na san 'yan uwan Sahabi mutane ne
masu son zumunci da son junansu, mu ba su hakkin
zumunci mu ga abinda za su yi, idan mun g
alalacewar ta Sahabi ta yi yawa, wallahi yanzu duk
ya fi mu tsufa na san ko rashin kwanciyar hankali ne
ya saukar masa da hakan.
To wannan kwaranniyar ita ake ta famar tsegumi
a gungun abokan Sahabi can Abuja da Kaduna, yayin
da cikin zuri'ar Sahabi abin ya soma matukar
damunsu, Hajiya kuma ta ce, aci gaba da addu'a
Allah zai maganin abin, amma ko an ce za ai fitina ba
itace ma fita ba, Shi ko sam gani ya ke boye-boynesa
bai bari na san abinda ya ke ciki ba, a zatonsa kowa
kalonsu ya ke lafiya lau.
Gidan su Mami ne kadai da kawayen take dauka
auren Mami (is perfect) wato ana zaman lafiya tana
daya daga cikin masu tarihin aure babu matsala, basu
san tsiyar da take shukawa ba don miji kam ta yi sa'a
bai cikin 'yan zamani. Don haka ma yanzu wani
lokacin ko ta taso aiki sai ta wuce gida abin ta iyana
da Abduljalal ba su damuwa tunda sun fahince auren
105
Mami da Sahabi har yanzu ba matsala, sai lokacin da
taga dama ta koma gidan Sahabi tun yana tsananin
damuwa har ya soma sawa ransa dangana.
*** ***
Yau Laraba tun da ya dawo daga masallaci sallar
asuba, a falo ya kudundune bisa doguwar kujera, da
casbaha a hannuns aya na lazimi, ya san kwana kusan
uku kenan bai jin dadin jikinsa amma a safiyar yau
ya fi jin nauyi da kasala, kirjinsa ya faye mai za fi da
radadi, kome zai sha? Dole ne ko yau ya je asibiti ko
kuma ya yi ma Hajiyarsa waya, ya jawo karamar
redio ya murda muryar Amurka, Kabir Isa Jikamshi
ne da Aliyu Mustapha ke sallama bai san kowanne
shiri suka kammala ba, ya dan ja tsaki lalle bai da
lafiya yau har bais aurari labarai ba, ya tuno zai
aikawa Aliyu Mustaphan Sokoto sako ta Internet a
dalilin dan uwansa ne ta fannin Hajiyarsa kuma suna
zuminci sosai da Sahabi, amma sai shirin Yusuf na
Kura Baban Hafsat ya dauki hankalinsa wato a shirin
iya ruwa fidda kai. Kafin Sahabi ya koma В.В.С
London da karfe bkawai tuni zazzabi ya rufe sa ruf,
ga kirjinsa na ta Kara suya, yana son ya yi amfani da
G.S.M din sa amma ya barota a dakin baccinsa in da
yasa ta (on charge) ga Mami ba waniz aman arziki
suke ba balle ya kwalla mata kira, duk ya kosa Ya'u
ya shigo domin yana can waje yana wanke masu
motoci, ya kwanta lamo, shi kadai yasan yadda
jikinsa ke matsa mai, ya saba da yawan zazzabi
106
amma zamanin yana sakandire, tun da ya shiga
jami'a bai iya tuna ko sau nawa ya yi Ciwo, Insha
Allah da ya yi ma Hajiyarsa waya zata taimaka masa
da magunguna. Bakwai da rabi daidai yana ji B.В.С.
su ka yi sallama da kyar ya iya fiddo hannunsa ya
kashe redion, lumfashi sama-sama, irin dan baccin
nan an mai zazzabi ya rinka dibarsa.
Mami daga daki ta ji yau gidansu shiru, sai
kwaramniyar Kiristi daga can kicin, ada ta saba a bisa
al'adun Sahabi ya kan kunna muryar Amurka sai
B.B.C. London wani lokacin ya mayas da faifan C.D.
na karatun alqur'ani cikin muryar Ahmad Suleman
ko na Limamin madina ko limamin Makka babu dai
kirar da bai sakawa, wani lokacin ma ya kan cika
gidan da wa'azin ja'afar Adam, duk da tsaurin Mami
ta kan so wa'azin Mallam ja'afar Adam. To amma
yau bata ji sautin komi ba, haka nan irin zirga-zirgar
Sahabi da ya kan yi, wato ya kai ya komo amma
shiru. Nan da nan duk da ta fita harkarsa sai taji babu
dadi, domin dai sabo wani abu ne, kuma ma dai ta
san tana son Sahabi ra'ayinsu ne dai kawai ba iri
daya ba.
Zaunė take gindin madubinta tana 'yan shafcshafneta take wannan tunanin, ta tsurawa madubi ido
ta na kallon sigarta har yanzu ita mai kyau ce amma
raman nan bata yi mat kayau ba, wai me ke damunta
ne, tabas suna son juna ita da Sahabi to me yasa ba su
iya zaman kwana biyu yanzu sai sabani ya shige su?
Shin wa ya fi dacewa ta kai kukan tane don samun
shawara mai kyau? Ko kadan bata son ta kashe auren
107
ta, saboda samun wanda za ta lankwasa kamar sa da
wuya, ko da ya ke bata lankwasa Sahabi tunda ya ki
amincewa da ra'ayinta ita ta san da ya mori aurnesa
fiye da zatonsa. Ta mike ta saka kayanta, tana
tunanin yau ba za ta fita ba zata zauna a falo sai taga
fitowarsa ta tabbatas lafiya kafin ta fita zuwa ofis.
hannu, zani da Jaka da G.S.M din ta rungume a
rigar da dankwali iri daya gyalen ne mahadin jakar,
ta fito, kwas-kwas, kwas karar da takalmanta ke yí
kenan, ta iso falo sai ta yi turus ganin Sahabi a
kudundune, ta jefas da komi ta isa gare shi ta
tsugunna ta sa hannu ta dafa kafadarsa, 'Sahabi
Sahabi, Ab-kar', ya dan bude ido kadan duk sun yi
jajir me ke damunka Ab-kar? Ya bude baki, ya ce,
Ban sani ba mami, kirji na ya fi damuna, don Allah
kisa hannu ki rinka danna man kirjina a hankali kila
na iya yin wanka ta zauna gefen kujerar ta dan yane
rufar da ya yi ta soma danna mai kirjin, amma Mami
taje jikinsa za fi, rau ta ce, Sahabi, kawai zazzabi fa!
Ya ce, 'Eh amma na fi damuwa da kirjin, tace, sannu
sahabi, yace yauwa, ta mike tace, ina zuwa ta je ta
dauko dan Raramin tawul da ruwa a roba ta zo ta
soma goge mai jiki, ta mikar da hannu tana shaf amai
kirjin yace, 'Yauwa na gode Mami' ta dau lokaci
tana yi mai haka sai da ta ji ya soma lunfashin bacci
ta mike ta je kicin ta umarci Kiristi ta kawo ruwan ti
a filas da kofi da suga da madara da ovaltine ta zauna
jikin Sahabi sosai ta tsura mai ido, kamar zata ba shi
lafiya, can ya yi kokarin ya juya sai ya yi ido hudu da
Mami, ya tsura mata nashi idon,r abon da Mami ta yi
108
mai kallo irin na yau har ya soma mantawa, kallon
yana birgeshi, ko kila ita bata sani ba ne oho!.
Ta taimaka masa ya juya amma jikin ya kara
tsananta da za fi, ta ce, sannu Ab-kar ka tashi ga
shayi, kuma ka dunga ma kwanciya ba magani? Ya
jure ya zauna, yau itace ranar farko da Mami ta hada
mai shayi da hannunta. Yana gama sha ya shiga
kewaye da sauri ya amayas tas ya kuskure bakinsa ya
fito ya kara kwanciya, Mami ta dube cikin kaduwa
tace, Na yi ma Hajiya waya an ce, suna dakin
ganawa? Ya ce, Nemo man anti Hadiza, a nan ma ta
sake yi ma Hadiza waya tana bakin aikinta, taga
wayar mami ta amsa da sauri ta ce, Yaya lafiya ko
Mami? Tace, Anti Babu lafiya wallahi baki ga Sahabi
ba, hadiza ta ce, "Assha, aje wayar zan zo yanzu,
Anti Hadiza sanin halin lajiyarsu tafi son akai iyalan
ta asibitinsu (Nursing home Ibrahim Abacha
Memorial) saboda haka sai ta nemi Abba ta G.S>M
din sa ta yi sa'a yana bisa hanya zai zo wajenta tace
juya mu je gidan Sahabi yanzu Mami ta yo minw aya
tace bai lafiya. Sun iske su a falo daga shi har mamin
sun yi yare-yare Anti Hadiza ta yi 'yan tambayoyinta
akan dole dai ta ce su je asibitin Hajiyarsu.
Har suka is alikita ya duba Sahabi ya bashi gado,
amma Hajiya basu fitoda ga mitin ba, a matsayin
hajiya Aisha na itace Senior Metron a wanan asibiti
Sahabi ya sami kulawa sosai amma dai ba su ce ga
ciwon da ke damunsa ba, misalin karfe goma sha
biyu na rana Hajiya ta fito a harabar asibiti duk
motocin iyalan t ane, ga motar Mami ga motar
109
Hadiza ga ta gida wadda Abba ya zo da ita can ga ta
Sa'adiya abinda ta soma tambayar wasu nas, nas da
suka tarbeta shi ne me ke faruwa yau asibitin ya hade
da iyalai na? Suka amsa mata Sahabi ne babu lafiya,
har likitoci sun bashi daki.
Hajiya Aisha bata ta sake cewa komi ba, ta nufi
dakin da aka warewa Sahabi, daya daga cikin
kayatattun dakunan asibitin, ta murda kofar ta shiga,
gaba daya aka soma gayas da ita su Anti hadiza
kenan, wani likit ana auna jinin Sahabi, ya gam aya
juyo ya gayas da Hajiya sannan ya yi mata bayanin
jininsa lafiya lau bai hau ba, sannan ya dauko rifot
din Sahabi da ke jikin gado yana nunawa Hajiyar,
suna kan bincike an kai jininsa awo ana son asan
sakamkao a kalla kashi uku a binda jininsa ya kunsa,
haka nan an debe bawalinsa shima ana neman
sakamkao kamar biyu, gaba daya suma lab muna sa
ran zuwan su nan da 'yan awowi. Hajiya ta nisa ta
kara zuba idanunta da ke boye cikin gilas akan
Sahabi, sannan ta sake jefawa likita tambaya wane taimako akai mashi? Ya amsa an bashi allurai na
(Pain reliver) da na bacci har sai mun gano ainihin
ciwonsa, ta ce Alah ya sawake, gaba daya dakin aka
amsa amin, Mami na can zaune ta gefensa inda ake
mai darin ruwa ta dafe mai hannu sanan ta yi tagumi
da hannu daya, duk ta yi zuru-zuru, Hajiya ta zaga ta inda take ta shafi kan Mami sannan ta dan rungumo
ta a jiki ta ce, Ba komi mami ki kwantar da hankalinki zai ji sauki yana tare da kwararrun likitoci
sai kawai Mami a wannan lokacin ta ji kwalla sun
110
zubo mata na tausayin mijin ta sanan 'yan uwanshı da
Hajiyarsa da ta tsana ta ji duk ba haka suke ba, yadda
Hajiya ta rungumo ta, sai tayi da na sanin yin
abubuwan da ta yi abaya.
Hajiya ta cigaba da shafar bayanta na tsayin
lokaci, sannan Hajiyar ta shika ta ta soma shawagi da
idanunta cikin dakin tana kallon kowa dai-dai ta dire
idonta akan Anti hadiza na lokaci mai nisa sannan ta
fita zuwa ofis din ta, Anti hadiza ta san matsayin
kallon da Hajiyar ta yi mata, don haka ta san kira ne a
boye ta ido, sai ta mike ta bita ofis sun jima suna
shawarwarinsu daga karshe Anti hadiza ta koma
ofishin ta da niyyar sai da yamma idan Sahabi ya
farka daga bacci zata dawo sannan kuma kila
sakamkaonsa ya fito an san abinda ke damunsa.
*** *** ***
Bayan an yi sallar issha'e Mami an zaune bakin
gado tana mai fuskantar Sahabi rike da fitel na abinci
tana rike amam shi ke ci da hannunsa, ya rinda
kokarin gyara zama, ta mike ta zare filon ta mikar da
shi ya mike bayansa, sannan ta cika kofi da juice ta
mika mai ta zauna, ya ci gaba da cin abinci ba wai
don yana so ba abisa tilastawas likitoci, daki ciki da
falo ne a falon su Abba ne da sauran 'yan uwansa, a
dakin in da Sahabi yake daga Sahabin sai Mami sai
su Anti Zainab da Anti Yasmin da lyana da suka zo
duba shi sannan Sa'adiya da mijinta suma suna
zaune, Hajiya da Anti hadiza tare suka iso, aka shiga
gaisawa tare da jajantawa juna, a nan Mami ke cewa
111
a gwadawar jininsa an kawo sakamako daya an sami
tayifod kadan, Hajiya dai tamkar bata gamsu ba ta ce,
'Ni kirjin shi ya fida mu na, don haka na ke son a
sake hanyoyi gwadawa, Sahabi ya ce, don ma ba ki ji
ciwon da na ke samu da shi ba, yan zun haka abin cin
nan da na ke ci a zaba ya ke karawa kirjin nawa,
Hajiya ta dubi hadiza, Hadizan ta ce, ya dace a yi Exray da safe in Alah ya kai mu ko Hajiya? Та се,
Abinda ya dace dai kenan, mami ta ce, akwai likitoci
uku da za su duba shi da karfe tara na dare din yau,
Hajiya t ace, 'Ace su saman a ofis ina jiransu.
Sun sami Hajiyar an gama tsare-tsarne abinda za
a yi mai gobe da safe, kowa ya koma gida, an bar
Abba da Shehu su ne za su kwana a falo inda Sahabi
ya ke a bakin Sahabi na gadon jinya an shinfida wa
Mami katifa, amma har misalin karfe sha biyun dare
mami na bisa gadon jinyar duk da zafin jikin Sahabi
bai sa sun rabu ba, can ne ma yace, ta rage karfin A.C
san yi ya ke ji, ya kudundune sosai cikin bargo,
amam duk da haka tana tare da shi, misalin karfe
ukun dare yace, Mami cikina, tace, me ya faru kuma
ya ce, bayan ciwon ciki yana man za fi tankar ana hura wuta, ta matsa kararrawa nas. biyu suka shigoda sauri, su Aba ma sun shigo nan da nan jikin Sahabi
ya rikice bayan ya dume da jante ya rinka kumaji gabanin asuba ya soma suma.
Tamkar su Hajiya da likitoci a nan suka kwana, kowanne na iya kar kokarinsa na neman ran sahabi, sai Rarfe takwas da rabi daidai na safe aka shigar da shi kunfuta rum don aunc-aune, an yi mai (Scarning)
112
sannan an mayas da shi dakin Ex-ray, tsayin lokaci
likitoci da su Hajiya ana gwadawa a karshe sun gano,
ciwon Sahabi filla-filla ulcer ce, Hajiya a lokaci guda
ta ritnse ido tana salati a cikin ranta ta tsani mami
tsanar da bata taba zaton zata yi ma dan adam ba.
Tasa aka kira Sa'adiya da Anti hadiza da mami a
ofis din ta ta ce, gaba dayan ku a nan ku ba jahilai ba
ne, sanin kan ku ne, babu abinda ke haddasa cutar
ulcer sai yinwa, ta dan tsaya tana kallon tebirinta
cikin dacin rai, sannan ta ci gaba, Mami da ke za mu
yi kuka abisa rashin kularki kin ga inda kika tura
Sahabi, burinki ya cika ko? Mami ta sadda kai ta
soma sheshekar kuka, Hajiya taci gaba na kira ki ne,
don na gargadeki, an yi na farko insha Allah an yi na
karshe, ba zan kara sa ido abinda ya faru baya ba ya
sake faruwa, don haka daga yau sai yau, baki da
sauran bakin da za ki hana 'yan uwan shi shiga
harkar gidanku, wannan tilas ne ya zama dole.
Mami ta koma dakin Sahabi taci gaba da 'yan
koke-kokenta, 'yan uwansa kaf sun nuna mata tsana a
hili kuma ko a gaban wa, hatta itama hajiyar yanzu
'yar gaisuwa kan hada su, yayin da na ta 'yan uwan
yawan zuwan su asibiti dubiya sun san rigimar da ta
kunno kai tsakaninS ahabi da Mami suma sun ara sun
ya fa sun dauki mugun za fi da zuri'ar su sahabi, don
haka idan an hadu a asibitin abubuwa maras kyau da
dadi kan faru.
Su kam likitoci tunda sun gano ciwo ba su yi
sako-sako ba sai kokarin magance ta. A yau ma
dakin tantsan ya ke da 'yan uwan Mami da na Sahabi
113
4
ana zaunc, ana dan jefa magana lokaci lokaci, ita dai
mami sai yanzu ma ta fahinci sahabi sosai,a she don
tsabar son da ya ke mata ako da yaushe yana kokarin
kare ta bai yadda aga laihinta a bisa wanan dalilin sai
taji son da take masa ya karu bata tunanin iya
rabuwa da shi, sai ma ya zamanto batancin da yan
uwan shi ke mata tankar suna kara zuga ta ne da
Kaunarsa G.S.M din Sahabi ta rinka wani dan taken
algaita alamun ana son magana da shi, sai mami ta
dan kawad da kai tana zance da Anti Yesmin, sai
Sahabi cikin siririyar murya wadda bai son magana
sosai ya ce, 'Mami" ya nuna mata G.S.M din sa da
ido, ta dauka cikin garari da isgilanci tace, Yes hello
Mami ce; ya ce, mami ina gajiya Ibrahim ne daga
Abuja na ke magana, dazun nan na samu' labarin
Sahabi yana asibiti? Ta ce, wallahi kuwa ya ce, Allah
ya bashi lafiya me ke damunsa ne? a nan Mami kuma
duk ta raina kan ta, ta soma 'yan kame kame, ta ce,
ciwo ne dai ga shi nan na zamani da ya dami jama'a,
sai dai Allah ya sawake mana, ya ce, amin, don Allah
ace ina gaishe shi sai an zo dubiya.
Su Sa'adiya da 'yan uwanta sai wannan ya dubi
wannan, wannan ya dubi wancan, suna dan
murmushi su Anti Zainab kuma sai 'yan harareharare ana sakin dan tsaki. Saboda Sahabi idonsa
biyu Anti hadiza ta rangwanta masu, dómin bata son
su yi abinda zai bata masa rai tunda ga halin da ya ke ciki.
To wanan al'amari na auren mami da sahabi sai
abinda kuma Allah ya yi, domin an zuba masu ido
114
yanzu kam sosai, 'yan uwa ransu ya yi mummunan
baci haka ma abokansa wanda duk ya zo asibiti ya ji
ciwon da Sahabi ke yi sai haushi da kunya su kama
shi.
Abu Sa'id tare da abokai uku ya zo, sun kebe da
Anti hadiza yana ta fada ya ce, a gaskiya idan ku
Anti ba za ku iya zartas da komi ba to mu kam
Kungiyar abokansa ashirye muke, yaushe za ace
mutun kamar Sahabi mai son ya ga ya ciyar da kai ka
koshi sanan ya yi ma alhairi yau shi ne kwance gadon
asibiti saboda horon yinwa kai Anti wannan masifa fa
ta isa ina dalilin soyayyar yinwar da zata ja maka
cuta, Anti hadiza tace, kuma dai kun fada ai ku
kwantar da hankalinku mun kammala shirin mu tsaf,
mu dai addu'ar mu Allah ya bashi lafiya, duk wannan
kadihurin da take yi na wannan lokacin ne, tun farko
abinda yasa ka ga an kyale ta har shekara daya da
auransu ta mayas da Sahabi sahorami dalilin
hajiyarmu, to yanzu ko hankalin ta ya fi na kowa
tashi,t ace ta amince da komi amma ban da ciwo!
Tun da mami ta zo duniya bata taba shiga rayiwa
mai wuya ba irin ta dan zaman su asibiti da sahabi
kwana biyar su kai ana jinyar Sahabi amma yadda
Mamit a rinka ji tamkar ta shekara biyar cikin kunci
da bacin zuciya, idan ma yanke shawara ta yi ta koma
gida ta bar auren Sahabi, to ai ba mijinta ya yi mata
ba, kuma ma su Anti Zainab sun ce sai dai ayi kare
jini biri jini ba za'a taßa yadda a raba Sahabi da
Mami ba domin a cewas su wannan hassada ce kawai
ba don 'yan uwan Sahabin sunda mu da shi ba. Sau
115
2
2
tari da yawa idan an faye matsawa Mami da ido ma
kawai ta kan bar masu dakin finyar ta shiga kewayе
da ke manne a dakin na Sahabi ta rufe ta zauna ta yi
kuka mai kunar rai ta wanke fuskarta ta fito, wasu
kan gane Mami kuka ta yi amma wasu ba su gane
hakan matsalar aume zamani kenan, lyaye su ke
tsunduma 'ya'yansu cikin fitintinu kala-kala, amma
daga bisa ne a fake da zagin zamani ne, yanzu ita dai
Mami mun amince abinda ke faruwa kenan a gidaje
da dama a kasar nan tamu, abinda 'ya'ya ke so shi za
su yi, ba kwaba ba tsangwama, to yau ga abinda tafi
so, ko ya sille mata ko ta yi masa sanadiyar shekawa
barzahu, duk a dalilin rashin samun kykayawar
tarbiya wadda subhanahu wata'ala ya umarci iyayen
kwarai su baiwa 'ya'yansu, Mami ta sha tuno da irin
wa'azin da sahabi kan mata a wasu lokuttai amman
sait a watsar da shi tamkar ba diyar musulmai ba,
yace shin wai Mami me ke damunki ne kamar ba
diyar babban gida, yaushe zamu rinka abin karanta a
kullun, bana ce, abincinda muke sawo wa ba babu
dadi ba ne, a'a, abinda ke damu na shi ne babu wanda
zai shigo gidan mu ya ci abinci, kin ga ai wannan ba
rayiwa ba ce, kuma ni f aba yaro ba ne, Mami ina
sane da rashin girmamanin da ki ke yi man a kalla ko
a shekaru na na ci mukamin da za a ce kina ban girma, amma kin ki, shin ke wai ba kya saurarne wa'azi ne? Rissar Nana Fatima in da ta je ga mahaifinta Manzonmu Manzon rahama (S.AW) ta ce, ita kam aiki ya yi mata yawa a gidan mijinta Sayidina Ali (AS) duk wahala itacc. Manzon Allah ya yi shiru
116
sannan ya ce akwai wata mata a cikin birnin Madina
idan ba ki sannu ba sai ta riga ki shiga aljanna saboda
kular da take ma mijinta da dinbin biyayyar da take
masa; Ahan hankalin Nana Fadima ya yi mugun
tashi, har ta kuduri niyyar sai ta gano wannan mata, a
hankali ta gano ta, tuaje gidan ta nemi,matar zata zo
kitsoematar ta amince amma da sharadin sai in ta
sanarwa mijinta idan ya amince, to ya amincen ta je
tare da dan ta Hasan amman sai matar tace a'a ban yi
maiki izziní ki shigo ba domin a jiya ke kađai ki ka
ce man saboda haka ke kadai na shaidawa mijina ban
ce mai za ki zo da Hasan ba sai ki koma sai an sanar
da shi za ki zo da Hasan idan ya amince ki zo, a nan
ma ta sanar da shi yace e ya amince, Nana Fadimah
ta zo lamma kuma sai ta zo wanan karon da Husaini a
nan ma imatar ta ce, aida Hasan ki ka ce ba Husaini
ba,s airan sanar da iko da gidan, a nan sai Maigidna
yá ceridan har Nana Fadimatu diyar Shugabanmu
Manzon rahama zata zo gidan nan da dukkan
mutanan Madina to na amince mata d tio
sbna Nana Fatima ta zo wannan baiwar Allah na yi
amatarkitso katsam, mijinta ya dawo ta ko kyalc nana
Fadima ta koma gare shi tana taryarsa ta sauke kayan
da ya 2o da su ita soma goge mai jiki tana ta gayas da
shi cike da kulawa da biyayya tana kuma yaba masa
akan kokarin da yake yi da su, ta kawo mai wannan
ta jawo mai wancan duk dai hanyar farantawa tun da
yasshiğo ita, matar nan take yi,ta rasa me ma za ta yi
anebidon ajin idadin mijinta? Iyakar girmamawa da
mutuntawaianatar nan ha nunawa mijinta, wanan. abu
17
テ
kuwa Nana Fadima na makale na kallon duk abinda
ke wakana, jikin ta ya yi san yi, ta amince da lalle
mahaifinta ya yi gaskiya, wannan baiwar Allah na
daraja auranta fiyc da mata da yawa a duniya, babu
abinda za ta yi ba tarc da amicnewar mijin ta ba
Sahabi ya dube ta amma kaar yana watsa mata
garwashin wuta, ko alama v a'azinsa bai shige ta ba.
to ire-irne hakan ya sha faruwa amma ana watsar da
Sahabi.
Yau a asibiti duk ta soma nadamar kin jin
wa'azin da Sahabi ke mata.
Ko da aka sallame su a rana ta biyar Sahabi ya
warke tangaran sai dai kuma rashin karfin jiki,
misalin karfe daya na rana suka isa gida, ita dai
Mami ta kira wannan lokaci da canjin yanayin
rayiwa, saboda ko a gidan na su jama'a ne bila adadi
'yan uwansu na Sokoto ma sun zo don haka gidan
cike ya ke kai ka ce Mami ce ta haihu, zan cne abinci
kuwa sai dai a Fidda a bayas domin ko ta wane gida
aiko da shi ake yi, girki kuma na musamman ake yi,
mami dai na cikin daki tare da 'yan uwanta ila kawai
zuciyar taf ba masaka tsinke duk zullumi ne da
fargaba shin yanzu kuma ko wane irinz ama za su yi
da mijinta? Lalle ta dai san yana sont a amma kuma
'yan uwansa da Hajiyarsa suna da matsayi a zuciyar
Sahabi, bata ma san cewa matsayinsu ya zarce kima
ba sai wannan dan lokacin, an ya ma ko za su bar
Sahabi ya ci gaba da zama da ita? Can daya gefne su
kuma 'yan gidan su su ruda ta domin sai yanzu suka
san auren Sahabi na da mahimmanci domin sun ci
118
burin janye sa su raba shi da zuri'arsa. Ta matsu
kwarai ta ga an bar masu gidan su ko taje wajen
sahabi ta ji mene ne nasa canjin? Tun da bata sami
sakewa ba har yanzu balle ta san matsayin
soyayyarsu.
Karfe goma duk mata sun koma gidajnesu, har
'yan gidan su Mami, sai Mami a yane labulen tagar ta
tana kallon harabar gidan su, motoci biyu suna nan
tsaye ama na abokan Sahabi ne, ta ja tsaki suma
abokan na sa ta fita hanyar su, domin ta lura da 'yan
take takensu, Ibrahim na Abuja da matarsa Umma su
kadai ne ba su nuna mata komi bada suka zo duba
sahabi a asibiti, kamar Mami zata saki labule sai ta ja
ta tsaya jin mai gadi yana kokarin bude get, motar
Hajiya ce sirikarta, a cikin motar Hajiya ce da Aba
sai Hafsat da Uwani mai yi ma Hajiya aiki. Mami ta
yi ajiyar zuciya sannan a lokaci guda ta ja tsaki, em
kuma Hajiyar ke so a wannan lokaci, Allah ma ya
sawake ba za a bar mutun ya huta shi da mijinsa ba,
in ku mayu ne kunci kan ku; wannan itace maganar
da Mami ta rinka fadi a hili ita kadai a daki, ta shiga
kewayenta ta hada Sabulen wanka masu kamshin
gaske, ta soma sabule farar fatar ta sai da ta ji ta yifes kamshi ya ratsa fatar jikinta sannan ta tsane ta
fito, ta zauna gindin madubi tana ci gaba da 'yan
gogc-gogneta fatar Mami ta debi walkiya amarya dai
sosai, ta shafa farar hodar ta mai daukar hankali sait a
mike a yau rigar baccinta mai nauyi ta saka
zulunbuwa har kasa, ta jawo wani dan kwali ta kulle
kai ta yi niyyar zuwa falo ta gaida Hajiya, amma da
119
1
さ
ta tunoda wani irin kallo da take samu da ga Hajiyar
tunda aka gano ulcer a tare da Sahabi sai ta fasa
zuwa, tana jint soron hajiya sosai Hafsat ta rankwashi
kofar dakin Mami kamar sau daya tace Anti Mami
kin yi bacci ne? ta ce a'a ban yi ba, Hafsat ce, ta ce 'E
Hajiya na kiranki a falo. Mami ta fito zuwa falo, ta
zauna kusa da Hafsat, shi Sahabi ma zaune ya ke bisa
wata luntsumar darduma, madara ce a hannunsa yana
kurba.
Ta ce, sannunku Hajiya ya gida? Ta ce, lafiya, ga
Uwani nan na kawo mai min abinci zata zauna a nan
saboda girkin abinci, kan Mami a Sadde ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13