hadda jini yake fitarwa tsabar qwarin dake cikin gashin suna Shan jininsu a maqale,
Sosai aka sake wankesu da ruwa me kyau kafin aka sake zuba musu kumfa sai da sukai wanka kusan so goma kafin aka sallamesu ana basu saqi na zanin Daurawa me kauri daya bayan daya suna wucewa.
Koda suka koma daki kusan da yawansu zazzabi ya gama rufe su na wankan duk sun shaqa ruwa wasu kuma sanyin ya shigesu sosai dan haka magani aka sake rabawa kowa koda haka zazzabin ance kowa ya sha.
Uniforms suka saka wainda bazasu iyaba kuwa zazzabi me karfi ya kwantar dasu Wanda ya saka da yawansu basu iya fitowa karban abinci ba harda su Ayanah wainda suke kwance sosai har jijjiga sukeyi.
Sakinah ce ta iya fita tabi Layi ta karbo musu abinci ta dawo dakin ta taimakawa Ayanah taci kafin ta taimakawa Zuhrah itama taci kafin ita taci daga baya.
Basu iya Shan maganin da aka basu ba sbd basusan tayaya zasu iya shansa ba,
Shiru sukai a daki babu Wanda yake iya ko tashi zaune a cikinsu sbd itama sakinar daga baya zazzabin bugar da ita yayi.
Sai dare kusan karfe daya tukuna suka Ji shigowan Sauran Mutum uku din dake dakin.
Babu wadda ta iya tashi a cikinsu suna dunqule guri daya sunyi Laushi sosai,
Dayar cikin wainda suka shigo dakin ce ta iya isowa inda suke taga yanda suke jijjiga sbd zazzabin dan haka tayi saurin daukan maganin da aka basu ta jiqasa da ruwa ta fara kamo kan Zuhrah ta bata a baki Tasha sosai sbd kishirwa take ji.
Sakinta tayi ta Kama Ayanah itama ta bata tareda ruwa sosai kafin sakin daga qarshe.
Amai sosai zuhrah tayi sosai Wanda ya saka Ayanah tattara karfin Hali ta miqe sbd kulawa da ita cikin wahalar nata ciwon.
Sakina ma karfin halin miqewa daga ciwon tayi itama suka taru dan kulawa da Zuhrah wadda take jin jiki sosai harma hankalin Ayanah yayi mugun tashi tsoro me karfin gaske ya kamata.
Daqyar suka samu gari ya waye jikin Zuhrah din ya dan samu sauki sosai tayi bacci wadda bata taba samuba a watannin.
Itama Ayanah baccin ne ya dauketa na wahala har tsawon lokaci Wanda shine ya taimaka musu suka samu Wani irin sassauci me girma da qwari sosai.
Guraren 10 na safe aka buga kararrawar kira wadda ta fiddo kowa suka bi Layi aka raba musu abinci suka dawo daki suka zauna suka Turawa cikinsu sbd basajin dadin rayuwar bare abinci
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#BEST ROYALTY STORY
#BOYEMS
#GHAZ
#NUAB BOYEM
#LOVE
#ROMANCE
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
21
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
************
Wuni sukai a daki ba komai ba wani hayaniya ko doguwar motsi koina tsit sbd kowa ya fice sai su sabbin zuwa,
Sai yamma aka sake kiransu wanka haka aka kuma wankesu tas suka dawo daki yau kusan kowa da Kansa yasha maganinsa sbd abinda ya hanasu Shan na farko rashin sanin yanda zasu sha amma ganin ya taimaka musu jiyan sai kowa yasha.
Da dare ma haka aka kuma kiransu aka raba abinci sukaci suka kwanta Wanda take baccin wuya ya dauke dukansu kamar bugaggu Wanda basu saniba harda maganin bacci ake basu sbd anason su samu ishashen baccin da zai warware qwaqwalwarsu ta sake sbd gudanar da rayuwarsu a natse dan komai a BOYEM nutsuwa ce tsagwaranta yake buqata.
Washe gari ma haka aka kuma basu ci da wanka tareda magani suka wuni suna bacci da hutawa,
Duk yanda zuciya da kwakwalwan su Ayanah yake cikin wani irin qunci da damuwa me nauyi maganin da aka Dora su akai fin karfinsu yayi bacci suke yi sosai batareda sunsan ma tayaya kansu ya fara sakewa ba yana dan dawowa da tinaninsu Akan hanya daga fatan mutuwar da sukewa kansu kullum.
*****kaman yanda doka da kaidar Masarautar BOYEM take sai anyi sati biyu cif Ana basu abinci fa Hutu sosai kafin Ayi wata daya Ana horar dasu komai na masarautar Bayan an gama tababbatarda sun yadda ce tarihinta da sanin kowane irin bayani Akan bautar da zasuyi dakyau Wanda idan Baka da qwaqwalwar haddace komai da riqe komai kan hidimar dake gabanka shine ake Tura Mutum bangaren wahala da azaba inda zaka gwammace rayuwa a wata qaramar masarautar daji da babu gabas bare yamma.
Haka su Ayanah suka share sati biyu Ana basu Hutu duk da babu Wanda yake cikin dadin zuciya ko kadan a cikinsu amma jikinsu da fatar su ya samu lafiya sosai dan kuwa ko gurin Kwanciyansu a tsare yake da tsafta da dokoki,
Sun sauya sosai gangar jikinsu ta samu nutsuwa dan haka aka fara koyar dasu mataki ma biyu Wanda kullum ne ake koyar dasu yanda ake aiki da komai a masarautar irin su wanke toilet da gyara tareda iya aikin koina da yanda zasu iya fuskantar rayuwarsu idan sun tsayu a gaban duk Wanda yake jinin BOYEM.
Rayuwar bayin BOYEM hatta inda zasu iya dagowa su kalla a qayyade yake hakama yanda zaka iya bude baki ko fidda Numfashi me sauti a gaban jinin BOYEM Akan kaida da doka yake hatta dukkanin gangar jikin bawa da abinda yake gangar jikinsa Akan kaida da tsari tareda amarni yake.
Wasu irin kaidoji da dokoki tareda tsari masu tsauri da karfi aka fara dorasu dan kuwa ko tafiyarka a tsari take aka dorasu,
Lokutansu na bacci da fitowa fara aiki tareda wata irin tsaftar gaske duka Akan tsari suke da yanda ma zaka dago kai Ka iya kallan inda kake sbd kaida ne koyaushe Kanka ya zama a qasa,
Duk jin dadi da nutsuwar da suka samu a BOYEM din tsari da dokokin tini suka daga hankalinsu tareda shiga tsoro me tsanani sbd laifuka da kurakuran da zasu iya rabaka da ranka a masarautar yawa ne dasu sbd mafi yawan hukuncin kasar cire kai ne kawai kokuma ciyar da dabbobi namanka dan haka babu Wanda yake yadda komai tsananin tsautsayi yayi laifi dan tsira da rayuwa,
Mataki mataki ne na bayin masarautar sai Wanda yakeda matakin saar karshe ta rayuwa yake samun damar yin aiki a inda asalin jinin BOYEMs din suke.
***Ayanah da Zuhrah harma da sakina basuda Sauran kowane zabi Bayan mayarda hankali suna daukan karatun da ake musu tareda samun qarin nutsuwa sbd a yanzu damuwa da kuncinsu a natse ma yake cinsu,
Sun sauya sosai kawai dai quncin dake kwance a zuciyarsu ne yake hanasu yin jiki ko mulmulewa suna nan basu wani qara kiban komai ba kawai dai yunwa tabar jikinsu.
Kullum da safe a kaida da doka zasuyi wanka su shirya a cikin uniform dinsu tsaf tsaf su isa gurin karban abinci abi Layi su karba abinci su ci kafin masu wucewa aiki su wuce su kuma su isa inda ake karantar dasu acan suke wuni sai yamma suke dawowa.
Sakinah data Saba da bauta zuwa yanzu ta sake ta karbi sabuwar rayuwarta da babu matsi hannu bibbiyu tareda samun nutsuwa da gode wa Allah daya rayar da ita ta fito daga hannun kusra batareda rasa komai nata ba dan haka a yanzu batada doguwar damuwa saita Ayanah wadda koda minti daya quncin dayake zuciyarta bai taba fita ba zuciyarta a qulle take tamau da wani irin qunci da damuwan da har abada kila bazasu fita ba dan rayuwarta ta Riga tayi rushewan da bazata taba gyaruwa ba,
Tana komai Akan lokaci tareda komai da ake Dorasu akai a natse babu hayaniya babu rawan jiki komai nata yayi sanyi ya koma zallan nutsuwa bata sake bude baki ta Ambaci Abaas ko Nurat ba komai ta tattara ta ajiye sa a cikin zuciyarta yana cin lafiyanta da kwakwalwanta a hankali ahankali batareda sanin kowannensu ba,
Sakinah datafi su wayo da shekaru sosai ta fahimci Ayanah ta kafe komai a tsakiyar zuciyarta Wanda illar da hakan zai mata tasan mai yawa ce sbd ta riqe baqin cikin da quncin gam a cikin rai ta kasa fitarwa amma ganin bata nuna ba tana komai na rayuwarta a natse ya saka bata ce komaiba sai itama ta sake sbd tinanin insha Allah lokaci na tafiya quncin kila zai ringa wankewa yana ficewa daga ranta.
Zuhrah da farko mamakin Ayanah ta ringa yi ta yanda ta Dena maganar su Abaas kwata kwata da iyayensu ta nutsu duk da tayi sanyi sosai kaman ba ita dinba ko dagowan magana bata iya yi yanzu Wani irin miskilanci da son kadaici ya aureta,
Zuwa yanzu kusan sunsan koina a bangaren nasu na bayi da yawan bayin da suka taho tare sun sake sun karbi wannan rayuwar dari bisa Dari farin cikinsu sukeyi da walwala tareda jin dadi,
Suna Sauran sati daya a kwashe su zuwa cikin asalin masarautar subar daular bayin hankalin Zuhrah ya tashi sbd tsananin tsoro da fargaban shiga BOYEM palace take dan abu daya ne akace a cikin biyun matiqar Kafarka ta shiga gate din masarautar aka rufe to tabbas gawarka ce kadai idan lokaci yayi zata fito bauta ce zakai har tsawon ranka sai kuma idan Ka zamo daya daga cikin bayin da zaa riqa kwanciya dasu Ka zama abar kwanciya kenan a duk lokacinda aka ga dama har tsufanka shima kokuma idan an gama jin buqatar kusantar taka zaka koma tamkar fankon da baida Sauran amfani a duniya shikenan.
Wannan tinanin ne yake saka zuciyar Zuhrah shiga mafi girman tsoro da tashin hankali harma firgita takeyi a cikin baccinta duk tabi ta firgice ta rasa nutsuwarta ga yawan mafarkin Abaas da Nurat datake suna zuwar mata cikin yanayi na tsananin tausayi.
Yanayin ya saka ta fara kasa maida hankali Akan karatun da ake musu ta fara zama yanayi na kaman tana Neman fita hayyacinta,
Yau ma cikin damuwa me tsananin yawa take zaune ta kasa saka Kayanta daya fito wanka ta qurawa guri daya ido hannuwanta qanqame da uniform dinta kanta bai ma San tinanin dayake ba.
Ayanah ce ta fito wankan daure da abin wankanta me tsayi da kauri fatar jikinta ta samu lafiya sosai haskensu kusan duka ya kusa dawowa,
Cikin sanyinta da rashin hayaniya ta dauko uniform dinta zata saka Zuhrah daya zuba mata idanuwanta da sukai jajir zuciyarta na Wani irin zafi da quncin dayake lullabe dasu ta bude baki idanuwanta na cikowa da hawaye tace,
‘Ayanah kin samu sabuwar rayuwar data mantar dake abaas na can wata duniyar yana gararin da zai iya rasa rayuwarsa koma ya rasa din?
Ayanah kin manta komai ne kin zubar da komai?
Sakinah data fito wanka ne ta iso gurin Zuhrah din da sauri tana riqe hannunta cikin tausasawa tace
‘Kar kice haka Zuhrah’
Fizge hannu Zuhrah tayi tana Miqewa tsaye idanuwanta na gangaro da hawaye tace iso gaban Ayanah din wadda bata iya juyowa ba ta kalleta cikin wani irin radadin zuciya tace
‘Maye a cikin wannan sabuwar rayuwar daya mantar dake yan uwanki da halinda muka shiga?
Daman damuwarki Akan yan uwanki na dan lokaci ne?
Daman akwai jin dadin da zai taho miki ki manta dan uwanki dake can duniya cikin garari da qunci?….
Riqota da karfi sakina tayi tana cewa
‘Ya isa haka Zuhrah,kinfi kowa sanin Ayanah ba haka take ba karki Bari Batan tinani yakaiki ga aikin dana sani’
Sake fizge wa tayi tana kallan Ayanah wadda ta dago ta zubawa Zuhrah idanuwanta da sukai wani irin jajir tsananin qunci da radadi me ciwon gaske yana cikesu amma bazata iya cewa komaiba Bayan kallan zuhran dake fada mata maganganu masu ciwo da radadin gaske.
Zuhran ma cikin tsananin jin ciwo da radadin ganin idanuwan Ayanah din taci gaba da fada mata maganganun da itama suke sosa zuciyarta tace
‘Ayanah su Amma sai sunyi Allah wadai dake da zasu dawo duniya su ga yanda kika zabi jin dadin duniya kika manta amanar da suka bar miki a lokaci dan qanqani,
Abaas zaiyi baqin cikin zabar sonki fiyeda Sauran yan uwansu idan yaga yanda kika zabi wata rayuwar akan tinaninsa,
Ayanah inama ace Nurat ce aka bar mana dan ita bazata taba manta yan uwanta ba koda bata cikin hankalinta…..’
Wasu irin hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Ayanah a karo na farko Bayan tsawon lokaci mai nisa,
Silalewa qasa take kokarin yi sakina tayi saurin riqeta tana fasa kukan kalaman Zuhrah itama sbd tsananin tausayin Ayanah wadda har lokacin ta kasa furta komai sbd rabata da ranta ne kawai kalaman Zuhrah basuyi ba amma sun gama ratsa zuciyarta sun yayyankata,
Kalaman sun qarasa karya duk wani kuzarin daya rage mata na rayuwa,
Kalaman sun yanka mata sabon Raunin da shima har abada bazai warke ba…….
Wasu irin hawayene ke gudu sosai a fuskanta ta kasa iya tsayuwa duk riqon da sakina tayi mata silalewa qasa tayi tana Dora tafin hannuwanta biyu a fuskanta ta rufe wani irin kuka mai qaramin sautin daya saka Zuhrah yin tsit yana zuwar mata jikinta na wata irin rawa sosai wadda ta saka sakina zubewa qasa tana rungumeta da sauri,
Zuhrah ma sautin kukan ya ringa sosa zuciyarta ta durqushe itama a gurin tana fasa kuka sosai zuciyarta na dana sanin saka Ayanah kuka irin haka.
Shiru dakin ya dauka babu sautin dayake tashi saina kukansu mara sauti sosai amma babu dadin Ji ko kadan.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
22
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
*********
Sun jima a wannan yanayin kafin Ayanah ta taqaita kukanta data jima bata samu yi ba sai yau ta miqe tareda sake komawa toilet.
Acan ma wani irin sabon kuka ta durqushe tana yi Wanda dukkaninsu suna jiyota daga bandakin sai data jima tayi ta gama ta wanke fuskanta da ruwa ta fito ta goge fuskanta ta shirya cikin uniform dinta tana jin kirjinta da zuciyarta na Wani irin ciwo amma batada abin yi musu kawai qarasa shirinta tayi ta koma gefe ta zauna tareda kallan Zuhrah dake kuka har lokacin ta taso ta rankwafo kawai ta sumbaci tsakiyar kanta da gefen fuskanta ta bude baki da tsananin sanyin murya ta bude baki tace
‘Ya isa haka ki wanke Fuska ki shirya mu fice’
Ajiyan zuciya Zuhrah ta sake tareda dagowa ta kalli Ayanah din zata bude baki tayi magana Ayanah ta girgiza mata kai tana cewa
‘Ba komai ya wuce kije ki shirya din’
Miqewa Zuhrah tayi ta fada toilet duk ta zama kalar tausayi.
Tana fitowa sakinah ma ta shiga suka gama shiryawa tsaf suka fito su ukun suka wuce zuwa hall din karatun.
Wannan sabanin da suka samu ya sake ruguza Ayanah ta qarasa rasa walwala da kuzarinta sbd damuwan datai mata yawan gaske a cikin rai dan haka ta sake zama tamkar qanqara sbd sanyi da rashin magana sosai,
Komai Zuhrah takeso shi kawai take mata bata iya hayaniya ko magana koyaushe indai suna daki Zuhrah na jikinta kwance zata rungumeta tana mata addua da shafata dan bata nutsuwa sbd tsoro da firgici na Neman taba kwakwalwan Zuhrah din tsoro mai tsanani kawai take samun kanta sbd ganin kaman suna shiga palace din sun rasa kansu kenan har abada kila ma harda junansu,
Tsananin tsoron rabuwa da Ayanah take ji fiyeda komai ma daya faru a baya,
Idan har zata rasa Ayanah so take Allah ya dauki ranta ta mutu,
Koba komai mutuwar ma take tsananin so sbd rashin nutsuwan datake ji a zuciyarta.
Ana gobe ne ranar tafiyarsu zuwa cikin palace a zaune suka kwana rungume da juna Sai a Daren Ayanah ta bude baki tayi doguwar magana da Zuhrah din tareda tinatar da ita babu abinda zasu iya yi a duniya yanzu su samu damar haduwa da Abaas wata rana irin su jajirce su rayu har zuwa lokacinda Allah zai sake kawo musu wani sauyin rayuwar,
Babu abinda zasu sakawa kowane dan GHAZ dashi Bayan su rayu su kai labari dan haka matiqar tanason Allah ya kawo mata ranar haduwa da Abaas ko jin labarinsa to tabbas zata jajirce ta rayu zuwa lokacinda Allah zai dauki ranta.
Zuhrah da Sai a lokacin ta fahimci karfin halin da Ayanah takeyi jin tayi jikinta ya sake mutuwa dan kuwa kaman ita bazata iya ba takeji amma ko bazata iya ba zatai kokarin bawa Ayanah karfin gwiwan rayuwa sbd itace kadai a raye wadda take saka zuciyar Ayanah bugawa daidai,
Ita dai kam bazata iyaba da gasken gaske duniyar take son Allah ya dauketa daga cikinta ta tafi ta huta amma kuma idan babu ta Ayanah zata zama mara amfani a duniya sbd bazata taba moruwa ba.
Koda asuba tayi suna tsaye sbd tin kafin asuba aka tadasu aka tarasu a babban guri,
Anan aka sake rarraba musu uniform da abubuwan amfani a jaka aka bawa kowa nasa,
Sallar asuba kawai suka koma daki sukai aka sake buga qararrawa kira suka ringa fitowa kowa dauke da jakarsa fes dasu,
Jikin Ayanah dana Zuhrah a sanyaye sbd Sai yanzu ne Ayanah take sake fahimtar tsoron Zuhrah na zaa iya rabasu a gurin aiki ko gurin kwana dan haka itama jikinta ya tsananta sanyi.
Motoci ne masu tsayi bus bus aka zuba su a ciki aka fice dasu zuwa cikin palace din.
A mota ma hannuwansu na riqe dana juna qamqam sakina na gefensu,
Ficewa akai dasu daga babbar gate din daular bayi aka miqa zuwa mahaukacin gate din shiga BOYEM palace wadda securities dinta suka mugun baci sbd tsananin tsaro,
Shi Karan Kansa gate din shiga Masarauta kashe idanuwansu sukaga kaman yana yi sbd kyansa dayake tamkar na zinari,
Scannin komai nasu dasu kansu akai daya bayan wuni guda Ana abu daya kafin Ana gap da kammala wa aka zo kan wasu su biyu wainda sunan mahaifinsu Yazo irin daya komai da komai.
Dakatar dasu akai tareda zagaye su da wasu irin securities da suka sakasu saurin durqusawa kasa kansu a qasa jikinsu na wata irin rawa cikeda tsoron dake Neman rabasu da bugawan zuciyarsu.
Chief security ne Yazo gurin da Kansa ya kallesu dakyau kafin ya kalli sunayen nasu
Akan wadda tafi girma ya tsaida idanuwansa ya bude baki yace
‘Meye alaqarku da sunanku Yazo daya??
Wani yawu babbar ta Hadiye kafin cikin sanyi kanta na qasa tace
‘Alaqar jini ce……
Ko rufe baki bata gama yi ba akai sama da ita tamkar ba Mutum ba aka jefa cikin wata motar da batai Kama da mota ba sbd tsarinta dayafi Kama da motar yaqi.
Wani ihu taje yi tana kokarin riqo qanwarta a lokacinda ake janta tana jin kaman ranta zai fita amma ko imanin kallanta babu take aka buga kanta da karfen motar ta zube a cikin motar jini na fitowa gefen fuskanta kadan.
Qanwar tata ma Wani irin kuka me karfin gaske takeyi tana ambatar sunan yar uwarta kaman ranta zai bar jikinta take aka sumar da ita da wata shocker a gurin akace a dauketa a maidata daular bayi.
Ganin hakan ya saka wainda ke bayinsu suma su uku fara rawar jiki sbd suma yan uwane uwa daya uba daya.
Suma Ana duba sunayen su take aka rarrabu su ukun aka soke lasisin biyu aka bar daya Sauran zaa rabasu zuwa dauloli daban daban ga Wanda yayi rashin saa kuma ciyar da dabbobi namansu kawai akeyi sbd tin farkon shigowa qasar baa karban bayin da suke da alaqa da juna,
Doka ce da kaida me tsananin karfin gaske baa barin masu alaqa a masarautar matsayin bayi duk lokacinda aka Kama masu alaqa kai tsaye hukuncinsu a kashe daya abar daya tin asalin asali wannan dollar take sbd a shekarun baya sosai da suka gabata akwai bayi uku da suke uwa daya uba daya da suka kulla shirin guduwan juyin mulkin daya haddasa fitina mai tsananin gaske a masarautar boyem wadda baa taba maimaita irinta ba dan haka tin kakannin kamanninsu aka tsauranta dokar tareda kafata mai karfin gaske kai tsaye duk bawan daya kasance yanada ahali to kai tsaye hukuncin Kisa ne ga ahalin gabaki dayansu sbd kawar da kowace irin barna,
Bayi da yawa tin shekarun da suka gabata sun rasa ahalinsu akan hakan,
Duk bawan dayake boyem Sai an tabbatarda baida kowa a duniya Bayan Kansa sbd Kaucewa fitar sirrin masarautar Shiyasa ko Ka samu yancin Ka baka taba barin qasar boyem sbd bakada kowa a duniyar sedai Ka Gina sabuwar rayuwa.
Dan hakanne yasa duk wainda suke kawo bayi qasar sai sun tabbatarda bayinsu basuda kowa a duniya ko sunada Sai a tabbatarda basa duniya an kawar dasu sbd Ka zama na masarautar ita daya,
Kusrawa tin a farkon shigowa qasar sun tabbatarda bayinsu basuda kowa a duniya dan hakanne kai tsaye a yanzu duk Wanda aka samu yana tareda wani nasa zaa kawar da daya a bar daya.
Doka ce da tsananin karfinta babu Wanda zai taba wucewa kai tsaye ba tsayawa tinanin komai ake kawai da daya dan haka yanzu dinma hakanne zai faru akan wainnan sabbin bayin.
Cikin masifaffiyar azaba suna tsananin fita hayyaci suke kasa rabuwa da juna inda daga karshe suka zabi a dauki ransu su duka ukun wainda suke Bayan na farkon dan hakan babu bata lokaci take aka jasu su ukun kai tsaye akai baya dasu sedai kawai yaji qarar bindigar cika musu burin abinda suka zaba amma babu Wanda yaga inda aka fito ko yi da gawarsu.
Zuhrah da Ayanah dake kusan qarshe dagowa sukai a Wani irin slow suka kalli juna dukkaninsu jikinsu na qarasa sakewa gabaki daya da sabuwar mummunan kaddarar dake gabansu wadda basuda ma tinanin yi akanta.
Jajir idanuwan Ayanah sukai Zuhrah kuwa gangarowa nata hawayen suka fara da idanuwanta da suka kasa daukewa daga kan Ayanah tanajin tin yanzu tamkar ruhinta na barin jikinta sbd rabuwa da Ayanah na nufin mutuwarta,
Ita zata zabi a kasheta abar Ayanah sedai kuma basuda masaniyar waye zaa Bari a cikinsu kuma waye zaa bari,
Ita tanason Ayanah ta rayu sbd tanada dauriya da tawakkali hakama zata rayu a cikin aminci anan din amma kuma tasan Ayanaah zata zabi a kashesu gabaki dayansu kaman yanda na gabansu suka zaba sbd bazata iya barin a rabasu ba.
Wasu hawayen ne masu zafi suka gangaro mata tana sake kallan Ayanah tanason rungumarta taji dumin jikinta na bankwana amma daman hakan ta gama qare musu har abada dan haka zata zabi su rayu sbd Ayanaah kawai koda hakan na nufin raba jininsu har abada indai tana ganinta hakan ma ya isheta.
Sakinah dake gabansu dan juyowa tayi ahankali ta shiga tsakiyar su itama idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin tausayinsu musamman Ayanah dake girgiza kai ahankali idanuwanta na tsananta ja hannuwanta na fara rawa ahankali ta bude baki tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 28