Share this page
kamar zai fito wajen dan tsabar bugu,take sai taji hawaye masu dumi na neman kufce mata a idanunta jin yadda suketa yaren yorubanci atsakaninsu suna mata dariya kadan kadan. Calmy and politely anty adizat ta cirota a mota sunata mata sannu da zuwa jikin adiahar sai rawa yakeyi batace musu komi ba har suka fara tahowa da ita cikin gida. Ahmed ya shiga cikin familynsa yay gaisuwa ya zauna acikinsu kenan Suka fara jin karar gudu anty ramatou ne ta dawo cikin gidan tana ihu da yare bayan ta tabbatar da cewa dagaske ne batun auren nasa. Gaban anty moju ta tsuguna hartana haki muryanta kasa kasa tana cewa _Ahhhhhhh Anty moju jẹ otitọ ooo, jẹ otitọ. Is truee oo is true_ Zumbur anty moju ta mike game da maida hanklinta bakin kofar tana jiran ganin shigowarsu. Ahankli suke tahowa da ita har suka iso ciki. Brother kazim yafara magana da yare yanamai ce masu anty moju suyi controlling emotions dinsu su kama kansu dan kar yarinyar tazo ta rainasu a matsayinsu manya, maganganun daya dingayi ne cikin mita yasaka suka dan daure suka zauna atsomare anty moju tana ta karkada kafarta kmr wacce aka mata mutuwa. Daidai bakin kofa suka saka Adiaha tacire takalmi tay bisimillah aka mata adduoin sann aka shigo da ita cikinsu cikin nitsuwa. Tafiya take kirjinta na tsananta bugawa dan Tsabar kallon da ake mata a palon yasaka tafara jin kafafunta na harhadewa sai wani jiri jiri dataji yana debarta. Hakanan daita daure har saida aka zaunar da ita snn aka dan yaye mata mayafin fuskarta tare da kammala zagawa da ita kan manyan gidan tana tsugunawa kasa tanamai gaishe su snn aka dawo da ita wajen zamanta danta samu nitsuwa. Babu wanda zai iya kushe halittar Adiaha dan kuwa itadin ma Allah ya bata kyaun fuska bazaka dai ce mata tana da muni ba kuma ba ramammiya bace. Tanajin akayi introducing dinta wa family members Din Ahmed daya bayan daya. Anty moju taki sam ta kulasu sosai. Sai jefa musu bakaken maganganu take cikin jimami wanda inba kana jin yarensu bazaka fahimce cewa masifa da bala'in take sauke musu. Acikin salo take kada kafarta tana maganan tanayi tana share hawaye dan gani take hjy khadijatune ta jawo musu wann abun _Emi ko le gbagbọ eyi._ I dont belive dis. _bawo ni o ṣe le ṣe Bello?_ _haaaaaa nitori obinrin ti o yi ẹhin rẹ pada si mi?_ (Haaa, akan mace yau ka juyamin baya?) Kowa sai hkri yake bata ana dada mata bayani akan yanayin situation din amma takijinsu sam sai maganganu take tun Adiaha bata fahimta harta soma ganewa. Anty ramatou ta rirrike ta _bawo ni o ṣe le ṣe itiju mi bi eyi? kini mo ti ṣe lati tọsi eyi lati ọdọ rẹ_ _brother bello, how can u disgrace me like dis? what ive done to dersve dis from u._ _Emi ko ni iye ninu igbesi aye rẹ, Bello_ (baka daukeni da daraja a rayuwarka ba bello). Awajen kusan kowa ya amshi batun auren Ahmed hannu bibbiyu sabida tausayin Adiaha amma bandasu anty mojushola da suke kan kukan cewa dan uwansu bai darajasu ba. Hakanan dai aka yanke hukuncin cewa Adiaha zata zauna agidan tare da hjya khadijatu zuwa gobe da safe idan komi ya lafa su anty moju shola sun sauko sai a saka ranar da za'ay mata waliman kaita sabuwar gida. A dalilin rikicinsu yasaka aka daga tarewar Adiaha da mijinta acikin dakin daya akan harsai sun koma sabuwar gida nan da sati guda. Yau kusan kwana su anty mojushola sukayi suna tsinewa hajy khadijatu a dakin su. Sam kwanansu a gidan nayau tare da Adiahan bai wani musu dadi ba sabida yadda anty moju take daukar komi da zafi zafi. Tunda aka yanke maganan cewa sai bayan kwana bakwai su tare Ahmed yay hamdala aransa dan dama bai shirya tarawa da mace acikin waynn yanayin tashin hanklin ba. Brother hamzat ya miƙa ragamar komi a hannun su anty adizat na batun koyawa Adiaha wasu abubuwan kafin akaita sabon gida. Washe gari da safe aka sake taruwa a falo anata bawa su anty mojushola hakuri Sabida cewa datakeyi an raina ta a matsayinta na babba an dauki matsayin ta an bawa hjy khadijatu. Sosai ta tuma ta dawo da maganan ya dawo wani babba ta daura laifin komi akan hjy khadijatu, tun safe ta tarasu tana ta surutu ran Ahmed saida ya sosu sosai idonshi yy jaaaa jin yadda suke fassara masa uwansa agaban idonsa suna ce mata babbar munafuka. Taruwar dangin suka so suyi mata subiyun sai ga hjy maimunatu tay sallama acikin gidan. Wani sabuwar rikicin ne aka bude dan kuwa nan ne itama tabude musu wuta tace musu bata yadda da rainin wayon nan ba. Haka sukata jefawa junansu baqaqen magana harsuka rusuna sukayi shiru sabida hjya maimunatun babbar mace ce mai izza da kudi gata da matsayi kowa na jin shakkarta awajen sosai. Zuwarta gidan da safen sosai yay amfani wa kowa dan kuwa itace kadai ta tsaya agabansu anty mojushola ta wankesu snn ta ajesu a matsayinsu ta musu tass tass ta rufe musu baki. Tunda tay musu gori akan rashin kulawa da suka nuna akan lamarin Adiaha data baro komi nata tazo cikinsu zaman aure sai basu kara kushe zancen auren ba. Dramar da akeyi aciki har waje ana jinshi dan haka kafayat datayi isowar safiya tazo ta samu ana kan baje kolin maganan auren Ahmed wanda ya doki kahon zuciyar a bazata. Bari jikinta yakeyi sabida babu abunda bataji ba. Harda warware maganan da akayi akace anty ramatou da anty adizat sune zasu shirya Adiaha kafin ranar tarewarta a sashen Ahmed na sabon gida. Adiaha was so down to earth sam batada hayaniya duk kiciniyar da akeyi dinnan saidai tay hawaye tashare wasu abun ma baji takeyi ba. Saiyau da safe da hjy maimunatu tazo ta saita kan kowa snn Adiaha taji dan dama daman zama acikinsu ganin har anty ramatou ta sauko da fushinta tadan amsa gaisuwarta ta fara kulata kadan kadan. Lokcin Kafayat tana daga waje ta jikin windownsu tana jeka ka dawo tanakan jiran wanda zaizo ya gaya mata gaskiyan abunda taji dan she is in shock irin daukewar brain dinan batama san mezatay ba. Tana cikin hakan sai ta hango motar banji yay parking a tsakar gidan. Ta Hanyar baya taga yay ta wawuro cikin sauri tabi ta wajen da niyyar zataje ta tsaresa, ko ina ajikinta rawa yakeyi har ta isa wajen bata cikin hayyacinta. Banji yana dosowa ta wajen saiga Ahmed nan ya fito daga cikin gidan nan ya biyosa ta baya inda babu hayaniya da waya a hannunsa. Cak kafayat ta tsaya tanata kallonsu daga dan nesa. Daga cikin gidan kuwa tunda aka kammala magana sai Kowa ya watse ababbn falonsu aka bar Adiaha da su hjy khadijatu suna masu kare mata kallon tsaf din suma. Har yanzu Adiaha ta kasa sakewa acikinsu dan tsoro takeji aranta sosai. Hjy maimunatu ne tacewa Adiahar akan da taje ta kirawo musu Ahmed suzo tare zata musu magana. Babu musu ta mike tabar wajen suka bita da kallo cikin kyabe baki Hajy maimunatu tacewa yar uwartata " Da dan juma ne da dan jummai, saiki saka mata ido itama karko kyaleta tazo dana nata salon kabilancin dan duk layin iri dayane ya kwasosu. Har Waje Adiaha ta zaga dan batasan inda zata sameshi ba,ahnkli take tafiya tana juye juye har tabiyo wani hanyar daya kawota waje Lkcin Magana Ahmed sukeyi shida abokinsa banji wanda bama jinsu kafayat takeyi ba, sai data matso kurkusa takejin yadda banji yake tambayarsa lpyar matarsa da yadda family suka amsheta, tun bai amsa Banji ba, kafayat ta katsesu, a mugun haukace ta karaso wajensu tanamai shigewa tsakiyarsu kamr wata tababbiya wanda ta rasa hanklinta shekaru tamanin da suka shude. Awargaje ta tsaya tana kallon cikin idanun Ahmed, nan take hawaye masu dumi suka wanke mata fuskarta then She decided to confront him akan abunda takeji akan zancen aurensa, muryanta na rawa zosai tace Ahmed wai dagaske ne kayi aure?...daidai fitowar Adiaha kenan sai ta tsaya agefe tanata kallonsu ...kafayat ta memeta masa tambayar ajere yakai sau biyar.. sosai Banji yaji tsoron yadda kafayat din take ɓari kar kar kar idanunta suka jujjuya sukayi jajir duk yadda taso tay control kanta ta kasa tafara masa tambayar acikin ihu da kuka mai ragwabarwa. Yadda kasan baisan me takeyi ba hakanan ya kalleta a kiyasce cikin bata wani irin cold attitudes mai bala'in kufularwa zaka rantse da Allah Ahmed baida imani ne acikin zuciyarsa. Wani irrin balamin gurnani kafayat taja wanda yasaka Banji ya sulale sidif sidif ya barsu wajen. Tafara masa raki cikin birkicewa tanakan tambayarsa akan meyasa zai yaudareta har yaje yay aure? Wacece ya aura? Yar waye a kasar nan?snn Dame ta fita? Yace mata ra'ayinshi ne yasaka yay aure, and he wont explain himself to her. Kafayat tafarajin kamr ta shakureshi awajen ta kaishi har lahira, inzai wuce saita birkita tasha gabansa, ran Adiaha sosai ya sosu datagan su a hakan,dan ba laifi ta fahimce cewa da alaman wnn din budurwan Ahmed ne koda ba agaya mata ba, yadda suke hargagin rikicin zaka gane cewa sun dade suna tare, a birkice kafayat take tambayarsa ko sonta ne bayayi yaje ya auro wata ba ita ba. "Tafara tuna masa irin dadewar datay tana dakon sonshi, da irin burikan data daura akansu. Rikici mai yawa ta balle masa dashi Har saida ta hatsala shi yace mata "baice mata baisonta , haryau yana sonta,She is his first love, kawai Allah ne baiyi ita zai aura ba. Numfashinta taji yana shirin daukewa cak dahar zata fadi kasa yay sauri ya tarota ya rungumota jikinshi, tafara masa bori sosai,sai kuka kawai takeyi ajikinshin ta wani tantameshi tammm jikinta na rawa rawa anashi jikin sosai, cikin yanayin tallafota jikinshi yace mata ta fahimce shi snn tay hakuri shima ba hakan ya tsara ba amma hakan Allah yay auransa da yarinyar qaddararsu ce ya jawo. Adiaha sai taji kishi mai yawa ya dabaibayeta musmmn ma dataji ahmed yace auransu na qaddara ne kuma yana son kafayat Hawayen da ya soma gangaro mata ne tashare da sauri taje ta buya awani bayan pillar dan kar aganta awajen. Ahmed yana barin wajen kafayat ta juya itama zata bi bayanshi,tana sauri zata wuce suka hade ido da adiaha nan suka tsaya jefawa juna kallon kallon batareda sunsan junansu ba. Duk jikinsu ya basu matsayinsu amma basucewa juna uffan ba kowa ya kama gabansa. Bayan yar nasihar da hajy maimunatu tay musu da Ahmed sai tay musu sallama akan cewa zataje gidanta dake katsina tay sati biyu kafin nan ta koma turkey dan su shirya dawowarsu nigeria gabaki daya nan da wasu kwanaki Tay musu nasihan zaman aure snn Tasaka musu albarka amma hanklin Adiaha baiyaji jikinta sabida tunowa da maganganu da kuma rungumar da kafayat din datagani sunayi tare da Ahmed dazu ya tsaya mata a wuyanta sosai. Hjy khadijatu tay musu sallama agidan itama nan suka fito tare ta raka yar uwanta har cikin mota, ta fito zata shige nata motar kenan sai ta hango Kafayat atacan baya tana tahowa a tsandare tana bari bari kamar wancce ruwa ya kwashota. Kallo daya tay mata ta fahimce cewa she is in shock na jin batun labarin auren Ahmed. Bakinta dauke da salati tazo ta rukota tana tabata kuwa ta sume mata a hannu. A motarta ta sakata suka bar gidan takaita asibiti saida ta farfado snn ta dawo da ita gidanta inda babu hayaniyar kowa. Haka ta dinga rarrashin kafayat tanamai bata hakuri, kafayat tay kuka harta dena, hjy khadija babu abunda bata gaya mata dan zucyarta yay sanyi ba. Itace ta bata labarin Adiaha da dalilin daya saka suka amince suka bar Ahmed din ya aureta, Karshe dai kafayat tace mata ta fahimce qaddara ne ya kawo Adiaha rayuwar Ahmed tace zata bukaci lokcin da zatay tunani akai domin ta samu nitsuwa akan hakan sosai. Har gida hjy khadijatu ta rako kafayat har cikin gidansu snn tazauna da ita nadan wani lokci ta dinga lallashinta tamkar yadda uwa zatay wa yarta na cikinta harsaida kafayat din dankanta ta fara nuna mata babu komi ta fahimce komi. In 7 days time za'a koma sabuwar gida tare da sabuwar amaryan Ahmed kowa na shiryawa wann ranar. Ahmed tuni ya koma bakin aikinsa.. Anan family house aka aje Adiaha,kowa yasan kan labarinta shiyasa daga ta zauna su anty mojushola saisuyita zaginta da yarensu suna kiranta matsayaciya yar ciranin arziki. Idan suna son cimata fuska sai suyi ta mata tambaya akan gayan gara ko akwatin aure ko suta zakwalo mata zancen iyayenta wanda azahiri yana sakata jin wani iri aranta sosai. Ga ahmed ya fara focusing akan aikinsa sosai sai baida lokacin zuwa dubata wani binma saida dare zaizo gidan inyazo ma baiya dadewa saiya koma gidan iyayensa dan bayason gulman su anty moju. Kafayat was going tru a mental depression duk dama kowa yana kkri akanta amma mahafiyarta taki bari suna zuwa ko suna kiran yarta awaya. Ahakan ta samu babban damar cusawa yarta ra'ayin plan dinsu. Ana saura kwana biyar a koma sabuwar gida jikin kafayat din haryau babu kanta, sosai hjy khadijatu ta damu, kusan kowani lokci takan mata aika dan taji lpyarta a boye, acikin daren kwana na biyar din ne hajy fatihat ta tasheta a barci takaita cikin jeji da tsakar dare suka yi wani ritual na musamman akan Adiaha( refer to prologue to read this part in detail) Bayan dawowarsu ne washe gari anty moju shola da anty ramatou suka fara fita suna yawo ixuwa wajajen da babu wanda yasan inda suke zuwa sai Allahnsu. Hkama aka kasa ganewa kan alhj bello jimada agidan kwana biyu sam baya walwala sosai sabida yawan kiranshi meeting da sukeyi a boye suna tattaunawa da shi Kwana biyu akaji sakat gidan yay shiru dasu anty moju suka dawo basa zama agida sosai, Nan kuwa Adiaha harta fara sabawa da zama da su anty adizat dake suna koya mata sallah da dabiarsu na al'adansu sosai musammn ma gaisuwa ladabi da yadda suke girki idan hidima ya taso ko idan akayi baki. Ranar da aka cika kwana bakwai ranar komawarsu new jimada mansion ranarne kowa acikinsu ya cancada ado aka ma Adiaha rufi mai kyau da kayan amare na alfarma da hjy maimunatu ta aiko mata da su kyauta,yau kowa saida yamugun shan mamakin irin gayun da sun anty mojushola sukayi. Da yamma lisss bayan duk an hallara, aka nemi alhaj bello aka rasa kwata kwata. Haka nan har aka debi motoci daga gida aka fara sako amaryan ahmed agaba za'a koma sabon gida da ita. Sun shiga gidan kenan har anyi addu'oi kowa ya wuce sabuwar sashen jim kadan saiga hayaniya da gangamin mata ana kida ana rawada yaren yorubanci, na musammn aka debo mawakar shela mata na yarobawa suka rako sabuwar amarya cikin sabuwar gidan jimada. Su anty mojushola ne agaba sun riko hannayen kafayat dayaji lalle an bata tsamiya da goro tanaci tana kumsa yawun abakinta tana tofarwa ana binta da kida ana mata wakoki masu dauke da habaice habaice masu zafi sosai. Wakokin da suke yi a tsakar gidan suna rawa suna shewa saida yasaka Kowa ya fito a sashensa acikin gaggawa kowa ya tsaya yana kallonsu. Tun hajiya khadijatu bata kammala isowa filin ba tafarajin rade raden cewa mijinta ne ya kara aure. Tana kuwa fitowa sarari tazo ta samu su anty moju da anty ramoutu tare da hajy fatihat da kawayenta na kasuwanci suna wani irin rawa suna karkada duwaiwakansu kafayat na tsakiyarsu tana taunar goro da tsamiya tana zubda yawu wanda hakan wani alamane na habaici da cin fuska da akewa uwargida na nuna mata cewa ita ta tsufa, dan haka ankawo fertile young woman wanda zatazo ta haihu da mijinta agidan. Haka suka cika mata gaban site dinta har ta inda take tsaye kafayat na tsakiyarsu idanunta a bushe tana rawar itama. Daukewar cak hjy khadijatu tay tanamai kallon ikon Allah. Wani doguwar capert suka shimfida akasa inda kafayat zata bi ta shiga gidan mijinta wato alhaj bello jimada kowani step tay sai anzuba wani irin ruwa a gora anyi habaici tare da addua kafin nan ta karaso. Hjy khadijatu data tabbata da cewa wai kafayat ne ta aure mata mijinta sai tay na maza ta juya abunta zata koma ciki saidai shock din ya riga dayay mata yawa ko wani nisa batayi ba jiri ya kwasheta tafadi ajikin danta Ahmed dayay sauri wajen rikota jikinshi. Agurguje ya karasa shiga da ita ciki dan shima shigowarsa gidan kenan jikinshi a ragwabe Bayan sunji labari awaje cewa mahaifinsu ne ya auri budurwan dansa kafayat yau a masallaci. Nan brother hamzat da su anty adizat suka yo kansu suka tayashi rike mahaifiyarsan jin har ta dena numfashi sukayi sauri suka sakata a mota hankli tashe suka wuce asibiti da ita batare da sun kula kowa ba. Hanklin Brother kazim ya mugun tashi sabida kukan da matarsa anty adizat takeyi data kirawoshi awaya abirkice tana gaya masa abunda yake faruwa musu agida, tun daga nan yay dialing lambar mahaifinsu yanata kirar wayarsa danya tabbatar amma baya daukar kiran. Jininshi har tafasa yakeyi yana diri shikadai Ji yake kamar ya bace yaga kansa a nigeria acikin dare Dayaji wai kafayat ce mahaifinsu ya aura... A rikice Anty nurat da Adiaha suka fito zasu bi bayansu,lokcin anty nurat taje dauko key din motar ta kenan Adiaha taji an riko hannunta an wani matseta da karfin tsiya. juyawarta keda wuya suka hade ido da kafayat da tay wani irin mugun hade rai tanai mata irin shakurarren kallo mai cike da baqar kishi da tsananin tsana. Sanda tay mata zagin kare dangi da yarensu snn ta zungureta tace mata "su zuba su gani, "yau tay maganin Ahmed saura ita, ynzu ne wasan zai fara atsakaninsu dan ita ba zaman aurene ya kawo ta ba"..tazo ne dan ta kwace Ahmed dinta kmr yadda taje ta kwace mata shi agarinsu, Tace tay mata alkwarin cewa saita kwaceshi agaban idonta tana kallon komi babu yadda ta iyayi.. Da wani irin kallon mamaki Adiahan take binta dashi taja tsaki mai zafi aranta tace mata "ga fili ga doki. Itama kallonta take ranta sai cewa takey Indai har bata samu Ahmed ba alkwari tay cewa babu wata ƴa macen da zata zauna lpya tare dashi hr Abada...... Galala Adiaha ta tsaya tanata kallonta harta juya cikin sauri bar wajen ta koma cikin yan kawo amarya ganin anty nurat tana dawowa kallonsu takeyi har suka bar gidan. Tun ahanyar asibitin Adiaha ta buga tagumi tay shiru kmr wacce akamata mutuwa dan babu abunda yake nanatuwa a kwakwlarta face maganganun kafayat na cewa zata kwace mata Ahmed dinta... ALHAMDULLHI... DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA ACIKIN LABARIN AHMED BELLO JIMADA DA MATARSA ADIAHA DA KUMA MATAR UBANSA KAFAYAT. DA KUMA YAR UWARSA YASRA HUSSAIN YARINYA YAR SHEKARU SHA TAKWAS DA ZATA ZO TA KASANCE WATA SABUWA ACIKIN SHAFIN QADDARAR RAYUWARSU DASHI DA MATARSA ADIAHA.. KISHIYAR KABILA IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF HATE TURN INTO ROMANCE KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA* *VIA 0152983148* *MOHD SULE SURAYYA GTB* EVIDENCE TO *08060712446* MTN CARD SEND ONLY PIN OR PICTURE TO *080607124476* OR TRANSFER VTU TRU *09132352275* ©SURAYYAHMS2023. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19