miki ba kinje kin baxa a gari wai shine mijinki and now u cant even move out peacefully sabida kowa sai ya tambayeki ranar aurenku,?uhmmmm maganinki kenan ai tunda kece kika jawo mutane suke kan depressing dinki akan batun aurenki da damilare cos ure the one acting desprate not him, ni dai baxan lamunci hauka ba _rara oti rara_ cmn get up and get back into ur senses we have some money making business to attend to.
Cikin wata malalacin qwuiya kafayat ta wulla kafarta kasa ta buga akan tiles dinsun tanata kukkuni, ohhhh mumy whats this now..shikenan
Mutum bazai dan huta ba saidan akan maganan auren damilare? Yes he is the man of my dreams kuma inajin haushin shi saboda yaki ya kula da maganan auren mu amma badan shi nake shan giya yanxu ba,i jst want to forget about evrything..
A hatsale matar tace ohhhh now i seee, kina so ki mance komi da komi kamar irinsu yadda damilare yake kakkaucewa maganan aurenku ba? Lie on, cos u cant lie to me kafayat,u cant!!! Dat boy doesnt even see ur worth, dama ai wanda yake da jinin northener, jinin hausa ajikinshi kwata kwata baisan darajar mace ba, inba haka ba wani ɗa namiji ne xai dinga wasa da hanklin matar auren sa kamr shi? And dat his family members dat are the worst walking liers on earth,sukuma basuda wani aiki sai karya,kullum damwrsu su miki karyan cewa dansu xai aureki, xaki shiga famylinsu. Ke kuma yen yen yen har kinje musu aikin bauta, _oya were?_ .continue, nidai bana da lokcinki ynxu kawai ki tashi ki wuce wajen business kiyi abunda ya kamata ki dubi agogo fa ynx is almost twelve noon wai dama yau bazakije shagonki bane?
Kafayat ta mike da kyar tana mutsaka idanun ta tana turo baki "wai Yaushe aka fara gaya min abunda zanyi ne agidan nan?mumy dan Allah kibarni.
Matar tayi shiru tana ta kallonta cikin rasa me zatace mata.
Sai Can ta tabe baki tace"hmm lallai kafayat ure so lost akan da namiji ahhhh Anyya kafayat, anya kuwa nice na haifeki?..nifa bansan ta ina kika dauko wann halin naki ba.
"Mummy im not lost,Im fine, just in an energy saving mood.
Daukar pillow tayi ta gwada mata akai,ni sa'arkice da zakice min haka,wani shegen enrgy saving mood ne wannan?rashin tunani da kasala dai dayayi miki yawa ajikinki, see making money shud come before any man, and not man before money, ke haryau bakiga abunda ya faru dani da ubanki ya rasu yabarni banda wani madogara ba? kullum senayi tunani ta yaya ne zaki iya rike kanki a gidan mijinki namijin ma wai Ahmed bello jimada, please tell me how..
Kafayat ta takune fuskar ta tana dada gyara tsayuwarta Haba mumy Ahmed din shi meye ne?maza fa in xaka basu good sex, kana da kyau ilmi, kuma ka iya kwaliya dan kisisinan sace xcyr familynsu ai shikenan ka gama dasu. My only issure now shine in samu hanklin damilare, and i am sure daga xarar ya yadda ya aureni randa muka hada gado shikann baxai iya cigaba da mun wann halayyar san ba,infact mumy xaki sha mamakin yadda ahmd xai dawo kamr kare awajena, sai abunda naga dama nayi dashi agidansu just wait and watch, As of now im calm cos i know i have his full family support
Matar tace hmmmmmm
Haka ne ko?oshey mrs family suport i greet u oloshi mumu girl, Wani irin banxan family support ne har ynxu sun kasa tsaida magana akanki bare akawo mana kayan aure? to tsaya kiji abunda xan yaga miki Nan ta same waje ta zauna turus tana kallon yartan data gama dora fuskar damuwa ayaynin ta,tsaki taja snn tace Kafayat, maganan gaskiya daci gareta amma dolene a fada miki, nifa tuntuni araina bana jin mutanen da akwai damshin wani gaskiya alamarin su cos something is really fishy abot them, ni ban yarda da wann game din da suke playing akanki bafa.
Kafayat tace like how mummy wani irin game kuma kike nufi xaki fara irin abunkin nan ko?why are u negative mumy Wani irin game kuma
Da harara mai xafi tabita tace the game ure too blind to see so just shut up,gyaran muryanta tay snn tace "so as i was saying, kinga wancan uwarsa bahaushiyar din can..? To bari na gaya maki walai Soyayyar munafurci take nuna miki tuntuni amma ke kinki fahimtarta she doesnt wnt u to marry her son att alll, kafayat cmon think about it,ke kin fini saninta da yadda take son danta,snn kinsan waye Ahmed da yadda yakema uwarsa biyayya, he is a mama boy evryone knws dat,duk abinda tace mishi yyi ko bayaso shiyake aikatawa, haka ma babansa itace take juyashi, duk tabi ta mallake su da sihirin su na hausawa da kayan mata,So now tell me, inhar dagske tana son aurenki da danta Ahmed meyasa haryau ba'ayi auren ba?both of them shida babansa acikin tafin hannun ta suke wallai, Inda har tana sonkii da danta degeske da baxamu kai wann stage din ba...
wani irin bugawar xucyane ya xiyarce kafayat dan ko itama ta dade tana xantar da ire iren wann tunanin aranta, saidai bata taba daukar hakan aranta ba sabida yanayin yadda ta rike hajiya khadijatu da amana dan itace ta raineta tamkar yarta a lkcn da mamanta take gwargwarmayan kkrin daga business din nan nasu da tabi ta watsar da dukkan lamarinta taje kasar waje ta barta anan hnnun masu aiki ayyin datake karama,.
Shkarar kafayat biyar mahaifinta ya rasu,ita da mamanta sun sha baqar wahala da family crisis akan maganan raba gado awajen yan uwan mahaifin nata sabida kafayat itace kadai yarsa ta mace sauran yaran kishiyoyin mahaifiyarta sune masu yaya maxa dayawa snn kusan rabin arxikin mahaifin nasu duk wasu aka bayar saidai dake mahaifiyrtan tana bautawa spirit of fire and revenge goddess yasaka tayi tsayuwar daka harta samu musu babban mansion din mijinta a matsayin gadon yarta kafayat. Banda babban mansion din babu abunda aka basu na gado,Bakin cikin rabata da dumbin dukiyar mijinta yasaka ta fanjama uwa duniya domin neman masu kudi. Saidai revenge, hatred da greed sune suka rufe mata ido sai bata damu da rayuwar yarta kafayat datake karama ba alkcin neman kudin kawai tasaka agaba.
Haka kafayat ta girma a hannun masu aiki da nannys dinta, when she was 7 she became so loney wanda shi yasaka ta xamo soo obsessed da abokinta Ahmed bello jimada,sun taso ne as grp of yoruba freinds.
omotola Kafayat buraimo,Ahmed damilare bello jimada,oyebanji Abdlsalami bakre sai na hudunsu shine ibrahim bankole Abdul fatahi, kafayar itakadai ce mace acikin abokan nata maxa su uku, saidai acikin sun nan duk tafi shakuwa da Ahmed damilare sabida jinin fulani ajikinshi dayasa yy dan fari da kyaun fuska saiya kasance he is very very intelligent and attractive to oda girls.
Kamr yadda kowa ke son rabarsa Hakanan kafayat itama ta taso da wann obsession din akansa har suka girma suka saba sosai tana binshi kullum har gidansu ko wani rana in suka tashi a makaranta.
Duba da yadda iyayensa suka fahimce halin da kafayat take ciki na kadaici da rashin kulawar mahaifyrta yasaka suka amshe ragamar kulawa da rayuwar kafayat hannu bibbiyu, musmmn ma mahaifyrsa hajya khadja,dan tamkar yar cikinta haka ta dauki kafayat ta bata kulawa, komi na nuna gata da soyayya tana nuna mata daidai gwargwado har yakaiga kafayat ta fara samun daman cike gurbin rashin uwarta dake damunta a ranta ta itama sai fara rayuwarta kamr kowa acikin jin dadi. She loves Ahmed alot, sabida aganinta shine saviour dinta daga mental depression dashi da familynsa.
Tsawon Shekaru goman nan cass daga primary 3 xuwa sss3 kafayat tayi shine a karkashin kulawar hajiy khadijatu snn dukkan wani abu da ya mace take bukata na rayuwa itace ta koya mata ixuwa wnn lokci.
mahaifiyar kafayat mai suna hajiya Fatihat Adetunji balogun da farko dai dataxo taga kafayat na xama a hannu mai kyau ta nuna godiyarta amma daga baya ganin yadda kafayat din take mutuwar son hajya kahdija da danta ahmed yasaka tafara jin tsananin kishin matar aranta, tun alokcin kammala schl dinsu na scndry tafara jan yarta ajiki sosai tanamai kkrin cusa mata wasu ra'ayina cewa babu amana tsakanin kabila da bahaushiya, sai tana nuna mata cewa ai hjya kadijatu muguwa ce, burin ta shine kawai ta rabasu shiyasa taje wajen malamansu na hausawa suka bata asirin manta uwa.
Kafayat wll alwys rebuke her mother intana furta mata hakan dan tasan dik karyane, wanda ake ganin kamar dan sabida son datake ma Ahmed ne yasa bata son taji ana furta laifin mahaifyrsa agabanta. bayan sun kammala scndry schl din ne mahaifyrtan ta karbe ta mai gabaki daya suka koma yin xamansu tare a mansion dinsu cikin daula sabida wani irin bunkasa da businesss inta yy, kafayat tace ta karanta law university of nigeria nsukka, dake result dinta baiyi wani kyau ba yasa maman taki nema mata aiki sai kawai ta bude mata business din salon da boutique tukuna, daga nan kuma kowa ya shiga tsabgar rayuwansa har suka girma sosai. ko aynxu ma kafayat xata iya cewa mahaifiyar Ahmed din itace take kan rainonta, da can ma itace ta bata ci sha sutura da emotional support of a mother kai hatta yadda ake wanka,wanki, saka pant,saka brexiya, tsafta, wankan tsarki,da komi na rayuwar ya mace matar nan ce ta koya mata yadda akeyinsu.
Idan tana da wani personal problem haryau bata iya kaiwa wajen mahaifyarta direct saidai taxo ta gayawa hajiya khadija dan itace kawai mai iya kwantar mata da hankli
Tun da take Bata taɓa samun shakku ko wani kokonto akan maganan matar nan ba har sai akan batun xancen auren ta da Ahmed which is now getting out of control a xucryta dan kuwa babu wani abu da batayi na nuna biyayya da bautawa Ahmed da familynsa waidan yace yana sonta a fili ba.
Kai Hatta jikinta saida tayi masa tallarsa a free amma duk da haka yaki yabata hadinkai.
Babu kalar shirya masa da batayi ba amma a kowani rana dabiar Ahmed baya nuna mata komi face cewa da akwai wani boyayye kuma babban lamari da xai iya bullowa a tsakanin su wanda take ganin kamar shine xai rabasu na har Abada.
A kullum yaumin idan mahaifiyarta na mata tambaya akan rashin yuwar aurenta da ahmed bayan tasan baya tsallake maganan mahaifyrsa abun yakan dameta aranta bana wasa ba.
Ganin jikin kafayat yy sanyi nan Hajiya fatihat ta cigaba da xugata tana cewa "that woman is busy planning sumting againts u. Hala ma bata son ki aure mata danta ne sabida dantaga ke ba haushiya bace irinta
Magangunu kala kala babu wanda bata mata akan lamarin ba
Wani Tunani kafayat tayi aranta sai taji kmr tafara amincewa sa xancen mahaifyrta, karde maganan mahaiyrtan gaskiyane,karde hajiya khadijatu kabilanci xata nuna mata, ta hada Ahmed aure da wata bahaushiya ba ita ba?
Lumshe idonta tayi sosai tanajin fargaba mai karfi dan da alama Da damshi damshin gaskiya acikin wnn xancen dan tasan kowacce uwa burinta kenan rayuwar danta ya xamo yana under control dinta..
Ta bude baki xatayi magana kenan wayarta yafara ringing nan take sabuwar wakar davido na timeless album dinsa wato "unavailable" ya karade ilahirin cikin dakin.
Kusan atare suka dubi kan screen din suka kalli lambar mai kirar atare.
Agaban screen an rubuta "Anty tems" yana yawo akai. Adan mamakance Kafayat tace why is Anty ramouto calling me kode har Ahmed yace musu xai aure ni ne?
Wani Doguwar tsakin takaicin mahaifyrtan taja muryanta kasa kasa tanamai cewa oya keep dreaming .
Ko kulata batay ba da rawar jiki ta dau wayar tabi ta rusuna kasa cikin girmamawa kamr wanda ake kallonta.
Acikin harshen yarensu ta fara gaishe da Anty ramatou. Wadda take ce mata Anty tems sabida bakaramin sabawa da su tayi sosai ba. Ita kanta Bata san Suna janta ajikin su ne bane sabida suna son Ahmed lallai yay aure daga kabilar su na yoruba dan sam basa son uwarsa tace xata hadashi da wata yar bahaushiya.
Har kasa kafayat ta tsuguna da wayar a kunne tanamai cewa
"o dara irọlẹ
Gud evening ma
Anty tems whatsup kiloshele? Any latest
Daga ta dayan bangaren Anty temi tace "Der is alot oo, but first thing first,i wll like to see u today.. we have a big meeting with u _iyawo wa_
Tsaye kafayat ta mike kalman _iyawo wa_ yana ringing acikin brain dinta cos its means "our future bride" jikinta harna rawa kmr wacce xata tashi sama tace really?
Hararar da uwarta take binta dashi yasa ta dan nitsu Ahankli tace Ahhhh but i hope dai Akan batun aure na da Ahmed ne anty tems.
Daga ta dayan bangaren anty tems din tadan gutsira mata labari sama sama na abunda ake ciki na batun cewa sun saka ma baban Ahmed daci sun takura mashi har yaje ya bawa Ahmed sati biyu akan daya kawo musu dalili ko su Aura mata shi. Kafayat taji kamr xata fashe dan murna dan tasan Ahmed will neva escape marying her in two weeks time din nan dan tasan dai baida wata budurwan daya shaku da ita sosai sai ita,
nan anty tems tace mata Kedai kawai kiyi kiyi marmaxa kixo family house kisamemu musan abinda muke ciki
Godiya ta mata snn ta katse wayar jikinta harna bari babu wani jira tafara shiri ta kwaso nan ta kamo nan kamar wata mahaukaciya, nan ta dauki karamin jaka tasaka hadaddun kaya guda biyar aciki da kayan kwalliyarta da su turare kala kala da jaka mai kyau da damin kudi dubu dari biyar kusan rabin dan ribar kasuwancin ta na satin da sauran tarkacen jewrlies dinta
Mamaki da takaici yabi ya ishe mahaifiyarta amma bata ce mata uffan ba harsaida ta kammala shiryawan snn tace mata wai ina xakije ne kafayat? Ke Daga kawai sun kiraki sun gaya miki magana saiki dibi jiki yuuuu xakije gidansu aikin shashanci da bauta.
Kafayat Tace Ahhh mumy nifa ba gidan su Ahmed xanje ba, Anty temi ne tace naje suna nema acan family house dinsu gidan Anty mojushola. Mum Wai bakiji me take cewa bane? She said in two weeks time xasu aura min Ahmed yeeeyyyy.. omo mi iyawo
Tsawa matar ta dakata mata tace "Shut up jare
Ure a disgrace to woman race _itiju lori rẹ_ awon desperate gang,omo busy body.. kafayat wai yaushe ne xaki san darajar kanki ne? Innice namiji yake having scnd tot akaina baxan jirashi ba, kafin ma yagama min yanga saidai yaga har na nemi wani wanda yake sona nayi aure na nabarshi. In Ahmed yana sonki why wud he take two weeks to decide. Ur just a desperate bitch girl.
A mugun masife kafayar ta kalleta tana huci da alaman maganan ya ci mata rai,a cikin yanayin tsawagoron rashin kunya tace mumy pleassse Abegggiiii. What is dis now, why are u alwys negative?
Mamar tata xatay magana tabi ta tsareta da tsefaffen ido tanamai cewa "i ave heard enough of u mum, me kika taɓamin arayuwata? U left me here to die wadann mutanen ne suka rikeni yanxu kuma a memakon Kiyi supporting dina akan abunda nake so sai dai kokarin juyamin mind dina kikeyi akansa ur evil plan againts me will not work witch.
Ta juya a xafafe xata tafi uwartata ta fixgota tare da daura mata mari akan fuskarta.
Kafayat is me ure calling a witch akan namiji? After all the insult i went trou in oda to secure ur future dan ubanki olodo shegiya,saketa tay tana mai cewa "Okay fine.. ga hanya nan jeki. Amma kisani, Idan har aurenki da damilare baiyu wann karon ba.
Cikin katseta kafayat tace are u going to trow me out of this house bcos this is my father house not urs...
A mamakance Fuska a matukar daure matar tace ohhh really? Ni ai baxan taba korarki nan gidan ba, akan me xan koreki acikin gidan danine na sha wahala wajen kwato miki shi?
Kafayat da kinki da kinso nine na tsuguna na haifeki snn nice agaba da kowa wajen son naga rayuwarki tayi dede.
Xatayi maganan ta tsareta da hannu tanamai cewa:
"listen and listen carefully kafayat, inhar maganan aurenki da Damilare baiyu ba wann karon kisaka aranki cewa nice xan xaba miki miji dakaina nan gaba.
Rai abace kafayat tace okay fine mum..nikuma nayi mikii alkwari baxan dawo gidan nan ba face saina auri Ahmed .
Tun bata karasa furta hakan ba mahaifyar taja doguwar tsaki ta fita tabarta awajen a tsaye.
Abun na mugun damun kafayat aranta amma hakanan ta basar da komi taja akwatinta ta wuce babban mansion din late Alhaji jimada dake anguwan gwarimpa inda family house dinsu Ahmed yake....
SURAYYAHMS. 08060712446 chat only..
" What did u guys think about this chapter? ....
[5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH 6..*
BY SURAYYAHMS.
Tunda kafayat ta dau motarta tahau kan titi tana tuki babu abunda yake dawo mata akanta sai maganan da sukayi da mahaifiyarta, tafiya take amma bakaramin bugawa kirjinta yakeyi ba, ta rasa da wanne xataji tasan dai inhar bata samu Ahmed ba babu Abunda xai hana mamanta yi mata auren dole, atake taji kasala na dirar mata akowani sassa na jikinta,da kyar da wuya ta kaucar da wnn fargaban tafara tunanin yadda xata yi tasamu cikar burinta akn Ahmed, musmmn aynxu data san da cewa xancen ya kwabe mata yaxamo mata tamkar kashin kifi a wuya, tasan dolene komin rintsi komin wuya tasan yadda xatayi su tsaida maganan auren nan nasu da Ahmed damilare kafinan tace xata shiryawa komawa gidansu taje ta gamu da bala'i da masifa irinna mamanta dayake jiranta.
wajajen karfe 1 dai dai na rana kafayat ta iso gaban babban gate na Jimada's family house dake cikin wani hadadden estate dake anguwar gwarimpa.
Duplex ne babban gaske sai parking space gari guda mai dauke da motoci kala kala da basufi guda takwas aciki ba. Kana ganin gidan xa kasan gidane daya kafa dumbin tarihi.
Mai gadinsu bahaushe dan garin yobe yana bude mata gate kai tsaye ta shiga bata tsaya kulawa da gaisuwarsa ba. Tana fita ta wuce babban sashin su anty mojushola, Kayanta ma anan ta bar ma masu aiki su suka ciro a booth suka kai mata cikingidan.
Dan babban falone dake shimfide da turkish carpet brown mai gida gida, ga saitin kujeru manya na daidai rufin asiri masha Allah palon sai kamshin turare yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon datti, Anty moju ne a tsakar falo tanakan dadduma tana sallan axhr, kana ganinta kasan tadan kwana biyu a duniya tanada jiki sosai da manyan maxaunai.
After some mints ta sallame sallan cikeda natsuwa sann ta daga kai ta kalli kafayat data kusan kwantawa kasa agabanta sabida tsabar nuna girmamawa.
A mugun ladabce ta shiga Gaishe ta _o dara irọlẹ_ ma..
Anty mojushola dake murmushi sosai tace _irọlẹ mi darling, iyawo wa iwaju_ (Evening my darling our future bride) tana murmushi sosai tace "kafayat hows ur mother? Fatan tana lpya ?..
Wani irin murmushi kafayat tayi kanta na can kasa tace Alhamdulillahi she is fine maaa _o ṣeun_
Anty moju tace its okay.
_ọlọrun bukun fun ọmọ mi_ (God bless u my child) ure welconme
Tace Ameen oo _o ṣeun_
A dede nan Anty temi ta tarar dasu, nan kafayat ta miƙe tana murmushi sosai ta koma gefenta itama ta rusuna har kasa suka gaisa suka danyi hira awajen lunch kadan kafin nan kafayat tayi xcusing dinsu taje quest room in da kayanta yake tayi sallahn axhr tayi wanka ta sake cancanda kwalliya snn ta sauya wani kayan mai kyau ta dawo kasa.
As usual bata xauna acikinsu ba direct kawai ta wuce kitchen ta shiga kkrin shirya musu wani irin hadadden dinner, she planned to cook igbin chops with yam wanda kafin ma ta fara hada girkin saida ta tsaya ta hada musu wani irin tasty mushy butter crumbs na taɓawa snn ta hado musu da cold and refreshing smoothie takawo musu har cikin falo inda suke xaune suna kallo, anan ma babu wanda bai saka mata Albarka ba, hirar lamarinta da Ahmed suketayi suna tabawa ita kuma tanacan kitchen tana shirya musu abincin dare. anty mojushola tayi tayi akan Ahmed yaxo gidan da daddare ayi dinnern tare dashi amma sunkira wayarsa sau babu adadi basu same sa ba,duka line dinsa a kashe suke tun da rana, kai Har gidansu sun kira amma duk ba a sameshi ba.
Kafayat kuwa tana kitchen tanakan aikinta happly da Farko ta tafasa doyarta ta xuba a wamer, sauran kuma tayi tuwon sakwara da shi shima tasaka shi a wamer na daban,for igbin dinta bata wani bata lokaci ba ta nemo shelled jumbo snails (dodon ƙodi) da scotch bonnet pper, tattasai da albasa da lemon tsami, bay leaf, manja, shrimp powder da seafood bouillon powder
Nan danan Ta hada igbin chops into 2 difrent ways, daya tayi sauce daya tayi stew. Wanda xa'a iya serving dinsu duka da tuwon sakwarn da tafasashen doya.
Bayan ta kammala hada abincin ta hado musu da drinks masu dadi kala kala ta jera komi akan dinning table snn tahaura sama domin yin wanka.
Kafin kace wani abu gida ya cika da yan uwa da jikoki cos Anty ramatou bata tsaya nan ma saida ta gayyaci surkunayen su wanda suke nan a nigeria suka xo da yayansu yin dinner. Anty Nurat itace matar babban yayansu Ahmed, wato brother kaziim AREMU yana da yaransa uku duk maxa, "shehu", "sulu"da "femi". Saidai shi mijin nata yana kasar waje bai dawo ba tukuna.
Sai Anty Adizatu itace matar Brother Hamzat dimeji, yaranta biyu duka mata, medina bolanle da karimat omolara. Brother hamzat Shine mafi kusanci da Ahmed dan haka komi na shirin da akeyi na bikin Ahmed shine yake saka bakinsa aciki kai tsaye.
Sai sistersu xainab moturayo wanda daga ita sai Ahmed din, itama bata nan taje oshogbo inda gidan mijinta yake ita kuma danta dayane dan karami shine shafi'u dake tadan samu matsalar rashin haihuwa.
Anty nurat taxo da Autarta femi, sai Anty Adizat kuma taxo da duka yan matan nata wato Medina da karimat 10 and 13yrs old.
Around 7:30pm lokcin kowa yaci kwaras an hallaro kan dinning table
Kafayat was really feeling like a bride musammn ma dataga matan yayun Ahmed sunxo da yayansu anacin abincinta anata xuba santi already su medina da su femi da karimat sunata kiranta da sunan iyawon Uncle Dami.
Duk dama rashin halattar Ahmed ixuwa wajen dinnern yaso yadan dameta aranta amma soyayyar da familynsa sukata nuna mata awajen ne yyita sassaita mata xuciya.
Itakanta ta nemei shi awaya sau babu adadi amma duka layukansa a kashe. Around 10pm aka kammala hira kowa ya watse.
Nan Kafayat ta koma makwancinta da tunanin hirar tsokananta da sukayi a tsakanin Anty temi da su anty nurat na cewa yakamata su hada ma kafayat da Ahmed grand surprise engagemnt party a gidan. Acikin wasa da dariya sukayi hirar amma da mamakinta sai taji washe gari da safe Anty temi tana sake dago mata da maganan.
A bangaren Ahmed kuwa aikinsa kawai yake kkrin kammalawa da wuri domin ya samu isasshen daman yin tafiyarsa cikin kwnciyar hankli batare da tashin hankli ba. Jiya monday din da sukata kiran layinsa akashe bai dawo gida ba ne, a office dinsa ya kwana yana aiki shiyasa bai kunna wayarsa ba.
Yau Tuesday morning da Asubah ya dawo gidan batare da sanin kowa ba yy wanka ya shirya kansa ya kara ficewa asibitin Dr hassan don ya kammala da can shima...
Gobe Wednesday by 9.am jirginsa xai tashi ixuwa calabar, and he want to beat it on time ixuwa lokacin daxa aci taron ogoja market festival dan anan ne kawai yasan xai iyacin karo da Adiaha.
Jimada family house
Tuesday morning
wajajen karfe tara saura na safiya kafayat ta fito ta kammala musu komi tana kan Goge goge a kitchen sai ga Anty tem ta shigo,hira suka kamayi suna dan raha a tsakanin su, Anty ramatou tafara gaya mata Yadda suke son komi yayu sabida dama sunkirata ne dan su shirya tarban Ahmed a matsayin angonta na next week.
Anty ramotou ta bata 100% tabbaci na cewa komi xai tafi musu daidai sabida aganinsu sati biyun nan kamar gobe ne so babu amfanin jira shiyasa suka kirata kawai domin taxo afara dan shirye shirye...
Idan ana maganan auren nasu Kafayat will be blushing all the way like jinjirin biri. Sai kaga har tana kasa iya haɗe ido da su anty temi a tunaninta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 19