Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💋❤️AUREN HUCE HAUSHI.💋❤️ MAMAN FATIMAH. DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIKAI SALATI DA DAUKAKA DA AMINCI SU TABBATA GA FIYAYYAN HALITTA ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD BIN ABDULLAHI DA ALAYENSA DA SAHABBANSA WANDA SUKA BISHI HAR ZUWA TASHIN ALQIYAMA. Wannan littafin kifkirarran labari ba'a yishi Dan wani ko wata ba duk abinda akaci karo dashi Arashi ne kawai. This Book is dedicated to you Ten sisters. Allah ya Kara Mana zumunci. Paga one ..........A hankali motar da shigo layin dai dai wani katafaren gate ta tsaya, yanayin yanda take fidda wani Dan Kara alamune dake nuna motar tayi dogon zangon tafiya, direban Bai Danna Horn ba bara a kaiga bude gate din gefen wata bishiyar dorawar tururawa ya karasa da motar, wasu dattawa ne su buyi suka fito daga bayan motar yayin da wani matashi ya fito daga mazaunin direba, Mika yayi dareban tare da salati. Kofar gidan suka nufo da kafarsu Dan matshin be yayi nocking kamar day biyu kafin wani dattijo ya leko ta wata karamar kofa jikn gate din. Da sauri ya bude kofar Yana fadin "A'a Alhaji barkan ku da zuwa kin Sha hanya sannunku" tare da Basu hannu sukayi musabiha suna fadar "wlh kuwa malam Sani ya muka sameku?". Cikin fara'a yake fadar "Alhamdulillahi". Kafin yayi gaba Yana cewa "Bari nayi Muku iso gurin Alhajin Allah ya taimaka Yana nan". Harabar gidan suka shiga suka rufawa malam Sani baya zuwa bangaren Mai gidan inda yake ganawa da bakinsa. Lokacin da suka karaso gurin kofar shi Kuma Malam sanin ya fito Yana fadin "Bismillah ku shiga, sannunku". Yayi gada da sauri Dan cika umarnin Alhajin na Kiran babban Amininsa na kankankan Malam Bukar. Da sallama suka shiga falon, Masha Allah komai najin dadin rayuwa akwai shi a falon tamakar fadar wani sarkin. Cikin fara'a da sakin fuska Alh Jafar Mai Yadi ya nufo bakin nasa Yana fadar "A'a! Alhaji Sulaiman kune haka cikin wannan ranar ga nisa". Amma kasan zuciyarsa mamaki ne fall a cikinta shi dai yasan ba wani abu daya taso da zai kawosu a irin wannan lokacin a kalla suna da sauran kwanaki uku kafin duzo duk da sun bada duk abinda ake da bukata lokacin kawai ake jira. Amma dai ko meye Allah yasa Alkhairi ne. Bayan gaishe gaishe na al'ada daya daga cikin 'ya'yan Ahj Jafar ne yayi sallama ya shigo Yana gaishe da bakin Yana aje musu lemon da ruwa ya fita. Wani matashin ne shima ya shigo da manyan warmers da wata yarinya da basket Mai dauke da plates da cokula da cups Suma suka gaishe dasu suka fita. Tunda aka Fara shigo da wannan karamar arzikin Alhaji sulaiman ya sadda Kai kasa zuciyar idan tayi dubu to a bace take. "Bismillah kuci abinci kafin mu shiga sallah tunda Azzahar ta gabato". Alh Jafar ya fad'a Yana nufar kofar fita. Bayan fitar Alhaji Jafar Alhaji Ismail ne ya kalli Yayansa Alhaji sulaiman "Nifa duk na rude wallahi har na rasa ta inda zamu Fara fad'a musu irin wannan magana duba da irin karamcin wannan bawan Allah". Ya fad'a yana Jan siririn tsaki. Dan matashin daya tukosu ne yayi magana "wlh Daddy naso kun hakura da zuwa ita Hajiyar tazo da kanta ta fad'a musu abinda ta kulla, ni ban taba ganin irin wannan ba anyi Abu cikin mutunta juna har an kawo wannan gabar Amma Rana tsaka irin wanna ta taso Babu Dadi ni wallahi tausayin Musbahun nakeyi ya shiga wani hali Amma ita ko a jikinta". Shi dai Alhaji sulaiman Bai Kara magana ba haka Bai ko kalli abincin ba duk da yunwa da yakeji leonm da ruwa kawai ya sha, Alhaji isma'il da Al-Amin ne sukaci abincin suka fita zuwa masallacin kofar gidan. Tare suka shigo gidan bayan idar da sallar har da Malam bukar domin shine limamin masallacin. Sabuwar gaisawa suka karayi Amma wannan lokacin Al-Amin Bai biyosu ba. Alhaji sulaiman ne yayi Qarfin halin Fara magana Yana kallon Malam Bukar "Dan Allah malam ayi hakuri da abinda mukazo dashi WALLAHI badan Nan gidan bane Babu abinda zai Kara dawo Dani garin Nan". Yayi shiru ya kasa karasa maganar saboda wani abu daya tsaya Masa a makogwaronsa yana masa tukuki. Shima Alhaji Jafar wani abune ya tsirga masa har tafin kafarsa ga wata irin faduwar gaba taba gaira ba dalili. Shiru falon ya dauka na wucin gadi kafin Malam Bukar ya magantu "Alhaji ka Fadi ko menene ba wata matsala ita rayuwa ba yanda Bata zuwarwa bawa ko Dadi ko akasin hakan, Kuma duk musulmin kwarai ai yasan kaddara, ba damuwa ai and Zama daya". Alhaji Ismail ne ya karbi maganar ganin yayan nasa bashi da niyyar cigaba da maganar. "Ayi hakuri Malam kan maganar auren yaron gurinmu ne da yarinyar gurinku, wata fitina ta taso yau kwana uku kenan ana Abu daya mahaifiyarsa ta kafe kaida fata Bata amince ya auri Zahra ba duk yanda mukaso gyara abun ya gagara karshe ma cewa tayi idan har Musbahu ya auri Zahra Bata yafe Masa nononta daya sha munyi munyi da fad'a Mana dalilinta na wannan cin zarafin Amma ta kekashe taki fad'a karshema abun ya zamar Mata lalura kamar ta jinni". Tunda ya Fara kora bayani Alhaji Jafar ke maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, domin duk wani karfin gwaiwarsa ya Kare wannan wace irin musiba ce kullum idan auren yarinyar nan ya taso sai an Sami wani akasin ya taso shi Lamarin Nan ya rasa yanda zeyi dashi. Malama Bukar ma rasa abin fad'a yayi duk wani kuzarinsa ya Kare. Yayin da su Alh Sulaiman suketa nanata ban hakuri. Cikin muna juriya da dattako Malam Bukar yace "haba Alhaji ba komai kasan komai nufi ne na Allah Daman Bai Qaddari shine mijinta ba, Allah yasa hakan yafi musu Alkhairi su duka'. Gaba data suka amsa da Amin. "Amma dai Abu baiyi Dadi ba wallahi ba Baki nayi musu ba Amma kafin a Sami Mai nagaratr yarinyar Nan zasu Dade suna nema" cewar Alhj Ismail. Har gurin mota suka raka bakin, har suka daga bakinsu Bai Dena bada hakuri ba. Bayan tafiyarsu falon su Malam suka dawo jiki a sanyaye duk Lamarin ya cakule wannan wace irin kaddara ce ke bibiyar karamar yarinya haka aure dai dai har uku ana fasawa. Cikin nuna damuwa Alhaji Jafar ya kalli Malam Bukar yace "malam inshallah Allahu wannan karon zan aurar da Fatima tunda Naga lamarin bana arzki bane ko meye in Sha Allah sai Naga bayansa'. Tunda Alh ya Fara magana Malam Bukar ke girgiza Kai shima lamarin ya kaishi makura yasan lamarin yarinyar akwai magauta a cikin Amma ganin an samu rata Mai yawa a tsakani ya dauka abun ya wuce ne. Cikin nuna alhini Malam ya kalli amininsa yace "Dan Allah Alh kayi hakuri kada kayi Abu cikin fushi da kace zaka aurar da ita kada azo ayi aikin Dana sani". Kujerar dake daura da Malam din ya zauna kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Ko daya banyi fushi da ikon Allah ba kawai dai na gaji da wannan wasan ne kullum na Zama karamin mutum saina Raba I.V na daurin sure azo ace an fasa wasu ma sai su zageni ace Dan bani na haifi Fatima ba na saka ido ana Mata wannan cin zarafin wlh da banyi alkawarin daina hada auren zumunci ba da yau ba sai gobe ba zan aurawa Abdul Hakeem ita. Amma yanzu ma Bata baci ba ka nemi shawarar Mahmud na Nan gurinka idan ya amince na bashi auren ta". Cikin kaduwa Malam Bukar ya kalli Alh Jafar yace "Wane Mahmud din, ba dai na Nan gurina ba?". Cikin yadda da Kai Alh Jafar yace "shifa nake nufi ko akwai wani Mai wannan sunan a gurinka?". Gargiza Kai Malam din yayi tare da fadar "Babu, Amma Alhaji al'marin Mahmud ba boyayye bane a gurinka kada duniya ta zagemu fa". Gyara Zama Alhajin yayi kafi ya fuskanci amininsa sosai. Wallahi Malam bana gudun duk abinda za'a fad'a na yaba da nutsuwarsa idan kaga ba'ayi ba to shima Allah Bai nufi mijinta bane Amma na jima Ina yiwa 'ya'yana sha'awarsa". Kai kawai Malam yake jinjinawa shi lamarin duk yazo Masa a baibai ya jima Yana nazari akan lamarin Fadima kullum Abu daya yake gani mijinta ba Nan kusa take ba bil hasal ma wani lamari yake gani Mai girma dangane da mijin nata da wani irin Haske Amma koda Wasa Bai taba fadawa Alhajin ba sai dai Yana yawaita saka almajiransa gurin yi Mata addu'a. Sun jima suna kullawa da kwancewa a tsakaninsu daga karshe suka tsaya a malam ya tambayi ra'ayin yaron idan yana so la'ba'as. _______ A hankali take sakkowa daga stair din tamkar wani dawisu Tasha make-up da wata gawon Mai azabar kyau Sai karamar pos a hannunta daga bayanta 'yan Mata ne su biyu ko wacce Tasha nata gayun, tun kafin su karasa sakkowa kamshinta Mai saka nutsuwa ya gauraye ilahirin falon. Falon a Cike yake da jama'a kowa ka gani ta amsa sunanta sai tsirarun yara. Da sauri wata ta matso gurin su tana rangada buda, tana fadar "Masha Allah Amarya Allah ya kade hau da bala'i ya bada zaman lafiya Hajiya Zahra suga bayi farin banza jikar hardon fulanin Mubi jikar larabawan Jodan da larabawan madinatul munawwara kaga musu kyawun asali Amarya a gidan Mushahu alherin Allah yakai Miki". Wata daga cikin matan dake zaune ta tashi ta sunga zubawa marokiyar kudin ita Kuma tana Kara Koda Amarya Zahra. Aunty Hasana ce ta fito daga wani Dan korido ta karaso tana kallon kanwar ta ta, tana Kara tasbihi ga ubangiji daya halicci wannan kyakykyawar surar. Hannaun Zahra ta rike tana kallon Baba Tabawa Mai aikinta yanda ta zage tana jero kirari kamar wata marokiya. Dan murmushi tayi tana fadar "Masha Allah, Baba Tabawa yaushe Kika Zama marokiya bani da labari?" Dariya tayi tana fadar " ai ko ban iya ba na koya mu Abu namu bikin uwar dakina guda kinsan biki na d farar kaza balbela ba gayya ce ba, yakuwar kan kabari kenan baking cikin 'yan taushe, murucin kna dutse Baki fito ba sai da kika shirya" Dariya sukayi gaba daya, har gurin da zasuyi bridal shower din kawar Aunty Hasana da Baba Tabawa suka raka Zahra. Sun chashe, sunyi hotuna kamar ba gobe sai dai duk Wanda yasan Zahra yasa Bata cikin walwala haka nan take Jin wata irin faduwar gaba da rashin dadin zuciya Amma ita kanta Bata San taka maimai me yake damunta ba gashi tun jiya take neman wayar Mushahun ta kasa samun shi, haka ta abokinsa Deeni itama shiru a yanda sukayi dasu yau ne ranar da zasuzo Dan har hotel din da zsau zauna sun Kama mukullan ma suna hannun magaji. Dadin dadawa yau sukayi za'a kawo ya'yan yayar shi da wasu cussing dinsa. Sai gurin karfe Tara suka Gama shagalinsu, Zahra Bata koma saman ba inda akayi musu masauki Sai ta nufi bed room din Aunty Hasana na kasa dakin ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta yake tashi ga danyi AC ya gauraye dakin. Head din ta cire ta aje kan bed side locker kusa lamp, gadon ta hau ta kwanta lamo kamar ba mutum akai Dan ko kwakwkwarwn motsi Bata sonyi wata irin kasala ce ta sauko Mata. Ta jima a dakin kafin taji alamun bude kofar Bata daga Kai taga ko wanene ba kamshin da taji ne ya sanar da ita Auntyn ce. Kusa da ita ta zauna tana Kai hannu jikin.wuyanta tare da tambayar "me yake damunki? tun safe Ina Kula da mood dinki Sam bakya cikin nutsuwa". Ta fad'a tana kafe Zahrar da Ido. Yunkurawa tayi ta tashi zaune tare da fadar "Nima bansan me yake damuna ba wlh Aunty Sam bana Jin dadin zuciya ta sai zafi take min Kuma gabana sai faduwa yakeyi". Ta karasa fad'a tana shashhshekar kuka kasa -kasa. "Meye Kuma abin kuka? keda zakiyi farin cikin Allah ya kawo lokacin bikin ba kamar lokutan baya ba da aka dunga samun akasi". Kanta ta kifa a jiki Auntyn taci gaba da kukan ta marar sauti. Bata hanata sai tayi Mai isarta kafin ta Sami zarafin magana. "Aunty wlh Ina ji a jikina kamar wannan ma za'a Sami matsalar kinsan jiya saida nayi irin mafarkin da nakeyi idan za'a fasa aurena". Ta fad'a tana Kara goge kwallar data ciko Mata Ido. Kallon ta kawai Aunty Hasana take ita fa lamarin yarinyar Nan Yana Bata tsoro kada fa namijin Aljani ya aure ta suna zaune Basu Gane ba. Karo biyu ana saka bikinta abun Yana lalacewa toga wannan ma, itama fa kawai daurewa tajeyi tunda Zahra ta fad'a Mata Musbahun Bai kira ba Bai kumazo ba ba wani Kuma nasa da yazo alhalin ba haka aka tsara abunba, Amma sai tayi ta maza tace. "Haba Zahra ya Zaki ringa fadar irin wannan maganar kiyi addu'a ba abinda zai Sami aurenki wannan karon sai Alkhairi, Ina ga da abinda ya hanasu karasowar har yanzu ki jira zuwa gobe Mana maza kiyi sallah kici abinci a sakonki can ki dauko zuwa an jima sai kiyi amfani dashi. _________' GIDAN MLM BUKAR Bayan idar da sallar insha'i Malam da sauran manyan Almajiransa suna Zama ana karatun littatafan fiqihu da hadisan Manzon Allah s.a.w.w, a Nan cikin baban falonsa ake karatun an kwata shi sosai a zuba kujeru na alfarma, saida aka Gama karatun sannan sukaci abinci kamar yanda aka Saba kafin Kuma kowa ya nufi nasa gurin duk da makarantar ta Sami cigaba sosai kamar ba makarantar amajirai ba anyi Mata tsari sosai a zamanace Dan har hostel garesu sama da kasa da gurin koyon sana'a Kuma ana musu abinci basa zuwa bara, sannan akwai malamai da aka dauka suna koyar da karatun boko tun daga mataki primary, junior, zuwa senior, secondary suna kokarin Fara turo dalibansu zuwa manyan makarantu, sun Sami wannan cigaban ne karkashin wata kungiyar NGO ne. Lokacin da Mahmud da Habib zasu fita Malam yayi gyaran murya duk su biyun suka juyo, Mahmud yayiwa alama daya dawo shi Kuma Habib ya fice.. Nan kusa da Malam ya zauna ta lakwashe kafafuwansa kamar zaman daukar karatu. A hankali Malam yake Kare masa kallo shi kadai yasa abinda yake kissimawa a zuciyarsa sai Kuma Allah daya hallice shi. Sun dauki kamar minti uku a haka kafin Malam ya magantu. "Mahmud" Malam ya Kira sunansa. Cikin ladabi ya amsa Masa da "na'am Malam". "Kasan dalilin dayasa nayi kiranka?". Cikin ladabi ya amsa da "A'a" Cikin wani irin yanayi Malam yace "wani nauyin Kuka aka Dora min Wanda na rasa ta inda zan Fara maka bayani". Zamansa ya gyara Yana Kara fuskacin Malam din Yana fadin "Malam ka fad'a min ko menene ni maiyi maka biyayya ne In Sha Allah". "Ai kasan gidan Alhaji Jafar nawa za'ayi bikin yarinyar gurinsa ko?" Kai ya gyada Masa tare da cewa "Eh na Sani ba Zahra za'a aurar ba?" "Eh ita fa, to an samu wata matsala ne wadda ta haddasa kasa auren a wannan karon ma kamar lokutan baya Amma wannan sai yafi na bayan Muni domin kuwa saura ba kaiwa ga Fara bikin Amma wannan Saida abun ya kurace har an saka yarinyar a lalle sun Fara duk kwaramniyar su ta Mata a lissafi saura kwana uku daurin aure sukace sun fasa, shine shi Alhajin yace na meni shawararka idan ka amince zaka iya auren yarinyar ya baka za'a daura muku aure ranar juma'a inshallah Allahu". Da sauri Mahmud ya dago Yana kallon Malama bakinsa har rawa yake yama kasa furta maganar dazai fad'a Kai ya shiga girgizawa dafa shi Malam din yayi Yana fadin "ka nutsu bazamuyi maka dole ba idan bass sonta sai a nemi wata mafutar" Da kyar ya tattaro nutsuwarsa ya kalli malam yace "Ba haka nake nufi ba, gani nayi yaushe nakai matsayin da za'a bani irin wannan yarinyar aure kamar tafi karfina ni almajiri ne wanda ban aje ba banba wani ajiya ba, kuma tana da ilimi Mai zurfi ba lallai ta yadda ta zauna dani ba". "Ba wannan nake son jiba daga bakinka fadin Kai ko wanene ba taso ba Alhaji shi yafi sanin Kai ko waye amsa muke bukata zaka iya aurenta ko bazaka iya ba ?". Cikin alamar sarewa yace "wane ni ice bana son wannan yarinya na karba na gode Allah ya saka da Alkhairi". Ya fad'a cikin wata irin murya Mai sanyi. "A'a kaje ka nutsu kayi shawara sai ka fad'a min duk huku cin daka yanke, tashi kaje dare ya farayi". Yunkurawa yayi ya tashi Yana fadar "sai da fade" "Allah ya tashe mu lafiya" cewar Malam. Daga falon malam Mahmud bakin titi ya nufa inda yake tunanin ganin Habib Yana son ya karbi lifan dinsa zaije wata unguwa. Gurin Ashiru Mai shayi ya Fara zuwa baya nan sai su salisu da Bashir Suma duk mutanen Mahmud ne hannu ya Basu saka gaisa sannan ya tambayesu Habib wani ne daga can gefe yace "ai yanzu ko runhu ka rike yana gurin Ubaidat kasan mutumin naka Yana neman dauko dala ba gammo". Ya karasa fad'a Yana dariya Bashir ne yace "ko wani Abu ne Naga ko Zama bakayi ba" Da tsaki yayi Yana Dan dafe kujerar kusa dashi Yana fadar "wlh lifan dinsa zan karba zan danje unguwa". "Kai haba saboda lifan kake wannan zagaye zagayen ga nawa kayi amfani dashi mana". Ya fad'a Yana Miko Masa makullin ya karba Yana godiya. Kai tsaye zaranda hotel ya nufa.💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️ MAMAN FATIMAH. ✨Page two✨ ________📖🖋️ Safa da marwa take tun bayan gama sallar insha'in ta, ta Kira layin wayar tafi sau shurin masaki Amma ta kasa samun Wanda take nema, gumi ne yake fama tsatsato Mata daga goshinta, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Gafen gadonta ta koma ta zauna Kara kiran tayi cikin ikon Allah sai Kiran ya shiga da sauri ta nufi kofar toilet dinta na daki ta shige. Bata tsaya amsa sallamar wadda ta Kira din ba ta Fara magana "Asabe me yake faruwa ne tun jiya nake neman wayarki Bata shiga Ina cikin tashin hankali komai fa Yana nema dagulewa, ba alamun nasara a wannan karon tunda komai ya kankama". Shiru tayi tana sauraran wadda ta Kira Asube ta jima tana sauraran ta kafin tayi dariya tace "haba yanzu naji magana da har hankalina ya tashi ki rike sauran maganar sai kin shigo gobe ma karasa". Ta kashe wayar ta bude kofar toilet din ta fito cikin farin ciki da walwala sabanin yanda ta shiga. ___ Mahmud. Ya jima a cikin hotel din kafin ya fito zuwa gurin securities din da alama sun saba sosai Dan yanda suke bashi girma sai abin ya baka mamaki makullin lifan din Wanda ya barwa ya miki Masa tare da fadar "Yallabai an zubo petrol din". Lokaci daya Kuma Yana Miko Masa kudi, kallon na mine yayi masa. "Kudin sunyi yawa ne a sayan man Saida naje na duba maga yawansu". Ya fad'a Cike da ladabi, hannunsa ya zura a aljihun wandon jikinsa ya dauko wasu ya Kara Masa, sannan ya Kuma dauko wasu ya bashi alamar ya baiwa abokan aikinsa. Godiya suka dunga jero Masa Dan inda sabo sun saba da Alkhairinsa. Kai tsaye gurin Ashiru Mai shayin ya nufa duk da dare ya Fara Amma yasan yanzu 'yan term din nasa Basu Isa tafiya gida ba Dan sukan Kai har daya na dare suna hira. Makullin lifan din ya mikawa Bashir Yana fad'a "Jazakumullahu khairan". Habib ne yace "Wai Dan Allah Ina kaje a rufe wayarka tun dazu nake nemanka fa daga inje in dawo kawai na nemeka na rasa sai su Salisu ne sukace kazo nemana ka wuce unguwa". Kusa da Habib din ya zauna na fadin "wash Allah wlh duk na gaji". "Da kayi aikin me". Cewar Habib. "Bari kawai ba aikin da nayi Amma Wanda yake fuskantoni ba sauki kazo muje gida akwai sakonka da Malam ya bani na baka". Ya fad'a Yana kikewa tare da mikawa su Bashir hannu yayi gaba gurin lifan din Habib. Dakinsu Mahmud ya bude daki ne madaidaici da gado guda biyu da wardrobe ta jikin bango sai mirror irin na croom din Nan da AC, kasan dakin shimfide da tayil, lokacin da akazo aikin NGOs din ne aka yiwa Malam nashi falon da Kuma irin wadannan dakunan guda uku sai Kuma dakunan Yara almajirai sama da kasa. Dakin sai kamshi yakeyi, sau da yawa Habib kanshi Yana mamakin wasu abubuwan na Mahmud sai dai ba fuskar da ze tambaye shi duk kuwa da amincin dake tsakaninsu. Saida Mahmud yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya Zauna a gefen gadon Yana fuskantar Habib kafin yace. "Kai inaga fa nan da kwana uku zan ankwance". Ya fad'a yana wani killer smile. Zabura Habib yayi ya tashi zaune sosai Yana fadar "Kamar Yaya?" "Kamar yanda na fad'a maka, tsayar Dani da Malam yayi kenan yace Alh Jafar ya bani auren yarinyar Nan da ake bikinta wadda Abdul Hakeem ya kawo Mana IV last week". "Ban Gane ba bafa ta Yaya hakan zata faru?" Kafada ya dage alamun shima Bai Sani ba. "Dan Allah kayi min bayani yanda zan fahimta a sakani a duhu wallahi". "Iya abinda na Sani kenan kawai ance an bani idan inaso inyi shawara". Cikin madaukakin mamaki Habib yace "to Kai ya kace masa?' "Me zance kuwa na karba na gode, kasan har abada ba jayayya tsanina dasu iyayene sak, sun min abinda kowane uba yakewa dansa sun min gata sun Kula Dani lokacin da bana Gane gabas bane Gane yamma bana Gane fari bana Gane Baki, Sun zamar min garkuwar data Hana kowane harbi ya sokeni, Toni kuwa wanen irin butulu ne da zan watsa musu kasa a Ido sufa sun san waye ni Amma suka runtse idonsu suka bani basu nuna min kyama ba, sannan ka dubi yarinyar da aka bani diamond ce fa a cikin gold kasan bani da abinda zan tunkari irin wannan yarinyar da sunan soyayya bare har aje ga maganar aure". Tunda ya fara magana Habib yake Masa kallom mamaki Yana jinjina karfin ikon Allah, lallai wani lamarin sai Allah. Da kyar ya Sami zarafin fadin "Masha Allah! Allah ya Sanya Alkhairi Abu yayi Dadi amma fa ka daina fadar

Chapter 1 of 31