Share this page
min auren dole ko? Ajiyr xcya tay snn tace "Toh ai kai ka ja ma kan ka Ahmed,tun yaushe nake binka ka kawo mata amma kana ta wasa kana kakkaucewa duk ka maida mu duka yan yara" komawa yyi ya kwanta baice mata komai ba Sarai tasan halin dan nata da abun da ke iya faruwa in yafara yin shiru shiru musmmn in yana cikin tashin hankalin nan da yake ciki, hakn yasa tace "toh ai sai ka kwantar da hankalinka my son,na shawo mana kan Baban naka amma fa da kyar, Nan da nan Ahmed ya miƙe xaune yana sauke ajiyar xucya xaiyi magana kenan ta tsare shi tanamai cewa Ka saurareni da kyau kaji yace min dai ya baka 2 weeks din da kace don haka kafin lkcn saikay kkri karkaban kunya ka gabato matar aure indai kana da niyya, kasan ni bana son abinda xai taba min kai ko? Pls Ahmed dont cause any trouble for me again..bana son na sake shiga damuwar dangin uban nan naka.. Kasani sarai baya tsallake maganan Elder sisternsa Anty mojushola she is very fragile in har xata girme baban ku ma baxai fi da shakaru uku xuwa hudu ba,amma kamar wata uwarsu data mutu haka dukansu suke daukarta kuma sukejin maganarta basa son bacin ranta sam. mikewa Ahmed yyi ya rungume mahaifyr tasa cike da jin ddi ya shiga mata godiya sosai yana lallabata yanamai bata hkri akan fushin dayake sakata aciki,sosai zake son Ahmed dan shine mata danta kwalli daya a duniya tasan dai ba sake wani haihuwar xatayi da shekaruntan nan ba. Ahankli sosai ta shiga shafa kansa tana dan masa murmushi har ta saka masa albarka snn ta mike yyi mata godiya ta fita xuwa falo wajen xainap da danta danta debe musu kewa wanda ajiya da darene sukaxo musu xiyara suka kwana tasan hala xuwa anjima xata wuce ta koma gidan mijinta. Kasa xama Ahmed yyi duk dama hankalinsa ya dan kwanta da aka bashi sati biyu sai dai yanxu damuwarsa dayace ta inda xai shiga ya fara nemo matar da xai gabato ma parent dinsa in 2 weeks witou a failure dan harga Allah aranshi baison ya kuma batawa mahaifyarsa ranta. Xagaye yake ya kasa xama ya rasa ta ina xaifara wnn jan aikin wanda iya tunanin hkn na mugun tada masa hankali da kyar ya nitsu snn yay wanka ya shirya ya fito sanye casual wears wandonshi baki yasaka farar polo short akai da face cap ya wuce gidan banji domin ya samu cikakken nitsuwa. Gudu sosai yake dan haka Tukin kamr minti 20 ne yakaisa har duplex flat din banji dake street din gwarimpa. Horn yy abakin gate mai gadi yaxo ya bude mai gate din ya shiga kai tsaye ya wuce cikin dan madaidaicin duplex flat din mai 3 bedroom dan dede haka dashi mai kyau sosai. Sau biyu yy knck sai yaji alaman kofar kamar a bude da mamaki a fuskar sa ya tura kofar ya shigo ciki dan yasan mutumin nasa bai barin kofarsa a bude haka nan musammn ma idan budurwan sa tana tare da shi. Tun da ya shigo yy sallama ya tsaya shibai kara gaba ba baiyi baya ba, hadadden falo ne wanda yaji set of sleek sky blue sofas komina wajen dan dede a typical bachelors setting. Banji yana kitchen yaji kamr motsin mutum saiya wanke hannun sa a sink ya goge da hand towl sann ya fito Tun Daga can nesa wajen kofar kitchen ya hango sa a tsaye, Da murmushi akan fusknsa ya karaso sukayi musabaha.. Banji yahau tsokanarsa yana cewa Kaga Angon anytime...hmm ure actually looking like a groom..ko kulasa Ahmed baiyi ba yaja tsaki.."i quest ur girlfriend is not here right? Banji yace "yes, "sartuday is for wedings. Daxu ta shirya Taje bikin wata colleques dinta na office, tun ma bai karasa xancen ba Ahmed yy rau da ido yace "Ahh thank god dan bason shegen gulman ta nakeyi ba, finally der is space for some more fresh air abeg!..banji yy murmushi baice komi ba Ahmed xai xauna kenan yace"guy muje kitchen mana Ina dan dafa abinci ne..i'am famished. Ko kai bakajin yunwa? Ahmed ya kallesa sama da kasa cikin basarwa ni Nay maka kama Da wanda xai shiga kitchen ne?... banji yace why not, ohh har wani kama muke dashi mudake muke shiga? Yace "Eh, man,nikam dai ina ɗa namiji lafiyayye kuma kyakkawa dani, nayi wanka na ina baxa kamshin turare,Allah ya sawwake min in shiga cikin kitchen wann ai aikin mata ne..waima me kake kwabawa awajen ne? Banji yana murmushi yace Toh ina ruwanka tunda kace aikin mata ne? See is not about a woman or man..learning how to enter kitchen to help clearly shows how responsble u can be to ur wife and future family. Ahmed ya masa wani irin matsiyacin kallo yace toh naji..go and get someting for me to drink..amma nikam baxanci abincin namiji irinka ba. Dariya sosai banji yayi yace makaryaci sau nawa kana ci? Sha u knw ur way, i am not going to serve u drinks..ka tashi kaje ka dauko drink din dakanka. A kasale sosai ya mike yana mita..mutum ma yaxo gidanka baxai huta ba? sai shegen son saka mutum aiki..yana tafiya yana tsaki mtsss, ahaka dai yaje gaban fridge din ya bude yanata kalle kallen abubuwanda ke ciki yanadan kyabe baki gani yy kusan komi dake ciki ya kusa karewa can yasaka hannu ya dauki cold coffe drink, da har xai xauna a falon sai ya fasa yabi bayan abokin nasa kitchen din da drink dinsa a hannu. Ahankli ya tura kofar ya shigo lokcin Banji yana kan gauraya wata arniyar greenish spagheti jollof dataji asalin manyan kifin sardines da vegies qamshin abinci ya game gauraye ko ina.. Kallonsa Ahmed yake yana ta shan mamakin yadda akayi banji ya mugun kwarewa a dafa abinci, bakaramin dadi qamshin abinci yy masa ba, take yaji cikinsa ta amsa, sai ynxu yake tuna cewa ashe shima baici komi agida ba. But he can neva cook like dat, dan Allah ma yasani wan aikin mata ne bana shi ba, Banji na famar gauraya abincin sa hadiyan yawun ahmed yasakashi ya juyo ta bakin kofa suna haɗe ido waje guda Ahmed ya wani tsime kamr baisan me yakeyi ba, girgixa kai Banji yy yana murmushi. "Mr Neat guy, How far? Meya kawoka kitchen kuma kohar ka dawo mace ne? Cikin shan qamshi mai ban dariya ya karaso da drink dinsa a hannu yace "nop..i need a fancy glass cup for my drink.."Banji ya fashe da dariya mai sanyi baice komi ba nan ya masa nuni da safe cupborad da hannu,a hakan ma saida yyita saibi kafin nan ya hkra ya saka hannu ya dauko wani glass cup mai shegen kyau wanda ko amfani dashi basu tabayi ba,yana cirowa kuwa karamin insect wanda ake cewa yan matan kaduna har guda biyu sukabiyo hannun sa a mugun firgice ya sake cup din akasa tay kara tassssss...Banji ya saka ihu "Ahhhhhhhhh Ahmed warris dis now? Kaxo ne dan ka fasa min komi da komi a gidana, dont u know dat this glass cup belong to my girlfriend hidaya..yanxu intaxo me xance mata. kirar sunan hidaya da banji yy sai ya mugun bawa Ahmed takaici a mugun masife yace "karka ce mata komi ka bata bayanka ta bugeka kawai, nonsense..toh saime dan ya fashe?arnt glasses meant to break? Banji yace malam dakata "Glasses can break mana amma ba ta hanyar ganganci ba, Ahmed da sannunka fa ka sake glass din nan a kasa...dats carelessness my friend Yana rufe baki Ahmed Ya hararesa Yace "eh To na sake din..Next time bani xaka kira careless ba kafara ma budurwan ka lectures akan tsafta tukuna, toh in banda kaxanta kullum tana gidan nan amma sai insect suna yawo akan kofin shan ruwan mutane? No wonder ure alwys purging..kullum acikin toilet kana xuba kashi mai wari sabida virusses din dakake ci haaaaaaaaa what level of untidieness is dis Banji ya rasa me xaice masa ya tsaya yanata kallonsa. Sai can yace toh shikenan saika dauko tsintsiya da parker ka kwashe broken pieces din kakai dustbin tunda kai kana da tsafta.. Sadaf sadaf Ahmed ya tsallake kan glass din ya koma gefe snn yace no way. Ajirata dai ta dawo taxo ta kwashe takai bola..ni ban iya shara bama..wnn aikin mata ne nd since u have one agidanka ai sai ajira taxo tayi aikinta..nikam i cant. Banji ya dafe kansa agajiye yace Ohhhh Allah na, Ahmed bello waime ka dauke mata ne?Marasa daraja, 'Bayi? Yace oh Ni bance maka haka ba. Banji ya kashe gas snn ya juyo yanata kallonsa yace dami u really have to change ur mindset about women. yadda ka dauke mata ba haka suke ba, women are special human beings ka dai gyara tunaninka akansu. Baikulashi ba ya bude drink dinsa yafara sha ahaka, saida yaji sanyi aransa snn yace Akan me? daga cewa budurwanka batada tsafta shikenan yadawo mindset issure. Ahmed ba haka bane, Ina magana ne akan aikin gida,dafa abinci, wanke wanke, gyaran gado, shirya yara ba aikin wani gender bane, is simply a shared responsibilty musammn ma awajen ma'aurata. Bana son kaje ka shiga hidiman aure kana cewa ehhh kayi wanka kay kyau baxaka shiga kitchen ba, or u cant sweep cos ure not a woman whats dat? Ahmed yy rau rau da ido Waidan naxo tayaka girkin shine xaka haumin wa'axi? .. Banji yace Amma ai cewa kayi kaxo daukar cup.. jokingly yace ohh did i said dat? Dariya banji ya fashe dashi __ure egba asiewere ni ore_ mahaukaci kawai Allah dai ya shiryamin kai. Ahmed yafara dariya yace ameen amma ba hakan ne yasaka ya share floor din ba, yana tsaye banji ya gama serving dinsu abincin,sai shi ya dauki plate din abincin da fork guda biyu yakai musu har falo Banji kuma ya share kitchen dinsa ya tattara ko ina yy tsaf snn ya fito ya same shi har ya dau fork yy bismillah yakai abincin bakinsa yana ci hankli kwance. Murmushi kawai yy yaje ya dauko musu ruwan sanyi snn ya xauna shima suka cigaba da ci, can yaga Ahmed duk yafishi cin abincin. Da kamar xai tsokane sa sai ya fasa yace guy ya ake cikine da maganan mu ka gama yin shawarar ne? Cos I have a girl on my mind wanda xata iya mana abunda muke so na contract marriage. Fadan hakan da banji yy yasaka Ahmed aje fork din nasa akan plate din ahankli sakamakon tunowa da yy da abunda ya faru da shi a gidansu daxu. Wani nannauyar ajiyar xuciya ya sauke ya dauke wipes ya goge gefen bakinsa snn ya sha ruwan sanyi ya dan samu nitsuwa kadan" ido kawai banji ya xuba masa ganin inda yanayinsa ya sauya gabaki daya atake.. Xai kara shan ruwan banji ya tsare sa da ido yace "Ahmed what is wrong?..wani abu ya faru dakaine?... Ahnkli ya kurbi ruwa, snn ya lumshe idonsa ahanlki yace "baba yace in 2 weeks banji. Baki bude Banji yace "2 weeks? Whats dat? Lumshashun idanunsa ya buɗe yana kallon sa idanunsa sun sauya sunyi wani iri kalar tausaiy snn yace Dad yace na kawo mata in 2 weeks ko ya auramin kafayat.. im just sooo confused. Kafadun sa banji ya dafa ahnkli snn yace cmon men, dont break down over dis small issure..toh meye ne abun damuwa aciki naga dai kafayat din nan tun muna kanana ake tare. And she loves u alot tun muna yara, kai kanka kasani..toh meyene matsalar Ahmed? Dama can ba itace matar naka ba? Kun dade fa kuna tare.. Agajiye ahmed Yace baxaka gane bane Banji, bawai bansan kafayat tana sona bane, and i liked her tooo, okay? A tunanin ka akwai wata ya mace dana sake mata fuska sosai kamar kafayar din ne? Banji yace "Okay just say u love her, admit it...kafada mata mana Ahmed sai kowa ma ya huta. Yace "In gaya mata me? Nine ma xance ina sonta ita meya hanata ta fito fili ta gayamin? Lallai kai mahaukaci ne.. Banji yace, Akan me?sau nawa kafayat tana fada maka? Wai shin mutuwa xakayi inka fada mata kaidin?.. Ahmed Yace baxan mutu ba, infact Ko ciwon kai baxanyi ba, I like her alot, she is fun, she is trustworthy, tana da dukan abunda mata ke tinkaho dashi amma gaskiya baxan iya ce mata i love her hakan nan kawai ba. I just like her, she is cool, and i think she knows dat. Oh cmon Ahmed, haba! Meyasa kake tsaurara wann lamarin? Kaine fa kasaka komi ya xamo a rikice..just u say u love her, u want to marry her, cos ders no perfect woman in this world Yace I know banji, nasani, but i hate alot of things about kafayat, xaman aure da ita inda ace xallan maganan in nuna mata kulawa itama ta nunamin ne baxai mana wahala ba,.amma ai xaman aure ya wuce haka banji, kafayat tana da baki sosai, gulma ajininta yake,and she sabi over do things yadda kasan mayya.. ..wallh yadda take nunamin too much obsession shi yasaka na kasa iya jincewa ina sonta araina, haryau bana jin kmr ina sontan dagaske, cos she is stalking me..kullum acikin nuna kanta take a matsayin matata ta, and i haaaaattttte it..and not only dat kafayat tasan komi da komi akan rayuwa na dana iyaye na dana family na. Har can wajen su anty tems da anty moju take xuwa tana musu bauta..she is making her self too cheap for my liking... Wani ajiyar xucya ya sauke snn ya cigaba da cewa "Banji, bana son na xo na auri kafayat taxo gidana ta samu waje ta rinka kunna mana series of gulma da munafurci a gidan mu, wallh she knw all my weaknesses, she can easily blackmail me, kartaxo tana cutar dani, and mind u family na gabaki daya bayanta xasu bi sabida ta riga ta gama dasu tun ynxu. Bansan ko kana fahintar mene ka fada ba, i dont knw but im so scared of maryying kafayat even thou i liked her..ynxu dan Allah mene laifi na aciki dan nayi wann tunanin banji? Banda ikon da xan protecting rayuwata na nan gaba ne?..i need a wife i can control and dat girl is not kafayat shiyasa bana son na aureta duk dama ita din daice nafi shakuwa da ita .. Ahankli banji ya tayashi rike hannunsa suka sauke kasa atare Dan tunda ya soma wnn maganan hannunshi da jikin shi da muryanshi duk gabaki daya rawa sukeyi tsabar abun yana damunshi aranshi sosai . sai yanxu banji yadan fara fahimtar nasa point of view din,even more than ever, Atleast yau Ahmed yy making small sense, all he said can be true duk dama babu wani dan adam wanda yasan gaibu sai Allah, Cikin muryan lallami yace "Damilare pls, calm down now Ahh ahhh. pls take a breath..aina fahimce ka ynxu.. Ahmed baice komi ba yadan jingina bayansa da kujera yay shiru sosai yanamai kame nunfashin sa...sai can cikin sanyin murya sosai yace "hmm nifa kowa laifi yaka kalla, and funy thing is dat no body want to understand me. Wallh aurena da kafayat din nan Da akwai matsala, gashi ko kunya bata da, badama taxo dakina tana son na taba mata nono, nifa baxan iya auren mace irin kafayat ba gani nake kamr ma tafi karfina. Banji yace A'a kar kace haka mana. Lets just find a tangible solution bamu da lokci dan Sati biyu fa kamar yau da gobe ne kuma kasan halin baban ka sarai bayason rainin hankli. Ahmed yace ni ai a shirye nake amma dai duk wani solution din da xamu nema kar asako kafayat cos she cannot be my option... Banji yace "she have to be. Bari dai mu aje ta a last option din mu ynx muyi maganan contract marriage din, ina fatan ka kammala shawara akai. Ahmed yace "nagama shawara na akai.. ina ga kawai abar maganan nan kawai. Kai tsaye yace "I am not intrested in it. Ajyar xuciy banji ya sauke batare da wata jayayya ko musu ba yace its okay,dats fine nasan kana da dalilinka. So who do u have in mind now? Shiru Ahmed yy cikin naxari baice komi ba har na kusan na tsawon minti biyar daya sauke nannauyar ajiyar xuciya. Banji ya kalle sa yace "ehen, ina jiranka, did u ave anyone in mind? cikin Lumshe ido da budewa ahankli ahmed yace "Yes... QUESTIONS OF THE DAY🔥 👉🏿 *I WILL DEDICATE NEXT PAGE MA WANDA YA BADA AMSOSHI GAMSSASHU.08060712446 save my number and dm ur coments idan bana kusa dakai🔥* *Q1- SHIN KUNA GANIN DAIDAI NE IYAYE SU TAKURA WA YAYANSU SUYI AURE AT A CERTAIN AGE OR TIME KAMAR YADDA AKEYI WA AHMED?* *SHIN RA'AYIN AHMED GAMEDA MATA DAYACE SHI YAFISON WANDA XATA SO SHI FIYEDA YADDA YAKE SON TA DAIDAI NE?* *A MATSAYINKI NA ƳA MACE XAKI IYA AUREN NAMIJI MAI IRIN RA'AYIN AHMED?* FOLLOW SURAYYAHMS ON WHATSAPP *08060712446* SAVE IT AND HI UR COMENTS, SHARE AND FOLLOW SURAYYAHMS ON WATTPAD. [5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH..5* By surayyahms. *OYA SHOUT OUT TO THE COMENTS/RESPONSE OF👇🏻 NAGODE🥰* *Mrs beatrice, balkisu suleiman, zara gambo, Maryam umar matusgi, najiba ibrahim danjalele, mmn aysha,zahraAhmed, M2, Danzaki,oum noor, hadiza salmanu,nameske surayya,mum taheer,Dr halima maude,zahra, manyaro,mamn munirat, vivacious,khadijamalan,mamn arfat,aysha imran muhd,beenat,mom iyad, anty mimi, maymuna.* murmushi mai sanyi Banji ya sakar masa snn yace wacece yarinyar?Ahmed ya dan bude lumsheshan idanunshi ahankli fuskarshi kamar na wanda yake cikin naxari da kokonto sai can kuma yace itace yarinyar Dana fada maka ranar..the girl i met in south east.. Baki bude Banji yace ohhhh ohhh so u mean yarinyar nan ce na can cross river i mean ur calabar tribe girl right? Yace eh ita.. Banji yace okay good, But are u sure about her? Babu tantama Ahmed Yace yeah am Sure. 100%. "Kuma ka tabbata iyayenka da nata iyayen baxasu kawo muku wani matsala akan maganan auren naku ba, Kasan sometimes yoruba family basu fiye son hada xuria da tribes from igbo regions ba and like wise igbo. Ahmed Yace Banji ka mance da duk wann shirmen tribalism din nifa nayi tunani sosai akai, and i know im soo desperate right now amma my decision about marrying her is not just out of a blue,nasan ita kadai ce dai xan iya aura naji kaina so safe and secured aynxu,besides the girl loves me more than anything, kuma nasan xata iyayin komi akai na,nide so kawai nake ka taimaka min, baxan iyayin abun nan nikadai ba, stay by my side har inje in sameta mudedeta,inyaso inta amince kawai itadin ce xan aura Ko da baxata canja addininta ba it wll be fine by me. And then na tabbata iyaye na xasu so ta even fiye da yadda suke son kafayat sabida sosai adiahar nan take da tarbiya da hankli, infact she is too sweet and good and she can cook very well too. Banji yace hmmm u seems too sure akan babe din nan, to Allah sai yasa itace mafi alheri agare ka, is okay. i will alwys support u,yanxu menene plan dinka? Gyara xama ahmed yy cikin nitsuwa yace ina tunanin na shirya naje garin sun ne in sameta muyi magana mu fahimce juna shikenan.. cikin datsar numfashinsa Banji yace yanxu Xaka je kace mata kana sonta ke nan ko ya?... A dakile Ahmed yace "what? So kuma? No pls cos Dats weird,ni baxan iya ce mata ina sonta ba dan bansan ko ina asalin son tan ba..kawai xanje ne in tambyeta ko xata aureni. U knw her consent is important for this union right?... Banji yes, and love too, Aure fa xakuyi Ahmed, kai kanka baxaka so ace love and affection din ya tsaya ata bangare daya ba. Ahmed yace karka damu dat wunt happen banji, i do care about her am sure shiyasa ma haryau kaga ban mance da ita ba. Nasan idan mukayi auren nan ma xata gode min,and she will be fine with me cos dats wat she alwys wanted. kallon sa banji yaketayi baice masa komi ba dan harga baisan mexai kara cewa ahmed akan yadda yake daukar mata aransa ba. Memeta maganan Ahmed din kawai yaketa yi a mind dinsa musammn ma inda yace wai "Inna aureta xata gode min cos dats what she alwys wanted? So Ahmed thinks he is doing her a favour by marrying her duk da shi din ma ya gudu ne wa trap din auren budurwansa kafayat dan sabida ya kare kanshi daga shiga taskon soyyarsu da yake tafiya a speed daban daban da kuma depressed marriage.. Yasan wann lamari dai nasa da akwai son kai da son xuciya aciki amma badai xai yanke hukunci ba tunda bai taɓa haduwa da adiaha din ba Karyaxo yay kkrin hana faruwar auren kuma ya cutar da ita batare da sanin sa ba,. Tuna haka aransa yasa kawai ya share maganan suka cigaba da harhada plans din su na maganan tafiyar Ahmed cross river, calabar domin samu consent din Adiaha!. Base on Poster din ogoja market festival dayagani ranan akan titi abakin shagon wani inyamuri suka shirya schedule na ranar tafiyar, sede Ahmed bai yarje ma Banji ya bishi har can ba, yace masa ya xauna kawai a Abuja sabida baison wani abu ya faru kuma iyayen sa suxo suyi suspecting na cewa tare suka hada plan din dan haka komin su a sirrance suke son suyi shi batare da sanin kowa ba. Yace In yaso in aka ci nasara akai toh shikenan sai a sako maganan auren nasu kowa yaji amma idan ba'aci nasara ba kuma shikenan bama sai kowa yasani ba. Acikin kankanin lokaci suka hade good plan na yadda abun xai kasance. Yau ranar sartuday snn kasuwar ogoja da ekpo festival xai fara ne on wednesday Dan haka xuwa monday wato jibi Ahmed xaibi jirgi yaje calabar yafara neman information akan Adiaha. Bayan sun kallama tattaunawa akan hakan suka dan yi kallon ball kafin nan aka kira sallah xuhr sukayi alwala tare suka wuce masjid suka gabatar. Dawowarsa keda wuya kowa ya nemi waje ya kwanta suka soma kwashar bacci, basuda farkawa ba sai wajajen 4 pm lokcin asr, atakaice dai yau gabaki daya agidan banji Ahmed ya wuni Sai can wajen after five snn yabar gidan lkcin daf lkcn budurwa banji xata dawo, tun da yabar gidan yake yawo acikin garin abuja shikadansa yanata tunani yanamai lissafin yadda komin shi xai kasance idan yaje calabar wajen Adiaha. Washe gari da safe Wata mata ce kalar fatar ta na wankan tarwada, gata nan a tsaye kuma doguwa, kibabbiya mai yelwataccen maxaunai ta sako babban leshi mai manyan holes dinkin riga da xani irin buban nan, matar tafi minti goma a bakin kofar yarta tana doka mata kira tana cewa "kafayat?,kafaya.. Kafayat..Kafayatiii,.tsabagen kiran datake yi sanda ta jawo hnkln duka masu aikin dake cikin babban gidan nasu. Haka Duk suka fito suna kallonta basu iyacewa komi saboda matar bata da dadi sam irin muguyen matan kabilan nan na gasken gaske. Juyawa tayi tanamai binsu da wani irin tsinannen kallon kyamata dana ban haushi,A tsawace tace musu dont just stand der and be looking at me ,ina kafayat take wai bata farka bane? maganan take tana duban golden watch dinta lokacin ana neman wajen karfe sha daya da rabi saura daya daga cikin masu aikin namji yace "Tana ciki Ma daxu dai kwalliya takeyi. Matar tana waigowa tace "What? Kwalliya? Nan Dukan su sukayi shiru suna ciccire idanu, kasa ce musu komai tayi takada kanta ta bar wajen within few minutes ta dawo da spare key ta bude kofar ta shigo ciki. Wata hadaddiyar yarinyace full option ke xaune agaban mirror ta gama rabxa kwalliyarta tsaf tayi kyau ta xuba red wine a cup tana kan shan wine din abunta gabaki daya sai wani layi layi takeyi da alaman tasha giyar da yawa haryana dan bugar da ita sosai. A mugun hargitse matar tayo kanta ta kwace kwalban nata da karfi cikin yanayin fada ta watsar akasa inda duk bacin ran yartan ya bayyana , she was wearing a green lace desire balconete fitted gown mai wani irin kyau saidai bakaramin matse surar jikinta yayi ba Inda kusan dukan kyaun surarta yake nunawa... ACikin layi tamiƙa tsaye tasa hannu xata amshe giyar a hatsale matar tace Ke da Allah ya isa haka ode, olodo, You are too useless kafayat, sai akace miki in kika cigaba da lalata rayuwarki shixai saka Damilare yasan kinayi ne? Why wud u even tell evryone that shine xaki aura for god sake, ynxu Bagashi kowa sai ido yake xuba

Chapter 4 of 19