Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da qunci dan haka sai abin ya fara taba zuciyarsa da daman bata taba fita tsananin qunci ba. Wasu bayin boukar ya siyo guda biyar masu karfi dan gadin gidansa da ako Yaushe ake kokarin kawo harin Kai karshen rayuwar Nurat din Wanda kaf garin suke ganin mugun abu ne a cikinsu zama da zabgegen namiji a cikin Kayan mata dan haka koda be bar garin ba to zasu kashesa dan zamansa a garin tamkar zunubi ne. Cikin wannan fitinar dake tashi koyaushe yan uwan boukar dake harin rayuwarsa suka shige sbd samun biya da cimma burinsu na shekaru masu yawa akansa sbd a yanda Nurat ta zama rayuwarsa da ‘yarsa bazasu iya rabuwa dashi ba dan haka suna samun ya fara shirye shiryen barin garin da Nurat dan komawa Wani garin suyi rayuwa hankali kwance tinda yanada dukiyarsa me yawan gaske. Ana cikin wannan halin rana tsaka kwatsam cikin dare kawai aka cinnawa bangaren abincin boukar dake gidan wuta inda tarin dukiyar abincin sa take me yawan gaske buhuhuwan hatsin da dukiya ce me tsananin gaske, Fitowa boukar din yayi cikin duhu da hayaqin daya gauraye gidan har Baka ganin komai yana kokarin isa bangaren idanuwansa da kunnuwansa sukai masa mummunan ji da ganin daya tabbatar masa da halin yan uwansa dayake zargi na shekaru masu yawa dan haka da sauri ya juya cikin hayaqin jikinsa na rawa zuciyarsa na Wani irin radadi da firgici sbd lamarin Yazo masa a bazata. Fada ne ya fara kaurewa da hayaniya tareda ihu a gurin kashe wutar wadda duk da tsakiyar dare ne amma take mutane da suka cika gurin da sunan kashe wutar da kuma son qaddamar da nufinsu a cikin hayaniyar kashe gobarar na kashe Nurat su kuma yan uwan boukar kashe sa dan hakanne ma suka fada sun tada wutar yanda zaa hargitse ana ihu da hayaniyar kashe wuta su kuma sukuma su aikata aikinsu tareda sace dukiyarsa dan haka basu taho da shirin barin ko ‘yarsa ta rayu ba bare bawansa. Fada aka fara tareda sare sare Ana fidda jini me yawa sbd bayin dake tsaron gidan da sukaga alamar fitina a tattare da kashe wutar dan haka suka fara hanawa sedai ko gama rufe baki na farkon beyiba suka rufu a Kansa suka sassarashi suna cewa shi bawa ne bai isa ya basa umarni ba sedai su su basa. Jin hayaniya da Ihun kashe karshen daya dauki gari ya saka boukar daya dauko makaminsa dakatawa ya juya ahankali ya kalli kofar dakin ayshahh sai kawai yaji tinaninsa ya sauya ko yayane yanason ‘yarsa ta rayu dan haka ya nufi kofar dakin da Nurat yake kwana yana zuwa Kai tsaye shiga dakin yayi ya tadashi da karfi tareda dagosa daga kwancen batareda yace komaiba ya riqo hannunsa da karfi suka fito tsakar gida yana sake shiga tashin hankalin hayaniyar da Ihun daya qarasa gauraye gari. Abaas na fitowa yanda wutar take ci da Ihun da akeyi ya sakasa jin Kansa na Juyawa zuciyarsa na bugawa da karfin gaske komai na yanda ya faru garinsu yana dawo masa sabo. Wani irin Zafi da tiriri yaji yana tasowa daga zuciyarsa yana gauraya jininsa komai na sake dawo masa tin daga gawar magaifiyarsu da suka fara rasawa. Rawa jikinsa keyi kowane irin radadin daya dandana a baya yana dawowa yana zama kuzari da fushinsa dan haka dagowa yayi idanuwansa jajir da wasu irin hawaye a cikinsu sbd bazai taba yadda ya sake shiga hannun kusrawaba koda zai rasa ransa gurin cetan Kansa da ayshahh da boukar sbd har abada bayason su dandana baqin cikin daya dandana shi da yan uwansa musamman ayshaahh datake mace, A baya rauni da rashin karfi ya sakasa zamowa nace yana kallo baida abin yi Bayan kuka aka tarwatsa rayuwar yan uwansa aka kashe masa Nurat dan haka wannan Karan a yanzu daya zama namiji ya zabi mutuwa Akan tafiya wannnan mummunan rayuwar. Takobi da adda boukar ya basa yana kallan Zafin dayake bayyana a cikin idanuwansa yace ‘Ka tabbatarda Ka bawa Kanka da Ayshaah kariya’ Wucewa gaba boukar yayi da dan gudunsa na fuskantar komai ai kuwa yana fita take fadan ya dawo Kansa amma dayake yanada nasa karfin sosai haka ya ringa fadan dasu. Shima Abaas baisan lokacinda ya fado cikin fadan ba idanuwansa a rufe komai na abinda ya faru dasu kawai yake gani dan haka kusrawa kawai yake gani a idanuwansa ya ringa fadan bayaji baya gani. Fin karfinsu fadan ya fara yi sbd kusan duk bayin biyar an kashesu hakama suma anfara musu rauni dan haka boukar da jini sosai yake fita jikinsa kallan Abaas yayi cikin tsananin galabaitar daya fara yace ‘Ka tafi Ka dauki ayshahh da jaka na nan gefen gadonta na ajiye ku bar nan kuje garin neruji ku tsallaka ruwa zuwa kiyoje ku jirani anan,Ka tafi da sauri…. Kasan Juyawa Abaas din yayi yana kallan boukar din tamkar yanda Abaa dinsu yayi musu hakan ce yake sake faruwa Ayau din dan haka zaiyi musu boukar damqi hannunsa da karfi yace ‘Idan ban taho ba zuwa gobe to bana duniya Ka dauki Ayshaah Ka tafi da ita inda zata samu rayuwa me kyau ita amana ce gareka duniya da lahira, Hakama idan ranar goben ta fadi ban bayyana gareku ba na ‘yantaka Nurat, Ka zama gatan ‘yata ka zama gatanta da dukiyarta’ Cikin tsananin baqin ciki da radadin zuciya a Karan farko Abaas ya bude bakinsa Bayan shekaru ya furta ‘ABAAS GHAZ’ Kallansa boukar yayi da Wani irin yanayin karyewan zuciya batareda yaddarsa akansa ta girgiza ba ya bude baki idanuwansa na yin jajir yace ‘Abaas ghaz ina fatar Ka zamo gatan ‘yata da bata kariya da rayuwarka har karshen rayuwarta ko taka’ Tura Abaas din yayi da karfi zuwa cikin gida shikuma yana sake bude kofar fita daga bangarensu zuwa bangaren da hatsin zuwa da kuma zuwa kofar ficewa da tini suka shigo. Da sauri Abaas ya juya yana jin zuciyarsa na yanka da Wani irin yanayin da yake sakasa jin kaman bazai iya tafiya yabar boukar ba amma kuma matiqar zasu bawa ayshahh kariya su tseratar da rayuwarta dole ya tafi. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 67 Kai tsaye dakinta ya isa da gudun gaske ya banka kofar bai tsaya komaiba ya dauki jakar da boukar yace ya miqa hannu ya damqi hannunta datake tsaye ta miqe cikin tsananin tsoro da fargaba. Janta yayi da karfi suka fito tsakar gidan Wanda yake hayaqi da ci da wuta take ta riqe hannunsa da karfi cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace ‘Meya ke faruwa, Ina Abbu?? Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta. Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa. Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta. Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa. Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi. Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba. Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shine gatan ayshahh da kuma zai samu yancin zuwa Neman yan uwansa da sune kadai rayuwarsa ya saka yake sake tattaro karfinsa yana cigaba da Wani irin gudun da kafafunsa ke fidda jini sosai amma bai tsayaba dan basu tsira ba. Gudu sukeyi har kusan asuba hakama karfinsa ya kare daqyar yake iya daga kafa sbd galabaita da jininsa daya fara qasa da kuma wata irin azababbiyar ciwon kirji amma hakanan yake dagewa yana daga kafa. Koda suka isa wani garin dayake daga shi sai inda boukar din tace suje anan suka samu suka tsare wa wainda suka biyosu amma duk da hakan bai tsayaba dauketa kawai yayi ya Kama hannunta tamkar wadda bata gani haka ya ringa Janta ba karfi a jikinta ko kadan. Tafiya me tsayi suka kuma yi kafin suka isa garin dayake bakin ruwan da zasu tsallaka Anan dinma basu tsaya ba cikin wata gona suka boye yayi sallah a galabaice kafin suka fada jirgi suka bar nahiyar kwata kwata. Tafiyar wuni guda sukai kafin suka isa inda zasu din suka fito jirgin tareda barin bodar bakin ruwan wadda sai anan ne Abaas ya gane garin da aka siyosa ne dan haka ya sake riqe hannunta gam suna kutsa mutane suna shiga cikin garin sosai Wanda yake a cike tamkar kasuwa koina hidima akeyi. Wani qaramin gidan baqi da yan gudun hijira ya isa dasu suka zauna Bayan ya tsaya a hanya ya siya mata gasashiyar fulawa da zuma. Suna Zaunawa ta cusa kanta cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana fasa wani irin kuka mai tsima zuciya koina na jikinta na jijjiga da tsananin quncin da batasan haka radadi da zafinsa yake ba. Shiru Abaas yayi a gefenta idanuwansa jajir yana Kurawa ruwan dake mamaye da bakin bodar ido zuciyarsa na yanka shima sbd anan ne aka rabasa da tasa rayuwar, Anan ne ya rabu da wainda suke rayuwarsa, Anan ne komai na rayuwarsa ya qarasa Juyawa harzuwa matakin dayake yau akai na rayuwa da bulayi cikin duniya shi kadai babu kowa acikinta. Radadin azaba me tsanani kafafunsa keyi Wanda ya ke sakar masa da zazzabi me Zafi amma bai damuba shiru yayi ido jajir Akan ruwan. Kuka tayi Wanda saida ya qarasa cinye karfinta kafin tayi shiru tana Kurawa hanyar ido itama batareda ta iya cin abinda ya bata dinba. A gurin suka kwana Zaune cikin mummunan halin daya tsananta yanayinsa dama nata datake wata rawar sanyi dan haka ya cire rigar jikinsa ya rufa mata Akan nata Kayan da babu ko kallabi a kanta gashinta a bude yake a sake sbd yanayin da suka fito. Koda gari ya waye daqyar sukai sallah a gurin suka tashi Zaune suna sake gadin hanyar da duk masu isowa, Duk yanda yayi da ita taci Wani abin qi tayi gashi tayi Laushi sosai ta fita hayyacinta kawai mahaifinta take son ganin ya taho din. Haka suka wuni har rana ta Kuma faduwa babu boukar ba labarinsa, Zuwa lokacin dagashi har ita daqyar suke Numfashi dan haka Akan dole sukaci abinci sbd suna Neman karfin cigaba da jiransa har ranar daya taho. Wani wunin suka kuma yi ba labarinsa haka suka kuma kwana, Ahankali ahankali kwanakin suka ringa tafiya ba boukar ba labarinsa su kuma sun kasa cire tsammani dan haka basu iya tafiya koina ba haka su kaita zaman jira a bakin bodar wadda tin baa Ankara dasu ba har aka fara ankarewa dasu Ana musu kallan mata da miji marasa hankali sbd yunwa da wahalar data Kama jikinsu take fara bayyana dan kuwa basa Wani iya cin abinci suna cikin tsananin damuwa da baqin ciki tareda rashin sanin inda zasu. Ganin an fara saka musu ido ya saka suna cika sati shida a gurin Abaas ya tattarata suka bar qasar sbd Wani jirgin na tahowa Wanda zaiyi gaba binsa sukai sbd a yanzu tafiya Neman yan uwansa zai tafi dan haka a qasar datake gaban wannan zai fara tinda daga nan gaba akai dasu Ayanaah. Tafiya sukai ta kwanaki a jirgin kafin suka isa qasar dake gaban wadda suka Baro, Isarsu qasar dole anan bakin boda ya samu aikin wahala Wanda zaa ringa biyansa dan yana buqatar kudin dazai nema yan uwansa bazai taba dukiyar Ayshaah ba a gurin nemansu, Gida suka samu Wanda ake biyan hayar daki daya ya biya hayar ya saka ayshan a ciki shi kuma yana kwana a kofar dakin. Rayuwa a qasar qunci tafara yi musu sbd yanda ake qyamarsa ganinsa namiji da Kayan maza amma yan kunnen mata ne a kunnensa wainda ya kasa cirewa sbd Ayanah ce ta saka masa su da hannunta bazai iya cirewaba. Ita kanta ayshahh tsangwamarta mutane suka fara yi sbd tana tareda shi babu aure a tsakaninsu dan haka rayuwa tayi mata qunci da nauyi bata cikin kowace irin walwala bare farin ciki dan haka suka bar garin suka koma can quryar qasar Wani garin suka fara rayuwa shima ahankali ahankali zaman yakasa dadi sbd qabilanci na qasar sam basason baqi dan haka dole suka tattara suka sake sauya guri Wanda duk inda sukaje kaman mahaukaci haka Abaas ke Neman yan uwansa. Shekara kusan guda da rabi sukai a qasar suka barta gabaki daya zuwa qasa ta gaba Wanda itama aikin wahalar gaske yakeyi wanda yake cin lafiyarsa sosai sbd duk wannan lokacin aikin wahalar gaske yake a rayuwarsa dan rufa musu asiri kuma har lokacin dukiyarta na nan wadda tace ta basa halak malak amma ya kasa tabawa sbd yanason ya Nemi inda zai ajiyeta dan bata rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa amma abin ya gagara. Ahankali suka fara Gagarin rayuwa a qasashe gurin Neman su Ayanah Wanda zuwa yanzu rayuwarsa ta qarasa macewa gabaki daya sbd ciwon wahala da azabar rayuwa da qunci da suka taru suka rufar masa dan haka ya samu qasa me dan nutsuwa yace zai siya mata gida y ajiyeta tayi rayuwarta ta huta da binsa gararin duniya kada ta qare rayuwarta kamar tasa ta mutu a banza. Kasa yadda da hakan Ayshaah tayi sbd bazata taba iya rayuwa ita kadai babu sa ba sbd a yanzu shine t Rabin jikinta rayuwarta, Shine kadai hasken dayake rayuwarta shi kadaine Wanda rayuwarta take dashi dan haka ta shirya mutuwa a gurin Gagarin duniya tareda shi, Ta shirya rayuwa da mutuwa tareda shi ko an inane ko awa ce qasane zata iya zama dashi. Da wannan suka fada qasar BOYEM Wanda Sam babu ta yanda zaa barsu su shigeta kusan watan su uku anan babu damar shiga qasar dan haka suka juya suka bar qasar. A border ta farko da baa shiga qasar BOYEM aka daura musu aure sbd hanasu gurin zama da akai koina garin sbd basada aure dan haka suka daura aure Wanda har cikin zuciya da ransu suna tsananin son junansu hakama sun shirya rayuwa da mutuwa a tare, Aurensu ne ya kawo wata yar nutsuwar rayuwa a rayuwarsu data cikin tsananin duhu da qunci tareda kadaici, Kusanci da sabuwar shaquwa da kauna tareda so me tsananin gaske sukewa juna suna sake Jin karfin gwiwan fuskantar rayuwa. Bayan wata uku suka bar BOYEM sakamakon cikin daya bayyana a jikin Ayshaah, Cikin ya taho mata da rashin lafiya sosai dan haka tafara wata irin rama taba kofewa alaman jininta yana yin qasa dan haka Abaas ya sadaukar da rayuwarsa da kudirin sa dan bata nutsuwan rayuwan daya kamata kodan abinda zasu haifa kafa suyita yawon duniya dashi dan haka suka juya inda suka fito, Shima kirgen garuruwan da suka Baro a baya tsawon shekaru lokacin da aka dauko su daga garinsu ya fara yi dan komawa qasar sa garinsa gidansu da iyalinsa sbd matiqar Ayanah tana raye to tabbas yasan zata je nemansa a cikin duniya kokuma anan gidan mafarinsu dan haka zai jirata daga yanzu har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa. *****tafiyar watanni sukai nai cikeda wahala da ukuba da tsinkewan zuciya ga yanayin ayshahh kafin Allah ya iso dasu dajin garinsu daya sha matiqar wuyar gaske kafin ya gane hakama dukiyarsu tayi qasa dan haka Koda suka iso ANJOM GHAZ cikin Ayshaah ya tsufa yakai wata takwas. A garin ANJOM babu mutane sosai sbd garin ya Riga ya mutu dan haka babu wata daula da tatttalin arziki kaman baya amma akwai kwanciyan hankali dan haka babu wahala ko tashin hankali aka karbesu tinda ansan waye shi hakama duk da shekaru sunja kamanninsa basu sauyaba. Babu kowa a fadar mahaifinsa dan haka Sauran dukiyar daya taho da ita ya bayar aka dan yi gyaran dazai yiyu suka shiga batareda tsoro ba suka zauna tareda kokarin daga ANJOM. Kokarin dayazo dashi da qwazo ya saka jamaar garin samun kuzari da qwazonsu suma ya dawo take garin ya fara komawa ANJOM dinsa na baya a bisa mulkin ABAAS GHAZ din. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 68 ANJOM GHAZ ta dawo ANJOM dinta duk bazata taba komawa ANJOM din baya ba amma Abaas yayi iya kokarinsa ya sake kafata da dukiyarsa da karfinsa da lafiyarsa datake qasa sosai amma ya tsayu ya kasa barin ciwon kirji da zuciyar dake damunsa yakai sa qasa, Ayshaah ma ta samu rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwar da Abaas ke fatan ya bata sedai yanayinta itama sai ahankali lafiyarta tayi qasa sosai musamman da cikinta harya wuce watannin haihuwa bata haihuba dan haka aka ringa kawo mata addua da maganin al’adarsu tana sha, Kauna da soyayya me girma tareda wata irin tsafta da nutsuwa take tsakanin Ayshahh da Abaas Wanda kusan duk ANJOM ansan irin son dayake mata da irin yanda ita kuma ya kere mata komai da duniyarta harma da rayuwarta dan haka yanayin jikinta ya saka duk Wanda yake garin mutuwar jikin halinda Abaas yake ciki Akan rashin lafiyarta. Cikinta na cika wata goma sha daya cif ta Wanda yayi daidai da wata su uku cikin na hudu da dawowa ANJOM da samun rayuwa me nutsuwa Bayan shekarun gararin duniya da gwagwarmaya a qasashe cikin rashin gata hakama shekaru biyar cif da rasuwarta mahaifinta ta haifi ‘yarta,yar Abaas,jinin ghaz,hasken idaniyar mahaifinta a duniya wadda tana haihuwarta a idanuwanta kadai ta kalleta ko a hannunta Allah bai bata ikon daukanta ba tabar duniyar ta tafiyarta tabi mahaifinta Wanda bata taba Dena kewa da radadin rashinsa ba a rayuwarta tabar masoyinta da ‘yarta a duniyar da basuda kowa sai junansu a yanzu. ABAAS GHAZ wannan shine farkon bude dukkanin kofofin karfin ciwon dayake cin tasa zuciyar wadda ta kasa dauka da jure rashin matarsa wadda itace take riqe da zuciyarsa dake a zube tin acan baya ta rashin yan uwansa a rayuwarsa dan haka mutuwar Ayshaah ta karya duk wani karfin hali da jarumtar dayake da ita ya fadi ciwon da bai taba samun waraka daga garesa ba, A haka ya rungumi ‘yarsa da sabuwar kaddararsa a cikin qunci da ciwo, Ya zama uwa kuma uba ga yarsa Ya zamo aboki da dangin uwa da dangin uba ga yarsa wadda ta taso itama a rayuwarta batasan kowaba Bayan mahaifin nata sai tarin sunayen da kunnuwanta da zuciyarta sun riqesu, Duhu ne a rayuwarsu da babu ranar shigowan haske a cikinsa, Qunci ne a rayuwarsu da babu ranar saukar sa sbd duk wani daci da qunci da baqin ciki tareda duhun rayuwar mahaifinta ta dabaibaye tata rayuwar ta shigo ciki tayi zaman da bata taba sanin menene farin ciki ba bare dandanon yanda yake, Bata taba sanin haske a rayuwa ba bare sanin yaya yake a ruhi, Bata taba sanin walwala ba bare sanin ya murmushi yake ba a zuci da Fuska dan haka a haka ta taso tin mahaifinta nada karfi da kuzarin kulawa da ita har karfinsa ya qare shima ciwo ya kaisa qasa yana jiyo qamshin mutuwarsa datake gap da iskoshi dan haka tinda ya kwanta ciwo ya sadaukar da Sauran numfashinsa gurin rokon Allah a kowace daqiqa Akan Allah ya kawo masa Ayanah kafin ransa yabar jikinsa sbd yarsa Ayanaah, Ya roki Allah a kowane Hali Ayanaah take Allah a kawota garesa kafi mutuwarsa sbd goben yarsa ta inganta, Ya roki Allah ya tsaya Akan rayuwa da duk wani lamarin BAHAR, BAHAR itace rayuwa da sanyin idaniyarsa da ayanzu yake rokon Allah ya zama gatanta ya tsaya a lamarinta ya bata kariya da tsari daga kowace irin sharri na rayuwa da zata fuskanta. Tinanin rayuwarsa na sake zuwa gangara babu haske ko daya a rayuwar dazai bar BAHAR dinsa ya saka ya roki Allah dauki ransa tareda ‘yarsa subar duniyar tare sbd zuciyarsa ta kasa riqe tsananin daci da radadin dayake ji na tinanin barinta a duniyar da babu komai a cikinta Bayan zalinci da son zuciya ita kadai ba uwa ba uba ba dangi ko daya sai tarin duhu da qunci.’’ ****Wani wahalallen Numfashi ya sauke ahankali daqyar numfashin yana sarqe wa ya dago jajayen idanuwansa Akan NUAB ya sauke yanason bude baki yayi magana amma karfinsa yayi qasa sosai baya iya jan Numfashi da kyau hannuwansa na dan rawa yanason dagawa ya sake Kama hannun NUAB din amma karfin ya qare, Da sauri Aleey ya da idanuwansa ke zubda ruwa ya qaraso ya mayar masa da oxygen sbd NUAB ganinsa ya dauke tsaf sbd yanayin mummunan Jan tashin hankali da jijjigar zuciya daya shiga hannuwansa rawa sukeyi yana riqe da hannun Abaas din daya gam, BAHAR da tinda mahaifinta ya fara bada labarin suka iso amma bata shigoba itada sakinah suna tsaye kofar sakinah na Wani irin kuka mara sauti jikinta da kafafunta na rawa, Ita kuwa jikin bangon gurin ta jingina tana rintse idanuwanta dake Wani irin silili da yajin azabar radadin dayake cikin zuciya da jininta da suka zama rayuwarta datake tamkar fanko, Shigowa tayi kafafunta na wata irin rawa hawaye masu tsananin zafi da radadin dayake Neman fasa zuciyarta ta iso gurinsa tana zubewa qasa kan kafafunta ta Kama hannunsa daya da hannuwanta biyu dake wata irin rawa ta Dora kanta Akan tafin hannunsa ta fasa wani irin kukan da bata taba fasawa ba a rayuwarta me tsananin tsima zuciya da tafa tsigar jiki tana kasa cewa komai Bayan sake hannunta da nasa datai kanta na kai batasan me takeji ba a yanzu Bayan gajiya da rayuwa, Bata taba shaawa ko so daya taci gaba da rayuwa ba idan mahaifinta yabar duniya sbd babu abinda zata tsaya ta samu a duniyar, Mahaifinta shine kadai hasken dayake rayuwarta idan ya tafi rayuwar batada Sauran amfani sbd duhun dake cikinta kasheta zaiyi dan haka bata taba sauya adduarta daga Allah ya dauki ran mahaifinta tareda ita ba. Ahankali ya bude idanuwansa dake rufewa ya Ambaci sunanta daga Wani irin sautin daya saka kukanta tsananta tana dukan kirjinta dake tsananin ciwon da tinda ta tashi itama dashi ta tashi sbd baqin ciki da qunci kawai. Aleey ne daya fita ya dawo ciki da sauri tareda isa gefen NUAB cikin nutsuwa da qasa qasa ya sanar dashi komai na tafiya da Abaas din ya zama ready. Gyada kai NUAB din yayi a hankali yana kallan Abaas da idanuwansa dake cikeda tsananin kaunarsa yana sake riqe hannunsa daya a cikin nasa yace a kira doctors. Babu bata lokaci doctors suka taho tare akai masa wata allura a cikin drip tareda Sauran abubuwan da suka kamata aka bada umarnin kowa a fice. BAHAR da NUAB ne kadai basu fice ba hakama babu Wanda ya iya sakin hannunsa a cikinsu saima Wani irin kukanta sanyayyan sauti dake tashi tana sake cusa fuskarta cikin tafin hannunsa daya sake baya motsi ko kadan. Fitowa akai dashi aka saka ambulance suka fada motoci suma kai tsaye aka wuce airport dashi inda komai yake a shirye. Private jet suka shiga Bayan dan dogon shirye shiryen dabai dauki lokaci ba Wanda akaiwa kowa tinda suka iso da Abaas din dan haka kai tsaye jirginsu ya daga gabaki dayansu. #MAMUH 09033181070 [09/12, 11:22 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 69 Bayan doguwar tafiya Greece suka isa inda suna sauka jirgin sultan me BOYEM na isa qasar tareda Ayanah wadda jikin yake buqatar ganin likitocin nan da NUAB din ya tanadar mata tini amma basu taho ba dan haka doctors din su buqaci a kawota sbd ta farfado a kusa dasu dan su tabbatar sun bata treatment din dazai hanata rasa hankalinta. Hakan ya saka NUAB shima kai tsaye tahowa

Chapter 27 of 28