Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bata taba daraja mahaifiyarsa ba. Rintse jajayen idanuwansa yayi yana sake Jin fushin da bai taba Jin irinsa ba yana danne kirjinsa da numfashinsa ya bude bude ido yana dunqule hannuwansa biyu da suke wata irin rawar tsantsar bacin rai da baqin ciki me tsananin gaske. Tsit bangaren nasa ya dauka harma da zagayensa dan kuwa niimar bangarorin duk Wanda yake jinin masarautar dumi ya dauka me karfin gaske sbd masifar da babu shiri data fadowa kowannensu a Daren. A bangaren sultan shima a Zaunen kaman yanda duka iyalansa suke ya kwana zuciyarsa cikeda abubuwa daban daban da suke shirye da karban tsanar kowace iri daga NUAB da kowa ma matiqar zai Kai qure lambar fushi da Zafin kan NUAB ya sakasa karban mulkin Masarautar dayake shirye da sauka ako Yaushe dan kawai ya Dora sa akai Wanda saiyayi hakan zai samu nutsuwa da sukunin dabai samu irinsa ba tinda ya hau mulkin. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 59 Koda safiyar garin ta waye kowa dake cikin ahalin da ciwon Kai masu tsanani suka ringa tashi dashi tareda ciwon rai shima me tsananin gaske ga wainda suka samu rintsa wa baccin kenan ga wainda basu rintsa ba kuwa kaman wainda suka kwana gadin gawa haka suka tashi da idanuwa kaman baqin china. NUAB ALMAZZ da duk Wanda yake bangarensa cikin Yaransa kaf babu Wanda ko gifta masa bacci yayi a ido, Dan haka Koda ya fito sallar asuba sukai sallah a tare daga nan geamin suka shiga dakin da aka tsara masa dan hakan suka fara geamin har lokacin suna iya ganin fushinsa da bacin ransa bai gama sauka ba dan haka a kiyaye da shirye da kowane shirin suke hakama kaman yanda baice komai gameda tafiyarsu datake a ranarba babu Wanda ya tada maganar sbd a shirye suke da qarasa rayuwarsu anan matiqar baice ga ranar da zaa wuce ba su a inda ya zabi rayuwa acan tasu rayuwar take suma dan haka bangaren tsit yake babu wulgawan kowane bawan da baa nan yake aikin hidimar NUAB ba Wanda ko ruwan shansa basu cika barin kowa na basa ba idan ba su din ba sbd tsaro. Tenya da Maa sakinah kuwa tinda garin ya waye suke juya yanda zasu isar da sakon sultan ga Ayanah wadda ta tashi da tsananin kulafucin son ganin NUAB sbd tafiyarsa da zaiyi a ranar ya tafi da ita dasu sakinah dan haka Ayau din ma koda bayinta suka gama hada mata ruwan wanka tana tsaye jiran su gama tayi ta shirya dan kuwa haka take Jin tsananin kewan Abaas Wanda a zuciyarta tana barin masarautar take ganin zata hadu dasu. Karfe tara na safe Ayanah ta gama dukkanin shirinta tana Zaune tana jiran NUAB Wanda ya kasa zuwa inda take dan baisan tayaya zai iya kallanta ba ya sanar mata ya daga tafiyar tasu data saka aranta sosai, Shi kansa tsoron Wani ciwon ya sameta ko jikinta ya rikice ya saka ya rasa ta yaya zai kalleta, A Karan farko rayuwarsa da Wani ya sakasa a matsatsen yanayin da komai nasa ya tsaya cak batareda ya kaddamar da danyen hukuncin akansa ba, Maganar data shafi mahaifiyarsa tafi masa business deal din billions na dollars a rayuwarsa, Akan lamarin da duk ya shafi mahaifiyarsa baya masa garaje hakanne ya saka sultan yakeson ya quntata masa ta hanyar bullo masa ya nuna masa karfin ikonsa dayake kanta shima. Karfe sha daya da rabi ya shirya cikin black fendi wears da black geometric shape glasses na tom ford qamshinsa na tashi a hankali ya fito ya tinkari bangaren mahaifiyarsa Aleey na gefensa yana waya a natse shima Akan Wani business dinsu Yaransa biyu ne a bayansa da umbrella sai bayi kusan goma a can Bayan yaran nasa da suke bayin da aikinsu basa Rakiya da tsaro na cikin masarautar Wanda Sarkin bayi ne ya tanadar masa su masu karfin gaske ya aiko a matsayin bayinsa. Ko kafin ya iso a daidai wannan lokacin Ayanah ta dauko wayarta zata saka kiran NUAB dabai taba kaiwa wannan lokacin bai taho gareta ba hakama a saninta yace da safe zasu wuce amma gashi har rana tayi babushi Wanda hakan ya saka zuciyarta rasa sukuni hankalinta ya fara tashi da shiga firgici. Tana kokarin saka kiran Sakinah ta kalleta tareda saka hannu ta karbi wayar ta ajiye gefe ta kalleta tareda zama kujeran datake kusa da ita ta sauke Numfashi tana kallanta ta bude Baki zatai magana tenya da itace takeda alhakin isar da sakon ta kalli Ayanah data zuba musu ido zuciyarta na Wani irin nauyi tana jiran Jin abinda zasu fada ta katse sakinah da zubewa gaban Ayanah kanta na yin qasa sbd cike al’adar isar da sakon sultan ga wishimah dinsa ta bude Baki da murya me sauti dake yankar zuciyarta ga abinda zata fada tace ‘Allah ya qara miki lafiya da tsawon rai da zaki sheda aure da mulkin LEUL BOYEM NUAB ALMAZZ me BOYEM da Moscow, Allah ya qara miki girma da daraja wishmah uwar NUAB,Zakin BOYEM,Sarkin BOYEM,diamond din BOYEM, Ina fatan Allah ya bakin karfin zuciyar da zata karbi sako me daraja daga me daraja sultan me wishmah da LEUL NUAB ALMAZZ boyem wato sarki YASAR ALMAZ me boyem, A Daren jiyan sakon me daraja ya iso sultan mai boyem yace a miki albishirin ya maida miki martabarki ta wishimarsa ya maida miki karban kwananki a tirakarsa daga Daren jiyan Wanda Ayau zaki far……… Cikin wani irin sauti da basu taba ji ba a muryar NUAB da basu taba tsammanin ganinsa lokacinba kaman saukar aradu sukaji cikin nutsuwa yace ‘What? Maa? Sakinah ce ta dago jiki a matiqar sanyaye ta kalli kofar idanuwanta na sauyawa sbd Wani dandanon zallar daci da bacin rai tareda baqin ciki me tsananin gaske da suka jiyo a muryansa da idanuwansa dayake zarewa glass, Kafe idanuwansa yayi Akan Maa tenya din wadda ta sunkuyar da kanta zuciyarta na ‘daci itama dan basuyi farin ciki ko kadan da hakan ba amma ba yanda zatai dole ta isar da sakon sultan ga wishmah dinsa a darajance. Ayanah data dauke wuta a Zaune sbd kwakwalwanta data kasa digesting komai zuwa hankalinta dataji yana gushewa ta dago ta zubawa NUAB din idanuwanta dake sauyawa suka ja ahankali tareda tahowan wasu hawaye masu tsananin zafi a cikinsu ta miqe tsaye tana girgizata Kai da sauti me karfi tafara cewa ‘HAYATEEM Karka tafi Ka barni, Bazan iya zama idan Ka tafiba.. Kayi mun alkawarin tafiya dani inda zaka mu rayu acan tare, Sultan zai rabani dakai ne, Bazan iya rayuwa babu kaiba a kusa dani Hayateem, Hayateem kada Ka tafi Ka barni kaima, Baa ya tafi ya barni,Ammah ta tafi,Nurat ta tafi Zuhrah ta tafi Abaas ya tafi kaima zaka tafi Ka barni?? Wata irin rawa da fizga jikinta ya fara yi mai tsanani tana ja baya tana maganar da karfi idanuwana jajir bakinta na wata irin rawa. Mummunan tashi hankalin tenya da sakinah yayi suka miqe tsaye dukkaninsu suna kokarin nufarta tayi baya da karfi tana kafe idanuwanta Akan NUAB tana maganganun dake tada tsigar jikinsa gabaki daya idanunwansa na yin jajir sbd kallanta tana ficewa hayyacinta Akan idanuwansa yana gani mafi muni na rayuwarsa gabaki daya. Riqota yayi da sauri yana son bude Baki yayi magana amma Ayau Rauninsa yana Neman bayyana ‘Ya Ammi’ ya furta da Wani irin mataccen sautin daya saka gashin jikinsu tenya tashi suna dakatawa cak jiki mace. Riqota yayi jikinsa yana kokarin rungumeta amma gabaki daya fita takeyi hayyacinta tana ture sa da karfin gaske tana cewa mutuwa zatayi itama bazata iyaba kowa yabarta itama zata tafi batason zaman duniyar. Yanda taje maganganun koina jikinta yana fizga da jijjiga ya saka abinda yakeji yana tsananta a jininsa tareda Wani irin mutuwar jiki sbd bai taba ganin mahaifiyarsa a wannan yanayin ba dan haka ya rungumota jikinsa da karfi yana rungumeta ta fasa wani irin kuka me tsananin karfin gaske da tsima zuciya Wanda ya saka su Sakina sake shiga mummunan Halin tsoron dawowan tinaninta tin daga lokacinda ta fara ambatar sunayen ahalinta data bata taba ambata ba a lokaci daya tinda memory dinta ya samu matsala. Kukanta ya sakasa bude bakinsa da yayi mummunan nauyi shima nasa jikin kakkarwar yakeyi da sautin daya ratsata yace ‘Ammi bazan taba tafiya koina na Barik ba, Zan rayu guri daya dake kaman yanda nayi miki alkawari, Zan tafi dake insha Allah ko ba yanzu ba…… Rufe idanunwata tayi tana fasa sabon kukan dayake gigita nutsuwa da rikita jinin jikinsa tace ‘Idan Ka tafi mutuwa zanyi bazaka sake ganinaba Hayate….. ‘Ammi babu inda zan tafi na miki wannan alkawarin matiqar ba dake ba to Hayateem yana nan babu inda zai tafi wannan alkawarina ne gareki Ammi…… Girgiza Kai takeyi tana sake rikicewa sbd wannan Alkwarin dayake yana sake haukatar da kwakwalwanta ne sbd haka ya fada a farko zai tafi da ita amma yanzu a karo na biyu zai sake tafiya yabarta kaman yanda kowa ya barta dan haka kwakwalwanta tafara kokarin dawo mata da memories dinta sa suke buga kwakwalwan tata gangar jikinta fa lafiyarta na kasa dauka fizga tafara me tsananin gaske tana Wani irin Ihun da batasan tanayiba wasu azababben radadin dayake Dakatar da bugawan zuciyarta suna dawo mata tana tsananta ihunta daya saka NUAB qanqameta a jikinsa wasu irin hawayen da tinda yake duniya basu taba zuwa idanuwansa ba suna taruwa a cikin manyan idanunwansa da sukai mummunan ja yanajin yakushinta da dukanta na sauka jikinsa ya Lumshe idanunwansa yana sake rungumeta da kyau sbd taci gaba da illatasa Akan ta illata kanta. Sakinah ma kuka takeyi sosai Wanda ta manta rabon dataisa sbd clearly memories din Ayanah dinne suke kokarin dawowa baqin ciki da quncin rayuwanta zai dawo kenan Wanda yanzu zuciyarta bazata iya dauka ba sbd girma dayazo gangar jikin batai karfin daukan baqin ciki da quncin rayuwar dasuka dauka ba abaya. Bangaren tsit yayi gabaki daya kowa ya shiga Wani irin sanyi da tsananin tashin tsigar jiki musamman bayinta kaf da suka koma kofar shigowa suka jeru kansu a qasa cikeda dacin zuciya da mutuwar jiki. Cikin wani irin mummunan yanayi NUAB yace Maa tenya ta sanar da Aleey yana buqatan manyan likitocin qasar boyem cikin awa daya zuwa biyu a cikin masarautar. Labarin abinda yake faruwa take ya isa kunnen sultan Wanda zuciyarsa ta sosu da Wani irin daci me kaifi amma bai nuna ba saima kiran likitanta da shi kadai ya yadda dashi akanta kuma shine mai bata kowane irin magani Akan umarnin sultan din. Koda aka kira likitanta labarin zaucewanta da ciwonta ya isa kunnuwan kowa dan haka su HAILE dake cikin jimamin baqin ciki har lokacin suka dan samu sassauci suna dasa sabon zaman jiran labarin cikawarta sbd tsananin gaske jikin nata yayi. Kamar abinda zuciyarsa zata iya jikin nata ya fara sai gashi a lokaci daya cikin mintinan da basu gaza uku ba ta fice hayyacinta tana rasa numfashinta gabaki daya Wanda hakan ya saka kowane motsi ya dauke cak masarautar sbd kokarin ceto ranta da ake Neman likitoci suyi da gaggawa. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 60 Cikin qanqanin lokaci Aleey ya fara zuba kwararren bincikensa na Neman manyan doctors da suke qwararri a qasar boyem din gabaki daya, Wayoyi masu zafi da bincike ta waya da kuma Neman qarin bayanai daga sources masu karfi Aleey ya ringa yi ba ba kakkautawa ba delay ba hutawa har saida ya hada sunayen likitocin guda kusan goma da suke kwararri a qasar tareda informations nasu da komai, Babban farko da shine number shine Dr Amed Sulaim Wanda shine asalin likitan da sultan yakeda cikakken ikonsa ya kuma nadasa likitan Ayanah din tin shekarun da suka gabata kuma shi kadai ke a qasar Sauran kusan duka basa nan a yanzu sunyi tafiya wasu qasashen wainda ke nan kuma qwarewansu batai na Sauran ba dan haka take aleey ya saka shirin taho da doctors dinsu dake wasu qasar dan zuwa boyem idan sun samu ta daidaita kenan idan kuwa komai yaqi tafiya yanda suke so dole ko zaayi yaqi to zasu fita da ita qasar sedai hakan ya bude babin yaqi a tsakanin Masarautar BOYEM Da Moscow. Likitan nata da sultan ya kira tini suma shi suka tinkari gidansa Kai tsaye da securities nasu da motocinsu sbd aleey baida lokacin batawa Akan duk abinda ya shafi abinda NUAB ke so musamman Amminsa da ayanzu uwa ce ga daruruwan ‘yayan da batasan adadinsu ba da ‘danta ya samar mata dan kuwa a Moscow Ana can Ana shirin turo wasu set din securities din mata sbd tsaron lafiyarta a yayin datake jinya babu ruwa su da bayin masarauta gurin tsaron lafiyarta sbd lafiyarta itace lafiyar ubangidansu. Koda kiran sultan ya isa ga Dr Amed Akan zuwan gaggawa ga Ayanaah yana fitowa motocin su GHAZ na tsayawa kofar gate din gidansa me girma dan haka ko dogon bayani bai samu ba tsakiyar motocin su suka saka tasa motar da suka sakasa Wani gudu a cikinsu dan kuwa gabansa da bayansa babu daga qafa gudu sukeyi kaman zasu tashi sama dashi su ajiye sa gaban Wishamar BOYEM. Tin kafin su iso irin yanda suke gudu tafe da motocin ya saka securities wangale musu gates din masarautar tin daga na farko Harna qarshe a lokaci Daya suna shigewa a guje da motar Dr Amed tana tsakiyarsu. Koda suka isa har kofar bangaren shiga NUAB gabaki daya jijiyan jikinsa sun gama fitowa kana kallan idanuwansa gabanka zaiyi mummunan yankewa ya fadi sbd zaka iya rasa hankalinta sbd rikicewa da firgici. Kai tsaye wasu doctors din Dr Amed ya buqata su taho masa da Kayan aiki sbd hatta oxygen tana buqata da gaggawa anan suka rufu akanta. Cikin tashin hankalin duk wani me kaunarta da danta yake jiran ganin sauki ko farfadowanta daga yanayin da ya saka jikin kowa sanyi sbd take ta sauya kamanni kamar ba zata taba tashiba kwata kwata. Zaman fada a ranar gabaki daya ya tsayawa yayi cak sbd Ayau duk Wanda yake masarautar ya sheda tareda tattabarda son Ayanah bai taba fita daga zuciyar sultanba duk tsawon wannan shekarun sbd al’amarim daya bayyana garesu na halinda take ciki da halin da suke iya hango wa qarara sultan ya shiga dukda ya boye hakan tareda danne wa amma a wasu lokutan sirrin zuciya idanuwa ne suke nunawa. Halinda ya bayyana daga idanuwan sultan dayake Neman tona zuciyarsa ya lalata sanyin zuciyar dasu HAILE ke samu ga wannan ciwon lokacin daya dayake Neman kawar musu da Ayanah a cikin sauki. Duk yanda likitoci ke kokarinsu sunyi sun samu daidaita numfashinta dake samuwa da taimakon oxygen amma bata farfado ba Wanda kuma a abida suka gani ba lallai ta iya farfadowa yanzu ba bare dawowa daidai hakama abu biyune zai faru idan ta farka shine zata iya dawowa daidai harma da tinaninta da memories dinta data rasa hakama zata iya tashi kuma ba lafiya ba ta rasa Sauran hankali da memoryn daya rage mata Wanda zata manya komai hatta dan data Haifa da sultan da duk Wanda ta taba sani a rayuwarta dan haka abinda sukafi buqata a yanzu shine kada ta farka kusa kusa hakan zai bawa qwaqwalwarta daman samun ishashen hutun da batai aikin komaiba dan haka tinaninta da nutsuwarta zata fi Saurin dawowa cif cif insha Allah sabanin ta tashi da wuri hakan zai iya harbawa cikin kwakwalwan ta buga gabaki daya dan haka zasu hada da nasu taimakon dazai saka bazata farfado ba sai Bayan kaman wata daya haka indai so samu ne. Wannan bayanin ya karya tareda jijjiga duk wani kuzari da zuciyar NUAB ALMAZZ yake dashi dan kuwa Amminsa duniyarsa ce idan har zata iya tashi ta manta wanene shi da girman kaunar datake tsakanin jininsa da nata zai iya rasa kansa a wannan duniyar. Gabaki daya duniyar su aleey suma sai data jijjiga da wannan bayanin na likitoci dan haka Kai tsaye Aleey ya buqaci tattaunawa a tsakanin nasu likitocin dake qasashe daban daban dasu Dr Amed Wanda suka tattauna tattaunawa me tsayi kafin suka fahimci komai anan doctors dinsu suka tabbatar musu da bayanin su Dr Amed din haka yake a yanda suka fahimci kowane bayanin yanayinta da results nata. Wannan tabbacin da suka samu daga nasu doctors din ya saka suka shiga sabuwar zazzafan yanayi suna jiran abinda Allah zaiyi a farfado wan nata. Su sakinah da tenya duniyar tayi musu tsananin quncin da babu kowace irin walwala a rayuwarsu dan haka suka duqufa fadawa Allah sbd dawowan hankalinta da tinanin wata sabuwar masifar ce a rayuwarta da kowane irin baqin cikin data dandana zai dawo mata sabo fil. Sultan tsananin tsaro ya qarawa bangaren Ayanah din hakama shima NUAB Zafafan securities dinsa mata sun iso daga Moscow sune ciki da wajen bangaren Wanda a yanzu Bayan tenya da sakinah sai likitanta Dr Amed babu me shiga dakin datake idan ba NUAB din. Sultan bai taba zuwa dubata ba al’adar dake kansa matsayin shugaba dan haka zuciyar NUAB take sake tsananta akansa. A bangare daya kuwa Wani tsananin bincike aleey yakeyi me gigitarwa Akan Neman Abaas Wanda NUAB yayi alkawarin Nemowa kafin watan nan daya da ake saka ran tashin Amminsa ya cika dan kuwa a yadda likitocin sa suka basa tabbacin indai aka samu abinda zuciyarta tafi tsananin so ko maitarsa fiyeda komai a memory dinta na baya aka gabatar mata dashi tana farfadowa to hakan zai iya tabbatarda tsayuwar hankalinta da memories dinta. Hakan ya saka Kai tsaye ya bada umarnin duk inda Abaas yake a duniya yanason aleey ya qure lissafin kwakwalwansa Akan inda zaa fara nemansa. Wannan ya saka qwaqwalwan Aleey budewa da kyau ya nutsu ya buqaci ganawa da Wanda yasan Abaas a duniya Bayan Ammin. Kai tsaye Sakinah ce wadda zata basa bayanan dayake so dan haka a lokacinda ya zauna a palon da zai tattauna da Maa sakina dagowa yayi a natse ya kalleta da idanuwansa masu sirkin blue blue na asalin baturen Russia ya bude baki Bayan ya dauki iPad din dake hannunsa dan dauka da tattara duka bayanan da zatai masa ya dago yana nutsar da duka hankalinsa akanta yace ‘Maa’ Kallansa tayi a natse itama batareda ta bude bakiba sbd nauyin da bakin yayi mata na rayuwarsu dake dawo mata, ‘Maa,waye Abaas?? Ina Abaas yake? Bata yayi ko guduwa yayi kokuma korarsa akai? Idan bata yayi daga ina ya bata? Idan guduwa yayi daga ina ne ya gudun? Idan korarsa akai waye ya koresa,me yayi aka koresa? Meye cikakkiyar alaqar Abaas da Ammi? Shekara nawa yanzu da rabuwan Ammi da Abaas?’ Numfashi me nutsuwa ya sauke yana kallan Maa din Wadda idanuwanta sukai jajir ya sake tausasa muryansa yace ‘Maa,Maa duka wannan bayanan shine zai bani daman dawo da Abaas rayuwarku, Da wannan bayanin da zaki mun Maa nayi miki alkawarin Nemo Abaas matiqar yana raye insha Allah dan haka kowane bayaninki Maa ki sani yanada mahimmanci da rawar dazai taka a wannan aikin.’ Numfashi me Zafi da wasu hawaye masu Zafin gaske suka gangarowa Maa sakinah wadda Bayan shekaru masu tarin Yawa Ayau NUAB kila zaiji tarihin mahaifiyarsa da bai taba saniba mai daci da rashin dadin ji. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 61 A hankali cikin tsananin sanyi da mutuwar jikin radadin dayake dawo mata da quncin da harsu mutu bazasu manya dashi ba Maa sakinah tace ‘ABAAS GHAZ shine ‘da na karshe a jinin sarautar GHAZ data shafe a duniya gabaki daya yanzu, Shekaru masu yawan gaske ne da bazan tinaba suka Baro mu da asalin ANJOM GHAZ wato garin da mahaifin Abaas yake mulki, Abaas da Ayanah uwa daya uba daye suke tareda yan uwansu biyu da duka iyaye daya ne suka haifesu, AYANAH GHAZ itace babba sai ZUHRAH GHAZ sai NURAT GHAZ kafin ABAAS GHAZ…….. Ahankali tafara basa mummunan labarin rayuwarsu dayake cikeda baqin cikin da bai taba gogewa ba daga zuciyoyinsu,baqin cikin da dashi zasu mutu,baqin cikin da shine ya kawar da lafiyar kwakwalwa da gangar jikin Ayanaah,baqin cikin da shine zai zama abinda zasu mutu dashi,baqin cikin da har zuriar Bayan baya tasu Ayanah zasuyi baqin cikin jinsa har cikin jininsu,baqin cikin da a yanzu shine yake Neman raba Ayanah da rayuwarta…. Wani irin kuka takeyi mara sautin daya saka aleey daukan tissue ya miqa mata idanuwansa jajir hannuwansa na rawa zuciyarsa kaman zata fado hakama hawaye ne masu Zafin gaske suke Neman cikowa idanuwansa yanajin komai cikin zuciya da kirjinsa, Babban abinda yake sake saka jikinsa rawa shine yanda wannan mummunan tarihin zai isa kunnuwan LEUL, Yaya tarihin nan zai isa ga zuciyar datake shirye da mutuwa Akan wadda wannan mummunan tarihin yayi kaca kaca da rayuwarta? Tayaya zuciyarsa zata riski wannan tarihin kaddarar dayake dabaibaiye da rayuwar Amminsa. Numfashi Aleey ya sake saukewa yana kallan Maa yayi mata alkawarin zai Nemo Abaas a cikin qanqanin lokaci insha Allah hakama wannan tarihin LEUL ba a bakin kowa zaiji Saba insha Allah Sai a bakin Abaas da kansa. Ficewa Aleey yayi daga palon yana danna iPad dinsa sbd fara tattara kan bayanan daya riqe tsaf a cikin kansa na tarihin da abubuwan da zasu taimakawa bincikensa. Bedroom dinsa ya isa ya rufe yana Zaunawa kan sofa da table a gabansa ya bude laptop yana fara bi takan qasashen dake zagaye da BOYEM ta kowane bangare gabas yamma kudi da arewa. ******A Daren ko kadan aleey bai rintsa idanuwansa da kwakwalwansa ba saida ya hada wasu irin fitinannun bincike da bayanai har asuba, Sallar asuba yayi ya cigaba da hada kan bayanan sa da zai gabatarwa LEUL kuma yana saka ran ta hakan insha Allah Abaas kaman yana hannunsu ne. Karfe goma na safe NUAB ya fito a shirye cikin brown gucci wears da takarmin berluti brown suma fuskarsa fresh duk da yana cikin tsananin damuwa a kwanakin amma komai nasa yana nan daukan ido da girgiza zuciya yakeyi, Koda ya fito aleey yana tsaye shirye a palon hannunsa dauke da iPad fuskarsa sanye da farin glass da girmamawa ya yi masa Barka da fitowa yana bin bayansa zuwa dining inda aka cikeda tsaf da breakfast dinsa sbd yanzu da Amminsa take kwance ya Dena cin abinci acan. Zaunawa yayi a daidai lokacin shima aleey din ya zauna Bayan yayi serving nasa. Cikin nutsuwa sukai breakfast din suka kammala suka Baro dining din NUAB ya zauna Akan lafiyayyar 2seater Turkish royal cushion dake palon ya dago fararen idanuwansa masu daukan ido ya sauke Akan Aleey Wanda ya sauke ajiyan zuciya a natse ya matso ya bude iPad dinsa ya kamo bayanin dazai masa ya miqa masa a natse da girmamawa kafin ya dan ja baya kadan yana bude laptop din hannunsa daidai lokacinda NUAB ya bude abinda ya gama hada masa yafara bayani da cewa, ‘ANJOM GHAZ shine asalin garin da su Ammi suka fito, Safarar bayi ce ta fiddosu daga can zuwa nan Wanda a yanda Maa tayi bayani babu sunan qasar da suka sani Bayan anfito dasu zuwa nan din BOYEM, Abinda na tattara a bayaninta shine tace qasa goma sha shida aka wuto dasu ta ruwa kafin suka iso BOYEM, A bayanin nata su qasashe shidan nan bawai ta tabbatar bane amma a iya lissafinta tsayuwa goma Sha shida akai dasu Wanda hakan ya tabbatar mun da qasashe ne suke tsayawa kenan dan babu jirgin ruwa me girman da zai ringa tsayawa koina idan ba bodar wata qasar ya isoba, Zoomin map din daya hada yayi yana cigaba da cewa ‘Batasan sunan qasar da suka rabu da Abaas ba amma qasa biyu suka qara tsayawa Bayan rabuwarsu dashi a ta ukun ce suke isa inda aka saida su maana nan BOYEM kenan, A binciken dana tabbatar bisa ga wannan bayanin nata dama hada shima to qasar LARASIA aka siyar da Abaas Wanda idan muka duba qasa biyu ce tsakaninta da BOYEM dan hakan nake da tabbacin larasia dince inda aka siyar dashi.’ Wani bangaren Aleey ya sake zooming yana cigaba da cewa ‘Idan kuma na aka hada lissafin qasa goma sha shida dake akwai daga nan BOYEM ta gabas to Nahiyar qasar BASSHAH kenan idan kuma daga yamma ne qasa sha shida daga nan qasar ALSIYASH kenan, Idan kuma ta kudu ne qasar BUHARAQS kenan Hakama idan ta arewa ne to qasar ANTARIA kenan. Duka duka wannan bayanin dana hada qasashen nan sune inda zaa fara binciken nemansa amma dole duk qasar da zamu tafi Bayan sauka qasar sai an tafi bakin bodar ruwansu tanan ne dole zaa iya gane garuruwa masu kusa da manyan oceans da zaa iya samun tabbacin samun sa. Dagowa yayi ya kalli LEUL BOYEM da idanuwansa da suke cike da Basira da wata irin kwakwalwa me hasko komai Akan lissafi da nazari, Shima

Chapter 24 of 28