Share this page
sun riga sun dawo surukunai. Sukuwa abunda suke so kenan suga sun same total submission and biyayya daga wajenta, ta inda koda anyi Auren sune xasuyi controlling Rayuwar Ahmed tunda Hajy khadijatu uwarsa itace take juya musu kan dan uwansu Bello, But with kafayat by their side sunsan xasu same nasu daman suma ata wajen Ahmed. Haka suka nitsar da kafayat suka nuna mata cewa babu wani abun kunya wajen ya mace idan tayi proposing ma namijin datake so dan ba haramun bane. Tunda Ahmed yaki ya furta mata yana son ta kuma yana son suyi aure sukace toh ita saita shirya furta masa dakanta inhar Ahmed ya amsata toh basai ma anjira 2 weeeks din nn ba xa'a fara shirin aure . Hakanan su anty nurat da anty najat suka taru suka cikama kafayat kasa aciki, aka fara shirya grand suprise proposal party wa Ahmed. Kasuwa suka baxama na musammn aka sissiyo kayan ado wanda xai saka Ahmed ya kasa iya rufe bakinsa inyagani. Wani hadadden backless red flowing gown kafayat ta siya mai tsada na dubu arba'in da biyar da takalmi mai tsini da head crown da flowers da rings dinta masu kyau. Har dare sunakan yawon siyayya agari suna shiri ma suprise engagement party kafayat kuwa tasha hadadden gyaran gashi da attachement cos batada dogon suma sai tayi manicure da pedicure tasaka nails dinta masu shegen kyau da tsada she is ready shining like a bride kowa sai yabonta yakeyi ranar Shiyana can yanata aiki baima san me sukeyi anan ba, Tun safiyan ranan tuesday din anty ramatou taxo gidansu ta same hajy khadijatu ta gaya mata abunda suke shiryawa, itama batayi kasa agwiwa ba tasaka albarka akan lamarin dan aganinta kafayat will make a good wife to her son ahmed inhar yana son auren ita bata da matsala sam. Sunyita nemansa awaya still yauma tuesday din amma basu same shi ba,sai can da yamma lis kafin nan yabaro asibiti ya taho gidan agajiye da niyyar shiryawa tafiyarsa na gobe da sassafe. Samu yy hanklin maman sa duk ya tashi dan ta nemesa awaya har ta gaji,tun bai Xauna ba tafara bashi labarin tafyar, haka tayi tayi dashi akan cewa ya shirya kawai gobe da safe karfe takwas suje gidan su anty mojushola tare amma haka nan yaki mata sam yace baxaije ba dan yasan baida wann lokcin domin kuwa karfe tara jirginsa xai tashi ixuwa garin calabar, toh gashi abun nasu suprise ne ba ason agaya masa harse yaje ya gani hjya khadija ta rasa ta yadda xata soma shawo kansa. 8:30 am na safiyar wednesday aka shirya masa suprise party din. Kafayat is already feeling sooo excited dan gani take ko ba dan Allah ba idan Ahmed yaxo yaga idanun manya awajen kamar irinsu anty moju da mahaifyarsa da su Anty temi hala xai hkra ya amsa batun aurensun kawai even if its out of compulsion. Sosai ta saka ranta akan wann lamari shiyasa ko wani baccin arxiki bata samu tayi ba. Batasan da cewa shawo kansa dan yace xaixo wajen ma saida akata drama da shi agidansu sosai ba... Karshenta ma Anty mojushola ne ta kirashi dakanta awaya ta dinga kuka tana kora masa ashariya ahakan ma saida ta hadashi da babansa kafin nan yace musu xaixo tare da mum dinsa Cos he is already very annoyed da yadda suka matsa masa akan saiyaje wajen musammn ma da basu gaya masa dalilin xuwan ba. Cikin dare adakinsa yau ko runtsawa baiyi ba yahau kimtsa trolley na kayansa na yin tafiyarsa ixuwa calabar,sassafe karfe shida ya farka a bacci bayan yy sallah yy wanka yaxauna yana shiri at same time suna waya da abokinsa banji. Bayan sun kammala maganan Adiaha Ahmed yafara bashi labarin irin matsa masa da akayi jiya akan wai yaje family house dinsu yau da safe, lokci guda banji ya soma dago kan xancen a mind dinsa. Ahmed yana kan mita banji ya datsi numfashinsa da cewa Guy wait..amma kayi magana da kafayat awaya jiya kuwa? Ahmed yace no, akan me ita uwata ce daxan mata magana..naga dai tulin miscalls dinta jiya ban bita kanta ba.. Banji yace hmm to mesa baka kirata ba. Tsaki Ahmed yaja yanakan daura igiyan booth dinsa yana cewa "I cant oo,ina maka maganan family na meya kawo maganan kafayat anan kuma, dat one na normal thing now..ai dama ta saba min irin waynn miscalls din sabida bata da aikin yi a rayuwanta sai bina. Banji yace hmm ba haka nake nufi ba,i just smell sumting fishy abt her cos she called me yestade tana tambaya na wasu abubuwa game dakai dana tambayeta tacemin wai gift take son siya maka, kuma naji surutun su Anty adizat anan gefenta sai nayi tunanin me sukeyi atare ahaka? Da mamaki Ahmed yace kafayat din ne take tare da sun anty adixat?? Banji yace yea i am sure naji muryansu sosai lkcin she was shouting at her doter medina, surutu awajen dai kmr suna kasuwa nace kodai wani abu suke shiryawa ne baka sani ba. Ahmed ya kyabe bakinsa a yanayin ko inkula snn yace "Oho nide sunki sufada min komi kawai cemin akayi wai muje family house before 8 amma karka damu koma miyene ni nasan mexanyi dasu. Banji yace toh shikenan dai inka sauka lpya dai ka kira take care bro. Ahaka suka kammala wayar kowa ya cigaba da abunda ke gabansa. After some few minutes saida ya lura kamr babu motsin kowa snn ya fito acikin sanda ya yaje ya bude bayan booth dinsa ya aje trolley dinsa aciki ya kulle snn ya dawo ciki tsaye agaban mirror yy lkcin harya kammala shiri yana fetsa turare yanata tunanin abunda xai gayawa mum dinsa idan yaje mata sallama qamshin jikinshi gabaki daya ya gama cika dakin yanamai dada gyara gashin kansa da brush. 8 o clck na bugawa aka fara buga masa kofa akan ya fito, Baiyi wata wata ba ya sauko kasa dan ya nufi dakin mum dinsa dan shikansa yana son ya isa airpot by 8.30 kuma baifi saura 30 min ne 8:30 din yy ba. Qamshin turaren jikinshi dayasaba sakawa ne ya dinga baxa ilahirin gidan ayayin daya sauko yana doka sallama a dakin mum dinsan ta juya tanamai tsaresa da idanuwanta da sukayi luhu luhu sabida kukan dataci. tun dagacan mahaifiyrsan ta xuba mai ido tana sauke sanyayyar murmushi datake fiddawa da kyar ganin irin mugun kyaun da yyi yau yasaka All black casuals ne na marks and spencer mai 3 qtr jacket, yasha booth dinsa ubansu da agogonsa na new police irin matte black din nan snn ya shafa mayukan gyaran gashi sai kyalli kansa yakeyi.. Yanayinta dayagani ne na ragwabewr jiki da jimami yaso yadan dagamai hankli nan take ya taho wajenta a gaggauce cikin tashin hankli, tambyarta yake amma bata amsashi ba har saida ya karaso ta wajenta tukuna ya lura da cewa video call takeyi da babban dadarta wato Anty hajiya maimunatu mohd gidado. Su biyunsu mahaifinsu ya haifa amma suna da wata kanwarsu yar kanwar mahaifinsu da aka rainesu tare. hjya maimunatu din itace Babbar yayansu, sai mahaifyrsa Hajiya Khadijatu,snn hajiya Aminatu wanda itace yar kawunsun snn itace karamarsu wanda bata wani jima da yin aure sosai ba ta rasu awajen haihuwa. Yau shekara 18 kenan da rasuwarta amma haryau sunajin mutuwartan kamr sabuwa domin kuwa wann mutuwarta yar uwartasu aminatu ya musu ciwo musammn ma da hjya maimunatu take da tabbacin cewa *Kishiyar kabila* ce ta kashe musu yar uwansu aminatu akan batun haihuwa. Mijin yar uwansu Aminatu Alhaj Amadu hussaini yy aure yakai sau goma amma bai taba samun haihuwa ba sai akan yar uwarsu aminatu wanda shiya jawo kishiyarta datake *kabila* ta hade baki da likitoci aka kasheta awajen haihuwa. Anyi case sosai bayan mutuwar aminatu saidai Kafin lkcin basu da wani kudi snn iyayensu kaf sun rigamu gidan gaskiya dan haka basu samu mai tsaya musu akan gaskiyarsu ba,snn alkcin shikansa mijin yar uwartasu yay gamone da wani irin kaddara na shanyewar rabin jiki sanadiyar hawan jinin daya turnukesa ayayin dayaji cewa matarsa Aminatou ta rasu awajen haihuwa dan bakaramin sonta yakeyi ba. hjy maimunatu itace tamkr uwa kuma uba agare su dukansu dan haka lamarin sosai yay mata ciwo fiye da kowa wanda shine sanadiyar dayasata shiga harkan siyasa da neman kudi har Allah ya daukakata. Sosai take son taga ta raya xuriarta da kuma jininta, Shiyasa haryau take kaffa kaffa da rayuwar yar uwarta hajya Khadijatu agidan yarbawan nan dan yanxu ita kadaice ta rage mata a duniya bayan mutuwar aminatu, Basu da kowa a duniya sai yayansu, wato yarta nafisa da kaninta sadik,da shi Ahmed din da kuma yarinyar da aminatun ta haifa kafin rasu ta bar musu mai suna YASRAH AHMED HUSSAINI wanda a hannun hjya maimunatun ta girma. Yau yasra take cika shekara 18 takwas a duniya wanda yy dede da ranar mutuwar mahaifyarta aminatu shiyasa duk suka taru sunata kuka suna masu tunawa da ita atare. Ahmed yana isowa wajen ya fahimce abinda suke ciki, jikinshi a mugun sanyaye ya xauna akasa yanajin conversation dinsu mai saka tausayi da jimami dan mahaifyr sa tasha bashi labarin rayuwar hajy aminatu da yadda kishiyarta ta bala'in axabtr da ita dan ance har hauka saida tayi da ciki ajikinta. Shidai yasan shi bamai son xumunta bane dan haka baxai iya kirga sau nawa ma yajeshi katsina wajen hajy maimunatun ba dayake karami, xai dai iya tuna lkcin da akayi sharia a kotu aka kwato custodyn yasra daga hannun dangin ubanta da suke son riketa na dole dan sabida sunacin arzikin mahaifinta tunda shi baida lpya,da asirin su ya tonu kotu sai tabawa hjy maimunatu amananta na har izuwa lkcin da mahaifin nata zai samo sauki, amma bayan nan bai san komi ba saidai duk da haka yasan dacewa antynsan tana son famlynta sosai. Xamansu A turkey na tsawon lkci a matsayin ambassada na kasa shiya dada sakawa xumuncinsu yyi nisa sosai wanda shiyasa ma kwata kwata bai taba sanin kamannin yan uwansa nacan turkey ba. yasan dai da akwai adda nafisa wanda take babban ƴa ga hajya maimunatu, dake ta girmeshi a shekaru ita a U.K ma take da aure, sai sadik wanda kusan ya girmesa da shekara guda ne,amma yasran kam baida tabbacin xai iya ganeta ynxu dan rabuwarsa da ganinta ido da ido tun tana yar shekara bakwai lokcin ma tana fama da ciwo sosai. Saida suka dan samu nitsuwa snn ya rusuna kai ya gaishe da anty maimunatu wanda ganinsan ne yadada sanyaya mata xucyrta taji dama dama, albarka ta rika saka masa tanamai masa adduar samun lpya da kuma tsari tanamai nuna alfaharinta dashi dan tana son jininta sosai. Lokacin kan yasra na kallon kasa sama sama takejin su suna gaisawa saidai sam bata iya dagowa sama ta kalleshi ba duk dama tasha jin labarinshi awajen hjya maimunatu itama tana son taga kamannin dan uwantan amma sabida kukan tuna mahaifyrta dataci sai bata iyayin hakan ba. Ahmed Yanata satar kallonta ashe itama satar kallonsan takeyi da shanyayyun idanunta da suka gama canxa kala bai sani ba,a cikin wani irin bakon yanayi ya tsinci kanshi mai tafe da rashin samun nitsuwa, sai can data tamaida idonta ta rufe ruf snn ta dago akayi akayi ta gaishe sa amma sam taki cemai komi, shima sharr yy da ido yanabin ta da kallo kamar bai taba ganin kyakwar mace irinta ba musmmn ma dan karamin bakinta mai kyau irin wanda bai taba ganin irinsa ba . Saida iyayen sukadan lallabeta snn Ahankli ta budi baki muryanta can kasa kasa kamr xatay magana, suka hade ido yarasa me xaiyi sai ya hade rai ya watsa mata harara, ta sake budan bakin ahankli suna kara hada ido taji wani irin kasala na dirar mata da yanayin irin kallon da yake jefo mata nan da nan ta girgixa kai yanayin ta cike da shan qamshi da shagwaba tayi masa shiru batace mai uffan ba sai shima ya basar. Cikinsu babu wanda yacema wani uffan. Anty maimunatu tana Dan murmushi tace Ahmed pls understand her kaji?, duk ranar birthdaynta haka take rigima sam bata son yin magana bare murmushi. Ta sake kallonta cikin lallami tace yasra, Ahmed fa babban yayanki ne kisaki jikin ki dashi kinji? Dan yauko da bana duniya sune jagora agareki da shi da sadeek, shine yau kuma baxaki iya cemai koda sannu ba? Batace komi ba ta dada sauke kanta kasa alaman dai baxata cemai komi ba Babu yabo ba fallasa Ahmed ya kyabe bakinsa snn yace its okay bakomi momy, ahnkli yana satar kallonta yace atleast muma ai baxamu ce mata happy birthday ba. Tashi tayi tabar gaban screen din tana tura baki ko irin murmushin nan batayi ba, atake sai yaji attitude dinta ya kuma shakesa a wuyarsa amma saiya ya basar cikin murmushi suka dan gaggaisa yanaji suna maganan shirye shiryen graduation party da xasuyi na gama scndry school din yasra idan suka dawo nigeria in few months time. Bayan sun kammala wayar hjya khadijatu ta sauke nannauyar ajiyar xuciya tana cewa Oh Allah ka nunamin ranan dawowarsun nan lpya,sounding sooo happy tace i just cant wait..dan kuwa katsina xan koma wajen adda maimu nayi hutuna ko kunaso ko bakwaso. Murmushi ahmed yy sigar tsokana yace Wann ai ma dad knan kike tura wnn sakon, nidai saidai na xama muku dan aika dan nasan shine baxai iya jure xama babu ke agidan nan ba.. Kunnensa taja tana dariya tace marar kunya kawai kaci kaniyarka kenan wato kai lkcin har kayi aurenka ko? Kansa ya girgiya yace no binki can xanyi ai dama rabona daganinsu na dade kafarki kafata,.. Dariya kawai tayi yace a babban gidanta na katsina xata xauna ko? Tace eh, kasan tunda tenure dinta ya kare acan turkey, already har president yay signing mata wani new political appointment anan senate house of assembly Abuja. Kaga ko da ban tare a katsina ba still xatana xuwa abuja akai akai sabida aikinta Yanxu haka ma maganan karatun yasra ne yake damunta tanata tunanin a nema mata university anan ne ko acan turkey ne xaifi, but i dont think xata iya kyaleta a wani kasa da karancin shkaruntan nan u knw sumtimes she can be soo protective. Inde anan din yasra xatayi karatu i think nice xan dauki ragamarta kawai sai anemo mata spot a nile ko base university tafara karatun anan Abuja kusa dani tunda kaikam ma aurenka xakayi. Baice komi ba yay murmushi sai can snn yace toh Allah dai ya dawo da su din lpya. Tace Ameen Agogonsa ya kalla ganin 8.15, yace mamy lets go mana akwai inda nake son xuwa and Its very important daman tun jiya naso na fada maki sai bansamu dama ba. Tace 'a a ,abar wann maganan kawai tashi muje dan tun asubahi anty temi take min waya akan na make sure naxo tare dakai. Inyaso idan munje saika fadamin inda xakaje din Yace mammy what is it dat ure not telling me? Wai meyasa akace dolene sai munje family house by this time Sharesa tayi ta dauki hadadden golden veil dinta ta yafa snn tace meet me outside my friend da already ma munyi latti.. Baice komi ba ya miƙe yabita abaya suka fita kusan atare, tunda suka dau hanya yake takurata yyi yyi ta gaya masa menene amma sam haka taki har suka isa kofar mansion din jimada. Ana bude musu gate yy ma mai gadi ido akan karya kulle kofa alaman yanxu xai juyo.. Lpya lpya ya sauke mamansa har kusan bakin main door,snn yace mata ta shiga daga ciki shi xai gyara parking din motarsa acan parking lot xai biyota abaya . Batasaka komi aranta ba ta shige cikin gidan kai tsaye, ko minti biyu batayi da rufe kofar gidan ba yay kwana snn yaja motarsa cikin gaggawa ya bar gidan aguje ya wuce hanyar airpot abunsa.... COMENT AND SHARE FISABILLAH. SURAYYAHMS WHATSAP ONLY 08060712446. SAVE AND CHAT❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 [5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH 7...* BY SURAYYAHMS. Tunda Ahmed ya kama hanya zuwa Airpot bai sake ya bar wayarsa a kunne ba acikin gaggawa kawai yake tuki dan already lokacin tafyr tasa baifi saura minti goma ba. Daga ta cikin gidan kuwa Ko ina yy fess fess kowa yaji kyau andau qamshi kowa ya saka hadadden kayansa mai tsari duk anyi kyau musamn ma kafayat buraimo data sako backless red flowing gown dinta mai tsada. Kowani lungu na cikin gidan anyi decorating dinsa ne da heart shape ballons da katoton red flyr an rubuta will u marry me ajiki mai ja da fari ana jiran shigowarsu Ahmad da mamansa ayi suprising dinsu. 8.40 am dot hajya khadijatu ta doka sassanyar sallama acikin gidan snn ta shigo ciki fuskarta dauke da fara'a tanamai furta wow wow masha Allahu ganin inda waje yy mugum kyau dn anka kashe kudine akayi romantic decorations da abubuwa masu ban sha'awa da burgewa sosai. Dukan tara tara sau goma kirjin kafayat yy dataji sallaman hajya khadijatu,rashin jin muryan Ahmed bai dameta ba ,dan a tunaninta lokacin cikar babban burin xuciyarta ne yaxo. She was soo nervous and excited to the wings tana jin kanta acan sama kamar wacce zata tashi sama dan murna. Nan Kowa yaja ya tsaya in position aka rage hasken wajen ya dawo dim ana jiran Ahmed ya shigo sai ayi suprising dinsa. After some min saiga haj khadijatu ta bullo ita kadai ,tun kafin su fara gaisawa anty ramotou tajata gefe murya kasa kasa, tace iya dami shushhh, pls dont talk loudly u will ruin the suprise for the kids. Tooh ina shi damilare din yake,ya baki shigo ciki tare da shi ba kuma? tun kafin hjy khadijatu ta amsata caraf kafayat ta juyo ta tsareta da ido da alaman tanajiran jin amsar itama Hajiya khadijatu tay murmushi snn tace ku kwantar da hanklinku Ahmed yana waje dan tare dashi mukaxo shiya jawoni ni ma a motarsa. Anty ramotou tay yake tana duban kafayat data sunkuyar dakanta kasa tana dan murmushi tace Alahamdulillahi rabboul Alameenà "Why is he not here yet." Anty moju ta katsesu Acikin girmamawa hjy khadijatu tace "ohhh He said he wll be parking his car outside, Nasan ma hala harya kammala parking din. Wani irin sihirtacyar ajiyar zcya kafayat ta sauƙe snn ta dauke idanunta akansu jin ta samu wani nitsuwa ta cikin ranta. Anty ramouto tace its okay, kowa yy shiru..any moment Ahmed will be in and in sha ALLAH he wll love this . Nan kowa yay shiru sunata murmushin jin dadi,after some few mins wajen kimanin 25mins ya tafi abanza anata jiran ganin Bullowar Ahmed sai shiru abun nashi har ya soma sakasu cikin suspense duk wani motsi ata bakin kofar sai sun leka amma sai shiru.. after like 20 more min Anty moju tafara mita kadan kadan da yaren su tana cewa wnn wani irin parking mota ne aiko kera sabuwar mota yakeyi albarka..anty ramatou ne ta dan fara calming dinta dan karta fara daga musu hnkli. Sosai kirjin kafayat yake bugawa taciki sai tafara jin tsananin bugun zuciya da fargaba mai karfi na neman hadiyeta amma bata san na menene ba. Da shirun yafarayin yawa Haka nan kawai sai ta soma tunanin ko Ahmed ya fasa zuwa ne dan tasan zai iya aikatawa, thinking of that make her soo weak tafarajin kmr ana suyar masa ne akan kaskon kirjinta. Gashi ta gama cika baki wa kawayenta na business cewarta ayau duk wani gulma da akeyi akan maganan jinkirin aurenta da Ahmed zai zamo tarihi, and she wll update them live dan suga engagement dinta da Ahmed. So One of her close business partners mrs Zikirat fasihu da gulma ya mata yawa, ta kasa hakuri tanajin labarin partyn already harta kira mahaifyar kafayat din awaya ta watsa mata labarin dan tasan me ake ciki,babu abunda zikirat bata sani akan rayuwar kafayat ba sabida yawanci idan kafayat tasha giya hakanan take zama ta juye mata dukkan wasu sirrinkan dake cikin cikinta. Hajiya fatihat najin wann batu batay wata wata ba ta dau jakarta ta kamo hanya izuwa jimada family house dan goddess dinta riga ta gaya mata cewa akwai abunda zai faru da yarta ayau marar dadi. 9.30 oclock dede aka kunna wuta acikin falon, a cikin gajiya da rudani da tashin hankli hjya khadija da su anty tems suka fito har waje tsakar gida domin duba Ahmed dan shirun nasa yay yawa.. Sosai jikin Kafayat ya fara ragwabewa zucyarta yasoma bata wani abu marar kyau dan haka atake tafara hauhawan numfashi.. Anty nurat da anty moju sune suka rirriketa suna kwantar mata da hankli duk yanayinta saida ya canja a lokaci guda tafara hawaye mai sanyi Sauran matan duk suna waje babu abunda sukeyi sai kwalawa Ahmad kira aduba nan aduba can Rashin ganin motarsa awajen parking yasaka anty temi ta tumu tafara mita tanamai kokarin lakawa mahaifyarsa sharri na cewa karya takeyi dama tuntuni bataxo da shi gidan ba. Kusan cece kuce suka farayi awajen hjy khadijatu ta rantse musu da Allah cewa tare dashi suka shigo gidan amma anty ramouto sam taki amincewa har saida mai gadi ya tabbatar masu cewa ficewa agidan Ahmed yay kamin nan hjy khadijatu ta samu sa'ida. anty adizat dake ita surkuwace acikinsu bata iyacewa komi sai binsu kawai takeyi tana kallon family dramarsu. Jeka ka dawo anty ramotou take a tsakar gidan tsakanin parkimg space da bakin gate cikin yanayin masifa da tada gurmi tana bambami tanamai cewa _nibo ni ọmọkunrin yii le wa? kini o ro_ ( Ina yaron nan ya fita yaje?..tunanin meyakeyi)..why wud he even go out..kini rizin?Iya Dami Can u pls explain urself, tana maganan ne tana huci tana wani irin hararar hajya khadija kmr wanda zata hadiyeta dan takaici. Sosai kan hjya khadija yay zafi ta rasa meke mata dadi Sai kirar layinsa takeyi babu kakkautawa amma abu daya ake cemusu switchd off. Sai can bayan kamn minti 30 da fitowarsu waje da basuji shi ba anty ramoutou tasaka ihu ta dora hannu akai cikin yanayin masifa sosai tace "what sort of disgrace is dis..Damilare is soo fond of disgracing the whole family. Ahhh, Ahhhhhh,Ahhhhhhhhhh Dami..Dami..Damilare _iga ti embrassement_ Tafada tana huci kamar kanta zai tsage dan takaici, Toh Yanzu me zamuje mu fada aciki kenan, shud we tell dem he ran away? Cos im sure he ran away, ohhh ohh poor kafayat, Kafayat, i really pity dat girl,such an irresponsible shild.. Ahhh Damilare is really a disgrace..hmm.. Hjya khadijatu ta haɗa rai tace pls anty ramotou kidena cewa haka akan Ahmed tunda dai bamusan abunda yasaka shi ya juya ya tafi ba, besides it might be an emergency.. Kamar jira anty ramouto take nan danan tayo kanta a masife tanamai cewa "wani shegen emergncy ne wnn? Hehehe awon emergency ehen...wato yanzu da aka sako maganan laifin danki kinyi caraf kin amsani zaki nema masa uzuri ko? Nasha fadawa anty mojushola cewa kece kike koyamasa wann halin na rashin respect, Ur son is a disgrace, just accept it iya Dami.. Tsaki hjy khadijatu taja ta dauke kanta batako amsata ba tahau neman layukan abokansa banji da bankole saidai a cikin su babu wanda yace mata yasan inda Ahmed yake ayanzu. Anty adizat ta naɗe hannunta ta koma gefe ganin kowa ya birkice da wayarsa ahannu yana mai neman layin Ahmed. Dagata bangaren Ahmed din kuwa 9:am sharp yayi hoarding kansa cikin flight din air peace dan shine mai zuwa straight to calabar in 1hr 3 mins time,earpice ya saka a kunnensa yanajin kida hnkli kwance batare da ya kawo tunanin kowa aransa ba.. Aransa yasan a yanayin yadda ya barsu stranded sunajiransa a gida hala inhar ya dawo abuja baizo musu da matar aurensa ba ya gama yawo awajen familynsa kenan, fargaba yakeji acan cikin ransa duk dama baisan laifin daya aikata musun ya wuce tunaninsa ba. Dan Ko kodan acikiin ransa bai kawo cewa suprise engagment suka hadamai shida kafayat ba,shidai ya bari ne akan shirmene kawai na maganan memeta masa kirgen kwanakin daya rage masa na batun kawo musu matar auren sa da suka sabayi yasa suka kirasa family house. Tun ahanya Ya tura ma babban yayansa hamzat sako akan cewa yana da wata maganan sirri dazaiyi dashi dan duk acikin familynsu jininsa yafi haduwa da brothersa na biyun, wato brother hamzat dimeji, cos he is a very calm and understanding person sabida yadanyi cudanya da garuruwan hausawa sosai.. Yanata son ya tura ma mahaifiyarsa tex ya fada mata cewa shi yy tafiya ne amma baisan ta ina zai soma fada mata ba dan ya tsani jin bacin ranta. Kafayat kuwa tunda taga su hajya khadija sun dade awaje basu shigo ciki ba tasan sa cewa

Chapter 6 of 19