sbd gajiyayyan kukan dake taso mata.
Kama hannuwanta yayi yana hawaye masu dumi shima ya sumbaci hannunta kafin ya kamo kanta ya sumbaci goshinta yana rungumeta cikin jikinsa yana share mata hawayenta.
Tashi tayi ahankali daga jikinsa ta juyo ta kalli Zuhrah tareda zuba mata ido tana kallanta cikeda tausayi da kauna me karfi,
Hannu takai ta shafi fuskanta ahankali kafin ta sumbaci gefen fuskarta tareda rungumeta ahankali ta bude baki tace
‘Zan tabbatarda na kashe kaina kafin wani ya lalamin rayuwarki sbd ke zuciyata ce,ke Rabin jikina ce,ke jinin jikina ce keda Abaas…’
Sake sumbatar goshinta tayi tana hada su itada Abaas ta rungume sukai shiru tsawon lokaci a hakan kafin ta janye su tana fara basu dambun alkamar da akai zalla babu komai a cikinsa tafara basu a baki da hannunta tana kallansu kaman zata cinyesu.
Basu takeyi a baki suma suna diba suna bata hakama Abaas na bata yaba Zuhrah hakama Zuhrah tabawa Ayanah din ta bawa Abaas a haka suka ciyar da junansu babu Wanda baya hawayen qunci da radadi a cikinsu.
Suna gamawa suka kwanta jikin juna sakinah na gefensu tana hawayen tausayinsu dana kanta da batada kowa a duniyar Bayan su.
A haka suka wuni shiru jigum babu motsin komai sbd se dare kuma zaa sake basu abinci dan haka ko motsi babu keyi dakin tsit yake.
Har dare suna jikin juna saida Daren yayi tukuna zaa fara cin kasuwar bayi ta garin dan haka aka zo aka bude kofar su dan diban bayi.
Ana budewa take suka fara diban suna turasu waje,
Bayi arbain zasu siyar dan haka Ana kirqa Talatin da Tara Wanda yake diban ya finciko Abaas kai tsaye ya jefa kofa yana cikewa arbain dashi,
A tsananin haukace Ayanah ta miqe tana riqe hannun Abaas din da tsananin karfin gaske har tana kife wa qasa sbd sarkar kafarta amma bata sake hannun Abaas ba Wanda shima ya riqeta da tsananin karfin gaske duka jikinsa na daukan mummunan rawa,
Zuhrah ma fadowa tayi kan Abaas din tana riqe sa da karfin gaske tana kiran sunansa da karfin gaske duka jikinta jijjiga tsabar rawa.
Ayanah miqewa tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa da karfin gaske tana cewa a siyar dasu tare dan Allah idan ba haka ba mutuwa zatai.
Zuhrah ma hakan ta riqe sa tana kukan da ko maganarta bata fita.
Ganin hakan y saka kai tsaye aka dauko buloli masu tsananin tsayi aka fara dukansu da ita amma Sam daga Ayanah har Zuhrah da Abaas din sun kasa sakin juna Neman zarewa sukeyi da tsananin tashin hankalin daya saka sakina ma fasa kuka tana fadawa kansu tana rufe su sbd tsananin dukan da ake musu jini na fita jikinsu.
Azabar dukan da ake musu sun kasa sakin juna jininsu na fita ya saka gangar Zuhrah kasa dauka ta fara zame wa qasa idanuwanta na Neman rufewa zuciyarta na tsananin gajiya wa da komai ta zube a gurin a some.
Ayanah data kasa sakinsa duk da komai nata musamman zuciyar sun gama gajiya da rayuwar gabaki daya sun gaza hannuwanta jini sukeyi amma ta kasa sakinsa daukanta ake cigaba da yi Sakinah na dan kare mata har itama sakinar ta some a gurin.
Karfin gaske Mutum shida suka saka uku suka jata uku suka ja Abaas suka rabasu yana Ihu a Karan farko itama tana ihu moqashinta harya kasa Dena fidda sauti shima hakan bakinsa na fidda jinin harshensa dayake cixa tana fidda jini itama ta hancinta sbd munin halinda take ciki a haka aka rabasu suna jansa suka fice dashi gabaki daya suna Wani irin kukan daya saka gabaki daya bayin dake gurin hawaye sbd da gaske dai zata iya mutuwa idan aka rabata dashi kaman yanda suka Ji tana fada masa lokuta da dama.
Ficewa akai dashi tareda rufe kofar Wanda yayi daidai da yankewan jikinta ta fadi a gurin ba Sauran numfashi ko motsin komai jikinta.
Shi Karan Kansa saida suka sumar dashi suka fice dashi Wanda cikin saa take shi suka fara siyar wa aka tattara gurin aka Bari dashi sedai ya farfado ya samu Kansa wani gurin.
Sbd ma yanda su Ayanah din suka kawo musu matsala ya saka basu kwana ba suka gama cin kasuwarsu sukai siyayya suka bar qasar a ranar.
Suna barin qasar kai tsaye umarni khams ya bada bazaa sake tsayawa kowace qasar ba sai ta BOYEM dan haka tafiya Sambai aka dauka zuwa BOYEM wadda ta saka aka fara sauyawa bayin abinci zuwa wadatacce me kyau sbd suyi Kyan gani da masarautar zata karba.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
17
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
***********
Koda su Ayanah suka farfado sun Riga sun bar qasar da ruhinsu yake acan babu sauran abinda ya rage a tattare dasu Bayan gangar jikinda babu ruhi babu zuciya sbd Nurat da Abaas sune ruhi da zuciyar Ayanah Zuhrah kuma rayuwarta,
Ita kanta Zuhrah yan uwanta sune rayuwarta da ita kanta dan haka tana farfadowa babu Abaas da gaske an rabasu rabuwar da har abada sun rabu bazasu sake haduwaba,bazasu sake sanin yana raye kokuma shi yasan sun raye ba hakama bazasu San halinda zai shiga ba ya rayu har zuwa mutuwar sa ba shima bazai San halinda zasu shiga ba na rayuwa ko mutuwa sai kawai ta sake sumewa batareda ta motsa daga inda take ba.
Ayanah kuwa tana farfadowa ta tabbatarda an rabasu da Abaas saita rarrafa ta isa kofa tana bugawa Da dan karfin da baifi na yaron goye ba sbd batada Sauran karfi ko kuzari kokuma wani amfani dan baqin ciki da qunci tareda rabata wainda sune kuzari da rayuwarta yariga yayi mata illar da bazata taba moruwa ba ko dawowa daidai abada
A karo na babu adadi take jin ta sake zabar mutuwa Akan rayuwa,
Inama ace mutuwa Abaas yayi a gabanta tasan ya komawa ubangiji baya duniyar yafi mata samun sassauci da nutsuwa Akan rabasu da akai batareda sunsan Ina rayuwa zata kaisaba shima,wace duniya ko sabuwar kaddarar zai fada duk basu saniba.
Kiran sunan Abaas takeyi duk lokacinda ta bugu kofar batareda akwai lakar komaiba a jikinta tamkar yar maye ko fita muryanta baya yi amma a hakan bata hakura ta Dena ba Abaas tsakanin buqata a kusa da ita kokuma a zubar dasu ko a ruwan qasar ne kafin a gama barin qasar.
Tsananin wahala,qunci,nannauyan baqin ciki,tarin gajiya da ruhi gangar jiki da zuciya sukai harma da idanuwa ya sakata silalewa qasa kwance a gurin tana fidda Numfashi gajiyayye tareda rufe idanuwanta ahankali jikinta na saki batareda ta some ba kawai dai ba lallai ta sake moruwa ba ko taba dawowa daidai ba.
Sakinah dake rungume da Zuhrah itama ta gama fita hayyacinta matsowa tayi gefen Ayanah din tareda dagota jikinta ta kwantar sukai shiru sbd yanzu kam babu wani qarshen qunci da baqin ciki dayayi saura Wanda basu gani ba dan haka koma me zasu tarar a gaba bazasu Ji komaiba.
Haka suka kwana suka wuni tamkar gangar jikinsu babu rai a jikinta,
Babu me iya kowane irin motsi idanuwansu ma a rufe suke ko abinci sun dena iya ci sedai sakina ce take karbowa ta rarrafo ta zauna tsakiyar su ta ringa basu a baki Akan dole sbd karfinsu dayake sake yin qasa sosai Wanda Sai a yanzu sakina ke sake tabbatarda kasancensu su duka hudun a tare da gaske shine rayuwa,ruhi,kuzari da karfin zuciyarsu sbd a yanzu Ayanah da zuhran gasunan sun zama tamkar marasa cikakken hankali.
Idan dare yayi haka zata zauna tsakiyar su ta kwantar da kansu a jikinta tana Shafa bayansu da fuskar su sbd samar da nutsuwa ko yar qanqanuwa ce a zuciya da gangar jikinsu.
Idan gari ya waye haka zata jawosu inda ake fiddosu Ana zuba musu ruwa sbd su wanke kullum kafin isarsu inda zaa kaisu,
Haka zata janyo su kaman qananun yara Ana dukansu duk da yanzu an rage dukansu sosai sbd duk anason suyi dan yi Kyan kallo dan haka kullum Ana fiddosu a hade guri daya a ringa zuba musu ruwa masu tsananin yawa suna goge jikinsu Wanda baya goga jikinsa lokacin da ake zuba ruwan duka yake sha da Bulala dan haka sakinah ganin kullum sai an dake su amma tamkar jiran duka sukeyi sbd ya wahala ta kashesu subar daniya ya saka koyaushe idan Ana zuba ruwan itace me wanke jikinta ta wanke nasu su dukan.
Ana gama wankesu haka zaa sake shanyasu a rana sai sun bushe a gargadasu a maidasu inda suke a rufe,
***********sake nutsawa tafiyarsu tayi Wanda a yanzu suna samun abinci sosai hakama wankan kullum ake musu dan haka yunwarsu ta ragu sosai sedai shi wanka kam ya saka duk fatar su ta bushe qayau sun koma wata sabuwar halittar daban kowannensu cikin bayin ka kalla tamkar an birkidasa cikin farin gari an ciro sbd kullum ruwan kawai ake zuba musu sannan a shanyasu a rana.
Har lokacin babu abinda ya sauya a sabuwar kaddararriyar rayuwar data samu su Ayanah,
A yanzu basa iya ko magana daga ido se ido sai kallo dan haka ne ita kuma sakinah nauyinsu ya dawo kanta gabaki daya fatarta dai suna isa qasar da zasu din a siyesu koda kashesu zaayi gwara a siyesu acan din da azo baa siyesu ba kusrawa su dawo dasu.
**********Tafiyar sati bakwai sukai tukuna jirginsu ya fara shigowa qasar da kowane tarihin zamanin ke fadar iko,girma,mulki,arziki da tsananin da masarautar qasar take dashi sakamakon sarakunanta da suke aje tarihi me girman gaske kafin rasuwa subar karagarsu.
Tsananin tsaro da tsari tareda dokokin dake zagaye da qasar daban yake da duka Sauran qasashen duniyar Wanda ya saka zuwa qasar yake tamkar samun babban rabone da saa a duniyar da suke rayuwar,
Suna gap da isowa kusan iyakar bodar da zata shigo dasu farkon ruwan qasar saida aka sake tsafta ce kowane bawa kafin suma suka wanke kansu da dan gyara komai na tsarinsu dasu kansu din.
Boda biyar ce tin daga farkon shigowa nahiyar qasar kafin isa cikin bodar ruwa ta cikin qasar wadda ita kanta bakin bodar cikin kasar daga nan bakin zuwa cikin qasar tafiya ce tsananin tafiya.
A bodar farko saida suka share kwana daya a bakin wajen qasar batareda sun samu damar shiga ba saida aka gama binciken tabbacin kasuwan bayin sukeyi kafin aka barsu suka wuce.
Wuni guda suka sake share wa Bayan barinsu Checking point na bodar farko kafin suka iso ta biyu.
Anan ta biyu ba saida suka share kwana daya harda wuni kafin aka gama tareda basu damar wucewa.
Shima tsakanin boda ta biyun zuwa ta uku tafiyar wuni guda ce sukutum sai tsakar dare suka isa dan haka baa duba kowane jirgin ba duka jiragen da suka taho a wajen bodar suka kwana sai washe gari aka fara aiki akansu.
Tashin farko abinda suka fuskanta anan shine bazasu shiga da jirginsu can bodar karshe ta cikin asalin qasar ba dan haka duka yawansu anan bodar zasu tsaya da jirginsu sedai shugabansu da wasu daga cikin manyansu da bazasu wuce Mutum Ashirinba dan a qaida baa wuce hakan dan hakan komai yawan bayinsu koda bayinsu sunfi dubu daruruwa to su dai da zasuci kasuwarsu bazasu wuce Mutum ashirin ba kuma da jirgin bakin bodar zasu biya su dauka su isa can sai sun dawo su koma jirginsu su koma inda suka fito.
Wannan dalilin ya saka kowace boda dake qasar girman bodar kawai yana fin girman qasashe da dama sbd irin tarin manyan mahaukatan jiragen ruwan dake tsayawa ko zama a gurin ba qaramar qasa ke iya daukansu ba,
Kowace boda dake qasar tamkar wata qasar ce me zaman kanta sbd gari ne da mutane sosai sbd duk wani maaikacin bakin boda na qasar anan yake rayuwa da iyalansa da yan kasuwarsu harma da sauran manyan huldodon kasuwancin qasar da akeyi kuma anan ma Ana cin kasuwar bayi sedai acan babbar bodar ake cin asalin babbar kasuwar bayin datafi kowace a duniyarsu,
Hakanne ya saka kowace bodar qasar gari ce guda mai zaman Kansa hidima sosai da cin kasuwanni akeyi tareda dubban Jamaa.
A nan jirgin kusrawa ya tsaya suka gama karba da biyan komai na tsantsar dukiya me yawan gaske kafin suka fiddo bayinsu kaf aka Kirgasu tareda biyawa kowane bawa daya Lasisin shiga qasar.
Saida suka kwana biyu a wannan bodar Ana harkar lasisin shiga qasar kafin aka kammala komai suka zuba bayinsu a sabon jirgi da zai kaisu suka wuce tareda barin dukannin Sauran kusrawa a garin bodar su samu shaqatawa da hutawa suma kafin su dawo Wanda a kalla basu San kwanakin da zasu shafe ba kafin dawowan tasu.
Bodar gaba baa tsaya komaiba lasisin bayinsu aka bi daya bayan daya Ana duba wa tareda tabbacin sa tukuna aka barsu suka wuce.
Suna wucewa khams ya sauke wata sanyayar ajiyar zuciyar samun nutsuwa da jin qamshin cikar Buri,
Qamshi da iskar da kake shaqa a kasar kusan daban yake sbd nutsuwa da tarin arziki kawai kake Ji da gani tako ina,
Su Karan kansu bayin nutsuwan ruhi da zuciya suka Ji suna samu ahankali cikin sanyi sbd koba komai sunsan yanzu kam sun iso qasar da zaa siyar dasu su fita hannu kusrawa,
Dukkanin bayin a lokacin aka fara fitowa dasu daga jirgin kusra a wancan bodar da suka fito duk Wanda ya saka tafin kafarsa ya taka qasar da allah ya shimfida a duniya sai hawaye sun gangaro masa na godia ga Allah daya sauko jirgin ya fito batareda ya rasa rayuwarsa ba ko mutuncinsa kokuma dai Allah ya masa arzikin fitowa daga balai da masifar datafi komai a rayuwa wato jirgin kusra.
Ita kanta Ayanah a lokacinda jirginsu ya isa asalin bodar cikin qasar dago idanuwanta tayi ahankali ta kalli ruwan qasar da suke shar iskar su na ratso musu sbd a wannan jirgin inda ake ajiye bayi ba a rufe yake ba cikin duhu a bude yake suna iya ganin koina sbd harda winduna wani sanyi na ratsa fuskarta zuwa gangar jikinta daya sakata rufe idanuwanta ahankali tana dan qanqame jikinta hawaye masu dumi na gangaro mata tinanin Nurat da Abaas na danne kirjinta da dayanzu dasu zasu shaqa wannan iskar da suka manta rabon da su shaqa sedai wari da zarni tareda tsami da karnin dakin bayin dasu ciki na jirgin kusrawa.
A bakin bodar su khams suka fara tabbatarda sun iso qasar datafi kowace a duniyar da suka sani sbd wasu Hasken wutattakin Turawa dake haske gurare daban daban hakama maaikatan mahukunta qasar gasunan koina,
Tsananin girma da fadin gari da kasuwannin bodar baa iya ganin iyakarsu sbd girman garin ya baci sbd akwai kasuwanni da gidajen da suka hau dubu Dari kuma a hakan ba baa shiga asalin cikin garuruwan dake qasar ba bare akai ga isa asalin babban birnin qasar da acan Masarautarsu take ba Wanda akwai ma tafiya me tsananin gaske.
Sake tabbatarda lasisin su na shigowa kasar cin kasuwar bayi akai tareda tantance lasisin bayin daya bayan daya tukuna suka samu saukowa suna taka qasar masarautar BOYEM Wadda take sanyaya zukatan kusrawan da bayin sbd Allah ya yanke musu azabar kusra.
#MAMUH
#BOYEM
#BOYEM
#BOYEM
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
18
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
*********
Sabuwar duniyar da kamar ba wadda suke rayuwaba suka samu kansu cikeda farin ciki da mamakin abubuwan rayuwan da suke gani da dama Wanda suke tinanin idan nan bakin bodar ruwan qasar ne yake da daukan hankali da mamakin duniya haka to yaya cikin qasar zata kasance musamman masarautar da a tarihi da labari suke jin tsaruwarta wasuma cewa suke da kalar asalin zinari akai adonta koina nata zinariya ce ke haskata.
Duk bawan da zai samu shiga masarautar BOYEM da sunan bauta ma a cikin tarihi sune masu saa da rabo ma dan haka ne da dama suke siyar da kansu a matsayin bayin BOYEM idan sunxo cin kasuwar sedai danginsu su dauka ya mutu sbd shikenan basa sake ganinsa.
Gidan ma sauki suka kama a cikin babbar kasuwar da zata fara ci ta bayin nan da kwana biyu dan haka rumfar da zasu ci kasuwa suka fara kamawa me girman gaske suka biya komai kafin suka zube bayinsu a rumfar tareda maida musu sarkar kafafunsu da duka aka cire sai aka Jere su tareda barin masu tsaresu Bayan sun saka tambarinsu babba Akan rumfar su dake nuni da kasuwancinsu.
Wucewa sukai zuwa masaukin da suka Kama dan hutawa a qasar BOYEM su kafar da tarihin hakan sbd hutawan gaske zasuyi da jin dadin da akace ana dashi a qasar.
Tinda aka Jere su Ayanah da sauran bayin duka a rumfar babu Wanda ya iya dagowa kan kowannesu a qasa yake suna kallan qasa sbd basuda ikon dagowa su kalli koina sai Angama cin kasuwansu.
Ayanah da batada sauran kuzari ko tinanin kanta bare iya kallan koina idanuwanta a rufe suke ta soka kanta a tsakiyar kafafunta zuciyarta na Wani irin yanka da radadi me zafi,
Ta rasa wasu gurbi masu girma a rayuwarta da bazata taba cikesu ba har karshen rayuwarta,
Rayuwarsu ta sauya ne a dare daya,kaddararsu tazo ne a daya dare,tashin hankali da baqin cikinsu duka Yazo ne a dare ya sauya rayuwarsu gabaki Dayan tamkar kyaftawar idanuwa.
Basuda sauran rayuwar da zasu kira rayuwarsu kuma,
Basuda komai da zasu kira nasu sbd gangar jikinsu da rayuwarsu gabaki daya ba tasu bace sbd basu da ikonta,
Daga yanzu a inda suke daga lokacinda wani zai saka kudi ya siyesu ta tabbas sun qarasa rasa kansu har abada har sai ranar da Wanda ya siyesu ya iya yantasu idan ma ya mutu batareda yanta su ba suna cikin gadon iyalinsa kamar wasu kadara.
Numfashi ta sauke me dumi tana sake rungume jikinta sbd sanyi dayake rata fatarta yana keta wa har cikin qashinta da yunwa ta gama rage masa kwari.
Zuhrah idanuwanta a bude suke ita sedai kanta na qasa ta qurawa qasa ido tana kallan qasar dake gabanta zuciyarta na Wani irin mutuwa da sanyin dayake na tsagwaron baqin cikin da qunci,
Motsa yatsun kafarta tayi ahankali suna shiga cikin qasa ta Lumshe ido ahankali wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata a karo na farko Bayan rabuwansu da Abaas da zuciyarsu ta kafe ta kangare,
Wannan itace qasar da a yanzu zasuyi rayuwa a cikinta babu ranar fita ko tafiya harsai rayuwarsu ta qare kenan,
Sun rasa uwa da ubansu da gidansu da garinsu da rayuwarsu da yanci su da qasarsu duka sbd kaddarar zuwa nan,
Anan Allah ya kaddaro zasu qarasa rayuwa Shiyasa duka wannan kaddarorin suka hau kansu,
Numfashi me dumi ta sauke ahankali mara sauti tana gode wa Allah Akan wannan jarabawar me nauyi da munin daya kaddaro musu tareda fatan su cika fa Imani su samu Hutu Bayan mutuwarsu sbd a yanzu da dukkaninsu kowa ya rasa babban bangare na rayuwarsa babu komai da yayi saura kuma a kaddararriyar rayuwarsu Bayan jiran lokacin mutuwa kuma dan haka duk abinda zasu gani na azaba ko baqin ciki basajin zuciyarsu ma zata girgiza ko kasa dauka sbd rayuwarsu bata shigo qasar d sauran kowane irin taushi ba a zuciya ta gama bushewa.
Sakinah dake kallan qasa itama lashe lips dinta da suka bushe tayi ahankali tana Hadiye wani busashen yawun daya wuce maqoshinta daqyar Tana jin itama wannan Karan takai karshen zamowa baiwa sbd acan baya datake baiwa a gidan GHAZ Ashe ba bauta takeyi ba cikin gata take Sai yanzu ne zatai asalin bauta Bayan zuciya da rayuwar gabaki daya ta bushe musu.
Dukkanin sauran bayin kowa da tinani da quncin tareda radadin da zuciyarsa take ciki kansu a qasa gabaki daya basa ma iyawa ko ikon dagowa su kalli mutane masu yanci kokuma wainda zasu iya siyensu.
A haka suka kwana gurin gari ya waye suka sake wuni a gurin sedai a basu ruwa so daya da dan abinci su ci kansu a qasa babu Wanda har lokacin ya dago bare yasan kalan duniyar da suka taho.
Haka suka wuni suka sake kwana babu kowane irin alamar zaa fara siyar dasu sai ranar cin kasuwar zaa bude tasu hajar a kasar dasu.
****kwana hudu sukai a gurin a Shanye sunsha rana sun bugu da rana da sanyi da iska da sauro harma da qwari Kala Kala kafin ranar cin kasuwar ta iso.
Tamkar ranar sallah ta duniya haka ake ta hada hadar kasuwar da zata ci sbd manyan mutane da wakilan Masarautu da suke zuwa cin kasuwar,
Daga qasashe daban daban na nesa da kusa ake zuwa cin kasuwar wasu daga qasashen nesa wasu daga qasashen kusa wasuma daga wata duniyar daban da baa San inda suka fito ba,
Dan haka wasu irin mutane ne tako ina ke cika koina wainda mutane da dama basu taba ganin yawan mutane irin hakan ba ciki kuwa harda kusan duka bayin da zaaci kasuwarsu basu taba ganin tari da taron mutane masu yawa irin hakan ba dan haka kusan harda tsoron tarin girma da yawan mutanen dake cike ne sha cika su.
Khams da Yaransa tin da sauran duhun safiyar ranar suka Baro gurin hutawar da suka Kama suna holewa da mata suka iso rumfar su aka sake tsara komai tareda fara tantance bayinsu daya bayan daya.
Kamar kwason dankali haka aka kasa su masu karfi da cikakkiyar lafiya daban,
Masu yar dama dama daban hakama maza daban mata daban hakama yan yaran da basu qarasa zama mata ba ko maza suma daban.
Yanda aka rabasu din a guri daya aka hade su Ayanah da Zuhrah da sakina basu samu an rabasu ba dan haka babu motsin ko wata kuzarin yin komai da su keda suna Zaune da sarqa a kafafunsu duka babu me iya ko doguwar motsi.
Rana tsaka kasuwar take kokarin fara ci amma a al’adar cinta ko a kaidar cinta bata fara ci sai wakilin Sarkin bayin qasar ya iso ya fara bude kasuwar da siyan bayin masarautar qasar kafin kowa ya fara siya daga baya.
Wannan Karan ma al’adu kala Kala aka ringa gabatarwa Ana siye da siyarwan Sauran abubuwan Banda bayi tareda dabbobin ruwa da tsiron ruwa daban daban duka gasunan anata siyarwa da siya.
Isowan wakilin Sarkin bayi na BOYEM ne ya saka kasuwar ta fara kokarin yin tsit duk girmanta sbd askarawan da suka shigo kasuwar tareda wasu irin manyan motocin Masarauta masu kyau budaddi dake Kwasar bayi zuwa Masarauta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 28