Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gata, to amma idan ta ki yadda fa, ta kara gaya mai bakar wadda tafi waccan? Ya, nisa ya mikar da kafarsa in da Mami take a nan ya yi karfin hali ya murde kafarsa da ta Mami, bai san lokacin da ya ji sanballelen hannun Mami bisa tsakiyar kansa ba, haba nan da nan Sahabi ya manta gaba daya Mami ta taba bata masa rai sun yi, (making love) kamar ran farkon aurensu, ko kuma muce lokacin zuwan su (honcy moon). 89 An yi na farke an yi na biyu an yi na uku, sannan aka soma kiraye-kirayen Sallah, amma abin mamaki har a lokacin sun kasa sakin ransu, saboda ba wanda yace da dan uwansa kanzil. Da safe sahabi tare da Usman suka je masallaci,a nan ne Sahabi ke cewa, karfe nawa ku ke son kalaci Usman? Ya amsa, gaskiya bacci mu ke ji za mu fito irin wajen karfe goma da 'yan mintoci insha Allah Sahabi ya ji, dadin hakan saboda shima amarci danye bai bari sun sami bacci ko ba komi zuwan su usman sun sami lada. Mami Maganar farko da sahabi ya soma yi ma itace da misalin karfe tara na safe ya ce, mami kina da baki fa ya dace ko dankali da kwai da agade a soya masu bai dace mu kai masu ruwan ti ba da kke sai burodi, kin san dai yadda suka karramamu lokacin zuwan mu gidansu a Bauchi. Mami ta ki tsinkawa ya ce, Ba ki ji an ne? Mami tace, in naji me zance, ka san dai bazan tashi zuwa kicin ba yin girki don kawai na birge Usman da Husna, ka sanarwa da kiristi mana ni gaskiya kana fa takura man, Sahabi ya yi shiru yana tunanin wai mace zata iya fadawa mijinta takura, don ya sa ta aiki? Shin yaya ma matan yau za su hada kan şu da matan da, har su yi sha'awar samun kwanciyar hankali irin na matan da! Kai lalle wanan rashin da'a da tarbiya ta Mami ta isa, amma dai ya san sauran matan abokansa da 'yan uwansa ba hakan su ke ba, wannan dai rashin sa'a ce ya yi. Ya mike ya jawo jallabiyarsa ya saka har ya kai bakin kofa Mami ta ce, haka kawai a hana min bacci 90 1 1 S sannan ace mutun ya tashi wai ya yi aiki, ta yi kwafa, ya juyo ya ce, rashin kunyar ta isa haka! Ta juya kawai ta kara rufe jikinta. Ya shiga kicin in da kiristi ke zaune tana shan shayi da biredi ta yi sauri ta aje, ta mike, tace morning uncle, ya ce, morning ya danne zuciyarsa da tsanarta akan warinta don ya samu ya fita kunyar su usman, ya ce, ta dauko deep fryer ta dauko ya ce ta san yadda ake soya dankali a ciki tace E Hafsat ta nuna mata, ya yi farin ciki da hakan, nan da nan yace ta fere dankalin, ta soma fira cikin sauri, ta harhada ya dawo falo yana duba jarida, a nan Usman ya fito, sahabi ya koma kicin ya ce, ta fara soyawa mana, haka ya rinda zirga-zirga kicin zuwa falo, har abin ya tsorata Usman ya koma daki suka yi dan kuskus da matarsa Husna, Usman bai sake fitowa ba sai da sahabi ya kwankwasa masu kofa, ya ce ku zo kalaci ya kammala, Husna da Usman suka fito cikin shiga ta alfarma sun yi adon su na dai-dai su har sun kusa kare kalaci sannan Husna ta ce wai ni na ji gimbiyar shiru, kamar ba ma'aikaciya ba? Usman ya ce, ina ruwan ki ke zamanin amarcin ki wa ke matsa maki suka yi murmushi yayin da sahabi ya saki 'yar gajerar dariya, haka nan ya rinka cusa abincin ba don yana jin dadin sa ba. Sun koma falo ana hira da kallo tashar CNN ana tattauna labarun da ke guda na Sahabi ya mike ya koma dakin Mami ya shiga kewaye ya yi wanka, har a wannan lokacin Mami Abduljalal bacci mai nauyi take yi ya shirya tsab ya fito, suka shirya shi da 91 Usman za su masalalci sallar jumma'a kasancewar ranar juma a, daman hutun (good Friday) su Usman suka zo domin ga (weekned) sannan (Easter Monday) kuma ranar talata da laraba Usman yana da mitin a nan Kaduna don haka suka zo da burin su kwana bakwai a gidan Sahabi. Daga masallaci sai Usman ya ce mu wuce gidan Abu Said mu kwashi gaisuwa kada na yi laihi, Sahabi ya dauki kan motar zuwa gidan Abu Said, Sahabi yace, kira shi ta G.S.M dinsa don mu san inda ya ke Usman ya nemo Abu Saida ka gaisa ya ce yana hanyar shiga gidansa ne ya dawo daga masallaci, Usman yace mu bisa hanyar zuwa gidan na ka mu ke. Ya yi muma gami da godiya. Yana isa gida ya rafka kira Zainab ta amsa 'na'am' ta shigo ta tarye sa ta amshi sallatiyar da casbaha daga hannunsa tana you are wellcome Dear! Ya shafi kafadarta yace, na gode abokiyar, suka yi dariya, yace me kika shirya mana, ina sanar da ke. muna da baki su Usman na Bauchi ne da Sahabi bisa hanya daga masallaci suma suka fito kinga kuwa ai ya dace su ci abinci a nan, cikin murna da rawar jiki ta ce, kwarai, kwarai ko dole ma su ci abinci a nan balle ma Usman! To me kika dafa? Tace, sakwara da miyan agushi, akwai doya bisa tukunya yanzun nan zan zuba cikin injin na hade masu sakwarar. Suna isowa Zainab ta fito cikin faragat ta tace, ai ni Sahabi kai daman na aje ka a gefe na lura ba za ai zumunci da ku ba, amma kai Usman yau ni da kai, wai ace mutuniyar na gari Husna baza a kawo man 92 1 Γ a r T a :i ita ba, ka sani lalle zan fa rama! Usman yace tsiya ta da ke kenan surutu caca-caca kamar ku, ba kya jira ki ga mun bar garin bata zo ba, kin san abinda ma Husna ba za ta iya ba kenan, Sahabi ya ce, ni wallahi saboda kai na zo amma tsoro na Allah tsoro na kaifin bakin Zainab, Usman ya ce, duk kaifin bakin ta bai hana mutumina kawo amarya, aka tintsire da dariya Zainab ta ce, ina da yaya na Ibrahim mai rike man kofa ranar da za ku shigo da amaryar; Sahabi ya ce, dan wannan saunan yayan na ki ba sai Abu ya yi aure sau biyu ba bai rike maki kofar ba. Ta koma kicin tana dariya ta shiga shirya masu abinci yadda ya dace matar kirki kuma 'yar manya ta yi ba masu hali irin na Mami Abduljalal ba. Allah ya gyara mana zuri'a. Sahabi dai yana dai cin abin cin ne kawai don yana jin yinwa amma saboda zullumin sun bar Husna a gida bai san yadda za ta kasance ba ko Mami zata mutunta ta har ta samar mata abinci? Don haka bai kula da dadin abincin Zainab ba, saboda matsalar da ke gidansa tunaninsa dai kar a wulakanta Husna kamar yadda aka saba yi mai ko 'yan uwansa. Kamar Zainab ta san damuwar sahabit ace, wai Usman a nan gidana Husna zata kare hutun ko? Usman ya yi dan murmushi ya dubi Sahabi ya ce, ga mai masaukinmu sai ki nemi alfarmar a wajensa. Sahabi yace, 'Ban da wannan hutun ki hakura sai (next time) Abu Said ya ce, To sai ku yi masu waya su zo nan yau Zainab ta shirya mana dina ayi hira sosai, kao da yaushe mu rinka tuna tare mu kai good Friday na wanan shekara. 93 Usman yace, wannan shawara ce mai kyau sai dai abinda za'ayi shi ne za mu koma da la'asar mu taho da su, domin kawai alkawarin za mu gayas da Hajiyar Sahabi da la'asar saboda haka ku saurare mu muna zuwa anan za ai dina, Sahabi dai zullumi ya cika mai rai ko ya zai kare da matarsa wadda bai iya lankwasawa, sai yadda ta so ake yi, shin zata yadda ma kenan ta zo gidan Abu Said? Karfe uku da rabi suka isa gida, tuni zuciyar Sahabi na ta dagawa sannan bakinsa ya mutu murus, zullun kada Husna ta shiga wani hali. Usman ne a gaba Husna na kwance bisa doguwar kujera, kasat din bikin su Sahabi da Mami ne a video suna kallo da kyar sahabi ya yi ta maza ya ce, ina mutuniyar fa Husna? Ta amsa ta shiga daki fiddo man kaset na 3 gaskiya Sahabi bikin ya yi kyau, ka sanni ban je Maiduguri ba sai Dear na ku ka dauke? Usman ya ce, sai ki jira Mami ta haihu ba ku ne yan zuwa Maiduguri suna ba a daidai nan Mami ta fito ciki da irin rausayar ta, jikinta irin jallabiyar nan ne mai hula fara ce sol, an zizara zare daga bakin hular zuwa wuyan hular sannan aka saki sauran zaran yana reto bisa kirjin Mami a bakinta ta fante sa da janbaki jawur sai bakin ke walkiya, cikin fara'a ta ce, tsiyar me ka ke man Usman na ji kana anbaton Maiduguri? Ya ce, wai in kin haihu mu ke magana, ta dan kada halshe ta ce, Haihuwa rufan asiri don Allah sai a wannan lokacin Sahabi ya dan saki ran sa, har ya iya dariya shi ma ya tsoma bakinsa, aka ci gaba da tsokanar Mami. A nan Sahabi ya duba agogo yace, ya 94 dace mu yi sallah. ku an fa gayyace mu dina giden Abu Said, ya fi zuba idonsa akan mami bata nuna alamun yin musu ba ko muzantashi wannan ya kara mai karfin gwiwar cewa mami ko ba komi tans kaucewa bakin mutane wato bata son ta nuna mai rashin kunya gaban mutane, don haka tun daga wannan lokaci ya rinka sakin jikinsa yana magana da tai da tursasata abinda ya ga dama, amma in sun shiga daki ya ci kaniyarsa. Sun kasance a dakunansu ana tsalo ado irin na 'yan boko 'yan zamani, Sahabi ya rinka kallon Mami ta madubi alokacin ta sunce tana kokarin zuba wata rigar dinkin Mali kamar ya je ya rungume ta su yi wasani ta bashi sha'awa amma yanayin fuskar ta nana shi shi ma dinkin na shi na 'yan malin ya zuba ya so yace, mata za su biya ta gidansu amma ya kasa sai dai yace me kika ba bakuwar ta ki Husna? Tace abinda na saba ci shi ta ci, ya ce haka ne. Sun fito su Husna na sha'awar su Mami su mami na sha'awar su Husna aka yanke shawarar ayi anfani la mota daya, Mami bata so ba amma ta jure, a motar le Sahabi ya ce, af Mami z amu fa biya ta gida Jsman da Husna na son gaida Hajiya ta, gabanta ya adi ras rabon ta da 'yan uwan sahabi balle ma Iajiyar har ta manta, amam da tun a daki Sahabi ya i mata maganar wallahi da ta san yadda ta yi ta soke uwan ga wannan kutsigaggar Husnan, shine tunanin nami amma a hili sai tace, 'Eh ai ya yi dai-dai. A falo gaba daya 'ya'yan Hajiya Aisha ne va'anda ba su yi aure ba suna zaune suna kallon 95 kaset din Ahmad Didat ana ta mahawara su Sahabi suk. shiga, sanin Usman ya zama fan gida don haka Husna ma an san ta a gidan nan da nan su Hafsat da sauran 'yan mazan akai ta cewa yau ga su adda Husna Hajiya ki fito Aisha yar auta ce ta je ta rungume Mami wannan sai yasa Mami ta ji karfi ta rage faduwar gaba, Hajiyar ta fitot ace A a'a mutanne Bauchi ne yau Husna sannunku, Husna ta mike ta koma kusa da Hajiyar ta zauna kasa bisa kafet tana ta kwantar da kai tana gayas da Hajiyar, ita kam Mami tana zaune a inda take ta rinka sunne fuska jikin Aisha (Auta) ta gayas da Hajiyar, hajiya ta ce, Mami na yi hushi kwana biyu gaisuwa ta gagara haba Mami! Wannan ya wanke zuciyar Mami fes, tace, Allah Hajiya ba haka bane wajen aikin mu ne an takura mana,s aboda biyan dalibai kudadnesu, ta ce, to na yadda na amshi wanan hanzarin, Usman ina labari? Ya ce, hajiya yana nan kamar yadda ku ka san shi, tace ina aka bar mai gidan nawa, Usman ya ce, yana can gidan su Husna ai Hajiya Satinsa biyu kenan da yaye, tace, masha Allah, Allah shi raya sa, sai mu hada manshanun yaye kenan, yaushe ne tafiyar taku? Husna ta ce, sai wajen rana ita yau; Husna kamar za ta kwantawa Hajiya kuma ta manne a jikinta don iya hila da biyayya, to haka aka neo su a gidansu babban gida, kuma gidan 'yan ilmi duka biyun, sannan samun duniyar ma akwai shi. Shi ko gogan ko jin dadi ne koko shagwaba ce oho, sai ya zauna a gaban T.V ya hada T.V game yana ta 'yanw asanninsa, Hafsat ta hado masu kunun 96 a zaki ginger drink ga wani irin cincin mai narkewa baki kowanne ci yake bai son bari, har dai Husna ta kare tace, wai Hafsat in ce ko ke ki kai wannan cincin din? ta yi dariya tace, E tare da Hajiya mu ka yi, ai ba wuya anti Husna da bread maker muka kwaba, amma kwabin da man gyada ko man kakidi zalla ake kwabawa ba'a zuba ruwa ko kadan, Usman ya rinka cika baki yana jin dadin Husna na koyon yadda ake yi shi ko goga na Mami sai 'yan mazurai ya ke yi, komi kwadayinsa bai da hali ayi mai a gida haka nan ba hali ya zo gidansu ya ci abinda ran sa ke so. 97 ami tafi kowa murna da jin za'a tashi a tafi, M saboda ta san dai su Hafsat da Abba sun canza mata ita ma Hajiyar tafi jin dadin ganin Husna da yawaita fara'arta ga Husna amma maganar da take yi da mami duk iya duniya ce da nuna manyance kawai a can gidan Abu Said din ma duk duniyan cin ne da iya salon zama da jama'a ke ta gudana, idan Mami na ganin beken Husna to Zainab ma tafi Husna kwainana, ita ba wai bata son sahabi ba ne ko bata iya nuna masa kula a'a ita a isar ta da irin tarbiyar sai dai ai ta lele da ita tamkar 'yar gwal rayiwar gidansu wadda akai masu koyi. Kamshi na dukan kamshi sannan ga kamshin abinci kala-kala daga can gefe ta kunna masu C.D wakar na fidda sauti ahankali amma a fassare wakar ta ma'abota bege ce, zuciyar kowanne ta natsu ta cika fam da nishadi, Usman na wurgawa Husna kalo na Kauna saboda jin dadin wakar shi ma Abu Said har murza tafin kafarsa ya ke yi bisa ta Zainab, ta rinka mai rausaya da ido, Sahabi ko ya kan yi ma Mami kuri da ido can idan ta lura kallon ya yi tsanani takan lunshe nata idon su yi luw gaba daya shima sai kwayar idonsa ta ntise, su shiga wata duniyar ta daban. Bayan an ci an yi kat ne Abu Said ya bude masu wani hili mai wadatatciyar iska, launin hasken ya na canza kalar jikin mutun, Zainab sai ta matso da C.D ta karo karar yadda zata zo masu kunnuwansu, kowane ya nitse cikin kujerar kwando manne da matarsa, in da za ku ga Sahabi da Mami a wannan 98 lokacin mutun ba zai taba son ya dauko idonsa ba akan su, domin sun birge sun kuma kayatar. Kowane zanc e ya ke a hankali da matarsa, dole Sahabi ya shiga nuna ma mami gaskiya, yace, mami na nuna maki iya kar gaskiyata a bisa kauna ta a gare ki amma wannan bai sa kin ban hadin kai ba, sannan na lallashe ki don dai kada wata 6araka ta shiga gidanmu har mutane su sami abin tsegumi akan mu anan ma Mami kin ki, na soma yi maki wa'azi kin nuna man haukama na ke, shin don Allah Mami me ki ke so na yi maki don ki zama mace mai da'a a gare ni, don Allah dubi su Usman da matayensu Mami fadi abu daya wanda aka fi mu amma ako da yaushe suna masu bin ra'ayin juna, dubi wannan dinar a matsayinki ke ya dace ace kin shirya kin gayyato abokaina da na ki amma sam Mami kin ki kula da wannan nauyin da ya hau kan ki. Mami dukan kirjinta ya na tsakiyar hakarkarin Sahabi duk dan wani motsi idan ta yi cikin jikinsa take matsawa, tace, ka ji irin abubuwan da kan hada ni da kai, ba ka da ra'ayin kan ka sai na wasu, daga yau ka debo man ra'ayin su Anti hadiza sai kuma ka ce na yi koyi da su Usman ina ruwanka da wasu, ka hakura da ni mana da irin ra'ayina in dai har da gaske kana sona, wallahi lokuta da dama na kan zauna na damu akan cewa son da ka ke man bai cika zuciyarka ba, domin sai na ga ina ruwanka da ra'ayin wasu balle har ya dame ka? Sahabi ya ce, mami babu abinda na kan nema gare ki na rasa illa son naga mun mayas da gidanmu 99 n an mutanne kwarai wannan shi ne, ta ce, kai dai venru na gane kai mutun ne mai son fitina akan abinda bai isa ayi magana kan s aba, yau haka na Neiwa Ya'u N1,000 ya yi mana (take away) ni da Husna kuma muka ci muka koshi babuw ata damu waba mu kuma shiga wahala ba, amma da kana gidan tabbas sai ka Bata man rai. Sahabi ya ma rasa yadda zai nunawa Mami abinda ya ke so ta gane amam ya rasa, ya kyale ya bar komi a hannun Allah shi zai masa magani. Misalin karfe goma sha daya da minti arba'in da tara an dare suka bar gidan Abu Said zuwa gidan su Mami ba su bata lokaci ba kowa a gajiya suka nufi dakunan bacci. Da Safe Sahabi ya riga kowa tashi ya baiwa Kiristi umarni sannan ya aiki Ya'u (bakers Delight) a hado masu kayan kalaci. Har tsayin kwana uku Husna da Usman na kallon abinda ke guda na a gidan Sahabi mami dai ba a cewa matar aure ce, ko alama dag ani sahabi na samun rashin jituwa tsakaninsu, bayan ramar da ya yi Sahabi gaba daya ya sukurkuce. Da la'asar Usman da Husna a dakin da akai masu masauki suna tattaunawa game da zaman su Sahabi ya ce, wai don Allah me ke jawo irin wanan matsalar ne ta rashin zaman lafiya ne don Allah, dubi irin masifar son junan da su ke kafin su yi aure haka bayan sun yi auren, kuma wallahi a iya sani na Sahabi mutun ne mai son farantawa jama'a to balle matarsa haka nan ya faye saukin kai, yana kuma da hankali kuma bai da son kan sa, ina tababtas maki Sahabi yaro ne natsatse tun zamanin samartakarmu 100 bai shaye-shaye, ko irin 'yan neme-nemne matan da muka yi wato na tashen balaga zamanin samartakar jami'a kin san Allah Sahabi yarinyarsa daya ce tak na san dai an ce a canada ya yi 'yan mata kamar kala biyu ko uku, to a zamanin nan a sai mu ce su Sahabi sune waliyai, amma saboda Allah me zai sa yarinyar nan Mami ta yi mai raini irin haka, itama kuma an ce diyar manyan mutane ce, shin me ke damun ta ne? Husna ta dauke hannunta daga tagumi ta ce, kasan Allah Dear na karanci Mami bata tare da komi sai tsabagne rashin da'a ga sangarta, irin yayan nan ne wa'anda ba'a sa su ba'a hana su,s annan kuma ba a koyar da su ba sanin darajar dan adam saboda haka ana shan wuyar zama da su gidan aure, ire-irne su ne ka ke jin an ce aune bai yin shekara ya mutu, yanzu jiya na fita zani falo kada ka so ka ji rashin kunyar da na ji tan ayi mai, sai na yi sauri na dawo daki domin na lura Sahabi a firgice ya ke baya son kowa ya gane halin da suke ciki, a gaskiya dear mu bar gidan nan a yau kada mu tada wata kurar koko? Yace, Nima shawarar da na yanke kenan, kuma a hotel za mu koma saboda komawar mu gidan daya daga cikin abokanmu tamkar tona asirin gidan Sahabi ne, tow ai maza kuma fa wa'anda suka sa mu reno irin na mami ya rayiwarsu ta kan kasance? Husna ta ce,w ai wai ka ji bala'in ai matar da ta auri namiji mara tarbiya ta bani, komi a sakarce bai san darajarta haka nan bai san darajar diyansa ba, lokuta da yawa matar ce zata zama mijin, amma duk a banza bai iya hasalawa kan sa komi, in ma an yi sa'a ya yi ilmin ya yi kwance a 101 D gida yace aikin ma bai yi, koko ya yi aikin albashin na mashaya ke hannun matan banza, kai sharrin irin wa'annan mazan ya fi na 'ya'ya matan yawa domin ita Mami yanzu idan Sahabi ya rike auransa gam addu'a da fada mata gaskiya sannan idan sun yi 'ya'ya ta shiryu a bisa dole. Sahabi na kofar gida a harabar gidansa zaune bisa kujera yana karanta mujalla, Usman ya fito ya iskos hi, Sahabi ya ce, AU na yi zaton baccin rana kake yi, yace, A'ah hira muke yi da Husna, Sahabi yau mu ke son ci gaba, Sahabi gabansa ya fadi, amam ya yi murna da hakan saboda yanzu Mami ta gamamai wulakanci akan zaman su Usman da Husna, yanzu haka ta fice gidan bai ma san inda ta yi ba, ya dan yi yake yace, in ce ko lafiya? Usman ya dafa shi yace, Sahabi kada ka ji komi wallahi I m your best frined, koda yaushe ina tare da kai, koma mnee ne ba ni da amini kamarka, ina son kaci gaba da zama namijin duniya irin ku a kullun sa'a na tare da ku, babu komi tsakanina da kai sai yaboda alkairi,z an ci gaba da nemanka ta waya. Ya'u ya fiddo da kayan su Usman da Husna ya loda a but din motarsu, Usman ya baiwa ma'aikatan gidan kudi kyauta sahabi ya shiga motars aya bi bayan su yana yi masu rakiya har (Halal Fountain) wani hadaddne hotel ne tamkar kana kasar turai, a nan akai ta gadaddami wajen biyar kudi, saboda sahabi ya ce shi zai dauki nauyin biyan komi da komi amma Usman ya ki ya ce, hidimar da kai mana wallahi mun gode har cikin ran mu. 102 Sahabi ya dawo gida ya yi kwance af alonsa yana rike da remote din labulensu ya matsa ya rufe sannan ya matsa ya bude, zuciyarsa na cike da sake-sake, wato yadda 'yan uwansa suka fara tsarguwa da halayyar Mami, to ga manyan aminansa irin su Usman sun fara guje masa saboda wani dan kalilin dalili, duk iya tunaninsa ya yi yadda zai warwarewa Mami kwalwarta ta zama macen kwarai amma ta ki, ya nisa ya dag akai ya dubi agogo karfe tara da rabi na dare, amma wai Mami bata dawo gida ba abinda bata taba yi ba tunda su kai aure, sai dai idan tare suka fita, amam yau don nuna mai garari shiru. Goma saura 'yan mintoci ta yi sallama ta shigo ya amsa, a sanyaye, ya yi kokari ya gaya mata magana amma ya danne ransa akan dole ya kyale ta ta gama 'yan bige-bigneta ta shiga daki ta kulle. Sahabi ya jima kwance a falo kusan mamu ce nan ya kwana, cikin kunci da dacin rai, saboda sai karfe hudu da aka soma kiran salah ya mike ya je ya yi alwala ya zo ya soma jera nafila. Da safe ma bayan ya gama abubuwan da ya saba rashin abin yi sai ya nufi ofis ya ko jima yana aiki, aikin da duk ya dauke masa wani tunani tunaninsa. Ita ko Mami a daren jiya gidan su ta je, ta mike kafarta a irin rayiwar da ta bari a zamanin 'yan matancinta, ta sami kwanciyar hankali har ta rinda jin tamkar kamar kar ta koma gidan mijinta Sahabi, har sai da mahaifinta ne ma ya fita harabar gidansa ya hangi motarta sannan ne ya shiga falon da ake zaman Shashanci ya ce, mami Sahabin ya je Sokoto ne ki ka 103 bar gidan na ki kika zo nan ki ka zauna? Ta ce, A'ah Baba yana nan, wasu abokansa ne suka zo daga Bauchi shi ne ba su zama gida, Abduljala ya yi dariya ya ce, a yi haramar zuwa gida wannan ai ba dalili ba ne, ta mike ta hau sama ta yi ma iyana sallama ta sauka ta ja mota cikin dacin rai ta nufi gidan sahabi, wanan yasa mami tasa wa fanta ta canza rayiwa zata rinka zuwa gida tana sheke ayarta zaman auren kuma ko oho! Allah shi daidaita mana zuri'a. Yawancin aboka su Usman tunda suka ji labarin cewa Usman na nan Kaduna suke nemansa su sada zumunci, da kyar ya bada hadin kai aka san suna Halal Fountain saboda tsananin kamun kai don bai son a san cewa ya bar gidan aminansa na kut da kut, sun iske shi a canw ato su Abu Said da Sani da Garban Zariya a nan Abu Said ya nuna amsu jin zafi zahir, ya ce, haba Usman yadda muke ace ba za ku sauka a gidan mu, sai hotel, me ye za fi hakan duk wani boye-boyneka kallonka mu ke, kai ne bako amma mu mun san halin da gidan Sahabi ke ciki, kai ma tun farko rashin sani ya kai ka sauka gidansa, Garban Zariya ya ce, duk cikin mu abokai ba mai hakurin Sahabi amma Allah ya hada shi da yarinya mara tarbiya abu daya ke damun Sahabi shi ne ya taye son ya kyautatawa jama'a, Sani ya ce, ga kyauta abun hannuns ana jama'a, idan Sahabi na da dubu goma cikin aljihu so ya ke ya ga ya kashewa wa'anda suke tare da shi su ji dai dadi yauwa! Amma yarinyar bata son kyautatawa mutanne Sahabi, Abu Said yaа ce, shi kansa Sahabin a dage take kallonsa; Usman ya 104 ce, abun da ya fi damu na ma daya ne Sahabi mutun ne mai son raya cikinsa, shi dai ya ci abinci mai kyau ya koshi, mahaifiyarsa saboda shi har mu sai an shirya mana kykakyawar walima amma yau Sahabi sai dai kullun ya aika a sawo, wanda bai saba da hakan ba, kuma bai son ayi zancen matsalar gidansa balle abashi shawara, sani ya ce, Ai kasan runbu na sa mai a makaranta, Ibrahim din Abuja ne ke kiransa mai cikin zani, suka kyalkyale da dariya, Abu Said da Usman ya ce, Ni

Chapter 7 of 13