aje kudinsa ta fiddo kusan
dubu biyar yace me kuma za'a saya? Ta cc ba ka ji na
yi baki ba ne, Mr Biggs zan aiki Ya'u ya ce, yadda ke
ma ba kya cin abincin gidan nan suma dole sai na
saync, Allah ya shirya!.
Ta dube saroro tace, kudinka na taba shi yasa za
ka gaya man haka, ta ja tsaki ta rufe kofar bam.
daman ransa a bace ykae ya bita yace rike mata
hannu yace, daga yau karki kara yi man tsaki, in ko
ki ka sake ranki zai baci a gidan nan, kafin ma ya ji
amsar ta ya /saki hannunta ya koma dkai abinsa,
amma dai babu wanda ya ji su a gidan. a
D
Mami ta zauna suna ta hira amma hankalinta bai
tare da ita, abin mamaki lokacin da Hafsat ta gama
abincin sahabi sai ta cika cooler daya ta hada farantai
da komi da komi da kuma kkc da meat pie din da
Kannan Mami suka sa ta yi masu ta kai masu,
kawayen mami suka soma santin dafuwar shinkafa da
ruwan kwkawa suka ce ke Mami wanan wacece?
Tace, 'Kanwar Sahabi ce,' Suka ce, to ki yi a hankali
in har da aure tsakaninsu dole ne ma ya aure ta
wannan hanhun ke ko mutuniyar mun san ki da
shegen son jiki kullun kina yawo Mr Biggs hala dai
yanzu kin dai na ziyara? Aka tintsire da dariya, tace,
Yanzu ko na ke ziyarar su Mr. Biggs wa zai man
aikin ga wannan aure da na lakabawa kai na ke
abubuwa dai kanana ga su nan,' Hauwa tace, Gara ke
Mami ni fa auren da ky na iya sati biyar ina zan iya
wannan fitina, amma ke na ga Sahabin na ki kawai
natsuwa ga kunya, Mami ta yi murmushit acе, В
alaifi kin fadi gaskiya kam.
Bayan komi ya kammala baki sun koma gidajen
hattà kannan sun gaji da sharholiyarsu sun tafi,da
suka tashi tafiya ne Mami ta ce ma kaninta Hasan
kace, Iyana ta je Abuja ko? Yace 'Eh, tace, Amma
Baba ai yana nan? Suka ce Eh yau ya dawo daga
Legas, tace, Ga takarda ku kai masa don Allah ku ce
mai ina son ganin amsa yau, ya ba baba Sadiq ko
cikin diribobinsa a kawo man.
Hasan ya kai ma Alh. Abduljalal takarda, ya
manna gilas dinsa ya karanta wasika kamar haka:-
75
Da Fatan kana lafiya Baba. Don Allah Baba ina
son kudi, kasan in nace ina son kudi lalle na matsu
nc.
Diyarka mami Abduljalal ya dan yi tumani sai ya
tuna halin yau kila basu da kudi ne daga ita har mijin,
ya kuma dace ya taimaka masu tunda dai shi ya rage
masu mahaifin sahabi ya rasu, nan da nan ya dauko
dubu dari cif ya ce a kai ma Mami. Baba Sadi ya jima
yana matsa hon a gidan Sahabi mai gadi bai da niyyar
budewa domin a ganin Maigadi kamar dare yayi
tunda har Sahabi ya rufe gida, can maigadi ya lcka
suka gaisa Baba Sadiq har kun yi bacci ne, maigadi
yanzu sha biyun dare Baba Sadiq ne daga gidansu
Mami don Allah a shaida mata. Maigadi ya je ya
rankwashi kofar falo a zamanin Mami na dakinta
tana kwance tana takaicin yin aure, in dai haka aure
ya ke bata gama anfaninsa ba a wajen ta tunda Sahabi
ya rike mata hannu ya yi mata fada bata sake saka shi
a ido ba har suka kwanta, wato shima ya soma hakura
da ita kenan? Wannan ko itace rana ta farko da suka
raba shimfida. Sahabi na dakinsa yana tilawar
alqur'ani mai girma ya ji maigadi, ya tsaya ya mike
ya fita, Maigadi yace, yallabai Baba Sadiq nc daga
gidan su Mami, yace muje bakin get din lafiya dai
ko?
Sahabi ya leka yace, yaya Baba Sadiq, ina
gajiya? Baba Sadi ya fito daga mota yace, yallabai
"lafiya lau" Shabi yacc, Yaya dai? Ya amsa, Alhaji
ne ya aiko ni wai na kawo ma mami sako ko Hasan
aka ce ta aika kuma ayau take so shine yace na zo na
76
bata, Sahabi yace, 'Mami kam ta kwanta Sadiq yace,
'Ai tunda gaka sai ka amsa da kai da ita ai duk ſaya
ne. Ya amsa su kai sallama.
Sahabi ya zauna falo ya zubawa kudin ido, kai
wannan masifa ko da yawa take daga wanan fitina sai
wannan, wato ita zata fara nuna mai gadara bai isa ko
kadan ya nuna mata kuskure ba, dole kaoda yaushe
ita ke da gaskiya bai yi wuwa ya biye mata tunda ya
yi lallashin bata ji ba zai soma yi mata wa'azi kila
Allah ya shirya masa ita.
Bai tayas da ita ba sai da safe bayan ya kintsa ya
gama kalaci mai kyau amma daga Hafsat, sai ya sami
mami a daki itama ta kammala har tana zabar
takalma daga jakkar da suka dace ta sa, sai ga Sahabi
yace, ina kwana? Tace lafiya yace, kin aika gida kina
son kudi ko, to ga su jiya kin yi bacci Baba Sadiq ya
kawo maki, amma ina son ki fahimci abu daya, so da
kauna ya hada mu mami har abada ba zan taba
muzanta ki ba, auren nan da muke yi don mu bautawa
Ubangijinmu ne ba don mu saba masa ba, ki tuna da
abinda Subhanahu wata'ala yace, wato da zan umarci
wani ya yi ma wani sujuda to da mace zan umarta ta
yi ma mijinta, anan Mami ki dubi matsayin mijin
wajen matarsa, shin mene ne laihi na don kawai an
kawo kanwata ta taimaka maka mu kare mutuncin
kan mu?.
Ta mike tsaye ta gyara gyalenta a kafada ta
dauko makullen motarta ga G.S.M. din ta manne a
tafin hannu tace, yaya ka gama? Ya girgiza kai gami
77
da murmushi yace, mu yini lafiya yasa kai ya fice,
itama ta fice.
Yau Mami bayan ta taso daga aiki a
Classyburgers. Ta tsaya ta zabi abincin da yayi maka
dadi ta biya ta doshi gida. Ta iske ko ina na gidanta
ya kaure da kamshi na abinda Hafsat ke girkawa, tana
zaune a falo da litattafan birjik tana tilawa tana kuma
lekawa kicin dubo girki, a nan zuciyar mami ta yi
kuna a gaskiya ta sakewa Sahabi yana son kawo mata
raini a gidan nan dole ne yau ayi mai yiwuwa ko ita
ko Hafsat.
Lokacin da Sahabi ya dawo aiki ya hango mami
ta fito daga sito tana fiddo kwalayen juice tana
zubawa a firij, da alamu kamar fuskar Mami a sake
take, ya dan dube ta cikin kasaita, yace, Hello
Madam ya ki ke? Ta juyo a yangace ta ce, i'm okey,
ya ofis? Yace, mun gode Allah, aiki ne as usual, ta
shiga daki shiko ya nufi wajen cin abinci, ta tsalo
wanka sannan ta sheko kwalliya ta fito cikin wata irin
shiga ta alfarma, wani yadi ne mai daukar ido,
kalarsa ruwan hoda amma ya turu kalar dinkin siket
da riga ne, rigar an tsuke tunda ga kirjin har kugu
amma ta sauka kasa sosai hanun ma ya dago ya kuma
yi tsawo, babu dan kwali sai dogon gulae madadin
dan kwalin, shi ta rufa tun daga sama har zuwa
wuyanta, ta yi kyau fa gaskiya. Takalman ta sai
daukar kunne suke ta isa falo tace, Sahabi na tafi
lunching din Fati Garba, ya dube ta tun daga sama
har kasa mace har mace amma bata cika 100% ba,
rashin kula da cikin miji. Yace, Na so yau ki kai
78
Hafsat wajen telanki ya auna ta, tace, yau kam ba zai
yiwu ba kasan matsayin Fati! Ya ce, 'Haka ne, sai kin
dawo, don Allah kada ki shige karfe takwas.
Tana bisa titi tana tukin motar ta kowa ya ganta
kamar ya dauka ya hade ta, amma ba su san mami ko
shinkafa bata iya dafawa, ba kyau har kyau, ga ado
ga kuma dukiyar adon. Ta zauna wata kujera daga
can baya a lokacin amarya na cashewa ita da ango a
gaban masu kidi, tunani kawai Mami ta ke yi, wai
wata hudu da su ka wuce ita da Sahabi kae ma irin
wannan shagalin amma yau ga Sahabi ya zame mata
dan zani, yanzu ita Fati gani take bata iya hada kowa
da Sagir? Shima a ransa hakan ya ke gani, to mnee ne
dalilin da so ke zama ki? Idan da 'yan mata za su
nemi shawarar ta ita kam da sun tsaya ga samartaka
da yan matanci kawai ya isa, ba su kai ga tkaurawa
kan su ga aure ba, yadda ma ta fahimci Sahabi bai
damu da al'amuranta ba sai na su Hafsat, wai ma ta
kai ta wajen tela? Dole fa ta budewa Sahabi ido game
da kilababbun 'yan uwan nan na shi. Ta Mamin
Sahabi ta juya ta mika mata hannu Maryam, ta kama
ta zagayo ta zauna suna mai fuskantar juna, maryam
tace, ran amarya ya dade, Mami ta dan duka kusa
sosai da Maryam ta ce, 'Na tsani aurne nan Maryam
kin huta da baki yi ba, haba don Allah kada ki kayas
man da gaba man, in ji Maryam sai Mami ta ce, ba
haka ba ne, still ina son Sahabi abinda na tsana 'yan
uwansa ina ruwansu da gidana so su ke su mayar da
ni 'yar renon 'ya'yansu shi ma sahabin na rinka
renonsa tamkar jariri to ni irin wa'anan abubuwan ke
79
sa na ji na tsani auren da shi ma Sahabin. Ke ma
Mami kin yi saurin sake masu ne, yaushe ku kai
auren da har za ace sun soma katsaladan a gidan ku,
mami tace, Wai! Ba ki san wa'annan ba wai su
masifar son juna suke yi, Maryam ta ja tsaki tace, ina
ruwanki da kaunar su, ke son da ki ke masa ai yafi
nasu, kin san Allah zan gaya maki, ki raba sahabi da
wa'annan tarkacne mutanne gaisuwa ma ta
musulunci su yi a waya, ko ba kya son sa ne? Mami
ta yi tagumi ta yi shiru ta tuno daren jiya ta yi
kwanan kunci a dalilin kaurace matan da Sahabi ya
yi, insha Allah baza ta sake amincewa hakan ta
faruba, ta daga kai ta dubi Maryam tace, 'Wallahi
Maryam har yanzu bani da gwani kamar sa, ni dai
canza tsarin rayiwa da yake yi min kawai ke hada ni
da shi, tace ki manta da wannan ki ci gaba da nuna
mai so ba wai kyale shi za ki yi ba, ai sai su yi nasara.
Can mai waka ya dau lokaci yana wasa mami
aminiyar Maryam ga amaryar Sahabi da ranarki, suka
mike suka nufi filin rawa suna tafe suna hirar su
wadda ta shafi auren Mami, a fage Mami ta 6alle
bandir na dubu biyar itama Maryam haka suna likawa
amarya daga bisani suka rinka likawa junansu.
Suka koma wata rumfa Maryam tasa 'yan
hidimar biki suka kawo forozin cikin soyayya, suka
ci sosai aka kawo masu juice Mami bata sha ba tace
me je Maryam ki raka ni farm fresh musha madara
mai san yi.
A farm fresh sun zauna a waje mai san yi suna
shan madara sun yi kyau wasu maza biyu masu aji
80
suka rinka son su tankawa si Mami, amma har
Maryam bata ba su fuska ba a dalilin auran Mami, a
nan ne har Maryam fin tace, To kin ga a nan gaskiya
ba kowa zai so ya kyale matarsa ta rinka zuwa irin
wa'annan guraren ba, dole ne mallam Sahabi ya yi
kishi! Suka yi dai murmushi.
Tkawas saura 'yan mintoci Mami ta shiga falon
gidansu, Hafsat ta ce, Anti sannu da zuwa, tace,
yauwa sannu da gida, ya sahabi fa? Tace, yana
masallaci, itama mamin ta shige daki ta yi sallolin ta,
ta gama ta koma wajen madubi ta gyara fuska hoda
da janbaki ta kara domin Sahabi ya sha gaya mata
janbaki na yi mata kyau. Ta mike kamar ta je falo
amma sai tace bari ta bashi lokaci ta san halinsa
runbu ne, yanzu abinci zai ci, idan ya gama ta je su yi
magana, amma sai taji an turo kofa, ya dube ta da irin
fara'ar nan ta kauna, yace, Mami yau kin yi min kyau
shi ne ko kice na raka ki bikin? Ta dan dube sa a
yangace tace, in da ka so zuwa da baka...' ya yi sauri
ya talalfe ta yace 'Mami' cikin dariya, ya rungumeta
cike da wasanni wanda ya saba mata har ya kai ga
kashe wuta, ta yi sauri ta kunna, tace Baka fa ci
abinci ba? yace, manta don Allahc an an jima na ci
tace, A'ah ka je ka ci abincinka, sannan a gaskiya zan
ga ya maka wallahi! Wallahi!! Ba zan iya zama da
Hafsat a gidan nan ba a yadda abubuwa ke tafiya,
haushi ya kama shi yace, me ki ke son na yi? Tace Та
bar man gidana na yi rayiwata da kai yace, in ba
hakan ba fa, Mami cike da rashin kunya tace, yadda
ita ke ba ka abinci haka nan kafin ka ce Mami ko
81
kiristi ka kira Hafsat sau goma a gidan nan to har
lalurar auratayya ka je na yafe ku yi da Hafsat. Ya
dafe kan sa yace Innalil....' Wani kunci da bai taba ji
ba a zuciyars asai a wannan rana, duk wata muguwar
sha'awa da ya ke ji ta Mami sait a gushe, yanzu da
haka sharrin mata ya ke amma har wasu mazan kan
iya tara mata hudu a gida yau ga guda daya wadda ya
ke so kamar ransa tana bata mai rai har bai son ma ya
bude ido ya ganta.
Yace, mami tunda kika iya budar idona ki ka
gaya man haka babu irin zagin da ba za ki maun ba,
haka nan tabbas komi za ki ce man na an baki son
'yan uwana, insha Allah daga yau Hafsat ta bar maki
gida. Ya mike a sanyaye yaf ita, ya iske Hafsat a
kicin tana shirye-shiryne abinda za'a ci da safe don
tana son shiga daki ta yi karatu, yace, Hafsat maza
fito da dukkan kayanki za ki koma gida, cikin murya
mi kauri jin haka yasa Hafsat ta razana, ta yi
hanzarin fitowa ta shiga daki ta hada komi nata, ya
kira Ya'u ya dauketa zuba mata a mota, ya ja sai gida
wajen hajiya Aisha, Hajiyar na zaune itama tana
rubuta wani rifot ganin su kwaran kwaran ta san babu
lafiya, ya dade zaune ba irin tambayar da Hajiya ba
taima Sahabi ba amma sai ajiyar zuciya, ya ki fadin
komi sai a karshe yace, hajiya Mami na fama da lack
of home training wato tana fama da rashin tarbiyar
daga gidansu, ta tsuke baki abinda ya dame ta kenan
atun ranar haduwarsu da mami tace Allah yas hirya
ba hushi dai za ka yi ba, sai addu'a sanan ka mike da
nuna mata iya gaskiyarka, kada kuma ka kuskura ka
82
la
le
la
a
ta
3.
la
n
a
i,
ai
in
di
n
si
la
i,
ai
la
yi
la
ar
la
ar
ns
a
ci
yi mata sanyi-sanyi da dokar Ubangiji, idan ka jure
wa'annan Allah zai baka sa'a a kanta, in ko ba haka
ba kai ne wahalalle. Bai dai sanar da Hajiya irin zafin
da mami ke hada masa ba.
Ya koma gida bai ma dubi abincin da Hafsat ta
shirya mai ba, ya hado ti mai zafi ya sha ya nufi
dakinsa yayi alwala ya gabatar da nafila da addu'a
sannan ya soma karatun alqur'ani ya gyara
shinfidarsa ya kwanta, tunani sannan bacci da
mafarkai barkatai suka ritsa da Abubakar Sahabin
Manzo. Ita ko 'yar gatan gidan Abduljalal da Iyana
har talatainin dare ta kasa bacci a zaton ta sahabi
zaida wo ya kara neman ya biya bukatarsa da ita a
nan ne zata kara nuna mai matsayinta ya zarce na
kowa a gare shis annan kuma ta sauraresa don dai ya
rinka tsoronta, ta rinka tukuburi, duk yadda ka ayi
sun yi gumar ta a gidansu, tunda haka ne ma ta fita
hanyarsa dag ayau baza ta sake haďa jiki da shi ba har
sai ya gane kurnesa.
Da safe babu mai saurarne wani kowane zuciya
ta cika sa taf, zaman kuma Mami da sahabi ya koma
irin aurne zamanin nan, wato ga dukiyar ga
abubuwan jin dadi ga dimbin so da kauna amma
rashin tarbiya ta hana aci moriyar ribar rayiwa.
An koma irin rayuwar da ana aikne Ya'u
kwaran-kwaran da kuloli sayne abinci, yawancin
abokan Sahabi na cikin gari ko sun zo sai dai su sha
ruwan sanyi da juice ayi hira su tafi, idan 'yan uwan
sa ne Kiristi ce zata kawo abinda ta dafa mai iya ci ya
ci wanda bai iyawa ya tsame hannu wannan kenan.
83
Yau wata shidda cif da aure sahabi ya dubi
kalanda a son ransa ya so shi da Mami su yi ko hutun
kwana uku ne su kadaice daga jama'a zuwa wata
Kasa African countries ko kuma wata jiha cikin
jihohin nan masu tashe su more rayuwar aurnesu,
amma ina! Shi rabonsa ma da Mami ko yana iya
tunawa ma? Duk ya komade ya motse kamar dan
shekara hamsin, itama Mamin wannan karon ta rame
ta yamutse, da ganin ta ba kwanciyar hankali, sun
rasa gwani a wajen girman kai a cikin ko da ya ke a
gaskiya Sahabi ba shi da girman kai, fata mai dai aka
yi, tunda bi kam ai yana iyakar kokarinsa.
Kao da yaushe idan Iyana na garin Kaduna tana
kai wa diyar ta ziyara, tsarabe-tsarabe irin su kayan
ciyc-ciye su na kwalliyar mata iyana kan kawo ma
diyarta a yau ma ta zo mata da wasu karori da na sha
irin na anfanin kara jin dadin jima'in mata Mami ta
amsa ran ta a 6ace ta bude wani dan kawati a ban
daki ta aje. Iyana tasa hannu ta shafi sassan wuyan
Mami tace, wai ranar me kike ne a 'yan kwankain
nan? Ni na ga mijin nkai kamar ba zai yi fitina ba, to
me ke sa ki rama, ko ciki gare ki? Mami ta yi yar
dariya tace, Iyana ciki! Ni jiya ma na yi wanka ba
abunda ke damuna, fitinar zuwa aiki dai ce in na
dawo gida bana samun hutu yawan baki da dai 'yan
Kananan abubuwa wanda ada ban saba ba, Iyana a
matsayinta na babbar mace wannan bayanin na Mami
bai gamsar da ita ba, ta tabe baki tace, bana son ki
kwari kanki in dai ya soma bullo maki da halayyarsu
ta maza ki sanar da ni, don in kai shi wajen malamai
84
i
na, saboda ban yi boranci ba banga dalilin da yayana
za su yi boranci, ina anfanin dukiyar da na ke tarawa,
in har ban yi ma ku maganin da za ku sakata ku wala
ba a gidan Ubanku da gidan mazajncku, mamit a yi
jigum murna ta lullube ta amma yanzu bata jin
Sahabi ya yi mata abinda zai sa akai shi gidan
Malami, tace, wani abu Iyana, kin san idan ina da
damuwa ke zan iya sanarwa, ni dai kawai ina jin aure
na da wuya koko soyayya ce ke da wuya? Iyana tå yi
dariya tace, 'Mamina manya kenan, dole ki zama
jaruma ki zama mai jan ra'ayinsa a kullun, shi zai sa
ki mallake zuciyarsa da ra'ayinsa har ya ji bai iya
hada jikinsa da kowacce irin mace, ki yi hakuri kin ji
Mami, kada ki yadda ya ga gazawar ki. Mami ta ce,
'To' amma dai a ranta bata san wacce hanya zata iya
kai kanta wajen Sahabi ba! komi take so sai dai ta yi
mai text shi ma haka sai dai ya turo mata text idan
yana son ya sanar da ita sako.
Yau ma bayan Iyana ta tafi ta tura mai text akan
cewa zata Rimi Driver gidan kawarta Turai za ai
Birthday party din yaronta, Sahabi yana gani ya tsaya
tunani shi koma za su ta6a haihuwar da Mami oho!
Zan cne da Mami bata yi mai kenan tunda su kai aure
amma gaskiya yana son jariri a gidan su kila ko don
ganin jaririn Mami ta zauna da shi cikin mutunci ya
ja dan tsaki ya rubuta mata amsa kamar haka:- Mami
a dawo lafiya: ta duba ta ga amsa kamar hadin baki
itama tsakin ta ja, wai Sahabi shi ne a yau zan cne
soyaya ta gagare shi rubutawa ada ko baya gajiya da
85
3
rubuto mata. Ran ta ya dan sosu kwalla ta zo mata
amma ba su fito ba ta danne damuwarta.
Ta tsala ado kamar yadda ta saba idan zata fita
zuwa sha'ani. Farin les tas ta saka ga zinaran nan ya
kama ta radam.
Gab da mangarib Mami ta dawo gida ta karyo
kan motar ta cikin harabar gidansu amma ta lura suna
da baki motoci ne har guda biyu, ta fito ta yafa gyale
a hannunta ga jaka a rataye kalar gyalen sannan ga
jakar leda a hannunta na tsarabar gidan da ta je ne na
bikin cikar shekara daya na yaron Turai. Ta tsaya
tana kallon lambar motocin bata gane dayar ba,
amma dayar ta san ta T.J ce wato jijjani. Can tunani
ya zo mata ba shakka wannan motar Usman ce
abokin sahabi na Bauchi. Ta shiga falo gabanta na
dar, dari-dar wai idan har Usman ne, ya za ta yi
kenan ga shi basu shiri ita da Sahabi kuma gashi bata
son surutu,t a ki jinin ace za'a zauna ana masu fada
don a shirya su, balle idan da wanan uwar iya yin ne
Sarkin kissa matar Usman Husna, tana wani jida miji
kamar zata sake haihuwarsa. Ta ji hayani a falo sai da
ta yi sallama kamar sau biyu sannan aka amsa mata,
Sahabi ya yi hanzari ya taso ya tarbe ta yace 'yauwa
mami kinda wo ba, mun fa yi man yan baki ga
mutuniyar Husna da angonta Usman itama mamin
dan danan ta saki rai ta shige masa su ka isa falon ana
ta barkwanci, Usman yace, Na so na yi hushi Mami,
sai ace man kin tafi liyafa abokina na gida zaune, a
takure duk rashinki ya baibaye shi? aka tintsire da
dariya tace, Haba Usman ina za shi taron mata? Sun
86
dan jima ana hira sannan sahabi ya janyc Mami suka
shiga dakinta, yace, Ina son kisa a gyara masu dakina
ko ni sai na dawo nan, ko kin ga na koma wani daki
daban? yin hakan ba zai zame mana tsegumi ba? tace
"Ya zan yi dole ka dawo nan din wannan kuma ya
kara dagula ran Sahabi amma ya kyale ta tunda ma ya
zai yi.
An shirya dkauna kamar yadda yace, an sawo
abinci kala-kala a Mr. Biggs da Classyburgers da kan
shi Sahabin ya je ya sawo komi da komi har wanda
za ai kalaci, aka ci aka koshi, amma abinda su usman
suka dauka shine don Mami ta je anguwa shi yasa
akai sawo a waje haka nan sun san halin Sahabi
mutum ne mai son burge jama'a.
An dauki tsayin lokaci ana hira har Husna ta so
yin bacci, ita da Mami suka nufi dakunansu su ka
kwanta, amma Usman da Sahabi suka dosa wata
sabuwar hirar ba ji ba gani.
Usman akwai labaran da ya ke son ya tambayi
Sahabi amma ganin Sahabi na yawan duba agogo
lokaci lokaci, tun da Mami ta shiga bacci, idan
Sahabi ya so ya saki jikinsa can kuma sai ya tsurawa
agogo ido, Usman ya san irin wannan begen dole
akwai abinda ke ran Sahabi, can Usman ya soma
mikewa ya aje kofin tin da ke hannunsa ya ce, sahabi
ya dace mu kwanta haka nan, akwai gajiya a tare da
ni, Sahabi ya yi ajiyar zuciya shima ya mike yana
dan gajerne murmushi, da alamun faduwar gaba a
tare da shi, kai idan ka ganshi ka yi zaton rannan zai
87
1
shiga angwanci a dakin amaryar da akai masu auren
dole.
Sun yi ma juna sai da safe kowanne ya doshi
dakin da matarsa Usman kawai labaranda ya ke son
ya tambayi Sahabi amma ganin Sahabi na yawan
duba agogo lokaci lokaci, tun da Mami ta shiga bacci,
idan Sahabi ya so ya saki jikinsa can kuma sai ya
tsurawa agogo ido, Usman ya san irin wannan begne
dole kawai abinda ke ran Sahabi, can Usman ya soma
mikewa ya aje kofin tin da ke hannunsa ya ce, Sahabi
ya dace mu kwanta haka nan, kawai gajiya a tare da
ni, sahabi ya yi ajiyar zuciya shima ya mike yana dan
gajerme murmushi, da alamun faduwar gaba a tare da
shi, kai idan ka ganshi ka yi zaton rannan zai shiga
angwanci a dakin amaryar da akai masu aurme dole.
Sun yi ma juna sai da safe kowanne ya doshi
dakin da matarsa ke kwance. Husna ta ajewa mijinta
komi na bukatarsa kafin kwanciya, ya kammala ya
kwanta ya karanto addu'o'insa ya shafa ya kuma
shafawa Husna, a nan ne ya jawo ta a jikinsa ya kira
sunanta kamar yadda ya saba ya kuma fi kowa iya
kiran, a hankali a natse cikin hikima da fasaha. Ta
amsa kasa-kasa kamar mai masa rada, haka din ya ke
so, ya ce, na yi fa missing Faisal ke fa? Ta ce, Haba
ina tare da kai ya zan yi rashiN faisal ai ka hade ko
ina, ya ce, kin san na saba na yi addu'a na shafa maki
na shafa masa yanzu sai na ji duk na tsargu kamar na
yi rashin wani abu, kin ga ko faisal ne; Husna ta yi.
dariya a hankali wadda iya karta kunnne Usman, ta
shiga yi mai wani irin (love making) mai shiga jika,
88
wannan shi ke karawa Husna kima da faukaka a
zuciyar Usman, a ko da yaushe ta kan yi saurin shige
masa da nuna so da kauna ba sai wai shi ya nemo ta
ba, wannan ke kara jin bai iya samun tankar Husna a
duniya.
Sahabi ya tura kofar dakin Mami a hankali
tsoron kada ya tayas da ita cikin firgita, ya yi mamaki
sosai da ya ga Mami ta bar (dim light) wato wuta mai
dishewa, yana iya hange dogon wuyan Mami bisa filo
da kanta ya langabe, dakin ya yi san yi kwarai, ta
rufa da katon (bed cover) a yadda ya ga rufarta ta
rage masa mayafin wato za šu iya rufa tare kenan,
wannan ya dan karfafa zuciyar Sahabi ya shiga
kewaye ya wanke baki da (mouth freshner) ya fito ya
zauna bakin gado ya yi addu'o'insa. Ya jawo mayafi
ya shiga ya rinka lunfashi a hankali, ya kurawa Mami
ido na tsayin lokaci, yana tunanin yadda zai kai jikinsa ga matarsa ämma yana kuma tsoron irin amsar
da za tai masa, domin har ya manta rabonsa da Mami,
kuma yana jin dacin kalmar da ta ga ya mai wadda
tasa ya yi fishi da ita, to amma dole ya hakura ya
neme ta tunda yau ga shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13