auren, ni da kai komi tare wanka tare
kawai zai shiga tsakaninmu amma ko wajen ofis ne
Hajiya za ka ga kafarka ga tawa, za ka san ka yi
auren cimgam! Sahabi ya yi zuru yana jin ta domin
29
zan cen ya yi mai dadı haka ya ke son su yi da
matarsa don haka ma ya tsani 'ya'ya da yawa, 'yar
yarinya 'yar kimanin shckara goma sha takwas ta yi
sallama ta shigo daukc da kayan ti flask na ruwa zafi
sai kofi da biskit short bread da ovaltine madara peak
milk da suga, kaida kowa ya san wa'annan sune
kayan tin Sahabi idan ya zo hirar dare. Da kan sa ya
hada tin domin yarinyar ta so ta hada mai amma ya
hanata. Ya soma sha, sannan ya ce, Mami ya dace, ki
matsawa iyana asa mana biki kin ga yanzu dai ta na
gari kada kuma ki sake ce man ta yi tafiya sai ta
dawo", ta ce, "Ka yi hakuri su sami natsuwa daga
bacin ran auren Rabi'a da Ali sannan sai su sa bikin
mu ko" ni ma ba zan so ace iyana ta sake yin tafiya
ba ba'a yi komi ba akan mu".
Ya bar Mami a wannan dare ya isa gidansa sha
daya da rabi na dare, ya kammala al'adun rayiwar sa
ya kwanta bisa gado ya jawo G.S.M ya aika mata da
text ita kan ta ta kasa bacci tunaninsa kawai take yi,
ta duba text din sa ta yi dariya ta sumbaci rubutun
text din da ke cikin wayar, sannan ta rubuta masa
amsa, bayan tafiyar ka kawu Abdukarim yazo daga maiduguri sun yanke lokacin aurenmu" ai ko ran nan
har karfe hudu na sulusu dare Mami da Sahabi ba su
yi bacci ba, sai da sahabi ya yi naci da kunata ya
tursasa Mami ya ji yaya aka sanya ranar bikin", itama
ta ja mai rai sosai sannan a karshe ta rubuta mai nan da sati uku cif ina nan manne da kai shikenan?
30
Da wannan ya rufe wayarsa yana murmushi. Bai
ma yi kokarin yin bacci ba sai yayo wanka da alwala
mai kyau ya zo ya soma aiwatar da nafila.
Kafin ma Sahabi ya kai ma Hajiyarsa labarin sa
ranar bikin su har iyayen Mami sun aika mata. Cikin
kwana ashirin din nan babu wanda ya huta daga cikin
zuri'ar su Hajlya Aisha Birnin Kebbi da zuri'ar su
Dr. Ahmad Shu'aib a Sokoto ba karamin shiri su ke
ma auren Sahhabi ba, haka nan mahaifiyarsa da
'ya'yanta anan kaduna. Can bangaren gidan su Mami
ma hakan sauran kwana tara akai Mami gidan sahabi
iyana ta tura mata wajen Hajiya Aisha a nuna masu
gidan da sahabi zai zauna da Mami Hajiya Aisha ta
sa Abba ya kai su Sullubawa road gidan da sahabi ke
zaune, tun Dr. Shu'aib na da rai ya gida gidan ya
kuma ce ya ba sahabi kyauta saboda hankalinsa da
irin kwazon sa a makaranta haka nan kuma yana jin
dadin ganin tun yana fan shekara shidda bai iya
sallah a gida sai a masallaci, harabar gidan tafi gidan
girma don haka nema da ya soma neman auran Mami
Hajiya Aisha tasa shi ya kara gina katon daki ya
bulla ta gaban dakunan bacci hudu, haka nan Hajiyar
tasa an rushe sito an hade da kicin an sami sabban
kicin saboda a cewar ta, shi ne yanzu uban 'ya'yanta
dole su rinka zumunci da iyalansa ga kuma zuri'arsu
ta sokoto dole ne girma ya hau kansa kamar yadda
mahaifinsa ya rinka yi zamanin ya na raye, ya kan
debo 'ya'yan kannansa kamar uku zuwa hudu ya
nemar masu babbar makaranta shi ne cin su shi ne
shan su, shi da ita Hajiya Aisha yanzu haka daga ace
31
wane ya zama director sai wanda ya zama lawyer ko
likita irin su ne kuna masu kula da zuwa duba Hajiya
Aisha shi ne a ganin ta in ba su shuka alhairi ba ai da
babu mai kula ta ita da 'ya'yanta. Sahabi ya ce, "Тo
Hajiya ina za mu samu sito kuma? Ta cire gilashinta
ta kara nazarin gidan ta ce a gina daga wancan korido
kaga daga sito sai a shiga kicin kenan. Tsarin ya yi
fasali sosai, bayan an kare gyare - gyaren ne za'a
soma fenti ya nemi Mami a waya ya tambaye ta wane
irin fenti take so? Ta yi murmushi ta ce, "Ayi kalar
motarka high blue" ya ji dadI sannan yace, me yasa
ki ke son kalar da na fi so? Ta ce, wallahi a lokacin
da muka soma haduwa a wajen shan ice cream na
dauki lokaci ina nacin son kara ganin mota mai
wannan kalar kila ko na dace na ganka, amma shiru
to sai kalar ta zame man ado a zuciya babu kalar da
ke burge ni sai ita.
To matan da iyana ta aika su gano mata gida sun
yaba gidan sosai babu ma dakin da hajiya tasa aka
kara ginawa girmansa yayi masu domin setin gado da madubi da ma'ajiyar kaya da akai ma mami oda daga China sai babban daki, don haka dakuna uku da falo daya suka nema, aka barwa Sahabi daki daya da falo.
Biki da daurin aure a maiduguri aka yi, tun ranar laraba su anti hadiza da yawancin yan uwa kamar su goma sha biyar suka isa maiduguri gida daya iyana ta aje ma su anti hadiza wato dangin ango, shi ko Sahabi da abokansa da yawa a guess house din kawu Abdullonr akai mnru ssesauki zan ce ne dai na 'yan
ilmi ta fannin ango da amarya don haka kowanne na
nima gwani nc, sai ko harka ta 'ya'yan banki suke ta
shan kanshi (NAIRA) babu wanda ya nuna gazawa
wajan bada hakkin aurc, bayan ka'idojin da
musulunci ya gindaya haka nan al'adun ma ba a bar
su ba, duk an cika ka'ida.
Yawancin 'yan biki ta jirgi suka dawo Kaduna
kamar ango su anti Hadiza sun yi hakuri sun biyo
motoci ne saboda dangin amarya masu yawan gaske
da suka nace da son lalle dole sai sun zo sun ga dakin
mami tunda ita ce diyar farko da aka fara aurarwa
gidan M.D Abduljalal, don haka sai da su anti Hadiza
suka tsaya suka ga kowa ya sami mota sun kuma biya
kudin motocin sannan suka baro maiduguri zuwa
Kaduna, ranar asabat kenan ran da aka daura aure.
Suma su mami gidansu aka sauke ta wato sultan road,
sai wanshekare ran lahadi su anti Hadiza da zuri'ar su
suka je bikon amarya. Zuwa gida Sahabi a sullubawa
road, wajen karfe tara na dare aka yi shirin zuwa cin
dina wadda ma'aikatarsu refinery ta shirya masa.
Wannan ina ta shiryu ainun Sahabi da mami sun
yi kyau kwarai matuka. babban abokinsa na kan-kan
ya gabatar da komi, ainihin tarihin Sahabi da yadda
soyayyar sa ta ke da mami, anan ne ma ya kwallawa
mami, kira ta ko yi har da ido ta firgita yayin da ta
amsa Rasa - Kasa na'am ya ce, "kar ki manta wannan
itace kalmar farko da Sahabi ya yi amfani a farkon
haduwarku amma Allah cikin ikon sa ashe ya kira
matarsa, gaba daya holl din aka tintsire da dariya
mami ta ji kunya ta dora kanta bisa kafadar mijinta
33
1
Sahabi ta cc, "yanzu Ab-kar haka ne ko? Ka fadawa
usman sarkin tsokana sirrin haduwarmu! Dubi yadda
ya firgita ni tankar yadda ka taba firgita ni a farkon
haduwarmu! Sahabi ya kwanto da bakinsa dai dai
kunnenta ya cc, "Ki man wannan hakuri, Usman ya
dau bashi amma zai ci...." Sahabi na lallashin
amaryarsa can daga sama, Usman ya kwallawa
Sahabi kira ya ce, "sahabi ina fatan za ka cika dan
halas ka ririta Mami sosai, domin tun a maiduguri na
lura Mami zinariya ce a gidansu, ina son ta zama
dayiman a gidanka, tabbas na san zaka iya, aka yi
dariya yayin da Sahabi ya rinka daga kai nuna
alamun ya amince, sannan ya ce, Mami kina daga
cikin mata masu sa'a a duniyà, idan har kin kula da
cikin sahabi da tarairayarsa insha Allah ba za ki ci
karo da matsalolin auren zamani ba, domin abokin
nawa runbu ne bai wasa da ciki", aka bushe da wata
dariyar.
Sai misalin karfe goma sha biyu da minta
arba'in, su Mami suka iso gida, bayan sun yi sallama
da jama'a. Suna isowa gida sahabi ya amshi G.S.M
din Mami ya manna su a caji.
Sahabi na da yaron gida mai natsuwa kuma
malami ne mai suna Ya'u, gyaran gida ya kan yi ma
sahabi sai wanki, amma ko soya kwai baya yi masa
sai dai ayo ma Sahabi daga gida, tun farko ya sanar
da sahabi jinsin gidansu ba su taba tukwanan girkin
mata, saboda haka sahabi na sa shi ko wanne irin aiki
amma ban da girki.
34
Da sassafe Hajiya Aisha ta turo dircba da Hafsat
da kayan karya kumallo kala kala akwai kosan
nama da fanken kwai da filawa ga soyayyar agade
sanna tasa Aisha (Auta) ta gasa masu biredi wanda
aka kwaba zalla kwai da bulu ban kana ci yana
narkewa a baki da zuma ma da 'ya'yan inibi akai
kwabin. Angon da Amaryar ba su fito falon ba sai
karfe goma sha daya da 'yan mintoci na safe, sun
kammala kalaci suka fada wanka sai gab la'asar
sannan suka fito suka iske Hajiyar ta sake aiko da
abincin rana shi ma kusan kala hudu ga sakwarar
doya sanna ga farfesun kifi ga kuma sinasir wanda ya
yi falan falan din nan ya yi gardI ko ba miya ba komi
za ka iya ci, sai kunun gyada wanda aka daure da
shinkafa, ya yi fari sol da daddare ma haka Hajiya
Aisha ta shiryo mau jerin kuloli tamkar masu cikin
mota. Kwana bakwai cur Hajiya Aisha na aika masu
da abinci safe da rana zuwa dare kala kala kuma
'yan'yanta Hafsa da Aisha sai 'yar aikinsu tinc ke
shirya komi. Ita kan ta Mami tasan cewa a gidansu ita
'yar gata ce, amma ta amince shi ma sahabi dan lelen
ne, wani abincin idan ta ci takan yi santi ta ce, "Abkar Hajiya na son shagwaba ni da cima da yawa, na
soma ji riguna na sun kame ni bana son kiba fa sosai,
sanin halin ku mazan zamani ba ku faye son mu yi
kiba ba ko" ya ce, very good korafinki na farko da
Hajiya ki rubuta an jima idan Hafsa ta zo sai mu bata
ta kai mata", ta ce "Lah! Ba haka ba ne, rufan asiri?
Wanshekare suka shirya ita da sahabi sai Sokoto,
a can din ma komi ya daure mata kai gidan sarauta ne
35
aoba rin ginin turawan zamanin da can, an yi ginın
a fidda sasse sassa. gidan anguwa guda ce, an yi
tsarin irin na sarakunan turaywan kasar faransa, sassan
Di. Ahmad ne aka baiwa yahabi a zamanin yana da
rai shi ne sarkın mahaifarsu amma anan sokoto su ke
zaune, sassan da ke kusa da shi na waziri ne kanin
Dr. Ahmad haka abın ya kasance masu abunda ya
Kara rikitarwa da Mami kai shi ne kowanne Kwai da
kwarkwata zalla 'yan ilıni ne gaba da baya kai ka ce a
zuri'ar su sahabi aka kirkiro ilmin zamani, ga su da
yawa amma kuma son junansu su ke tsakani ga
Allah. Ana shiyo masu abinci dare da rana da safe iri
iri daga gidaje masu yawa, amma kuma da wuya
sahabi da Mami su ci abinci su ka dai a rana, koda
yaushe 'yan uwa kan zo a zauna ana ci ana sha ana
kuma debe masu kewa sati daya suka yi a sokoto su
ka yi shirin komawa kaduna. kifi busasshe da kwai
har sai da su sahabi suka rasa inda zasu zuba domin
but ya cika fam da tsaraba. Wani tsohon kakan sahabi
ya aika akai kiran sahabi ana gobe za su koma yace,
sahabi nasa an yi man kiran ka ne saboda na aika wa Hajiyarka da kyautar sadaka har guda biyu nace a
baka amma ta kI amsa. wai zamanin mahaifinka ma
bai amsa ba balle kai ni ko a ganina taimako ne a
gare ka, kuma gatanci ne akai maka hakan zai sa ka
sami kyakykyawar kulawa, amma ina mutunci ku zauna da mace daya bayan kuna 'ya'yan manya masu daraja ai gara ku bari darajar ku ta fito fili; tunda ya soma zancc sahabi zuciyarsa ke 6ace bai taba jin wannan zance ba, tabbas yasan gudun ransa kada ya
36
Baci shi ne dalilin da Hajiyarsa ta KI sanar da shi, ya
yi na sanin zuwan su Sokoto tsoron sa daya shi ne
kada ma a daga maganar har Mami ta ji a tada mata
hankali a rikitar masa da kwanciyar hankalin gida,
don haka bai tsaya bata lokaci ba, ya cc, "Ai abunda
ba zai taba yiwu ba ne, wannan ba irin rayuwa ta ba
ne don haka ne ma Hajiyar bata ga ya man ba, don
Allah kada ma a kara yi man irin wannan tunanin",
Dattijo ya yi ma sahabi zuru shi a rudaninsa har yasa
an shirya 'yan mata biyu 'ya kimanin shekara goma
sha shidda shidda zai baiwa sahabi a matsayin
makulla, a ganinsa yin haka zai kura birgesa ya
daukakasa, amma sam sahabi ya Ki.
Ya koma gida ya cimma, Mami yau har ta yi
wankan dare ba tare da shi ba, ta shafa mayukanta na
'yan maiduguri wa'anda akan kwabawa amare
'ya'yan wanc da wane ta zizara turaruka a gaba -
gaba na jikinta, sai wata irin hoda mai kyau da tsada
da iyana ta sawo mata a saudiya ta shafawa fuskar ta
nan da nan fuskar Mami ta koma kamar kwan
lantarki, sai ya dauko kwarar maganin da iyana ta
bata wadda tacc, kullun ta sha kwara faya idan ya
rage saura awa daya su sadu da mijinta, da kofin ti
za'a sha, shi ma a saudiyan ta sawo mata. Rigar da ta
saka da ita da rashinta duk uwarsu daya uba daya,
tana zaune bisa kafet a dakin baccinsu tana kallon
tashar daya daga cikin na tauraron dan adam, wasan
kwaikwayo ake yi na rikin aure, ya dauke hankalin
Mami tsab, sahabi ya dawo tun daga hanyar falonsu
ya soma shakar kamshin amarcin Mami, bai taba jin
37
Kamshi mai tada sha'awa irin wannan lalle ya amince
muddun mace zata shafa irinsa ta fita ta ratsa ta
gaban maza tilas ta dawo gida ta yi wankan janaba
tamkar yadda ya zama tilas suma mazan sai sun yi.
Ya isa gare ta ya zauna dirshan a gabanta ya kura
mata ido babu kiftawa na tsayin lokaci sai da kallon
ya razanata sannan tasa baki ta hure mai ido, ya hade
yawu ya ja ajiyar raı, suka yi dariya. Yace, amarsu ta
ango kai Mami akwai wanda ya dace da angwanci iri
na? ta kada kai ta ce, "Babu domin naka na sani, ban
san na sauran maza ba! Suka kyalkyale da dariya ya
matsa jikinta sosai kamar zai hade ta lunfashinsu ya
hade suna anfani da iska daya, can ya ce, Anya yau
zan iya wankan nan ni kadai ita kam Mami ta soma
nuna don haka shiru ma amsa ce, ya nuna mata kauna
ta zahiri, kamar yanzu aka mallaka mai ita sun yi
soayya sun yi wasanni na lokaci mai tsawo, a kullun
suna kara fiddo salo - salo na zakulo sha'awa, hakan
ko na faruwa ne saboda masifar son juna da suke,
idan sahabi ya bullo wani sabuwar hanyar ya kan jira
ya ga yanayin Mami shin ta gamsu ko ta yaba? Lokacin da suka isa kaduna mangarib ta yi don
haka sahabi ya bada shawarar su wuce gidan Hajiya Mami ta ce "E ko don saboda mu aje masu wa'annan kaya su kifi", ya cc, 'Ai wa'annan na ki ne" ta ce
haba sahabi yaushc za mu yi amfani dasu, bayan ka ceji bi za mu wucc Bauchi State mu gama hutunmu"
to itama Hajiyar ganin kwan da kifin akwai yawa sai
ta ce, Mami a raba biyu mana ku je gida da rabi" Mami ta ce, "a'ah Hajiya ku bar shi kawai idan yayi
38
ma ku yawa ne ana iya kaiwa su anti Hadiza" to
abunda dai su Hajiya su ka dauka Mami mai son
zuri'ar mijintă nc.
A nan gidan Hajiya su kai dina su kai sallah anan
ma su kai hira sai can wajen karfe goma na dare
sauka nufi gida tare da Hafsat zata kwana a can.
Hafsat ita kadai ta mike da safe ta shirya masu
kalaci mai kyau toye toye kama kala uku daman ta
zo da yawancin kayan amfani da ga gida, ga ti ga
kunun tsamiya saboda sahabi wani lokaci ya kan so
koko da kosai ko kunun gyada ko kuma kunun
tsamiya. Sun fito daga dakin baccinsu daidai lokacin
da suka saba fitowa, Mami ta doshi tebirin cin abinci
ta cc, "wai Hafsat nan gaba sai kun sa an kara bude
man kofa in wannan gara" Hafsat cikin dariya ta ce,
haka mu ke so yaya Mami mun iya kiwo kenan".
Da rana ma doll man da farfesun kaji da kunun
zakI ta yi masu, amia da yamma Hajiya ta aiko da
hura mai kyau da Jamil yogot don haka sai harfsat ta
gasa masu naman rago wanda ta aikı Ya'u ya sawo a
anguwar Sarki. Gaskiya ko shi sahabi ya yabawa
Hafsat da kokarin da take yi na kula da su.
Wanshckare da safe koko da kosai mai kyau Hafsat
ta shirya masu a cikin kosan ta daga kwai ta yanyanka cikin kullin kosan, a idonka zaka iya
amincewa Rosai ne amma lokacin da ka ke ci a bakt
sai ka rasa ko menene don dadi.
Sha biyu na rana su kai shirin tafiya Bauchi,
abun mamakin sahabi da Mami shi ne lokacin da
hafsat ta soma fiddo masu kaya don Ya'u ya shirya
39
masu a mota sai ta fito masu da hadadden kek da
zafinsa ran ta nade da jarida ta saka a plastic roba mai
rufi, shi ma a kwabin kek din ya sha inibi da suga
hade da zuma irin dai wanda ba a ba yaro mara kunya
ga hadadden juice wanda ta zuba a kula ta watsa
Kwankara. Sahabi ya nunawa Hafsa godiyar sa a
zahiri haka itama Mami saboda sahabi mutun ne mai
son yabawa mutumin da ya kyautatawa cikinsa. Su ka
biya ta gida suka aje Hafsat kai tsaye suka dauki
hanyar Bauchi. Sahabi ke tukin motar Mami na zaune
ta gefensa dan kidan da suka saka na wakar 'yan
sudanis ne, kidan yana da laushi da sanyi a kunne,
sahabi ya lura Mami zata soma yi mai bacci sai ya ce
fiddo wayarki na ba ki aiki! Ta fiddo ya ce nemo man
usman abokina ki sanar da shi ga mu nan bisa hanya
zuwa gidansa" ta ce, haba don Allah dazu da safe fa
ka sanar da shi zamu zo, kuma kasan yana ofis ka bar
shi mana ya yi aiki". Sahabi ya juyo ya dube ta suka
murde idanunsu cikin idon juna ya rinka ransayar
mata da kwayar idonsa sannan suka yi murmushi ya
mikar da hannu ya shafi haßar ta ya ce, "Be a nice
girl kin ji" ta amsa cikin shagwaba da cewa da man
cen nice, ta nemo usman a G.S.M din sa, jin muryar
mace ya kara duba numbar sosai bai dai gane ba
yace, "Assalamu alaikum" a murtuke Mami ta kyalkyale da dariya ta ce, "Wai wanna fa ai kai ne ragon maza ka ke tsoro, 'yan matan zamani? Ko madam din tana kusa ne? ya dai cije ya yi 'yar dariya har yanzu bai gane mai magana yana kuma tsoron tambaya kada a kara yi mai
40
wata shegantakar, ta се,
Aa tabbata mijin ta ce, to Mami din sahabi ce" ya yi ajiyar zuciya ya bushe da dariya ya ce, "Ba kya da
laihi, laihin mijinki ne, za mu gamu kuma, ya kina
lafiya" ta cc, "lafiya lau, muna nan bisa hanya nan da
awa uku insha Allah zamu iso", ya cc, "muna zuba
ido, a ofis na ke na bar madam ta na shirin taryar ku,
ki buga mata ga wayar ta...." Suka yi sallama ta nemi
Husna matar usman lokacin Husna na cikin wani
super market wayar ta rinka kukan tsuwan mashin ta
6alle jakarta ta fiddo wayar sannan ta raße gefen da
babu jama'a sosai ta amsa "Hello Mami ta ce,
"Husna ni ce Mami" ta ce, lah amma kin kyauta da ki
ka neman, dear ya ce man yau za ku zo ko? Tа се,
wallahi muna kan hanya ma yanzu insha ALLAH,
ALLAH kawo ku lafiya don Allah Mami wane irin
drink ki ka fi so ne? Mami ta yi murmushi ta ce, haba
Husna, kowanne is okcy; ta ce, "Ai babu kunya
tsakaninmu; Mami ta, ce na fi son (eva) amma
pincapple juice Husna tace angon fa Sahabi? Tace,
wai shi wannan yana ganin ire - iren wa'annan ba su
faye damun sa ba in dai zai ga su kunun zakI mai
wadatattcen kayan kamshi ai kuma shikcnan" Husnata ce, "Ka ji sauran mazan jiya, to sai na cc Allah ya
kawo mana ku lafiya"
Ta amsa 'amin
Mami ta juya ta dubi Sahabi tana lumlumshe mai
ido ta ce, Ab-kar na ci gaba da bacci na ko na dai
kammala da sakonka", ya cc, amma bayyana man
aikan da na yi maki ba", ta ce, ka daure idan mun je
Zaka ji daga bakin mutumin na ka" ya yi murmushi
こ
ya ce, kai wannan idon na ki yana jin bacci da yawa gara na hakura da hirar yanzu ko na sami ta an jima,
Mami ta nade kafafunta tsab cikin kujera ya kara karfin A.C ko minti goma ba ta yi ba duk jikinta ya
saki alamun bacci mai nauyi ya dauke ta. Lokacі -
lokaci sahabi idonsa na bisa titi rabi yana kallon
kyakyawar matarsa wadda ya radawa suna Sleeping
Beauty tun wata ran a Sokoto da ya bata kimanin awa
daya yana kallonta yayin da ita ko take ta bacci, ya
rasa a wane yanayi Mami tafi kyau tana bacci ko idan
tana zaune ido biyu koko idan yana making love da
ita? Shi dai yana mamakin masoya, abinda
marubutan suka fi nunawa zamanin ma'aurata kan
dakusar da zumar amarci, to shi dai har yanzu bai ga
chanjin hali ba a wajen Mami, ko awa nawa zał yi
yana (makin love) da ita bata nuna mai gazawarta illa
ma ta kara karfafa mai gwiwa, sannan irin kallon da
take mai yana birgesa wanda kan dasa mai sha'awa a
rai, tun ranar da ya soma zuwa wajenta ta ke mai irin
wannan kallo amma har zuwa yau bata dai na ba,
haka nan abu daya ya fi birge shi da kara kaunar
Mami wato shi kadai take ma wannan kallon bai taba
ganin ta dubi kowa da irin wa'annan idon ba tamkar Mami na da rigar idon guda biyu daya tashi ce ta
musamman dayar ko ta ya ku bayi.
Sai da suka isa Bauchi ya latsa na'ura gilashi ya sauka kasa iskar garin Bauchi ta soma ratsa Mami a
hankali a hankali ta bude ido, ta dire idanunta bisa kan mijinta, shi ma na sa idanun sun yi jajur alamun gajtya da rashin isasshen bacci, don haka ya za6I su
42
je yankari inda za su huta sosai babu kowa balle a
dame da hira hatta wayoyinsu rufewa za su yi idan
sun so magana sun nema da kan su.
Ta mike zaune sosai ta gyara jikinta, ta се,
"Allah sahabi kai ma kana bukatar hutu kaga
idanunka kuwa, ya ce, yana iya! Ta dube shi cikin
yanga ta ce, ya ka iya kamar yaya? Ya ce, "ni fa
maigida ne yanzu nauyi ne akai na nauyi bisa nauyi
ko? Ta kai mai duka ta ce naugthy man ya ce, yau dai
ba za mu iya wuce wa yankari ba ko? Ta ce, "Don me
ka daure don Allah, ko Usman ya baka aron direba ya
kai mu ya dawo, bana son kwana gidan mutane" ya
ce, gara ko ki saba, domin 'yan uwana za su so ki je
ki kwana haka ma amine na.
Mami na jin bayanin Sahabi amma dai abinda
zuciyarta ke raya mata da ban, ita a ranta ta dauka
babu yadda za ai ta sauka gidan su tare da Sahabi har
kuma ta hole rayuwarta bayan akwai masaukan baki
wato (Hotels) barkatai ko ina a duniya, ta danne ma
zuciyarta bata ce ma Sahabi komi ba.
Usman na tsaye bakin matakala ta biyar a kofar
shiga gidansa ya rungume yaransa Fesal mai kimanin
wata shidda, ya tarye su da murna Sahabi ya amshi
Faisal ya yi masa dan wasa sannan ya mikawa Manir
yaron, suka isa falo, a nan ne Husna ta bullo daga
kicin tana tafi da hannaye cikin murna ga waka tana
Oyo-yoyo! Suka zauna ana ta barkwanci da gaishegaishe irin na abokan da ke son juna, anan kuma
Husna ta mike tace, to a bani makullen motar ka
Sahabi a kwaso kaya, a nuna ma ku dakinku saboda
43
bakarta shiga kewaye ko? Nan da nan Sahabi ya
firgice a tsorace ya rinka satar kallon Mami, da gani
dai kasan ya na tsoronta ne a bisa wani abu, sai yace,
An ya! An shigoda kayan nan kenan ai sallah kawai
za mu yi mu wuce yankari. Usman yace, Haba Sarkin
angwance, wane kai, wallahi ba ku isa ba, ku hana
man mata zama ta huta yau yini tayi hidimarku amma
ku ce wai ba za ku yi mana kwana biyu ba, banda
wanan ma mitin mu ke yi amma dole na tkaura
ma'aikatanmu na dakatar da mitin din a dalilin
zuwan ku.
Sahabi ya yi sukuti ya rasa madafa, ga dai
gaskiya kiri-kiri yana ganin Usman ya fadi sannan ga
gajiya likis ya yi amma kuma a fuskar Mami taki
bashi hadin kan da zai ba Usman amsa ya nuna shi
ma magidanci ne ya jure yayi hikima yace, bari dai
mu yi sallah sannan mun ga ya ma ku komi kenan".
Husna ta shige gaba ta nuna masu sassan baki
wanda kawai nisa tsakanin zuwa na su dakin, ta
koma falo gurin mijin ta suka dubi juna su kai dariya
wadda kawai magana cikin dariyar su. Dakin da aka
ba su kawai kewayen wanka da na bayan gida, dakin
tafkeke ne, ya sha kayan shimfidu na alfarma, sai
kamshin Ambi pu (room freshner) ya murde da
sanyin A.C. Sahabi ya lura da dan karamin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 13