Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma ba daga ke ba, me na yi maki na tsana haka? Ta kasa matse kwallanta cikin hawaye ta ke magana, ta ce yanzu kai ne me bakin gaya man haka? Yaushe ka damu dani, ka zo garin saboda ni ne wa'anda ka zo domin 135 su ai ka neme su, kana isowa ka nemi 'yan uwanka da Uwani, ni ko waya ka yi man ka sanar dani zuwanka? Ni na san matsayina a wajenka, don me zan matsawa kaina da zaman jiranka, in da farkon aurenmu ne na rantse wallahi ba ka iya nesa da ni har na tsayin lokacin da ka dauka. Ya zauna bakin gado ya gyara baki ya ce, To menene kuma na kukan in har maganar gaskiya za'ayi, saunawa na ke zama ina gaya maki ga yadda yada ce mu zauna, amma sai ki basar da ni, wallahi kin ga abinda na ke tsoratar mana, amma dai har yanzu ba mu makara ba, ki gyara halayyar ki na zama macen aure sosai, ni kuma ki sanar da ni kuskure na wallahi a shirye na ke na gyara kome, ta zauna bakin madubi tana tukke gashinta ta ce, kai dai kawai ka je ka cuce ni, son da na nuna maka ya kwaran, Sahabi sai abin ma ya dai na bashi haushi ya soma dariya ya isa gare ta ya dora hannunsa abayanta, yace, I do hope you still love me, as I love you ta muskuta ta ture hannayensa tace, kaje ka yi abinda ranka ke so is your time, ni ma nawa lokacin na zuwa zan rama, ya rusuna yana sunbatar sassan bayanta ya ce, haka ki ka zaba? to shikenan. Sahabi ya rinka sintiri daga falo zuwa waje wajen su Peter sannan ya dire dakin Mami kamar wani bugagge har dai ya kammala da komi sha daya na dare ya kwanta saboda mami ba wai don ya gaji ba, domin ya saba ya wuni tsaye ya kwana zaune suna aikace-aikace, sun yi auratayya mai tsabta domin su duka tsabtabtun ma'aurata ne, duk da 136 sangartar Mami a nan kuma Allah ya shirye ta bata cikin sangartattun da basu da haramiya wato abin nufi a nan yawancin yaran yanzu masu dabi'u irin na su Mami shedanancin lalata sun fi karuwan kasar nan illa domin su tsarinsu irin na turai ne, (Allah ya shirya mana zuri'a amin). a Mami ta kwantar da kai bisa kirjin Sahabi tana ci gaba da sheshekar kuka, Sahabi ya mikar da hannun sa ya kunna fitilar bacci duk da bula ce mai duhu sosai amma yana iya ganin hawayenta na diga Kirjinsa, ya tsura mata ido, yasan dai dalilin kukanta, don hake bai son tambayarta amma abu daya ya ke bashi mamaki duk yadda ta rinka yarfas da shi tun zuwan sa amma babu daya daga cikin hakkinsa wanda ta danne masa, sai ma cigaba da ya ji ya kara samu. Ya mayas da hannu ya kashe wutar sannan ya zuba hannayensa gaba daya ya rungume ta tsantsa, ya ce, wai kuma mene ne yanzu? Tace, koma mene ne ai ka sani tun da kai ke kulla komi, yace ban fahinta ba? ta ce, Ni dai Sahabi in har akwai kauna tsakanin mu, to mu tafi tare, zan dauki hutu idan na ga zan iya to, idan na ga ban iyawa idan hutuna ya kare zan dawo wajen aiki na, yace, idan kuma kina iyawa fa! Tace, shikenan zan ci gaba da zama na hakura da aikin. Sahabi ya yi shiru, ya amince matarsa Mami na matukar sonsa, amma shi yasan ko ta je ba zata taba iya wannan zaman ba, kuma rigima ce sun fara kenan wanda na iya sanadin rabuwar shi da ita, amma dai ya tsarata don a rabu lafiya yace, To shikenan ta shirya a 137 hankali, idan ya koma zai ma Oga dinsa bayani daga nan bayan kwana 7 sai Peter ya zo ya tafi da ita. Idan kuwa son ran Mami ne Uwani ke sata wannan kukan ita bata son ta bude ido ta ga duk wani mai halaka da gidan su Sahabi wannan shi ne ainihin damuwarta, ita a tunaninta sun fita matsayi a zuciyar Sahabi. ba Da safe fiye da karfe goma mami bata fito amam shi Sahabi ya dade da fitowar har wasu gungun abokansa sun zo tare ma suka yi kalaci, sun ma wuce da alkawarin za su dawo an jima. Can Sahabi ya fakaici idon su Uwani ya kwashi kayan kalaci ya kaiwa Mami har daki ya tayas da ita, ta dubi abuwan da Uwani ta dafa cikin borin kunya tace, Ni yau konfiles kawai na ke so ya ce. Haba ga agade da kwai da koda da dankali an soya ki daure mana kici ko dan kadan, tace, Bana marmarinsu. Ya kwashe kayan ya fidda kwalliyar mami yau na wata hadaddiyar shadda ce, siket ne da riga amam rigar 'yar Firit ce iyakar ta gaban cibi amman dinkin ya yi kyau da ita shaddar mai ruwan siminti ta baza turare, ta shiga kicin cikih yauki da yamutsa ta hada abinda ranta ke so, sai da Kiristi ake watsawa turanci har da barkwanci, amma Uwani sai hararta ake yi, wannan bai damu Uwani ba dominw anda ya fita ya kawo ta gidan. Mami ta shiga falo kenan zata zauna, adaidai nan Sahabi ya shigo daga waje ya yi ma wani abokinsa rakiya, yace, Yauwa Mami kin fito ba, zo nan don Allah ina son ganinki, suka jcra zuwa ainihin dakin 138 baccin sahabi na da, kaya ne a jakunkuna birjit bisa kafet, Mami mamaki kawai ya cika ta, yaushe Sahabi ya shigo da wannan dukiyar? Ya juya ya dube ta yace, cauna mana, ta zauna bakin gado ya zuge wata bakar jaka a London ya sawo ta, ya fiddo wa da Mami Sufofinta biyu da leshinta biyu da wani material baki ne suduf y ana daukar ido, sai Shaddoji galilah, amma dai material din ya fi daukar Mami ta rinka yafa shi a kafada, Sahabi ya yi murmushi ya се, Kema kin yaba da shi ko? Ni ma wallahi duk ya fi tsuma ni, kuma ke kadai na saya mawa, a wajen matar wani ogan ogan mu a Delta, kin ga waccan jakkar duk kayan ki ne na kale-kale, ai ina jin ban yi mantuwa ba ko? Ta kwantar da kai bisa kafadarta ta ciko fuskarta da fara'a ga murmushi wanda ya juyar da kwayoyin idanunta sukai matukar kyau, ta ce, gaskiya Ab-kar tsaraba ta yi kyau Ya ce, Na ji dadi tunda na zama yaron kirki, yau Mami ta yaba mani ta ce, don Allah kada mu yi haka da kai ai ni ma yarinyar kirki ce ko? Ya girgiza kai, ya juya yana dariya ya jawo wata leda Shaddoji ne irin na maza masu tsadar gaske, kala biyu ga turaruka kala biyu 'yan dubi ashirin da biyar ya dora bisa cinyar mami ya ce, wannan na Babanmu ne na san za su dace da shi ko ba haka ba, ga turamen holland uku ki baiwa su Anti Zainba ai sun yi ko? Dadi ya lullubc ta, wane irin kudi Sahabi ya samu haka ne ya ce, Mami na yi tunani na rasa abinda ya dace na sai ma lyana domín na ga ba abinda bata kawo wa na sayarwa saboda haka ga kudi zan ba ki kila kin-san abinda ya dace da 139 mu kai mata, ita dai tama rasa bakin magana domin taga hidimar ta yi yawa. Ya mike ya jawo jakarsa ya bude ya fiddo dubu hamsin ya dora mata. Ya kara jawo matcrial din nan "Ya ce, kada ki dinka shi a nan, ki jira sai mun je Legos domin nasan sun fi nan iya dinki, Ta ce, Ai daman! A nawa ka sawo shi? Ya ce, Dubu talatin da biyar na so kwarai na sawo ma Hajiyata to nasan ba zata daura ba sai ta barwa su Hafsat; nan da nan Mami ta ji wani yu a zuciyarta, ta daure tace, to sai ka sawo mata me? Ya ce, Sufofi ne da lesisis, suma yaranta da su Uwani haka, ki dan sami dubu biyar ki sawo ma Kiristi wani abu a kasuwa. Ai tuni Mami ta tsani komi da Sahabi ya sawo mata, shi kan shi Sahabin haushi ya ke bata, ya yi magana tafi sau goma amma Mami bata tsinka masa ba, sai dai uhm ko a'ah ko ta jinjina kai, Sahabi dai ya fuskanci Mami ta shiga yanayin da ya tsana sai shi ma ya tsani komi ya mike ya fice abinsa. Bai tsaya ko ina ba sai wajen Hajiyarsa inda ya sake ya baje ya manta da duk wata damuwa illa walwala da jin dadin hirarraki, duk irin labaran da ya fis o hajiyar ta sanar da shi ya dauki lokaci mai tsawo a nan suna hirarsu, yayin da ita ma Hajiyar ta rinka tambayarsa yanayin can wajen nasa, ya bayyana mata komi dalla-dalla har ta gamsu da cewa lalle yana bisa hanyar samun kudi, ba wai kudin kanfani ya ke ta'asa da su ba. Ko da Uwani ta ga la'asar lis babu Sahabi lalle tasan ya ci abinci inda ya ke, don haka sai ta kara adana masa na ranarsa. Shidda saura kwata na 140 yamma ya iso zida, wayarsa ta G.S.M manne a kunnensa yana magana da wani ofisansu da ga Dalta, har ya shiga falo ya zauna ya nemo takarda yana daukar gundarin sakon da ake sanar da shi, ya fi minti sha uku yana daukar sako, har Mami ta zauna, ta yi tagumi tana kallonsa. Ta na tsanarsa a ranta, amma kuuma gargadin su Zainba na danne damuwarta. Ya kammala da wayar ya nade takardar ya soka aljihu, ya dubi Mami a gajiye ya cc, Uwargida ya dai! Tace, lafiya lau, su Anti ga sun zo, Baba da Iyana suka turo su ayi ma sannu da zuwa, tare da godiya yace. haba babu komi, kin san dalilin wayar nan, aiki ne oga ya turo man dole na yi asubanci naje Abuja amma a goben zan dawo, ko zamu tare? Ta yi dariya ta ce, muje mana don ma Abuja; ya ce, shikenan idan munyi Sallar issha'e sai mu je mu gaida su Iyana anjima ko? Ta ce, to. Sun caba ado na ganin sarki zuwa gidan su Mami duk mai kaunar su idan ya gansu zai yaba ya kuma ji dadi babu ma kamar mahaifin Mami Abdujalal wanda ke son Sahabi tsakani da Allah. Da asuba Peter ya debe su sai Abuja ana aje Mami gidan abokinsa Ibrahim amma sam Mami ta ki, dole sai hilton Peter ya kai ta ta yi masu kamun gurin kwana. Ta dan fita yawo ita da peter zuwa gidan kanan Iyana da wata kawarta, sai karfe tara da rabi na dare Sahabi da peter suka je daukarta zuwa hilton. Wanshe kare ya kammala ayyukansa suka koma kaduna to haka dai hutun Sahabi ya zamanta na 141 kwana biyar a kodayaushe dai shi ne matan Mami ce mijin, sai dai ayi yadda ta ke so. 車車 *** Kamar yadda Sahabi yayi wa Mami alkawari sati guda ya turo peter azo a tafi da ita, ya rubuto mata ta biya gidan Hajiyarsa ta zo mai da hura da dambun nama, Hajiyar sa tayi muma da ganin tafiyar Mami, domin tafi sha'awar ganinsu tare, tunda itacc kariyarsa. Tun Mami na sheka bacci a mota, har ta gaji idanunta suka kekashe, sai azabar gajiyar tafiya tama rasa abinda ke mata dadi ta sha lemon gwangwani taci naman da Hajiya ta bata na Sahabi, sun tsaya wani resturant ta sayi abinci amma kuma kyama ta hana ta ci abincin. Ba su isa River ba sai karfe tara da minti arba'in na dare kai tsaye peter ya kai ta masaukin Sahabi kamar yadda Sahabin ya sanar da ita gidan bai dace da matar aure ba yar mutunci a harabar gidan abin da ya soma bata tsoro kabilu ne zaune bisa kujerar kwando ana ta kwankwadar barasa, gaba dayansu kuwa sukai wa Mami ca da ido kamar mage ta ga bera, tun ana hankalin Mami ya soma tashi, ta hana Peter fitas da kayanta daga but G.S.M dinta ta soma tsuwwa ta balle jaka ta fiddo ta kanga a kunne, ta ce, Mami ce, sai ta ji muryar Sahabi nan da nan gabanta ya fadi ras tace. A'ah me ya faru kada dai kace man bazan samcka ba aа 142 dakinka! Ya ce sannunku da zuwa, hala kun iso ko, wallahi na yi iyakar kokarina amma sam oga ya ki amince man, ina nan Werri insha Allah komi danre zan kasance, tare da ke, ki yi man gafara: ta ce Amma dai wannan shi ne wulakanci kana nufin na zauna cikin wa'annan kabilun ni gaskiya tsoronsu na ke kyi! Ya ce, ka da ki damu na yi masu bayani cewas matata zata zo, ba abinda za su yi maki ki kwantar da hankalinki please! Suka isa kofar dakin Sahabi makwabcinsa musulmi ne mutumin Kogi ya fito ya mikawa Peter makullai ya gaida Mami cikin girmamawa, a lokacin ne ta soma jin dan san yi san yi kila zai iya ceton ta idan wa'ancan sun zo afka mata. Tana shiga falon Sahabi ta mayas da kofa ta rufe gam da makullai duk da sanyin A.C da kayatarwar da akaiwa falon bai kwantar da ran Mami a ganin ta zama da wa'ancan komi na iya faruwa, ta shiga dakin baccin Sahabi kato har ya fi na su na Kaduna girma, an shirya shi sosai abu daya ya faranta ran mami hotunan ta ne kaf a dakin baccin sa, ko wanne bangare, amma a falo sai na shi da mahaifinsa da Hajiya. Ta tsaya gaban gadonsa tana kallon wani hotonta da ya dauke ta tana kwance daga ita sai shimi a yankari. Ta kewaya bandaki ta dade zaune, tana tunane-tunane, a karshe dai ta sakarwa kan ta ruwan shawa, ta fito fes, ta yi zaune bakin gado ta zuba tagumi duk dan motsi ta zabura a tsorace, haka dai ta yi ta zirga-zirga ta sunce tawul din Sahabi ta jawo jallabiyarsa ta saka sai karfe goma sha biyu da 'yan 143 1 . mintoci na dare Sahabi ya dawo ya rinka kiranta а hankali yana rankwasas tagar dakin baccinsu, ta saurara a hankali ta tabata muryarsa ce, sannan ta bude tagar ta mike mai 'yan makullan. Yana shiga ya kamata ya rungume amma ita ko ta saka mai kuka, ya shiga lallashi gadangadan, da kyar ta hakura ta zauna ta sauraresa, ya ce Na ga duk abin cin da nasa aka shirya maki ga sunan a falo ba ki ci komi ba why? Ta daga idanun ta ta dube shi tace, wallahi na yi dana sanin zuwa na, bayan bakar tafiya, sannan yanayin gidan kwata-kwata bai yi min ba, yanzu Ab-kar ya zan yi? Ya ce, A to komi na yi kokarin nuna maki Mami ba kya yadda ke kan ki kin san halina da son mu kebe mu yi hutu, tunda ki ka ga ban gayyace ki ba, ai dole kin san babu hali ne, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same ki insha Allah! Ya shiga sunbatar da ta dauke dukkan damuwarta da fargabarta sannan ta gusar mata da doguwar gajiya, ta sami kuzarin karfin dogaro da kanta, ya daga ta zuwa falo ya zaunar da ita ya jawo kayan abinci ya cika mata filet ya tura a gaban ta ya ce, 'To bissimillah tace, kai kuma fa? Ya ce, I'm okey, ai duk inda muke akwai abinci zagaye da mu, wannan na ki ne nasa akai maki oda zan shiga wanka, kin amince? Ta juya ta dubi bakin kofa, tace, ka tabbata ka kulle ko ina? Ya ce Haba Mami kada ki rikita kan ki me za su yi maki, yanzu haka kowanne tare ya ke da budurwarsa, ki manta da su don Allah Ya mike zuwa wankansa. 144 Duk yadda ya saba nuna mata gwanintarsa ta fannin soyayya bai ga alamar Mami ta gamsu ba kamar yadda ya saba birgeta a kullun sukai love making, yau dai da banbanci, bai kuma san dalili ba. Da safe ma sun sha rikici kwarai da zai tafi ofis duk da ta yi sa'a ba za shi ko ina ba a nan Rivers zai yi aiki, da kyar ya shawo kanta ya tafi ofis, ita cikin kuka shi kuma ran sa a bace, a gaskiya Sahabi ya soma tsanar wannan aure, yadda mami ta taba cewa takura ce, shi ma yau cikin ransa ya ce takurar ce. A ofis haka nan Sahabi ya rinka aiki ba cikin jin dadi ba, lokaci-lokaci yana kiran Mami ta waya amma sai ya ji ta cikin kunci da damuwa, misalin karfe biyu na rana ya samo shawara ya tuno da wani dan uwansu Hajiyarsa wanda ke aiki a Inter-City bank wato Abdullahi tun zuwansa Rivers sau biyu ya taba zuwa gidansa amma suna yawan gaisawa ta waya, ya yanke shawarar kai mami gidansu wajen Iyalinsa sai lokacin bacci ya rinka dauko ta, nan da nan ya yi ma Abdullahi waya, a mamakinsa har Abdulahin ya so ya bata rai ganin ai shi ya zama dole ne ma ya kai Mami gidansa tun da bashi da kamarsa anan Rivers. Suna aje wayar ya nemi izzini zuwa gida ya je ya sanarwa Mami shawarar da ya yanke, nan da nan ta mike ta hada dan abinda zatai amfani da shi ta bishi ya kai ta gidansu Rakiya. Ta yi murna kwarai da ganin Mami, wannan ya karfafa zuciyar Sahabi ya koma ofis cikin murma, ya shawo kan wannan matsalar. Rakiya ta shiga ririta mami kamar 'yar tsana har itama Mamin ta sake sosai duk ta saki 145 ranta. Sun ma fara kulla shawara ran asabat za su saye-saye wata kasuwa mai arhar kaya da kyau ita Rakiya 'yar gari ta san kan kasuwar, a nan ne Rakiyar tace insha Allah zan amshi kudi a hannun Abdullahi na yi ma Hajiyar su Sahabi sarin zannuwan gado yadda zata sayar a Kaduna taci riba sosai, wallahi ina son hajiya, ina girmamata kamar ita ta haifi Abdullahi saboda mutuncinta da kamun kanta, kin san Abdullahi a hannunta ya zauna ya yi hidimar kasarsa, idan yana yabonta har bana so, domín ni ce zan nuna mai halin hajiya yadda take nuna man, kin san haihuwar da na yi ta farko a hannunta na haihu tace kuma na zauna a gidanta wallahi ni kam ta yi man abinda uwata zatai mani, ki rinka addu'a kina godiya wajen Allah Mami da Allah ya baki suruka irin Hajiya. Wannan zancen na Rakiya shi ya kara jagula ran Mami, ita a yadda ta dauki Hajiya makiyiyarta, don haka ma yanzu ta tsani Rakiya da Abdullahi suma sun zama layin makiyanta, duk yadda ta tsani zama masaukin Sahabi gara can sau dubu da ta zauna da Rakiya tana wani yabon wannan muguwar Hajiyar da bata san komi ba sai 'ya'yanta, (a shirmen Mami fa!) A gidan Abdullahi Sahabi ya yi sallah mangarib da Isaha'e, bayan sun ci sun yi kat, ya dauke ta suka tafi. A nan Sahabi ya shiga yawo da Mami lungulungu har ma'aikarsu sai da ya kai Mami, ba su koma masauki ba sai can cikin dare. Wan shekare da safe yace, idan kin shirya Peter zai kai ki gidansu Rakiya yau ni Imo zamu amma yau zamu dawo, sai dai na 146 san za mu yi dare sosai, don heka zan yi kokari na yi ma Abdullahi waya na sanar da shi ta sha mur tace, 'Kar ka sha wahalar yin waya yau ba inda zani ya fiddo ido me kenan kuma? Ta dube shi yadda ta saba a wofance, Haka na ga dama sai me? Da zuciya ta kule shi bai san lokacin da ya ce. 'Gaskiya, gaskiya ke matsala ce Mami, nan da nan ta mike zaune ta се, Nice matsala ko, to wallahi ka gama zama da matsala, sai kai magani na, ina dalilin wannan takura kai ban kira ka matsala ba sai kai! Ya debe kayan aikinsa ya fice shi dai yinin wannan rana bai san yadda ya gudanar da ayyukansa ba, shifa ya soma zullumin Mami din nan ko dai wani abu ya shafi kwakwalwar tane iyayenta ba su gane ba? har yaushe za'a ce yarinyar ba ai mata komi ba a ko da yaushe sai tsiya, kai wannan ya zarce rashin tarbiya, yanzu kuma idan ya nemi ya kai ta asibiti a diba kanta ta sa mai ihu ya dora mata hauka, shin to mene ne abun yi, shi kam ya gaji! Lokacin da ya dawo ko ina a bude bata kulle da makulli ba, ya duba agogo karfe daya da rabi na dare, gabansa ya fadi anya ko Mami na nan! Har ya shiga dakin baccinsa gabansa na faduwa bal,6al a mamakinsa Mami na kwance bisa kafet ko filo bata saka ba yace, ikon Allah ya isa inda take ya tsugunna yace, Haba Mami kamar yau'mu ka soma samun problem ki yi man hakuri ki koma bisa gado ki kwanta, ki tuna nan ba jihar mu bace, mu bakin kwadago ne, idan rayukanmu sun 6aci wa zai damu da mu? Sai mu imu, ta galla mai harara tace, wannan 147 ita ee cutar da ka yi man inda a Kaduna har ka isa ka zo ka yi man wannan surutan marasa ma'ana, bari na gaya ma, daga yau ba ni ba kai na gaji da kai ka fita raina, kasan Allah idan kaci gaba da matsamanz an koma harabar gidan nan da zama har sai ran da ka gama ikon ka kasa aka mayas da ni gida ya jima a tsugunne yana dubar kwayar idonta lalle da ta yi mai abinda tace gara ya hakura da ita har ta koma Kaduna, ba tare da ta wulakanta shi ba. Yace, Na amince da sharudan ki, amma ni ma don Allah ki taimakan ki koma bisa gado daga yau ba zan sake yin abinda zai kusanto ni gare ki ba zan kasance a falo har ki bar garin ta mike da sauri ta haye bisa gado ta kudundune. Kwanan ta bakwai cif ko gaisuwa bata hadasu, hatta kudin da za'a sai ma su Hajiyarsa kayan lanbu Peter ya baiwa, da sassafe karfe biyar ta gama shiryawa, ya kawo kudi dubu hamsin ya bata ya сe, zai turo mata da cek sati biyu masu zuwa, tace, ka bar kudinka na ga yama gaskiya ka yi ma kan ka maganin matsala, ba fa za ka sake zama da matsala ba, ta yi mai wurgi da kudinsa ta fice, ya bita har mota ya bude but ya turo a aljihun akwati ba tare da ta sani ba. A Abuja su ka ci abincin rana ana mangarib suka iso kaduna tace ya wuce da ita gidansu,ta yi kuma sa'a Iyana na nan, bayanta sallami Peter ya tafi, sun kulle daki ita da Iyana, Mami ta hade kanta da gwiwa ta shiga kuka wiwi, Iyana ta zuba mata ido kawai tana kallon ikon Allah can ta nisa tace, Wai ya sake 148 ki ne? Cikin kuka mami ta daga kai ta dubi lyana tace, Ni wallahi lyana yanzu neman sanadin da Sahabi zai sakan na ke, na gaji da fitinarsa wai yanzu ni Sahabi ke ma gori na zame mai matsala! Iyana ta yi tsaki tace, To mene ne abin damuwa har za ki sawa kan ki damuwa ki ta rusa kuka, daman can ke ki kace kina son sa, tunda har ku ka kai tsayin wannan lokacin ba'a haihu ba, ai kila ba rabo ne a tsakaninku, saboda haka banga abin tayas da hankali ba anan, inda kun haihu ne a tsurawa zuciya damuwa kan 'ya'ya, yanzu ba shike nan ba kowa ya kama gabansa. lyana tace, tashi mu je can falo wajen Babanki, suna shiga Alh. Abduljala yasan ba lafiya saboda a cikin kwayar idon lyana ya kan fahinci rigimar da ta zo mai da ita ako da yaushe, ya hade yatsunsa ya dunkule hannu yana jiran ya ji ko mene ne, can Iyana ta zauna ta tsara yadda ranta ya raya mata zan ce dai duk na bata mutun wanda ita kanta Mami ta yi mamaki sanin Sahabi bai taba yi matan haka ba. Abduljala ya dafe kansa yadda ransa ke masa daci tamkar ya bar duniya domin shida i yana soń zuri'ar Sahabi kuma yana son halayyar Sahabi koma dai mene ne shi yasan ba duk ba ne laifin Sahabi dole ne itama Mamin da laihinta. Abduljalal ya lumfasa ya ce yanzu ke Mami raba auran shi ki ke so? Bata cc uffan ba ta yi kuri da ido a kasa can tace, Ni Baba na yanke shawara England zan koma na karo ilmi zan je na yi Second Degree dina, Babanta ya ce, Ni zan dauki nauyin karatun ko Sahabi? Ta ce Ni Baba kai 149 zaka dauki nauyi, yace, in dai ina da iko da ke kina son kuma tafiya karo ilmin to ki koma gidan Sahabi, ina son ku zauna lafiya ki je karatun a bisa umarnin mijinki, yana rufe baki Iyana ta hau shida bala'e, akan don bai san 'ya'ya mata shi ne ya ke son, bakin cikin Sahabi ya kashe Mami to ita ba zata yadda ba, ta mike ta bar falon, mami ta sadda kai tana ta sharban kuka ganin yadda Iyana ke neman ta zagi mahaifinta saboda ita ko da yake dai tasan Iyana ta saba zagin mahaifinsu a duk lokacin da ya 6ata mata rai, ko kuma ya nemi ya canza mata shawara, a nan dai Alh. Abduljala ya rinka lallashin Mami wanda ya san shirme ya ke yi sai Iyana ta ga dama zata bar ta ta koma gidan Sahabi a wannan daren da shi ya ke bukata. Ko da Peter ya kaiwa Hajiya sakon Sahabi, ta ce, saukar yaushe, yace, zuwan su kenan amma ya sauke Mami gidan Iyayenta har da kayan ta gaba daya Hajiyar bata zargi komi ba ta san sangartar mami, amam da Peter ya ce, a nan gidan Hajiyar Mami tace ya kwana sai ta san to akwai wani abu, a nan Hajiya tace, Abba ya kai shi dakin baki ya zo kuma ya kai ma Peter abinci, kafin ma a kawo mai abincin Peter har ya shiga shawa, ya ji dadi da Mami ta ce ya kwana a hannün Hajiya domin yasan kula ta musamman har sai yace ta isa, ga alhairi da zai samu idan zai tafi. Sai da Mami ta share kimanin kwana goma zaunc a gidansu tana juya rayiwarta yadda ta ke so ba kwaba ba tsargwama. a wanan ranar ce lyana zata 150 Abuja suna sallama da Mami, ta ce, lyana na gama rubuta takardar neman makaranta har kala biyu a England, insha Ållah kuma zan samu idan ma baba ya ki biya mani ina jin zan samu a biya man a ofis din mu under

Chapter 10 of 13