kamar ba ciki jikin ta "My Ammar mekace kano zaka.......
_Manage plsπ_
*_AMATALLAH_*πΉ
[11/3, 10:54 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
( *_SHORT STORY_*)
_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)
*_51&52_*
_*INA MATUK'AR K'AUNAR COMMENT D'INKU YANA K'ARA MIN KWARIN GWIWA SOSAI DA SOSAI*_ππ
"My Ammar mekace Kano zakaje kayo me?''
"Daddy ke nemana a yau yace kuma na isa. A daren yau.....
binshi tayi da kallo tunani ta tafi "Shi da wannan tsohon bacin nayi Blocked d'in number sa kuma kiran me yake masa ne?''
_Hmmm kujiman Feenah mahaifin shi wadda yayi silar zuwan sa duniya ya raine sa yayi masa duk wata wahala ta rayuwa yabashi Ilimi yayi masa tarbiyya ya zamana abin so ga kowa da girman sa ta ganshi tace tana so kuma lokaci d'aya tace zata rabashi da mahaifinsa hakan na yiyuwa ko feena?_
Dawowa tayi taga tunanin da take waigawa tayi taga bata ga Ammar ba wata ashar ta saki tare da nufar d'akin iske sa tayi ya d'auko jika ya zuba kayansa ciki,
Feenah cikin Fusata taje ta karb'e kayan tayi wurgi dasu "Mekake nufi kake ta had'a kaya ne katafi kabarni da wannan cikin waxai yi hidimar gidan ne Abinda bazaiyu bane ba Ehee don haka tun wuri ma ka canza shawara kabarni cikin gida ni d'aya ba kowa bazan iya ba."
Ammar kallon Feena yayi cikin sanyi murya yayi kalar tausayi don Allah My Queen kibarni naje ba jima zanyi ba ranan Sunday zan dawo fa saboda office please My Queen don Allah kada Daddy yayi Fushi dani kada ya tsine man My Feena yace in banje ba zan had'u da Mummuna b'acin ransa."
_Waiyazubillah!! Tur da Hali irina su Feena Anya akwai tunanin Mutuwa a ranta kuwa anya tana tunanin kodayaushe ubangiji ya buk'ace zata zataje Allah katseremu ka tsare zuciyoyinmu daga aikata mummuna aiki kiri kiri ta rabashi da mahaifinsa kaico duniya duniya ba gidan zama gidan aro tanason ko taga daidai_ ??
Hawaye taga Ammar yanayi da idonsa yana gogewa tab'e baki tayi tare dacewa "Na Amince katafi Amma kasani fa kada kawuce kwana biyun dakace kuma kasan ba iya yin komai zanyi ba zanje Area d'in su Mama talatu k'awar Mommy ta bani house girl d'in ta d'aya ta tayani zama don haka sai kabani Abinda zanyi hidima dashi"
"Kiduba cikin Locker Akwai kud'i ki d'ebi ko nawa kikeso My Queen Thank you."
Samun k'ujera tayi tazauna duk Haushi ya cikata Ammar zaya kano shiryawa yayi cikin wani marron d'in yadi ya shirya taje sumar shi ya d'ora wata hula milk wow Masha Allah karkuso kuga yadda Ammar yayi kyau. Feena tana binshi da kallo wani kishi ya kamata gudun kar a airport ya had'u da wata wadda zata kyasa tsaki taja Ammar waigowa yayi
"Meyafaru Queen."
"Bakomai."
Turere ya d'auko ya Fesa k'ara d'auko wani yayi zai Fesa dasauri Feena ta fizge sa "Kamar zaka gunta ko zaka neman Aure sai b'ub'ula ma jikin ka turare kake."
"Sorry Queen."
D'aukar jikar yayi ya rataya "kitaso muje daganan sai kije gun Mama talatun kisamo House girl d'in wadda zata zauna dake kafin nadawo ko Queen."
"Ok bari na d'auko mayafin muje."
Bada jimawa ba Feena ta d'auko wani siririn Mayafi ta yafa kuma wata doguwar riga ce jikinta duk ta lafe mata jiki.
Haka suka shiga mota sai airport cikin sa'a yasamu jirgin da zashi kano nan da 20Minutes nan yayi duk abinda zaiyi sannan ya dawo gun Feena
"My Ammar gabana ke fad'uwa inajin tamkar wani abu zai faru dake inkaje kano don Allah karikeman Amana don Allah kada ka kula kowa kai Miji mace d'aya kuka tasa domin ji tayi duk yanayinta ya canza da tafiyar Ammar kano ji take tamkar wani abu zai faru da rayuwar ta.
Ammar Hugging d'in ta yayi "My Queen kiyarda da Ammar d'inki babu wadda zan kula da wuce ke kinji matar Ammar rarrashin ta yayi Feena shiru tayi domin itakam duk yanayin ta ya canza
Kiran suna aka farayi Ammar ya b'anb'are jikinsa da Feena yanayi mata bye bye har ya shige jirgi yana d'aga mata Hannu.
A hankali jirgi yafara tashi har ya lula sararin samaniya sai *KANON DABO*.....βπ» β
_*Kyan Alk'awari cikawa wallahi banyi niyyar typing saboda rashin nepa Amma saboda na faranta muku rai na cika Alk'awari nayi muku ko yayane*_
_*AMATALLAH*π_
[11/3, 10:55 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
*_BY AUNTY HAFSY_*π
( _*INDON KAUYE*_)
_*52&53*_
"Khadeeja bazaki je unguwan ba Mammy tace kishirya fa tare zamu tafi baki d'aya."
"Aunty Fateema mara na ke ciwo tund'azu shiyasa bazan iya zuwa ba shar! Hawaye suka zubo mata saboda masifar murd'uwa da take mata Amma bata nuna mata saboda kadda su shiga rud'u iri na waccen watan da tayi domin haka in zatayi period ko a gida ne tana shan wahala sai inna ta jik'a mata magani take samun sauk'i..."Subhanallah Sannu Khadeeja sannu bari na fad'oma Mammy ko?''
"Don Allah Aunty Fateema kadaki sanar da ita tana iya fasa tafiyan nan kuma ba sosai nakejin ciwon ba insha Allah zai fad'a kafin ki dawo kibani maganin da Likitanan ya bani kwanakin baya"
"Anya Khadeeja bakijin ciwon nan sosai kuwa?"
"Allah Aunty Fatyma danasha magani nasan zan samu sauk'i karki damu.". "Shikenan bari nad'auko miki maganin ko"
Loka ta bud'a ta b'allo mata magani har guda biyu tasha
"Bari naje Gun Mammy ko kar taji shiru."
"Aunty Fatyma kada ki d'aga mata hankali fa."
Fatyma kafad'ar Dije ta dafa bakison na d'aga ma Mammy hankali ko shikenan zance kawai baki lafiya Amma ba sosai ba"
Fatyma fita tayi daga d'akin can bada jimawa ba sai gata itada Mammy
"Ashhha My daughter ba lafiya sannu kinji daughter ina fatan bakyajin ciwon rin waccan ?''
"Eh Mammy banaji ya lafaman Aunty fatyma ta bani magani nasha."
"Kodai nafasa fitar nan dai Khadeeja."
"A'a Mammy dasauki fa."
"To kidawo palour muma bazamu jima ba zan dawo don kince da sauki bazan fita mezayo miki tsaraba ne badon dai zaki don kinga halin da kike."
Dije sunkuyar da kanta kasa tayi "Aunty Fatyma ta zabaman."
Shikenan daughter sai mundawo yanzu insha Allah ki shiga ki gyara kanki sai kidawo palour ko television ta d'ebe miki kewa ko...."
"Allah kiyaye sai kundawo."
Dije dafa bango tayi har ta shiga toilet wanka tafarayi sannan ta kimtsa kanta tafito jerin kayanta ta nufa wata doguwar rigar Atamfa ce ta d'auko irin wadda daga samanta ya matse kasa ya bud'e ta zira ko powder bata shafa ba kawai ta fesa turare kallabin tayafa kamar gyale,kallon kanta yayi A madubi.
"Allah sarki Ban taba kukan rashin Baffah da Inna Kusadani ba me zance ma wad'ad'anan mutanen sunyi man dukkan wani _*KARAMCHI*_ arayuwa ban taba kukan rashin wani abu ba ko kokarin sa ya faranta man rai Ammar kake kowa bakayo halin iyayenka ba ko kad'an inama ka biyo halinsu na sanin darajar mutum da mutatanshi a rayuwa Amma bakasam wannan ba."
Tunowa tayi Mijin ta fa yau kimanin wata biyu kenan da kwanaki da zama matar shi Amma har yanzu bata saka shi a idon ta wai itaje gidansa A mezan d'auke ta *MATA KO BAIWA*??
Ajiyar Numfashi tayi tare da goge hawaye "Baffah bazan tsallake umurninka ba zan zamo mai biyaya ga wannan auren haka Bazan *BUTULCE* ma wadda suka nuna man k'auna ba naki d'ansu."
Dafa bango tayi tafito palour bisa doguwar kujera tazauna ta kalli television A arewa 24 suna cikin shirim Kyautata rayuwa har sunyi nisa dan kwanciya tayi saboda marar dake mata wani ciwo kuma tanason shirin tunda tazo tafara sabawa take zama tana kallon sa Neesa Ablah tana burge ta..da marar ta motsa mata sai dai ta cije baki ta rike ciki...
_*MALAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORTβ*_
A hankali yafara saukowa daga sararin samaniya har ya sauko kasa ya d'auki wani lokaci sannan Matafiya suka fara fitowa daga cikin jirgin A hankali yafara saukowa daga matatakalar jirgin har ya sauko lumshe ido yayi jin ya shaki iskan garin sa gabansa kuma ya fad'i yana tunanin Abinda zaije ya tarar yasan ba k'aramin Abu ne zai sa Daddyn sa wannan fushin
Kallon Airport d'in yayi yadda wasu daga cikin familyn su ne sukazo d'aukar su cikin farin ciki da walwala tsaye yayi yana kallon su burgeshi yaji yayi.
Taxi yasamu yashiga yafad'amasa unguwar dazai kaishi Sharada phase 2 yana nuna har k'ofar gida aka aje Ammar zaro kud'i yayi ya biyasa ya nufi gate d'in gidansu kwankwansa gate d'in yayi maigadi taso wayayi ya bud'e masa zaro ido yayi ganin wadda ya gani.
"Yallab'ai kai nake gani yanzu?''
"Nine malam garbati sannu da aiki."
''Yauwa yallab'ai watanni da yawa rabon ka da gida."
Malam Garbati ai kasan yanayin aikin mu bud'eman k'ofa inkafara wannan surutun naka baka bari Daddy ya dawo?"
"Aaa babu kowa sai Khadeeja yarinya mai kirki da tarbiya yallab'ai inkiganta tamkar balarbiya take?"
"Wacece kuma Khadeeja ?"
Yallabai kana nufin bakasan ta ba matar ka wadda aka d'aura aurenku kimanin wata biyu da suka wuce fa yallabai sai kace baka sani ba gaskiya kayi dace mata."
Ammar dariya yayi malam garbati kenan badai Ammar bakaji daidai bane Amma badai ni ba nida aurena ko kamanta ne"....
Malam Garbati ya bud'a baki zaiyi magana dasauri Ammar ya dakatar "malam garbati kabarni na huta da surutunka don Allah bakaga daga tafiya nake ba."
Ammar kutsa kansa yayi cikin gidansu yana shiga palour yaji shiru
"Kuma su Mammy basanan sai subar kayan kallo kunne wucewa yazo zaiyi ji yayi tuntube da wani abu yafad'a bisa doguwar kuj'era hannunsa ya fad'a bisa wani mai matuk'ar taushi k'ura mata ido yayi yadda take bacci hankalinta kwance lips dinta ya k'ura ma kallo ganinshi kamar na jarirai sai Giran ta dake gazar gazar kamar tasa Eye lashe Dije jin nauyi taji bisa jikinta bud'e idon ta tayi wata zabura tayi dasauri Ammar ya dawo hankalinsa Dije cikin kyarma murya ta fara magana...."San...nnu da zuwa....βπ»
*BATTERY LOW*π
_Bamu samun cikakiyar nepa shiyasa kuke ganin sa kadan wallahi kuyi hakuri my fans_
_Watakila gobe kuga wani Amma sai naji ruwan comment ta ko ina fa_ππ»
[11/3, 10:55 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
_*BY AUNTY* *HAFSY*π_
( _*INDON KAUYE*_)
_*62&63*_
"Daddy don Allah ka gafarceni in har nayi muku wani don Allah Mammy ku gafarceni fushinku duk ya sakani cikin tsananin tashin hankali duk don Allah kuyafeni."
Cikin Fushi Mammy ta fara magana "dakata da wannan game d'in dakake kaji ko kai ba yaro bane kasan abinda ke daidai kasan akasin haka zaka kawo ma mutane maganar banza tunda matar ka tafi iyayenka dakayi zaman ka bakaxo ba bama neman ka."
Mammy cikin Fushi ta mik'e zata bar palour baki d'aya
"Na'ajatu" tsayawa tayi bisa kiran da Dady yayi mata "dawo ki zauna Naja'atu zamuyi wata magana dake Mammy dawowa tayi ta zauna tana harara Ammar
"Mammy don Allah kiyafeman kidaina fushi dani Mammy na inga dariyar ki a fuska shine farin cikina Mammy don Allah Daddy kuyi hakuri kudaina Fushi dani."
Ammar d'ora kansa yayi bisa jikin mammy yana kuka jikin Mammy yayi sanyi tsakanin uwa da d'a sai Allah kasa janye shi daga jikinta tayi tana jinsa yana kuka
"Ammar tashi muyi magana dakai."
Ammar tashi yayi zaune Amma yana kusa da Mammy Daddy kallon Ammar yayi "ka natsu magana zamuyi dakai."
"To Daddy Amma don Allah kuce kuyafeman sannan zan samu natsuwa mammy don Allah kuyafeman kidaina fushi dani don Allah"
Mammy kallon Ammar taji fuskar ta babu yabo babu fallasa tace "Nayafe maka."
"Mammy na nagode Daddy na kayafema kaima."
Nayafe maka Ammar Allah yayi maka Albarka."
"Ameen Dady."
Daddy gyaran Murya
"Ammar zuwa gobe da safe zan fad'a maka dalilin kiranka danayi."
"Shikenan Daddy."
"Fatyma jeki had'ama Khadeeja ruwan wanka kotaji k'arfin jikin nata."
"To Mammy."
Fatyma toilet tanufa don had'a mata ruwan wanka.
"Khadeeja me zaki iya ci ne a had'a miki ne kafin kiyi wanka ?''
"Mammy bana shawa'ar cin komai yanxu."
"Aa Khadeeja yazakice haka jeki fito nahad'a miki kunun Gyad'a kisha."
Fatyma ce tafito bayan ta had'a mata ruwan wanka d'in
Khadeeja mik'ewa tayi tanufi ciki Ammar binta yayi da kallo har ta shige ciki yana waigowa suka had'a ido da Mammy sunkuyar da kanshi kasa yayi yana sosar kai Mammy kauda fuska tayi kamar bata ganshi ba
Daddy mik'ewa yayi ya shiga ciki Mammy mik'ewa tayi itama ta shiga ciki can ta kwalama fatyma kira
tashigo "Fatyma kada ki sake ki sanar da yayanki wani Al'amari inhar ya tambayeki gobe yaji komai gurin Daddy."
"To Mammy."
Juyawa tayi ta koma palour kamar Ammar jira yake yafara tambayar "Fatyma wannan wai wacece bansantaba A familyn daddy ko na Mammy.naga yadda Dady da Mammy ke bata kulawa sosai."
"Yaya Ammar baka santa Amma Daddy zai sanar dakai matsayinta gobe bari naje na taya Mammy aiki."
Fatyma mik'ewa tayi zata shiga ciki Ammar ya tsayar da ita
"Inki gama ki had'oman coffee ina d'aki."
"To ya Ammar."
Mik'ewa yayi shima ya shiga ciki
_____________" Doctor yazakace haka gaskiya duk hanyar daxakabi kafidda man wannan ciki kabi zan iya baka kud'i ko nawa ne karabani da wannan jarabben ciki nan."
"Am sorry A gaskiya zaki iya rasa rayuwarki in har akayi k'ok'arin Zubda saboda cikin ki ya shiga yana wata bakwai ne yayi kwari sosai in har akayi kokarin zubda shi zaki iya rasa rayuwar ki."
"Doctor Rabe ka dade kana wannan aikin fa tayaya zakace haka Haba Doctor kada kabani kunya mana."
"Khairi kinsan indai ta fanni abortion ne na kware Amma a gaskiya banzan iya yi ma Friend d'inki aiki ba saboda cikin ta 7months ne da dai bai wuce 3 or Month tuni zan markad'eshi."
Tsaki Feena taja "Khairi tashi muje ai banan kad'ai ne akeyi ba tashi muje da Allah."
jan hannu Feena tayi suka bar asibitin suka shiga mota sai da Feena sukaji asibitin 4 Amma duk maganar d'ayace a karshe wata asibiti sukaje wadda can wajen gari yake shima da yafad'a mata karshe wasu magani ya bata wadda zata sha sau biyu wadda zata sha sannan suka taso suka tafo Anan tsakiyar palour suka baje takira wannan yarinya ta kawo musu abinci sukaci suka had'a da syrup suka baje tsakiyar palour d'in suna kwasar bacci sai da Yarinya mai suna Murja ta fito ta gyara wajen tana kallon su yadda basu gajiya da bacci ko dayaushe,
*KATSINA*
*K'AUYE*
_______________"Haleema Haleema!! dasauri ta saki tagumin da take "Haleema zaman mekike ga gora gabanki bakiyi Alwallah bane kinyi tagumi na lura a kwanakin kina cikin tunani meke damunki Haleema ko kewar Dije ne ya taso miki haryanxu baki daina ba ne?"
"A'aaa Malam kwana biyu ne nake mafarkin Wanna yaron ina yawan ganin shi a mafarki na sai nai ta ganinshi kamar tare da Dije suna tare da juna."
"Haleema Ashe can baya manta da wannan yaron ba sai yaushe zaki fidda ranki da shi ne Haleema kidaina saka ranki shi shekaru Ashirin da uku ya kamata kisaka ma ranki ya mutu Dije shaid'an ne kawai zai saka miki wasi wasi a ranki itakuma Dije kiyi mata add'uar zaman lafiya a gidan mijin ta tunda yau ko sati d'aya dajin Muryar ta tana lafiya."
"Shikenan Malam zan cire damuwa a raina."
"Yauwa Bari naje massalaci gayacan ana kira."
"Shikenan adawo Lafiya nima bari nayi Alwallah."
Baffah yana fita Inna ta fara Alwallah Amma akwai tunani a ranta kawai jikinta tsawon shekaru ashirin da uku taki manta d'an ta wadda ya b'ace yanada shekaru shidda zuwa biyar.
_*WACECE DIJE*_
Baffah mutum garin marad'i ne acan wani k'auye ne da akayi wani fad'a da yan kusada garin ne duk aka kashe wasu dangi nasu dama iyayenshi duka sun mutu sukayi Hijira suka dawo nan cikin marad'i suka samu gidaje suka zauna anan ya auri yar uwar shi wadda take marainiya wato haleema suka zauna anan ana haka sai ga Yaya Jabiru dake zaune a cikin wani kauye dake cikin kauyaki ta jahar katsina yana sana'ar shi yanada rufin asiri daidai misali yazo ya tafi da Baffah a can yana kama mishi wani abu har yayi gidan shi yaje ya d'auko matarshi suka zauna shekaru su biyu ta samu ciki ta haifi d'anta namiji inda Aka samishi sunan Mahaifin Inna Aliyu Amma suna kiranshi da Gadanga shekarunsa hud'u Inna ta k'ara Haifar masa k'anwa Dije yana matuk'ar ji da ita komai yasamu sai yace Inna zan ba dije har tafara rarrafe itama tana kaunar d'an uwan ta data ganshi zata dinga zillo zai d'auketa har ya dinga fita da ita waje kuma bai bari kowa ya tabata inko bata lafiya ya dinga Kuka kenan.
Rana kwatsam wata rana Aka nemi Gadanga aka rasa acikin kauye sako da lungu babu inda ba'a nemeshi ba aka rasa Baffa da inna hankalinsu ya matukar tashi ga dije dake ta kuka itama tana bidar dan uwan ta Ana ta Add'ua Amma shiru bayan kwana biyu sukaji labarin wai antsinci wani yaro a cikin ruwa ya mutu a harma ya rub'e anan suka sadakar dacewa gadanga ne ya mutu Inna tasha kuka domin kuwa tana k'aunar yaranta sosai har dai ta hakura Baffah ya dinga yi mata nasiha har ta hakura, Amma jikinta yaki bata Gadanga ya mutu, sai kuma kwanan datake mafarkin sa shida Dije.....
_Dawowa Labari...._
_*AMATALLAH*_πΉ
πβπ»
[11/3, 10:55 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
_*BY AUNTY* *HAFSY*π_
( _*INDON KAUYE*_)
_*58&59*_
"Khairi kinsan irin kaunar da nake ma Ammar kuwa cikin raina kinsan ko tsananin kishin shi da nake a cikin zuciyata Khari kidaina Ambatar hakan khairi banason ji hakan"
Khairi kamo Hannun Feena tayi tazaunar da ita ganin yadda ta zauce take ta sakin magana akan Ammar "calm down Fee daga nayi wannan abu duk kinbi ki firgice bance Ammar zai rabu dake ya samu wata aikece tal d'aya mata a gun Ammar har abada ai babu ba wata kishiya har abada uwar gidan Ammar ai ba'ayi ma irin mu kishiya kin sani ko dako mun tarar da ita zatayi waje ba shiri ba haka nake nufi ba meyasa kika yarda dane kikayi ciki da wuri tun baki gama cin kuruciyar ki ba kina yarinyar ki fara d'awaniya raino tun yanzu kinga wannan Breast d'in da kike tak'ama dashi kina d'aukar ma Ammar hankali dashi kina mishi yadda kikeso da kin haihu kikafara shayar da baby zai zube, yadda kike yadda kikeso kina shan make up kina fita duk inda kikeso zai rage saboda wannan babyn zai miki cikas duk wata jin dad'in rayuwa da kika sani zaki bar jin ta yara zasu farayi miki yawa kashin su zarni fitsarin su duk kece zaki koma tamkar mahaukaciya saboda hidimar wannan Yaran dake gabanki daganan shikuma namiji babu abinda yake bukata irin ya ganki cikin gyara da kamshi kin tara yara ina kikaga lokacin kanki ki ga na yaranki da bare kije ga naki daganan zaiyi tunanin auro wadda zata kula dashi kinga kin koma bola kenan shara a wajen miji yana can yana soyayarshi ke kuma kinan kina hidimar yara",
Feena kallon Khairi tayi bayan tagama bayanin ta "Khairi ina hankalina da waye na suka tafi na manta da wannan abun Khairi na yadda na bar cikin nan a jikina Khairi wace hanya kike ganin zamubi ne Khairi bana son na bud'a idona nak'ara ganin cikinan jikina Khairi ki bani mafita mana."
"kwantar da hankalinki Aminiya bud'a jika Khairi tayi kwalbar syrup ta d'auko tashi tayi ta d'auko cup bisa dinning table ta bud'a firji ta d'auko swan water da sukayi kankara tajuye a cup d'in mik'a ma Feena
"Amshi naga kinshiga tension fa."
Tsaki taja tunda nasamu wannan cikin doctor yace wai nadaina shan zai iya min illah shine nake shansa duk bayan one week saboda bazan iya hakura ba."
Amshi kisha zuwa anjima munyi magana Feena ta mik'a zata Amshi cup d'in dasauri ta janye "yahaka Khairi zaki bani abu ki janye bana son haka fa kinsani."
"Kada Ammar ya dawo ya iske cikin yanayin da bahaka ya barki bafa."
Mswttt in ma yanan mezaiyi ne yaje kano wannan jarabbabun parents d'in nasa suka kirasa fa a yau kuma yatafi bana khairi ko narage tension kafin musan abinyi" Khairi mik'a mata cup d'in tayi aikam feena bata jira komai ba takafa cup d'in a baki sai da shanye ta dire sa haka khairi itama haka suka dinga shaye shayen su a tsakiyar palour daganan kowace ta baje suna sambatu har wani bacci mai nauyi ya d'auke su suna sambatu marasa kan gado,
_*Hmmm mutuwa bata sallama bare kwankwansa k'ofa bata sanar da bawa tazo d'aukar ransa bata nuna maka Alamar tazo domin ta dauki ranka inda ka aikata khairan zaka gani inka aikata shairan zaka gani basu tsoron su mutu a halin da suke ciki insu mutu suje suce ma ubangiji me Allah yakara tsaremana zuciyoyonmu daga sabonsa*_
_______________Doctor Hafeez matsowa yayi kusada gadon da Khadija take kwance yayi "Sannu yanzu bakya jin ciwon wani abu a jikin ki ne?"
Gyad'a masa kai tayi .
"Kin tabbatar da komai normal bakya jinki cikin wani Feeling ne?"
Dije cikin murya ta kasa kasa wadda bata d'aga ta ba tace "Doctor banajin komai sai dai karfin jikina Amma banajin wani ciwo a jikima yanzu."
"Shima k'arfin jikin naki zai dawo normal kinji idan kuma kinason lafiyar ki sai kin rage saka damuwa a tattare dake kinji ko."
"Insha Allah Doctor zan kiyaye duk abinda kafadaman nagode."
Ammar dake gefe d'aya tunda suka shigo kuwa yaga yadda Doctor Hafeez ke ma Dije magana kasa kasa tamkar wasu masoya wani abu yaji yana masa yawo wani haushin Doctor Hafeez yaji yarasa kuma haushin ko nameye yakeji tsaki yaja wadda Mammy ta juye ta kallesa tab'e baki tayi ta kauda idon ta daga barin kallon sa Ammar ya juyo zai fita ya bud'a kofa cin karo yayi da Daddy zai bud'e ya shigo cikin wani fad'uwar gaba da ganin Daddy ya dawo da baya......
_*Wallahi wani uzuri ne Babban yakatseman typing d'inan kuyi hakuri*_ππ»
_Ga masu tambayan number ta basu samu yau ga number ta a free duk mai so ya dauka ina maraba dashi indai babu wulakanci tattare da kai ko wata bak'ar magana_
ππ»
08164042255
_*AMATALLAH*_π
[11/3, 10:55 AM] ππ: π· *_MATA KO BAIWA??π·_*
_*BY AUNTY* *HAFSY*π_
( _*INDON KAUYE*_)
_*54&55*_
_Dije tana miko gaisuwa tace agaisheku sosai tana godiya da kaunar ku gareta sakonku yana iso mata_
_Mss hafsy stylishlady_ ( _Ranan d'aurin aurena_)
_Ummun fadeela_
_Maijidda_
_Nanawo special_
_Khadija jabeer sanda_
_Jidda bin usman_
_Mairo ta Ado_
_Zakiyya_
_Salma jb_
_Beauty_
_Princess_
_Aysha naseer_
_Nana Khadija_
_Ramlat Mahmood_
_π€¦π»ββKunadayawa wallahi Amma a hankali duk zan lissafo ku_βπ»
"S...annnu da zuwa."
Kallon ta yayi can kuma ya d'aure Fuska tunani yake a ina yasan wannan voice d'in nan kuma duk inda ya tab'a ganin wannan fuskar ya tab'a ganin ta don kawai wannan ta canza mishi ba wadda yasani a kauye bace k'azama,
Bin ta gefen sa tayi zata wuce muryar sa taji
"Inasu Mammy ne?"
Cikin kyarma Murya tafara magana domin har ga Allah tsoron sa takeji tun had'uwar su a kauye,
"Sunje Unguwa Amma yanzu zasu dawo."....murya tana kyarma take fad'in maganar kafar ta d'aya na shiga cikin d'aya zata bar palour cikin sauri ta shige ciki maida k'ofar tayi ta rufe ta haye bisa gado ta shige cikin Blanket ajiyar numfashi tafarayi "Nashiga Uku meyakawo mugu nan."
Wata zuciya taji tace mata
"Mijinki ne fa yanzu yana da iko Akanki."
Wasu hawaye taji kwanciyar taji ta