Share this page
dad'in k'auye mu Allah sarki habu ko yanzu wane hali yake." Dasauri Laure ta rufe mata baki. "Dije ki manta da auren wani bisa kanki kuma kinsa babu kyau ki Ambato wani namiji da sunan soyaya haramu ne." "Astagafurallah! Allah na tuba." Goge hawayen da suka fara zubo mata tayi Tasowa tayi daga bisa gado "To laure ina band'aki ne?'' ''Dije nima bansani shi ba gashi dama fitsari nakeji saura kad'an nayi na kwance." Dije dariya tayi kai Laure Allah kin cika shishirita fitsarin kwance fa sai kace wata y'ar k'aramar yariyanya." "Allah kuwa.." Suna cikin wannan maganar turo k'ofar akayi aka shigo dasauri suka maida idanuwansu ga mai shigowa.. Cikin far'aa tayi sallama Amsa mata sukayi. "Har kun farka ne?" Laure kallon ta tayi "Eh Aunty fateema." "Ai nashigo naga kuna ta sharar bacci Mamy tace a kyaleku." Duk maganar kan dije yana k'asa bata d'ago ba hannun Fateema taji. "Auntyn mu Amaryamu An tashi lafiya." Dije rufe Fuskar ta tayi cikin kunya. "Shikenan tunda kunya kukeji ku shirya ku fito." Aunty Fateema bansan ina kewayen ba." "Kai Laure Kodayeke bazanyi mamaki tunda baki tab'a zuwa wannan sabon gidan ba tunda muka dawo." Kama hannu laure tayi ta nuna mata band'aki dake cikin d'akin "Aunty fateema ai bamu san yadda zamuyi Amfani dashi ba." Dariya tayi tare da nuna mata duk wannan Abun da ake Dije na gefe d'aya babu abinda tace Bayan laure ta gwada ma laure tafito gun dije ta nufa dije hannu taji bisa kafad'ar ta.... πŸ“šβœπŸ» _Sai yaya nura ya kaini kaduna sannan zakuji niπŸ˜‰_ [11/3, 10:51 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _Kai naga comment_ _sosai Ashe dai Ammar_ _yana da masoya hakan_ _Godiya mai yawa ga_ _masoyan MATA KO_ _BAIWA_πŸ’–πŸ’– _Tawan maryam Abdul my mairamu (zuri'a d'aya)_ _Wannan page d'in naki_ _kiyi yadda kikeso dashi_ _naki ne Amma fa_ _feenah na gaisheki tace na had'aku k'awance,πŸ€­πŸ˜‰_ _Munajin dadin zur'ia d'aya sosai a cigaba da gashi ina gaida Aymana da mua'zzam❀_ _Kun sako Feena gaba ko tam_🀨 _*31&32*_ "Khadija!" d'ago Fuska ta tayi jin an kira ta da cikaken sunan ta murza zoben dake hannu ta ''Haba! Aunty khadija kidaina jin kunyar mu yanzu fa mun riga mun zama d'aya tunda kin zama matar ya Ammar kinji ki dinga kallo na tamkar k'awar ki kidinga yi man kallon laure kinji Aunty khadija." Dije k'anta yana k'asa tana mamakin yadda y'ar gayu nan take ce mata Aunty khadija kuma ta d'inga yi mata kallon kamar laure. "Nasan zaki sake kafin ya Ammar yazo bari naje kafin ku shirya ko." Fateema mik'ewa tayi ta fita, tabar Dije d'ago Fuskar tayi bayan ta fita tagumi tayi ''yau nice da auren wani wadda banda mugunta babu abinda yake nikam wace irin rayuwa zanyi dasu a gida d'aya." Tana cikin wannan tunanin muryar Laure taji bisa k'anta "Dije!" D'ago Fuska tayi ta kalle ta ''Laure har kin fito ne." "Nafito Dije kai! Wallahi Dije kedai zakiji dadi wannan irin dad'i a binni yadda Aunty Fateema ta koyaman nayi wanka Allah sai da nayi yafi sau 10 saboda wani irin dad'i." Dije dariya tayi har fararen hak'oran ta suka fito Laure yafi sau 10 fa kikace kina ta zubama jikinki ruwa laure." "Wallahi kuwa dije ga wani d'an famfo kita ra ciki kiyi Alwallahr ki fa a cikin kai wallahi binni tayi kamar na dawo ciki." Dije mik'ewa tayi "nidai muje ki nuna man yadda zanyi Amfani dashi." Toilet d'in suka nufa Laure gwadama dije kwamin wanka tayi kinga inda zakiyi wanka nan ga famfo dazaki dannan ruwa su zobo sai kikashe in ki tarar ga sabulai na kala kala." "Laure akwai sauran fahimtar Abu yanzu duk kin rike kenan?" "Tsaf ko nake rik'esu dije cikin kaina ga kuma inda zaki wanke bakin ki ya fita tas! Ji nawa yadda ya fita Dije." "Rabani da shirmenki Laure ida gwadaman nidai." Laure ida gwada mata tayi kamar yadda fateema ta gwada mata. Sanna taja mata k'yaure ta fita Dije kallon kewayen tayi tsaf kamar kayi shimfid'a ka kwanta k'asa komai tsaf tsaf.cire hijabin tayi tare da kayan dake jikinta wani d'an guri da laure ta gwada mata ta rataye kayan ta sannan ta soma sak'a k'afar ta fiddo ta tayi wani tsoro taji can kuma ta k'ara sokawa sai datayi yakai sau hud'u Sannan dai tashiga kunna famfo da laure ta gwada tarar ruwan tayi kad'an saboda tsoro da takeji sama sama tayi wanka ta fito ta d'aura zanin ta Alwallah ta d'aura ta fito Laure ta gani gaban mirror tana ta rambad'a wani abu mai ruwa ruwa a cikin kwalba, A fuskar ta. Kallonta Dije tayi batasan sadda ta saki wata dariya ba "Laure kin ganki kuwa kinga yadda kika koma kuwa ki kalli fuskar a madubi ko?" ''Bangane bagashi nan gabana kuwa Aunty fateema tashigo kawo miki kaya ne tace man A fuska ake shafamawa ne hoda ce shine zaki ce man naga Fuska ta yadda tayi ki kyaleni nima nayi kwalliyar yan binni." Cikin Fushi ta idar da maganar. "Allah baki hak'uri Aminiya ta.". Laure murgud'a mata baki tayi sannan ta cigaba da shafa hodar ta a fuska. Dije kallon kayan da akawo mata tayi atamfa ce mai calour d'in pink da blue sai mayafi shi kuma blue aje su tayi gefe guda. "Nikam Laure ko kinsan gabas d'in gidan in yin sallah ne" Laure gwada mata tayi dije shimfid'a abin sallar data gani a gefen ta tayi ta k'abbara sallar ta bayan ta gama ne tayi Add'uoin ta ta linke abin sallar koma tayi gaban mirror ta k'ura ma laure ido ta shafa janbaki har bisa hanci gashi kuma da idon ta ta koma kamar dodoniya, Dije guntse dariya datake niyyar fitowa mata tayi tasan yanzu sunyi fad'a da laure kayan da akace nata ta d'auka ta zira gani tayi sunyi mata cif cif kamar dama ankwatata sikert d'in yayi mata das sai riga wayyo masha Allah masu karatu naso ku hango yadda dije tayi kyau duk da ba wani make up tayi kayan kawai suka karb'eta tayi kyau. Laure juyowa tayi ta kalli dije zaro ido laure tayi "Dije kece kuwa kodai mai kama dake kece." Dije kallon laure takaimata harara "Bani bace." Alqu'ran baki ga yadda kikayi kyau sai kace kin dad'e zaune binni kamar wata yar gayu." "Laure rabani da shirmenki." Dije k'ok'arin d'aura kanta take gashinta cunkushe yakiyi d'aurin d'an kwallin d'in. tana cikin rigamar da d'an kwalli ne Aka turo k'ofar d'akin fatyma ce ta shigo " khadeeja baki gama shiryawa bane.".... Maganar ta ida mak'alewa ganin yawan gashin Dije ga kayan yadda sukayi masifar amsar jikinta.. "woww masha Allah yaya Ammar gaskiya yayi dacen mata wannan kyakyawar kamar balarabiya ji yawan gashin ta jin kirjin ta cike yake dam ga wani hips masha Allah Allah yayi mata hallita." Muryar laure taji ta katse mata zance zucin da take "Aunty fateema mun kusa Dije ce tak'asa d'aurin kallabin ta ne." Fatyma kallon laure tayi ganin yadda ta koma wata aljana guda dariya tafarayi har da hawaye "Laure kin ko kalli yadda kika koma ko kamar wata Aljana wannan in aka ganki sai gudu yanzu nima kingin kad'an na ruga fa." "Aunty Fatyma batayi man kyau bane." "Kinga jeki d'auraye Fuskar ki sannan na d'aura Khadeeja d'aurin kallabim sai na gyara miki laure kewaye ta nufa don wankewa. Fatyma amsar kallabin tayi bayan tattara gashin dije ta d'aure da ribbon "Kinga bari nayi miki simple make up su dady na palour suna jiranmu ayi Breakfast." Sharp sharp ta gama ma dije make up masha Allah dije tayi kyau sosai sai kace ta dad'e binni mayafin ta d'ora mata tare da feshe mata jiki duk da turere sai tashin k'amshi ta ke ga wasu takalma masu tsini ta bata. Fatyma shirya laure tayi itama tayi kyau sannan suka rungud'a suka nufo palour saboda takalma dake k'afar ta yasa ta yanga har su laue da fatyma suka shige bata shiga sallama tayi cikin muryar ta mai sanyi k'anta yana k'asa ta nufi gurin Daddy...... _Babu abinda zance nidai my fans kuyi hakuri da indon ku kunji ko naso yafi hakan yawa wallahi Amma hakan bai yuyu ba ku k'aranta wannan insha Allah bazan kara jinkirin post ba godiya ga d'umbi masoya na a ko ina kuke_😍 [11/3, 10:51 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *_35&36_* _Ki kasance mai kokarin faranta mishi rai kodayaushe ko da baki son Abu daure ma zuciyar ki karki nuna mishi ke baki so ko kingaji A'aa lallbashi ki bashi girmanshi_ _Ki kasan kullum kina cikin tsafta haka gidanki da d'akin da shimfid'arki da yaranki suma suna cikin gyara ba cikin kazanta zaki jama yaranki tsana karki yarda kibarsu dagaje dagaje da majina ko zarni fitsari_, _Duk lokacin da mijinki zai fita rakashi kice Allah Kiyaye mijina yabaka abinda zaka ciyar damu dashi kinayi masa Add'ua har yafita_, _Kafin yadawo kingyara jikin ki kin gyara yaranki in kuma basunan sun tafi islamiyya jeki tsalo_ _wankanki ki feshe duk wata gab'a ta jikin ki yana kamshi karki yadda mijinki yaji kina tsami sai dai k'amshi_, _Yana shigowa jeki tarbo abinki kina mashi shagwab'a kina magana cikin sanyi rai andawo lafiya maigidana ki tarbeshi da ruwa mai sanyi ki bashi sannan ki kalleshi Cikin sanyi murya kice maigidana wanka zaka fara ko_ _abinci zaka faraci domin komai ya kammallah isowar ka kawai yake jira_ _In wanka ne kije ki had'a masa ruwan wanka kafin ya fito kifiddo kayan shan iska dazai zauna dasu kin k'ara baza turare a jikin ki ki k'ara baza powder da jambaki_ _Bayan ya fito ki shirya shi tsaf! Kamar yaron goyo ki rik'o hannun sa kufito palour, wajen cin Abinci kina basa a baki ki dinga shawagwab'ewa kema sai ya baki har kugama ciyar da junan ku in kuma kinada yara kin zuba musu nasu dabam suma sunaci ki ku kula da tarbiya yaranki ki kula dakai da kawon su yar wa domin duniya ta lalace bakaga mazan ba suma lalatasu ake_, _Ki koma tamkar jaririya a gun mijinki ki fidda kunya domin ki kasa kunya kina kallo wata zata amshe miki shi kina kallo ba yadda zakiyi banda yi masa magana gatse gatse ko kuma da tsiya sai yayi miki abinda kikeso bin umurnin shi inhar bai tsallake shar'ia ba karki yadda kiyi wasa da kaima Allah kukanki kodayaushe domin ba abinda mutum zai miki wadda Allah bai miki ba da kin shiga wani hali ringa Ambato ubangiji da salati ga Annabi Muhammad s.w.a. zakiga haske A Al'amarin ki bari na tsayanan nasan zaku fahimci koyayane daga abinda nafad'a_ Add'ua Malama _Amatallah tayi aka rufe taron inda aka raba kayan arziki anyi hidima inda wajen magariba taro ya watse kowa ya tafi kowa yana farin ciki_ Shigowa yayi cikin palour gajiye domin kuwa iya gajiya yau ya gaji idanuwan sa har wani lumshe wa suke saboda gajiya ga wata Azabibiyar yunwa da ya kwaso domin cake ne kawai da lemo a cikinsa, Ragwab ya fad'a bisa kujera kamar kayan wanki ya dafe kanshi tsaki yaji anja bud'a idon sa yayi ya d'ora bisa Feena data sha kwaliyya da wata riga red breast d'inta duk sun fito Abinka da da mai ciki sun k'ara wasu girma. "Lafiya zaka k'ureni ne da ido?'' Ammar Murmushi yayi "My Fee don na kalleki har nayi Laifi kefa matata ce." "To bana son irin wannan kallon kamar dai zaka cinye ni ko baka tab'a sani na bane." "Tam Allah huci ran my queen in nayi laifi a yafeman." Yamutsa baki tayi tashi tayi da gayya ta dinga juya jikin ta Ko ina ya motsawa ta nufi gurin Firji d'auko lemo tayi sannan ta dawo ta zauna ta zuba a cup ta shiga k'urb'a a hankali, Ammar da tun tashin Feena ta rikitashi A hankali ya taso daga k'ujerar da yake ya nufo gunta cikin sanyi murya ya fara yi mata magana, "My Fee ina nawa juice d'n sai ki d'auko naki kawai kin san kuma na kwaso gajiya fa." Wani kallo ta wurga masa "Ance maka ni baiwar ka ce ne don ma na tashi na d'auko bance ka d'auko min ba ko baka ga Abinda ke jiki na bane". "Am sorry My queen." Rik'o hannun ta yayi ya shiga murzawa ganin batayi magana ba yasa shi fara sinsinar wuyanta dariyar mugun ta Feena tayi ganin yana niyyar d'age mata riga ne yasa ta rik'e hannun sa ta kalleshi. "Meye haka My Ammar." D'ago idonsa yayi wadda sukayi ja ya kalle ta "please Queen ki bari na samu natsuwa mana don Allah karki ce man A'aa please ina cikin kishirwar rashin ki My Fee." Kallon shi tayi ya bata tausayi Amma da tuno da wulakanta da yayi kafin ta samu soyyayar shi har da marin ta da yayi da irin magagun da yayi mata sai taji bata tasauyinsa. Fizge jikinta tayi zata mik'e dasauri ya rik'ota " please Ki tausayaman my Fee yaushe rabon dana kasance dake ne Queen." Ganin hawaye na fita daga idanuwan sa ne yasa ta dawo "Na baka minti biyar domin ni bana iya jure wannan jarabar taka," Ammar yayi nisa baya jin gyad'a mata kai kawai yayi ya rungumota jikin sa yafara sakar mata hot kiss a jiki Feenah ganin zai rikita mata lissafi domin Ammar cikaken namiji ne da zai rikita ko wace mace ce komai takeji ko dole ko bakiso kema ki maida mashi martani, Kwace jikinta tayi daga Ammar "five Minutes d'in sun cika har kana neman wucewa," Ammar rik'e cikin shi wadda marar shi kemashii Azabatar ciwo idon shi taf da kwallah ya dubi Feenah pls ki tamaike ni na fidda abinda ke mara ta Fee don Allah ki fad'in duk abinda kikeso nayi miki." "Bana buk'atar komai kaima kasani in nashirya zan nemeka Amma ban shirya Ace mutum sai jarabar tsiya kullum kana manne da mace." Tsaki taja ta kwashi wayoyin ta tabar palour, Ammar saukowa yayi daga bisa k'ujera ya kwanta k'asa yana mirgina saboda wani ciwo da marar shi take mishi hawaye na zarya a fuskar saboda azabar da yakeji, tashi yayi rik'e da cikinsa yana dafa bango ya shiga d'aki toilet kawai ya shiga sakar ma jikin sa ruwa yayi ta ko ina, sai da ya jik'e sharkaf yaji sanyi sanyi sannan ya cire jikakun kayan da ya cire, ya ratayesu ya fito d'aure da towel wani d'an madaidaicin firji ne ya bud'a wata kwalbar ta magani ce yake sha wadda ke rage masa ciwon marar,Kafa kai yayi ya sha yana gamawa ya kwantar da kanshi bisa gado ji yayi bai iya kwanciya domin wata yunwa dake murkukusa tashi yayi ya zira wata t shirt mai yankaken hannu da wando there quarter ya fito kitchen ya shiga cooker gas ya d'ora tukunya indomie ya dafa ya juye ta plate sai kamshi take Amma daga kalli fuskar Ammar kasan yana cikin wani yanayi, Zauna yayi a palour yana cikin cin indomie sai ga Feenah ta fito kunnen ta sanye da Earphone Kasa nuna b'acin ranshi yayi daga Abinda tayi mishi duk da yana jin b'acin ran tsintar kanshi yayi da yimata murmushi. "My β™•." Batayi masa magana zauna tayi kusa dashi "Shine zakayi girki baka sanar dani ba ko ina buk'ata ne" Cikin kyarmar murya Ammar ya fara magana "Kiyi hakuri bansan kina buk'ata ne." "To ina bukata katashi kaje ka girka man idan ka ida." "Angama."... ## "Dije ce yanzu gobe kamar haka bamu tare kou?." Gaban dije ya fad'i. raurau sai ga hawaye rungume juna sukayi itada Laure suka fara Kuka babu mai rarrashin wani fatyma dake nufo d'akin taji shashekar kukan su dasauri ta nufi d'akin ta tura k'ofar..... _Aradu nagajiπŸ˜“k'iwar kin typing ta kamani fans kuta hak'uri kunji sai na warkeπŸ˜“πŸ˜“_ *_AMATALLAH_*🌹 [11/3, 10:51 AM] πŸ˜˜πŸ’•: ..πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _Hassana d'an larabawa ina godiya sosai da k'aunar ki gareni Allah yabar zaman tare my hassana_❀😍 *_33&34_* "Ina kwana." Dady cikin fara'a ya juyo wajen Dije." "Lafiya d'iyata kun tashi lafiya ya bak'unta?'' K'anta yana k'asa tace "Lafiya lau." Kusada Mamy ta nufa ta durkusa kamar yadda tayi ma Dady. "Ina Kwana." Jitayi an kama kafad'ar ta "Lafiya lau y'ata taso ki zauna kusadani kinji ko." Dije cikin kunya ta tashi ta zauna kusada Mamy Amma kanta yana lullub'e da mayafin ta "Ki daina jin kunya ta kinji y'ata ki daina yi man kallon surukarar ki." Dije gyad'a kai kawai tayi. "Mamy Allah ta cika jin kunya fa nifa har yanzu banji maganar ta kwara biyar sai dai in suna tare da laure.." Mamy dariya tayi "Zata sake fatyma kinsan bak'unta tunda ta had'u da irinku masu surutu." Fatyma zumb'oro baki tayi "Kai Mammy sai kita cewa wai surutu na yayi yawa..." "Kinga tashi muje dinning table ina fatan dai kin had'a masu gwagwo komai ko." "Eh komai na kai musu Mamy." "Yauwa". mik'ewa sukayi Mamy kama hannu Dije tayi ta rik'e domin lokaci d'aya Allah ya sanyo mata soyayar Dije bata kallon ta a suruka sai y'a. K'ujera Fatyma taja ma su laure suka zauna, sannan itama ta zauna tafara had'a ma kowa abinda zai ci custard ta had'a ma Laure da Dije yaji madara sosai ta mik'a kowa Dije k'anta yana k'asa Fatyma ta lura kunya takeji.Laure ko har ta k'afa cup a bakin tana sha har da lumshe ido, Dije kam kurb'a kawai take ta sunkuyr da kanta,k'asa tana sha Mamy ta lura da yadda Dije ke Breakfast tsakura kawai takeyi. "Khadija ki saki jiki kiyi Breakfast a gidanku kinji ko karki d'auke mu surukanki mu iyayenki kinji d'iya ta." Dije gyad'a kai kawai tafara sha Amma badon ta saki jiki ba Dady shima ya gani yana ganin Sungama suka bar gurin ko Dijen ta saki Jiki tayi Breakfast d'in. Fatyma mik'ewa tayi "bari naje nayi shirin school yau zan lek'a Amma bazan jima zan dawo saboda waleemar da Mamy zata shirya" "Yauwa Aunty Fatyma tambayarki nake sonyi." "Ina jinki Laure tana yi tana tattara plates da cups. "Wai meye wannan Abun naji yayi kamar kokko Amma ba kokko bane saboda gard'in sa sosai kamar kada nadaina shan sa Alqur'an." Dariya fatyma tayi "Wallahi Laure kin cika Abin dariya kedai." "Ai gaskiya Aunty Fatyma." "To sunansa custard haka yake ana dama shi ne kamar yadda ake dama kokko." "da muciya kenan" Fatyma zaro ido tayi. "A'a Laure kibari in nadawo munyi magana bari naje kila ina shiga ciki khadeeja ta daure tayi Breakfast d'in." Fatyma shiga tayi ciki don ta shirya shirin School, Sai data shiga ciki sannan Dije ta tsakuri wainar kwai da dankali da custard d'in. "Muje b'angaren su gwagwo" tanayi tana gyara zaman mayafinta. "kibari na,idar mana " Dije zaro ido tayi "Haba laure har yanzu baki hamdala haba ki tashi ko kinason cikin ki ya fashe ne?" "Allah Dije kayan binni gard'i garesu ko koshi sai kaji bazaka iya daina ciba nidan na koshi Amma bakina yakasa daina barin ci Alqur'an inaga har guzuri zanyi na tafi dashi." "Haba laure." Jan Hannun ta tayi sannan suka mik'e b'angaren da aka saukesu su gwagwo dakuma wasu daga cikin dangin Dije. Tun kafin su shiga suke jin hayaniyar su. Sallama sukayi suka shiga palour kowa bin Dije yayi da kallo ganin yadda ta koma y'an binni y'ar gayu lokaci guda tayi wani kyau. Wata gwagwon ta ce k'anwar inna tace "Wai dije wannan kika samu wata d'aya a binni munko gani ki jibi daga jiya har kin canza mana kamar bake ba." Murmushi Dije tayi "Kai gwagwo yanzu sai kice bazaki ganeni ba." "Eh mana." Dayake Dije bamai yawan son magana bace sai dai kawai kaga fuskar ta tana murmushi. Gaidasu tayi duka sannan ta koma ta zauna Gwagwo larai matar yaya jabeer kallon dije tayi "Dije ya kwanan bak'unta ne ?" "Lafiya lau Gwagwo." "Dije ki godema Allah,Allah ya had'aki da surakai masu sonki kiyi musu biyaya kinji ko kinga dai yadda suke nan nan dake kiyi biyaya ga mijinki karki bijerma umurnin shi kinji ko kar kiyi Abinda zai sa kiyi bak'in jini gurinsu kinji ko." "Insha Allah Gwagwo" "Yauwa Allah yayi miki Albarka." Nan dai sukai ta yi ma Dije nasiha akan biyayyar aure fashewa tayi da kuka domin kuwa hango rayuwar ta a gidan Ammar ta yaya zata zauna dashi ne wane tarba ne zai yi mata shi da matar shi. tana cikin kukan ne Sai ga fatyma ta shigo tayi shirin school, "Khadeja har kinfara kukan rabuwa dasu gwagwo ne" Dije batayi magana kukan ta kawai take Fatyma dafa kafad'ar Dije tayi "haba Aunty khadeeja Ki daina kuka kinji bazaki kukan rabuwa dasu ki daina kuka." Dije maganar zuci ta fara "Ta yaya bazanyi kukan rabuwa da Baffah da inna ta bazanje Hannun mugu Azzulumi ban san yaya zai d'aukeni ba *MATA KO BAIWA*" shiru tayi dai Fatyma ganin dije yasa ta mik'e ta nufi school, Dije tanan zaune har mammy ta shigo ga iske su hakan itama zama tayi cikin su domin Mammy mace mai son mutane mai kuma girmamasu nan take fad'a musu sai zuwa gobe zasu tafi domin akwai waleemar da ta shirya, K'arfe hud'u gida ya cika tam da mutane duk an k'afa rumfa na na bak'i motoci sai sauke bak'i take y'an gayu mata masu ji da naira suna ta shigowa Lokacin Dije tana can ana shan make up domin mai kwaliyya ce aka d'auko tana yi mata, Laure ce zaune kusa da Dije tana ganin yadda ake gyara dije ''gaskiya Dije kamar bake kinga yadda kikayi wani kyawu kuwa nikam in zamu had'u bazan ganeki bama." Itadai dije tayi shiru mai kwalliyyar itama sai yaba kyawun Dije take, Fatyma ce ta shigo cikin wata gown maroon tayi rooling mayafi brown masha Allah tayi kyau, K'ura ma Dije ido tayi anshirya ta cikin wani lace dark purple mayafi light purple "Wooo Beautiful girl beautiful lady khadeeja gaskiya kinyi kyau da ya Ammar sai ganki hakan sai kin rud'ashi."photo na ta fara d'aukar ta ta d'auke su tare ta d'aukesu tare da laure haka sukai ta d'aukar pictures, woo masu karatu na barku kawai ku hango kyawun da Dije kawai tayi basai na fad'a ba na barku. Mammy tana shigowa itama kyawun Dije ta gani yaba kyawun tayi rik'on hannun ta Mamy tayi suka nufi gurin waleemar da aka tara y'an gayu da y'an boko wayayu, wata k'ujera ce aka zaunar da dije, A haka akafara gudanar da waleema cikin tsari da burgewa inda wata malama ta kware a fannin wa'azi Malama Amatallah, tayi nasiha da wa'azi akan aure, wasu daga cikin mata jikin su duk yayi sanyi sun kuma ayyana a ransu zasu gyara rayuwar auresu inda ta basu wasu shawarar ri tana cikin brown d'in hijabi da siririn glass d'in tafara magana, Yawacin mata sai suta korafin mijinsu baya kulasu yana kula wasu mata a waje baki samun cikakiyar kulawa daga wajen su baki zama da miji kuyi hira, mata muke sanya wasu abu da kanmu, _Ki kasance mai bin umurnin mijinki yadda Allah yace ki kasance mai ladabi da biyaya gareshi_, _Ki guji b'ata ma mijinki rai ga duk abinda bayaso_...... _Zan d'ora a page na gaba insha Allah wani uzuri ne ya tasoman na tsaya daganan_ _*AMATALLAH*_🌹 [11/3, 10:52 AM] πŸ˜˜πŸ’•: .πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _Inasonku masoyana masoyan littafin mata ko baiwa a ko ina kuke a fad'in duniya_❀🌹 _*37&38*_ Turus tayi gani Dije da laure sun had'a kai sun rungume juna sai rusar kuka suke, "Subhanallah! Khadeeja, Laura meyafaru ne kuke kuka ne tun kafin na shigo nakejin tashin shashekar kukan ne?" Laure Fuska cike da hawaye ta d'ago ''Aunty Fatyma muna kukan rabuwa ne gobe kamar yanzu bamu tare da dije Mun saba komai namu tare mukeyin sa makaranta dandali tare yo ittace tare d'ebo ruwa tare Komai tare bacci kawai ke rabamu da juna Amma daga yau mun rabu.." K'ara

Chapter 5 of 11