Firig a
kusurwar dakin ya isa wajen ya bude kayan marmari
ne su tufa, ni'ibi, goba, lemo, ayaba, da mangoro,
sannan ga wani hadadden ginger drink, ga juice nan kala-kala irin wa'anda Mami ke so, sahabi ya dauko
ayaba ya bare daya ya soma ci sannan ya bare daya
44
ya je ya mikawa Mami ta amsa ta ci, itama ta nufi
firig din ta tsiyayi juice ta sha ran ta ya yi mata san yi
ta dubi Sahabi ta yi murmushi, ya yi hanzari ya je
gare ta ya jawo ta ya rungume ta ce, wannan hidima
da su Husna ke mana bai yi wa mu basu kunya mu
shige a yau", yace, 'Yauwa my Mami ni ma abinda
na gani kenan look duba jikin bangon kofa wani kati
ne aka lika mana duk na murnan zuwanmu, amma fa
ba zan so na tursasawa zuciyarki ba yadda ki ke so
haka zan yi". A tsaye su ke tsakiyar fakin iskar A.C
na kada su, Mami ta kwantar da kan ta bisa kafadarsa
ta dama yayin da ta sakala hannayenta tsakiyar
bayansa, ta ce, Bana iya canza ra'ayin su Husna da
Usman a gaskiya sun tabbata masoya na kwarai". Sun
dauki tsayin minti goma a tsaye suna gudanar da
(love making) sannan ta janye tace "Ana fa jiranmu a
falo", ya ce, Bayan ma jiran ba mu bayas da faralli
ba, abinda za'a yi sai ki soma yin alwala ni kuma zan
je nasa a kwaso mana kayan mu".
Mami ta shiga kewaye ta tura kofa a bayan kofar
an manna wani dan karamin kati mai dauke da rubuta
da ruwan azurfa an rubuta, you are highly wellcomes
with all our love, wato muna maku kykakyawar
maraba a bisa dukan kaunarmu, muma fata zaman ku
da mu zai dada zurfafa kauna da zumunci mai karfi a
tsakaninmu amin.
Dear Usman and Husna
45
Always yours
Mami ta shafi katin da yatsunta alamun yabawa ta yi
murmushi, sannan ta sakarwa jikinta ruwan shawa ya
ratsa kwarin bayanta kuzari da sabon karfi ya rinka
shigarta, ta dade tana shekawa jikinta ruwa sannan ta
zare fant din ta, dan kanfai ta aje shi a wajen wanke
baki (sink) ta yi alwala ta dauko sabon tawul ful
wanda Husna ta aje masu a kewayne ta tsane tsab, ta
bude kofa ta fita ta samu Sahabi ya kammala shirya
masu kaya, ya mike ya nufi kewaye, yana rufe kofar
sai wannan katin ya kai ma idonsa gaisuwa ya
karanta cike da jin dadi a ransa, sai ya dubi wajen
(Sink) in da Mami ta bar dan kan fanta ba tare da ta
wanke ba, ya yi murmushi yace, "Kai su Mami
manya, ita dai raguwa ce, yasa sabulu ya wanke tas
ya shanya mata a inda kae shanya kananan kaya a
nan cikin kewayne. Abinda Sahabi ya ki yadda ya
fahimtarwa kan sa shi ne, mami na daya daga cikin
'ya'yan hutu abin nufi shi ne gaba daya 'ya'yan iyana
kowacce da 'yar aikinta, Mami har ta gama zaman
gidansu bata iya wanke rigar nononta balle dan
kanfanta inda ta yi wanka nan take barinsa mai
aikinta zata kula da sauran bayani. Saboda haka
yanzu tun da ta zo gidan sahabi shi ke wanke mata
wa'annan abubuwan kao da yaushe yana ganin kamar
ta gaji ne, bai san tsabagne rashin tarbiya ba ne.
Turarukan da Mami ta ckaude suturar da jikinta
da su, sun faye sanyin dadi ga azabar taushi irin na
mata dai, na Sahabi kuwa mai karfin nan ne irin na
maza masu karfin jini nan da nan gidan su Husna ya
dauki kamshin dadi na tabbacin kawai amarya da
46
ango a gidan. A falon ma Usman da Husna sun yi
wanka suma sun yi canji sun zuba tsadadda shadda
mai maski mai ruwan cincinbale, Husna tace, Nasan
dai a gajiye kuke mu zauna bisa kafet ne ko ko mu
dai yi ta nasara jan fata mu haye bisa tebir? Mami
tace "A zauna a kasan ya fi sakewa", Usman yace,
Gimbiya kenan, wannan ko zkai bari mutumin nawa
ya je ofis? Ta yi dariya ta ce, haba Usman kawai
matar da zata hana miji zuwa ofis? Yace, Akan ki za
a fara? Tace Dan Allah kar kai man addu'a, insha
Allah ba zan hana ba".
'Yan aikin su Husna Mary da Sam suka shigo da
kayan dina, duk wani abinci mai sa yawun dan adam
ya gudana Husna ta aikata ma bakinta, an ci an sha,
an yi sharholiyar ban dariya, ta yabawa Husna, akan
iya tsare-tsarne girkin ta. To a haka dai sai da su
Mama da Sahabi suka kwashe kwana uku a gidan su
Husna, kuma duk girke-girken da kae ma su Mami da
kulawa da kae ba su ta musaman Husna ke
aiwatarwa, sai dai ta baiwa Mary 'yar aikin umami
saboda Usman mutun ne mai tsabta ba zai iya cin
abincin mai aiki bа.
Sun rabu ana ta begen juna kwarai ko sun mori
wa'annan kwankai uku cikin jin dadi da walwala sun
kuma kara shakuwa Usman da Sahabi Mami da
Husna, Usman ya so kwarai ya baiwa Sahabi
shawarar zaman aure amma ya kasa ganin kwatakwata da fuskar da za'a yi ma sahabi zan cen iyalinsa
duk wanda ya kwana daya da su ko ya wuni zungur
da su zai gano Sahabi ke ma Mami biyayyar aure ba
1
ita Mami ba bayan a al'adarmu da addininmu matá
aka sani da biyayyar aure, (Alah ya shirya mana da
zuri'a)
A yankari ma dai bata canza zani ba yadda rai ke
so haka kac bata, Sahabi bai da lokacin kowa sai na
mami illa dai duk bayan kwana biyu ya kan yi ma
Hajiyarsa waya ya gayas da ita, idan ya yi gidansu
mami sau daya ya taba samun iyana sai su Anti
Zainab don haka ma bai cika yi ba ka'idar kullun
itacc idan sun fita yawan yada rana suna zagaya leke
dabbobi, ma'aikatan masu tsabtace dkaun yankari za
su shiga dakin su mami a gyara masu ko ina fes,
kawashe kayan da suka fidda aje a wanke, amma ban
da kanfan Sahabi da hankicinsa da na Mami da
rigunan nonon ta da siket din ta wa'annan kao da
yaushe sahabi ke wankewa bai taba damuwa ba balle
har ya zargi wani abu.
A yau suna yawon yada rana la'asar lis, Sahabi
ya kara matse ta a jikinsa ta dago kai ta dube ta ce
"oh ni, so ka ke ne na shige cikin kirjin ka ne? ya ce, da zan iya mami da na manne ki a kirjina kila na
samu gamsuwa, kin san ko dazun da na yi ma Hajiya
ta waya cewa ta yi tun farko da mun sani kasashne
turai na fita da ke yadda za mu ji dadin holewa sosai", Mami ta ce, Ni ka sani ko cikin kejin can ka kai ni in dai zan kasance tare da kai na tsayin awa ashirin da hudu cur walahi ban damu ba, bukatata ta biya", Sahabi ya dora labbansa tsakiyar kan Mami ya sumbaci gashinta sha'awa ta zo mai ya kara narkewa
a jikinta kai ka ce ba a tsaye suke ba kuma a gaban
48
1
3
L
kejin giwaye, sun dan yi nisa da wasu gungun family,
amma gaskiya zaman amarcin sahabi da Mami ta
bata shi ta rage masa kunya kashi biyar daga cikin
ashirin gaban jama'a yanzu Sahabi yana iya hada
jikinsa da na ta amma ada ina!.
Kwanansu goma sha daya cif a yankari a ranar za
su bar garin a Kaduna garin gwamna haka nan dole
amarci zai ragu domin za'a koma aiki, Sahabi ya
gama shirya masu kaya ya mikar da katon kawatunsu
tsaye ya dauko karamin na kananan kayayykainsu shi
ma ya kammala da shi ya aje kusa da inda ya aje
babban, Mami ta kare wasannin motsa jiki ta zauna
dirshan tana gwama lumfashinta tsane tace, "Sahabi
ya amsa "yes my love ta ce 'Kai man alkawari za ka
sake dawo wa da ni nan yankari bayan wata shidda
kuma ka nuna so da kaunar da ka nuna man na
wannan karon', Sahabi ya kyalkyale da dariya ya je
ta bayan ta ya durkusa ya kwantar da hannayensa
bisa wuyanta suka dira bisa kirjinta, yace, ko ni na yi
irin wannan tunanin da asubar yau domin raina ya yi
daci ganin shikenan mun bar wannan hutun! To
amma shawarar da na yanke itace hutunmu na gaba
warri za mu kawai wani waje mai kyau na hutawar
masoya ire-irenmu insha Allah za ki so wajen, zan
kai ki ta yi murmushi irin wanda ta saba yi mai idan
ya yi mata wani abu na bajinta, ta mika mai la6banta
ya yi abinda ya fi so.
Kamar yadda suka saba duk tafiyarsu sai yamma
suke isa,w annan din ma haka ne da mangarib lib
suka isa gida. Sahabi ya yi ma Hajiyarsa waya, yace,
49
2
Hajiya isowar mu kenan Sallah kadai muka yi, tace,
sannunku da sauka yaya Mami ya amsa lafiya lau
Hajiya gata ma ku gaisa, (kan Mami na bisa cinyar
Sahabi) don haka sai ya manna mata wayar a
kunnneta, cikin shagwaßa tace, Hajiya ina wuni, yaya
su hafsat? Ta amsa duk lafiya lau, to ga Sahabin
hajiya, ya amsa yace, "Gobe za mu koma aiki Hajiya
Hajiya tace, Ya son ranka! Kai ta zuwa hutu domin
kan ka farau aurc? Ya yi dariya yace, ka ji hajiya don
Allah, tace, 'To kuna son wani abu ne? ya ce, 'Eh
Hajiya muna son abin ci, in da hali direbanku ya
kawo mana, sannan azo da Hafsat saboda safe' hajiya
ta ce, don nan da wata daya kada kasa ran Hafsa zata
zo gidanku ta kwana saboda sun fara karatun
jarabawa an kusa yi masu hutu, kuma direba na baya
nan ya je Zariya tun jiya dibo mahaifinsa bai lafiya,
amma me zai hana ka turo Ya'u ya amsar ma ku ya
ce to shike nan ga shinan zuwa.
Da za su kwanta ya bar wa Ya'u sallahun da safe
ya je kara komawa gida zai amso masu kalaci. Hakan
aka yi da safe Ya'u ya je ya amso masu kayan karya kumallo hadadde yadda dai Sahabi ya saba tun farkon rayiwarsa.
Sai karfe goma sha biyu da 'yan mintoci suka sami tafiya ofis, Mami ce ta soma fitowa harabar gidansu sanye da wani lanfaya les mai ruwan gwaiduwar kwai ta lanfaye jikinta ruf, hannayenta kunshin aurenta ya fita sai na kunba da ta yima kanta ya yi kyau domin a cewar Sahabi yama fi son kunshin na kunbar ta, dahan din da ta watsa a
50
masangalin tsintsiyar hannunta guda tkawas ne sun
kame ta, da zabba wa'anda suka shiga da
awarwaronta sarkar da 'yan kunnne kirar dubai ce
fnedal da 'yan makale, takalmi da jaka kanana sai
tsadar tsiya. Ta tsaya tana rausaya yayin da Sahabi ya
rinka baiwa motar ta wuta ya yi rubas ya fiddo mata
ya kawo mata har inda take tsaye, motar ta Mami
sabuwa ce ful a yau zata fara takata, wani aminin
mahaifinta ya bata ita gudunmawar biki, motar na da
masifar kyau irin masu mannewa bisa titin nan ce,
kalarta mai ruwan ganye ce amman ganyne ya turu,
sai wata munafukar walkiya irin ta daukar hankalin
jama'a. wato 206 kenan, ya fito Mami ta shiga ya
leka ta taga yace, "Ke Mami I'm jealous', ina kishi ta
ce, 'Amma da ka ba ni kunya, bayan ka gama da
komi nawa bana iya sarrafa zuciyata da kaunar kowa
illa kai, haka nan bana sha'awar komi ni dai sai
Sahibina Ab-kar! To wa kuma zan iya duba, in ma
wani gaulan ya tsaya sha'awar Mamin Sahabi wallahi
ya sha haushi. domin ni dai an san don rai daya aka
halittani; ya shafi kumatun ta suna dariya yacc, "You
should take care please, ta ce I promise you I will; sai
da ya ga fitar ta sannan ya koma ya debo kayan tafiya
ofis ya tayas da tashi motar ya tafi ya soma biya wa
asibitin da Hajiyarsa take aiki, ya same ta a ofis sun
dan gaggaisa yace, Hajiya na zo na roki arziki ina
son a rinka kawo mana abinci na yamma da na rana
kafin mu sami mai aiki, Hajiya ta yi shiru tace,
Sahabi ba zan ko so na kawo ma ku abinci ba har iya
lokacin da ku ke so, to amma matsalar itace kana
51
nufin ita mami ba za ta taba shiga kicin ba sai 'yar
aiki in haka ne ko ashe bata cika mace ba, kuma kai
kullun abincin mai aiki za ka ci kcnan, ban ce ba za a
nemo mai aiki ba, amma itama ya dace acc ko sau
daya a rana tana shiga kicin, to ina anfanin na'urori
da mahaifiyarta ta saya mkau a ka zuba mkau a
kicin? Sahabi ya amince gaskiya Hajiya ta sanar da
shi to amma ta ina zai bullowa Mami domin bai ga
tana da niyya ba? Hajiya ta ci gaba, idan gani na ne to
ranar da na yi tafiya yaya za ku yi? Ya ce, 'Ai
nufinmu Hajiya shi ne a dai sami mai'aikin sai su
rinka yi tare, ba wai mai aikin za'a bar ma aikin
abinci ba", ta ce, ku dai yi tunani, za'a ci gaba da
aiko ma ku amma randa mai aiki ta zo sai a bar mani
gidana mu huta,af mahaifin direbana ya rasu, an jima
zani zariyan da su Sa'adiya don haka sai ka sami
lokaci ku je gaisuwa kai da Mami, ya yi mai addu'a
yace, insha Allah za mu je.
Wannan kenan, Sahabi ya is aofis gaba daya aka
soma yi mai sowa ana murnar yi mai barkwanci ga
ango, Mr Obi ya doki kafadar Sahabi yace, a gaskiya
ka yi sa'ar mata lalle tana kula da kai, ka ga yadda ka
yi haske da kiba? Sai Mallam Jibiril yace, 'Wai
amaryar fa fara ce sol irin jinsin larabawa ina ganin ta
soma shafawa Sahabi haskneta; aka kyalkyale da dariya gaba daya, sannan oga Ibrahim yace, A
gaskiya muna murna da ganinka Sahabi ka mori aure domin you look happy and healthy masha Allah- Allah ya bada zuri'a dayyaba' aka amsa amin.
52
*** *
Sati biyu aka samu su Mami na zuwa aikin ofis
kullun gidansu hajiyar sahabi kae kawo masu abinci,
anti Zainab ce mai nemowa Mami mai aiki ko waссе
aka kawo sai Mami tace bata yi mat aba ta yi tsofa ko
tace ta faye kazanta, an yi jiran wadda ta yi ma
Mamin aikin lokacin tana gida amam shiru bata dawo
daga ganin gida ba, rannan daiw ata Rawar Anti
Zainab ta samo masu wata katuwa mai suna Kiristi
mutuniyar Ghana ce bata jin hausa, daga yamesu sai
ko dan burokan turanci, ganinta mai siffar karfi
Mami tace yawuce ta yi mata, aka tsadance abunda
za'a bata dubu goma sha biyar a shekara, mai biyan
Sahabi ya ce, ya amince.
Mai mkaon a samu toshewar baraka a'a sai ma
matsaloli suka soma kunno kai, Kiristi irin mutanne
Kauyen nan ne tikis masu talauci wanda ba su iya
girkin komi ba sai aikinw ahala gidan su Mami kam
ana gyara shi kal-kal komi na Mami hatta kanfai ita
ke wankewa tas, kewaye da ko ina fa cikin gyara ya
ke. Ranar farko Sahabi ya baiwa Ya'u kudi masu
yawa aka yo cefane raga-raga, ranar ta kama asabat
duk suna gida babu zuwa ofis, sai ya cije yace, Tо
Mami yau sai a fara yi man girkin amarci nima na yi
alfahari da irin girkin mata ta; ta yi 'yar dariya tace,
na shiga kicin! To mnee ne amfanin zaman Kiristi, ai
ni ko agidanmu ban taba shiga kicin ba ko da dora
ruwan zafi, wallahi ban san yadda kae dafa ko da
shinkafa ba, babu dalilin da zai s ana yi ma karya a
53
kan abunda bai zama tilas akai na ba. Sahabi ya ji
wani dam, an ya ko kawai shashashar macen da bata
iya girki ba aduniya kai karya ne, wannan wacce irin
rayiwa ce! Yanzu me ye abin yi? Tabbas dai ba zai
hauta da fada ba, ko ya matsa mata domin abisa duk
kan yanayin Mami wannan zance haka ykac, tun
farko ma ya dace ya gano ko gidansu yaje ruwan sha
bata iya kawo masa illa tasa a kawo, babu abun yi sai
lallashi domin dai ya san Mami na son shi a dalilin
soyayyar yana hadawa da lallashi insha Allah zai
shawo kan ta har ma wasu matan su zo koyin girki
wajan Mami.
Ya gyara zama ya matsa kusa da ita ya kamo
hannunta ya soma wasa da 'yan yatsunta yace, Mami
na gano manufarki amma kin san abinda na ke so da
ke shi ne, ki jure a dalilina ki shiga kicin ki rinka yi
mana dan abuncinmu da gani sai ke ita kuma kiristi ta
girka na ta da maigadi da Ya'u da sauran baki masu
shigowa, idan kin man haka wallahi kin birge ni kin
kuma nuna man lalle ina da matsayi, kuma ma aikin
wannan zamanin Mami bai da wuya kawai na'urori
wa'anda cikin minti talatın komi ya nuna, kuma duk
muna da su, ki jure nima ofis zan koma yanzu,
saboda ina da aikin don nan da wata daya da kyar zan
kammala in ba na sami mai taimkao ba, amma zan
bıya gidan Jabiril na ji ko zai sami lokaci ya taya ni
me ki ka cc, tawan? Mami jikinta ya yi san yi akaro
an farko ta soma tsanar aure, don me za'a tkaura wa
mutun akan abinda bata ga gidansu ana yi ba, dole ne kuma ta yi abinda Sahabi ke so domin bai dace ta
54
a
ni
na
ke
애
ey
ta
al
iri
d
ik
n
a
ט
batawa abinda tafi so rai ba; ta yi murmushin da bai
je ciki ba, tace, to zan shiga kicin amma komir ashin
dadi kada ka zarge ni, yace, "Haba ni na fara komi a
hankali kae yi kin san Allah ni a shirye na ke mu
rinka shiga kicin din tare ko daman Ubangiji bai ce
mu mai da ku bayi ba don dai an maida girki cikin
neo ne kuma meo na iyaye mata ne, mu kuma mu
fita mu nemo mana.
Da kar ya ja ta zuwa harabar gidansu inda
motarsa take, a nan ma sun dade tsaye yana daga
cikin, mota zaune ita kuma ta kama marfin kofa ta
rike, koma mu ce ta kwatnar da rabin jikinta a marfin
motar har yanzu dai lallashin ya ke yi, tace, af to Abkar me zan dafa? Ya ce, wallahi mami ba ni da zabi
komi, ki ka ga dama ki dafa, ni dai buri na naci girkin
sahibata kamar sauran maza, ya yi dariya amma ita ta
yi dan siririn murmushi ya dan lallaba ta ya nufi ofis,
ita kuma ta nufi kicin.
Kiristi na 'yan goge-gogneta wadda bata son
zama haka, kamar jikinta na mata kaikayi, nan da nan
cikin burokan turancinta ta ce, Anti me kike so? (Anti
take cc ma Mami,s anan kuma ta kira sahabi Uncle)
Mami tace, wareware ledojin nan na nama da na
kayan miya mu gani, Kiristi ta debo manyan robobi
daga suto ta ware kaji manya-manya ya zo da su har
guda shidda, sannan ga naman rago mai kyau wanda
ya dace asa a (oven) a gasa sai naman shanu na yin
miya, sannan ga kayan miya wa'anda ya dace a gyara
a aje a firiza a kalla sun yi masu sati biyu, kudin da
Sahabi ya baiwa Ya'u na cefane kimanin dubu goma
55
ne, haka nan tun rannan yasa aka cika firij din falo da
su kankana gwanda, Icmo ayaba mangwaro da tufa,
Sahabi namiji mai iya kula da iyali matar cc dai ko
zata zama matar kwarai? (Ga mu dai muna ta bin su
aka sa kiristi ta yanka nama ta wanke shi kalkal
kamar ana wankin jariri sabuwar haihuwa, har saida
ka fidda zakin naman tas, ta fiddo injin markade
daga ita har kiristin ba su iya markaden ba, amma sai
Mamin ta karanta takardar da ke cikin kwalin ta g aya
ma kiristi yadda za ta yi, nan da nan kirsiti ta yi
markade Mami tace ta iya kunna kuka kiristi ta ce 'Е
Ya'u ya nuna mata da zata dafa masu ruwan shayi
tace to ki kunna ki yi miya wadda za'a ci shinkafa da
ita, tace 'Yes Anti ita kam kiristi yadda ta ke son
aikin ta ko bata iya abu ba, sai tace, to gudun kada ta
batawa mami rai, a nan Mami tace ta fere dankali ta
hada cikin shinkafar a dafa, wato yadda kac dafa
shinkafa a watsa dankali a ciki.
Mami na tsaye na kallon kiristi ta dauko
tukunyar miya ta zuba nama ta zuba manja ta zuba
mangyada ta zuba markaden kayan miya, idan muka
auna mangyadan da manjan sun fi markadne kayan
miyan yawa tirkashi! Aka zuba magi da gishiri ta
rufe ruf ta dora bisa kuka gas, sai aka koma sito aka
farke buhun shinkafa aka debo kusan tiya daga aka
wanke aka zuba ruwa aka dora bisa wuta duk Mami
na kallo, zuciyarta cike da tsanar Sahabi, in dai dole
sai ta zo kicin lalle za su bata kwanan nan kenan.
A sito din su Mami kimanin shinkafa ce ta kai
buhu talatin, danya ta tuwo buhun goma, ta dafawa
56
t
1
,
e
i
i
31
13
Z
a
a
k
buhu ashirin, katon na taliya ashirin, garewani
ashirin, katon na magi uku buhun gishiri ashirin,w
annan gara ce iyayen Mami suka kawo ma Sahabi,
haka sun kai ma Hajiya Aisha rabin komi na Sahabi.
Kiristi na gama fere dankali ta watso cikin
shinkafar a lokacin ko tafasa shinkafa ba ta yi ba,
mami ko ta koma falo ta murdo tauraron dan.adam
tana kallon irint ashar bakantar nan wadda Sahabi ya
ke son ya soma hanata bayan basu da wani aiki a
gidansu sai su kai asuba suna kallon irin wa'annan
tashoshin, batsace kiri-kiri can ta yi nisa ita kadai a
falo Sahabi ya yo mata waya ta layin gidansu,t a
dauka tace, 'Yes hello Mami ce yace, 'Nima
Sahibinki ne, ya gida, lafiya yace, wallahi kamar na
dawo gida na ta ya ki aiki amma aikin ofis ya ritsa da
ni ba hali gobe ma lahadi dole sai an zo tace, Nima
gobe salun za ni, su wanke man kai na ya yi dariya
yace "Ke ko gashinki ai ya sha ruwa da yawa wannan
watan kila ma ya soma tsami" ya kyalkyale da
dariya,t ace, "Au haka ne ma, shikenan ka jama kan
ka daga yau yace, 'Haba beby na ke kin soma kar
kisa na hadi zuciya na mutu ta yi dariyar da ya fi so,
suka dade suna sokoncinsu, yace, Afa yi maan
farfesu ta amsa a dakale 'To' sun aje waya ya yi shiru
yana dubar konfutar da ke gabansa idan har zai yi
zancen abincin lalle zai ji mami ta canza murya to
wai ita bata tunanin abinda ya dace ne, kamar yadda
shi ya ke tunanin abinda zai kayata mata rai a koda
yaushe any way Mami bkauwar aure ce zata saba a
hankali, zai cig aba da lallashinta, ba kuma zai taba
57
tona asirin gidansa ba har sai wannan matsalar ta
zama tarihi, yanzu ya gano ma'anar jama'a da kae
cewa Allah ya bada hakurin zama, maganar dai
kenan ayi hakuri ita cc addu'ar aurc, ada ya dauka
mene ne na hakuri tana so yana so ba auren dole akai
masu ba ayau ya soma sinsinar dalilin cewa ayi
hakuri insha Allah zai yi bai ga abinda zai gagaresa ba.
Mami ta shiga kicin ta ce ma Kiristi ta dora
farfesun kaji, kiristin a nan har ta yi hankali ta се,
'bata iya ba, ko ita Mamin zata yi waya gidansu
Hajiya a gaya masu yadda kac yi Mami taji haushin
Kiristi ta rufe ta da fada tace, zancen banza mnee ne
abun wuya a farfesu da har za ki ce na yi waya gidan
surukai na? Ta ja tsaki ta fita zuwa falo, ta zauna tana
jin zafin sahabi duk dai shi ya ja mata domin ita ko a
gidan ubanta da wuya taci abinda aka dafa a gidan
komi dadinsa, tsarin rayiwar mami itace da safe ta
sha tea da ckae ko biskit wani lokacin ma haka nan,
da rana ta aika ko taje da kanta Mr Biggs ko Bkaers
Delights ta sawo abincin dari biyar taci, da daddare ta
sha ice-cream ko juice ta yi kwanciyarta ko tasa mai
aikin abincin Babanta a gasa mata kaza, bata son ta
aika masu anti Zainab don taimkaon girki domin ta
san 'yan tsegumin cikin gidansu na da yawa daman
an ason aga faduwar ta, haka nan me zai sa ta nunawa
uwar mijinta da danginsa cewa bat aiya girki ba? a
nan ma wani tsegumin ne balle can gaba? Amma bari
ta nemi sháwarar aminiyarta Maryam Bishir, ta yi mata waya tace, "maryam wai kin ji Sahabi dole sai
58
abinci na zai ci, ni ko dai kin san komi? Maryam ta
cc, Ba na ga kin sami Kirsiti ba, ko bai iya biyanta
ne? ta cc, zai iya mana, Maryam tace, zancen banza,
yanzu ke son da kike masa har zai ja ki zuwa ga
wahalar da uwarki da ubanki basu saka ki ba, ki bude
mai ido tun yanzu ba sai zama ya yi zama ba, a
lokacin baki iya lankwasa shi, idan bai iya cin na
kirsiti to zaman me su Mr. Biggs su ke? Kada dai ki
yadda da ya rinda amsowa a gida, Mami ta yi ajiyar
zuciya tace, "Ai ba ki san sharrin ba Kiristi bata iya
farfesu ba yanzu ya yo waya yace ayi mai ya kenan?
Maryam tace, Dole za ku hakura har ta iya kar ki
soma neman taimkao gidan kowa kin san 'yan
tsegumi ta kwallawa mai aikin Hajiyarsu kira tace,
wai ya kae farfesu ne ta gaya mata? Tace to Mami
ashe ma abun duk shirme ne wai kazar da ruwa da
kayan miya za'a hada shikenan, suka bushe da dariya
aka aje wayar.
Mami ta koma kicin ta iske Kiristi tana ta gurzar
naman kaji ta wanke fari kal-kal yadda babu zan cen
dadi balle ya yi amfani a jikin dan adam, Mami tace,
sai ki hada komi da komi kamar yadda ki ka hada
miya amma banda mai. (Kai wannan abun haushi da
ban dariya da yawa ya ke a gidan Sahabi da Mami)
wai Kiristi har da dan durkuso da yi ma antinta Mami
godiya nand anan ta hada ta dora.
Mami an fito falo cikin sanyin A.C ga Pineapple
juice mai sanyin gaske cike da tanbulan tana kurba ta
kunna tashar Sky movies wasan dai da kae yi inda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13