwa Mammy ta siyo ma Dije wasu tsadadun turirinka masu matukar kamshi da matuk'ar tsada domin kuwa bata sai mata da d'an kasa da 10k wadda k'amshi su dabam yake
Sai abubuwan da ba'arasa domin komai na Amfani na b'angaren kwaliyya Dije tana dashi
Mammy zab'ar mata chocolate da biscuits masu dadi da tsada tayi daganan suka shiga studio d'in dake kusada super market d'a suka shigo aka d'auki Dije photo aka wanke akabasu, daganan gurin wata mace ce yar sudan Mammy ta nufa mammy suka shiga itada yar Sudan d'in d'aki mai suna yagana tafad'a mata shirin da takeso tayima Dije domin gobe zasu bar garin yagana yar sudan tace ma Mammy tunda tafiyar gobe ce tabar ta takwana zuwa gobe sai ta dawo.Mammy kiran Daddy tayi ta sanar dashi cewa yayi tabar ta haka Mammy tabarta akan za'ayi mata wani abu zuwa gobe zata dawo gida rarrashinta tayi sannan suka tafo itada fatyma tunda suka tafo yagana tafara shirya Dije da wasu turirinka na jiki dana tsugunno da wani abu data bata tana ci cikin wani karamin lokaci Jikin Dije yafara wani k'amshi tare da canzawa mamaki take wannan abun na menene ake mata..ga wani abu da ake ta tutura mata ba dadi gashi ba dadin dandano ko kadan matar tana mata kwarjini kawai tana ci wani had'in Ferfesu ne taga anbata babu kashi ko kad'an tana tauna ba dadi gaban yagana har ta cinye ta shanye romon ga kayan Fruit da aka had'a tasha bayan kamar minti biyar zuwa goma Dije tana mik'ewa taga wasu ruwa suna tsiyayo mata zaro ido tayi sai ga yagana ta shigo murmushi tayi tare da nufar dije tayi
"Lalai yarinya irinku kunada karanci cikin mata iri kune ake ganin kamar kun asirce miji ya koma muku bita zaizai ko baku sha komai ba kunada cikakiyar ni'ima."
Itadai Dije bata gane kan zance yagana ba..βπ»
_wallahi typing ba saukiπ₯_
_*AMATALLAH*_π
[11/12, 9:04 PM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??_*π·
_*BY AUNTY* *HAFSY*_ π
_*INDON KAUYE*_
_*69*_
Yagana kama Hannun Dije tayi suka nufi kewaye tara mata ruwa tayi masu d'umi bama su zafi ba ta d'iga mata wani abu "kiyi tsarki dasu."
Wasu ruwan ta sake had'awa masu tashin kamshi ta aje "in kiyi tsarki sai kiyi wanka da wannan"
Dije gyad'a mata kai kawai tayi yagana k'ofar toilet d'in tayi tafita Dije tsaye tayi tana tunani ''wai duk wannan abun da ake man na menene haka hadda bari na kwana duk ayiman ko duk na tsarin ne daga miyagu ne indai hakane bari na maida hankalina nayi."
Dije tsarki tayi tayi sannan tayi wanka da ruwan tanayi tana shakar k'amshi saboda yana mata dadin kamshi sosai har tagama wankan ta d'auki kayan ta, ta maida tafito yagana tagani rik'e da wani d'an karamin kasko Dije cikin ranta tayi magana "tofa menene kuma wannan abu ne?"
Haka ta ida k'arasowa cikin d'akin "maza kiyi tsugguno da wannan "yarinya wannan duk gyara muke maki sosai don kizama abin tinkaho gidan miji kizama abar so ga mijinki wadda a kodayaushe office da gida a ko ina yana tunaninki bashi ba kallon mata waje balle har yayi sha'awar su cikin ransa bari nazo inki kagama."
Dije k'ofar tabi da kallo sannan tayi ta tafi wani tunani "tayaya metake nufi da magaganun na ta tana nufi zan zama abin so ga wannan mugu ne har ya dinga tunani na tab! Abinda bai yuyuwa kenan daga jin kamshi a jikina sai yafara tunanin badai wannan mugun ya Ammar d'in ba" haka ta dinga zance zuci ita kad'ai har ta tsugunna wajen kaskon tureren na shiga k'asanta.
Mammy da fatyma suna shigowa dama fatyma ke tukin Ammar yana waje yayi zuru ya rasa abinda ke masa dadi kwata kwata tunanin mafita kawai gani yayi Mammy da fatyma sun fito zasu shiga ciki kallon Mammy yayi "Mammy har kun dawo daga unguwar ne?"
"Eh" tabashi amsa a takaice ta wuce Fatyma ce ta tsaya tare da zama kusa da kujera dake gefen sa "Ya Ammar meyasameka ne bayan tafiyar mu."
d'ago fuska yayi ya kalleta "me kika gani ne?''
naga idon ka ne yayi zuru zuru kamar wadda ya jima yana ciwo."
"No babu abinda ya sameni."
Kaci abinci ne?''
Girgiza mata kai yayi
"Ya Ammar na lura tunda Daddy ya fad'a maka matsayin Khadeeja a wajen ka kuma yace zaka lagos da ita naga kana cikin damuwa ko?"
Ajiyar zuciya yayi
"Bakiyi k'arya ba Fatyma ina cikin tashin hankali ne sosai da wannnan batun da Daddy yazo man wai akwai igiyar auren wata akaina wata bagidajiya yar kauye ita zan had'a da Queen a gida d'aya da sunan *MATAR AURE NA*
wane irin d'auka Queen zatayi man tanada masifar kishi akaina bata so taga ko wace mace ta rab'eni nayi mata Alk'awarin ni *MIJIN MACE DAYA* ne daga ita bazan kula ko wace mace ba Amma Daddy zai had'ani aure da wata k'aramar yarinya yar kauye"
Fatyma kallo ta bi Ammar dashi yadda magana kamar ya zautu.
"Haba ya Ammar iyaye fa aka ce ta ta yaya zaka had'a matar da iyayenka don Daddy ya had'aka aure da Khadeeja shine abin tashin hankalin da zaka tunkari matar taka dashi Ya Ammar akan wannan Banzar matar taka wadda batasan darajar iyayenka ba wlh..."
Kafin ta ida ne taji saukar wani mari a kuncin ta yakara mata wani a d'aya kunci wata k'ara tasaki wadda gaba d'aya gidan ya Amsa domin tunda take bata taba jin mari mai masifar zafi ba sai yanzu.
"Uban me tayi miki da zakice mata Banza ne dole sai an had'ani aure da wannan village girl aure ne bana son ta wallahi duk rannan da nasake jin kin zagi mata sai nayi miki tsinanen duka.."
saukar marin da yaji ne shima ya hana shi kin k'arasa zance dayakeyi kallon Mammy yayi fuskar ba Annuri ko kad'an "ance mata banza jahila wadda batasan darajar iyayen mijin ta ba marar tarbiyya ce akan tace mata banza zaka marar ma y'a wallahi ka kiyayeni Ammar Khadeeja kuwa dole ka zauna da ita domin kuwa nasan wata duk wannan wulakacin naka wata rana itama zata rama yar kauye da kake raina wata rana zakayi mata kuka akan ta amshi kaunar wata rana zaka tsugguna gwiwar ka kasa kana rokon ta amshi soyayar ka kai meye asalinka bacin kauye ina tushen mahaifinka bace kauye dazaka tsani yan kauye."
Kwafa tayi tare da jan hannun Fatyma dake sharbar kuka suka bar wurin suka shige cikin gida.
Ammar kuwa kwafa yayi tare da cize lips dinsa ya had'a hannusa waje d'aya maganar mammy tana masa kuwaa cikin kunne wai zai dawo yana sonta zai zubar da hawaye akan kucaka yar kauye "Allah ya tsareni da fad'awa soyayar da yar kauye Allah ya taimakeni ta gudu ane