Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Shcoolership. lyana ta ce, Dolensa ne ma ya biya, ina laifinki ma da ki ke son karatun, duk ba ga 'ya'yan 'yan uwansa ba nan suna zaune a gidan nan ba karatu ba sana'a, sai in ya fita msallaci ko cikin gari su kwashe mai kudi, amma ku 'ya'yan cikinsa ne zai wahalad, shima ya san ba ni za ai ma diyana haka ba. To bayan tafiyarta da marece Abduljala ya kira Mami daga shi sai ita sai Allah yace, mami ni nasan ban isa na gaya maki ba, kuma kema ba ki daukan a bakin komi ba tamkar mahaifiyarku, a zatona ke ce babbar diya ta zaki zaman mani mai ceton gidan nan daga bala'e, duk shashancin da su Zainba ke yi ina sane karfina kawai aka fi na zuba masu ido, sun ki aure tun da suka kashe aurensu ba su da sauran sha'awar yin wani saı aikin masha'a, idan har ba ki hankali ba wallahi sai sun dulmiyar da ke bisa irin hanyarsu, kuma ina kara jaddada maki wallahi wallahi a wannan zamani samin miji irin Sahabi yana da matukar wahala, idan wani ki ke hange to wannan yaron ya mallaki komi. Ba zan hana ki ci gaba da karatu ba, amma ki tallafi aurenki shi ne gaba da komi, idan kina sha'awar rayiwar aurenki ta zamanto irin ta Iyana ce to ina ta ya ki bakin ciki sai kuma in ce kaico da ke Mami. Tun da ya soma magana kan ta a sadde amma wannan lokacin ba kukan take ba amma dai ranta a 151 bace yake, saboda tun fil azam a rayiwarta tafi babanta fiye da lyana, tama fi sabawa da shi abaya ne ma har take iya hira da Iyana, a nan ta mai alkawarin zata yi abinda yake so,a mma ita d kada ya hanata zuwa karatu kasar turai, ya ce ya wannan taci gaba da neman makarantar amma dai zai yı magana da Sahabi kafin komi. A can Rivers ko da Sahabi ya ji yadda ta kasance da Mami ta bar gidansa har na tsayin kwana ki sun yi waya da Hajiya tace zata tura su Anti Hadiza ya сe, Bada yardarsa ba, a kyale su ta yi abinda ranta ke so. Tun daga wannan rana ya share Mamida ga ransa kamar wasa ya fara tsanar kansa dama ya ci gaba da zama da ita tun ada ba abinda ya ke so ya ji ta aiko ko iyayenta sun ce basu yin wannan aure.. haka kawai kamar ita kadaice diya mace a duniya. Mahaifinta Abduljala da kan shi ya kaita gidanta ya kuma shiga har falonsu ya ga komi lafiya yace, Bata bukatar kudi ko makamancin haka? Ta tuno da akwai ma wasu kudin a dakin Sahabi ya aje mata sannan ta ga kudinda ta ki amsa cikin akwatinta, gaskiya bata son komi ya kara mata nasiha mai tsinke jijiyoyi, ta hakura zata zauna don kaunar mahaifinta amma ba don tana sonz ama da Sahabi ba. Sahabi sun yi waya da Sa'adiya ta gaya mai an ce mahaifin Mami da kansa ya maida Mami gidan ta, ran Sahabi ya 6aci domin yana ganin girman iyayenta bai iya musa masu komi. Mami takan kwanta ta rinka tunani da tausayin mahaifinta, domin sanin kan ta ne bai mori rayuwar aure ba saboda yadda Iyana ke 152 masa tamkar dan ta, bai dace ana yi mai cin kashi irin haka ba, irin su sahabi ya dace ace ana cusganar mawa, ta tsani Sahabi babu abinda ta ke so irin ace yau gata ta sami karatu ta bar kasar, ai dole su rabu da Sahabi kamar yadda shi ma a can ya tsane ta har bai son ya tuna wai akwai nąuyin wata aba akansa wai Mami. Tun Hajiya Aisha bata damu ba da rashin zuwansa abu ya soma damunta, dominr abonsa da Kaduna an kwashiw atanni, kuma a yanayin aikinsa sun aje shi Abuja sau biyu ya kan fita turai ko jihohin Kudanci da ke da mai, aike ne yana yo masu akaiakai haka nan sakonnin Mami ta hannun hajiya ya ke biyo wa yadda ba hali taki amsa. A yau Hajiya ta soma yi mai korafin tun daya dawo Abuja ya dace ya rinka zuwa Kaduna ko sau daya a wata. To ya jure ya zo a wannan satin duk yadda Mami ta dauki Sahabi ya wuce nan, a zaton ta wai kudin da ya yi ne suke gaya mai karya ko me? Duk da ba su magana amma ta sanar da Ya'u ya shaida masa ya je gidansu Babanta na nemansa, kememe Sahabi ya ki zuwa, a nufinsa in ma Abduljalal ya nemai ta waya yace Mamin ce bata ga ya mai ba, saboda yasan fada dai zai mashi su zauna lafiya da ita, to wannan kalmar ta gundureshi, amma kuma ba dalilin kiran kenan ba, dalilin shi ne na batun karatunta ne. Duk abinda zai bar mata ya aje a dakinsa, da yaso ya bar komi hannun Uwani amma sanin Riyayyar da take nunawa Uwani ya fasа. 153 2 *** Gidan da aka ba Sahabi a Wuse ne zone 2, makwafta sosai da amininsa Ibrahim kuma daya daga cikin manyan Sahabbansa, wannan ba karamin dadi ya yi masu ba, ada a hotel ya ke kafin ya sami gida, yanzu da ya sami gida Ibrahim yace abincinsa kaf daga gidansa za'a rinka shirya masa, hatta yaro Ibrahim kin amince ma Sahabi ya yi ya dauka, da kyar Sahabi ya dauki yaron gida. Shi wani abin cin ma Sahabi kusan ya ce a gidan Ibrahim ya soma ci, ba'a taba nuna gazawa da shi ba. Umma kenan matar Ibrahim aminiyar Husnar Usman da Zainba din Abu Said, mata ne 'yan usuli wa'anda suka san hakkin mutum sannan sun lakanci zaman duniya duk iya yin mace sai dai ta yi kos din hila a wajen wa'annan mata, kowacce kuma ta fito a gidan da ya dace ace an yo auren mutunci. Ummalkulsum diyar wanit sohon ma'aikacin gwamnati ce a can cikin garin Gombe, Ibrahim hidimar kasa ta kaishi can Allah ya hada shi da Umma a lokacin tana shirin shiga jami'a, mahaifin Umma ya dade da rasuwa sun girma ne cikin kulawar 'yan uwansu maza ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya goma sha uku maza 7 mata 6, dukkansu kuma sun shahara a cikin Nigerian nan ta mu, domin babban yayansu Umma wanda ya zan shi ne da na farko a gidansu mai suna Kanal Kalil gwamna ne a daya daga cikin jihohinmu a zamanin mulkin 154 Shugabe Marigayi Sani Abacha. Gaba daya kannansa kowanne ya kama gabansa mazan sun kammala karatu sun yi aurc, matan ma kowacce ta horu da ilmi an aurar da ita sai 'yar autar su kadai ta rage wato Nana ta kammala jami'a zata fara hidimar kasa, Kanal Kalil ke rikonta yanzu haka cikin takun saka suke, saboda aurenta ya zo, wanda ke nemanta shi ne Kanal Ahmada minin Kanal Kalil ne na zahiri matarsa daya 'ya'yansa biyu, kusan ma abinda ake iki Kanal Kalil ya bashi, yayin da Asma'u itama 'ya'yar Nana din ce ta baiwa wani kanin mijinta da ke masifar son Nanan wato Shamsu, ita dai Nanan tana dai jin yadda za'a yi saboda duk wa'anda ake rigimar domin su basu birgeta. Kanal Kalil a Abuja suke zaune da iyalansa, to a wannan lokacin da Nana ta soma hidimar kasa ya sami cig aba inda aka maido shi rikon jaji, yaso ace ya aurar da nana kafin ya koma jaji amma rigimar auren bata bashi halin hakan ba, gidan kaninsa wanda ke aiki a Presidency wato Kabir ya so nana ta zauna amma Umma da Ibrahim suka roko arziki dole ta zo gidansu saboda Umman na da tsohon ciki. To yanzu duk wani girke-girke Nana ke yi a gidan Ibrahim bata yadda Umma ta yi komi, saboda nana ta horu a gidan yayyunta maza da mata, kowanne gida ta je ba kasafai suke sakarwa 'yan aiki kicin ba su a ganinsu masu yin haka ba mata ba ne. Wani abin mamaki tun Nana na karama bata da wata sha'awa sai ta aikin asibiti da son girke-girke, don haka ne ma duk mukamin da Kanal Kalil ya rike 155 lokutta da yawa Nana ke shirya mai abinci, har matar Kanal din ma ta saba, itace ma ta bada shawarar Nana ta yi digiri din ta a fannin girke-girke a nan ne ma Nana tace, to adda idan na yi digiri a wannanf annin taimakon me zan yi a kasa? Kanal Kalil ya yi dariya yace, ke dai akwai ki da shagwaba, Ina laifin idan ki ka sami aikin koyarwa, ko da iya ke ma ganin wanda za ki aura ai kila ba za ki aiki ba a gidansa, amma zai iya bunkasa maki guraren shigowar kudi, kin san mutumi na ke son ki ko Ahmad? Nana ta bata rai, Kanal Kalil ya ce, ki saki ranki zai baki duk iya irin lokacin da kike so, har sai kin fahimci irin son da ya ke ma ke wanda ba za ki iya goce masa ba. A iya sanin Nana Kanal Ahmad duk ya karade zuri'arsu babu wanda bai ci alhairinsa ba, ita daita na ganin yaya zata iya zama da mutumin da bai damunta balle har ya burge ta? Ko da ta matsawa yayarta Asma'u ta bar kanin mijinta ya fito don dai ta yi anfani da shi ne ta kori maganar su Ahmad, to amam sai ma ta haddasa masifa tsakanin Asma'u da Kanal Kalil. Nana baka ce Suduf babu abun da ke haskakawa a jikinta daga fararen idanunta sai hakoranta, bakin Nana irin bakin da ake alfahari da shi ne mai sheki da dibar ido, kyan idon ta kansa ka shagalta da Kalar Nana tana da yalwar gira domin duk sati sai ta je salun sun gyara mata ita saboda tana neman ta hade. Nana tana cikin mata matsakaita bata faye tsawo ba balle gajarta, tana da yawang ashin kai har ya kan so ya yi mata nauyi akai saboda yawansa, a kumatunta 156 akwai lotsa, da ta yida riya sukan lotsa har guda biyu a kowanne gefe, wannan da kyan idonta da yawan fara'arta ke bata ciakken farin jinin maza da mata, akwai ta da silin gurun wuya guda biyu. *** *** Wannan zuwan da Sahabi ya yi Kaduna gidan Hajiya ya soma isa, bayan yaci ya koshi, ya ce Hajiya a bisa dalili biyu na zo Kaduna tace, Allah yasa alhairi ina jin ka yace na farko na ga lafiyarku na biyu maganar Fegunan nan namu wa'anda ke garki Abuja na gadon mu ina son ki ban takardun dan ina son a cikin satin nan zan soma ginin gida na a Abuja ta yi dariya tace, Ai ina tsammanin daga nawa sai na ka ne a Garki Abuja amma na sauran yaran ba a nan Garkin su ke ba, ta mike ta je daki ta yi dogon bincike ta zo mai da su ya amsa ya duba yana dariya yace Duk karshenta sai na zo mun yi ciniki da Sa'adiya can gaba, don ina sha'awar filayenta Hajiya ta ce, ai ko in Sa'adiya ce ka sha kudi, ya ce insha Allah zan iya ina tsammanin gobe ma zan koma Abuja; Hajiya bata ce komi ba tunda ta san gidans arziki ake ba. aba wani zaman Ko da ya isa gidansa wanka ya yi ya shiga cikin gari, yana gidan Abu Said, duk sha'awa tana damunsa yadda Ibrahim ya ke da diya har ga wani* cikin shima Abu ga na shi 'ya'yan, kowanne gida 157 gwanin ban sha'awa, amma shi gidansa ba 'ya'yan sannan ba kwanciyar hankalin. Wanshekare ranar asabat ya shirya, Mami ko bacci bata fito ba ya ce ma su yau zai koma Abuja saboda hidimar shirin gininsa. Kafin ya shiga gidansa a Abuja gidan Ibrahim ya kutsa kai sai yaronsa ne ya shigar da kayansa gidansa. Ya shaidawa Ibrahim game da batun gininsa ne ya ke son ya rakasa wajen wani kamfani da ya zabi irin tsarin ginin da ya ke so, suka rankaya sai can. Ginin dai bai yi yawa ba irinsa a kasar nan, wato an dauko sihirin gine-ginen kasar Hongkong ne. Gaba daya hankalin Sahabi ya karkata ya juya kan al'amuran gininsa, sai ko aikinsa wanda ke bunkasa ta inda kudi ke shigo masa tamkar a majigi. Suna isowa gida Sahabi da Ibrahim kenan a nan ne kuma Nana ta dawo kasuwa ita da direban Ibrahim, suna kallon juna wato, Nana da Abubakar Sahabi sai zuciyar su ta buga a lokaci guda ba tare da dayan su ya san dalilin ba, Nana ce ta yi saurin kawar da idonta daga kallon Sahabi, amma sai har ta gama gaishe shi ta soma yi ma Ibrahim bayanai na wasu laluran can daban, Sahabi bai dauke idonsa ba akan ta, ta shiga gida, Sahabi cikin muryar da bai amince tashi ba ce, ya ce, wacece wannan Ibrahim? Ya ce, baka san nana ba, ai kanwar Umma ce, Ubansu daya a nan take zaune tana hidimar kasa kasan Kanal Kalil ya koma jaji mai rikon ta kenan, ya ce, wallahi ban taßa ganin taba. Nana ta fi minti goma da shiga gida amam zuciyar Sahabi bata daina dakan uku-uku ba, 158 yaushe rabonsa dajin haka akan diya mace? Fiye da shekara uku tun zamanin nemansa da Mami, bai sake yin wata magan aba mai tsawo da Ibrahim har kowanne ya shiga gidansa. A nan ne kuma lissafi ya kwancewa Sahabi na tsananin tunanin Nana shin wai me ma ya hana shi bin Ibrahim can gidansa. Misalin Karfe goma sha daya na dare har a wannan lokacin Sahabi na zaune a kujerar farko, kamar an tsafe shi tun daya shiga gida tunani ne dai ya ke yi bai taba raya ma ransa zai sake son wata daya mace ba, balle ya kai ga tunanin aure, wai ya ma samu ya kare lafiya da ta gidan wadda ta zame mashi kaya, ina kuma zancen ya karo aure ai kila Mami kashe shi zata yi da takaici, amma da ya tuno da fuska da cikar halittar wato kirar Nana sai ya ji zuciyarsa ta bada dam mamakinsa daya ya sha haduwa da ire-iren Mami da ire-iren su nana da ma wa'anda suka fi su komi amma don mi bai ji abinda ya ke ji a yau ba? sau nawa 'yan mata na tunkararsa ko ajirgi ko a wasu gurare amam bai iya bin su! A nan G.S.M din sa ta soma busar sarewa kamar ya tsinka amma ya dauka ya ce Yes Ibrahim (domin ya ga nambar Ibrahim din) lafiya ko? Ya ce, ina ko lafiya? Gaban Sahabi ya kara tsinkewa a zatonsa ko ya tsinci dami akala ya ce, me ke faruwa? Ibrahim ya ce Madam dina ke nakuda, lalle haihuwa ce, zamu asibiti shi ne nace bari na sanarwa amini kuma makwabci. Sahabi ya yi ajiyar rai yace, ikon Allah ka ce za mu asibiti yanzu, uwar dakina ba lafiya assha, Allah ya sauke ta lafiya. 159 Nan da nan kowanne ya fiddo motarsa, akan idon Sahabi nana ta fito dauke da katuwar jaka da karamin akwati a kafarta italiyan Silifas farare sol ta saka doguwar riga mai ruwan cincinbale, bai iya kallon kowa sai nana, har Ibrahim ya wuce rungume da Umma a kafada da kyar ya iya gaishe ta, dukkan idonsa na kan Nana. Asibitin dai kayatacce irin dai tasu ta 'yan gogewa, daga Ibrahim sai Umma ma'aikan asibitin suka amsa, shi din ma Ibrahim sun aje shi wani daki na musamman in da ya rataya wata riga da safar kafa tamkar likita mai shiga tiyata, a nan zai rinka hangen Umma ta taga su Nana da Sahabi an aje su falon farko na musamman har Nana ta zauna sai ta mike ta nufi wata nas ta tambaye ta ko ina kewaye ya ke? Nas din ta nuna mata,ta shiga ta yo alwala ta dawo ta balle jakarta ta fiddo dan Karamin alqur'aninta wanda bai fi girman tafin hanu ba, ta soma karantawa, tana rokin Allah ya sauki Umma lafiya, Sahabi ya dade yana tunani duk ya dace ya binciki Mami sanin addinin ta a tun farkon haduwarsu amma sam bai kula ba, ya tsurawa Nana ido, ya raya a ransa wato bayan wani tsananin kyau da ke gare ta sannan tana da cikar natsuwa,ta yi addu'a ta shafa shi ma ya shafa, sai yanzu suka hada ido cikin ido, ya yi mata fara'a itama ta yi, ta birgesa kwarai matuka, ya matsa kusa da ita, sai yanzu ya ji tana kamshi wani (body spray) mai taushi yace, Hala Umma ki kai ma addu'a ta ce "Eh ya ce zo mu je cikin mota na ina da wani littafin addu'o'i sai mu duba ta mike suka jera zuwa 160 inda motarsa take ya bude ya shiga yayin da nana ta jingina da motar ta dora hannayenta saman motar ta daga kai tana kallon sararin samaniya, har ya fito ya tsaya yana kallon kwayoyin idonta, wa'anda suka Kara razanar da shi ya ce, Nana! Ta sauke kanta sannan ta amsa kiransa. Ya bude wata addu'a mai mahimmanci ya soma karantawa yayin da Nana ta rinka binsa da amin, sun sami kimanin minti ashirin suna ma Umma addu'a sannan ya rufe littafin ya mikawa Nana littafin yace, kina da irinsa? Ta rinka dubawa a hankali can ta girgiza kai tace, ina da shigen irinsa, amma babu wasu addu'o'in a ciki, ya ce, ki dauki wannan ki yi anfani da shi tace lah! Amma fa na gode, wallahi na ji dadi na gode yace, babu komi ki man addu'a nima Allah yasa next year kamar yanzu ina taryar bebina kamar Ibrahim tace dan wannan insha Allah zan yi maka addu'a, kana nufin kace man kai da Mami ba ku da yaro? Ya kura mata ido yana mamakin tasan shi tasan Mami, amma bai nuna mata ba sai ya bata amsa yace, ki bar Mami da shirme mana wait soron haihuwa take yi, Nana sai da ta kwantar da katan sannan ta yi murmushi domin itama bata san dalili ba ta cika jin nauyi da kunyar Sahabi amma kuma bata son ya gane tan ajin kunyarsa, babu wanda ya sake cewa kanzil can Sahabi ya ce, Nana na tambayeki mana amma da sharadin zan ji gaskiya, tace, wallahi in har na sani zan gaya maka yace, Madallah yanzu 'ya'ya nawa kike sha'awa Allah ya baki? Nana ta vani juyar da kwayar idanunta ta lumlumshe su, 161 Nan da nan kowanne ya fiddo motarsa, akan idon Sahabi nana ta fito dauke da katuwar jaka da karamin akwati a kafarta italiyan Silifas farare sol ta saka doguwar riga mai ruwan cincinbale, bai iya kallon kowa sai nana, har Ibrahim ya wuce rungume da Umma a kafada da kyar ya iya gaishe ta, dukkan idonsa na kan Nana. Asibitin dai kayatacce irin dai tasu ta 'yan gogewa, daga Ibrahim sai Umma ma'aikan asibitin suka amsa, shi din ma Ibrahim sun aje shi wani daki na musamman in da ya rataya wata riga da safar kafa tamkar likita mai shiga tiyata, a nan zai rinka hangen Umma ta taga su Nana da Sahabi an aje su falon farko na musamman har Nana ta zauna sai ta mike ta nufi wata nas ta tambaye ta ko ina kewaye ya ke? Nas din ta nuna mata,ta shiga ta yo alwala ta dawo ta balle jakarta ta fiddo dan Karamin alqur'aninta wanda bai fi girman tafin hanu ba, ta soma karantawa, tana rokin Allah ya sauki Umma lafiya, Sahabi ya dade yana tunani duk ya dace ya binciki Mami sanin addinin ta a tun farkon haduwarsu amma sam bai kula ba, ya tsurawa Nana ido, ya raya a ransa wato bayan wani tsananin kyau da ke gare ta sannan tana da cikar natsuwa,ta yi addu'a ta shafa shi ma ya shafa, sai yanzu suka hada ido cikin ido, ya yi mata fara'a itama ta yi, ta birgesa kwarai matuka, ya matsa kusa da ita, sai yanzu ya ji tana kamshi wani (body spray) mai taushi yace, Hala Umma ki kai ma addu'a ta ce "Eh ya ce zo mu je cikin mota na ina da wani littafin addu'o'i sai mu duba ta mike suka jera zuwa 160 inda motarsa take ya bude ya shiga yayin da nana ta jingina da motar ta dora hannayenta saman motar ta daga kai tana kallon sararin samaniya, har ya fito ya tsaya yana kallon kwayoyin idonta, wa'anda suka Kara razanar da shi ya ce, Nana! Ta sauke kanta sannan ta amsa kiransa. Ya bude wata addu'a mai mahimmanci ya soma karantawa yayin da Nana ta rinka binsa da amin, sun sami kimanin minti ashirin suna ma Umma addu'a sannan ya rufe littafin ya mikawa Nana littafin yace, kina da irinsa? Ta rinka dubawa a hankali can ta girgiza kai tace, ina da shigen irinsa, amma babu wasu addu'o'in a ciki, ya ce, ki dauki wannan ki yi anfani da shi tace lah! Amma fa na gode, wallahi na ji dadi na gode yace, babu komi ki man addu'a nima Allah yasa next year kamar yanzu ina taryar bebina kamar Ibrahim tace dan wannan insha Allah zan yi maka addu'a, kana nufin kace man kai da Mami ba ku da yaro? Ya kura mata ido yana mamakin tasan shi tasan Mami, amma bai nuna mata ba sai ya bata amsa yace, ki bar Mami da shirme mana wait soron haihuwa take yi, Nana sai da ta kwantar da katan sannan ta yi murmushi domin itama bata san dalili ba ta cika jin nauyi da kunyar Sahabi amma kuma bata son ya gane tan ajin kunyarsa, babu wanda ya sake cewa kanzil can Sahabi ya ce, Nana na tambayeki mana amma da sharadin zan ji gaskiya, tace, wallahi in har na sani zan gaya maka yace, Madallah yanzu 'ya'ya nawa kike sha'awa Allah ya baki? Nana ta wani juyar da kwayar idanunta ta lumlumshe su, 161 - amma a zahiri ita bata san tana yi ba, amam sai zuciyar Sahabi ta sukurkuce ta kanannade na juyayin Kauna cikin sha'awa tace,w ai da nasan wannan tambayar za kai man da ban yi saurin rantsuwa ba (ta dan kanne ido) sannan ta ce, idan san samu ne wallahi ina son 'ya'ya da yawa, a kalla biyar ko shidda kasan 'ya'ya rahama ne, saboda kamar akai na naga misali kala-kala, saboda ban san Uba na ba ban san uwata ba duk sun rasu, sai yayye na wa'anda suka rene ni suka ban tarbiyar da suka samo daga hannun mahaifanmu, to shi ne na ke ganin, ko a nan ai haihuwa ta zamanto rahama a gare ni ko? Ta dubi Sahabi cikin idon sa, ya amsa mata ya ce, wallahi kin yi gaskiya, domin akai na ma na amince da hakan, mu takwas iyayen mu suka haifa amma a gaskiya wani lokaci har ji take Hajiyarmu kamar mun yi mata kadan saboda kowanne mu akwai ta hanyar da ya kan debe mata kewa. Sun jima suna wannan hirar wadda ta dauke dukkan lokacinsu a Karshe Sahabi bai san dalili ba sai kawai ya ji bakinsa ya furta cewa Nana za ki yadda ki zama mata ta ta biyu? Ta wani zuba masa ido cikin jin nauyi da kunya ta ce, kai ko don Allah me yasa ka yi wannan tunanin? Ba dai zan cen so zai sa ka ce na aure ka ba, saboda ban ga sabon da muka yi ba da zai s ana shiga ranka, don haka ina rokonka arziki kada ka kara man irin wannan maganar: Cikin sarkewar murya yace, 'Ko dai ke ce ba kya so na, ko kuma mai matar ne bakya so, ko in ce kin tsaida miji! Tacе, idan da ka fahinci bayani na na rayiwata da son 162 haihuwata ba za ka zargan ba da rashin son zama da matarka ba. Ibrahim ya fito a gigice ya ruko Sahabi ya ce wallahi ta haihu ans ami yaro! Sahabi ya kankameshi amma idonsa akan nana wadda ke zakwadi cikin maradin murna tana fadin Alhamdulillah, mun gode Allah suka diba agogo karfe daya da minti uku na dare Ibrahim ya ce, karfe daya saura minti goma daidai ta haihu ka ga a musulince asabat kenan ba mu shiga lahadi ba! Sahabi ya ce, Me kake so mu yi maku yanzu? Ya ce ka kai man nana gida don ta karade 'yan uwa da waya ta sanar da su batun haihuwar a nan asibitin za su bata duk irin abincin da take so, saboda haka zan zauna da Umma da sabon yaro na a nan. Hakan ya fi komi dadiw ajen Sahabi, a mota duk yadda ya bullowa Nana sai ta kauce. A karshe da zai aje ta ya jure ya ce, ina ganin dai na yi maki tsufa ko Nana? Ta balle marfin kofa zata fita, ya ce, ji mana, don Allah mene ne lanbar G.S.M. din ki? Ta gaya mai a gurguje, kan Sahabi kamar komfuta nan da nan ya dauke ya yi sauri ya zuba cikin ta shi G.S.M din yana hangenta ta shiga gida a ransa yace kai yarinyar nan bata son sa domin ko irin waiwayen nan batai masa ba. Ya shiga na shi gidan cikin kwanciyar hankali da wani irin sanyin rai ko ba komi a yau yana jins a tamkar kowanne namiji. Ya fiddo (diary) din sa ma'ajiyar rubuta sirrinsa ya yi sharhi mai yawa na canjin rayiwar da ya tsinci 163 A kansa a wannan rana na farko a yau ya fara shiryeshiryen ginin gidan da ya ke mafarkin mallaka a rayiwarsa na biyu yana jin a ransa ya hadu da macen da ya ke jin itace tushen warwarawar matsalar rayiwar aurensa, yana jin a jikinsa shi ma zai zauna da macen kwarai, ta girmama shi ta mutuntashi kamar yadda ake wa sauran abokansa. Ya rufe diary ya mike ya yo alwala ya gabatar da nafila tare da shugaban Istahara wadda Manzon Allah (SAW) ya yi koyi da ayi wato idan har abu alhairi ne za ka ji son abun a tare da kai ko yaushe yana karuwa idan ko babu alhairi za ka ji abun na fita ranka a kullun. Duk irin tsananin aikin Sahabi bai hana shi tunanin Nana ko yi mata waya, cikin kwana shidda kafin suna sun saba sosai da juna, sai a wannan lokacin ya gane duk girkin da ake aiko masa daga gidan Ibrahim ashe Nana ce mai girkawa, wannan kuma ya kara ruda Sahabi. Ana gobe suna ya yi mata waya da yamma akan ta zo ta raka shi su yo ma bebin sayayya. Ta fito kuwa inda ta yarfo kwalliya, da wani farin les mai rashin nauyi amma kai da ganin yadda ya lafe jikin Nana kasan zai yi tsada, ta tusguda daurin kallabinta gwanin ban sha'awa saboda ana hangen walkiyal gashinta tuli guda ta inda ta faure shi a keya ga gyale irin na 'yan matan

Chapter 11 of 13