Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Abaas din nan dan ganin likitocin, Manyan motocin ghaz dake qasar ne suka taho har airport suka daukesu shikuma Abaas ambulance ta asibitin ce ta taho dan haka kai tsaye asibiti suka dunguma gabaki dayansu. Koda aka isa asibiti da Abaas ya farfado sedai zuwa lokacin gabaki dayansu jikinsu yafara mutuwa me tsananin gaske ta yanayinsa dan haka Koda suka iso abinda NUAB ya saka akai musu shine hade Abaas din da Ayanaah a daki daya. Koda suka iso asibitin babu kowa sbd baa barin relatives shiga kai tsaye dan haka sultan Bayan an kammala komai na admitting Ayanah dashi da tenya tareda securities dinsa da fadawansa barin asibitin sukai zuwa masaukinsu sai kuma idan an nemesu dan haka Sam basuma San isowan su NUAB ba. Duk wani taimakon gaggawa da doctors zasuyi wa Abaas dayake fidda jini a bakinsa a duk ya yunqura da tarin da bayama fitowa sbd rashin karfi ko kadan daya rage a jikinsa sunyi sunga ma sunbarwa Allah dan haka NUAB shigowa yayi dakin a sanyaye kafafunsa da Wani irin mugun nauyi ya tako ya iso inda yake. Tsayawa yayi ahankali bakin gadonsa tareda miqa hannunsa a tsananin sanyaye ya Dora Akan na Abaas din Wanda ya fara bude nasa idanuwan da ganinsu ya fara ragewa ya saukesu Akan NUAB din. Wani irin Numfashi me tattare da sanyin jiki NUAB ya sake tareda daga hannun Abaas din ahankali ya Dora Akan na Amminsa dake kwance har lokacin bata farfado ba ya hada hannuwansu guri daya ya matse musu su da nasa hannuwan biyu yana sunkuyar da Kansa qasa wasu hawaye masu tsananin Zafin gaske suna ciko idanuwansa ya kasa cewa komai…. Kokarin tsayawa Numfashi da bugawan zuciyar Abaas sukeyi sbd abinda ya dirar masa zuciya ya Lumshe idanuwansa ya bude ahankali da qurawa fuskar NUAB dake sunkuye ido batareda ya juyoba yaga fuskar hannun dayake hade da nasaba sbd bazai iyaba. Aleey ne dayake Bayan NUAB din ya tako a sanyaye shima nasa idanuwan na cike da hawaye masu zafi ya Kama kan Abaas din cikin kulawa da ya juyo dashi setin fuskan Ayanaah dake gefensa Akan nata gadon daban idanuwanta a rufe fuskarta fayau asalin kamanninta babu abinda ya sauya sai manyanta datai…. Wasu hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Abaas daya kasa kyaftawa daga kafe idanuwansa dayayi Akan fuskar Ayanah hawayensa na tsanananta gangarowa da Wani irin dumi, Bude bakinsa yakeson yi ya Ambaci sunanta amma Allah bai basa damar hakan ba dan haka hannunsa ya dan iya motsawa ahankali ya Kama hannunta cikin nasa tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi ya rufe idanuwansa ahankali wasu hawayen suka gangarowa ahankali idanuwan na rufe. Shiru gurin ya sake dauka me tsananin gaske Wanda ya saka NUAB sauke ajiyan zuciyar daya sauka tareda wasu irin hawaye masu Zafin gaske daga idanuwansa da suka kasa riqe dukkanin jarumtarsa. Aleey ma Juyawa yayi ahankali yana saka hannunsa daya ya rufe idanuwansa dake fidda hawaye sosai har hannuwansa rawa sukeyi kaman yanda na NUAB ke wata irin rawa sbd tabbatarda Ran ABAAS GHAZ ayau yabar jikinsa ya amsa kiran ubangiji. Sakinah dake bakin kofa rawa jikinta itama ya dauka me tsananin gaske ta saka hannu da karfi ta rufe bakinta tana fasa wani irin kuka Mara sauti zuciyarta na tsananin ciwon me Zafi. BAHAR da bata fahimci meya ke faruwa ba tana tsaye daga waje idanuwanta jajir ganin irin yanda sakinah ke Wani irin kuka jikinta na jijjiga ya sakata fara takowa ahankali ta sako kai cikin dakin kafafunta na rawa. Gap da isowa ga mahaifinta data kafe da ido takeyi Aleey ya sake fasa wani irin kuka me sautin daya sakata fahimtar Abaa dinta ya bar duniya yabarta. Duhu ne ya rufe zuciya da idanuwanta ahankali Wanda ya sakata kafafunta gazawa ta yanke jiki a gurin ta zube jikin NUAB Wanda ya tarota da hannu daya har lokacin Sauran hannunsa daya yana riqe da hannun Abaas da Ayanah. Doctor shigowa sukai suka fara kashe naurorin dake manne da Abaas din bayan sun rubuta time of death nasa. Daganan ficewa sukai sukabar fmly da jimamin rashin. Kuka sosai sakinah takeyi kaman rayuwanta tazo karshe sbd wannan itace kaddarar karshe data qarasa yanke farin cikin dasuke sakaran yi a gaba, Ayau Abaas ya tafi yabar duniya kaman yanda Nurat da Ayshaah suka tafi sun barsu da tabo da gurbin da bazai taba cikewaba har abada. NUAB daukan Bahar yayi yakaita Dayan dakin da doctors zasu dubata kafin aleey ma da yasha kuka sosai ya fara shirin komawansu da gawar da bazaa rufeta a nan ba dole zasu koma dashi ghaz acan zaa rufesa. Zaman qunci da damuwa tareda zullumi me tsanani sukai kafin cikin saa suka samu jirgin dawowa da gawar wadda Washe gari tinda safe suka Juya kuma har lokacin Bahar bata farfado ba haka suka dawo da ita. Haka suka kuma doguwar tafiya kafin suka sauka kai tsaye suka sake daukan manyan motocin da suka kaisu har cikin ANJOM ghaz da gawar Abaas GHAZ Wanda a lokacinda Bahar ta farfado rungume gawar tayi ta kasa cewa komai hatta kukan ya kasa zuwar mata idanuwanta ne kadai sukai Wani irin ja. A haka babu bata lokaci akai janaizarsa aka rufesa a cikin masarautar gefen kabarin mahaifinsa da mahaifiyarsa da Ayshaah da akai a cikin masarautar duka dan haka Ana gama janaizarsa suka tattaro suka juyowa tareda Bahar wadda gabaki daya baa San ma Wani halin rayuwarta take ciki ba sbd ko kyaftawa kaman batayi komai nata ya tsaya cak tana rungume a jikin sakinah wadda take jinta har cikin jinin jikinta. Suna isa qasar inda zasubi jirgi anan NUAB ya bada umarnin Maa sakinah da Bahar a wuce BOYEM dasu shikuma zai koma ga Amminsa. Zasu wuce Bayan kowa ya fice kallan Maa sakinah NUAB yayi da manyan idanuwansa da sukai tsananin Laushi ya tattaro dukkanin nutsuwansa ya bude baki yace ‘Maa ina Neman wata alfarma da nakeson kimun alkawarinta a yanzu, Inason kimun alkawarin idan Ammi ta farfado bazaki taba fadawa mata Abaas yabar duniyaba sbd bazata iya dauka ba a yanzu da muke kokarin Neman lafiyanta, Kimun Alkwarin bazata taba sani ba Bazata zan komai ba har sai ranar dana fada mata hakan da kaina, Zuwanmu ghaz da duka abinda ya faru Inason ya zama sirrin da bazai taba fita ba sbd lafiyarta da bazata iya dauka ba, Ki riqe ‘yarsa Amanace ya bar miki amma kada Amminah tasan wace ce ita sbd sanin ita waye din zai saka dole tasan anga Abaas ankuma rasashi dan haka ita din batada kowa sai ke sbd auren da aka daura ba aure ne dazaa tinaba bare qararwa, Maa Inason kiyimin wannan alkawarin’ Numfashi mai tsananin dumi sakinah ta sauke tareda dagowa ta kalli NUAB tukuna ta Gyada kanta alaman tayi wannan Alkwarin har karshen rayuwarta matiqar ba shine ya tado zancenba ta rufesa kenan har ranta ya fita. Numfashi me nutsuwa ya sauke kafin yayi sallama da ita aka wuce dasu airport ba bata lokaci jirginsu ya daga zuwa BOYEM. Suna wucewa da awa hudu suka nasu jirgin yayi daga zuwa ga Amminsa wadda bazai taba dawowa da ita ba matiqar lafiyarta bata daidaitaba. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualir *_HAYATEEM_* Mamuhgee 70 A jirgi kwance jikin Maa sakinah Bahar ke kwance idanuwanta da sukai ciki ciki jajir da galabaitar rayuwa da zuciya tareda sarewa da fidda rahama ga rayuwa gabaki daya, Rungumeta cikeda wata irin kulawa da kauna me tsananin gaske da Jinta har jininta Maa sakinah tayi sbd BAHAR itace Abaas da suka rasa har abada sai kuma Aljannah idan Allah yayi sunada rabon haduwa, BAHAR itace jini daya tak ta Abaas dinsu a duniya da idan basu jita har cikin jininsu ba me zasuyi? BAHAR itace jinin Abaas da duniya Ayanah batada kamarsa, Ayanah Allah baiyi tanada rabon sake Dora idanuwanta Akan ‘dan uwanta ba rabin jikinta ba sedai tanada rabon rayuwa da ‘yarsa a matsayin matar ‘danta da bazata saniba sbd ita kanta koda NUAB bai sakata alkawarin kada ta fada mata Abaas ya tafi yabar duniya ya barta ba itama kanta bazata taba iya fada mata mutuwar Abaas ba Wanda Ayanah bazata iya dauka ba dan haka wannan Alkawari ne ta daukanwa kanta itama bazata iya fada matan ba sedai shi NUAB din duk ranar dayaga ya kamatan, BAHAR Amanarta ce a yanzu da zata riqe da rai da rayuwarta tareda bata kariya da dukkanin kauna da kulawan tareda tattalin data rasa tin tasowanta, Insha Allah indai kulawa da nuna kauna da soyayya me tsanani sune suke kawo haske a rayuwar datake cikin duhun kadaici to tabbas zata cikewa Bahar duhun rayuwarta da haske koda kuwa zasu qare a cikin wannan sirrin su mutu matiqar hakan na nufin kariya da samun tsaronta. Numfashi ta sauke ahankali me sanyi da mutuwar jiki tana tina rayuwarsu ta baya da yanda suka Baro ANJOM GHAZ da kuruciyarsu dukkaninsu amma ayau gasu sun manyanta wasu sun rasu sun bar duniya wasu kuma basa tareda su ita kuma gatanan ayau da ‘yar Abaas a hannunta batareda dukansu sunsan hakan kaddara ta tanadar musu ba. Wasu hawaye ne suka ciko idanuwanta tana kallan tata rayuwar da babu komai a cikinta face kaunar jinin GHAZ da bauta musu har qarshen tata rayuwar da batasan Yaushe ne ba amma koma Yaushe ne tana fatar Allah ya dauki rayuwarta itama a cikin aminci da kauna. Shafa fuskar BAHAR data rufe jajayen idanuwanta a hankali tayi tanajin kaunar Bahar din na sake ratsata sbd rayuwarsu a wannan matakin da suke kai yanzu iri daya ce, kaddararsu iri daya ce, Basuda uwa basuda uba basuda Wanda kai tsaye zasu kira nasu Bayan Ayanah dake kwance basu San yaya tata kaddarar zata kasance ba sai NUAB Wanda ayau idan ya rasa Amminsa kila shikenan yabar BOYEM da duk Wanda yake cikinta har abada su kuwa kila duniyar zasu bi sbd rashin Ayanah a BOYEM zamansu a BOYEM din ya qare sbd ita sakinah ba baiwa bace a yanzu hakama Bahar din duk da a yanzu basuda zabin daya wuce a shiga da ita masarautar a matsayin baiwa tinda babu Wanda yasan ita wace ce hakama babu damar fadar ita din waye Wanda sakinah batada zabin daya wuce ta tafi da ita a baiwa matiqar tanason kasancewa da ita batareda Ayanah tasan komai Akanta ba bare mutuwar Abaas. Tausayin Bahar din ya sake cike zuciyarta sbd batasan tayaya zata fara fuskantar rayuwar da zasu tarar din a BOYEM ba musamman da suke ba kowa ba basuda kowane karfin kansu, Hannun Bahar din na hagu dayake ajiye Akan kafafunta ta zubawa ido Akan lambar 99 dake zane a hannunta Baro Baro tayi baqi sosai Akan farin hannunta daya keda fari sosai sbd zamanta bata Baro komai na mahaifiyarta ba, Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwan sakinah dake Haba kukanta zuwa sbd da wuta aka rubuta lambar 99 din wadda take lambar Abaas ta Shedan zama cikakken bawa da kusrawa sukai musu, Lambar mahaifinta Abaas ce a jikinta zeti da inda akai masa tasa shima a gefen hannu daga sama gurin gwiwan hannun, Rufe baki da hannunta daya sakinah tayi tana kukanta bayyana sbd Bahar dake shiru a jikinta, Nata hannun ta kalla inda tata lambar take Baro Baro a jiki 96, Zuhrah ce 97 sai Nurat 98 tukuna Abaas dinne 99 Ayanaah 100 Wanda haka akai musu su a Jere babu Wanda a cikinsu haryanzu wannan lambar bata jikinsa Wanda da ita zasu mutu, NUAAB tin da ya tashi yaga mahaifiyarsa da wannan lambar a jikinta da hannunsa ya zanawa Kansa lambar a jikinsa da wuta sbd itace lambar dazai tabbatarwa Abaas shi din ‘dan Ayanah ne dan haka da lambar mahaifiyarsa ya tashi a jikinsa bata taba dauka Abaas shima yayiwa tasa yar lambar sa ba sbd koda baya raye da lambar sa zasu yadda da Bahar ‘yarsa ce. Kuka sosai Maa sakinah din tafasa tana kasa riqe kanta sbd har abada sunyi rashin da bazasu taba manta radadin sa ba, Sunyi rashin da shine mafi ciwon rashin da sukai a baya Bayan nan. BAHAR dake kwance shiru zuciyarta bata iya komai Bayan bugawa ahankali sbd komai ya tsaya mata cak tana jin sautin kukan Maa sakinah yana shiga kunnuwanta a hankali yana ratsata sbd tasan kukan rashin Abaa dinta ne akeyi. Bude idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikinsu a sanyaye tana sake Numfashi me sanyi Mara sauti batareda ta motsa daga kwancen datake a jikin matar da bata taba saniba a zahiri Sai a tarihi amma ayanzu da ita kadai zatai rayuwa. Tafiyar kusan wuni guda sukai kafin jirginsu ya sauka a qasar BOYEM suka fito tareda securities din NUAB din duka da aka hado su dasu shikuma daga shi sai aleey suka koma. Motocin alfarmar GHAZ ne suka daukesu daga airport zuwa Masarautar BOYEM me tarin abubuwa da tarihi dama Wani tarihin da zaa kafa. Ko a cikin mota hannun BAHAR din yana cikin na Maa ta riqe cikin nata tana bata dumin dazai Haba gangar jikinta qarasa rasa kanta. Duk duniya da Aljannar duniyar dake tin daga babbar gate din farko ta masarautar bai shiga idanuwan Bahar ba bare zuciyarta sbd komai na rayuwarta a yanzu rufe yake gap babu kowane irin Sauran shaawa ko burgewa a rayuwa da zai shigeta dan haka idanuwanta a kafe suke kawai a waje tana kallan wajen amma kwata kwata tinaninta baya jikinta ko daya tayi nisa a tinanin rayuwar datai a baya da mahaifinta Wanda a yanzu yana kwance cikin qasa, Tafiya sukai suka sake wuce gate na biyu har zuwa gate na uku suka shige akai parking motocin bakin hanyar da zata kaisu bangaren cikin gida kai tsaye aka bude musu motocin dukansu su biyun a lokaci daya. Maa ce ta fara fitowa a natse cikin sanyin jiki ta sauke ajiyan zuciya da Numfashi kafin ta zagayo ta miqa hannu cikin motar ta Kama hannun BAHAR wadda bata motsaba tinda aka bude mata motar ta janyota a hankali cikin kulawa ta fito motar, batareda ta saki hannunta ba ta jata a natse zuwa ciki suna tafiya babu me karfin jiki. Duk Taku daya da Bahar ke yi Wani siririn sautin sarkar kafarta ta mahaifiyarta data gada ne yake tashi tareda Wani irin sakar da nutsuwa da saka son juyowa ga duk Wanda sautin ya shiga kunnensa dan hakane duk tayi Taku daya bayin dake jere a hanyar sai sun sauke kansu qasa cikeda girmamawa ga Maa sakinah wadda kowa yasan matsayinta na shaqiqiyar Wishmah kuma jakadiyar bangaren wishmah ta biyu. Kai tsaye hanyar bangarensu Maa ta nufa da BAHAR wadda har lokacin duk inda Maa ta jata saka kafa kawai takeyi ba Wani kuzari a jikinta. Isowarsu gap da hanyar data raba bangaren Queen HAILE da bangaren Wishmah Ayanah a daidai wannan lokacin Li’uli ASIM ALMAZZ ya fito bangaren mahaifiyarsa cikin shigar sky blue cashmere mai fitinanniyar tsada qamshinsa yana sauya niimar gurin take dukkanin bayin dake hanyar suka sauke kansu qasa suna tsayawa cak inda suke har saiya wuce. Maa sakinah dake gap da shigewa da Bahar bata juyowa tayi a natse dan basa girmamawa itama a natse Banda Bahar da batasan me takeyiba daga kafarta tayi tana cigaba da Takawa ba karfi a gangar jikinta ko kadan. Sautin takunta ne da sarkar kafarta ke fiddawa a natse a gurin daya dauki tsit tamkar babu rai ko daya a gurin sbd bada girmamawa garesa ya sakasa tsayawa da takunsa cak yana dakatawa. Sake ratsa kunnuwansa sautin yayi Wanda ya sakasa juyowa da Wani irin nutsuwa da mamaki yabi inda sautin ke fitowa da kallo a daidai lokacin Maa Sakinta ta riqota cikin nutsuwa da juyo da ita a hankali sbd inda yake dosa ba can zasu nufa ba. Kafafunta dake rufe cikin doguwar rigar dake jikinta ash Kala wadda batada adon komai sedai daidai jikinta take ta sauka qasa sosai harma tana dan ja da kasa kadan mayafin rigar ne kadai yakeda adon dayake qawata rigar da fuskar da zata saka kayan ya tsayar da idanuwansa yana kalla amma babu ta inda kafarta ta fito se sautin. Dagowa yayi a natse ya maida kallansa kan fuskarta zuciyarsa na dauka Wani irin Zafin mamaki da jin abinda bai taba ji ba a bayi sedai yayan sarautar ne kadai sukeda iko da wannan damar dan haka mamakinsa ya dan qaru yana bude idanuwansa da kyau a kanta. Fuskarta dake bayyane ya zubawa idanuwansa yana kasa daukesu daga kanta mamakinsa na sauka ahankali tamkar wutar da aka zubawa ruwa, Bin fuskarta yake sakeyi da kallan dayake sake saka zuciyarsa mamaki da jin Wani irin yanayin daya sakasa kasa dauke kallansa akanta. Shiru gurin ya sake dauka musamman da Bahar din bata sake ko motsawa ba har tsawon mintina kafin ya dauke idanuwansa daga kan kyakkyawar fuskarta ta jinin GHAZ ya juya a natse batareda yace komaiba ya wuce zuciyarsa na riqe kamanninta da kai tsaye suka isa gareta. Yana barin gurin Maa sakinah ta Kama hannunta suka nufi kofar da take aka bude musu ita gabaki sbd girmamawa suka shige aka rufe. Babban palon dayake na farkon isa suka shiga Maa sakinah ta sake ajiyan zuciyar samun isowa gida cikin Amintci. Dakinta kai tsaye ta wuce da Bahar, Komai na dakin a gyare yake sbd babu ranar da baa Shara so biyu a kunna qamshi, Ac ne kadai baa kunne ba sai wuta dan haka kai tsaye remote ta dauka ta kunna komai Wanda take haske ya haske dakin gabaki daya tamkar fitowan rana, Makeken bedroom ne dayake dauke da royalbed me kyau da girma sosai sai Sauran set din royalbed din su wardrobe da dresser tareda bedside da wata lallausan Turkish carpet da table sai couch masu Laushi da tsari, Duk wani jin dadi da tsarin dayake bayyanarda Hutu da kwanciyan hankali shine a dakin komai a tsaf ga sanyin ac din ya fara ratso wa yana kokarin Kama dakin. Zaunar da ita Maa sakinah tayi tareda zare mata rufar kanta a hankali gashinta dayake rufe ya zubo a hankali yana bayyana Maa ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan baiwar data shigo dakin dauke da babban tray da kayan sanyi da fruits masu sanyi ta bude baki tace ‘Ki hada ruwan wanka masu dumi’ Gyada kai baiwar da ake da Salmah tayi tana ajiye tray din ta juya kanta a qasa ta nufi toilet din dayake dakin na Maa ta shige dan hada ruwan wankan. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali End of part 1 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 28 of 28