Share this page
jikinta sosai. Tay niyyar ta gaya mata cewa zata yi mummunar nadamar juya musu baya, da dora burinta akan ɗa namiji dan in akwai abunda yake gaba da rashin tabbas a duniya da sunan shi namiji ne. Cikin kukan ta girgiza kanta ta daga ido ta kalle Adiaha snn ta mike tsaye tace "lokaci na zuwa da zaki neme mu adiaha. I wish u gudluck with ur marriage. Tana fadin hakan ta fice itama jiki a sanyaye bata kara juyawa baya ta kalleta ba Alhaj aliyune ya bi bayansu domin ya kara musu nasiha koda da za su sassauta ma adiaha aransu amma dukansu basu kulashi ba. Hanklin hjy hajara bakaramin tashi yay ba sai taji tsoro wa rayuwar adiahan bana wasa ba Tana hawaye cikin lallabi Tace ma Adiaha tayi tunani sosai fa, intasan hakan datay bai dace ba marmaza ta tashi tabi bayan iyayenta tabisu sukoma garinsu koda zasu yafe mata. Irin birkicewa da kukan da Adiaha take yi awajen zakayi tsammanin cewa zuciyarta akarye yake sosai amma ina a duk sanda ta tuno da cewa rayuwa zatay da Ahmed na har abada zai taji kamar bazata iya juyawa da baya ba ta gwammci ta rasa komi a duniya amma banda lamaribta da Ahmed dan sosai tasaka aranta. Haka Taki sam tacema grand ma dinta auren Ahmed is her final wish tunda iyayenta sunki bata goyon baya sun tsine mata ai shikenan itama bata bukatarsu ai akwai Allah. Bayan nan ta wuce daki tanata kuka gashi a musulunci baa ashan giya, dan haka kukan kawai tayi tayi dan abun ya fice mata aranta koda zataji sakat. Ata fannin kafayat kuwa wajajen karfe sha biyu na rana ta isa nasarawa state ta wuce gidan Alfah lamidi inda ta tarar da mahaifiyarta tana zaune akan dadduma ta idar da sallah kenan ta nemi waje kusa da ita ta zauna Bayan ta samu nitsuwa tafara gaya mata duk abunda ake ciki da familyn jimada she was so sooooo excited akan maganan komawa sabon gidan dan gani take kmr a matsayin amarya za'a kaita. After a while bayan Alfah ya dawo daga wajen sallah acikin wani private Masjid din gidansa inda sukenan da shi da almajiransa.. Daga dawowarsa ya aika aka kirawo su ciki suka shiga suka zauna akan tabarma, nan suka fara magana mai dan tsayi da yarensu, yafara gayawa kafayat abunda ya gano acikin qaddararta da Ahmed damilare, kafayat taji kamr kanta bazai iya daukawar komi ba, can sai ga kafayat din nan ta fito daga cikin wajen a rikice cikin tsananin fushi da firgici tana kuka sosai ta rike kirjinta datakeji kamr zai balle ya fito waje, kuka takeyi tana girgiza kanta har ta isa gaban motarta snn ta rgwabe ta fadi kasa awajen tanata kuka sosai. Mahaifyartan ce ta biyo bayanta arikice zata yi waje,Alfahn shima yabita yanamai kara jadadda mata yana cewa "iya kafayat, ki nitsar da yarki sosai fa, inba haka ba both of u will regret. Ta juya tana kallonshi da fuskan neman alfarma da tausayawa da harshen yarensu ta kuma tsugunawa har kasa tana rokonsa koda akwai abunda zaiyi domin ya temaka ma yarta Alfah yace mata ai zancen destiny akeyi duk yadda sukayi qaddarar mutum saiya cika shi, yace mata "kafayat ba matar Ahmed bane" tauraronsu baiyi matching ba sam sam snn daren dadewa kuwa qaddarar kowa zai cika, yace mata destiny can only be delayed but can neva be erased kawai ta riƙe yarta suje sunemi wani mafita acikin gaggawa amma tasani cewa duk evil din da zataje tay aure tsakanin kafayat da Ahmed bazai taɓa yuwa ba. Inhar ya yuwa to tasani yartace zata mutu a ranar da aka daura auren. Godiya tay masa itama ta bar wajen a rikice tanamai kiran sunan kafayat da tuni takai kanta can waje Ganinta a kasa tay rigijib ajikin mota tanata kuka wanda hakan yasaka tay saurin tsugunawa kasa tare da rungumeta ajikinta sosai cikin sigar lallashi. Kafayat dake bori kamar na wanda iyayenta suka mutu suka bar duniyan sai ihun sunan Ahmed takeyi tare da nata tana karyata zancen cewa shi ba mijinta bane na qaddara har saida taso tarawa mahaifyarta mutane awajen. Da kyar ta kwasheta ta sakata a mota suka bar wajen izuwa gidan babban aminiyar mahaifyarta wato hajiya rakiya. Dukansu yayn goddess of fire ne a harkan tsafin su suka soma shakuwa, hjy rakiyan Itace shakijiyar ta aharkan business snn atare suke duk wani infidelitynsu na rayuwa. Nan ta kai yarta kafayat dan ta rarrasheta inda suka taru ita da kawartan sunata bata baki duk dama kafayat tay ta bori tana zarginsu da cewa ko biyan Alfah kudi sukayi dan amata karya su rabata da Ahmed dinta. Saida suka sha wuya kafin su kayi controlling din kafayat din har ta rusuna ta dan samu bacci. Ata fanninsu Adiaha kuwa tunda Kura ya lafa sai adiaha ta taurara ranta ta aje komi agefe saidan in abun ya fado mata kaga tana zubda hawaye musmn inta tuno da kalaman iyayenta aknta. Tanajin tafara shiga damuwa zata bige da tunanin rayuwarta tare da Ahmed sai kaga kuma hanklinta ya kwanta sosai . Ata fannin Hjy hajara kuwa tunda hakan ya faru ta rasa nitsuwarta yau din gabaki daya ko wani abincin kirki bata iya sakawa abakinta ba Tunanin rayuwar jikarta Adiaha shiyafi komi daga mata hankli bama tunanin yadda komi ya kare musu tsakaninsu da familynsu da kuma zuriarsu ba. Yau har dare ya raba bata samu sukuni aranta ba dan tasan Lamari mai wuya Adiaha ta jefa aknta aciki dan duk wani mai hankli yasan namiji badan goyo da zani ba tunaninta kar Adiaha tay auren nan taje ta gamu da wani sabuwar tabun da bazata iya gogeshi acikin zuciarta a dalilin da namiji ba. Sosai ta damu, mijinta Alhaj aliyune ya zauna da ita washe gari ya dinga bata ingantattun shawarwari, ciki harda maganan kawo zancen auren Adiaha da ahmed din anan kurkusa dan hanklin kowa ya kwanta. Dukansu sun manyanta sunga rayuwa shiyasa jikinsu yake ta basu cewa Adiahan ce kawai take son yaron sosai. Washe gari da safe kafayat ta farka da wani irin zazzabi mai zafi irin mai saka maganganun nan, sai maganan Ahmed takeyi, tana cewa sai ta aureshi, itace matarsa. Duk dai ba acikin hayyacinta ba. Rashin ganin dawowarta a jimada family yasaka hajy khadijatu ta kikkira wayarta lokcin tana barci sai basu dauka ba. Kusan sau uku tana nemanta bata same ta ba, sai can dare kafin nan Alhaj bello ya kira sabida matarsa ta riga ta gaya masa abunda ake ciki na cewa bata samu kafayat a waya ba, sau biyu ya kira hjy fatihat na kallo bata daga ba, sai can hajy rakiya ta zugata akan cewa ta dauka ta gaya masa cewa kafayat din tana tare dasu batajin dadin jikinta ne tana bacci. Hakan kuwa akayi ta fada masa cewa kafayat na wajenta, as usual sai yadan nuna damuwarsa akanta sabida tamkar yarsa haka yake jinta aransa. Tunda suka fara wayar hajya rakiya take ta lisafe lisafe aranta amma batace maa kawartan komi ba. Duk zamansun nn zagin familyn jimada sukeyi dake ma abun nasu ya hadu da haushin rashi da kuma hassada sabida kowa yasan jimada family sunada kashin arziki azuriarsu shiyasa kaf yayansu suke tasowa a matsayin hardworking men masu gina kansu da kansu da kuma taimakawa iyayensu . Bakowa kecin sa'ar samun kansa acikin family mai kyau irin wnn ba wanda babu wata gaba ko fada mai tsanani, bbu kyashi tsakanin yan uwa, babu cin kafa ma juna sai kkrin kawo cigaba da nunawa yan uwansu hanyar cigaban suma Washe gari da safen ma saida Alhaj bello jimada ya kira wayar kafayar domin yaji ya jikin kafayat din yake suka ce masa da sauki amma bata farka abacci ba tukuna. Sam sam hjy rakiya taki sukale maganan kafayat Da jimada family tun jiya take cewa mahaifyar kafayat akan su dauki fansa, kar ta bar rayuwar kafayat ya kare alalace, kawai ra zage su yage rabonsu ajikin familyn jimada amma haryanzu bata fito mata da maganan cikin sarari ba. Dagata bangaren Su hajya khadijatu kuwa shiri kawai sukeyi na komawa sabon gidansu Yau da sassaafe babban dadarta hjy maimunatu ta kirata take gaya mata cewa nan da wata daya zasu dawo nigeria gabaki daya dan haka ta amince mata afara batun neman wa yarsu yasra gurbin karatunta a Abuja . Sosai wnn kalma yay wa hajy khadijatu dadi sosai aranta,yau ta kasance cikin nishadi ne marar misaltuwa dan dama can tana da bukatar wani na jikinta wanda zai zauna agabanta a babban sashenta na sabin gida dan tasan cewa danta Ahmed zaiyi aurenshi snn attention dinsa zai fara komawane ta wani waje ba aknta ba. Bisa ga behaviour din kafayat na kwana biyun nan ma sosai ta fahimce cewa in ta aure mata danta hala Bazata ma kyaleta dashi acikin sauki ba dan taga alama sosaine yarinyar take zumudi akan zancen aurensu .Amma idan har yasra tana zama a gabanta a matsayin yarta hala komi zai iya kasance mata cikin sauki Kuma dama babban burinta ne ta nunawa yasrar gata sosai. Bayan kwana biyu. Yau Ahmed yake kkrin cika kwana goma sha daya dayin tafiyarsa. Yau da safe tana farkawa yaga sako daga wajen kakar Adiaha da cewa suna son ganinsa da shi da magabantasa. Kanshi yaji yafara maaa ciwo dan harga Allah bawai son auren na harcan can yakeyi aransa ba amma toh ya zaiyi yariga da yafara dolene kawai ya karasa.. Tura tex din yay ma duka yayunsa maza bai cire ko kalma daya ba. Kafin ya kammala wanka ya shirya yay break fast saiga video call na brother kazim daga U.S Duk abunda yakey ya bari ya taho Saida ta nemi waje ya zauna snn ya dauki kirar tare da rusuna har kasa cikin girmamawa yahau gaishe shi da yarensu na yorubanci cikin bashi girmansa sosai. Yace masa sun gama magana da brother hamzat da wani dan uwan babansu uncle bakre , dan haka ya shirya Suje yola yau yau yake son ayi maganan auren nan agamashi gabki daya .ko musu Ahmed baiyi ma yayansan ba ya amsa masa da toh acikin ladabi Bayan ya kammala fada masa dukkan abunda zasuyi insunje can snn ya katse wayar. Ahmed ya kira abokinshi banji yace masa yazo ya rakasu yolar shima, around 10:30 am na safe kowa ya iso garin jos sukayi booking next availble flight to yola su hudunsu sukazo garin yola inda suka dan kama lodge awani five stare hotel dansu shirya kansu. A fannin adiaha kuwa tun jiya da safe alhaj aliyu da hajy hajarat suka zaunar da ita suka mata nasiha ahead of rayuwar data zaɓa ma kanta, anan ne suka nemi shawarar ta akan maganan auren tundata amince musu shikenan sai suka gayyace magabatan Ahmed din dan suzo sai asamu akarkare komi. Kafayat kuwa tunda ta samu saukin jikinta takewa mahaifyarta bori saidai dake hjy karimat tana wajen yasaka rashin kunyartan yake yin sanyi sabida yadda hajy karimat din take fayyace mata komi tanamai shigar mata da reality cikin kwakwarta. Sosai suke taruwa su kashewa kafayat gwiwarta musmamn idan suka soma jefa mata bakar magana da gori kala kala akan cewa Itace take son Ahmed amma Ahmed basonta yakeyi ba.. Tun kafayat bata son fahimtar gaskiya har saida ta fahimce gaskiyar sarar amma sin shi datakeyi yasaka ta cigaba da musu taurin kai tanata zarginsu da cewa sun hada baki ne da Alfah lamidi dan amata karya ta rabu da Ahmed. Sukanso basu san da cewa duk zugi da bakar maganan da suke gayawa kafayat na shigarta sosai ba, hjy karimat ta dada ce mata ai mahaifyar Ahmed da Ahmed din shikansa da mahaifinsa duka sune suka taru suka lalata mata rayuwa. Acewarta sune saka bawa zuciyarta hope din jin cewa ita tasu ce bayan sunsan ba hakan bane bazasu taɓa bata space arayuwarsu ba. Duk suka maida maganan ya dawo kamar kafayat ne victim na betrayl a gidan jimada. Sai suka nuna mata cewa suna jin matkar tausayin ta yadda ta zama kamar kwallon kafa atsakanin familyn jimada. Kwana biyun nan haka suka hanata yin waya da kowa agidan suka ki su gaya mata cewa hjy khadijatu takan kira wayarta, saidai ma suce mata ai gashinan tunda kika bar abuja bata taɓa ta nemeki ba sabida bata damu dake ba kuma tana jin kishinki, hjy karimat tace mata lallai kishi hjy khdijatu takeyi da ita shiyasa take jin kanta insecured inta na gangan da mijinta. Kafayat ta nemi karya acikin maganganunsu duk ta rasa, bisaga abubuwan da ita kanta tay nazari duk gani tay kamar gaskiya kawai suke gaya mata wanda tunda can ta kasa bude idonta ta gani amma duk da haka sai bata nuna musu alaman cewa magangnunsun ya taba mata zuciyarta ba. Tunda suka mammata wnn magangnun take zama tay doguwar nazari akan rayuwarta. Ata dayan bangaren kuwa tuni hjy karimat ta fayyace ma Hajy fatihat duk wani shirinta na daukar kyakkwan fansa acikin familyn bello jimada wanda tuni itama tay na'ammm da wa n shirin nata aranta ayanzu haka kafayat kawai suke jira ta basu hadin kai. [5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH 15.* BY SURAYYAHMS. Yola: Wajajen karfe 4pm na yamma su Ahmed suka kammala shiryawansu izuwa gidan Alhaj Aliyu mijin kakar adiaha. Already brother kazim Aremu daga can u.s haryay magana da wani Abokinshi mai kudi dan siyasa ne honourable sabo, nan da nan aka musu arranging motoci guda uku na kece raini da zasu je gaisuwar dashi, black colour lexus guda biyu da DBX jeep, dukan su suna zuba kyalli aka dire musu agaban hotels din snn aka hadasu da official drivers. Dukan su manyan kaya suka saka, dan uwan mahaifinsu mai suna uncle bakre da brother hamzat sun sako shadda ubansu mai gare da hulunansu masu shegen tsada wanda daga ganin su za kasan cewa shigar tasu ta barazana ce kawai da suka shirya musu dan suja girma wa familynsu sosai, brother hamzat dimeji yasaka golden colour shikuma uncle bakre ya saka wata royal blue getzner, Banji ya saka black half jumfa bugun kamfani, Ahmed kuma ya saka full fitted jumparsa sky blue colour mai wani irin kyau da sheqi dukansu sun sako hulunan da sukai matukar dacewa da kayansun sosai. Fadin irin kyan da sukayi dukansu acikin shigar tasu bazai iya misaltuwa ba,banda qamshin turare masu dadi babu abunda yake bibiyarsu dan a kallo daya kamasu zaka iya sanin cewa tabbas suna dashi snn sun kece raini. Already sun siyo duk wata tsarabar gaisuwar su ta aure na alfarma wanda zasu kai gidan alhaj aliyun domin Adiaha,brother kazim ya riga ya gaya musu cewa yana son ayi komine a lokaci guda batare da bata lokaci ba,yace idan har mutanen Adiaha basuda wata matsala har kudin sadaki ya tanadar su bayar sabida baison ayita memeta jeka ka dawo tsakanin Abuja da yola. Tun safe Adiaha take cikin zullumin abunda zatayi kafin su Ahmed suxo danko kayan da zata sakanma ya zama mata damuwa dan data gudu agarinsu batazo da kayanta ba sai wanda yake jikinta. Tay girki kala kala ta aje dan al'adarsu ne su bada abinci awajen neman aure. Komi tay ta shirya snn tay wanka tay kwalliya Karshe wani tsohon Abaya mai kyau hjy hajarat ta dauko ta bata akanda tasaka kafin suje sumata siyayya washe gari. Shekarun su yaja sosai yanzu ba wani neman kudin sukeyi sosai ba, iya dan abunda suka tarar ne suketa lallabawa ahankli sai temakon da yayan alhaj aliyun suke kawo musu. Wajajen karfe biyar saura motocinsu Ahmed suka bayyana acikin harabar gidan alhaj Aliyu inda aka musu iso izuwa cikin babban falonsa ta alfarma. sallama sukayi daga waje sai akazo aka shigo dasu ciki, nan suka tarda shi a falonsa tare da manyan yayansa maza su biyu, da kuma limamin da ya musuluntar da Adiaha da wani dan uwansa malam shehu. Tunda su Ahmed suka shigo ciki Sai satar kallonsu awajen akeyi sabida yanayin shigarsu ta kece raini da wayewa. Cike da girmamawa Da karrawa akayi yar gaishe gaishe snn aka fara tattauna dalilin daya tarasu. Tunda manya suka shiga tattauna zancen auren Ahmed baice uffan ba dan tunda ya rusuna kanshi ƙasa babu abunda yake tunani sai komawarsa gidan dan sosai ya gaji da batun auren nan. Iya abunda yaji awajen shine da akace musu ai Adiaha ta riga ta musulunta snn harma ta amshi sabuwar sunanta na musulunci wato REEMA BASSEY Sunan REEMA suna ne mai kyau na larabci,duk dama wasu yararruka suna amfani dashi da wata ma'ana daban,a harshen larabci sunan REEMA yana nufin "white gazelle" or "a Good and polite at heart person"... Sosai sunan ya dace da Adiaha dan ita yarinyace mai kyawun hali da saukakken zuciya mai taushi. Saida akayi kabbara snn Ahmed ya daga kai shima yay dan murmushi jin kowa na mata murna, yanajin su uncle hamzat da uncle bakre suka karkare maganan nasu acikin mutuntawa. An yarje an amince za'a bawa Ahmed auren Adiaha,saidai ko da aka kawo zancen saka rana sai dukansu suka fara yin baya baya da zancen hidiman biki musmmn ma da aka ga kamar su Ahmed din suna da shi sosai Alhj aliyu bai boye musu komi gameda abunda ake ciki da iyayen Adiaha ba sabida inma wata hidimar biki ne zata tashi susan dacewa Adiaha fa bata da kowa ata fannin iyaye bare ace zasu mata wani hidiman aure. Bayan ya musu bayanin hakan ne uncle hamzat yy magana cikin katse musu hanzarinsu shi yace musu subar zancen dukkan wani hidiman biki da kayan gara su zasu mata komi tunda basu rasa ba. Atakaice dai mata kawai suke so. Jin hakan yasa Kowa yy hamdala aka sanya musu albarka, Anan aka yanke sadaki Aka ce musu su kawo ko dubu hamsin ma yayi,nan Uncle hamzat suka ciro kudi suka bada dubu dari biyu da hamsin. Snn suka ce musu sunason adaura auren ne ranar Asaba dats nan da kwana uku..nan aka tsaida magana. Ata cikin gidan kuwa Sosai Adiaha ta matsu dan tana mugun son taga Ahmed ido da ido yau sosai, dan sosai tay kewarshi aranta kwana biyun nan da basa tare, tana son ta fada masa abubuwa dayawa aciki harda damuwarta dale damunta aranta na rabuwa da iyayenta. She want him to atleast hold her and comfort her abit sabida haryanzu abin bai dena damunta aranta ba. Saidai koda aka kammala shirya komi Ahmed din ne yafara matsa wa yayansa akan su tafi kawai shiya gaji. Alhaj aliyu ne ya matsa akan lallai su tsaya suci abincin da aka shirya domin su, musmmn ma ganin irin kayan tsaraba na Alfarma da suka kawo na auren Adiaha. Duk wasu abubuwanda yake wajen brother kaxim da bro hamzar ne sukayi shi shibaima san komi akai ba dan sosai yayunsan suke sakaltashi tun yana dan karami. Da kyar Ahmed ya daure ya shiga cikin gidan suka gaishe da hjya hajarat a falonta wanda yawanci ma banji ne yake amsata dan Ahmed kam ya dawo musu tamkar amarya kmr wanda baison yay magana a cikinsu sosai,hjy hjara ta lura da shi yaron bakaramin jamusu aji yakeso yay ba, yanayin sa da kasaita, da kuma kamiya musammn ma dayaga jikin Adiahar na rawa akansa duk ta zautu da alaman tana sone su kebe sugaisa suka dai. Koda ta gaishe sa acikin mutanen ma bai wani sake mata fuskansa sosai saidai kawai yay mata murmushi, batun zanca addininta saiyace mata "congrats" daganan baisake kulata awajen sosai ba sai sama sama in ana hirar lamariin tasu. Badon banji yana ta saka su dariya yanajan su a hira ba da tuniwani zaice ko hala auren dole za'ayi ma Ahmed da yarinyar danko ruwan da adiaha ta kawo musu awajen shi baisha ba abun duk saiya dame hajy hajara ganin inda Ahmed yake dan babbasar da komi. Bayan tafiyarsu ne hjya hajara ta dinga yima Adiaha surutayya akan behaviours din Ahmed. Takaici kamar zai kashe tsohuwar ganin yadda Adiaha take ta murnan kayan tsarabar gaisuwar Da suka lodo suka kawo. A tunaninta soyayya ne yasaka aka kawo mata kayan tsaraba na Alfarma.Ga goro, ga buhunan abinci,manja, gishiri,doya,kudin katoton rago, banda kananan carton carton na wasu abubuwan. Suna zama zasu ci abinci grand ma ta kasa hkr Cike da masifafen mita Tace Adiaha kina bani kunya fa, am actually ashame of u today.. Dolene ma yaron nn yana hura mana hanci ni banga laifinsu dasuce su zasuyi komi ba saboda kin nuna masu we are nothing,memakon ki kare martaban familynki ure here getting excited kinzo nan kinata murna akan abun duniya bakiga yadda yaron nan yake daukar kansa agabanmu tamkar wani sarki ba... Why is he behaving like temakonmu zaiyi, mune zamu bashi mata amma Shine yake mata fadi da jan aji ? See oo My grandoter, ki bude idonki dan Bai kamata ace Duk wann wahalar da kikayi akansa kwana biyun nn ace ko minti biyar bazai samu dominki ba, Atleast ai yasan halin da kika shiga ciki na rikici da iyayenki akansa but im deeply suprise all he has to say to u is congrat, Kai kai..nide wann abu baimin ba. He is such a jerk. Adiaha ta bata rai sosai tace grand ma wai sau nawa zan gayamaki ne haka fa Ahmed yake, shi bamai son magana sosai ba idan kin fahimce shi sosai zakigane cewa he is a good man. Hjy hajara batace komi ta nade hannu cikin mamaki tanata kallon yadda maganan yy ma Adiaha zafi tanata hargagin fushi. Nan ta fara kare Ahmed akan dukkan korafin da kakartan tay, harda ce mata ai yanajin kunyan yayunsa ne shisa bai sake jiki da ita ba, snn dan yace mata congrt akan zanca addini ai dama badan shi ta sauya ba. Babu ta yadda zaka kushe Ahmed agaban Adiaha batare da kawo maka wani dalilin da zai kare shi ba. Sai cewa take ai tausayin halin da take ciki da iyayenta tare soyayyar dayake mata ne yasaka familynsa suka ce zasu mata komi na hidiman auren and she is happy nd grateful for that. Adiaha ta dauka duk wasu kalmomin nata datake kare Ahmed dashi agaban grandma masu ma'ana ne saidai batasan da cewa Maganganun datake furtawan yanayiwa kakarta ciwo aranta bana wasa ba. Aranta cewa take Adiaha is blind and desperate about this guy. Batasan da cewa mutuncinta take sayarwa ba. She wont have value to them musmn ma indan sunajin kansu a matsayin cewa sune sukayi komi na aure. Ta rasa abunda zata ce mata kawai ta fasa cin abincin ta tashi cikin fushi ta koma dakinta tabarta awajen ita kadai tana ta bawa kanta dalilai akan Ahmed na cewa lallai yana sonta ne sosai shiyasa zai aureta Jin abun yafara dan damunta saita tura masa sakon tex a sabon layin sa and she foolishly told him cewa grand ma dinta is not really pleased with him, ganin hakan ne yasaka ya daure ya kirata suka fara gaisawa. Rabon shi da kiranta awaya tun ranar da suka rabu a calabar dan yace mata bayason tana kirarsa koyaushe musmmn ma indan tana tare da familynta. suna kammala gaisuwar Yy kmr bai karanta tex din sosai ba, sai Yace mata ta memeta masa meyene grand ma dintan take cewa akansa.. Tafara gaya masa duk abunda kakarta ta fada da irin bayanin da itama tay mata akanshi. Ahmed ya daure fuskan sa sosai cikin yanayin basarwa da bata rai yace "Toh shikenan naji,.zan gayawa yayunq sai azo ayi magana a tsaida batun auren tunda grand ma dinki tace bata aminta da halina ba. Adiaha ta kwalo ido waje tace "Ahmed meyasa zakace haka? Da Bai amsa ta ba sai jikinta yay mugun sanyi dan Sam batay tsammanin jin hakan daga gareshi ba. Tuni yanayinta ya canza cos its seem he is gaslighting her now sabida yasan babu yadda ta iya dashi, Cike da bugun zuciya da damuwa Adiaha tace Ahmed pls ni ba hakan nake nufi ba, kay hakuri karkakai maganan gaba,grand ma is just being worried about me sabida yadda taga na rabu da iyayena duka akanka. Cikin yanayin hade ransa Yace " okay, yanzu kenan laifina ne da iyayenki suka rabu da rayuwarki Ko dama akaina ne kika zanca addini? Zatai magana cikin katseta da shakurarren murya yace "silent,ya isa haka. "kar ke ko kakarki ku fara tunanin daura min wani laifi akan wani abu daya shafi rayuwaki dana iyayenki sabida ni aurenki kawai nace zanyi Amma bance ki canza Addini ko ki bijirewa iyayenki akaina ba...ya lumshe ido jin tafara kuka tanamai neman tafara bashi hkri, ya kuma bata ransa muryansa kasa kasa cikin shan qamshi sosai yace ..'look ni ba hkuri nake so daga gareki ba, i' m quite disapointed in u ryt

Chapter 16 of 19