yau bai dace ba ace tun da akai
rasuwar nan ba muz auna mun yi magana ba
sosai da sosai ko saboda rayuwar kannarnki,
wannan zan ce yayi ma Mami gardi domin
tana son ayi ta ta kare saboda dai rayuwarta
ba wani anfani tsakaninta da Sahabi, nan take
ta shirya.
Yadda suka tsalo ado suka zo cikin
raharsu,s ai ayau Abduljala ya yi farin ciki da
Mami, nan da nan ya bude masu falo na
musamman suka shiga aka sha hira sosai.
Sannan Sahabi ya ce, baba na zo wajenka da
Mami a matsayinka na mahaifinta don ka
zama shaida a nan Abduljala ya yi sukuti
yace, mene ne? Ya ce a zato na dai Baba ban
taba kawo ma karar mami ba kuma ba wai
don muna zaman lafiya ba ne, a'a ina ganin
dai ko an kawo karar ta ta babu amfani
saboda irin tarbiyar da Mami ta samu kenan
Baba ka yi hakuri ba ina son cimaka fuska ba
ne, a'a ina amaye maka kululun da ke damu
na ne, to a yau din ba ban kawo ta kara ba,
na kafa ka shaida ne a matsayin mahaifinta,
shaidar kuwa itace, Mami na dauke da ciki
181
2
na har na tsayin wata hudu ama ta je asibiti a
debe mata saboda zata yi tafiya turai karatu,
to na ji na amince tana iya tafiya bayan
duniya ma amma ban yadda ta je da ciki na
ba, haka nan ban yadda ta zubar man da ciki
ba, in wani abu ya sami wannan cikin to
wallahi zan yi sanadiyar kai ta kurku ku ta
kare rayiwarta a can a dalilin ta yi kisan kai.
In kuma kin dauka karya ne ba zan iya ba, ga
fili ga mai doki mu zuba ni da ke.
Abduljala zuciyarsa na tafasa ya ce,
Mami kice man karya ne sharri ake maki, ba
ki nemi zubar da ciki ba, Mami ta yi shiru
yayi tambayar duniyar nan ba amsa. Sahabi
ya ce, wallahi baba kaga ma takardun ni ina
da shaida duk in da za'a. Ya nuna mai
takardu ya duba ya girgiza kai yace, tur da ke
Mami Sahabi ya mike zanbur ya ce ki zauna
a gidanku ki yi duk abinda ranki ke so amma
ba zaki kisan kai a gidana ba, kuma ina kara
tuna maki ko cikin nan ya zube daga Allah ne
ba zan kyale ki ba, don bazan iya amince ma
raina ba. Ya yi wa Alh. Abduljala sallama ya
fice abinsa,
Gidan su Mami basu waiwayi Sahabi ba;
gidan su Sahabi ma ba a waiwayi su Mamin
182
ba, illa dai kawai su Hajıya an duka ga
addu'a.
Rannan Sahabi ya zo wajen Hajiyar rai a
bace hankali a tashe, yace, Hajiya Kalil dai
yayan Nana yasa rana zai daura auren Nana
sauran sati uku, amma kuma wai ta gudu can
wani kauye a kasar Gombe, ni abun
damuwata yarinyar nan bata san love din uwa
ba bata san love din uba ba, sai ni kadai ta ke
so, shin anya ba'a dauki alhalin ta ba kuwa?
Kuma na je kauyen da ta gudu gidan kanin
Baban su ne, wallahi ba ki ga yanayin gidan
ba, ba irin gidajen da ta saba zama ba ne;
Hajiya ta ce, ban ji dadinw annan labari ba,
to kai din ma ka ga yadda ka koma kuwa ka
yi hakuri za mu shirya mu je muga Iyayen
nata.
Mota biyu Hajiya ta shirya ta maza daga
Sokoto da ta Hajiya da 'ya'yanta, har
Gombe, suka soma sauka gidan maman
Abdul, daga nan maman Abdul ta yi masu
jagora ita da mijinta har gidan Iyayen Umma,
an yi sa'a Kanal Kalil ya zo aka rinka cusa
mai magana, mahaifiyar Kalil tace, kaiwa
Allah ka dubi girman Manzo ka hakura da
zancen Amadu din nan, kamar yadda Nanan
183
tace ne zuwan Sahabi ai rahama ne ga
rikicinka da Asma'u ba ace dai ta auri daya
daga cikin wa'anda ku ke so ba, wannan
Sahabi shi ne zabin Nana kuma daga ni zabin
Allah, domin ya yi maganin duk wata rigimar
gidan nan akan Nana.
Kanal Kalil cikin cika yana batsew ayace,
na ji sai aban lokaci na yi bincike na kuma yi
nazari, su same ni a can Kaduna gidana.
Cikin sati biyu kusan kullun Hajiya sai ta
tura su Mallam Adamu gidan Kalil, har yau
dai ba ashawo kansa ba, Hajiya ta ce wai
Mallam Sahabi kuwa ya sa ka yi istahara
akan wannan aure na Nana? Yace E to, ya yo
man waya tun lokacin da ya soma nemanta,
duk wanan rigimar ba komi Hajiya kafin dai
ta je gidan ne, amam da zarar an yi auren
za'a samu natsuwa a tare da yarinyar. Ku
kwantar da hankalinku ba komi insha Allah.
Sahabin da kan shi ya yo ma Hajiyar
waya yace, to Hajiya na je Gombe an ce dai
an bani nana yau ma sauran sati biyu daurin
aure da biki. Gidana na Abuja komi ya
kammalu, kayan da na yi oda daga Italy sun
iso tun watan jiya, yanzu tunda hankalina ya kwanta zan je na yi kiliyarin din su. A nan za
184
ai bikin ne a Abuja? In ji Hajiya ya ce, Eh, ai
ita Nana ma tace, yini daya ne bikin nata bata
son bidi'a, ran juma'a za'a daura aure a kawo
ta rannan ran asabata yi yini kowa ya watse,
hidima ce, gatanan kan Sahabi ga aure ga
sabon gida, gida kuma ba irin wanda irin mu
ya ku bayi muka saba gani ba, idan ma mun
yi dace da ganin irin sa sai a finafinan turawa
ko 'yan kudu.
Nana ta shige sukuf gidan mijinta Sahabi,
in ma sakayyace to a gaskiya Allah ya yi ma Sahabi, domin Nan aji take dashi kamar
kwai, abinci sai dai wani ya iske wani, bayan
wannan ma nana ce mai kula da hankicinsa,
singileti, panties, hatta takalmansa Nana ta
adanasu a ma'ajiyarsu daban, kayansa itaсе
mai fidda wanki na dry cleaning daban
wanda yaronsu zai wanke ya goge daban,
tana da yarinyar mai tayata aiki amma Sahabi
sai ya kwana uku bai sa yarinyar a ido ba,
nana ce dai a dama da hagunsa, in dai suna
tare basu gundura da juna su yi ta hira har
idan mutun na gidan ya rasa wai me suke
fadawa junansu ne? Nana ta saba da su
Hafsat da Aisha kamar ciki daya suka fito
2
185
dan lokaci Kankani nana tana ganin ta sami
uwa, wato Hajiya kenan.
Mami na fama da tsohon ciki ta ji labarin
auren Sahabi, bata yi mamaki ba, tasan dole
hakan ta faru saboda wulakancin da ya yi
mata a gaban mahaifinta abin ya daure mata
kai,w ai Sahabin da ta mayas banza, shi ne ya
yi mata haka? Kuka ma bai da amfani, duk
wanran ma ba shi ne matsalar ba ta gidansu
tafi da munta, saboda Abduljala amininsa ya
bashi auren kanwarsa a Kano don haka yanzu
bai da lokacin kowa sai na zukekiya kuma
kamilarliyar amaryarsa, domin ya baiwa su
Anti Zainba notice ko su yi aure ko su koma
gidajen iyayen su can maiduguri, hatta
samarin gidan masuyin sakarcin yace a koma
gida na kirkin kamar su Baba Sadiq ya nemar
masu aiki ya kuma samar masu gidan zama.
Cikin dare haihuwa ta zo ma Mami a
zamanin Sahabi ana gabar amarci shi da
Nana, su kannen Iyana wa'anda aka dauko
don su lura da mami ada can mami ta tsani su
lyagana amma yau saboda tsananin azabar
ciwon haihuwa bata san lokacin da ta
rungume Iyagana ba tana kuka tana fadar
zancen da ba su kamata ba, tabbas yau ciwon
186
haihuwa ya saukarwa da Mami ladab a fili da
zuci.
Da asubar fari Mami ta haifo sanbalelen
yaro mai kama da ita, komi na Mami, inda
diya macece kila da an yi Mami 'yar small.
Saida aka sallame su suka koma gida sannan
Iyagana tasa Zainba ta yi ma Hajiyarsu
Sahabi waya tace Mami ta haihu kuma lafiya
lau sun yi murna, fiye da zaton dan adam,
kafin kace me ye wanan zuri'ar su Sahabi sun
cika gidan makil da kayan su na beby
rakatakam, wannan ya dauka ya yi mai
addu'a wanan ya dauka ya yi mai addu'a,
addu'a kam ya shata, tun da ya zo duniya
hannun a baki Iyagana ta ce, don Allah kusa
mana baki ta soma bashi nono Mami tace, ita
so take ma su tafi da shi suba Sahabi dan shi,
Hajiya ta dafa Mami tana yi mata nasiha tace,
Haba mami idan kina fada da Sahabi sai ki yi
hushi da dan ki,w annan dan Mala'ikan Alah
me ya sani a duniya, ki tuna hakkin da da
mahaifi, ba wai ba mu iya rike shi ba ne a'a
kín ga Sa'adiya ga tanan da jariri sabon
baihuwa zata iya hada su ta shayar baki daya,
1o amma ke da jaririn na ke tausayi, can gaba
a ki nadamar da babu amfani.
187
kugunta da marar ta duk sun bude hatta cibiyar ta ta
fito fili, ta dora hannu a mara, jikinta ya kara
tsinkewa ta yadda koma mene ne a jikinta ya soma
zama gudan mutun, ta fashe da kuka tana zagin
Sahabi akan ya cuce ta, wai ciki! Kuma da Sahabin
da ta tsana a yanzu? Ta maida kayanta ta koma daki
ta balle sabon babin kuka.
*** ***
Sahabi ya linke takardu ya soka a aljihu
yace, ba komi Hajiya zan yi maganin
al'amarin ya mike zai fita tace kada dai ka yi
hushin zuciya ka aikata aikin dana sani, ya
ce, kada ku ji komi Hajiya zan bi komi a
hankali.
Ya isa gidansa a lokacin mami na gida
tana kwance a falo, ganin motarsa ta mike da
sauri ta shige daki, a ranta bata so zuwan sa
ba amma wani bangaren tana so don in ta
kammala da zubar da cikin zata sanar da shi
zancen tafiyarta. Ya iske ta cikin dakin
kowane cikin mamaki shi da ita, domin
kowannensu borin kunya ya cika shi, ya ce,
Au Mamis hi ne kika boye don kin ji zuwana,
ine gajiya? Tace lafiya lau? Ya jure ya zauna
kusa da ita, ya kamo wancan ya kamow anan
188
lyagar a yi masu barka aka miko masa
jaririyi mai addu'a mai makon ya ji tausin
Mami sai ma ya rinka jin haushinta, wai
wannan kyakkyawan yaron zata zubar mashi?
Son dansa ya shiga rans aya yi ma Allah
godiya. Cikin dacin rai ya dubi Mami kamar
ya ce mata babu abinda ake bukata? Amma
kuma sai ya fasa ya dube ta ya watsar ya aje
jaririn gefen kafarta inda take kwance ya
juya ya fice. Ta yi iyakar kokari ta yi kuka
kwallan suka ki zuwa, kirjinta ko kamar zai
tsage don bala'in bakin ciki, wai ma Sahabi a
cikin mutane shi zai yi mata haka! Ta kurawa
dan su ido yayin da yaron ya soma kukan son
nononsa amma kamar Mami bata cikin dakin,
bata dauke shi ba, sai can Iyagana ta shigo a
guje ta dakawa Mami tsawa tana yi mata
fada, Mamin ta dube ta galala tamkar mutun
mutumi, har dai Iyagana da fahinci halinda
Mamin ke ciki ta isa gare ta ta rike ta tana
bata magan a anan en Mami ta fashe da kuka,
ita kuka jariri kuka.
A ranar suna ya zo ya ci sunan Abduljalal
hajiya da Sahabi suka zabar masa. Da azuhur
motoci shidda niki-niki da akwatuna na bebi
da maijego da 'yan uwa 'yan suna suka isa
189
gidan su mami a cikin ayari har da Nana ta yi
kyau ta yi kyau har ta gaji zinari da zinari dai
sun kama jikinta sai haskakawa kawaita ke
yi, kamshin ta kuwa na (Ihsan colection ne)
don haka da gani kasan matar wani ce wadda
mijinta ya kama kasa, itama kanta Mami tana
ganinta nan da nan ta sare ta amince jar fata
ma suna suka tara, bakar fata ma da ranar ta,
da gani babu tambaya Sahabi da 'yan uwansa
sun sami irin tasu, nan ne kishi ya nemi
kashe ta don dai kwanan ta na gaba.
Shekara daya cif da auransu nana ta aje
ma Sahabi 'yar diya mace sunanta Aisha
amma suna kiranta Ihsan. Babu abinda ya
canza a zamansu, har tsokanar ta ya kan yida
cewa ina son na ga hushinki Nana, ta kan ba
shi amsa bana maka fata don ba ni da kyau in
na yi hushi. To ba wai zuri'ar Hajiya ba
kadai hatta zuri'arsu ta Sokoto yanzu Nana ta
yi karnene a cikinsu domin lungu-lungu tabi
ta saba da su, duk wani biki yadda su Anti
Hadiza za su itama daga Abuja zata je tare da Hafsat wadda ke zaune tare da ita tana karatu
a nan jami'ar Abuja.
Yadda ya shirya gida a Abuja yanzu haka
ya kusan kammala wani a Kaduna shi din ma
190
ya kusa na Abujan. Mami ta amince bata
son hail va amma kuma mai iya raba ta da
danta sai mutuwa, don haka akan dole ta
janye girman kanta ta roki mahaifinta dan ya
roki sahabi ta koma dakinta tun da dai ba
sakinta ya yi ba.
Alh. Abduljala ya je har Abuja ya iske
Sahabi a ofis sun gaisa sosai sannan ya zare
gilas din idonsa kogin idonsa cike da kwalla
yace bana son kace man komi ni nasan ka
sami kwanciyar hankali wadda ba ka samu ba
tare da mami, amma ka dubi girman Allah ka
dubi darajar Iyaye ka yi hakuri ka bar Mami
ta dawo gidanka. Tamkar Abduljala ya daба
mai wuka a kahon zuci nan da nan ya
tunbure rai ana so a 6ata mai rayiwa kenan,-
me ya ke so a mace wanda bai samu ba a
Nana? Abduljala ya katse tunaninsa ya ce, ka
yi hakuri tunda ka ga na zo har ofis din ka ni
nasan Mami ta canza ne, idan ada ne ai da
ban matsa maka ba ka dai taimaka mani.
Irin kwallan da ke zuba a idon Abduljala
dole ya ce to ya amince, amma zai yi tafiya
sai in ya dawo.
Kasar Taylan suka fara zuwa Nana da
sahabi da 'yar diyarsu Ihsan, sannan Japan a
191
Kasar Toki ne Sahabi ke fadawa Nana
bukatar mahaifin Mami me kika gani? Tace
kana zaton kishi zai sana baka shawara kada
ka zauna da matarka? Haba SAN ai ban cika
diya mace ba kenan ina sane da ita fa na
kallafawa raina son ka, ba abunda ya dame ni
da ita, ka dawo da ita wallahi, ka taimaka
mata yace kin san Allah idan na tuna zan
sake zama da mami har zazzabi na ke ji? Ta
ce, kada ka damu ka tuna yanzu ba ita kadai
bace, kana zaton zan kyale ta ta yi ma irin
abubuwanda ta yi maka ada? Kasan Allah
daya ne, ba faďa ba zagi, ko dai ta canza hali
ko halin ta ya koreta, tana tsammanin maza
irin ku ba tsada ku ke yi ba dan ta samu zata
wulakanta? Ya fada akan nana ya makalkale
ta suna kyalkyatar dariya tace, kada fa ka yi
ma Anti Hadiza asarar ‘ya'ya kasan a wayar
da ta yi man kwanan baya tace, 'yan biyu
take jira.
Ya bude baki fuska cike da fara'a shi ko
ba'a fada mai ba yasan Nana ce uwar
'ya'yansa kuma gurun hutunsa abin biyan
bukatarsa aminiyar shawararsa a kullun.
192
*** ***
Mami ta koma, itama ta shige sabon gida
da dan saurayin dan ta Abduljala, bai faye
waye ba Ihsan ta fishi wayo duk da ya fita
girma, ta zama shiru-shiruda ga sahabi har
'yan uwansa yanzu tausayinta suke ji.
Nana ta kwallawa Hafsat kira ina Karamar
jakar nan? Ta ce wacce mai takaddu a ciki?
Ko wadda aka zuba shaddoji da atanfofi?
Tace A'a me takardunta ce, Gaba daya duk
mun zuba a mota! Nana tace very good, na
gidan Anti Bilki ne, kin san zamu tsaya
Funtuwa kafin mu shige Sokoton Sahabi ya
shigo ya ce, Hello my Queen na ji ana zancen
zuwa Funtua ba na ce ki jira sai mun je
London mun dawo ba? ta ce Haba SAN na yi
ma Anti alkawari 3 x fa kenan kuma ni kadai
take jira ta fitas da litafin nan ka ga ya dace
ai taja ma jama'a rai? Ya ce, wane littafin
kuma? Ta ce Na Girke-Girke mana, na yi
mata alkawarin zan rubuta mata wasu, to na
gama tuntuni ko a daran jiya mun yi waya
nace zan je Sokoto zan biyo na kai mata,
yanzu kuma sai ta ji shiru? Ya daga hannu ya
193
.
۳
ce, Yes kin fini gaskiya. Ki gayas man da ita
kice ban manta da sakon taba kar ta yi hushi
da ni don Allah tace, ka san halin Anti ba
ruwanta yanzu haka ma ta manta da wannan
ya ce yaushe za ku baro Sokoto? Tace kwana
uku za mu yi, ina jin zamu Birnin Kabbi ni
da Anti Hadiza ka san za mu kai kudin auren
Abba ko? Ya ce na san da wannan zan dai
jira ki a Kaduna.
Ya dauki Ihsan yana mata wasanni sai da
ya raka su har cikin mota ya ga tashinsu
sanan ya tafi hidimarsa.
*** *** ***
Bayan wanan tafiyar da 'yan watanni
Nana ta haifi 'yan tagwaye maza, Ahmad da
Muhammad. Anti Bilki ta aiko mata da litafin
girke-girke a matsayin gudunmowarta ta 'yan
tagwaye. Duk macen da ke ji da kanta ta je
suna a cikin kayan sunanta zata tsinci littafi
mai suna mu koma kicin na Anti Bilkin Funtua.
194
Mata sun yi murna sun yi alfahari da
wannan littafi Nana na shan waya akan ko
litafin ya je kasuwa?
Itama Mami ta zauna a tsanake ta karanci
littafin tun tana jin za fi saboda kishi har ta
soma natsuwa tana baiwa kan ta shawar
alalle Anti Bilkida Nana sun yi gaskiya MU
KOMA KICIN wanan ma kamar dan ita aka
yi saboda har yanzu bata sami kan Sahabi ba
ko ya zo weekend a gidansu ya ke cin abinci.
A karo na farko Mami ta yini zungur a
kicin tare da sabuwar mai aikinta, domin tuni
Kiristi ta yi aure ta sami Mairo 'yar karamar
yarinya. Yau ta iya tuwo, ta iya miya, tun
daga wannan rana Mami bata sake zama ba,
sai koyon girki.
Musamman ta yi ma Anti Bilki addu'a
lokacin da sahabi ya zo ya ci abincinta ya
zauna dirshan shi da dan sa Abduljala
wannan yasa mamita aje aiki domin kudi na
Sahabi matarsa bata bukatar komi a duniya
sai neman lahira.
Wata irin sabuwar mota ce Sahabi ya
sayawa Mami da Nana kalarsu daya mai suna
(Jeep C.R.V) ja ce shar mai kashe ido Mami
ce a ciki ta tuka zuwa tudun wada ta shiga
195
ce, Yes kin fini gaskiya. Ki gayas man da ita
kice ban manta da sakon taba kar ta yi hushi
da ni don Allah tace, ka san halin Anti ba
ruwanta yanzu haka ma ta manta da wannan
ya ce yaushe za ku baro Sokoto? Tace kwana
uku za mu yi, ina jin zamu Birnin Kabbi ni
da Anti Hadiza ka san za mu kai kudin auren
Abba ko? Ya ce na san da wannan zan dai
jira ki a Kaduna.
Ya dauki Ihsan yana mata wasanni sai da
ya raka su har cikin mota ya ga tashinsu
sanan ya tafi hidimarsa.
*** *** ***
Bayan wanan tafiyar da 'yan watanni
Nana ta haifi 'yan tagwaye maza, Ahmad da
Muhammad. Anti Bilki ta aiko mata da litafin
girke-girke a matsayin gudunmowarta ta 'yan
tagwaye. Duk macen da ke ji da kanta ta je
suna a cikiń kayan sunanta zata tsinci littafi
mai suna mu koma kicin na Anti Bilkin
Funtua.
194
Mata sun yi murna sun yi alfahari da
wannan littafi Nana na shan waya akan ko
litafin ya je kasuwa?
Itama Mami ta zauna a tsanake ta karanci
littafin tun tana jin za fi saboda kishi har ta
soma natsuwa tana baiwa kan ta shawar
alalle Anti Bilkida Nana sun yi gaskiya MU
KOMA KICIN wanan ma kamar dan ita aka
yi saboda har yanzu bata sami kan Sahabi ba
ko ya zo weekend a gidansu ya ke cin abinci.
A karo na farko Mami ta yini zungur a
kicin tare da sabuwar mai aikinta, domin tuni
Kiristi ta yi aure ta sami Mairo 'yar karamar
yarinya. Yau ta iya tuwo, ta iya miya, tun
daga wannan rana Mami bata sake zama ba,
sai koyon girki.
Musamman ta yi ma Anti Bilki addu'a
lokacin da sahabi ya zo ya ci abincinta ya
zauna dirshan shi da dan sa Abduljala
wannan yasa mamita aje aiki domin kudi na
Sahabi matarsa bata bukatar komi a duniya
sai neman lahira.
Wata irin sabuwar mota ce Sahabi ya
sayawa Mami da Nana kalarsu daya mai suna
(Jeep C.R.V) ja ce shar mai kashe ido Mami
ce a ciki ta tuka zuwa tudun wada ta shiga
195
can kasa kusa da kasuwar bacci, ta karya
daidai Getso resturant, sannan ta dauki layin
gidan Kifi a daidaí gidan kifin ta hango inda
take nema wato Shagon Anti Bilki,ta tsaya
bakin Shagon duk matasa aka yo mata ca da
ido, ta shiga ta zabi dukkan litatafan Antin ta
biya har zata tafi ta juya ta ce ma yaron in ka
je kace ina gaida Anti ya ce, to amma wa
zance? Ta yi murmushita ce, kace mata
Mamin Nana da Sahabi.
Har motar ta bace yaron na mamaki.
196
TUNA BAYA
Tun zamanin da na soma wallafa littafi,
wa'annan bayin Allah suna tare da ni, tafe su
ke da kafarsu gare ni aike bisa aike, waya a
kullum ba su taba nuna min son komi su kai
mani sai na mayas masu ba, amma a kullun
suna kokarin su nuna man zuminci da kauna
ta fisabilillah a bisa baiwar da Allah ya yi
man.
Bana iya tuna iyakar alhairin da su ke
man, sai dai Allah ne shaida ta domin ina
yawaita addu'a akan ya hada mu a aljanna
Fiddausi. Ta farko:-
Hajiya Ummu Dasuki
Uwargidan Maman Daura
Nafisa Ado Bayero
Mrs. Garba A.D Kano
Hajiya Anisa Shehu Galadanci
Mrs. Tajuddeen.
197
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13