Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ka 'yan uwan, ko ma dai wata fitinas can da ban, kamar tun farko na ga ya ma yawaita addu'a zai kawo komi cikin natsuwa, kuma Allah ma na iya juyar da komi". Jikin Sahabi ya yi sanyi likis domin shi ada yana ta murna ne a fassarar ta shi da ya yi ma istaharar sh shi ne zai auri mami za su haifi wa'annan 'ya'ya da 14 u ek a S ur va sa m aub un yar ne ce lan ya fa ar ka ar a :e n T 日 t ya rinka gani a mafarkinsa, to ashe abun ba haka ba ne. Mallam Adamu ya ce, kada dai ka canza ra'ayi akan mami kaci gaba da zan cen ka, ko babu komi yanzu fa shekararka talatin Sahabi ya dace ka ajc iyali, addu'a zan ci gaba da saka cikin addu'a, kada ka yi wasa da gaya ma sarki Allah ka ji", Sahabi ya yi godiya ya mike ya kawo kudI sadaka ya baiwa mallam. Abunda ma ya dan razana Sahabi shi ne a mafarkinsa na karshe ganin yadda ya ke sakkowa daga bene tabbas ya dan ji bawai domin ba kasafai ake son sakkowa bene ba a mafarki lalle dole matsala ce, sai kawai ya ture duk wani tunani ya yi anfani da hudubar mallam Adamu, soyayyar mami ta natsu cikin ransa da gangar jikinsa, har baya zullumin shawo kanta, domin ya san a tun farkon haduwarsu ya soma tsinke mata jini ya lura da hakan ya kuma tabbataswa ransa, sai dai ya dan karance ta lalle za ta yi dan jan aji ko kuma miskila ce kawai? Ya tuno da samartakarsa da 'yan mata a Canada inda ya kwancewa wata yarinya baturiya jar fata sai har sai da ya raba ta da ainihin saurayinta wanda a kai mata baikon aure da shi, bayan a zahiri Sahabi ya san ba wai kaunar gaskiya ya ke mata ba iya ka kawai ayi samartaka. Yana zaune a falonsa shi kadai ya jawo remote ya rage karar T.V sannan cikin natsuwa ya rubutawa mami text cikin wayarta kamar haka: MAMI haduwa ta da ke a gidan ice cream ya haddasa man 15 canjin rayuwa saboda haka ni Sahabi Ahmad na ce kulle... Mami kwance ta ke a falo ita da Rannan mamanta su anti Zainab da anti Yesmin ga samarin gidan su nan zazzaune ana ta hirar duniya, kan mami na bisa cinyar anti Zainab sai text din Sahabi ta shigo G.S.M din mami ta dan yi fito alamun nunan an aiko da text tasa hannu ta dauko ta bude, gabanta ya bada ras, ganin sakon Sahabi ina ya sami nambar wayarta? Wannan ba shi ne abun tambayarta ba, ta mike tsam tana wata 'yar rawa tana rausaya ta ce, 'yan uwa sai da safe yau ina da abun yi wanda ya fi komi mahimmanci a rayiwata" ta haye sama a guje zuwa dakin baccinta, su Yasmin akai dariya Samaila ne yace, anti Zainab duk aji a kare bana kila mami ta sami wanda ya fi karfin ta kwana biyun nan bata da sukuni, in da hajiya na gida kila da ta matsa mata mun san ko wanene" yesmin ta ce mami ce fa! Me shegen zurfin cikin tsiya amma gaskiya wannan text din bata kawa ba ce kuma ba ta dan bawan Allah ba ce Sani", su Yakubu da Ibrahim su ka ce ina ma ruwan ku da mami ne, koma wanene in dai mami ce zata sanar da mu a falon nan sai kowa ya saba da shi". Ga amsar da ta baiwa Sahabi saboda ta riga ta galabaita don haka bata tsaya wani jan aji ba ta ce, "Mami Abduljalal ta amsa tayin ka ta ce CAS; wayar Sahabi ta bada wata 'yar jiniya ya yi sauri ya dauka ya duba ya yi harndala da amsa mami don haka sai kawai ya yi mata wayu sai da ta duba taga nambarsa 16 da a a a a 2 ce sannan dadi ya lullube ta ta dauka, gaisuwar cikin rudani aka rinka yin ta saboda wata irin soyayya mai zafi ce ta afka masu a lokaci daya. Ya kira sunanta cikin kasan makoshi "Mami" ta amsa a dan tsoracе domin tabbas bata iya fassarawa kan irin yanayin da Sahabi ya tsundumata, ta dai amince lalle maza suna suka tara, haka nan wato duk irin soyayyar da za ka yi a duniya soyayya dai daya ake, koma dai wanene Sahabi Ahmad ta amince shi kan sa Sahabin take so ba komi na sa ba ko na iyayensa. Daga can ya cc, na ji ki a sanyaye ko na matsa maki da surutu ne kina jin bacci? Ta ce "Bacci Sahabi ina tare da kai din? ya lunshe ido zuciyarsa tai mai gardI mami ta samu sai kuma me, sai addu'ar zaman lafiya, ya ce sunan mutumin na ki na gaskiya Abubakar amma in kin fi son Sahabin duk daya ne a gare ni domin ina son sunayen duka", ta yi wata irin dariya wadda ta burge Sahabi tamkar ya bude wayar ya rungumeta, ta ce wa zai kI Sahabi masoyi fa kenan? Gaskiya zan rinka dana kowanne zuciya ta ta raya man, sunayen duk sun yi min kyau," ya ce, ko dai me sunan" ta ce, "Gaba daya na amince" Sahabi ya dan yi murmushi ya ce, "Kai lucky me yau ni dai nayi sa'ar wannan rana ta wa ce ko kin san dama a wannan rana aka haife ni? Ta ce, laraba! Daman hausawa sun ce wai ranar samu kowa ya samu da ita zai kara samu," ya ce "Na yarda, na zo duniya ran laraba na sami amincewar my special one a yau laraba, ki kokari ki haifa mana bebi a ranar laraba mami, "ta yi sheshekar dariya, ta ce "tsoron haihuwa na ke ka yi hakuri da 17 wannan", ya ce, haba mami bebies ke kara dan kon kauna" idan ya ce, mami ta kan yi kamar ta yi tsuntsuwa ta hade shi gaskiya ya iya tsuma ta, ada ta yi alkawarin ita ba za ta haihu ba saboda yadda ta gani ta kuma karanto wahalar haihuwa amma yau maganarsu da Sahabi ji yake ko zata mutu sai ta yi mai abunda ya ke so," ya lunfasa ya ce, Ai ban faye zari ba mami yara biyu sun ishe mu mace da namiji", ta ce, "Wai lah! Sahabi zan baka litafin haihuwa ka karanta, Allah zaka tausaya man, koko a saukake zan so ka dubi tashar Reality T.V a tashoshin DSTV zaka ga haihuwa a zahirinta da wuya ka yadda na haihu",, ya kyalkyle da dariya, ya ce, kin faye ban dariya ga ki da saurin raki, idan zan baiwa Hajiyata labarinki a gobe har da rakin haihuwa zan sanar da ita", ta ce, "Don Allah Ab-kar kada ka ce ina tsoron haihuwa in tace ka canza ra'ayi fa! Ya ce, haba my dear no way, babu mai iya raba ni da ke sai Allah, ita Hajiyarmu ba haka take ba, ta amince da so don haka ba ta cika katsalandam ba a al'amuran auren mutane sai dai ta yi kyakyawar addu'a", wayarsa ta soma 'yar kara alamun kati zai kare hirarsu ta daren farko ta ci naira dubu kusan biyar yace, mami ki dan jira ni zan saka kati zan sake kiranki yanzu", ta ce ko ka bari ni na kira ka, mana", ya ce "Haba Hajiyata yau ni ke neman aure dole ni za'a caza", layi ya yanke, ya dauko kati ya zuba sannan ya duba agogo karfe daya ta shige ya sake nemanta a layi, ya cc, mami ya dace mu kwanta gaba daya muna zuwa ofis gobe ko? Ta lumshe ido ta ce, yadda mai gida ya ce ai haka za'a yi 18 1 1 1 1 " ko? Ya ce, wai wannan amarya tawa da wayau take! Ta amsa ko! Cikin sati daya gidansu mami an gano an kuma san ko su waye iyalan marigayi Dr. Ahmad Shu'aib ya yin da dan lokaci gaba daya family din su Sahabi an san mami 'yar gidan M.D Abduljalal su anti Hadiza anti Sa'adiya da sauran kannen Sahabi ana zaunc a falon hajiya Aisha mahaifiyar su, ko wanne ya zubawa hotan mami Abduljalal ido, anti Hadiza ce ta soma sharhi kan mami ta ce, ai ni na san Sahabi son komi na sa ya zama daban dole ya auro mace mai kyau irin wannan", aka bushe da dariya Sa'adiya ta ce "Ai ni zalkin son da take nuna masa har tsoro take ban, shekaranjiya sun je wajena da ita, na ce, mami yaushe ne bikin na mu ne", ta ce, Sahabi za'a tambaya", wannan zan ce ya yi ma hajiya Aisha dadl domin ita dai tana son mai son na ta, ya yi murmushi ta ce, ai sai ku shirya cikin satin nan mu je gidansu mamin mu gaisa da iyayenta. Anti Hadiza da Sa'adiya sun zo da kwalebani turaruka har kwalba shidda designers masu tsadar gaske da set din rigunan bacci da undis, Hajiya Aisha ta yi murmushi ta ce, shikenan ni sai na huta ba sai na kai ma matar ta ku komi ba", gaba daya suka ce a'ah Hajiya ba mu yadda ba ai na ki da ban". Kwana biyu Mami na sanar da kowa cikin gidan har masu gadi cewa uwar mijinta da dangin mijinta zasu zo. Duk da Hajiya iyana bata nan amma ta bar sallahu ayi masu kyakyawar maraba saboda dai ko ba komi Mami ce babbar diya a gidan. 19 R Tun isar su Hajiya gidan M.D Abuduljalal su Zainab da 'yan aiki suka rinka dawainiya da su, su kawo wannan su dauke wannan hatta itama uwar gayyar Mami tana manne da su kamar zata kwanta masu, abu daya ya yi ma Hajiya Aisha cikas wato suturar da Mami ta saka irin wandon nan da riga matsattsu tsantsan wato hugs bakake wuluk ta rinka karairaya kamar macijiya duk surorinta a bayyane su ke, amma sai Hajiya Aisha ta rinka rayama ranta dan Hajiya iyana bata gida ne shi yasa Mami ta yi wannan shirmen dressing me zai faru? Mami ta mike tamkar tarwada ta kamo hannun Hafsat ta ce, Hajiya ku zo mu je falon Baba yana jiranku za ku gaisa. A falon M.D Abduljalal gaba daya su anti Hadiza da kannanta a bisa kafet su ka zauna illa Hajiya Aisha da ta zauna kujerar da ke saitin Alhajin, yayin da ita kuwa gimbiyar Mami ta je ta nade cikin jikin mahaifinta shi ma ya rungume ta yana shafar gashinta tankar 'yar shekara biyu. Bayana 'yan hirarraki da ban dariya da suka rinka gudana a tsakanin family biyu da suka zaku da dokin jin dadin za'a kulla dan kon zumunta mai karfi ta fannin auratayya. Can Alh. Abduljalal ya shafi kan Mami yana mai kallon Hajiya Aisha dauke da murmushi a fuskarsa ya ce wallahi kwarai na yi murna da samun Sahabi a matsayin daya daga cikin sirikai na domin na yi mai intabiyu ya dace kwarai da ra'ayi na, haka nan kullun sai na shi ma Mami albarka da ta kawo man al'umar Sokoto da Birnin Kebbi za su zama jini na," gaba daya falon aka yi 20 'yar dariyar girmamawa Hajiya Aisha ce ta ce, Alhaji mu 'yan Sokoto da Kebbi da ban mu ke da sauran jinsin mazan da ke sauran jihohi? Alhaji ya yi dariya ya ce, Bana so wannan maganar ta yi nisa a tsakanin mu saboda tamkar na tsakalo magana ne, kowanne mutun na duniya akwai baiwar da Allah yayi mashi, amma a zahiri in mace na son ta more mijin aure farko ta auri mutumin Kebbi ko dan Sokoto tabbas sun san hakkin mace, amma son kai ya fi, anan sai in ce a duniya babu kamar mutumin Maiduguri aka bushe da dariya, Hajiya Aisha ta ce, "Eh lalle wannan magana akwai son kai duniya gaba daya? Alhaji ya ce, "To madallah na gode kwarai, kwarai, idan mun yi waya da Hajiya an jima zan sanar da ita kun zo, kuma abunda ido na ya nuna man Mami zata fada hannun zuri'a ta gari, Allah yasa albarka a shirya mu yi addu'a" sai a wannan lokacin ne da aka soma addu'a Mami ta bar jikin mahaifinta ta zauna kasa ta lankwashe. Ya kawo addu'o'c masu na garta yana karantowa suna amsawa amin, suka fito ana jin dadl Aisha 'yar auta itace ta debo kayan su anti Hadiza ta baiwa Mami yayin da Hajiya Aisha ta umarci yasmin ta nemo namiji ya fiddo kaya a but, wato katon shidda na swan water katan shidda na five alive yayin da shi ma Alhaji Abduljalal ya baiwa Mami dubu hamsin ya ce ta baiwa su Hafsa da Aisha. Bayan sun dawo gida sun iske Sahabi zaune a falo yana jiran zuwan su, Hajiyarsa dai bata nuna mai komi ba a fuskar ta ya ji dadin haka a zatonsa Hajiyar ta yaba da komi, amma kuma ganin ta kI zama ayi 21 ; hira lokacin sallar mangarib bai yi ba amma ta shige ta yo alwala tana zaune bisa sallayarta tana ta wuridi, tabbas yasan akwai abunda Hajiyar bata so tare da Mami, domin halayyarta kenan in abu bai mata ba sai ta ga ya ma Allah. Abu daya yasa Hajiyar ta kyale Sahabi game da Mami shi ne tun farko mallam Adamu ya zo a asirce sun yi binciken su kan iyayenta lalle Abduljalal ya samu shaida mai kyau an ya bi halin sa domin hatta karatun islam da sallar da su Mami su ka iya ance shi ke tsare su yana koya masu, 'yar kwaba da uwa ta dace ace ita ke yi to a gidan su Mami shi ne mai yi, haka nan duk irin sangartar da akai ma su Mami a gidansu sa'a daya Abduljalal yayi ba su cikin group din 'yan matan kaduna masu shaye - shayen banza da sace - sace ga shegiyar karya ta ba gaira ba sabar sannan duk wani iyar shege da da namiji zai yi suma wa'annan 'yan matan na gaba, batun ma karatu wannan ma ba nasu ne sai karyar zuwa makaranta kullun amma ba karatun ba ne. ita dai H. Aisha ta sinsino akwai wata rashin tarbiya da bata dace da zuri'ar ta ba, amma dai ba komi ta san halin Sahabi namijin duniya ne zai fi karfin iyalinsa insha Allah. Sahabi ya dubi 'yan uwansa ya ce, Anti Hadiza yaya na ga Hajiyar ta mu kamar da matsala? Ta yj murmushi ta ce, "a'a kada ka damu sun yi murna da mu sosai, kasan Hajiya dai, ina ganin dressing din mamin ne, to yaran yanzu yana da wuya ka hana su saka irin wa'annan kayan", Sahabi ya ce, kin san Allah bata fitowa waje a irin haka sai ta dora 22 jallabiya a gida kafai ta kan sanya, Allah Mami na da tarbiya anti. *** *** Haduwar Mami da Sahabi kwata kwata wata shidda su ka yi amma sun amincewa rayikansu daya bai iya rayiwa sai da dan uwansa, sun kagu kwarai a mallakawa kawunansu junansu, ta ka'idar musulunci, duk wani aboki da Sahabi ke ji da shi ya kai shi ya ga Mami sun kuma yaba, kowa ya kan ce gaskiya kun yi mugun (Marching) wato sun dace a takaice abokin Sahabi daya ne yace, "wai lalle ka isa asaka a news line a yi hira da kai domin nasha jin labarin Mami ta wulakanta maza masu son ta, amma kai haka gaba daya ta mato kan ka tamkar ta hade ka, ban yadda ba 'yan Sokoton nan kuna da lakani" suka bushi da dariya. Ita ko bangaran kawayen Mami akwai lokacin da Mami ta rinka tuka Sahabi a motar suna yawo da wani marecen lahadi a karshe suka tsaya wajen shan lemo anan ne suka hadu da kawarta Jamila Idris suka dan kebe wajen motar Jamila shi ne Jamilan ta ce, Gaskiya gaskiya you are a lucky girl, ke yarinya ce mai sa'a domin addu'ar 'yan matan gidanmu itace mu auri miji daga Sokoto ko Birnin Kebbi, sai muka ji maryam Bishir ta ce mana ke kin samu tsantsa, don Allah dubarsa ga tsayi ga mutunci ba irin samarin garin nan ba yawanci shashashshu Mami ta kara lumshe ido ta rungume kafadar Jamila ta ce, "Wallahi 23 Jamila Ab-kar yana da mutunci kwarai ni ban taba saurayi mai kunya da tsoron Allah irin sa ba in kin ga Sahabi ya saki jiki sosai da ni to yana aiko man da text ne a waya a kullun darc sai na farka na nemo text din sa na karanta raina yayi man dadI" Jamila tacc, "Ki rike sa ki kuma kula da shi da kyau irin su sun yi Karanci, sannan ga tsada! Gaba daya suka kyalkyalc da dariya ta ce kin ya ba da rabin raina insha Allah zan kawo shi har gida ya gaida mutan gidanku". A kwai wani darc agogo ya nuna karfe uku na sulushin dare, Mami ta kasa bacci, domin Sahabi yayi tafiya Sokoto shi da su Hajiya yau kwana biyu ba su tare sau daya ma su kai magana a waya, domin G.S.M bata isa can Sokoto ba don haka babu damar aiko da text ita kuwa tafi jin dadin ganin text din sa domin yana rubuto mata abubuwan da ke fasa mata kai yana tsinke mata jijiyoyi. Ta ja tsaki ta jawo G.S.M din ta ta rinka dawo da irin text din da ya aiko mata a baya tana jin sanyi a ran ta ga irin su: - Mami morning greetings does'nt simply means good morning it silently says that I thought of you when I woke up, hope you're okey. Anan ta tsaya ta yi shiru tana tunanin cewa lalle irin so daya sukewa junansu ita da Sahabi ta kara budo wani text din inda ya ke cewa: - Mami you know what? I did three things today, I miss you, I miss you and you know what am doing right now am missing you: Randa ya aiko mata da wannan text ta yi dariya sosai kamar yadda yanzu ma da ta dawo da shi bayan 24 sai ta rinka kyalkyatar dariyar ita kadai a daki, ta sake dawo da wanda yayo mata a daren da zai yi tafiya, tafi son wannan text fiye da kowanne, wato Goodnight Mami I sent two angels to look over you, but they all came back and said angels don't look over angels. Jin dadin wa'annan text yasa Mami bacci mai nauyi. Wan shekare ya kama lahadi su Sahabi suka dawo a motar Hajiyar ne da kanwar mahaifinsu gwoggo Inno da anti Hadiza da Sa'adiya da direba a motar Sahabi su Aisha ne da Hafsa sai Abba, yana isowa dai dai A.B.U Zariya daga nan G.S.M ta soma aiki ya tsaida motarsa ya aikawa da Mami text, sannan ya ci gaba da tukI, ga abunda ya rubuta. Mami someone told me that hrs is 365 day, one week is 7 days 1hr is 60 mins but no one told me that one second without you is eternity. Text din ya sami Mami a lokacin tana tare da Hajiyarta ta zaunar da Mami tana lissafa abubuwan da take so Kawata mata gida da su, ganin sakon Sahabi yasa Mami ta kwalla kara ta ce, Iyana ki yi hakuri oga na na bisa hanya ba zan iya ci gaba da lissafi ba. Ta dauki G.S.M din ta tana tsatsalla kafafu ta shige daki abin ta. Iko sai Allah! In ji Iyana. Su kadai suka san yadda suke ji da junansu a rai, don haka ko da iyayen sahabi suka zo daga Sokoto da karfinsu suka je neman aure, aka ce ana son su je maiduguri ba su bata lokaci ba suka je da murnar su da jin dadinsu, suna fadin ko bayan duniya aka ce 25 mujc idan har ana zuwa ai dole muje, wanda zai baka gudan jini! Ai ya fi ka har abada. Duk abubuwan al'adun 'yan maiduguri babu wanda ya gagari iyayen Sahabi duk sun yi. To meke faruwa ne, ga shi dai tafi kowa murnar acc Sahabi ya yo mata text amma sai muka ji Sahabin cikin rudani da rashin ganin amsar Mami amma dai ta ce tana son ganinsa bayan sallar issha'i, saboda haka bara mu bi shi muji me ke faruwa ba dai aurcn Mami zata rushe ba ko, kamar yadda tasa aka rushe mata baikon baya? Ya koma gida ya shirya tsab cikin kananan kaya farare sal sai dan ratsin baki, turaren da Mami tasa iyana ta sawo mai ci Dubai ya shafa kadan, bai ji dadin yadda Mami ta taryesa ba domin ta zuba wata shadda ganilah mai maikon tsanwa suduf siket da riga ta dinka, a gaskiya ko ba a idon sahabi ba a idon kowa ma Mami na kyau da komi, amma a yau matsalar daya ce wato fuskar Mami ta yi fari sol idanunta sun kara girma, saboda rashin gyara ta, ta zauna a daidai kusa da kujerar da Sahabi ya zauna, ta ce, Abkar ina gajiya? Ya ce, Babu ta sake cewa me kake so na sanarwa Anti Zainab? Yace, for goodness ke Mami me ke faruwa ne yaya za ki fito man haka tamkar kin yi kuka, sannan ki daman da cewa mc na ke so zan ci idan ma har na zo da yinwa a yau kam na hakura ni ki gaya man abunda ke damunki". Ta dan sadda kai Kasa na dan lokaci sannan ta dago suka kulle kwayar idanunsu hudu na lokaci kila sakan uku sannan ta nisa, ta ec Ab-kar me ke damun 26 mu ne mutancn yanzu a gani na mun fi mutanen da ilmi mun fi su jin dadl domin Allah ya kawo mu zamani na ci gaba, haka nan mun fi su, to amma me yasa suka fi mu kwanciyar. hankali? Haka nan yanzu za a kulla soyayya mai tsanani har daya bai iya rabuwa da dayansa ga dukiyar ga hutun ga ilmin amma kuma ba kwanciyar hankali why! Ka san abunda yasa yau wuni na yi ina tunanin wa'annan tambayoyin amma wallahi Sahabi na rasa amsa, abinda ya jawo man tunanin shi ne na sha ba ka labarin 'yar uwata Rabi'a wadda ke auren Ali dan nan Kaduna ne amma yana aiki a Nigerian Embassy can London, duka duka shekara daya kenan da yin aurensu, wallahi Sahabi lokacin da Ali ya soma kyalla idonsa akan Rabi'a kai kace baya da sauran rayiwar kan sa a duniya, ya so Rabi'a son da ban taba gani ba sai ko kai na da kai, yarda mu ke kusan kwana bisa waya su ma haka suke yi, tunda su kai aure sun fi sati ba su yadda kowa ya san inda suke ba, amma wallahi bayan wata biu da na saka su a ido tamkar a rannan Ali ya soma ganin Rabi'a son nan na nan. Me kuma zai faru akwai lokacin da Rabi'a ta zo Nigeria daga London, amma saboda tsabar soyayya sai Rabi'a ta kasa yin kwanakin da ta ce zata yi nan da nan ta shirya ta koma wajen Ali me zai faru ta isa gidansu Ali na ofis amma abinda ta gani shi ne ma farin rikicewar gidansu, wato rigar nonon budurwarsa ta gani a dakin baccinsu, to ka ji sanadiyar rushewar gidan Rabi'a da Ali, sun fi wata hudu ba zaman lafiya, shi ne a daren jiya ya bugo ma Iyana waya wai 27 ya basu notice na awa goma sha biyu su aika gidansa na nan kaduna a kwashe kayan Rabi'a in ko ba su aika ba zai ba masu gadinsa umarnin su fiddo mata kayan ta bisa titi saboda ya saki Rabl'a saki uku". Sahabi ya dan muskuta ya gyara zama ya fuskanci Mami sosai cikin natsuwa da kamewa ya ce, amma Mami kin so ki ban kunya, ashe akwai wa'anda za ki iya hada su da mu? Look! Abunda na ke son ki gane, duk rayiwar da ki ka ga tangarda ta yi tasiri to wallahi an bar dokar Allah, tabbas za mu iya samun kan mu cikin bala'i fiye da na su Rabi'a duk ko irin son da mu ke ma juna wato idan na zamanto mai cin amanarki ko kuma kin zamantoi mai cin amanata, kinga abu biyun nan sune amsar tambayoyinki cin amanar aure da kuma barin dokar ubangiji fakat! Mami ina son tun yanzu ki fahince ni akan irin hali na, ba wai alfahari ba amma bana jin zan iya zama mai cin amanar mata ta, sannan kuma matar da nake so fiye da kowacce irin mace a duniya, a gaskiya Mami zamu shirya rayuwa wadda babu mai sanin sirrin mu daga ni sai ke haka nana ba wai irin rayuwar nan za mu yi ba ta yaudarar juna ba a'a rayuwa irin dai wadda manzo ya zo mana da ita. Har abada ni Mami ba zan sakarwa kowa zuciyata ba sai ke, balle wai har na baiwa wata kai na, kuma a gidan da yazan na mu ne na raya sunar manzo, don haka ki saki ran ki, in don ni Sahabi ki yi ma sauran mata rantsuwa kin auri salihi tsantsa, komi ma ya faru ki yi kuka da kan ki amma ba ni ba". 28 Mami ta rintse ido tuni Sahabi ya gama mata komi ta amince da shi 100% yadda aka wuni yau ana fallasar halayyar maza, ita yanzu ji take lalle zata iya rantsuwa nata da ban ne wato Sahabi kenan. Mami ta debe kafafunta ta dora bjsa kujerar da takc zaune ta nade gaba faya, akoda yaushe daman irin zaman Mami, kenan amma ban da in ta je aiki ofis, ta noke fuskarta a kafadu tana irin murmushin nan na jin kunya ka yi ma masoyi laihi shi ma yayi murmushi ya cc, "Kin gamsu da bayanai na ko? Ta cc, "Wallahi na amince" ya ce, Na gode, ina son ki yi magana akawo man ti, mami ta mike cike da yaukl zuwa falon da su anti zainab su ke, yayin da Sahabi ya bi ta da ido yana kallo, shi dai koma menene yana dai son Mami komi na ta kuma yana birgesa har yana ganin ta, a ganinsa zai iya yafe mata komi ta yi masa sannan ya ci gaba da son ta. Mami ta dawo ta zauna ya ce, you are a very lazy woman ke dai raguwace tin ma ba kya iya daukowa sai kin bada umarni a kawo ma mijinki! Lalle zan sha shagwaba" ta ce, Ai lalle gara ma ka saba, kai kuma ga mulki na lura" ya kyalkyale da dariya ya cc, "Kin sani ko sarki za ki aura! Ta amsa caf dijam! Kar kasa nace na fasa, ina zan iya zama da kai kullum kana can fada tare da fadawa, sannan cikin gida mata hudu ne ko biyar sai na yi kwanaki kafin na samu sakewa da kai, ai bana iya irin wannan

Chapter 2 of 13