Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya da cewa ‘Banda rashin tinani irin na Ubansa da tsufan dayake cinye kwakwalwansa tayaya zaiyi tinanin ma sauya Ka daga zama mai mulkin BOYEM Akan Wanda yagamo yawon duniya da taaddanci’ Numfashi meryam kawai ta iya saukewa me zafi tana fatar koma menene kowa zeyi yayi itadai buqatarta ASIM ALMAZZ ya zamo me mulkin BOYEM ya dauke hukuncin dayake kansu ta auri koma Wanene zata samu. Aslam kuwa can qasar zuciyarta Wani irin tsoro da fargaba takeji Wanda yake hanata cewa komai dan kuwa koma yayane dawowansa su dai ba alkhairi ce a garesu ba, ASIM ma a qasan zuciyarsa wata shakka ce ke son shigarsa da matsuwa da son haduwa da NUAB ALMAZZ dan yaga menene yake dashi a yanzu sannan ya sheda cewa shi ASIM ALMAZZ yanzu ya fisa komai musamman ilimin daya samu cikakke me kyau Wanda ko hakan zai saka a basa mulkin shi a hana masa dan babu ta yanda dan taadda zaiyi mulkin BOYEM baa taba ba kuma bazaa taba farawa ba. HAILE ma kusan bazasu taba gane abinda take ji a zuciyarta ba sbd har abada indai NUAB ALMAZZ yana raye batajin akwai ‘dan da sultan zai so kamarsa duk da baya tareda NUAB din shekara da shekaru amma hakanan take Jin bai taba Dena sonsa ba kawai abinda ya sakata kwantar da hankalinta shine koda yana sonsa baya tareda shi yana tareda ‘danta ne kuma gaggawar datake yi shine a Dora ASIM kafin ranar dawowan NUAB tayi gashi yanzu ya dawo batareda burinta ya cika ba dan haka yanzu sabon yaqi ne garesu su dukansu Akan tabbatarda burinsu ya cika kota halin yaya. *****Se karfe goma da mintina ya Baro bangaren Amminsa Bayan yaci abinci tareda ita cikeda kwanciyan hankali sun samu kasancewa da juna yanda yakeso tukuna ya fito ya fice. Lafiyayyan gyaran da akaiwa bangarensa ya saka yana zuwa Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa Wanda yake da Wani palon hutawansa a ciki kafin asalin bedroom din. A jikin bangaren nasa akwai manyan bedrooms guda biyu da sukeda girma sosai da toilets a ciki anan Yaransa suka sauka aleey kuwa bedroom daya dayake cikin bangaren nasa ya sauka dan haka dukkaninsu shigewa sukai sbd lokacin hutun LEUL ne. Wanka yayi da dukkanin abinda ya saba amfani dashi sbd babu abinda yake amfani dasu da aleey bai siyo ba baa. Dogon wandon bacci na lebarto ya saka mai wani irin santsi da Laushi sbd tsadarsa sai farar rigar wandon Kwantawa yayi ransa da ruhinsa cikeda nutsuwa take baccin hutun dayake buqata ya daukesa. Gabaki daya bangaren da zagayensa tsit yayi sbd Yaransa da suka tabbatarda hutawa yakeyi babu kowace hayaniya da ake buqata. Daga shi har Yaransa Hutu sukeyi Bayan an bada cikakkiyar umarnin kada Wanda ya tinkaro bangaren. Acan fada kuwa kowa ya cika duk wani babban masarautar yana cikin fada Zaune, Hakama duk Wanda yake gari ko qasar datake kusa da BOYEM indai jinin BOYEM ne sun iso suna cikin masarautar wadda ta dauki dumi dan kuwa a cike take da masu fada a ji na mulkin BOYEM, Shi kansa sultan Bayan dogon lokaci daya dauka kafin fitowansa ya fito daga karshe Bayan kowa ya gama Halarta kenan shi kadai ake jira da LEUL din Wanda baima San mesuke yiba, Zaman fada da meeting din zafi ya fara dauka Wanda ya saka sultan yake sake jin baiyi danasanin aika dansa ba harma ya zama koma menene ya zama yanzu din dan kuwa a bayyane wata irin zazzafar qiyayya ce yake gani tako ina a idanuwa da kalaman duk Wanda yake fadar Akan sai hukunci yahau kan duk Wanda ya taka dokar Masarautar BOYEM koma wanene. Sultan da abu dayane yake cikin zuciyarsa yana Juyawa shine rashin zuwan NUAB din garesa Bayan shigowa sa masarautar da shine yake mulki da ikonta hakama shine uban daya haifesa komai Zafin kansa da ikonsa wainda a gurinsa cikin jininsa ya gajesu, Dagowa yayi ya kalli taron manyan qasar BOYEM din gabaki dayanta da idanuwansa da tsananin zallar mulki da ikon dayake jininsa yana bayyana, Umarnin suke jiran ji dan haka akai tsit Ana kallansa tareda jiran abinda zai fada kowa zuciyarsa har rawa takeyi sbd jiran umarnin da sultan din zai bada. ASIM da idanunwansa sukai jajir zuciyarsa har wani fizga takeyi ya kafe sultan din da ido yaja baza kunnuwansa jiran abinda zaa fada, Bude bakin sultan umarnin kiran LEUL BOYEM ya bada tareda tabbatarda umarni ne me karfin gaske. Dan aike Koda ya isa tin daga nesa ya zube qasa bakin kofar bangaren yana daga muryansa ya isar da sakon cikin tsananin girmamawa. Dukkanin sakonsa a kunnuwan Yaransa ya isa amma babu Wanda yakeda niyar isar da sakon sbd lokacin gurinsa bai qareba dan haka manzon sakon yana zube a qasa bai tashi ba sbd Sai an amsa masa sakon zai tashi koda kuwa zai kwana ya wuni a hakan. Shiru shiru ba dan sako Wanda ya saka fadar sake daukan zafi babu Wanda ya iya cewa komai sedai xukata sun dauki Zafi. Awa kusan biyu manzon sakon ya shafe a durqushe cikin rana kafin me BOYEM din ya tashi baccin sa Kai tsaye ya shiga toilet yayi wanka ya bata lokaci sosai kafin ya fito daure da towel fari qal daidai nan wani manzon sakon ya sake isowa sedai wannan Karan bayi biyu ne daga bangaren mahaifiyarsa aka turo Wanda hakan ya sakasa Dakatawa cak daga abinda yakeyi sbd bayin saida suka gabatar da kansu suka isar da sakon ya kuma San me ake nufi da aiko bayin mahaifiyarsa Wanda take zuciyarsa ta fidda Wani irin Numfashi me dumi ya ajiye towel din dayake hannunsa na goge Kai ya juyo ahankali cikin isa da wata irin izza ya nufo kofa ya fito. Aleey dayake palo a tsaye yana jiran fitowansa yana ganin fitowansa da towel take ya dauko sunglasses na Versace ya miqa masa hannu kadai ya saka ya karba yana nufar kofa Kai tsaye wadda tini aka wangale masa ita, Yana fitowa umbrella biyu a take aka bude take a kansa batareda ya tsaya ba suka biyosa dukkaninsu tamkar zasu fashe sbd karfi ga tattoos nasu daba wasu dake bayyane sai daukan ido sukeyi, Cikin mummunan tsoro da firgici bayin dake kofar bangaren sukai qasa da kansu jikinsa na wata irin tsima sbd firgice wa, Wani irin daukan ido fatarsa keyi wadda azababben Hutu ne ke bayyana a kowane babu na jikinta, Kai tsaye fadar ya isa cikin wata irin izza gashin kansa yana zube a bayansa towel din dayake qugunsa yana sake fidda lafiyar kakkarfan jikinsa dayake a murde, Tin daga nesa securities din fadar da kaf bayin dake hanyar suka zube qasa kawunansu a qasa zuciyarsu na wata irin harbawan da kansu yake kasa dauka. Wasu irin samudawan da babu alamar rahama ne ASIM yaga suna shigowa fadar jikinsu na zanen tattoo din da idanunwata sun gane masa daidai guda uku daga cikinsu fuskar NU’AB ALMAZZ ce zane a jikinsu matsayin tattoo, A kofar shigowa suka tsaya daidai nan LEUL me BOYEM ya sako Kai cikin fadar cikeda Wani irin zazzafan iko da izza, Gabaki daya wuta daukewa duk Wanda yake fadar tayi cikeda matsanancin rikicewa da girgiza me tsananin gaske suka zubawa kofar daya sako Kai ido bakunansu a sake suna wata irin rawa. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 55 Takowa yakeyi kansa tsaye cikin isa da Zafin kansa dayake a bayyane sbd sun samu kunna inda baa kunnawa a zuciyarsa dan aika bayin mahaifiyarsa Kai tsaye kunnasa sukai shi kuwa a gurinsa bayin mahaifiyarsa sunfi duk Wanda yake cikin fadar daraja a gurinsa idan aka cire uban da yayi cikinsa. Duk takunsa daya zuwa tsakiyar makekiyar fadar girgiza zukatan duk Wanda yake gurin yakeyi sun kasa Nemo tinaninsu da kalamansu, Qasa suke yi da idanuwansu cikeda sake shiga mugun shock daya wuce firgici dan bama zasu iya kallan fatar jikinsa dake Wani irin daukan ido kakkarfan jikinsa dake murde yana sake shigar dasu rudewan shin a fadar BOYEM suke ko kuwa, ASIM da idanunwansa suke rarrabuwa Akan samudawan dake tsaye a kofar wani yawu ya Hadiye da karfi a sirrince sbd tsananin mamakin dayake Neman rudar dashi Sake bude idanunwansa yayi da kyau Akansu daya baya daya yana San tabbatarda shin fuskar NUAB ce yake gani zane a dantsen hannunsu wasu kuma a wuyansu wasu kuwa kirjinsu dayake dan bude sbd rigar da bata rufe ba botiran sama na rigar a dan bude, Yana yana yaji idanunwansa sunayi ya maida kallansa da sauri Akan aleey dayake tsaye riqe saida waya da iPad da baya rabo dasu sbd koyaushe a shirye yake da buga waya ko aikatar da sako ba delay, Zancen tattoo din jikin Aleey ya qarasa rikitar da tinanin ASIM sbd ‘LEUL BOYEM’ ne Baro Baro rubuce a hannunsa tin daga gwiwan hannun har zuwa gurin da tafin hannunsa ya fara, Juya fuskarsa yayi a slow yana maida kallansa inda NUAB yake ya Dora idanunwansa da suke cikin rudani akansa ya kafesu akan bayansa dayake daukan ido sbd haske da lafiyar fatarsa idanuwansa suka sauka Akan tsakiyar bayansa da sunan ‘GHAZ’ yake rubuce cikin wani irin rubutu daya sakasa saurin dauke idanuwansa Akan rubutun yana miqewa kafafunsa na wata irin rawa ya Riga NUAB saurin isa tsakiyar fadar ya zube gaban sultan a hankali yana sunkuyar da Kai ya bude Baki zaiyi magana daidai nan NUAB ya iso gurin ya tsaya cak tareda dagowa ya zare shades din fuskarsa ya saukar da idanuwansa da suke zak na ubansa da suka sauya babu abinda yake bayyana a cikinsu Bayan zallar wutar bacin rai na shakaru ya sauke su Akan sultan Wanda idanuwansa suke kafe Akan NUAB din tin daga lokacinda ya sako kafarsa a fadar yana takowa a cikin takun dayake tabbatarda shi din jininsa ne tsatsonsa ne da a kowane hali bazai taba dana sanin haihuwansa ba da rayuwar da suke akai yanzu, Cikin tsakiyar idanunwan NUAB din yake kalla cikeda Wani irin yanayin dayake tabbatarda alfaharinsa da samun cikar burinsa da NUAB ya rayu a duniyar datake cike da maqiyansa, Ya rayu ya zama tsayayyen da zai iya tsayawa Ayanah ya bata kariya da rayuwarsa batareda shakkar kowa a duniya ba, Babban burinsa ‘dansa jininsa ya tashi ya rayu a duniya batareda shakkar komaiba bare kowa ba Bayan Allah daya haliccesa, A yanda ya tashi ba shakka ba tsoro ba fargaba ba kunya ba wasa babu abinda yake girgiza dan kuwa ko mutuwa baya tsoro koyaushe tazo zai amsa kiranta haka yake burin jininsa ya kasance gashi burinsa ya cika harya zarta sbd Zafin wutar dayake gani a idanuwan NUAB bayajin akwai abinda zai kashesu, Ba qiyayyarsa yake gani a idanuwansa ba zafinsa da fushi me tsananin gaske yake hangowa Wanda yasan da hakan yana ganin hakan tin yana yaro dan haka bai damu ba tinda ya zama Zakin dayake fatar ya zama ko da wannan qiyayyar ta idanuwan NUAB din zai rayu tinda a cikin idanuwansa take baa zuciyarsa ba,hakama indai wannan fushin nasa da nisan dake tsakaninsu zaisa ya tsayu a cikin zarrarsa sa fushi ne yake da qarin karfin riqeta ya shirya rayuwa da hakan har sai ya tabbatarda yahau mulkin da shine zai gama bawa Ayanah cikakkiyar kariyar dayake mata yaqi hakama dashi kansa da ake fatan fizgewa daga tarihin BOYEM dan haka saiya tabbatarda wannan burin nasa Akan NUAB din ya cika kafin ya nemi kusanci da ‘dan nasa dayafi masa duniyarsa gabaki daya. Cikin sautin daya saka fadar sake daukan tsit NUAB ya bude Baki muryansa ta shiga kunnuwan duk Wanda yake gurin kaman saukar Aradu yana juyowa yace ‘Waye yaga ya kamata a aika bayin Amminah kirana??? Rufe idanuwa sultan yayi a hankali Wani radadi na ratsa zuciyarsa na yanda ‘dansa ya zabi kasa masa magana a bainar mutanen fada da suma duk sukai tsit sbd kafe fadar da Yaransa sukai da ido ba ko kyaftawa kamar robot suna jiran Wanda zai motsa bada amsar shine su fasa kansa da bindigar dake hannuwansu ko Jeho masa wuqar da zata tsaga kansa biyu dan haka ganin sultan baice komai ba har lokacin kallan NUAB yake son dayake masa yaci karfin mulkinsa da matsayinsa dan haka sukai shiru babu Wanda ya dago tukuna dan kuwa duk karfin mulkin BOYEM aka fasa kan mutum da bindiga kafin masautar ta dauki mataki ko nuna ikonta da zafinta Akan hakan andai Riga Kai an kasheka a banza da wofi ihu ne kawai ze biyo Bayan hari gashi da alama kafiran samudawan thugs din dake tsaye basu San dokokin masarautarba tukuna dan haka ba wata bata lokaci zasu aikaka ba shiri. ASIM ne ya motsa cikin tsananin mamaki da baqin ciki me girman gaske ya miqe shima ganin NUAB bai durqusaba ya kalli NUAB din ransa na tsananta tafasa da quna mai tsanani ya bude Baki zaiyi magana NUAB din ya sake bude Baki da mahaukaciyar muryan data saka ASIM din ja da baya cikin sauri ‘Waye ya nuna wannan rashin daar ga mahaifiyata???? Aleeyyy………. Cikin karfin murya datake tattare da umarni da iko mai karfi Sultan ya Katsesa sbd hanasa abinda yake niyar yi koma menene yace ‘LEUL NUAB ALMAZZ ka nutsu kasan inda kake, A gaban me BOYEM kake, Nine me mulki a nan ba kaiba, Nine me fada aji anan ba Kai ba Nine Wanda ya isa ya kira kuma dole a amsa, Sake kallan jikinsa sultan yayi cikeda bacin rai kafin yace ‘Nan fadar BOYEM ce ba gurin wankanka ba dan haka umarni ne ka koma Ka sake shiryawa fada zata sake nemanka amma Ka sani hakan da kayi na yanke maka fita Masarautar BOYEM bisa umarni me karfi sai Bayan wata daya zan buqaci ganinka’ Da mamaki me karfi da shakkar dake cikeda zukatan yan fadar kowa ya dago ya kalli sultan sbd zazzafan furuci suke jira daga garesa da hukunci me Zafin gaske amma suma tsananin shock da mamakin da suka kasa fitowa a cikinsa na ganin tantirancin karshe ganin idonsu ya saka suka bazasu iya cewa komai ba ko yin komai sai tinani da nutsuwansu ya dawo daidai jikinsu tukuna dan haka barin fadar a watse meeting din suke buqata yanzu suje su sako tinani, NUAB kuwa juyowa yayi cikin nutsuwa da sabuwar tafasar datake cin ransa zai kalli sultan sai kuma ya fasa ya juya yana barin gurin sbd bayason jijjiga duniya da ikon sultan din a gaban mutanen da ikonsa yafi komai a duniyarsu. Yana Juyawa gabaki daya bayi da securities din fadar suka sake zubewa qasa suna sauke kansu jikin bayi na tsima, Su aleey ma Juyawa sukai suna bin bayansa sultan ya zubawa Bayan NUAB din idanuwansa yana kallan sunan GHAZ din dayake Baro Baro bayyane a tsakiyar bayansa daga sama. Kaman yanda ya taho haka aka daga masa umbrella ta basa kariya daga Zafin rana hakama shades dinsa na rage masa hasken rana ne da zai keto a cikinta, Har suka fice sukai nisa babu Wanda ya motsa saida suka bace wa fadar gabaki daya tukuna aka ringa sauke Numfashi me Zafi da bacin rai me tsanani musamman ASIM daya kasa motsawa daga kallan inda suka wuce din idanuwansa jajir da sbd tsananin ja da bacin rai da baqin cikin dayake ciki har wasu ruwa ruwa suka cike idanuwan fuskarsa tayi jajir hannuwansa na dan rawa ya saukesu yana juyowa ahankali ya fara bin palace officials din wato manyan fada da kallo daya bayan daya yana debe musu albarka a zuciyarsa tareda Jin zazzafar tsanarsu da baqin cikin ganinsu ma a gabansa sbd shiga rudin da sukai har suna kasa cewa komai a fadar da sun isa su yankewa ‘dan mistress kowane irin hukunci, Wasu yawu masu daci na baqin ciki ya Hadiye yana dauke idanuwansa daga kansu ya dawo da kallansa kan sultan Wanda tin kafin ASIM din yayi magana yace ya tada zaman fadar na yau sai kuma wani lokacin. Cikeda girmamawa da son barin fadar su shaqi iskan nutsuwa a waje kowa dake fadar suka zube qasa a hankali suna masa a huta lafiya. Koda ASIM ya zube qasan shima zuciyarsa kaman zata fado yake jinta tsabar baqin cikin sultan da duk Wanda yake fadar dan haka har sultan ya bar fadar ta kofar da shi kadai yake bi ASIM bai dago ba, Sultan na ficewa aka fara ficewa daya bayan daya daga fadar babu Wanda ya samu cewa dan uwansa komai har suka watse, ASIM ne yayi na qarshen fitowa tareda babban yaronsa Salman Wanda shima zuciyarsa taje cikeda baqin cikin dayake kusan na ubangidansa haka suka bar fadar Kai tsaye suna nufar bangaren HAILE. A kofar bangaren da babu me wucewa sai jinin BOYEM da bayinsu mata kadai, Tinda ya tinkaro bayin dake bangaren suka ringa zubewa qasa kansu a qasa suna masa Barka da shigowa amma babu Wanda ya kalla zuciyarsa gap take da bugawa ya isa palon hutawar mahaifiyarsa inda ya tadda su a tsaye dukkaninsu Banda meryam dake Zaune itama tana dafe da goshinta Aslam da HAILE kuwa a tsaye suke qyam kowannensu abinda ya faru a fadar yake son ji dan kuwa suna tsammanin jin zazzafan hukuncin da zai saka NUAB zuciya ya sake barin qasar gabaki daya. Yana shigowa suka zuba masa ido dukkaninsu suna jiran jin bayani a bakinsa amma ganin yana yinsa ya saka jikin meryam da Aslam sanyi suka zauna batareda sun furta komaiba sedai HAILE ne tace ‘Meya faru? Yaya akai a fadar? Wane hukunci sultan ya zartar masa? Zai bar qasar dai ko? Zazzafan fushi me tsananin zafi ne ya taso masa ya saka hannuwansa biyu ya dauki table din dayake gurin cikeda Kayan marmari da Kayan ciye ciye ya daga sama ya buga qasa da karfi komai ya fashe da karfi tareda watsewa da kara me karfi. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 56 HAILE data ga hakan take zuciyarta ta tabbatar mata da basu samu abinda suke so ba kenan, NUAB bai karba kowane hukunci ba daga sultan kenan, Matsalarsu akwai yiyuwar zata fara ne daga yanzu matiqar NUAB yana nan, Kallan ASIM da idanunwansa suka mugun jajir tayi tana bude Baki zatai magana ya Katseta da cewa ‘Ba dan taadda kadai bane mahaukaci ne,haukace da kanta take kwance a cikin jininsa bawai a cikin kansa bama,ya tabbatarda shine bastard son da sultan YASAR me BOYEM yakeda shi a Idon duniya’ Aslam da duka ba wannan take son ji ba dan bata jin kowace hauka ce akansa zai gagaresu su da suke su hudu ga kuma manyan fada a bayansu hakama ASIM ALMAZZ shi BOYEM ta sani a matsayin ‘dan sultan dayake tareda shi kawai ita hukuncin da akaiwa NUAB din takeson ji dan jin hukuncin ne zaisa su sani ko NUAB din zai tafi ne yanzu ko zaman qasar. Meryam kuwa da tsananin quncinta da rufewan Idon son cikar burinta ta samu abinda takeso to ita koma waye se hau mulkin BOYEM yanzu indai zai janye musu hukuncin dake kansu babu abinda ya shafeta muradinta kawai tayi auren kada ta qare a haka ta mutu a hakan tsufa na cimmusu a ba aure bare ‘yaya. HAILE kuwa guri ta nema ta zauna haka shima ASIM din zaunawa yayi yana zayyana musu abinda ya faru a fadar tas. Shiru Aslam da meryam sukai kafin suka dago suka kalli juna meryam na shaqar Wani Numfashi me zafi sbd tabbas ita kam yanzu takai karshe bazata yadda a fara wannan sabon rikicin da zai zama babban al’amariba a lalata Sauran lokacin da suke tinanin suna dashi na samun abinda suke so dan kuwa komai rikice zeyi yaqin Neman mulkin ya dawo sabo duk suna nan suna jiran a gama me hawa ya hau ita kam yayi mata tsayin da tabbas ba lallai ta iya jira ba dan haka duk inda taga alamar nasara da gaggawa wlh can zata koma ba bata lokaci koda kuwa hakan na nufin tabar ‘dan uwanta uwa daya uba daya ta zabi bastard son din. Aslam ma Zurfi tayi a tinanin da babu alkhairi ko daya a cikin ranta dan ita kam ko zata qara shekara nawa batajin zata taba kaunar ko Inuwar Wanda ma yake kaunar Ayanah da NUAB. Shiru sukai dukkaninsu suna tinanin ta inda zasu fara wannan sabon yaqin da suke ganin kaman yana tinkaro su batareda sunyi tsammanin Wanda sukewa kallan baida banbanci da almajirin yan taaddan shine taaddancin ma da kansa, Kuma idan har zai iya tsayuwa a gaban sultan me BOYEM da babu dan Adam din dayake BOYEM da zai ita tsayawa gaban idonsa ya kallesa bama bare tsayuwa ba kaya daga shi zai towel a gaban dukkanin manya fada da suma iya karshen rashin girmamawan rayuwa sun samesa a hakan da yayi musu to tayaya suke expecting akwai abinda zai girgiza sa, Numfashi HAILE ta sake me Zafin gaske kafin ta dago ta kalli ASIM da idanuwanta da sukai jajir itama ta bude Baki tace ‘Ka saka salman yayi kwakwaran binciken qarshe Akan NUAB din ya binciko waye shi da wainda yake tare da huldodinsa da matsayin dayake tinanin yanada shi dan da alama akwai Wanda ya tsaya masa, Hakama ta Dayan bangaren babban abinda zai kawo sassauci a wannan yaqin da zaayi dashi nasarar mu ta zarce tasa shine tabbatarda qiyayyarsa da sultan bame warware wa bace har abada hakama Ka tabbatarda an gano menene abinda yafi so da’ Shiru ASIM yayi baice komaiba sai idanuwansa jajir daya kafe Hailen dasu yana sauraronta dan kuwa ta hakan zai fara tabbas yana buqatan sanin komai Akan NUAB sbd abinda aka fara musu akansa ba shuke idanuwansu suka gane masu akansa ba. ******Sultan kuwa tinda ya bar fadar yake Zaune palon sa cikin nutsuwa Zaune yana jin tinanikansa da burikansa suna gauraraya da warware wa da saqawa sbd duka burinsa Akan NUAB ya zama tsayayyen Zakin BOYEM ne da zai riqe uwa da qasar da Amana amma hakan ya budewa alaqarsu sabuwar babbar alaqar nisanta da juna tareda zama Wanda fushinsa da zafinsa yayi yawan dabai tsammata dan haka ya basa umarnin tsayawa cikin masarautar ne batareda ya fita koina sbd ya samu lokaci isashe me tsayi da nutsuwa tareda mahaifiyarsa kafin ya basa umarnin dayake ransa na shekaru Akan amsar mulkin BOYEM cikin lumana dan kuwa ana fara wannan yaqin bazai samu irin wannan nutsuwan kulawa da mahaifiyarsa ba dan tako Ina fitina ce zata bude kofa musamman ga wainda suke jiran amsar mulkin da manyan fada dan shi koma menene NUAB din ya zama shi shine yake son ya zama mai mulkin BOYEM bayansa kota halin yaya ya shiryawa kowannensu a tsakanin shi NUAB din da bazai karba ta lalama ba da wainda zasu tada hankalin baa basu ba da manyan fada da duka zasu iya kasa Aminta da hakan a shirye yake da kowa. ******a bangaren LEUL kuwa koda suka koma saida ya sake sabon wanka ya shirya cikin ash Rb wears da suka zauna jikinsa a natse qamshinsa me sanyi na tashi ya fito palonsa inda aka kawo abincin rana daga bangaren Amminsa aka cika dining din a Jere babu kalan fruits din da babu Bayan lafiyayyan abinci Kala uku. Zaunawa yayi a natse batareda damuwan komai a ransa ba duk da har lokacin zuciyarsa daukan dumi takeyi idan ya Tina rashin daar da aka nuna ta aiko bayin mahaifiyarsa kiransa, Bai damu da hukuncin sultan akansa ba sbd bayajin akwai dalilin daya isa ya hanasa fita idan ya tashi fitar musamman da Ayau din ya basa umarnin aleey ya fara shirin tafiyarsu da Amminsa barin qasar gabaki daya Wanda da kansa a shirye yake da samun sultan ya fada masa da Amminsa zai tafi Kai tsaye idan shirye shiryen suka kammala kenan. Tareda Yaransa gabaki daya suka ci abinci a dining din Wanda hakan ke qara musu kaunarsa da tsayuwa Akan kowane lamarin sa dan babu kyama ko nuna banbancin matsayi a tsakanin sa dasu, Cikin kulawa da sakewa sukaci abincin aleey na sake koro masa bayanin manyan fada guda nawa ne a tarihin Masarautar hakama guda nawa ne suka Halarta taron yau din da dukkanin yanayinsu daya nuna a fuskarsa tareda sunayensu babu Wanda bai dauko komai akansa ba tsaf dan haka kwakwalwansa take tamkar computer. Bayanin full binciken rayuwar ASIM daya hada da abinda ya qara karanta tattare da yanayi sa na yau din shima ya fara koro bayanin a tsare dalla dalla cikin ilimi da tabbaci tin daga kan karatunsa na primary har zuwa yanxu dayake da har masters da Sauran ilimin wasu abubuwan tas. Dakatar dashi NUAB yayi daidai lokacin da zai zayyana bayanin su Aslam da mahaifiyarsu tas sbd baya buqatan sanin kowa

Chapter 22 of 28