zai
yiwu ace ya tsaya can kasar wa'anda suka shirya
559
wasan to amma ina a yadda duniya ta lalace, sai
addu'a wanda zai iya kwabawa iyalinsa ya kwaба.
Kiristi ta leko tace, Anti abincin ya dafu mamit ace,
To ta je sito kawai set din kuloli masu guda uku ta
dauko ta wanke ta zuba abincin ita Mami da Sahabi
sannan ta zubawa maigadi ta kai mashit a kuma kai
ma Ya'u ko ta kira sa ya dauka. Kiristi ta yi yadda
aka cc.
Mai gida Sahabi ya kuke aiki ya je bisa
wa'annan in jina ya koma bisa kumfuta har dai can
ya ji kamar zai fadi ya shafa cikinsa yinwa ta ci
kariinsa ya duba agogo biyar ma ta shige, yace, "Wai
gara aje gida ko ba don abinci ba don aga
kykakyawar amarya ma ai ya dace ya kulle komi sai
gida, Mami na tsaye wajen takalar shiga falonsu a
harabar gidansu Sahabi ya yi hon maigadi ya yi sauri
ya bude get, suka yi ido hudu da ita ta daga mai
hannu shima ya karaya kan motarsa sannan ya sun
baci tafin hannunsa ya daga mata, tayi irin
murmushin nan najin dadi ta sunne kanta cikin
kafadunta alamun jin kunya, ya fito ya dauko wata
leda a bayan motar sai da ya kusan isa gare ta sannan
mami ta karasa a hankali ta taryeshi ya bude hannun
sa na dama, Mami ta shiga cikin hakarkarin sa, suka
shiga cikin gida kowannne su cike fal da fara'a, kai
tsaye dakin baccin su suka shiga Mami tayi tsaye
tana dubarsa ta rungume hannayneta bisa kiji shi
kuma yana kokarin fitas da kayan shi ya fiddow ata
jallabiya ya zuba, ya isa gare ta ya yi mata yanw
asanni, ta gamsu sannan yace, raka ni falo man na ci
60
abinci ko na sami kuzarin kula ki sosai, hala har kin
ci na ki? Tace, Na zauna ina jiranka mu je mu ci, ya
rike hannunta suna tafe yana tsokanarta da zance,
yace, "Mc ki ka dafa mana? Tace, gaskiya Kiristi na
baiwa umarni ta dafa mana ta dafa shinkafa da
dankali an kuma yi ma farfesu. Yace, to bai dai so ba,
amma ya danne sanin kan shi ne idan yace, ta kawo
kayan lanbu da ruwa, Kiristi zata kwalawa kira ta ce
ta kawo don haka sai ya tsaya gaban firij ya debo
masu.
Foodflask na farko da ya soma budewa na
shinkafa ne, sai dai ba iya banbancewa shin faten
dankali da shinkafa ne ko mnce ne? sun hadu sun
narke gaba daya ba'a iya banbance shinkafa balle
dankalin, a karo na farko Sahabi yayi mata tsawa
yace, Mami mnce ne wanan? Ta sha mur tace, me
idonka ya gane maka shinkafa ce! Ya bude filas na
miya mai yayi mai anbaliya ya zubo, nan ma ya ja
tsaki ya bude filas din farfesu babu mararraba da
miyar ja irin miyar nan wadda tumatur zalla bai nuna
ba, ya ja tsaki, ya tsaya ya yi shiru, ya ce, an ba masu
gadi? Kan Mami a sadde tace, 'Eh' yace, to a kara
masu wanan idan za su iya ci, ya dauki kayan lanbu
ya koma falo ya zauna bisa doguwar kujera ya murda
talabijin zuwa ga tashar N.T.A Kaduna, ya soma cin
ayaba sannan gwanda ya koma kan tufa ya jawo
lemo, duk bai samu natsuwa ba, ransa na mai zafi, ko
me kuma zai yi don dai ya zauna lafiya da Mami,
lallashin ta dai zaic ig aba har Allah ya sa ta amince
ya ncmo mai koya mata girki kunya ma kawai ta ishe
61
shi ta maigadi da Ya'u ace wai daga iyalansa aka
fiddo wannan kwamacalar. Mami tuni ta koma dakin
baccinsu, shi ko daga falo bai zarce ko ina ba sai
masallaci, aka sallaci mangarib da shi sai ya jawo
alkur'ani ya soma karantawa bai tsaya ba har sai da
akai issha sannan ya tsaya ya yi kirari ga sarki Allah
a karshe ya roki Ubangiji ya kawo mai mafita game
da al'amarin aurmesa.
Ya koma gida falon gidan zuwa kicin ko ina tsit
itama Kiristi jikin yayi san yi ganin abincinta ko Ya'u
ya kasa ci sai maigadi ya zuba aleda zai kaiwa
almajirai a can anguwarsu Judunwa. Sahabi ya shiga
dakin baccinsu yace, assalamu alaikum Mami da ke
tsaye gindin madubi tana daura zani ta amsa ba tare
da ta dube sa ba, super holland mai ruwan cincin bale
ta zuba dinkin ya kame ta tsantsan, yace, "E ye 'yar
gaye kenan har kin yi wanka, ni ma ki ban minti
goma yanzu zan fito, ba ta dai tsinka ba, tana gama
wa ta mide akan kujerar da ke cikin dakin baccinsu
wato (Lazy man) ta soma karanta wani novel din ta
na turanci Sahabi ya fito yana shirinsa tare da dan
fitonsa da 'yar waka, ya saka kananan kaya, ya je
gaban ta ya zauna kusa da ita ya ja mata hanci, ta ture
hannunsa, ya ce "Haba my dear me zai bata mana rai
bayan mun mallakawa junan mu zukatanmu, don
Allah kada ki yadda wani dan kankanin lamari
wanda za mu iya maganinsa ya tsaya mana a gaba har.
ya hana mu cin moriyar kuruciyarmu, yanzu me kike
so na yi kin san dai ba zan yadda ba ki kwana da yinwa? Mami ta lumshe ido zan cen yayi mata dadi
62
sosai can tace, Wai mnee ne amfanin irin su Mr.
Biggs da su Bkaers Dclight? Ka baiwa Ya'u mana
yanzu zai kawo mana abunda ranmu ke so, a gaskiya
zan ga ya ma ni da man su ke dauke man lalurar
yinwa ta, in dai abinci ne matsalarmu wannan ba
dalili ba ne tunda ba a kauye mu ke rayiwa ba".
Yace, "Su Ya'u fa da maigadi? Tace Kiristi ta rinka
dafa masu har Allah yasa ta iya yace, kin kawo
shawara amma tashi mu je da kan mu mu sawo goben
mun aiki Ya'u ta dauko gyale wanda ya dace da
alanfarta ta yana a kafada amotarta akai tafiyar.
A Mr. Biggs Mami ta yi ma kanta hade-hadne
N500 na sahabi ma hakan su ka yi take away, sai
suka sayi kke da biredi don kalacin safe daga nan
suka tsaya a (Farm Fesh) suka sayi madara mai san yi
da gardi kamar kala uku farm fresh Sahabi yasa aka
kawo mai madara kindirmo mai zaki kofi daya, ya
kwankwade sanyin harabar da san yin nonon ya rinka
yi mai dadi a gabobin jikinsa. Sun dawo gida aka
zauna Mami cike da nishadi suka ci suka sha madara
ita kam ta koshi sosai amma shi ango ba dai haka aka
hore sa ba, ammai horo da abincin gida lafiyayya.
Amma kaunar Mami a ransa ya hana ya ga aibin
komi, suka kwanta da wuri don su mori amarcin su a
kuma tashi da wuri domin zuwa aiki.
Kawai wani hutun karshen mkao su Mami da
Maama 'ya'yan Anti Hadiza suka matsa akai su yini
gidan Uncle Sahabi, Anti Hadiza tasa direbansu ya
kai su, tunda suka je. sai kallo suke yi da Mami irin
kallace-kallacneta da ta saba, sai dai ta sa kiristi ta
63
debo masu juice a sito har karfe uku suna famar shan
juice har sai da Kiristi ta gama jalof din shinkafa,
Mami tace a zubowa su Maama, ga dai yinwa ta
matsawa yara sannan ga abinci an kawo sun kasa ci,
na farko kawai tsananin barkono ga masifar gishiri ga
mai na shake ka, yaran nan suka kasa cin ko cokali
biyu suka aje. Ganin haka yasa Mami ta yi ma Sahabi
waya a ofis ta ce, karfe nawa zai dawo gida? Ya ce a
gaskiya ba lokaci tace idan ka tashi ka zoda abin cin
ka, ni zan aiki Ya'u ya sawo mana nida su Maama,
ya ce, 'To' ta shiga fakin baccinsu ma ajiyar kudin
Sahabi ta debo dubu daya ta aika aka yo masu take
away ita da su Maama.
Har su Maama direbansu ya zo daukarsu amma
Sahabi bai dawo ba, biskit da lemon gwangwani ta
zuba masu a leda. A wanan dare Mami 'yar gidan
Anti Hadiza kwana ta yi zawo, nan da nan hadiza ta
yi anfani da aikinta ta tambayi yaranta dame-dame
suka ci a gidan uncle sahabi su ka gaya mata tsab a
nan ta gano iallar da Mami ta samu ta bata allurai da
magani zawo ya tsaya, babu zancen zuwa makaranta
da safe, abubuwa suka damu Anti Hadiza amma bata
son yi ma Hajiyarsu maganar gudun kada al'amura su
dagule, daga irin haka ne rigima kan shiga tsakanin
dangin miji da matar dan uwa, amma kuma ta bar
gidan dan uwanta ana sayen abincin, wannan ba
mutuncin su bane, dole zata sami hanyar warware
wannan matsalar.
Wannan kenan, watan su mami uku cur da aure
jijiyoyi da katon kai su suka bayyana tattare da
64
Sahabi, duk wanda ya san Sahabi kafin ya yi aure da
farkon watan sa na aure idan ya gan shi yanzu bai
yadda shi ne, ya zama jijiya ga wani irin tsufa ya
lullubesa duk na sanadiyar rashin more aure ne,
yinwa ce dare da rana, wai ya auro 'yar hutu, idan
yana ofis bai da hutu aiki ne mai yawa a gabansa
domin yayi hutun jkai da kaya aka ne, idan yana gida
yana famar tarairayar Mami, haka dai tashi kaddarar
ta zo mái sai addu'a.
Sa'adiya ta yi ma Anti Hadiza waya, bayan sun
gaisa da 'yar hirarsu tace Anti bawai zan cne gulma
ba ko tsegumi shin yaushe rabonki da ganin Sahabi?
Anti Hadiza ta ce, yau za'a yi sati uku kenan ko?
Sa'adiya tace, kune likitoci ya dace ki bincikesa
wannan irin jijiyoyi! Labaran da na ke ji wajen yara
abin ba dadin ji, Hadiza ta ce, Ai ni yara na har zawo
suka yi a dalilin sakarcin da kae yi a gidan Sahabi
don haka an dai na kai su, zan bincika don kada gidan
ya lalace har ya zamanto bai gyaruwa, kin ga ba za
mu so hakan ba, domin mun fi kowa farin ciki ace
Sahabi ya zauna lafiya da matarsa, ko ba komi shi ne
babba da a gidanmu kuma ya auri macen da ya ke so
baida ce ace ya sami tangarda ba hakan na iya sa shi
ya zama rudadde game da kowacce irin mace.
Wanshekare daga ofis Anti Hadiza ta yi ma
Sahabi waya,t ace tana son ganinsa, yace 'Me zai
hana su zo da daddare shi da Mama? Tace, Ina son
ganin ka ni da kai sirri ne, yace ina nan zuwa idan
mun yi breka ya iske ta a ofis din ta, ta kulle don
kada a dame su ta dauko kula da farantai guda biyu
65
tace, To bissimillah ta soma zuba masu wainar
shinkafa mai dadin gaske irin wainar 'yan Bauchi da
miyar kaji yadda taga Sahabi ya shaga yana cin
wainar sai ta zuba guda uku kacal ta bar masa sauran,
rabon Sahabi da ya ci abinci irin haka har ya soma
mantawa, Anti Hadiza ta rinda tausayinsa cikin rintsi
kwalla ta zo mata ta matse, wai Sahabin da Hajiyar su
ke shiryawa abinci kala-kala fiye da na kowa a
gidansu yau shi ne ya lalace da sayen abinci? Sai da
ya gama ya bude dan mitsitsin firig na ofis din ta ya
tsiyayi lemon ginger ya sha.
Yace, 'To Anti lafiya kae nemana? Ya duba
agogo yace, kin san irin, aikina tsauri ne da shi,t ace,
'Eh haka ne, ka yi gaskiya ama wai Sahabi dan gata
kamar kai da Mami a garin Kaduna me ya yi mkau
zafi da ba za ku dafa abinda ranku ke so ba sai kun je
wani Mr Biggs can kullan kuna yawon neman abinci
kamar gwauraye, ya yi shiru bai son zancen gidansa
da kowa tunda dai shike son mami dole ya jure da
kowanne iri ne halin ta" yace, Ba haka ba ne anti,
gaba daya aiki mu ke zuwa, kuma Mami da ni muna
da kyama, duk da na san mahaifiya ta ma aikin ta ke
yi amma kada ki manta kowa da irin halinsa, ina
hakuri ne a hankali har ta saba da hidimar aure Anti
hadiza tace, 'Amma kuma an ce kara tun yana dan ye
kae lankwasasa idan ya yi gauri to...'. Sun yi shiru na
tsayin lokutta, sanan yace, yanzu me ye abun yi?
Tace, Wai girkin ne ba ta iya ba, koko kuyya gare ta?
Ya ce, ina jin duka tace, idan haka ne dole Aisha ko
Hafsat ta dawo gidan ka ta koyar da ita da 'yar aikin
66
ta ku Kiristi na ko wata daya ne, ita Mamin sai ta rinka aje Hafsat din makaranta da safe yace 'E to ana iya yin hakan, amma bana son kuma Hajiya ta san
wannan matsalar' tace, ka da ka damu na san dabarar
da zan yi ba tare da Hajiyar ta san manufar mu ba,
yace, 'Ni baban bakin cikin ma shi ne wannan Kirsitin irin arnan nan ne masu warin tsiya wallahi
idan ta shigo falo kawo wani abu sai falon ya fi
mintia shirin yana warin ta, yanzu kwata-kwata bana
iya shiga kicin saboda ita, anti Hadiza tace, Ai daman
illar irin wa'annan arnan kenan, to babu wankan haila
balle wankan janaba sannan ga warin kashi ga girman
daji cikin kazanta, abinda za ka yi shi ne Mamin zaka
matsa mawa ta sawo mata roll on masu kyau tasa ta
yi wanka da sabulu mai kamshi sau uku a rana tana
shafa (rollon) to lalle za ku sami sauki ya duba agogo
ya mike yace, 'To shikenan zan jaraba sannan ina
sauraronku.
Kamar yadda Anti hadiza ta tsara an nunawa
Hajiya ne ana son Hafsat ta je ta taya Mami zama
kila juna biyu gareta, amma fa nace kila, wannan ko
shi hajiya ke son ji don haka nan da nan ta amince,
tunda Hafsat ta je ta shirya kayanta a dakin da ke
kusa da falo, ta shiga kicin ta soma da Kiristi inda ta
ga an girka shinkafa da miya a shashance ta koya ma
Kirsit yadda kae miya da dafa shinkafa, ta sanar da
ita ta rinka aunawa da wani jan kofi haka nan man
gyada dole ki auna don kada ya yi yawa, ki dai na
hada manja da mangyada, kowanne kawai inda ya ke
da daraja, Kiristi da ykae tana son aikin ta tsaya sosai
67
ta saurari Hafsat abinda bata gane ba ta yi tambaya. Da yamma ne tace, ma Mami, Anti Mami yau dai da
daddare ki zo mu yi ma yaya Sahabi Funkasu ko nafulawa ne, domin idan muka kwaßa shi da yis awa daya ta isa ya tashi sosai, Mami ta yi murmushi ta ce
ki bari sai gobe, sai hafsat cikin wayon ta da iya hila
tace, to Anti mu yi biredi mana, wani iri ne da Hajiya
ta koya man dadin tsiya wallahi, kin ga breadmeker
din ki babba ce, iya kar mu mu zuba komi da komi
ita zata kwaba sannan ta gasa biredin ta kuma kashe
duk da kanta, a nan dai hafsat ta hilan ce Mami tas,
har ta jata suka fita shofin na kananan kayan girke- girke baking powder, Yis, Filawa kori, theme, da dai
abubuwa kanana da dama, suna kicin har misalin
karfe goma na dare Mami dai bata saka hannu daga
Kiristi sai Hafsat ke ta girki su dafa wannan su kashe
wannan a kalla a daren nan sun yi girki ya kai kashi biyar dadi da murma suka lullube Sahabi yana zaune a
falo shi da gimbiyar sai ya rinka kwallwa Hafsat kira
ta kawo wannan yace ta kawo wannan ya rinka yi mata fara'a fiye da kullum, wanan ya soma batawa Mami rai wai me kae nufi ma shin da zuwan Hafsat har ta kama daki ta zuba kaya, kuma me yasa Hajiya ta dame ta da waya kullun tana gaishe ta ta na tambayarta shin babu dai wani abu ko?
Da safe kamar jiya hafsat ce abin kiran sahabi bakinsa a bude fuskan nan cike da fara'a komi ita ta iya ita ya ke tambaya, ya soma cin abinci wanda ya saba ada can, sun kare kalaci Mami ta koma dakin baccinsu sahabi ya bi bayanta, ta rungume hannu bisa
68
kirji ta ke fuska tace, 'Me ke faruwa ne, na ga
wani canji wanda ba haka mu kai da kai ba, yau
kwanan Hafsat nawa? Wannan iya yin da sanaben da
take yi na manee? Ya yi shiru amma ta soma kai shi
iya wuya fa, ya ce, 'Na lura Mami gaskiya ce dai ba
kya so, mnee laifin Hafsat, aumeki fa take rayawa,
sau nawa 'ya'yan su Anti Hadiza na zuwa nan su yini
da yinwa don sun taimaka maki cikin sirri an kawo
Hafsat komi ya daidaitu sai ya zama abin jin zafi?
Tace, su wa suka taimaka man? Yace, Ba wata ba ce
Antin ki ce Hadiza", ta ce, What! Wacece haka
Hadiza na ke aure ko kai, ita zata tsara man gidana ko
kai, waye ya yi mata katsalandan a gidanta? Sai ta
jira sai ranar da na haifa 'ya'ya idan na bar 'ya'yana
suka je gilan ta ta hana su abinci, koko ta taba ganin
kwanona gidan ta ina rokon abinci ko ina rokon
maka? To a bar ni na yi rayuwar da na ke so, iyaynea
da suka kawo ni duniya basu tkaura man ba, babu
mai tkaurani.
Yana ta kallonta ashe dai aure is not easy,
tafdijam! Mamin da ya ke so kenan ta ki fahintarsa
tow acece zata iya fahimtarsa? Yace, "look Mami
ofis za mu mun ma riga mun makara, iki yi hakuri sai
mun dawo zan fahimtar da ke, ta ja tsaki tsuw, tace,
zan cen ka ke so na riga na yanke magana, bana zama
da Hafsat 'yar sirrin Hadiza, wai har ka iya zama da
'yan uwanka ana tsegumi na, to ban yin abinda su ke
so, tsarin dana girma da shi shi na ke so, idan na
mutu su auro ma wata, ta bude kofa ta fice, ta je da
69
kan ta ta tayas da motar ta bata ko kira Hafsat ba ta yi
tafiyarta, sai shi Sahabin ya aje Hafsat makaranta.
A ofis sau biyu Sahabi na aikawa mami text babu
amsa, ya yi waya tana ganin lambarsa ce ta kashe,
yau ma kin zama fos din ta yi ta koma nan da nan ta
umarci kiristi ta kwashe mata kayanta tsab daga
babban dakinsu na bacci ita da Sahabi ta yi nata
dakin da ban ta shiryo abincinta daga Bakers Delight
ta yi kwance a daki tana kallonta tana cin abincin ta,
itama Hafsat da ta dawo ta shiga kicin ta shirya
abinci mai kyauta ci nata ta aje wa su Sahabi na su a
tebir. Shima ya dawo ya ga canjin da dakinsu ya
samu hankalinsa kwarai ya tashi, amma dai ya tuna
shi ne mai gida shi ya kawo Mami dole yayi hakuri
da ita, haka nan kuma dolensa ne ya daidaita
tsakaninsu Hafsat domin tun zuwan Hafsat ya soma
dawo wa hayyacinsa, wata kasala da yawan jin jiri ya
rage ji yanzu.
Ya doshi dakin da Mami ta zabarwa kanta, ya
murda ya shiga ba tare da ya yi sallama ba haka nan
fuskarsa ma babu wani annuri balle ayi zaton fara'a.
Ta dube sa kasa da sama ta mayas da fuskarta bisa
kawatin T.V yace, Mami kenan! Yanzu ke ce za ki
man haka ko to manee abun burgewa don kin raba
mana dakida gani sai ke agida, ba ni fa da wadda tafi
kusa da ni kamar ki a yanzu, tace, don Allah bana son
zakin baki, ka je ku yi hidimarku da 'yan uwanka, ka
bi shawararsu ai sun fi ni kusa da kai, ka manta ne?
ya dan kada kai yayi murmushin ta kaici yace, 'To zo
mu je a ci abinci, sannan azo a zauna a yi maganar, ta
70
ce, Allah ya sawakc ai ni ba mayya ba ce, da za a
tursasa man abunda ban so, idon ka baya gani ne ka
duba mana ai ni na ci nawa, ina kuma tsammanin
abinci duk abinci ne, in banda san iyawa na wasu
mata, sahabi va ga dai Mami ta yi nisa dole ya fita ya
je ya ci abin cinsa, bai so ko kusa ya hango Kiristi
domin tana tayas mai da zuciya.
Bayan ya dawo masallaci ne sallah isha'i, ya
koma dakin da wai Mami tace ta zaba wanda shi har
yanzu bai amince ba, dole ta koma yadda suka saba
ya je ya zauna tana rike da wayarta tana aikawa da
text, ita da aminiyar ta ne maryam suna shirmnesu ne
can na tuna da, amma bata gaya mata halin da take
ciki ba, ya fi minti goma sha biyar a zaune bata ce
dashi uffan ba duk abinda yace bata amsawa can ta
kare text din ta ta jawo remote na C.D din ta ta karo
wakar da ke yi, yace, kin san wani abu Mami,
gaskiya ya dace a yi wani abu akan kiristi din nan
ta dan maida hankalin ta gare shi tana neman karin
bayani, yacc, aiki da ki ka sata ta yi maki yau wallahi
lokacin da na dawo na shiga dakin baccin mu, naji
dakin ya dauki warinta wai ke warin kiristi baya
damun ki'ne? Mami tayi shiru, eh ta san lalle kiristi
na irin warin kashin nan to amma ina ruwan su da
warin ta tun da ba zama falo ko daki daya su ke yi da
ita ba, zuciyarta ada ta soma sauka amma kuma
yanzu yana so ya kara jagula mata lissafi, tace yanzu
kanta tsanar taku ta koma, in don ni ka kori kiristi a
yau din nan, ba matsala,' yayi yar dariya yace, bazan
cne kenan ba, ta tsagal galo masa tace, look Sahabi
71
kan iya bawa Hafsat duk ukon gidan nan bai daman
ba, ni yanzu so na ke ka kyalc ni kayi hidimarka da
Hafsat na yi hidimata ni kadai! Yace, ni so nakc ki
taimakawa kiristi tinda ke take ma hidima, bana son
nayi baki ki ce ta kawo ruwa ko lemo a falo, duk ta
cika falon da wari zuciyata na tashi bana jin dadi a
gaskiya, saboda haka ki debi kudi ki aika Hafsat ta
sawo mata rollon da sabulai masu kyau kisa ta rinka
yin wanka.sau uku a rana ina ganin kila mu sa mu
saukinta ko? Mami ta galla mai harara tace, mc zai
hana ka baiwa Hafsat kudin ta sawo kai kuma ka
rinka shafa wa kiristin roll on din, sarkin iya yi,' ya
bude baki yace wai ikon Allah! Haba Mami menene
na zafi kewai daman can ba a zama ayi shawara da ke
ne. har abada sai dai na bi shawararki amma ni a
matsayina na mijin ki ban isa ince ayi ba ayi, haba
Mami kiyi tunani nima fa mutum ne kuma namiji mai
so ya nuna mutuncin gidansa a idon duniya, idan har
ban yi shawara da ke ba to dawa zanyi, shin menene
anfanin auren kuma mene ne amfanin da iyayenmu
suka ba mu damar mu auri wa'anda ran mu ke so, ai
don a zauna lafiya, wallahi a shirye na kc na yi maki
duk abinda ranki ya ke so ba ni kuma da niyar na 6ata
maki dai-dai da rana daya Mami' Ya dan tsaya a nan
ya yi shiru amma ita Mamin ta kawar da fuskarta can
gefe, zuwa can ya soma jin shehsekar kuka, Sahabi
ya dafe kai ya tsananta da tunani yanzu me ye abun
kuka anan? Abinda ya zo a zuciyar Sahabi shi ne duk
yadda akai su mami haka nan suka girma kara zube,
ba kwaba ba tsangwama. babu
72
wanda ya tsaya basu
wata cikakkar tarbiya, kila ma daga su Anti Yesmin
su Zainab sai kallon tashoshin turawa sune tarbiyarsu
Mami a cikin gida, duk ma yadda akai su mami basu
san ace masu a'a ba sai dai ace ch. Tirkashi yanzu shi
ya zai yi kenan tunda shi dai Maki kadai ya ke so.
kuma kwatakwata al'adunsu da tarbiyarsu tasha
banban yaya kenan za ai wannan zama? Wa'annan
sune tambayoyin da suka addabi Sahabi domin kansu
ya soma daukar zafi. Ya ja dogon lumfashi a ransa ya
karanta 'yar karamar addu'a ta neman saukin lamura.
Ya mike ya je gare ta ya kamota ya doro bisa
Kirjinsa ya soma lallashi a nan ma ya kwashi kusan
awa daya kafin ya shawo kanta ta yi shiru, yace,
"Tashi mu je dkai mu kwanta, ta ja tsaki ta ture shi
tace, ina nan ba wani dakinka da zan sake shiga,
yace, come on Mami please ki huce mana, an taba
hushi da miji, hushin kuma da ba dalili? Ta mike ta
shiga kewaye ta yi buros din bakin ta ta kuma wanke
fuskarta saboda kukan da ta yi sannan ta shafa lotion
din baccinta ta koma ta saka riga rbacci, ta kwanta
abinta, Sahabi ya bita da kallo kawai shi ma y aje ya
yo shirin bacci ya kulle ko ina na gidan ya tofe ko ina
da addu'a sanan ya bi mami dakinta ya kwanta kusa
da ita ya so ya yi zancen da ya ke jin zai sa ran Mami
ya yi sanyi, to amma shi ma sai ya sami tasa zuciyart
a cushewa da dacin rai, har ita mami ta sami bacci
can ya juya ya dauko ta cka ya dora a jikinsa ya kai
bakinsa daidai kunnneta ya rinka yi mata radar how
murch he love her.
a
73
Kullun dai kawai abinda Mami kan tsana game
da Hafsat, zan cen wai ta koyi girki wanan ma bai
taso ba bai cikin tsarinr ayiwar Mami, itama kanta
kiristin ba komi ta iya ba in ban da jalof da doya da
miya saui shinkafa da miya, to ba laihi ta koyi amfani
da yawancin na'urorin Mami,s aboda tsanarlin yawan
aiki su wankin Mami gyare-gyare, komi dai kiristi za
ta yi, to itama Hafsat yanzu nauyin ya fara yi mata
yawa saboda kannan Mami sun soma sarfatar gidan
sahabi, ita kuma Hafsat tana tsananin karatun (Final
year) din ta ne to sai Sahabi ya lura an mayas da
Hafsat 'yar girki ita da Kiristi kullun tana kicin, bata
da lokacin karatu kannne Mami agaban Sahabi suka
ce, ta gasa masu mcat pie da ckae tace 'To' ya koma
dakinsa da kunfutarsa yana aiki, sai kuma ga
kawayne Mami har su biyar a nan kuma za su ci dina
don haka Mami ta kutsa kai dakin Sahabi ta yi
sallama ta bude dirowar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13