jami'a ta watsa shi a kafada. bata
son rike G.S.M din ta a hannu don haka ta dauko 'yar
Karamar jaka ta jefa wayar a ciki. Kamshinta mai
taushi na tsayawa a ran Sahabi, shi ma ya fito ya yi
sa'a bata kure sa ba wajen kwalliya domin irin
164
ya basar bai takura mata ba. Sun tsaya a wani
shahararren shagon saide-saide, komi (mother care)
ya nunawa nana ta rinka fiddawa bebin, tun nana na
Kiyasta irin dubunnen da za'a caji Sahabi, har ta ja ta
tsaya ta ce kudin sun yi yawa, ya ce, ba yaron
abokina za aima sayayyar ba, kuma dan uwar dakina
ko kin manta ne, Kila ma suna na za'a saka masa ta
dan bude ido tace, Na yi zaton ma yaya Ibrahim ya
sanar da kai ya ce, wallahi bai gaya man ba haka nan
na cafka. Sun gama da na bebin ya tsaya akai ma
Umma nata a kalla ya kashe dubu saba'in.
Sun dade tsaye a kofar gida wajen duhu Sahabi
ya kwantar da kai bisa sitiyari yana ta kakasheta da
lafuzza masu sanyi ita kam ta soma bada kai amma
rigimarta na da yawa, wai yaya zata yi da yayanta
Kanal Kalil?
Umma na zaune bakin gado tana shayar da
yaronta nono su Husna da su Zainab duk sun iso, duk
dai wata matar aboki ta zo don halartar sunan gobe,
in banda mamin Sahabi da ta fi karfinsa. Nana ta
shiga da ledoji niki-niki ta jibga bisa gado Umma ta
daga kai ta dube ta tace, Daga ina kuma? Nana tace,
in ji Sahabi, na ki ne da na bebin' Husna ce ta soma
dubawa, tana daga kai tace, Mama Umma lalle kin
tabbata uwar dakin Sahabi irin wannan leshi! Aiko
zan ba Usman labari kun amshe mana Sahabi Zainab
ta ce, sai ki zauna nan Husna bayan na soma jin
Kishin-Kishin Mama Umma zata zama sirikar Sahabi?
Umma tace, ku rufan asiri da yaya Kalil, da su Mami,
wai Nana da mijinta; Husna ta ce, don Allah kada ku
166
ya basar bai takura mata ba. Sun tsaya a wani
shahararren shagon saide-saide, komi (mother care)
ya nunawa nana ta rinka fiddawa bebin, tun nana na
Riyasta irin dubunnen da za'a caji Sahabi, har ta ja ta
tsaya ta ce kudin sun yi yawa, ya cc. ba yaron
abokina za aima sayayyar ba, kuma dan uwar dakina
ko kin manta ne, kila ma suna na za'a saka masa ta
dan bude ido tace, Na yi zaton ma yaya Ibrahim ya
sanar da kai ya ce, wallahi bai gaya man ba haka nan
na cafka. Sun gama da na bebin ya tsaya akai ma
Umma nata a kalla ya kashe dubu saba'in.
Sun dade tsaye a kofar gida wajen duhu Sahabi
ya kwantar da kai bisa sitiyari yana ta kakasheta da
lafuzza masu sanyi ita kam ta soma bada kai amma
rigimarta na da yawa, wai yaya zata yi da yayanta
Kanal Kalil?
Umma na zaune bakin gado tana shayar da
yaronta nono su Husna da su Zainab duk sun iso, duk
dai wata matar aboki ta zo don halartar sunan gobe,
in banda mamin Sahabi da ta fi karfinsa. Nana ta
shiga da ledoji niki-niki ta jibga bisa gado Umma ta
daga kai ta dube ta tace, Daga ina kuma? Nana tace,
in ji Sahabi, na ki ne da na bebin' Husna ce ta soma
dubawa, tana daga kai tace, Mama Umma lalle kin
tabbata uwar dakin Sahabi irin wannan leshi! Aiko
zan ba Usman labari kun amshe mana Sahabi Zainab
ta ce, sai ki zauna nan Husna bayan na soma jin Kishin-Kishin Mama Umma zata zama sirikar Sahabi?
Umma tace, ku rufan asiri da yaya Kalil, da su Mami,
wai Nana da mijinta; Husna ta ce, don Allah kada ku
166
zama masu son kai mana Sahabi ya cancanci matar
kikir kamar Nana, shin wai ba mun riga su mami aure ba, in Mami na da hali har sahabi ya isa ya soma kwadayin aure, ni kam na tsaya masa insha Allah
bana shi ma sai ya ji dadin rayiwar aure; Zainab ta ce,
kyale Mama Umma kin ji Husna ai mu yau kwana
uku kenan ni da Abu mun saka Nana da Sahabi cikin
addu'armu, insha Allah sai mun yi nasara.
Nana dai na zaune ta rufe fuskarta da gyale,
maganganun su Umma kadai ke mata ruri a tsakar ka.
Ta mike ta nufi kicin ta duba abinda ke gare su
sannan ta nufi yin sallah. Bayan ta idas ta koma kicin
ta shirya abincin Sahabi ta aika masa.
Wanshekaran suna Ibrahim ya iske sahabi a
gidansa sun dade suna hira, can Ibrahim ya сe,
Sahabi na zo ne don na gargade ka akan nana, a
gaskiya ko alama ban yi zaton za kace kana son
aurenta ba, da tun farko na yi maka kashedi, saboda
akwai mai son ta tunta na karama ta hanyar Kanal
Kalil kuma amininsa ne, bayan wannan ma, rigimar
da ke tsakanin kanal Kalil da yaya Asma'u bana so
acc muna yinta ni da shi da Umma saboda auren
Nana yanzu ko gidansa Asma'u bata zuwa, kasan ko
uwarsu daya Ubansu daya ka yi hakuri idan
matsalarka ce da Mami zan taimaka maka ka samu
matar kirki.
A nan Sahabi ya tsaida shi ya ce, No! No!! No!!!
bana sha'awa! Nana son ta kadai na ke yi ba wai
wani dalili zai sani aure ba idan haka ne na sa
mahaifiya ta mana ta nemo man matar kirki, ka yi
/167
hakuri Ibrahim, ba zan iya kyale Nana ba sai in naga
ta yi aure? Ibrahim ya taße baki ya ce, wannan
ruwanka, ni dai idan Kanal ya ji maganar don Allah
ka fidda ni ka fidda Umma.
Tamkar ya kara haukatar da Sahabi, yanzu ma
kirikiri ya ke shiga gidan Ibrahim, don ya yi zance da
nana ya kuma riga ya rikitarwa da nana lissafi kaf,
har itama ta soma tunanin sai dai in ta mutu babu
aure amma 100% Sahabi ya yi mata, babu makusa
game da shi.
A yau ya je Legos aiki, duk kokari ya ke su fito
wani dan gajeren mitin don ya keße da Nana ta waya,
amma sai ya jiw ayarsa ta hannu na kira yanzu ko ina
ya ke bai rufe wayarsa saboda Nana, kada wani abun
ya taso ta neme sa ta rasa. Ya dauka ya yi sallama
amam sai ya ji hajiyar sa ce, tace yanzu a ina ka ke?
Ya ce, Ina nan Legos ne muna dakin mitin ta ce da
kun fito ka kirani ya ce in ce ko lafiya Hajiya? Та се
lafiya lau.
Yana fitowa bai yi tunanin kiran Nana ba sai
Hajiyarsa, ta ce, Ina fatan ba a cikin mota ka ke ba.
Ya ce A'a ina cikin ofis din mu ne na nan Legos da
wayar ofis ma na kira ku, ta ce To sai ka dau hakuri a
bisa hakurin da ka ke da shi, sannan duk wani dacin
rai ka aje gefe guda ka tausayawa matar ka mami
domin a yau mun yi rashin mahaifiyarta Iyana". Ya
dauka da salati da fadar Inna lillahi... ya kare da
cewa, Hajiya me ya faru da ita? Ta ce, sun sami
mummunan hatsari a bisa kan hanyarta ta dawowa
nan kaduna yanzu ake shirin kaita, Na tura Kannan ka
168
su duka uku mazan ga hadiza nan ta iso za mu biya
mu wuce da Sa'adiya don mu kasance muna can za'a
kaita. Ya ce, Nima daga Legos nan zan taho Kaduna,
ayi masu gaisuwa sai na zo.
Su Hajiya ba su isa ba sai da ta biya ta dauki
Malamanta mata su biyu suma su Abba ta ce su biya
su tafi da malaminsu na anguwar Sarki wato Mallam
Adamu. Suna isa su Mami da kannanta da dukkan
sauran jama'ar gidan ana ta shure-shure ana kuka
wasu na bugun kansu da bango, sai mahaifinsu ne
Abduljalal ke falo yana karatun qur'ani, Hajiya Aisha
ta daka masu tsawa gaba daya ta ce A uzubillah me
zan gani haka, wannan shirmen na ku ne zai dawo da
ita? Ku je ku yo alwala kowa ya zo yayi mata abinda
zai iya, wannan shi ne, gatancin da zai shiga
tsakaninku a yau. Nan da nan Hajiya tasa gida ya
natsu me salati na yi me istingifari na yi, amma ita
Hajiya da 'ya'yanta da wa'annan Malamai biyu, suka
tasa gawar Iyana a gaba suka bude Kur'ani mai girma
suka sauke mata Yasin kafa 7 da Tabaraka da
Kananan surori suna mai rokon Ubangiji yasa ta zama
mai ceton Iyana a ramin kabarin ta. Hajiya Aisha da
wa'annan Malamai da kansu sukai mata wanka fes
sukai mata sutura suka feshe ta da turare dizayna
sannan suka dukufa kwararo mata addu'o'i ingantattu
ga mamaci, har aka raka Abduljalal shi ya ma ya
karanto nasa addu'o'in ya tofa mata a kunne, a nan
Hajiya Aisha ta ce, Alhaji a madadinta da lyalanta
tana mai neman gafararka, kwalla ta ciko aidon sa,
Mami sai ya fada a kasan kunnenta amma darajar su
169
Allah ya gafarcemu baki daya na yafe mata muma
Allah ya yafe mana aka amsa amin.
Tuni Iyana ta tsufa a gidanta na gaskiya, daga ita
sai Allah sai ko halinta yau duk abinda ta yi a duniyar
nan ta mu mai cike da rude, zata bayyanar da abin ta.
(Allah ka shirya mu kasa mu cika da kyau da Imani
amin).
Karfe hudu Sahabi ya yo ma Abba waya akan ya
dauko motarsa ya tarye sa filin jirgi. Tunanin Nana
yana nan tare da shi, yau litinin sun saba yin bude
baki tare shi da ita a gidan Ibrahim, ya tabbata a yau
zata yi rashinsa amma kuma ya jita damu damutuwar
Iyana sosai har ta rinka tunasar da shi addu'o'in da za
su rinka yi ma lyana, tare da yin alkawalin yi mata
shinfidar nafila ta musamman a yanzu da sun aje
wayar a karshe ta rokesa ya yi iyakar kokari ya
kwantar da hankalin mami domin kasan ba wanda ya
fika kusa da Mami a yanzu.
Da wannan tunanin ya sauka gidan su mami,
gidan kam ya cika tantsam a harabar waje babu
masaka tsinke, zuri'arsu ta Maiduguri ta iso aminai
da 'yan uwa na kusa da nesa sun bayyana. Sahabi ya
kutsa nan ya kutsa can yana ma surukansa gaisuwa,
sannan shi da su Abba suka shiga cikin gidan anan
din ma abun babu dama mata ne bila adadin, a haka
Sahabi ya rinka rintsatsawa har cikin dakin Iyana
inda ya hango Mami rungume bisa cinyar Hajiyarsa
amma rike da cashabah a hannunta sai dai duk iyakar kokarinka baka iya ganin kwayar idon Mami don
170
azabar ja. A haka Sahabi wani irin tausayi ya zo masa
ya mikc ya koma kofar gida.
Suna nan wajen zaman makoki sai da akai kiran
mangarib sannan ya nufi gidansu inda Hafsat da
Uwani suka shirya masa kayan bude baki ya koma
gidan sai tsakar dare ya sami ganin mami ya yi iyakar
Kokarinsa wajen kwantar mata da hankali a karshe ya
bar ta anan gidansu shi kuma ya nufi gidansa in da su
Ya'u suka ci gaba da yi mai ta'aziyya.
Wanshekare bai san iyakar kudaden da ya kashe
ba na fannin abinci a gidan Abduljala itama Hajiya da
su Anti Hadiza an yo dahuwa iri-iri daga gidajensu
zuwa gidan Abduljalil A ranar sadakar uku gaba daya
matan abokan Sahabi su Ibrahim kenanda Usman su
Abdullahi da matayensu sun zo yi ma mami gaisuwa,
amma da shi ke Mami ba mai cikakkar tarbiya bace
ko ta dauki Abubakar din Umma balle ta yi mata
barka,s ai su Hajiya ne da su Anti Hadiza su kai ta
nuna farin cikinsu akan haihuwar Umman ga shi har
an saka sunan Sahabi amma sam Mami bata tsinka
ba. Direban da ya kawo su Umma ya dan ke be
Sahabi ya yi mai gaisuwa sannan ya ce, ranka shi
dade ga wasika in ji Nana Sahabi ya ji dadi fiye da
tsammanin nana domin ya fiddo kudi ba baiwa
direban amma bai san ko nawa ba ne ga wasikar:-
171
SAN
Dear,
Ya ku ke? Ya karin hakurin mu? Allah ya gafarta
mata muma in tamu ta zo Allah shi yafe mana. Na so
zuwa kwarai to amma ina jin kunya kuma ban san
yadda mamiz ata amshi al'amarinmu ba wannan shi
ya hana ni zuwa. Don Allah ka da ka manta ako da
yaushe kana raina.
Yours truly,
NANA SAN
Insha Allah
Sahabi kawai a kidime ya ke yana ma'amalla da
jama'a ne amma sam hankalinsa Nana ta kwashe
tsab, ya rubuta mata amsa a 6oye ya baiwa direba.
Sai da aka yi sadakar bakwai a wannanr ana ne
Alh. Abduljala ya hada kan Mami da Sahabi ya yi
masu nasiha a nan ya ce wa Mami tunda an yi
sadakar bakwai ya dace ki bi mijinki ki koma gida.
Abinda ya daurewa mami kai shine me ya hana
babanta ya yi ma Sahabi zancen tafiyar ta makaranta
England bayan tuni ya yi mata alkawarinz ai yi ma
sahabin zancen tafiyarta? Domin ita kam yanzu
makaranta ta zamar mata tilas, saboda haka nan suke
zaman doya da manja da Sahabi rabon da wani abu
ko da magana ya shiga tsakaninsu tun zuwan ta
Rivers. Wannan ba karamin ba kantawa Mami rai ya
172
1
yi ba, zata cigaba da hidimarta iyaka ta sanarwa
babanta in lokacin tafiyar ta yi.
Suna cikin mota mami da Sahabi ta yi tagumi
tana ta sharben kuka shi dai lallashi ya ke yi a
ganinsa rashin mahaifiyarta ne amma ita jin takaicinta ta rasa mai share mata hawaye a duniya
saboda ita ta amince Babanta ya fi son Sahabi da ita bayan ita kadai tasan bakin cikin da ya ke tura mata.
A kan dole Sahabi bai yi niyyar shiga fakin
Mami ba amma dole ya je, saboda gargadin Nana bai
son ya saba alkawari mami na kwance lamo bisa gado har yanzu kwallan ke fita mata, ya je ya zauna baking ado ya kamo hannunta ta runtse ido hawayen
suka ci gaba da jika girar idonta, yasa hannu ya goge,
yace, Mami kamar yadda na sha gaya maki kuka ba
zai dawo mana da ita ba, wallahi inda kina yawaita
mata addu'a ke kanki za ki sami sauki a ranki, ki tuna
fa Sarki Allah ne ya yi kiranta yaya za ai ta zauna
don mu mu ji dadi? Ako dayaushe mu zauna cikins
hiri zamu iske su, domin su da suka tafi basu yi sauri
ba, mu kuma ba mu dade ba, rayiwarce haka aka fara
haka zata kare, ki ma Allah godiya da ya bata yaya,
anfanin 'ya'yan nan addu'a, ta dan bude ido ta dube
shi cikins anyin murya tace, N agode Sahabi, a nan
ya ji dadi a ransa sai yau Mami ta yi mai kallonr
ahama, ya duka yana sunbatarta. Gaba dayan su babu
wanda ya yi la'akari da komi suka shiga aiwatar da
auratayya, amma kuma dai zukatansu babu dadi har
suka yi suka gama kome ne ne dalili? Sahabi ya duba
lokaci karfe tara da 'yan mintoci na dare sai kunya ta
173
kama shi ya mike zuwa turakarsa ya yi wanka ya fita
harabar gidansa ya yi zaune kan kujerar kwando cikin
duhun filawa, sai hasken farin wata kadai ke haskasa.
Ya jawo waya ya rubutawa Nana text kamar
haka My Sweety ki ban ma'anar SAN
Kwance take da gaskiya na makwafinta a hannu,
ta ajiye tasan dai kila shi ne amma babu tabbas tunda
yana tare da mami a wannan satin da wuya ya nemota
da dare irin haka, ita har yanzu bata san irin zaman da
suke yi ba domin a kullun yana nuna mata komi
lafiya lau.
Ta dauka ta duba, daga dai Sahabin ne rahin ran!
Ta rubuta masa: Idan kana son sanin Mana'ar SAN
sai ka yi rantsuwa zaka rike amana.
Sakon ya je garesa duk dai ya na zaune a tsakiyar
filawoyin harabar gidansa ya karanta, ya yi dariya ya
sake bata amsa:- Wallahi na dauki amana har karshen
raina, idan ma da alqur'ani ke ki so zan iya rantse
maki, don na tabbatas maki ni mai rikon amana ne a
gareki. Na ki Text din ya je mata ta kyalkyale da
dariya bayan ta duba, sannan ta rubuta masa amsa
haka:- Duk musulmin kwarai bai yiwa musulmi dan
uwansa fatan shan alqur'ani, To balle kai rabin rai,
(Sahabi amanar NANA) wannan shi ne ma'anar SAN
ka amince na ci gaba da kiranka MY SAN?
Sun kwashe fiye da awa biyu suna zantattukansu
cikin text na so da bege a karshe ya danna mata waya
aka dan kashewa juna jiki suka yi sai da safe.
Da safe bayan ya kintsa mami da ban
maganganu, sai ya nufi gida wajen Hajiyarsa, bayan
1.74
sun dan jima suna hirar mutuwa a karshe Sahabi yace
Hajiya daman ina son na zo maki da wata shawara,
amma ganin al'amarin na kwan gaba kwan baya sai
na dan dakata, shawarar kuwa itace Hajiya ina neman
aure! A nanta ke ta tsaya cak tana kallonsa don son
karin bayani, ta ce Aure fa kace? Yace, kwarai ko
Hajiya? Ta ce Rigamar ta ka da Mami ta kai dole sai
ka kara auren? Ya ce Eh to gaskiya har da rashin
kwanciyar hankalin na damu na, amma kuma a
gaskiya Hajiya ina son Nana! Sun yi shiru na tsayin
lokaci, hajiyarce ta soma magana tace, Ba zan iya
hana ka aure ba, amma kuma kar ka ji da wai ba zan
taba amincewa ka kara yo man auren sonr anka ba,
dole sai na yi bincike akan irin zuri'arsu da halayyar
gidanda tarbiyarsu da irin halin ita kanta yarinyar
Sahabi yace Hajiya yarinyar kanwar Umma ce matar
Ibrahim a 'yar fahimtar da na yi mata akwai ta da
tsoron Allah tana da natsuwa kamar dai su Umman
Hajiya tace,w annan binciken kane zan yi nawa, halin
Umma bai taba zama halin Nana.
Hajiya bata amince da lale Sahabi ya yi nisa da
son Nana ba sai bayan wata hudu da yin maganarsu,
domin ya kai kansa ga su Kanal kalil bai kuma ji ta
da dadi ba, don haka har ya soma tsiyayewa wato
alamun rama saboda shi Sahabi sakaran jiki ne da shi
dan abu kadan sai ya zabge ya rame dan kwanaki
kadan sai ya maida jikinsa. Da ta lura da matsalolin
sun rincabe masa, ga Mami har yanzu babu hadin kai
2a rigimar gininsa sannan ga zirga-zirgan aiki yau
yana can gobe yana kasar waje, sanan ga uwa uba
175
nanar da ya kallafa ransa akai a ganin sa itace
Karshen matsalarsa kwata-kwata Kanal Kalil ya yi
mai iyaka da ita ganin ta ma ya gagara sai waya
wadda wayar ma akan jima kafinta samu sukuni ta
bugo.
Hajiya Aisha ta tuno da tsohuwar aminiyarta
wadda sun taba zama a wajen aiki tare, sun yi
makwabtaka kusan lokaci daya ne ma su kai goyon
'ya'yansu wato ana kiranta Maman Abdul, mutanen
Gombe ne, suna can zaune a Gomben bayan mijinta
ya yi ritaya. Hajiya ta shirya direban ta da Uwani ta
cika but da tsarabar dankali da doya sannan ta yi
ciakken bayani a rubuce ta aiki su Uwani har Gombe
da yake fitattu ne nan danan suka gane gidan.
An yi muma kwarai da zuwan su bayan sun
kintsa, Maman Abdul ta kware wasika ta kwanta,
tace, ikon Allah ai Uwani al'amarin na gida ne kin ga
yarinyar dakin nan kawar Nana ce ta kut da kut.
Nana ta girma ba uwa b uba, amma zuri'arsu
mutanen mutunci ne, sun rene ta hanyar da Allah ke
so ni kam kwanan baya yarinyar dakin nan kece mani
nana ta samiw anda take so mutumin Sokoto ne
amma yana aiki Abuja har na ke cewa Nana lalle kin
yi sa'a mutanen Sokoto jama'ar aure ne domin akwai
mutunci,wallahi har tarihin, zamana da su Hajiya na bata ban san wai dana Sahabi ake so ba masha Allah
na yi murna sosai da wannan al'amari yadda zan Sada ciakkar shaida kan ta tamkar yadda zan bayas ne a
kan Sahabi da iyayensa. ko alama kada ayi shayin komi game da al'amarinta ita dai uwani sai wangale
176
baki da zuba godiya zuwa ga rabbi take duk dadi yа
kamata.
Wanshekare suka dawo dauke da zungureriyar
wasika. Sai da Hajiya ta gama shan kanun labari daga
bakin Uwani sannan ta karanci takarda inda kuma
gwiwoyin Hajiyar sukai sanyi, domin maman Abdul
ta fayyace mata komi, wato duk halin da Nana take
ciki Rabi diyar Maman Abdul ta sani don haka ta
nemi Rabi don karin bayani Rabin tace, Gaskiya
Mama Nana na cikin mummunar matsala domin a
yadda ta sanar da ni yau a waya 'yan uwa kaf sun
juya mata baya, banda Adda, Umma itama Adda
Umman bata iya fitowa fili ta goyi bayan Nana, don
Kanal Kalil ma cewa ya yi in bata amince da zabinsu
ba to ta bar masa gida, ita kuma a yadda ta gaya man
dazun in har ba su amince da Sahabin ba zata bar
masu gidan.
To wannan bayanin na Rabi shi Maman Abdul ta
rubutawa aminiyarta amma a karshe tace ba wani abu
kada a karaya a ci gaba da addu'a aure da rigima ya
kan zamo alheri, nema a nan daga yau zan soma
azumin kwana bakwai tare da nafiloli masu karfi,
insha Allah in har da alhairi aurensu za mu yi nasara.
Hajiya ta rike wasika rai 6ace tana yi ma Uwani
bayani sai ko itama Uwanin ta sha mur ranta ya басі
kwarai murna ta koma ciki, amma kuma Hajiyar ta yi
juriya ta rinka karfafawa Uwani rai ta mike ta je inda
kabinet din su yake ita da tsohon mijinta marigayi
Uban 'ya'yanta ta rinka zakulo litattafai amma duk
na addu'o'i nau'i nau'i ta zauna a tsanake tana fiddo
177
addu'o'in da ya dace ta dukufa Anti Hadiza ta yi
sallama ta shigo ita ma abisa dukkan alamu da wani
bacin ran ta zo. Ta durkusa ta gayas da Hajiyar
sannan ta koma bisa kujera ta zauna, ta zuba ta gumi
da hannu bibbiyu, Hajiya ta yi ajiyar rai tace, ke
kuma mene ne? ta ce Wallahi Hajia Mamin matar
Sahabi ce mana, ni har tsorota ke ban, na ya ko
wanan abokiyar zama ce ta kirki? Uwanita yi karaf
ta ce, ina kuwa ni zan ba ki labari ni da ke ganin
zahir! Hajiya tace, Allah ya sawwake, me kuma ta yi
duk da ya iba mata ido yaga iyakar gudun ta?
Hadiza ta c/anzu nan wata colleque dina Dr. Bello
da ke aiki a wata asibiti mai zaman kanta, likitar
bayerabiya ce, ta same ni har gida da wa'annan
takardar,w ai mami ce ki shirye-shiryen zuwa
England karatu har ta gama komi shi ne aka ce ta
kawo rifot din ta daga asibiti na shaidar lafiyarta to
ana cikin awon fitsarinta da jininta sai aka bata rifot
din tana da shigar ciki wata uku da 'yan kwanaki
yanzu ta je asibitin su Dr. Bello ne a kwashe mata
cikin, kin ji bala'i fa? Hajiya ta rintse ido tana ta
addu'ar kaucewar bala'i daga zuci, daga can kuma ta
fada a hili tace, ikon Allah shi kuma Sahabi irin tashi
Kaddarar auren kenan! Oh Allah kai mana maganin
wa'annan bala'o'i, wai abunda mu ke mafarkin samu
kullun mu ga jinin Sahabi amma shi ne Mami zata yi
mana haka! (duk irin taurin ran hajiya sai da kwalal
ta ciko idonta) Uwani ta yi sauri ta bar falon domin
kuka ya zo mata.
178
Hajiya ta hada kan kanan Sahabi gaba dayansu ta
raba masu addu'o'in da take ganin ya dace ayi ma
Sahabi. Kowanne yana amsa a lokacin ya dukufa
yayin da Uwani ta shiga girka abinci da safe ta yi
kosai a rabawa yara da rana tiwon shinka miyan kaji
a rabawa yara da gidajen marasa galihu, sun yi ma
Sahabin waya ya kuma zo a wanshekarc. Hajiyar ta
sanar da shi ta kuma bashi takardun ya duba a
tsanake, a nan ya shiga dogon tunaniw ato a ranar da
lyana ta kwana bakwai da rasuwa ya je yana lallashin
mami har suka... lalle ya amince a wannan dare
Ubangiji ya aiko masu da wannan rabon domin shi
ma ya yi mamakin abinda ya yi alhali bai da sha'awa
balle ya ce, ya biya bukata, rashin saninsu daya ne,w
ato ada can ire-iren kayan da'anda Iyana ke bai wa
Mami ne suka hana ta samun ciki domin yawanci duk
na tsarin iyali ne don dai da halshen Larabci ake
rubutawa. Saboda haka ita mami ta saki jikinta bata
taba tsammanin wani abu mai kama da suna ciki zai
iya faruwa da ita ba, a wannan 'yar saduwa da suka
yi dashi, don haka ma rashin ganin al'ada bai dame ta
ba, don ta saba yin hakan, ta samu karuwar kasala sai
yawan bacci amma tunda ba cikin ta taßa yi ba
wannan ba zai sa ta gane tana dauke da dan Sahabi
ba.
To a ranar da aka bata tabbacin cikin ne da ita, ta
koma gida da sauri ta fada kewaye ta sunce kayan
jikinta kaf ta tsaya gaban madubin kewayenta, daga
nononta abin ya soma firgita ta domin sun yi tantsantantsan ta tsurawa madubin ido tana kallon surar
179
Wa'annan maganganu yasa mami ta
hakura, a gaban hajiya ta soma bashi nono.
Nana ce ta rinka amsar kudi tana yi ma
jariri da uwa saye-saye, a daren da za su taho
Kaduna Sahabi ya rinka duba kayan da Nan
ta saya yace, wa'annan lesis din kuma fa? Та
ce Na mejego ne ko? Ya ce a wane dalilin
kuma ni dana kawai nace ki ma sayayya, ta
ce, SAN! Ashe haka ka ke, don me za ka
tsani Mami irin haka, ni fa bana son haka,
don sai kasa na rinka zullumin ni ma ko
hakan za kai mani ya mike ya isa gare ta, ya
zauna daf da ita ya ce, nana kamar yadda na
ce maki ba na son zancen mami to mu bar ta
a haka, amma ga ki ga ta nan bari ku kai
mata wa'annan kayan za ki ji tace ba ta so, ta
ce E ka dai bata ai hakkin ta ne, zamanka
take kuma kai ta yi ma haihuwa ba wani ba,
darajar dan ta taci abinda ya fi hakan.
Sahabi ya tabe baki ya rungumo Nana
yana yi mata rada, suka kyalkyale da dariya.
Suka isa gidan Hajiya a nan ya aje Nana da
kayan da suka zo da su, Hajiya ta yaba sayesayen.
Sahabi shi kadai ya je gidan su Mami ya
shiga har dakin da take jegon, ya gayas da su
180
Haiiva ta hode bos fa
a karshe dai ya ce. Mami Baba na gari? Ta
ce, "Eh yana nan ya ce, ya dace muje mu
ganshi a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13