Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani irin mummunan tashin hankali sbd gari kam an gama cinyesa wutar ta kawo gurin su sosai dan haka yake tsananta gudu. Gida ya nufa da tsananin tashin hankali sabo sbd dai dole yabar garin da yayansa sbd kowane lokaci zaa iya kashe su ko kamawa sbd wutar harta fara shigowa gidan nasa sosai. Yana shigowa ajiye gawar Amma yayi daga gefen dakin ya fizge rigarsa ta sama me dan kaurin saqi ya rufeta da ita. Ihun shigowan mutane dake Neman hanyar tsira ne da Ihun wainda wuta ke ci ne ta cike gidan nasa dan haka da gaggawa idanuwansa jajir fuskansa duk jinin Amma daya dauko koina ya bata fuskansa hakama hannuwansa da jikinsa koina jini ne. Tura kofar dakin yayi da karfi Wanda ya saka dukkaninsu miqewa tsaye cikin tsananin firgici da tsoro, Nurat ce ta fara cewa ‘ABAA’ cikin mummunan tashin hankali Tana nufosa da gudun gaske ta fada jikinsa. Abaas ya miqawa hannu ya Kama ya janyosa hakama Zuhrah koina jikinta wani irin mazari ya dauka ta fara ja da baya tana fita hayyacinta, Ayanah ma jinin jikinsa da fuskansa take kallo Tana kasa hawaye ma sai rawan jiki da jajayen ido, Fizgo Zuhrah Abaa din yayi yana cewa Ayanah ‘Muje,ku fita da sauri,Kuyi sauri ba lokaci’ Daqyar Ayanah ta iya bude bakinta daya bushe qayau sbd masifar tashin hankali tace ‘Abaa Amma bata nan,taje nemanka, Ina zamu ba tareda ta dawo ba? Qin kallanta Abaan yayi ya Kamo hannunta itama da karfi ya fito dasu Sauran mutanen da zasu samu kubuta tareda su suna biye dasu. Nurat dake da kokarin wucewa kaman ance ta juya idanuwanta suka sauka akan gawar Amma dake shimfide fuskanta kawai ne a rufe abin hannunta ta gane take ta tsaya cak tareda cewa ‘AMMA’ cikin wani irin sanyi da mutuwan jikin kasa yadda. Ayanah ce ta kalli gurin da sauri itama Tana Jin jininta na Neman kafewa, Abaas ne ya kwace daga riqon mahaifinsa ya nufi gurin da gudun gaske yana isa ya yaye rufar take ya some a gurin, Nurat ma silalewa tayi a gurin some sbd kasa dauka da zuciyar su tayi Ayanah ma salalewa qasa tayi zuciyarta na Neman bugawa ganinta yana disashewa Abaa yayi saurin dagota da karfin gaske shima zuciyarsa radadin gaske take kaman zata Dena bugawa amma sbd su bazai iya karyewa a lokacin ba sbd kubutar da rayuwarsu daga garin, Girgizata yayi da karfi tareda ambatar sunanta yana danne abinda yake Ji a kirjinsa na bugawan zuciyan dayake kokarin samu yace ‘Ayanah karki karye ke uwa ce a yanxu da babu Amma, Kece zaki zama garkuwan yan uwanki, Kece Amma yanzu, Kece madubi fitilar da zata haske hanyar da rayuwanku zatabi, Karki karye kiyi jarumta ba yanzune lokacin kukan rashin Amma ba, Ki dake zuciyarki ki kubutar da yan uwanki daga nan Allah ya Riga ya karbi Amma karki Bari burinta na kubutar da rayuwanku ya tashi a banza.’ Wata irin jijjiga jikin Ayanah keyi taba girgiza kai kuka me tsananin gaske na zuwar mata tace ‘Abaa bazan iya ba, Abaa ina buqatan kai da Amma a gurin zamtowa uwa garesu, Abaa kune hasken rayuwanmu,kune garkuwanmu, Abaa kune rayuwarmu tayaya zan iya babu dayanku?’ Rungumeta yayi jikinsa da karfin gaske yana rintse idanuwansa da a Karan farko rayuwansa suka zubewa hawaye ya kasa cewa komai yana sake qanqameta a jikinsa Tana wani irin kuka me tsananin karfin gaske hannuwanta na kakkarwa. Sakinta Abaan yayi ya janyo Zuhrah datai mutuwan tsaye bata ko motsawa jikinsa itama ya qanqameta yana hanasu ganin hawayensa. Sakinta yayi sbd da alama an shigo gidan nasa dan haka Abaas da Nurat ya zubawa ruwan dake gurin da suka fara daukan dumin wuta suna bude ido ya fizgesu tsaye Da gudu Ayanah tazo gaban gawar Amma ta saka hannu ta shafe idanuwanta suka rufe hannuwanta na tsananta kakkarwa ta saka hannunta cikin na Amman ta zare abin hannunta na zallan azurfa Wanda yake dauke da sunan Amma din tayi mata addua hakama Sauran adduar sukai mata a tsaye Abaa ya fizgesu suna kuka me tsananin gaske na tashin hankali. Turasu wata qaramar hanya dake baya yayi cikin sauri yana waiwaye sbd yana jiyowa sun shigo gidan da yawansu. Kirjinsa wani irin radadi da ciwo yake masa Wanda yakejin bazai iya Nisaba amma ko yayane zai tabbatarda ‘yayansu sun tsira, A bayansu yafara Jin takunsu me karfi da tsanani dan haka cikin sauri ya juya ya kalli hanyar kafin ya kalli gabansu da akwai Sauran tafiya kafin su bulla daji harma su isa bakin ruwa gashi sunada yawa fa qananun yara. Tsayawa yayi tareda kamo hannun Ayanah ya kalleta taje dukkaninsu suka tsaya cak kowa ya zuba masa ido, Ganin irin kallan dayake mata ya saka Ayanah fizge hannunta tareda ja baya Tana rintse idanuwanta Tana girgiza kai da karfi Tana fita hayyacinta gabaki daya. #MAMUH #SLAVERY #ROYALTY #BEST LOVE #GHAZ #BOYEM HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 7 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** ************* Matsota Abaa yayi tayi saurin sake yin baya da karfi tana fasa kuka me karfin gaske numfashinta na sarkewa. Abaas da Zuhrah da Nurat kuwa gabaki daya riqe Abaan sukai kowannesu jikinsa na rawa suna tsananin rokonsa akan ya biyo su su tafi karya sauya hakan. Zafafan hawayensa ne masu tsananin zafi suka Riga akan fuskan Abaas dake jikinsa ya sauke Kansa yana banbaresu daga jikinsa yace suyi sauri subar gurin shi zai rufe hanyar kafin kusrawa su qaraso sunyi nisa zai biyo su daga baya. Girgiza kai dukkaninsu suka hau Ayanah kuma tsananta kukanta yayi tana Jin kirjinta na wani irin radadi me tsananin gaske. Harbin mashi suka fara Ji tako ina ba tsammani take suka fara gudu dukkaninsu wasu kuma kibiyar na samun su dan haka suka shiga firgici me firgitarwa suna Neman rarrabewa amma Abaa ya kasa barin hakan ya taresu ta baya suna gudu me tsanani batareda sunsan inda suke jefa kafafunsu ba. Biyosu kusrawa sama da arbain sukai suna harbosu da kibiya tako ina suna wani irin ihu dake girgiza duk wani me sauraro. Duhun dajin suke bi suna gudu sosai Wanda kusan da yawan wainda suke tareda su suna Jin yanda suke mutuwa amma babu daman tsayawa wa hakama Abaa cikin tsananin tashin hankali ya hanasu juyawa su waiwaiya baya yace suyita gudu karsu tsaya. Cikin gudu da tsananin ciwon dayakeji a kirjinsa na tsananta yace ‘Ayanah duk tsanani kada ku tsaye kuyita gudu harsai kun tsira’ Sanyi jikinta yayi zata juyo cikin karfin hali da daga murya yace karki juyo Kuyita gudu Ayanah. Muryansa da bataji daidai ba ya sakata juyowa da sauri idanuwanta suka akan kibiyar data bullo gefen kirjinsa ta bayansa da aka harbo Tsayawa zatai Ya fizgeta da karfi yana turata yace ‘Ku tafi karku tsaya, Ku tafi Ayanah, Ki tafi dasu karki Bari kowa ya juyo bare tsayawa’ Kasa wa tayi ta juyo tareda riqe hannunsa suna gudu tare yana turata daga jikinsa zuwa gaba yana cewa ta tafi ta kula da yan uwanta ta tabbatarda sun tsira sun kubuta sun Gina rayuwa me kyau. Fara gazawa yayi dan haka turata da karfin gaske tana kokarin dawowa ya dago idanuwansa jajir yace ‘Ban Aminta ki tsaya ba bare dawowa gareni ki tafi Allah zai zama gatanku insha Allah, Burina burin Ammanku shine ku tsira dan haka Ayanah ku tafi ku cika mana wannan burin ku rayu, Duk rintsi ku hada kai karku rabu da juna’ Sake turata yayi sa karfi tana qara riqosa amma ina jini sosai yake fita a kirjinsa harma da bakin sa take kafafunsa suka kasa daukansa ya durqushe a gurin ta kira sunansa da karfi tana kokarin durqusawa Kaman daga sama taji bayanta an riqeta. Cikin tsananin azaba ya dago idanuwansa ya kalli Asamah wadda bata hayyacinta sbd kukan baqin ciki da danasanin datake ciki tareda fatan tayi mummunan mutuwan data jawa rayukan dake ANJOM. Daqyar ya bude baki jini na fita sosai yana kallan Asamah yace ‘Ki tseratar dasu, Karki bari kowannesu ya tsaya bare dawowa ANJOM ‘ Janta Asamah tayi tana Hana su Zuhrah dawowa suka fara ihu ganin halinda Abaansu ya shiga ransa na kokarin barin kirjinsa sbd wani irin jinin dake fita bakinsa. Kaman daga sama sai ganin Mutum biyu sukai akansa ba Imani a tare suka soka wuqa biyu a wuyansa idanuwansa na kan yayansa dake Ihun gaske suna Neman zarewa sbd mummunan tashin hankalin sheda mutuwan mahaifinsu akan idonsu. Asamah cigaba da turasu tayi suka kutsa dajin suna tsananta gudu hannun Ayanah yana cikin na Abaas hakama Nurat da zuhrah suma hannuwansu na riqe dana juna. Biyo su akai wannan Karan an Dena harbin da alama da rai ake sonsu. Kuka sosai sukeyi suna tsananta gudunsu Banda Ayanah datake Jin zuciyarta na kokarin nema bugawa hakama idanuwanta basa ganin komai jefa kafa kawai takeyi. Dukkaninsu sun kasa yadda a awannin da basu wuce uku ba sun rasa iyayensu duka cikin dare daya a Masifa da mummunan kaddara daya, Neman sarewa sukeyi amma Sam Asamah ta kasa Bari saima hanya data sauya musu sbd an kusa kamosu dan haka cikin wani irin qazantaccen rami ta turasu suka shige suka boye tareda sakina wadda take riqe da Zuhrah a yanzu. Suna shigewa Asamah ce ta saka hannuwanta ta toshe bakin Nurat da Abaas ita kuma sakina ta rufe na Zuhrah sbd yanda suke kuka suna wata irin jijjiga. Ayanah ta kasa komai ta koma tamkar marasa hankali da kwakwalwa kwata kwata dan haka batace komai bare kukan Wanda ya kasa fitowa tsabar muni da girman tashin hankalin datake ciki. Suna Ji kusrawan na wucewa da gudu da karfi suna ihu me ban tsoro amma basu motsa ba har saida suka Ji sun gama wuce kafin Asamah ta zare hannunta a Bakinsu Sai a lokacin Nurat ta fasa wani irin kukan daya saka Idon sakina fara zubar hawaye Asamah kuwa kukan itama ta fasa me tsananin ciwo tana rungume Zuhrah dake jijjiga kaman me wani ciwo. Rintse idanuwa Ayanah tayi tareda sunkuyar da kai tana fasa kuka mai tsima zuciya da girgiza kowa. Babu Wanda yace komai a cikinsu dukkaninsu kuka ne sukeyi mara dadin Ji bame rarrashin wani sbd kaddarar tayi musu nauyin da zuciyarsu take kasa dauka, Ayanah hannu ta Dora Akan kirjinta tana duka kukanta na sake tsananta sbd kirjinta ya toshe Jin takeyi kaman ta mutu tabi iyayenta. Har asuba tayi gari ya fara haske suna cikin ramin idanuwansu sunyi wani irin kumbura da ja babu me iya dogon motsi sbd mutuwa da jas ne shima yayi kanta da gudu hakama sakinah Ayanah Sakinah kuwa Nurat ta riqe sbd kada itama ta juye ta bisu ta fada ruwan. Har Zuhrah ta fada ruwan Abaas ya Riga Ayanah isa gareta ya riqota tana fizge wa tana kuka me karfi tana rokonsu su tafi. Rungumeta Abaas tayi sosai jikinsa yana bude baki cikin karfin Halin dake zuciyarsa data fara bushewa yace ‘Zuhrah zamu jure,zamu jajirce,zamu tsira,zamu rayu insha Allah zaku ma mu sake amsa sunanmu GHAZ wata ran…. Girgiza kai takeyi tana cewa ‘Aa Aa Abaas bazamu sake amsa sunanmu ba har abada gwara mu tafi dan Allah’ Girgiza mata kai yakeyi shima yana sake daurewa kukan dayake zuwar masa Ayanah ma rungumesu tayi dukansu tana maimaita abinda Abaas ya fada Akan sun rungumi hukuncin ubangiji duk tsananin tsanani zasu jure zasu jajirce zasu rayu a cikin kowane Hali dadi ko wuya. Kuka Zuhrah keyi sosai tana girgiza kai a hakan haka har suka fito ruwan suna samun guri suka zauna suna yin shiru tsawon lokaci kafin suka kalli juna suka sake daukanwa kansu alkwarin jurewa da rungumar kaddara tareda kasancewa da juna sbd duk masifa da munin rayuwan da zasu fuskanta idan suna tare da juna zasu jure dan rabu wa da junansu shine mafi muni da girman kaddarar da suke tinanin zai samesu Wanda gwara musu mutuwa Akan hakan. Fitowa rana ya saka suka miqe suna sake cika cikinsu da ruwan sosai suka bar gurin Bayan sun jiqa kayansu sosai da ruwa har suna tsiyaya ta yanda zasu yi tafiya me tsayi basu azabtu da tsananin Zafin rana da kishirwa ba. Komawa sukai cikin dajin suna kallan hanyar gabas suka miqa suna riqe hannun juna Nurat kuma tana hannun Abaas ya riqe hannunta gam cikin nasa. Wuni sukai suna tafiya har rana ta fadi duhu yayi suka nema guri suka zauna babu me iya numfashin arziki sbd wahalar yunwa da kishirwa. Dukkaninsu sunyi galabaitar da baa magana dan haka tinda suka zube a gurin babu Wanda ya sake motsi kaman matacci har gari ya kuma wayewa yayi haske. Numfashinsu fara Neman gagararsu yakeyi amma a hakan suka tashi suka sake bin hanya suna kasa ko riqe juna wannan Karan, Wuni suka sake yi suna yawo a dajin batareda ma sun San inda suke jefa kafafunsu ba gashi kaman dajin dayake da wani sirri dan baka iya gane gurin fita.. Kwanaki suka dauka suna ragaita a mummunan dajin Wanda zuwa lokacin tini suka fara cin ganyen duk icen da suka samu Wanda yafara maidasu kaman wasu dabbobi, Kamanninsu sun sauya daga mutane zuwa wasu kalar, Fatar su ta koma kaman busashiyar dabinon daya fito cikin qasar sahara, Bakinsu ya bushe ya far fashe jinin dayake fitarwa shi Kansa ya bushe, Wata irin dauda da qasa tareda qazanta ce kala kala a jikinsu Wanda bushewan da sukai qayau yake rage warin dake tashi a jikinsu, Zuwa lokacin dukkaninsu sun gama cire rai daga rayuwa harda Sakina kanta me basu kwarin gwiwa wannan Karan mutuwar take fata da son ta dauke su sbd rayuwa dai ta qare musu a inda ko gawarsu basuda me kalla yayi musu fatan rahama sedai tsutsa su cinye namansu iska ya busar da saura sbd ko dabbar da zata cinye namansu a dajin babu. #MAMUH #BEST STORY #ROYALTY #SLAVERY #BEST LOVE #BOYEM HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 11 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** Idanuwan Ayanah da suka koma manya sbd gabaki daya naman fuskanta daya tafi babu shi sai qashi zalla Wanda Kana kallanta zaka dauke idonka akanta sbd gabaki dayansu haka suka koma babu Kyan gani sbd babban cin kamannninsu da wanda qwarangwal fata ne da dan abinda baa rasa ba sai Sauran rai dayake jikinsu, Kallan kannenta dake kwance gefenta dukansu kaman gawar dataqi rami takeson yi amma ganinta yayi Raunin da bata iya gane wa sosai dan haka bushashen hannunta ta motsa daqyar yakai kan fuskan Abaas wanda wasu haqoran wahala kawai ta iya Ji a fuskan tasa wainda sune kadai a tsaye sbd babu komai a fuskan tasa idanuwansa sunyi zurfin data kasa iya tantance ramin ido ne ko kuwa ramin bakinsa dan haka ta sauke wani wahalallen Numfashi daqyar tana taba Zuhrah wadda cikinta ya hade da bayanta ta koma halittar da zata iya firgita qananun yaran gata. Hawayen da babu su ne a jikinsu Ayanah ke kokarin hada wa amma babu yanda zasu taho sbd basu da Sauran ruwan komai a jikinsu sbd fitsarinsu ya dade da komawa baqi qirin sukeyinsa alaman babu Sauran ruwan komai a jikinsu. Nurat wadda kowane lokaci ranta zai iya fita jikinta ta sauke hannunta akanta tana Jin kanta ba komai sbd gashin kanta data ringa figewa a kwanakin sbd azaba da rashin cikakken hankali. Rufe idanuwanta tayi tana Rokan Allah ya kawo musu daukin da shine ya kamacesu. Sakina ta dan kalla daqyar bata gane kamanninta tana fatar ko a Aljannah Allah ya hada su guri daya da Sakina sbd ta zama jininsu koda basu hada jinin gaske ba. Zafi garin ya sake dauka sosai da tsananin azaba har rana ta fadi suna kwance har duhun dare yayi, Tsakiyar dare ruwan sama ya sauko wanda da ruwan saman ne daman suke samun sauki a wasu lokutan. Yanzunma ruwan saman ne dayake sauka kansu sosai ya dan saka wasu daga cikinsu motsawa amma ba wanda ya iya tashi har saida ruwan ya dauke da safe tukuna dukkaninsu suka bude idanuwansu amma babu me iya tashi. Zuhrah ce kunnuwanta suka fara jiyo mata takun mutane me dan karfi kadan kadan sai ta Lumshe ido tana fatar abinda take Jin da gaske ne dan kuwa suna buqatan koma masu kashe su ne a yanzu suzo su kashe su tinda a yanzu basuda ma karfin yi da kansu. Hanyar ta qurawa ido daga kwancen datake duk da bata gani sosai gabaki dayansu dishi dishi suke gani ganinsu ya samu matsala wanda kaman illar ganyan da suke ci ne kaman dabbobi. Ayanah ma ahankali ta fara jiyo takun amma bazata iya Juyawa ba bangaren ta kalla sedai Lumshe idanuwan datai na jiran tsammanin koma menene sbd su yanzu kusan tsoro ya cire daga rayukansu. Sauran ma dukansu suna jiyo takun da sautin sa ke amsawa a dajin ta nan bangaren da suke, Sakina ce tafara daga hannu Daqyar tana fatar a hangosu su samu koma wane irin dauki ne. Shiru shiru baa nufo ta bangaren da suke ba har yamma basu Dena jin hayaniya sama sama ba, Duhu ya fara harsun cire rai da tsammani ita Zuhrah da Nurat harma da Abaas duka sun some babu me Sauran numfashi a jikinsu. Sakina da Ayanah ne keda Sauran numfashi amma suma idanuwansu a rufe koma sun bude basa ganin komai se duhu ga kuma dare. Tsakiyar dare sosai Ayanah itama ta some gabaki daya bata numfashi sakina data rage sama sama taji magana akansu Ana cewa ‘Muna buqatan hada wa dasu tinda sunada Sauran rai idan anje can zasu farfado tinda kams yace duk wani dan Adam koma dabba ce idan har tanada rai a tattaro a kawo masa sbd yaune ranar mu tanada qarshe a wannan nahiyar Bayan tsawon shekaru idan muka tafi yau har abada munbar nan tinda a yanzu babu gari anan sedai a tarihi kuma., Daukansu sukai dukansu tsaf suka bar gurin dasu suna dorawa Akan dokuna masu karfi bakyan gani suma sbd abubuwan da duk suka Shafa musu da adon ban tsoro. Suna barin gurin itama sakinah ahankali numfashinta ya tsaya bata sake sanin inda take ba. Mutane sosai suka tattaro a dajin duk sun galabaita wasu kuma sun mutu harsun bushe wasu kuma suna gap da mutuwar wasu kuma macijai sun kashesu wasu kuma sun zare sbd gane ganen Masifa hadda jinnu. Fiyeda Rabin tarin yawan rayukan garin ANJOM sun kashesu dan haka wainda suka mutu sunfi wainda suka Kama sosai dan haka basu wani samu yanda suke so ba Shiyasa ya bada umarnin a sake shiga dajin da zagayensa a kamo wainda suka tsira sbd ya samu tarin bayin da zai siyar wannan Karan su haura daruruwa dan yanada wasu tarin bayin dasuka safaro daga nahiya daban daban a cikin jirginsa me kamar gari guda. Bayan gari ya waye har rana ta keto tukuna suka samu gama hada bayinsu a cikin bangarensu daban can qasan jirgin wanda kowace bawa kafafunsa a daure suke da kaca hannuwansu ne kadai a sake, Su Ayanah da ire irensu da suka gama lalacewa mutuwa kawai suke jira daban aka ware su Ana zuba musu ruwa duk bayan dan lokaci. Yamma sosai kusrawa suka daga daga nahiyar gabaki dayanta har abada sbd basa maimaicin zuwa gari komai nasarar da suka samu akansa, Sun dauki shekaru a nahiyar ANJOM din wanda daga karshe sun samu abinda suke samu dan haka kai tsaye daga nan nasararsu da cikar burinsu zai cika sbd wainnan bayin na kaiwa MASARAUTAR BOYEM ne, Masarautar da duk suka samu ta karbi bayinsu to tabbas burinsu ya gama cika na duniya. Masarautar da babu kamarta a iko da tarin mulki da arzikin dayafi na kowace Masarauta tarihi, Idan har BOYEM ta karbi bayinsu to tabbas zasu shiga cikin littafin tarihi da ko Bayan shudewansu zaa San kusra. Jirginsu ahakali ya daga daga nan yana keta wa tareda Kama hanyar ruwan da zasu tsallake sama da nahiya hamsin kafin su isa nahiyar BOYEM. ********* tafiya me nisa akai ta kwana da wuni baa gama fita nahiyar dajin ANJOM ba wadda a qalla sai sunyi kusan sati kafin su fita dajin. A wannan kwana da wunin babu wanda ya farfado a cikinsu Ayanah saida aka kuka wuni tukuna suka fara farfadowa shima sbd ruwan da aketa zuba musu ne masu tsananin sanyi. Suna bude idanuwansu cikin Ayanah ce ta fara bude ido taga inda take cikin wani irin rikitaccen karfin da baifi ma jaririn rago ba ta yunkura tana tashi amma bata iyawa sosai, Sunan Abaas tafara ambata cikin dan karfin datake dashi tana dudduba gefenta dataga mutane barkatai sama da Dari duk wasu a kwance. ‘Zuhrahhh,Abaas,Nurat,Sakinah…….. Haka ta ringa jerosu tana kiransu jikinta na Wani irin mummunan rawar tashin hankali. Zuhrah ce ta fara jiyo Ayanah din da sauri itama t bude idanuwanta tana kwala sunan Ayanah din da dan karfi hankalinta a tashe ko gani batayi ta miqe tana kokarin takawa ta kife sbd kacar dake kafarta. Bude ido tayi a inda ta fadi sai idanuwanta suka sauka Akan Abaas cikin sauri ta cakumosa tana kwala kiran Ayanah. Ayanah gurin ta rarrafo ta iso suka rungume juna da karfin gaske suna jin sassauci. Nurat suka fara kira itama tareda sakina sai kuwa gasu sun gani a guri daya take suka rungume juma kaman Ana partyn ‘yayan aljanu sbd yanda suke hada qasusuwan jikinsu suna rungumewa. Can Kurya suka rakube inda baida haske sbd basason Abaas na bayyana sosai kada tsautsayi yasa a gane duk da bazaka taba kallansa kai tsaye kace ga ba macen bane suka maqale juna a zazzaune kowannesu da kaca a kafansa. Tsoro ne zuciya da gangar jikinsu sbd sun gama tabbatarda sun Riga sun zama bayi, Sun zama bayinda har abada basu yancin rayuwarsu sai yanda akai dasu, Sun rasa sunansu,sun rasa asalinsu rayuwa kuma yanzu sedai wadda aka zaba ko hukuntar musu. Bude kofar qaton dakin da suke akai daga sama kofar take. Kallo wanda ya bude kofar yayi musu tsaf kafin ya fara Jeho musu daurin gayar tuwon alkama da akai da nono. Masu dan karfin cikinsu take suka fara ruguwan Abinci suna tura Bakinsu cikin tsananin yunwa da ficewa hayyaci. Sakinah ma cikin karfin Hali ta yunqura tana wawaso abincin tana jefo musu take jikinsu na rawa suka fara sararsa suna Turawa Bakinsu hannuwansu na rawa. Zuhrah dataji kaman bazata iya tsayawaba yake itama ta rarrafa ta fada cikin wawason tana Turawa bakinta a haukace. Abaas ma fadawa yayi hakama Ayanah da Nurat Take suka zama kaman mahaukata kowa wawa yakeyi yana Turawa bakinsa a haukace. #MAMUH #BEST STORY #BEST LOVE #ROMANCE #ROYALTY HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 12 A cikin Hali na wawason suka ringa Turawa Bakinsu ko taunawa basa yi hadewa kawai sukeyi yana wucewa maqoshinsu da wani irin karfin gaske, Wani irin kuka hanjinsu keyi na samun abinda suka dade basu samuba wato abinci, Danne juna ake yi sosai Ana yiwa juna rauni da hakan suka samu suka cika cikinsu sedai kusan dukkaninsu sun samu rauni dan haka suka rarrafa gefe suka rabe suna dunqulewa sbd tsananin ciwon ciki daya taso musu. A kwance suka wuni ba lafiya sosai sbd ciwon ciki da lafiyarsu da daman babuta yanzu, Tsakiyar dare haka aka sake zuwa aka kawo abincin Ana jeho musu suna wawaso sedai wannan karan

Chapter 2 of 28