Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cé, 'To Hajiya sai Hajiyar tace, Uwani shiga daki, tashi Hafsat raka ta dakin da kika zauna a nan zata zauna, bayan su fita daga Hajiya sai Sahabi da Mami a falon hajiya tace, Duk wani shirme Mami da kuke zartas wa a gidan nan ina son a daina matsalar rashin girki kinga in da ta kai mijinki,w annan kuma duk mai sauki ne, irinw anan rashin kular tafi illa ga yara Kanana yanzu idan da Allah ya ba ku rabo da wuri haka zaki ki kula da yaran ki bar wa su Kiristi 'yan aiki sune abincinsu sune kula da ciwonsa sune komi nasa har tarbiya ta zo 'yan aiki za su ba 'ya'yanki tarbiya, Mami wannan ba rayiwa bacc, idan za kj, canza to idan ko ba canji ba zan dauki sashanci ba. Aure mami amanar Allah ce, ke amanar Sahabi ce shi ma amanar ki ne, daidai da sakan dayanku ya zalunci daya Allah f aba zai kyale sa ba, to me ke damun ki aurcn so ku ka yi fa Mami? Na yi zaton kafi kula da abinda ka ke so? 120 To ga dai Uwani nan na kawo duk yadda na ke ma iyalai na girki tare da ita na ke yi,s aboda haka ta san komi ta iya komi, dole ta sa ido akan Sahabi domin ciwon da ya same sa mai son kula ne. Ina baki shawara ko in ce ina son Mami ki samarwa kanki kykakyawar tarbiya, domin wallahi sai an sami tarbiya ta gari sannan ake samun kwanciyar hankali har a sami ci gaban zama bazan taba so a ce gidan sahabi ya rushe ba, kullun ci gaban zamana ke so amma ba ci baya ba, ina fatan za ki amince da abinda na shirya maki. Bayan Hajiya ta dade da yin shiru Mami ta daga kai a hankali wanda ta fara kallo Sahabi, t alura babu komi a ransa illa farin ciki sai kuma haushi ya kama ta wato shi dan gata! In haka ne itama ai 'yar gatance idan har so ake a gaya masa gaskiya me zai hana a kira lyana, sannan Hajiyar ta yi wa'anan maganganun. Shi mai uwa a bakin murhu ko? Ta juya ta dubi Hajiyar tace, shikenan ko Hajiya? Hajiyar ta dubi tsabar idon Mami lalle yarinyar na da masifar kyau amma dai bata da tarbiya, ta mike ta koma daki abin ta. Hajiya ta ce, Sahabi tun farko ka zamanto bawa ga yarinyar nan, tabbas yanzu ina tausaya maka, an ya ma kuwa kana da daraja a idon yarinyar nan? Ina gargadinka, ka koma hanyar Ubangiji, ina kana nemawa 'ya'yanka tarbiya ta gari". Sahabi ya ce, ina iya kar kula ta Hajiya amma insha Allah zan ci gaba ta mike ta kwallawa Hafsat kira shi daman Abba na cikin mota yana jin kida. 121 Sahabi ya mike Uwaní ta dawo raka su Hajiya, Sahabi ya kira ta yace ta zot a kwashe kaya a falo, shi ko ya je ya yi wanka don ya kara jin karfi domin Rafafunsa suna yi mai nauyi da rashin karfi. Ya shiga dakin mami ya ce, Mami kin yi bacci ne? kamar ta ga ya mai bakas amma har yanzu tana tausayinsa saboda rashin lafiyarsa domin ta san baig ama wartsakewa ba, sai ta ce, Haba ya za'ai na yi bacci bayan baka kwanta ba, ya yi dan murmushi ya je kusa da ita ya kwanta, suka kudundune juna ba don komi ba sai don kulawa, amma zukatansu cike da tunane-tunane. Kwana daya kwana biyu a ranar kwana ta uku, Uwani ta kai matukar kule Mami, domin abinda dangin mami da mami su ke cewa, Hajiya ta kawo Uwani a jami'ar tsaro wadda in mamit a zo sakawa sahabi guba Uwani za tai gaggawar karewa, saboda tsananin kulawa duk wani surutun 'yan uwan mami yanzu takai bata sauraronsu,t ana dai jiran Iyana ta dawo daga Abuja ne ayi wadda za'ayi. Zuri'ar sahabi da Uwani sun hana Mami zartas da komi tamkar ba Sahabin t aba, kuma ba gidanta ba wa'anda ta saba iko da su. A yau ma dai Sahabi ya sanar da ita baki da baki yana da isassar lafiya, don haka sai ta shifya, amma ita duk wanan ba shi ne gaban ta ba, abinda ke tayas mata da hankali ya fi gaban lissafi, mahaifinta Abduljalal yana gari amma bata sha'awar ko kadan ta kai mai korafin damwuarta domin ta san mutun ne mai son abu komi filla-filla in ta dauro yana iya bin 122 bayan su Hajiya, kuma ma bata tat ganin wanda ya ke so ba tamkar Sahabi. Sahabi ya riga ta zuwa shinfidar su a yau, mami ta je ta zauna a bakin gado ta zuba fuskarta a tafunan hannayneta, ta yi shiru, a zaton sahabi ya dauka Mami addu'a take yi, don haka ya saka mata ido kawai. Tsayin lokacis annan ta sauke hannayenta ta ratsa daya tsakanin Sahabi ta zuba mai ido, ta cikin (dim light) ya hangi kyallin hawayncta, ta kawo ajiyar zuci cikin kuka, a lokacin tace, Sahabi I'm leaving! ya kwalo ido domin ya dan rame ya ce, me ki ke nufi ina za ki?t ace, Dole ne mana zan bar ka, zan kuma bar maka gidanka! Ya ce, A wane dalilin? Ta ce, Sahabi ni fa yanzu a matsayin guba na ke a gidan nan, to na zauna na ci gaba da halaka ka, ya daga mata hannu ya ce, look Mami duk abinda ke gudana tsakaninki da 'yan uwana da na ki 'yan uwan ina kallo, ban ga dalilinw annan ruda ni ba, ni dai na yi imani Ubangiji Allah shi ya aiko man da ulcer ke muna tarc da ke ko ban tare da ke wannan dole ne, laifinki daya a wajena Mami shine ba kya tattalina kamar yadda kowacce macen kwarai ke ma mijinta, kuma a zahiri wallahi ba kowanne dan uwa zai ji dadi ba yaga dan uwansa a wulakance, kamar yadda dangin kowacce diya mace ba za su ji dadi ba suga miji na wulakanta 'yar uwarsu, shi yasa na yi iyakar kokarina naga cewa kai na da ke hade ya ke, don gudun irin wannan 6acin rai, na shaida maki I love you, I need you and I want to be with you for the rest of my life, to bayan wannan me ki ke so na ce ma ki 123 Mami? A nan ta langa6e, kukan ya ci gaba da zuwa mata shar-shar, ita a son ranta ya kori Uwanit abas su Anti Zainab sun ce za su kawo masu mai girkin Iyana ta rinka masu abinci. Sahabi ya biya bukatarsa son ran sa ba tare da takura ba ko alama, sannan ya rungume matars aya soma sharara baccinsa cike da nishadi, sai dai ita Mami ba baccin take yi ba, hanyar da za samu a korar mata Uwani kawai take nema, babu ma dalilin da zai sa ta hakura da gwarzon miji tankar Sahabi, ta san tana murza shi son ranta amma shigowar su Hajiya cikin al'amuranta ba karamin batanci ba ne. Yau kwana goma sha uku da sallamar Sahabi daga asibiti sauki kam ya samu, bayan haka har ma ya yi wani dan haske na alamun samun lafiya Mami ta dawo aiki ta fito daga motarta tana rufewa, wayarta GSM ta soma karar jiniya, ta fiddo daga cikin jaka ta latsa Hello Mami ce! Iyana ta ce, 'sannu Mami kuna lafiya ya jikin mijin na ki? Ta ce, lah! Iyana lafiya lau kina ina wallahi ina son ganinki Iyana, tace, sauka ta kenan ina gida, me ke faruw ana soma jin zance barkatai wajen su Zainab Mami na rike da hannun motarta ta juya ta dubi harabar gidansu babu kowa sai maigadi daga waje, tace wallahi Iyana an yi sake duk zuri'ar mijina sun jagula man lissafi yanzu sam Sahabi ya fi sauraron 'yan uwanshi da ni, amma dai har yanzu bai soma wulakanta ni ba, sai dai 'yan uwansa sun fi ni iya komi a gidan nan. Iayana ta yi shiru tace, Maganar ta isa haka nan ki saurari sako an jima ta hannun Zainab, ta ce, Tо, 124 suka yi sallama ta rufe wayar, ta shiga gida, Zainab ta kawo sako da yamma ta ce, Iyana ta ce Ga wannan ki/ yi duk yadda za ki yi Sahabi ya ci a cikinsa, wannan kuma ko ki shafa masa a jiki ko a ruwan wankansa. Mami ta yi shirut ace, Amma fa da wuya yadda wannan muguwar Uwanin ke tsaye kan sahabi ba ni da halin bashi komi, Anti Zainab ta ce, you should try mana; tace, zan jarraba amma dai..... Duk iya kar kokarin Mami babu maganin da ta samu ta jaraba akan Sahabi, ita kuwa Iyana duk Malaman da take hulda da su ta aika masu sun kuma bada sakonni, amma sakonni sun ki shiga cikin Sahabi. Yau sahabi a guje ya shigo gidan, kasancewar. kuma jumma'a ya kira Mami ta zo da sauri tana son jin bayanin, ya mika mata wata zungureriyar takarda, ta zauna a masangalin kujera tana karantawa, ta dafe Kirji ta ce, Tafdijan! Oil Company Ab-kar! Ya ce, Ga shinan fa, kin san na dade ina son aikin nan, wallahi tun kafin mu yi aure na ke rubuta masu sai bana Allah ya ci she ni, ta yi murmushi itama dadi ya cika mata rai tace, gaskiya na yi farin ciki!" Yanzu suna nemana a Rivers a Babar Hedkwatarsu Part-Harcourt, ta lumshe ido tace, ba dai can za ka zauna ba ko? Ya ce, Ina kuma na sani saí na je na gani, idan can ne mnee ne? Ya dube ta yana lunshe ido, ta yi murmushi ta ce, yanzu shikenan sai ka tafi ka bar ni Ab-Kar? Ya ce, ikon Allah ashe rigima zamu yi ba kya son mu cigąba Mami, ko ko barin na ki aikin za ki yi? Та се 125 Σ haba wasa na ke maka, kawai ga fa jirgi ga waya ga motoci me zai matsa mana. Amma cikin ran Mami wanan itace hanyar wargajewar shirin dangin mijinta, kai gara da Allah ya kawo wannan aikin a daidai wannan lokaci komi ma ya tarwatse ta huta. Dangin Sahabi kaf uwa da Uba sun yi farin ciki da samun ci gabansa. Sun yi shawara da Hajiyar sa Uwani ta dawo gida domin zaman su ba zai yi tasiri ba da Mami. A daren Lahadi daren da Sahabi zai yi tafiya, abokansa da dama sun hallara har Mami ta ji zafin zuwansu domin sun hana mata sakat tana son sakewa ta ji dadin yin sallama da shi. Sun dauki lokaci mai tsayi suna hira Sahabi da abokanansa, ba su rabu ba sai karfe daya saura na dare, bayan ya yi masu rakiya, ya dan tsaya ya baiwa maigadi salallahu, ya kebe gefe daya da Ya'u shi ma wasu sakonnin ya ke bashi, har tsayin wannan lokacin Uwani na nan kicin ta zaman jiran ta bashi madara kamar jariri, ya yi 'yar dariya ya ce, in da madara da wani abu kika hada man ba zan iya sha ba to don dai madaran ce, zan taimaka na sha, ma ita ta yi 'yar dariyar ta ce, to mu kwan lafiya yallabai yace Allah yasa na fa gode kwarai da gaske Allah ya bar zumunci Uwani irin wannan yawan godiyar da ya kan yi ma 'yan aiki yana bata ran Mami, sai ta ga yana zubar da martabarsu. Ya yi addu'o'in rufe gida ya kuma rufen sannan ya kutsa kai dakin Mami abin mamakinsa tana zaune bisa doguwar kujerarta wato 126 irin (lazyman chair) ga hasken wutar lantarki kwanyar rike da katon novel a hannunta, ta jima tana karatun littafin amma bata fahinci labari daya ba, saboda tsananin damuwa da tasa kan abokan mijinta ba damuwa akan tafiyar mijin na ta ba. Ya tsugunna gabanta, ya ce, ina tuba sarauniya tace, ka damu da zaman jira na, wa'anda su ka fi ni sun dauke hankalin ka gaba daya; ya ce, Ni ke na kan ji kai na ya yi man gingirin idan kin fadi maganganunki akai tsaye yanzu ke kina iya barin kawayneki idan sun zo gare ki! Don Allah ki rinka tunani kan al'amuran duniya; Ya mikar da hannu ya amshi litafin ya rufe ya aje kusa da kafafunta, ya rike hannunta dukka biyun yana wasa da tafin hannunta tare da yawan tsura mata ido fuskarsa cike da fara'a ita din ma ta manta da komi sai tsananin nishadi a tare da ita. Ya mike ya zauna kusa da ita, ta ja 'yar farar singiletin da ke jikinsa ta ce, duk f ayau da rigar nan ka yini a jikinka, ba ka ko jin ka yi tsirarci, ya kyalkyale da dariya ya fada bisa jikinta, ya ce me ki ka ce? Tace, Ni don Allah daga man jiki kada ka karya ni, ka gudu Rivers ka bar ni da jinya, komi nace ai kunnenka ya ji ya ce, Mami kamar so ki ke ki tsani Rivers din nan, kin dai san halin mijinki Mallam ne babu masha'ar da zan gani ta burgeni face in hanyar Allah ne. Bana tsoronka a Rivers, kasan abinda ya ban takaici yan gidanmu ne, suka tsorata ni a yau da suka shigo daki, suka ce man wai shi Sahabi yau haka zai yini d asingileti da dan gajeren wando bayan duk cinyoyinsa gargasa ne? ko yana tsammanin ku kadai 127 ne a gidan? To bana so ka saki jiki da irin wannan al'adar a gurin mutane, kasan dai Rivers kasar inyamirai ce: ya yi murmushi, ya lakuci bakin Mami da dogon yatsansa ta yi kokari ta kai ma yatsan cizo ya goce hannun shi bisa dogon wuyanta ya jawo ta ya soma rada mata irin zancensu wanda su biyu kadai ya dace su yi, sun fi awa daya zaune a kujera suna aiwatas da love makin mai tsabta kafin su mike ko kо Sahabi ya mike da Mami bisa kafadarasa. Asubar farko Mamice ta soma son tashi, Sahabi ya zuba mata ido ta hasken da ke shigowa daga taga yace, Mami ina zaki? Baka sauraron Kiran sallah ne ko so ka ke ka makara? In ji Mami, yace na gode da hakurin da ki kai da ni a daren yau harki ka hakura da bacci: ta ce kar ka damú wanna na cikin abinda ba za mu taба mantawa ba a tarihin rayuwar auren mu;. karfe shidda Sahabi ne zaune a mota sun doshi Rivers ga kayan abinci nan kala-kala Uwani ta shirya masa, mahaifiyarsa da yan'uwansa da Uwani har ma da abokan sa sun kyautata masa, itama Mamin mai yawan bata masa a daren jiya ta yi mai abubuwa da bai iya gusar da su daga ransa sai dai kuma ya yi alkawari zai dauki lokaci bai zo Kaduna ba, don ya sami isasshen lokaci ya fahimci aikinsa haka nan ya baiwa Mami lokaci ta yi nazari a kan rayuwar aurensu. Satinsa biyu kacal da tafiya Mami ta soma yi mai korafi gidan ya kan yi mata girma idan dare yayi ta waya kenan ya kan bata amsa me zai hana ki dawo da Uwani ta rinka taya ki kwana? Idonta a rufe fuskarta 128 a tsuke ta bashi amsa da cewa, ALLAH shi rufan asiri in don haka ne me kannena sukeyi? Ya ce, ni wallahi da za ki birge ni, ki kuma kayatar da ni da sai ki koma gidanmu wajen Hajiyata ki zauna a can har na dawo, gidan mu kuwa abar wa kiristi da su Ya'u, ta wannan hanyar ne kadai nake ganin za ku yi kyakyawar fahimta da su Hajiyar mu kuma wallahi Mami ki ka gane halayyar 'yan Uwana sai kin mayas da su 'yan Uwanki na Uwa daya Uba daya tayi niyyar jan tsaki amma ta fasa domin ta tuno da gargadin da ya yi mata, tace, ina dai da niyyar tambayar ka ni kam zan koma gidanmu sai ka zo, amma ni ba zan iya zama gidankuba, dama dai tare da kai ne: yaji zafi shima yace, ban yadda ba domin ni ba irin wa'anna sakarkarun mazan ban ne, ba amince ba; ta sha mur tace, lah!lah!! Sahabi menene kuma na son yin zagi don na ce ina son komawa gidan mu, ni fa na fara gajiya da halayyarka zan fa sanarwa da nagaba da mu, komi na nema amincewarka sai ka dauki zafi da ni, ko dai ka gaji da ni ne Sahabi? Ya ce, kin ji halin na ki ko, a kullum ba kya son na fadI ra'ayin zuciyata sai ki ji zafi, sai dai nabi son ranki, to ban dai amince ba idan kina zuwa gidanmu ki je idan ba kya zuwa ki zauna a gida sai anjima; ya matse wayarsa. Sahabi ya kan so ya yi ma Mami waya amma tun lokacin da ya taba yi ya ji ta tsayc-tsaye sai ya manta da ita ya rungumi aikinsa kai tsaye. Gidan da suke zaune gucss hause ne, na ma'aikatarsu su biyar nc a gidan kowanne ciki da falo amma fa sun kayatu 129 ainun, usa da dakin Sahabi na wani mutumin kogi ne tun daga get din gidan zuwa harabar gidan an shirya yadda mazauna iden suji dadl, sannan an saki kayan alatu a ko ina cilki da bai din gidan idan mutum n ciki ya kan manti a nijeria ya ke. Babm abinci kuwa Sahabi bai da matsala saboda ma'aikatarsu ta tanaji wajen na musamman don hirya wa jama'arta abinci, saboda haka sai abinda ranka ya ke-so ake dafa maka lokuta da yawa Sahabi ya fi yin oder tuwon shinkafa ko sakwara da daddare abinci, rana kaji kuwa da naman shanu ana juye mai launilauni, babu wani banbanci da gida kaduna, wata daya da yan kwanaki oga dinsu Sahabi ya soma fahimtar Sahabi mutum ne me kwazo da zafin aiki, saboda haka sai ya sa shi gaba a kullum aiki ne ba dare ba rana karfe daya biyu shine lokacin zuwa gida don su kwanta wannan yasa Sahabi ya manta da duk wani boki da zakin aurensa da Mami, bai da lokaci tunani balle har sha'awarta ko jin zafin batancin da take mai ya bijiro masa. A daidai lokacin da ya cika wata biyu rabonsa da iyalansa awanan lokaci ya soma tunani zuwa ganin su Mami amma sai kuma shugabansa ya ce, masa za su aiki lagos a gobe, kuma ya tafi da shiri domin yana jin aikin na su kila har london zasu na yan kwanaki, to hakan ta sha fruwa a yan' tsakanin nan, ba su, Delta ba su Abuja, don Abuja kusan duk bayan kwana biyu ne su je aiki su dawo Rivers, kwanansu daya rak da yini daya a legos aka shirya musu biza ta tafiya England a can din ma aiki kwana biyu suka yi 130 a rana ta uku suna Abuja daga abuja ne Sahabi yayi wa Mami sako (by Courier) a ranar da ya aika a wannan rana sakon ya isketa, a ofis ta amsa ta sa hannu. Bata bude ba sai da ta tashi aiki a rannan bata wuce gidansu ba kamar yadda ta saba a yan kwanakin nan sai ta wuce dakin mijinta, a dakinta tayi daidai da kaya takalma kala uku kowanne da jakarasa wa'anda ake masifar ya yi a zamanin sai rigunan bacci sumа uku, sannan agogon hannu wata yar siririya mai tsadar gaske, a lokucin da Sahabi ya saye ta yaso kwarai ace shi zai daurawa Mami a hannunta domin sanin kansa ne zata manne da fatatta ta yi kyau saboda yanayin halittatta. To itama Mamin ta bude tana yaba agogon a hannunta kafin ta yi ajiyar zuciya ta daga yar karamar wasikarsa:- My Only Mami, Ya ki ke? Naso zuwa kwarai wallahi aiki ya yi yawa, aikin kuma na tafiye-tafiye, wannan shi ne dalilin. Love always Ab-kar Takardar taso tayi mata dadi amma tasan Sahabi ya rage kaudin soyayya a rubuce, amma kuma tasan yana sonta, abinda ya fara bata tsoro game da tafiyetafiye da ya yi mata korafi shine, duk tsarabar da ya aiko mata taga daga london ya siyosu, kwanan sa 131 nawa a london kenan? Bata faye son zuwa aiki Kasashen urai nan ba, komi yasa? Ta jawo wayar ta ta nemi layinsa amma wayarsa a rufe take, wanna ya kara jagula ranta, sai ta rubuta mai text, shiru shiru shiru bai bata amsa ba, har ta gaji ta kwanta bacci ta hakura Cikin bacci karfe biyu daidai amsar ta ta shigo, ta dauki wayar da take ajiye kusa da filonta, ta duba shi din ne, ta ce, Ab-kar ka tayas da ni bacci; ya ce, Sorry love wallahi yanzu na ke tashi aiki; ta bude ido tace, me ya sameka kasan lokaci kuwa? Ya ce karfe biyun dare Mami naga sakonki tace ch tabbas haka yake abinda na rubuto maka yace, Mami ni kaina zan fi so ki zo amma babu hali saboda tsarin inda na ke ba halin aje matar aure, kuma aiki na ba na zama ba ne, kin ga yaya zanyi ki zo man hutu! Kiyi hakuri ina nan zuwa kwanan nan, ni kaina wani lokaci na kan shiga cikin 6acin rai, kin dai san ma'anar sunan wannan jihar wato (Ruwa) to akwai ta da rafuna ko ina saboda haka sun kayata ta da gurarèn jin dadin al'uma, na kan so ace nayi dan gajeren hutu ni da ke, amma kiyi hakuri har su mallaka min gidana domin naji oga ya ce idan munyi wata shidda zan zauna Abuja amma nan din ma zirga zirga ce; Mami bata san lokacin da ta saki tsaki ba ta ce; kasan ALLAН wallahi har cikin raina na fara tsanar wannan aikin na ka: ya ce, haba don ALLAH kar ki sa gwiwata tayi sanyi mana: ta çe; kamar yadda na rubuto maka na fi sha'awar ganinka fiye da sakonninka, mu yi bacci lafiya: ta rufe, wayarta. 132 Sahabi ya tsaya galala yana kallon wayarsa kafin ya kashe ya girgiza kai yace, Mami na kenan muyi tsiya muyi dadī kamar da gaske tana zuwa nan kwana daya ana biyu dole muyi fada. a Su Hajiya da su Anti hadiza kan jure haka nan su kawo ma Mami ziyara don dai su duba lafiyarata, amma lokaci lokaci ne sukan yi dacen samunta gidan amma lokuta da yawa sai dai su bar sakon abida suka zo mata dashi hannun su kiristin ko Ya'u. wani lokacin kuma akan dole Hajiya kan yo mata waya ace ta shirya za su kobarkar haihuwa ko gaisuwar rashin lafiya na yan'uwansu Hajiyan ko aminanta, wai don dai kada ace an bar Mami haka nan, mijinta bai nan su kuma ba su kula ta, amma duk wannan bai sa Mami ta saki jikinta da dangin mijin ta ba. Tun ana sauran kwana hudu Sahabi zai zo Kaduna ya rinka turawa Mami text na cewar ga shi nan zuwa insha ALLAH daga Abuja zai taho kaduna kuma sai ya yi mata kwana biyar ko shidda, Mami ta kan yi banza da text din sa, domin ita a ganin ta Sahabi ya wulakantata ace har wata biyu dayan' kwanki bai zo ba, ita kam ba zata iya zama yar tsaron gida ba, ko yar rakiyar Hajiya anguwa. Ranar laraba Mami na tasowa aiki gidan su ta wuce, ta yi wance dakin su anti Zainab bayan jikinta na bata lalle rannan Sahabi zai zo, hatta kawarta me zuga ta Maryam Bishir ta bata shawarar kirki inda ta ce ya kamata ran da Sahabi zai zo ki zauna gida ki yi masa kyakyawar maraba Mami. 133 Karfe biyar da rabi daidai bawa bai gwada lokaci Sahabi ya iso gidansa na kaduna a cikin galleliyar motarsa wadda wajen aikinsa suka bashi ga cikakken direbansa peter, but fin motarsa cikc take fam da tsaraba. ko super holland turmi shiddace ya aje ma Mami biyu hudun yace aje ma Hajiya da su ga lcs guda biyar na Mami biyu na kannansa uku, sauran tsarabar kuwa kayan ciye ciye ne, ya hada peter da Ya'u suje gidan Hajiyan ya ce, azo mai da Uwani daga nan, su kan su Uwani sun yi shirin zuwan Sahabi domin abinci hatta peter sai da ya ture, uwani da kiristi da Ya'u sune suka gyara ko ina suka shirya komai, Sahabi ya shiga dakin baccinsa ya zauna gefen gado ya yi sukuti, a iya tunaninsa bai san dalilin da ya sa Mami ke masa irin wannan cin Kashin ba, wai duk masu auren soyayya haka suke tsintar kansu koko dai shi ne dai marasa'a? komi yace zai aiwatas kan Mami aikin banza ne, sam bata tsoransa balle shakkarsa, haba don ALLAH duk irin zakwadin da ya ke.yi na son ya zo ya ganta amma wai ita bata damu da ganin sa ba, kuma mako ba zai zo ba, ina amfanin ace bata gida har zuwa irin wannan lokaci? Shin ko dai addu'a zai fara yi ne idan har Mamiba Alheri ba ce agareshi ALLAH ya rabasu anan kuma so ya yi rinjaye. Sam bai iya yin wannan addu'ar kai tsaye! Mami ta yi anfani da karim magana nan da ake cewa (kowar bata ya sani, kowar gyara ya sani) saboda haka sai ta daidaici daidai lokacin shigarsa 134 masallaci sallar isha'I, sannan ta shigo gidan. Su Uwani ana ta kai kawo ta yi sallama ta shiga, anan ne Uwani bayan sun gaisa ta ce, O'ohh amaryar ce sai yanzu? To mun cinye tsarabar sai ki jira wata: Mami ta dan yi murmushi amma cikin ran ta ta soma tsinewa Uwani, ta bude dakin ta ta shiga, ta yi wurgi da kayan ta ta mikar da hannu ta Sabuli ribon din da ta tukke gashinta, ta yi war ta shiga ta yi wanka ta fito ta saka zulun buwar riga ja, tana tsaye tana sharce gashinta zuciyarta na ta tiriri dangane da zuwan Uwani, gaba daya ma ta tsani zuwan Sahabi har bata kwadayin ganinsa ya fi minti goma da dawowa daga masallaci a bisa dole ya doshi fakin Mami, ya shiga ya tsaya yana kallonta ita ma ta dago ta dube shi, abinda idonta a gani ya bata tsoro domin ya yi kiba ya yi fari, irin farin nan mai kyau, ko lokacin farkon haduwarsu Sahabi bai kai kyan haka ba, nan da nan sai zuciyar ta ta saduda tabbas Sahabi bai tunanin ta don haka ma ko kusa tasan bai damu da ita ba, shirme take yi akansa, idanunta su kai rau, rau kwalla ta cicciko, ta jure cikin rudani ta ce sannu ya ce menene sannu: wai kina ko da hankali Mami a matsayina na mijin ki na dauki lokaci mai tsawo bani gida amma ace a wannan lokacin ba za ki iya tsayawa ki nuna man mutuntawa ba ta zahiri a ko da yaushe sai dai na sami kyautatawa daga wasu jinsin jama'a

Chapter 9 of 13