Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
NUAB din gama kallan bayanin da duka suke a rubuce da map din Bayan duk bayanan dayayi masa da baki kuma, Dagowa yayi ya kalli Aleey ya bude baki a natse yace ‘Meye karshen tinani da bayaninka ya hada? Ajiye laptop din hannunsa yayi tareda kallan NUAB din cikeda girmamawa yace ‘Tinda ta ruwa suka iso qasar to dole bangare biyu ne Hagu da dama Wanda yake kudu da arewa kenan dan haka a cikin biyun zaa fara da daya maana a faro binciken daga inda suka fito tin farko ANJOM GHAZ kenan dan kuwa akwai yiyuwar tinda Abaas namijine to tabbas a tsawon shekarun nan indai ya samu yancinsa to tabbas ya koma gida dan sake ginawa da farfado da sunan GHAZ da bazai taba barin ya shafe ba Bayan ya nema yan uwansa be samu ba kenan, Dan haka inaga a fara daga can din Kai tsaye sbd tabbatarwa idan bai komaba Sai a Nemi Sauran qasashen. Kallansa NUAB ya dago a natse yayi cikin yadda da kowane bayanin aleey a koda Yaushe Akan komai sbd baya taba hada lissafin da bai qure kwakwalwansa akansa ba dan haka Numfashi me sanyi ya sake tareda dagowa yace ‘A gobe Inason a shirya tafiya zuwa qasar buharaqs din Wanda a cikinta ANJOM GHAZ take insha Allah. Gyada Kai aleey yayi sbd yanada tabbacin insha Allah haka bayanin yake ba tantanma indai Abaas na raye yana saka ran ya koma dan farfado da GHAZ matiqar shi namijin jinin GHAZ ne dan ‘dan halak ko baida zarra bazai yadda sarautar gidansu ta fadi ta shafe a tarihi ba. Juyawa yayi ya bar gurin yana daga wayar sa dan fara shirin tafiyar tasu da bazata wuce kwana biyu su wuce ba. Bayan barin aleey shiru NUAAB yayi yana Jin Wani irin yanayi na rashin sanin tinanin Kamawa Akan me haduwan mahaifiyarsa da Abaas zata kasance hakama a yanzu da mahaifiyarsa take cikin halin da bazata iya basa labarin cikakken tarihinta ba a bakin Abaas dayake jininta yakeson jin asalin tarihin komai na Amminsa. ******* Cikin kwana biyu aleey bai hutawa ba sbd bai taba wasa da duk abinda yake na LEUL ba dan haka shirin tafiyar ya tsaya tsayin daka saida ya tabbatarda ya hadata a cikin sati guda Bayan ya gama tanadar da komai na tafiyar wadda ya hadata hadda Maa sakinah da zata kaisu har cikin ANJOM GHAZ Bayan sun isa qasar kenan. Tenya batasan da tafiyar ba sai ranar da zaa wuce kai tsaye NUAB ya sanar dasu dan haka jiki a mace da tsananin zullumin daya saka jinin Maa sakinah mummunan hawa sbd komawa inda komai ya faro. Karfe Dayan rana motocinsu a Jere suka fice daga Masarautun zuwa airport Wanda motocinsu na zuwa gate din qarshe daidai nan motocin da suka dauko mai girma YUNAR BOYEM daga airport tareda ‘yarsa LEYLAH YUNAR BOYEM ‘yar amaryarsa ZUHRAH GHAZ BOYEM wadda ya kawo a matsayin tukuicin dawowan MAGAJI LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya basa aurenta a matsayinta na jinin BOYEM itama. Ficewa motocinsa sukai tareda securities dinsa Bayan motocin mai girma YUNAR din sun shigo sukuma batareda kowannensu yaga junaba musamman LEYLAH YUNAR data gama mutuwa akansa tin kafin ganinsa a zahiri sbd kallo daya datai masa a hoton labarai ta shirya zama ko mistress dinsa ce ba matarsa ba dan haka wannan tukuicin da mahaifinta ya badata na aure shine abu mafi farin ciki da girma na rayuwarta dan haka batada baqin cikin dawowan su Masarauta da zama. Su kuwa suna isa airport Kai tsaye jirginsu ya daga yabar qasar. Tafiyar awanni masu yawa sukai kafin suka isa qasar bhariqs din wadda saida suka kwana a wata qasar kafin suka sake hawan jirgi suka isa. Tinda suka iso daga shi kansa NUAAB din Wanda baisan kaddarar mahaifiyarsa da zai tarar acan ko tasa sbd zuciyarsa dake Jin rashin nutsuwa da sukuni, Maa sakinah ma sosai ta shiga mummunan halin daya sakata fara ciwo me dan karfin da har saida taga likita kafin suka dauki wasu mahaukatan motoci zuwa tafiya me tsananin tsayin da zata kaisu ruwan dake qasar Wanda tacan zasu bi sakinah ta gane dajin garin ANJOM. Kwana daya da wuni sukai suna tafiya kuma saida suka dauko likita ma musamman sbd ciwon Maa dazai iya tashi koyaushe, Sun iso garin dayake bakin ruwa basu tsaya komaiba Aleey ya siya musu jirgin ruwa gabaki daya suka shiga dan barin gurin. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 62 Tafiyar wuni guda da kwana daya sukai suna zagaye ruwan da tafiya ke tsayi kafin Kaman a mafarki sakinah ta daga hannu tana nuna gurin daya saka idanuwanta jajir hannuwanta na rawa. Bakin dajin suka tsaya su aleey da Sauran Yaransa suka fidda drones dan duba duk abinda yake cikin dajin da gari ma idan akwai. Aleey ne yake riqe da iPad din dayake kallan dajin da drones dinsu suka shiga suna yawo a sama, Sauran yaran kuwa a tsaye suke da mahaukatan bindigoginsu a shirye da harbe ko dabba ce tayi motsi a gurin, NUAB yana ciki Zaune yana jiran bayani daga aleey Wanda yake sake kallan iPad din hannunsa da kyau sbd tabbas yaga gari. Wasu mahaukatan bikes dake shiga daji suka fidda daga jirgin ruwan suka hau tareda kutsawa cikin dajin a shirye da bindigoginsu da wasu manyan wuqaqe masu shegen hadari. Tafiya sukeyi suna kutsawa kafin sukai tafi me Nisan gaske basu isa garin ba sai yamma lis wanda ya saka sakinah yanke jiki ta fadi tama Dora kafarta a qasar garin ANJOM GHAZ kenan. Cikin kulawa da bada umarni yace a koma da ita jirgi taga doctor ya dubata abarshi daga shi se aleey su fara ganin lafiyar garin ma tukuna. Sauran yaran da bikes din tareda Maa sakina Juyawa sukai suka koma. Kafarsa ta dama ya fara dorawa a cikin garin ANJOM GHAZ daya saka tsigar jikinsa tashi sbd ganin yanda garin ya zama tamkar ba garin da mutane suke rayuwa a cikinsaba sbd duk tsawon shekarun garin bai dawo daidai ba sun rasa niima da tarin albarkar garin nasu. Akwai mutane sosai da gidaje sosai da kasuwanni a garin amma ba kamar baya ba sbd kusan kowa na garin yasan kowa tinda ba yawa sosai. Ganin baqi a garin ya saka gabaki daya mutane shiga tsoro da tashin hankali dan haka Kowa ya fara silalewa yana komawa gidansa ya shige ya rufe tinda dai shugaban garin nasu baida lafiyar dazai basu kariya, Fiyeda shekaru tara yana kwance yana jinyar da ba lallai ya tashi ba sbd yayi mummunan nisa. Gidan shugaban garin Aleey ya nema a taimaka a nuna musu babu musu kuwa Wani ya kaisu har kofar gidan asalin sarautar GHAZ. Fadawane suke gadin masarautar amma tsirarru Wanda yake nuni da Masarautar batada karfi ko Kwata kwata tinda garinma duka ba Wani karfi bare Ayi mulki me karfi. A fada suka zauna nan Sarkin fada ya shigo yana kallansu tareda zubawa NUAB idanunwata kaman zasu gado sbd ganin kammanninsa da jinin GHAZ dayake Neman shafewa daga Yauma kila sbd jikin Shugaba yau yayi tsananin da sai Allah. Kwarjinin NUAB ya saka shine ya gaidasu yana musu Barka da zuwa maimakon su su gaidasa sbd shine kila me mulkin GHAZ anan gaba. Aleey cikin nutsuwa shima ya dan gaidasa da yarensu Wanda NUAB yakeji sosai sbd mahaifiyarsa dake masa tin yana yaro hakama Maa sakinah shikuwa ya kullafa saida ya iya yaran shikuwa aleey baya wasa saida ya iya shima sbd uban gidan nasa da idan ta Kama. Kaman daga Sam Kai tsaye NUAB yace ‘Menene sunan shugaban jinin GHAZ daya rage a yanzu??? Da mamaki Sarkin fada yace ‘ABAAS GHAZ sai ‘yarsa qwalli daya tak AYANAH BAHAR GHAZ sune suka rage jinin GHAZ a duniya… Wani bawa ne ya fado fadar da sauri yana zubewa qasa yace ‘Sarkin fada jikin Maigirma yana sake tsananta kana buqatan zuwa. Miqewa Sarkin fada yayi yana barin gurin a rikice Wanda ya saka Kai tsaye NUAB miqewa yabi bayansa sbd kowane Hali Abaas din Amminsa yake yanason ganinsa. Sarkin fada na saka Kai dakin NUAB ma yana sakawa idanuwansa suka sauka Akan fuskar datake sak da sak data mahaifiyarsa. Abaas dake aman jini ahankali dagowa yayi idanuwansa na sauka Akan NUAB take ya dauke wuya komai nasa na kokarin tsayawa cak yayi baya zai zube Taku biyu NUAB yayi ta tarosa jikinsa yana Jin dukkanin nauyin dake zuciyarsa yana qaruwa da ganin sanyin idaniyar mahaifiyarsa a wannan halin. Feso Wani jini Abaas yai da karfi cikin azabar dayake kasa riqewa NUAB ya katse azabar ciwonsa da cewa ‘NUAB ALMAZZ ‘da ga AYANAH GHAZ…… Rintse idanuwana Abaas yayi cikin wani azababben yanka daya ratsa zuciyansa data gama yanke kauna da yan uwansa har abada musamman yanzu dayake kan gadon mutuwarsa, Riqosa NUAB yayi cikin rashin bata lokaci sbd kafin komai yana Abaas din na buqatar likita da gaggawa, Girgiza Kai Abaas yayi cikin wani mummunan rashin kuzari da ciwon da baida sassauci ke kadan ya damqi hannun NUAAB din da karfin gaske yana jan Numfashi da qyar yace ‘Ayanah tana raye??? Cikin sauri NUAB din ya Gyada masa Kai tareda bude baki yace ‘Kana buqatan likitan dazai duba lafiyar Ka da gaggawa daga baya duk zamuyi magana amma Ka sani Amminah tana raye, Tana son ganinka itama kafin tabar duniya dan haka kada Ka tafi Kabarta zuciyarta bazata iya daukaba sbd kaine hasken zuciyarta da idaniyar Abaas ghaz. Girgiza Kai Abaas ya sake yi yanajin kaman bazai iya ko minti dayaba a duniya dan haka koma yayane Allah yayi masa rahama ne tinda Sauran ransa daya kawo masa dan Ayanaah zai cika a hannunsa Bayan burinsa na hada jini da Ayanarsa ya cika Akan gadon mutuwarsa. Sake qanqame hannun NUAB yayi yana bude baki daqyar yace ‘Ka cikawa mahaifiyarka Dani burin da muka tashi dashi na hada zuria da juna Ayau cikin Daren yau na mutu da nutsuwar na bada ‘yata daya tak ga jinin Ayanah…… Wani kallan rashin fahimta NUAB yayi masa yaja kallan aleey yace Ayi gaggawar daukansa dan tafiya dashi ga likita. Abaas zamewa yayi yana sake dan girgiza Kai daqyar yace ‘Lokaci na yayi Allah ya yanke ganawata da Ayanah bazan Kai koinaba zan bar duniya, Kokarin daukansa aleey yakeyi amma jikin sake rikicewa yakeyi dan haka ba bata lokaci Aleey ya fita ya fidda wayar sa ya saka kiran Sauran yaran yace a kawo Maa sakinah yanzu. A lokacinda aka iso da Maa sakinah Abaas cikin tsananin ciwo da rashin karfi ya zayyanewa NUAB labarinsu tas Wanda baida dadin ji me tarin qunci da baqin ciki. Nasa labarin yake kokarin Dora masa Maa Sakinah ta shiga kafafunta na Takawa ahankali cikin sanyi da rawar zuciyar dake gap da bugawa. Suna kallan juna Abaas ya fashe da Wani irin kukan daya saka dakin yin tsit gashin jikinsu na tashi. Itama Maa sakinah zubewa tayi qasa tana fasa kuka a gabansa koina jikinta na rawa tana kiran sunansa da sauti me ratsa jiki. Bude baki yakeson yi ya Ambaci sunata da tambayar yan uwansa amma karfinsa yayi qasa sosai dan haka ta rarrafo da sauri tana bude bakinta dayake rawa cikin sautin daya sake saka gurin daukan tsit ta fara fada masa dukkanin halinda suka shiga har zuwa halinda ake ciki yanzu da Ayanah dake tsananin so da buqatarsa a rayuwarta. Magana zeyi harshensa ya fara kokarin karyewa dan haka take aleey yace securities su daukesa Ayi gaggawar tafiya dashi. Riqe hannun sakinah Abaas din yayi da karfin dayake na barin duniya yana kallanta daqyar ya iya furta ‘yata jinina AYANAH BAHAR…. Kasa qarasawa yayi jikinsa na sakewa gabaki daya. Gaggawar fita dashi suke kokarin yi sbd har lokacin akwai Sauran rai a jikinsa Sarkin gida na ganin hakan buga tsalle ya tare kofa tareda kiran fadawa yana cewa kada a Bari su fita koina da Shiguba da yarsa har sai ancika burinsa na auren yarsa Wanda hakan zai basu tabbacin kariyarta Bayan tabar nan sbd igiyoyin auren sa zasu tabbatar musu da zaa iya riqe amanarta matsayinta na ‘yar shugabansu hakama basuda tabbacin Ayanah din da gaske tana raye amma tinda ga ‘danta a gabansu bazaa tafi dasu ba saiya aureta koda Abaas ya rasu kafin akai to ta samu gatan zama Inuwar aure. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 63 Da Wani irin yanayi me ‘dacin gaske da jajayen ido NUAB da aleey suka dago dukkaninsu suka kalli Sarkin fadar Wanda ya sake tsayawa Akan maganarsa ba tsoro sbd wannan shine gatan da adalcin da zasu wa ‘yar shigabansu jinin GHAZ data rage a duniya a idanuwansu, Su dai bazasu bi su ba hakama bazasu Hana a tafi da Sugabansu ba dan nema masa lafiya sbd yana tsananin buqatarta amma kuma basuda tabbacin zai rayu ko bazai rayu ba a yanda sukaga jikin nasa yayi nisa dan haka gwara ‘dan Ayanah kaman yanda ya fada ya auri Bahar ‘Dinsu a gaban idonsu ta yanda koda Allah bai tashi kafafun Abaas ba sunsan zaman aure zatayi a cikinsu ba zaman garari ba dan haka tsoro ya cire a zuciyarsa matiqar ba auren BAHAR zasuyiba gwara abar musu shigabansu ya cika a gabansu su dauki amanar yarsa wannan shine tsayuwarsu matiqar ba hakan ba kuma sedai a kashe su a tafi da Abaas da BAHAR Bayan ransu. Kuka Sosai Maa sakinah takeyi tana Jin zuciyarta kaman zata fashe sbd idan Abaas yabar duniya Zuhrah ce kadai ta ragewa Ayanah wadda tafi tsananin kauna da son Abaas a rayuwarta fiyeda komai, Tayaya Ayanah zata iya jure wannan rashin? Sake qanqame hannun Abaas din sakinah tayi dake cikin hannunta tana rintse ido da sabon kuka me tsananin rasa zuciya. Aleey da ransa ya gama baci gashi ba lokaci da gaggawar gaske suke son tafiya da Wanda shine rayuwar Ammmi, Kallan Securities yayi da idanuwansa jajir yace su kawar da kowa har sai sun fice dashi. Sarkin fada na Jin hakan ya sake tare hanyar tareda fidda wata irin mahaukaciyar wuqa a jikinsa me munin da zata zata aikaka lahira ba bata lokaci. Wuqar sa ba komai bace a gurinsu sbd sunada wainda sukaci uwarta da ubanta a jikinsu Wanda zata katse jijiya take kafin kyaftawar ido kawai banbanci tasa dafin gaske ne a cikinta da shine zai kasheka bama kaifinta ba kila. Bindiga suka daga cikeda rashin tausayi suka seta Sarkin fadar tareda Yaransa da suka taho suka zagaye kofar dakin da makamai masu hadari a hannunsa. NUAB da jikinsa ke wata irin fizga sbd tsananin tsoron rasa Abaas Wanda shi kansa bayajin zai iya Hadiye radadin rashin sa sbd tsananin kaunar da son dayake masa tin kafin ya gansa sbd shine mutum daya da Amminsa tafi so a duniyarta da rayuwarta fiyeda kowa, Ko shi kansa data Haifa baya iya gane tsakanin shi da Abaas wane tafi tsananin so dan haka da kaunar Abaas shima ya tashi a ransa hakama da ita zai mutu dan haka bazai taba iya barin ya mutu sakamakon rashin likita ba indai ba Allah ya Riga yayi anan zai cika din ba lokacinsa yayi kenan ba dan haka dagowa yayi da jajayen idanuwansa da sukai mummunan ja kamar ma hadda hawaye a cikinsu ya kalli Sarkin fada Wanda yaja baya kadan sbd tsananin kwarjini da shakkar NUAB din data dakesa zuciya da kafafu amma duk da hakan bayajin zai iya ja da baya Akan abinda ya fada sedai Ayau ya rasa ransa gurin tabbatarda gyara goben BAHAR. Bude baki NUAB yayi da wata muryan data saka tsigar jikin Sarkin fada tashi gabaki daya yana sake Jin shakkar NUAB na shigarsa yace ‘Ku Bari na ceta rayuwarsa nayi muku alkawarin bawa rayuwarsa data ‘yarsa kariyar da matiqar ina raye sun wuce kowane matsayin da zasu fuskanci kunci ko rashin gata tako ina…….. Girgiza Kai Sarkin gida yayi yana kasa kallan NUAB din Wanda hatta fuskarsa tayi jajir jikinsa rawa yakeyi. Aleey da zufa ke gangarowa umarni me Zafi ya bada Wanda ya saka aka taqa bindigogin zaa fasa kan Sarkin gida NUAB ya daga hannu daidai nan Maa Sakinta ta zube qasa itama tana fasa sabon kukan daya saka kowa juyowa ya kalleta ahankali da jajayen idanuwa Banda NUAB daya rintse ido hannuwansa dake dauke da Abaas suna wata irin rawar dake bayyanarda halinda zuciyarsa take ciki. Cikin tsananin kukan data jima batai irinsa ba sakinah ta bude baki tareda dagowa ta kalli NUAB tace ‘NUAB Ka aureta kodan cika alkawarin daka daukanwa mahaifiyarka zaka kawo mata Abaas, Ka aureta sbd cetan rayuwar Abaas da zuciyoyi da dama bazasu iya jurewaba idan aka rasashi, Alkwari ne da aka dauka anan cikin masarautar GHAZ tin kafin sanin yaya kaddarar zata taho ba a tsakanin mahaifiyarka da Abaas Wanda idan Ka cikasa Ayau anan inda aka dauki alkawarin zaka cike musu burinsu ne da shi kadai ya rage a tsakaninsu sbd ko baka kaiwa Ayanaah Abaas ba Ka Kai mata auren ‘yarsa dake hannunka Ka cike mata gurbin da Abaas zai bar mata sbd ‘yar Abaas tamkar Abaas dinne a gurinta….. Tsit gurin yayi kowa na shiga sabon mummunan yanayi Banda NUAB da already yake cikinsa idanuwansa a rufe danan. Kallansa su aleey sukai dukkaninsu cikin shock da tashin hankali da firgici sbd babu kowane irin tarihin shigowan nace rayuwar LEUL daya tsara, Bai taba son kowace mace ba sbd baima taba sakasu a tsarin rayuwarsa ba,Amminsa ita kadaice wadda yayi Alkwarin ta ishesa rayuwarsa, Mata uku ne a rayuwarsa kuma su kadai ne wainda zaiyi rayuwa dasu baya buqatan kowace irin mace Bayan ukun nan iyayensa dan haka aleey yasan babu ta yanda zaayi mace ta shigo rayuwar LEUL dan haka dagowa yayi ya dawo da kallansa kan Sarkin fada Wanda jikinsa ya mace da maganganun sakinah da shima sune yake tsaye akansa. ‘A daura mun auren da ita ni zan aureta indai hakan ne kadai zai saka ku Bari mu tafi dashi da ita din…….. Kallansa Sarkin fada yayi da sauri cikin tsananin mamaki da fargaba kafin ya maida kallansa kan sakinah wadda ta fasa sabon kuka tukuna ya maida kallansa kan NUAB Wanda ya bude idanuwansa a hankali ya Dora Akan Sarkin fada din batareda ya kalli kowa ba ya saka hannunsa cikin aljihun wandon kakin dake jikinsa na shigowa daji ya ciro Wani kakkauran awarwaron zinari daya me kaurin gaske dayake dauke da sunan mahaifiyarsa da Abaas din Wanda yake nata ne shine ya bata kyautarsa da hannunsa ya qera sa ya saka sunanta dana Abaas din a yanzu dazai taho yaje har dakinta ya dauko sa sbd nunawa Abaas shedan shi dan Ayanah ne ya miqawa aleey dayake mutuwar tsaye cikeda rudewa da mamaki Abaas shima ya miqawa securities yana dawowa gurin NUAB Wanda ya saka hannunsa daya ya kamo hannun Sarkin gida ya saka masa zinarin ya bude baki da sauti me Kai tsaye da tarin tsananin son cikar Buri daya wato tafiya da Abaas dan ganin likitocin gaggawa. ‘Sadakina,a daura auren a yanzu anan a wannan daqiqar bana buqatar qarin mintina ko kadan batareda an daura ba.’ Jikin Sarkin fada rawa ya dauka sbd shakka da firgici amma hakanan ya tattaro karfin Hali da jarumta ya juya da sauri yace a kira masa Sauran masu dan matsayi a fadar da gaggawa. Aleey matsowa yayi zeyi magana sbd sanin NUAB zaiyi auren ne batareda kaunar ko taba shaawar hakan ba dan haka shi a shirye yake da auren koma yaya take yarinyar sbd LEUL kuma zai rayu da ita komai tsananin yanda lamarin zai kasance dan haka bude baki yayi zaiyi magana, Daga masa hannu NUAB yayi a natse cikin yanayinsa da baya son magana ko daya sbd koina fuskarsa yayi jajir hadda hannuwansa ma duka sunyi jajir. Sauran securities ficewa sukai da Abaas cikin gaggawa zuwa jirginsu na bakin ruwa da akwai Dr a cikinsa dan fara basa taimakon gaggawa kafin a gama daura auren. Sakinah barin gurin tayi ta fito kafafunta da tsananin nauyi ta nufi dakin Ayanaah na baya wainda a yanxu yake na BAHAR din kaman yanda aka fada tana kallan koina a hankali zuciyarta na yanka kuka mara sauti na taho mata hawaye na gudu suna tsiyaya a fuskarta kowane memory na rayuwar da sukai a kowane lungu da sako na gidan suna dawo mata. Inda daidai Baa ya shimfide gawar Ammah a lokacinda sukai ido biyu da gawar tata idanuwanta suka sauka ta rintse idanuwanta tana dafe kirjinta dake Wani irin ciwo hawayenta na tsananta gudu. Fara zagayawa dakunan kowa da aka Bari tana fashewa da sabon kukan baqin ciki me tsanani da kewan rayuwar da suka bari anan wadda koda basuyi arzikin da suke dashi a BOYEM ba ko kadan nan din yafi musu farin ciki da nutsuwa tareda kwanciyar hankali. Koina ya mutu ta zama tamkar kango babu komai da aka sauya,babu komai da aka gyara tin asalin yanda gini d tsarin gidan haka yake haryanzu babu cigaba ako ina dan haka koina a mace yake iya inda suke rayuwa a cikin masarautar yake gyare. A kofar bakin dakin Ayanah ta tsaya cak Wanda yake fes a gyare koina asalin qamshin jinin sarautar GHAZ na tashi yana fitowa daga dakin na flowern Ahlighazania Wanda gabaki daya ahalin shine qamshin da suke amfani dashi tin farko dan haka suka kasance kamshinsu daya me shiga rai da sanyi tareda wata irin nutsuwan kwanciyan hankali da kashe jiki. Lumshe idanuwa sakinah tayi tana Jin bugun zuciyarta na tsananta da Wani irin mutuwan jiki da baqin tareda quncin rashin kasancewan su a rayuwa daya koda duka suka Haifa iyalansu, Idan har mahaifiyar BAHAR bata raye yaya Abaas yayi dawainiyar kulawa da tarbiyantar da ita shi kadai babu dan uwansa ko daya a tattare da ita? Idan yanzu Allah ya kaddara ciwonsa bana tashi bane yaya zasu fuskanci BAHAR dik a matsayin dangin mahaifinta daya rasa shekaru? Yaya zata iya rayuwa a cikinsu batareda tasansu ba ko sabo dasu? Tayaya ma zata iya rayuwan nan babu uwa babu ubanta da shine gatanta, Zata dandana ‘daci da quncin da iyayenta suka dandana na rashin iyaye da tafiya Wani guri rayuwan da batama san yaya zatayi ba, Shi kansa auren da ake daura mata a yanzu basusan a mizanin wace kaddara zai hau ba sbd abu ne da babusa a tarihin GHAZ kuma bazai taba zamaba ga asalin jinin Wanda yake kan mulki kuma Wanda yake magaji bazai taba auren wadda ba jinin BOYEM ba haramun ne ma ga jinin da mahaifinsa ya mulki BOYEM kuma shima Ana sakaran ya mulki BOYEM auren wadda ba jinin BOYEM ba. Tayaya zasu fuskanci wannan auren da zaa kulla yanzu a masarautar da Kai tsaye mutuwarsu ce hukuncin wannan auren da akai indai ya isa gaban sultan da Masarautar BOYEM. Bude idanuwanta tayi ahankali jajir dasu sun kumbura ta miqa hannunta a hankali kofar dakin ta tura a natse bakinta na budewa da disashiyar murya tai sallama tana saka Kai daidai nan kunnuwanta suka jiyo mata sautin FATIHAR da aka shafa ta DAURA AUREN NUAB ALMAZZ BOYEM DA AYANAH BAHAR ABAAS GHAZ Wanda ya ratsa kunnuwan duk Wanda yake cikin masarautar GHAZ din Banda BAHAR wadda bacci takeyi a kishingide idanuwanta a rufe sbd kanta dayake tsananin ciwon damuwan dake zagaye da rayuwarta Akan ciwon BAA dinta Wanda shine gatanta,rayuwarta,hasken idaniya da rayuwarta. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 64 Rufe baki da hannuwa Maa sakinah tayi a lokacinda ta tabbatarda auren ya dauru Wanda hadarine zalla a cikinsa da zai iya raba mutane da yawa da rayuwarsu sbd sun aikatawa masarautar BOYEM gagarumin haram din da zai tono sirri Ka da dama amma koma menene ita saina shirye take da bawa Auren kariya da lafiyarta da rayuwarta har karshen rayuwarta da ba lallai tanada yawa a nan gaba ba. BAHAR da motsi ya sakata bude manyan fararen idanuwanta da suke sak na mahaifiyarta asalin balarabiyar SHEMALI masu daukan hankali da saka baki da jikinka mutuwa sbd Wani irin sirrin kwarjini da nitsatsen kyau dayake cikinsu, Akan sakinah dake kofar dakin tana shigowa ta sauke idanuwan a natse tana qarasa budesu gabaki daya akanta tareda tashi Zaune cikin nutsuwa da jinin mulkin GHAZ dake yawo yawo a jikinta batareda ta bude baki ba tayi magana sbd koma wanene shine yakeda damar bude baki ya sanar da ita shi waye meya kawosa dakinta dan haka kafafunta ta ziro a hankali cikin nutsuwa ta saka a cikin Takarmin dayake bakin gadonta tana kafe idanuwanta Akan sakinah dake qarasa shigowa tana bayyana fa hasken dakin na wutar gargajiya dake dakin take ta bayyana a idanuwan BAHAR din wadda Kai tsaye kukane idanuwanta suka fara cin karo dashi matar na yi Wanda ya saka bugun zuciyarta

Chapter 25 of 28