sha uku ba aka fice dasu suna kuka da ihu nai karfi Ana dukansu duka mai tsanani sbd duk Wanda yayi kuka ko ihu duka sosai ake masa kuma a tafi dashi a hakan,
Wainda suka San babu ceto a harkar basa kuka haka zaa tafi dasu zuciyoyinsu cike da tsantsar baqin ciki mara misaltuwa.
Yarinyar wadda Ana fizgota cikin rikitaccen yanayi ta Kama hannuwan Ayanah duka biyu Tana fasa Ihun kuka a cikin mummunan tsoron daya saka hawaye gangarowa idanuwan Ayanah harma da Abaas lokaci daya Tana jin ciwo na yankar kirjinta na tausayin yarinyar duk da basusan yaya tasu kaddarar zata qare ba a wannan tafiyar amma dai suna fatar mutuwa ce ma kawai ba wannan mummunan aikin ba.
Ficewa aka gama yi dasu aka sake rufe Sauran bayin take daddaikun su suka dan sauke ajiyan zuciya suna rintse Idanuwanu.
Ajiyan zuciya suka sauke suma Zuhrah da Zarah fa suka toshe bakin Nurat suka Sakinta sbd duk lokacinda wani zaiyi ihu itama Ihun takeyi Wanda suke tsoron hakan ya saka wata rana mummunan kadarrar da basa fata ta hau kanta Wanda basa fatar gani.
Tinda aka fice dasu bayin ranar dan sauke buqata akansu jikin Ayanah ke rawa ta rintse idanuwanta sbd Ihun yarinyar datake Ji har lokacin a kunnuwanta wadda da alaman dakin dayake saman inda suke aka shiga da ita dan haka kusan kunnuwansu na jiyo musu komai.
Hannuwanta biyu ta saka ahankali hawayenta na tsananta saukowa ta rufe kunnuwan Nurat shima Abaas Tana cewa ya rufe kunnuwansa
Zuhrah ma dake wata irin jijjiga sbd tsoro sedai sakina ta rufe mata kunnuwa.
Ihun yarinyar da gurnanin Wanda yake ketata kunuwan Ayanah da sakina yake tareda sauran bayin suna jin yanda yagata yana fadar abinda yakeji na budurcinta dayake keta wa,
Wasu irin hawaye da kuka mara sauti Ayanah sakewa tana tsananta rufe kunnuwan Nurat dan hanata jin wannan masifa.
Kamar sakina ma kuka takeyi sosai tana sake rufe kunnuwan Zuhrah itama.
Tsawon lokaci wannan masifar na saukar musu a kunnuwa har saida yarinyar takai bata iya kuka ko ihu sbd azaba da yanda yake shigarta tako ina gaba da bayanta yana ihunsa da maganganunsa tsawon lokaci me tsayi tukuna ya gansu yana sauka kanta ya fito zigidir yana sauke Numfashi da shakar iska me dadi yana jin Kansa wasai hakama ya samu gamsuwa sosai da ita duk da bata tsaya ba.
Yaransa biyu dake gadin kofar dakinsa ne suka fada dakin suka daukota tareda fitowa da ita suka fice zuwa maida ita.
Wasu bayin ne guda biyu suka fada dakin suka gyara masa tareda hada masa ruwan zafi a qaton bahon dayake shiga ya kwanta ciki yayi wanka suka fice.
Komawa dakin khams yayi yana jin bacci sosai a idanuwansa ya fada ruwan ya wanke jikinsa kawai ya fito ya fada gadon ba komai a jikinsa ya bige da bacci.
A kofar dakin kafin a maidata suka ajiyeta aka kawo ruwa masu sanyi aka zuba mata a jikinta jinin dake fitowa gabanta yafara bin ruwa yana wankewa batareda ta San meya ke faruwa a rayuwarta ba suka bude kofar tareda jefata suka rufe suna barin gurin.
Kasa motsawa kowa yayi bare dogon numfashi a dakin hakama babu Wanda ya iya ko Juyawa ya kalleta duk da duhu ne bare tabata ko bata taimako.
Ayanah data rintse idanuwanta da karfi Tana dauke Numfashi sbd tsoro da bugawan zuciyar gabansu data fado har hannunta na sauka kan kafafun ayanar batareda ta farfado ba.
Tsawon Daren a wannan mummunan halin suke haka aka ringa dawo dasu Dayan bayan daya sedai Mutum biyar kadai suka dawo sauran biyun an kashe an jefar.
Asuba tayi har gari ya waye sosai su Ayanah sunyi tsit baccin wahala da ake yi daga Zaune a dan sauke su Ayanah taji an Kama kafarta a razane jikin na daukan rawa ta bude ido Tana firgita sedai kafin tayi baya yarinyar ta sake riqe kafarta tana son bude baki tayi magana amma bazata iyaba sai hawaye masu radadin dake bin fuskanta.
A sanyaye Ayanah ta Dora hannunta akai nata din Tana kasa cewa komai.
Daqyar cikin azabar yarinyar tafara kokarin miqewa amma take jini ya balle mata Wanda ya sakata Lumshe ido Tana sake qanqame hannun Ayanah ranta na fita take.
Ayanah batasan ta rasu ba ta sake riqe hannunta dan bata sassauci sbd duhu ne.
Baa basu abincin safe ba haka suka wuni a rufe har saida Ayanah taji jikin yarinyar yayi sanyi sosai ya sanqare ta gane mutuwa tayi dan haka ahankali ta zare hannunta daga nata tana kuka mara sauti jikinta na qarasa mutuwa sosai.
Sai dare aka zo basu abinci akaga gawar yarinyar aka dauketa tareda fiddata daga cikinsu aka jefar a ruwa.
Abincin da aka basu ranar cikin damuwa da sanyin jiki suka cisa sbd zuwa lokacin dai sun sake tabbatarda rayuwar ba sauki a tsakanin wahalar ko mutuwar.
******** Nisa rayuwarsu da tafiyar keyi a cikin kusrawa dan zuwa lokacin sunkai watanni biyar a cikinsu batareda sunkai inda Allah zai yanke tasu wahalar ba,
Qasashe sosai daban daban ake tsayawa anata rage bayi Ana kuma tsayawa wasu garuruwan Ana qara wasu.
Tsawon wannan rayuwar da sukai ko so daya Nurat bata taba dawowa hayyacinta ba,
Abaas bai taba bude bakinsa ba maganarsa ta jima da qarewa,
Zuhrah bata taba fita tsoro da firgici ba,
Ayanah bata taba Dena kuka na fili dana boye ba,.zuciyarta bata taba samun Hutu da sassaucin baqin ciki da qunci ba koma daqiqa ne,
Sakinah kuwa bata taba Dena adduarta akansu ba da zubda hawayen tausayin su da kanta ba,
Dan hakanne rayuwar take tsananta tsanani a garesu,
Nurat yanayinta a kwanakin rikice wa yakeyi Wanda hakan ya karya dukkanin kuzari da juriyarsu,
Wata irin rama takeyi Tana yin fayau dan haka suka Dena cin abincinsu suna tattarawa suna bata saisu ci na Mutum biyu su kuma su taru suci sauran.
Babu wani sauyi dan haka jikinsu ke sake yin sanyi da shiga sabuwan damuwa,
Daren da zasu isa qasar Gaku baccin wahala da damuwa ya dauke su daqyar sai aka bude kofar wannan Karan ba hasken farin watan dan haka cikin duhun kawai aka fara damkosu kawai Ana jeho wa waje saida aka dauki mace tara tukuna aka rifesu.
Ana rufe su gurin yayi tsit Zuhrah dake maqe da jikinta Tana rawar jiki sosai sbd yau duk har gurinsu aka taho saura dakan a damqota Allah ya kubutar da ita dan haka jikinta ke rawa sosai tana kakkarwa.
Motsawa tayi Tana fidda hannunta daya dan sake kamo Nurat datake riqe da ita tashin hankalin ya raba hannuwansu sai taji babu Nurat din a gefenta.
Zuro hannuwanta tayi duka biyun taba lalubar gefenta da sauri hannuwanta na tsananta rawa taji babu Nurat da karfi ta Ambaci sunanta saida gurin ya amsa gabaki daya da hakan.
Ayanah da zuciyarta ta tsaya cak da bugawa hannuwanta na muguwar rawa ta miqa tana lalubar Zuhrah Tana cewa
‘Meya faru?
Ina Nurat din??
Girgiza Kai Zuhrah tayi Tana Neman zarewa tace
‘Nurat banjitaba,bata nan,banji ta ba’
Abaas ma cak kirjinsa ya Dena bugawa ya Kama hannun Ayanah da karfin gaske yana son magana amma ba dama sbd alkawarin dayake kansu dan haka cizon harshensa yafara yana jijjiga Ayanah da karfin gaske.
Ayanah da karfi itama ta kwala kiran Nurat din wadda kaman daga sama suka Ji saukan muryanta a tsakiyar kunnuwansu Ta kwalla qara me karfi tareda kiran sunan AMMA saida kunnuwansu suka amsa Amo zuwa kirjinsu musamman Ayanah datasan ita Nurat din take kira da Ammah.
Saman dakin suka kalla da wani irin mafi girman firgici sbd jin baa cikin dakin take ba dakin dake samansu ne na shugaba khams…
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070
15
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
************
Miqewa tsaye dukkaninsu sukai kafafunsu na kasa daukansu sosai sbd zaman dayake cinye lafiyar kafafun,
Jijjiga da fizga jikin Ayanah yakeyi bama rawa ba ta bude Baki da karfin gaske Tana kwala kiran Nurat wadda take Ihun itama sosai.
Abaas harshensa yake cizo yana wani irin gurnanin kiran Yar uwarsa a zuciya jini na fitowa bakinsa sbd mummunan tashin hankali da yanda yake cizan harshensa.
Zuhrah Neman zarewa takeyi itama kaman Nurat Tana qwala kiran Nurat qafafunta na kasa daukanta.
Sakinah ma kuka takeyi sosai zuciyarta na bugawa kaman zata fado,
Miqewa tsaye Ayanah tayi cikin tsananin duhun tana kokarin taka mutane ta isa kofar ta kife sbd sarkar kafarta amma bata tsaya komaiba jikinta na tsananta rawa ta sake miqewa kwala kiran Nurat da karfin daye amsa dakin dukansa har sama inda Nurat din take Tana sake faduwa taba sake tashi tana taka mutane hankalinta gabaki daya ya gushe daga jikinta Ihun kiran Nurat takeyi Tana jin kaman mutuwa zatai a lokacin,
Ihun Nurat dinne yafara ratsosu itama cikin tsantsar azaba tana kiran Ayanah da sunan Ammah muryanta ba dadin sauraro.
Isowa setin kofa Ayanah tayi tafara bugawa da hannuwanta tana wani matsanancin kukan da ihu,
Yanda take bugawa hannuwanta duga biyun da karfi batareda damuwa da yankewan da hannun keyi ba ga qusa dake jikin gurin Tana fasa hannuwanta jini na fita jin kawai takeyi tamkar ranta ne zai fita idan rayuwan Nurat dinta ta lalace.
Kukan datake yi Sam bata hayyacinta sbd da a gabansu ne ake kokarin hakan da yau duka zasu bar duniya sbd bazasu tsaya kallo ba zasu qwaceta koda hakan na nufin rabasu da ransu.
Jini sosai taje fiddawa a hannuwanta amma ta kasa denawa sbd bata ma Jin Zafin komai kukanta na qaruwa sosai har maqoshinta na kasa fidda sauti.
Abaas da Zuhrah harma da sakina da suma kowa ke cikin mummunan Hali suka rarrafo basa gani zuwa inda sautin muryan Ayanah din yake fita
Zuhrah ce tayi saurin riqeta Tana rungumeta sbd jinin dataji hannuwanta nayi data lalabo ta tareda fasa sabon kuka itama jikinta na fizga,
Abaas ma Kansa yake bugawa a kofar yana wani irin kuka zuciyarsa na yagewa tako ina da radadi me yawa ga bakinsa bazai budu ba dai harshensa yake taunawa yana jini yana cigaba da buga Kansa a kofar,
A daidai lokacin da Nurat ta qwalla wata mummunan qara wadda take tabbatarda azaba ce ta keta ta da akai da wasu irin surutai da khams ke sakewa a cikin kunnuwansu suna ratsa zuciya da kwakwalwansu take kowannensu ya silale qasa suna yin tsit sedai sakinah ce ta saki wani irin kuka a lokacin Tana riqe hannuwansu su duka ukun a cikin nata duka biyu sbd yanda suke jijjiga batareda sun iya sake kowane irin yunquri ba alaman zuciyarsu bugawa zatai ko ta dauke wuta,
A cikin kunnuwansu sautin duk abinda khams keyi yake sauka tareda kukan Nurat dake fita har tayi tsit babu kowane irin sautinta sai nasa Wanda duk abinda yayi da ita kunnuwansu sunji musu Wanda kuma sauti ne da zai zauna a kunnuwansu da zuciyoyinsu har abada har ranar da jinsu zai dauke Bayan rai ya fita a jikinsu,
Zuhrah juyewa kanta yake yi itama sbd dukan da zuciyarta ta samu mummunan dayake Neman buga zuciyarta.
Sakinah rungumesu tayi da hannuwanta Tana qanqamesu kukanta na tsananta sbd yanda dakin yayi tsit kowane bawan dake jirgin ranar duk da halin da suke ciki kukansu Ayanah din ya sanyaya jikinsu tareda hawayen tausayin qaddadarsu su duka da basusan ya zata qare ba.
Ayanah zubewa tayi jikin sakinah gabaki daya jikinta na saki idanuwanta na kasa Juyawa ta koma kamar wadda aka zarewa komai aka Barta da rai kawai.
Jin hakan sakinah ta sake rungumeta jikinta kukanta na tsananta Tana Jin inama a ranar da suka so kashe kansu ta barsu sun mutu sun bar duniyar da sun huta da ganin wannan balain da daace iyayensu na raye mutuwa zasu yi idan suka Ji wannan mummunan ranar.
Tsit babu Wanda ya iya ko dogon motsi a dakin kwata kwata kaman yanda babu Wanda ya sake Jin ko kukan su Ayanah ne dukansu sun mutu a inda suke babu abinda ke motsi a jikinsu Bayan zuciya dake bugawa.
Gap da asuba aka bude dakin Wanda ya saka su Ayanah daga Kai ahankali suna kallo aka turo Nurat wadda Kayan jikinta gabaki daya suke a yage harma kusan Rabin jikinta duka a bayyane.
Abaas ne ya Tara hannuwansu biyu ya tareda ta fado jikinsa ya rungume ahankali yana rufe jikinsa ta inda jikinta yake bayyane yana sake rungumeta tsamtsam.
Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga idanuwanta Wanda ya sauka tafin hannuwan Zuhrah data motsa zata tabata,
Saukar hawayen nata ta saka Zuhrah kallan fuskanta cikin duhun bakinta na budewa da tsananin sanyi tace
‘Nurat,Yene(my/tawa) Nurat,Yene fikir(love/masoyiya)
Nurat Rabin Raina.’
Wasu sabbin hawayen ne suka gangarowa Nurat din Tana son Dora hannunta Akan na zuhrah din ta kasa dan haka ta rufe idanuwanta bakinta daqyar ya iya budewa tace
‘Ammah’
Kalmar yanka zuciyar Ayanah da dukkaninsu tayi Ayanah ta rufe idanuwa hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mata ta motsa hannuwanta dake rawa ta Kai fuskar Nurat din taji wani abu yana gangarowa ta hancinta Wanda ta tabbatarda jini ne yake fitowa ta fasa wani irin wahalallen kuka Mara sauti tareda Kai fuskanta ta hade data Nurat din tayi sumbaci goshinta ta sumbaci hancinta tareda sarqe hannunta da nata Tana kasa furta komai sai sumbatar hannunta taje yi tana wahalallen kuka Mara sauti jikinta a mace gabaki daya ba karfi ko daya.
Zuhrah hannuwanta ta kasa janye wa daga hawayen Nurat din dake zuba suna zuba a hannunta itama kukan takeyi sosai kaman ranta zai fita mara sauti,
Nurat data dawo hayyacinta Tana jinsu amma babu inda take iya motsawa a jikinta sbd jininta dayake qarewa yana qarasa zubewa sbd tin acan take zubar da jini sosai haryanzu sosai yake fita a jikinta batareda yan uwanta sun saniba duk da ko sun sani basuda abinda zasu yi sedai zubawa sarautar Allah ido.
A haka suke Zaune kowannensu kuka ne na fitar hankali sukeyi mara sauti har lokacin Abaas yana rungume da ita cikin jikinsa hakama Ayanah na riqe da hannunta tana sumbata Tana kukan da shi Kansa kukan ya gaji sai Zuhrah dake tare hawayenta da hannuwanta duka biyu kowace diga yanka zuciyarta yakeyi,sakinah ma Tana Bayan Ayanah kuka takeyi kawai tana kusan abinda dukansu suke Ji,
Gari ne yi yi haske sbd safiyar datai dan haka duhun dakin ya ragu sosai suna iya kallan fuskanta kuma har lokacin babu Wanda yayi hayaniya ko doguwar motsi a dakin sbd duk da suna qangin bauta suna sheda tsananin kauna da son da yan uwan kewa juna kaman rai,
Ahankali Nurat din ta sake bude ido ta zubawa Abaas Wanda ya kasa kuka sedai jinin dake fitowa daga bakinsa idanuwansa sunyi jan da gap suke da fara fidda jini,
Hannunta ta daga daqyar yana rawa sosai ta share masa jinin bakinsa Tana kallan cikin qwayar idanuwansa hawaye suka sake gangaro mata ta kasa iya cewa komai kafin ta dauke idanuwanta a galabaice tanason kallan Zuhrah da Ayanah amma Allah bai bata ikoba jikinta ya sake ahankali ranta na fita.
Dukansu babu Wanda ya motsa sbd tashin hankalin daya wuce Kai tsaye cikin kansu ya sanqarar da komai nasu,
Sakinah ma mutuwar Zaune tayi dukansu suka dauki mintina a hakan kafin Ahankali Ayanah ta motsa tana tallafo fuskan Nurat din datai haske sosai tareda duka jikinta sbd jininta daya gama tsiyayewa tas ta hade fuskanta da tata muryanta na rawa tace
‘Nurat rayuwata,
Nurat hasken rayuwata,yene Nurat,Nurat kece kuzarina,
Nurat kune haske da kuzarin rayuwata da ruhina da bazan iya rayuwa babu ku ba,
Nurat kune karfin daya saka zuciyata take bugawa haryanxu batareda ta tsaya ba,
Nurat ke suka keta amma mu rayuwar ce aka keta sbd kece rayuwarmu,
Nurat ki bude idanuwanki ki kalli halinda muke ciki
Bazamu taba dawowa daidai ba har abada idan babu ke koda kuwa mun samu sauyin rayuwa,
Nurat,Nurat…….wani irin kuka me tsananin jijjiga duk me saurare da ratsa zuciyar kowane dan Adam dazai jisa ta sake Tana sumbatar tsakiyar kan Nurat din da goshinta kafin ta rungume kanta a kirjinta tana rufe idonta kukanta naci gaba da fita.
Zuhrah ma hannunta Nurat din ta riqe ta sumbata Tana rungumewa kukanta na fita da tsananin kashe jiki,
Abaas a kirjin Nurat din shima ya kife Kansa a Karan farko da sautinsa ya fita Bayan tsawon watanni yana fasa wani irin kuka mai tsananin taba zuciya da narkarwa.
Basu taba tunanin samun kansu a cikin wannnan mummunar halin ba da zasu rungume gawar daya daga cikinsu ba a Hali mafi muni irin wannan,
Koda iyayensu suka bar duniyar sun mutu a hanyar Neman tsira da sauran mutuncinsu,
Amma ayau Nurat ta rasu tabar duniyar da ciwon baqin cikin abinda ya faru da ita,
Bata rasu ba saida tashin hankalin data fuskanta ya dawo da hankalinta jikinta dan hakanne baqin cikin abinda y sameta dashi ta rasu a ranta dole.
Kaman yanda Baqin cikin rashinta bazai taba barinsu ba hakama harsu mutu sautin kukanta a lokacinda ake keta haddinta bazai taba fita daga kunnuwansu da zuciyarsu ba shikenan ya musu rauni a zuci.
Har rana ta keto suna rungume da gawar Nurat sun kasa sakewa saida aka bude su dan basu abinci,
Jeho abinci akeyi masu karba na wawason karba amma babu Wanda ya motsa a cikinsu suna rungume da ita har lokacin babu Wanda idanuwansu ke Dubuwa sbd kumburi da ja.
Saida aka gama Rabon abincin a daidai lokacin suka iso qasar hidua jirginsu ya tsaya a bodar qasar zaayi abinda aka Saba tukuna aka shigo dan diban bayi Sai a lokacin akasan da akwai gawa a cikin gurin.
Zabar bayinsu suka fara yi wainda zasu siyar suka fitar dasu kafin suka dawo suka dauki gawar wadda aka cire daqyar a hannunsu Ayanah da suka riqeta gamgam dukkaninsu ganin bazasu sake ba aka dauko Bulala aka fara dukansu da karfi jikinsu na fashewa amma har lokacin kasa sake gawar sukai.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
16
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
***************
Wani irin mummunan dukan Bulala aka ringa saukarwa hannuwansu Ayanah Wanda ya saka hannuwan nasu fara fashewa harma dukan yana sauka kan gawar Nurat wadda tayi haske sosai fuskanta tayi Wani irin fayau idanuwanta dake rufe sun boye mummunan ramar dasuke ciki kafin rasuwarta,
Ayanah Akan gawar ta zuba ido tana kallan dukan dake sauka akanta Wanda zuciyarta ta sake gabaki daya taji tana hakura da dangana tinda Nurat ta rasu hakan shine saukin data samu da hutawa daga wannan duniyar da babu komai cikinta sai qunci da azaba hakama babu abinda gawar Nurat ke buqata Bayan Hutu koda kuwa ba binneta zaayi ba taba buqatar abarta ta fita hannun kusra dan haka ahankali ta sake hannuwanta suna saki idanuwanta na tsananta ja jikinta gabaki daya na sanyi hawaye takeson yi amma sun kafe Idon ya gaji da kuka.
Zuhrah ma azabar dukan dayake fasa hannunta y saka hannuwanta saki tana sunkuyar da kanta kasa hawaye na diga babu sautin kuka sbd karfinta daya qare tas.
Abaas ne ya kasa sakin Nurat din dan haka suka taru akansa suna masa wani dukan dayake fasa fatar jikinsa har jini na fita ya kasa Sakinta kuma y kasa kuka dan haka suka tsananta dukan har saida Ayanah da bata hayyacinta sakinah ta girgizata da karfi ta tana cewa
‘Abaas zai rasa ransa’
Dagowa Ayanah din tayi tana kallan dukan da ake masa jikinsa duka yana jini da dan sauran karfin datake dashi ta fada Kansa ta rungumesa tareda Kama hannuwansa tana banbarewa daga Nurat jikinta na wata irin rawa sbd itama Jin takeyi kaman bazata iya barin a tafi da Nurat din ba.
Girgiza Kai Abaas keyi da karfi yana kasa Sakinta yana kallan Ayanah wadda ta kasa dagowa sbd yanda jikinta ke rawa ta zare hannuwansa tareda rungumesa tana basa kariya daga dukan da ake masa har lokacin aka hada su tare akai musu mummunan dukan daya saka Zuhrah bata kariya itama dukan na sauka kanta.
Saida suka gaji dan kansu sukabar dukansu suka dauki gawar Nurat suka fice da ita.
Babban arzikin da Nurat ta samu Bayan rasuwarta shine suna bakin bodar wata qasar dan haka ba damar yar da gawa sbd cikin mutane ne dan haka rami akai kaman kowace gawa aka rufeta a qasar.
Kwanansu biyar a qasar suka barta aka wuce sedai tamkar zuciyoyinsu Ayanah ne aka Bari a qasar haka suke Ji sbd tamkar sun rasa barin rayuwarsu a qasar da bazasu taba mantawa ba tinda Nurat dinsu na qasar.
Rayuwarsu ta raunana daga lokacin dan haka ko abinci sun wani Dena ci sai sakinah ce take wawusowa ta kawo musu ta takura musu tareda roqo ta samu su ci amma gabaki daya rayuwar ta qarasa fita kansu barin duniyar shine kawai fatansu a yanzu,
Quncin da suke ciki ne ya saka duk wahalar da suke ciki yanzu basa jinta dan kuwa a yanzu kusan babu abinda bazasu iya jurewaba a rayuwa illa rabuwa da juna.
******Tafiyar sati biyu sukai a ruwa suka isa qasar Nuggi wadda qasa biyu ce a gabanta kafin isa BOYEM,
Tinda suka tinkaro qasar jikin dukkaninsu yayi sanyi duk da basusan suna tinkarar kowace qasaba a taqaice ma basusan ina suke ba kokuma ina suke dosa,
Da asuba ne suka iso bakin bodar qasar dan haka baa bude su ba saida gari ya fara haske tukuna aka basu abinci.
Yau Ayanah da kanta ta shiga karban abincin ta rarrafo gefensu ta zauna ta kallesu kowannensu ya zama wani halittar daban yunwa na yawo koina a jikinsu da wahala.
Zaunawa tayi tsakiyar Zuhrah da Abaas din ta sauke ajiyan zuciya me sanyi da mutuwar jiki kafin ta dago ta kalli Abaas ta saka hannuwanta biyu ta Kamo fuskarsa ta sumbaci goshinsa ta sumbaci gefen fuskansa da tsananin sanyi murya tace
‘Bazan iya rayuwa babu Kai ba hasken idaniyata ka riqe hakan kada ka yadda ka sake laifin da zasu illatamun kai kaji????
Dago idanuwansa da sukai ja yayi take ya sauke Akan fuskanta da idanuwanta suka ciko da hawayen rauni da tsananin kaunarsa dake bayyane a fuskanta.
Gangarowa hawayenta sukai tace
‘Kamun Alkawarin bazaka taba sake abinda zai saka rayuwanka a hadari ba koda bana raye tareda ku?
Saurin kallanta yayi yana son rufe bakinta da hannunsa ta riqe hannun tana girgiza masa kai hawayenta na gangarowa da gudu tace
‘Kamun alkawarin hakan Abaas,
Kamun alkawarin zaka kula tareda kiyayewa sbd mutuwa zanyi idan wani abu ya samu daya daga cikin ku biyun,dan Allah Kamun Alkwari…..’
Qarasa fada tayi muryanta na karyewa sosai tana sunkuyar dakai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 28