Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wai baka da abinda zaka tunkare ta wlh kafin wanna lagwanin Wanda zata aura say millions shi har wani namiji ne kawai Abu daya Sani yana da kudi mu Kuma bamu dasu Amma muna da abinda bashi dashi". "Kamar Yaya me muke da shi Wanda shi bashi dashi? ka duba fa kaga irin yanda yake shiga babban yaro ne ga manyan motoci mu Ina muka gansu" Dan karamin tsaki Habib yayi Yana fadain "ana gabas kana yamma ana maganar nagarta da mutunci da cikar Kamala da siffar mazantaka kana wata maganar, mu an fad'a maka haka zamu dawwama bazamyu arzikin ba". Dariya Mahmud yayi "maida wukar abin Bai Kai haka ba ko Daman haushinsa kakeji ne ban sani ba?" Habib tsayawa yayi galala Yana kallon Mahmud kafin ya karayin wani tsakin "Allah ya sauwake zanji haushinsa Ina ruwana dashi kawai da Daman can no banga dacewar su ba Kai Nifa idan Malam yasa Yara suyi Mata addu'a har cewa nake suyi Mata addu'a Allah ya Bata gwarzon miji na nunawa sa'a". "Amma wallahi Habib baka da mutunci shi wannan ba gwarzo bane?" "Ina fa namiji Yana rausaya kamar mace". "Kaga Yi closing din wanna chapter din yayi zamuyi da wannan lamarin kaga dai komai fa Sai a hankali Dan abinda nake Sami daga wannan organization din ba Isa wannan shidimar zasuyi ba ga yarinyar Mai zafi ni kamar ma tsoronta nakeji fa". Ya fad'a Yana dariya. Sun jima suna tattaunawa yanda zasu bullowa lamarin. _______ Tunda garin Allah ya waye Amma take ta kaiwa da kawowa tsakanin kitchen da dakinta zuwa dakin Baki, Saida aka kammala abincin breakfast aka babba mutane sannan ta samu ta koma daki inda ta samu kanwar Babarta Inna Maimuna a uwar daki. Kallonta tayi "Asma'u ya kamata ki karya kinsan Ina tunanin zuwa anjima gidan ze Fara cika bazaki Sami damar Zama kici wanti abun karki ba, waini ina Hajiya Mama ne Naga yau Bata leko ba?" "Tana bangaren Alhaji Nima nayi wannan tunanin Amma ai lafiya ita keyin shiru". "Hakan ne Kam". Cewar Inna maimuna. ****** Katagum road A dakin Aunty Hasana Zahra ta kwana ita da Autart Haneefa, sai kusan goma ta tashi daga barci wayarta ta Fara dubawa ta tarar da missed calls rababa Amma Sam babu nasa ko na wani daya dangance shi, duk na kawayen da abokanin arziki Bata bi rakansu ba ta shiga toilet wanka tayi, lokacin data fito Sajida ta Samu a dakin ta shigo Mata da breakfast dinta nan, tunda ta fito Sajida ke kallon ta har ta karaso gurin mirror inda sajidar ke zauna murmushi Zahra tayi Mata tana fadin "wannan kallon fa ko na canza Miki ne?". Kai ta gyada Mata "gaskiya Kam ba haka na Saba ganinki ba, meye yake faruwa ne? nifa tun jiya nake nema Deeni da wannan cussing din na Mushahu Aliyu, ta Aliyun tana shiga ba'a dagawa Amma su sauran wayoyinsu switch off". Da rausayar da kanta tayi tana Dan watsa hannuwa "wallahi bani da masaniyar me yake faruwa nima hakan take kamar ke Amma nasan dai kome aje ciki yau dole su shigo garin. Ni wallahi da Aunty Hasana zata yadda da an hakura da wannan mother's day din nifa duk abin ya fice min daga Rai gani nake shima wannan aure ba yuwuwa zaiyi ba nasan dole da wata a kasa ai ba haka muka tsara abubuwan ba Amma kin ko daya fa basuyi attending ba". Ta karasa maganar idanunta na cikowa da hawaye. Hannunta Sajida ta kamo ta rike tana fadar. "Hqba Bestie kada kiyi Kika in Sha Allah ba wani matsala sai Alkhairi kada ki Bata lokacin farin cikinki mana". Aunty Hasana ce ta shigo da sauri alamar wani Abu zata dauka turus tayi tana fadar "ke me zan gani Zahra kukan dai? haba you have to be very strong Mana kada ki yadda aga rauninki a kowane janibi ki Zama jaruma Mai iya fuskantar ko wane kalubale, kada ki kara saka damuwa a zuciyarki zan fita Amma in Sha Allah bazan Dade ba ki shirya kuje sama naji suna cigiyarki". A bangaren Mahmud kuwa bayan anyi sallar Asuba a masallaci ya zauna yayi azkar dinsa Saida gari ya Fara haske sannan ya fito lokacin su Malam sun Gama karatun da sukeyi da maza magidanta. Da sallama ya shiga falon nasa lokacin Abubakar Yana mayar da littatafan mazauninsu, sai da ya zauna sannan ya Dan rankwafa Yana gaishe da malam, Amma sai ya moko Masa hannu sukayi musabiha Yana fadin. "hakan shine sunnar Annabin Rahama Muhammad s.aw.w." Shiru falon ya dauka bayan fitar Abubakar Malam Bai tofa ba haka Mahmud shima, Malam ne ya kauda shirun "Ya ake cikin Mahamuda wace shawara ka yanke?". "Ba damu Baba Malam na karba na gode ayi min godiya Allah yasa hakan yafi Alkhairi". "Allahumma Amin. Allah ya Sanya Alkhairi ya Baku zuri'a Mai Albarka Allah yasa ace gara da akayi hakan" A zuciyarsa yake ta amsawa da Amin. Harya yunkura zai tashi Malam yace "koma ka zauna, Ina zaka bamuyi maganar inda zaka ajeta ba da sauran shirye-shirye". Sadda Kai yayi haka Nan yaji wani irin nauyin malam din ya taso Masa. Kansa Yana kallon kasa yace "so nake muyi shawara dasu Habib yanda muka yanke saiya fad'a maka". "A'a ba haka za'ayi ba nizan bada sadaki da kayan goro da alewa sai Kuma shaddoji da za'a kawo an jima Suma dinkakkune tunda abun yazo a kurace, sai Kuma gidan Nan na Hayin Banki mukullin na gurin Binya tun jiya na bashi nace yau zakuje a duba abinda za'ayi Masa". Mahmud kasa magana yayi shi wannan gatan har yayi Masa yawa komai anyi Masa. Rarrafawa yayi kamar yaro har gaban Baba Malam ya rinka godiya har Saida yayi Masa fad'a. ******** Amma ce da Inna a uwar dakin Ammar bayan dawowar Ammar daga bangaren Alhaji cikin tashin hankali Innar ta kalli Ammar tana fadin ke Asama'u wace irin magana ce wannan yaushe hakan ta faru duk bamu da masaniya?" Dan nisawa Ammar tayi. "Wallahi Nima ban sani ba Amma yace kada yaji kada ya gani naja bakina nayi shiru yana zargin kowaye yake lalata lamarin auren yarinyar Nan na kusa yake tunda yace min Malam Bukar ne yayi binciken Dan haka bazai cewa kowa komai ba har sai bayan daura auren tukunna". "Ya fad'a Miki waye mijin?" Kai ta girgaiza Mata alamar A'a. Nifa Ina gudun garin AUREN HUCE HAUSHI a kwaso bara gurbi Wanda za'azo ana Mana dariya". "Gaskiya bana tunanin haka Inna mu bita da addu'a kawai Allah ya Zama gatanta yasa albarka a ciki. 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️ Story & written By ✨MAMAN FATIMAH.✨ INA MIQA SAKON TA'AZIYYATA GA 'YAN UWANA HAJIYA MARIYA ALIYU ( JIMMAN ADO) HAJIYA BILKISU ALIYU (UMMA IKKI) HABIBA ALIYU (UMMA HABIBA) Na rasuwar mahaifinsu ALHAJI ALI DAN HAYA MAGAMA KAZAURE. Allah ya jikansa ya jaddadda Rahama a gareshi tare da sauran musulmi. Page three 🔷 📖🖋️ .............. Tunda Mahmud ya fito daga gurin Baba Malam yake nazarin yanda zai bullowa lamarin, baya son ko kadan a Sami kurkure, guri ya Sami nesa da makarantar kasancewar Alhamis ce Yara basa karatun safe sai ya zamana yawancin su suna dakunan su. Waya ya Ciro daga aljihun wandonsa yayi dialing din number Bata jima tana ringing ba kada daga magana ya Fara "kana jina Sameer sakon Dana turo maka kada a samu kuskure kayi kokarin ganin komai yayi yanda ya kamata fa". Dan Jim yayi alamun ana fad'a Masa wani abu "Ok to shi kenan take care". Ya kashe wayar. __ Nama ne da kayan miya ake ta shigo dasu cikin gidan da manyan kuloli sabbi Hajiya mama ce a kofar kitchen din na tsakar gida tana bada umarnin abinda za'ayi, yaran dake shigo da kayan ta kalla "wannan fa daga Ina?". Magaji ne ya Bata amsa kafin yaron data tambaya ya fad'a Mata "tare muke Mama na abincin bakin Abba ne". "Ikon Allah Naga ai an kawo wasu da sassafe dazu gasu nan har an kusa Gama aikinsu". "Eh to shi dai yace a kawo wadannan ma". Magajin ya fad'a Yana shiga dakin Amma. "Kai dawa Kuma kake tafiya kana magana" Cewar Inna maimuna. Kusa da ita ya zauna Yana fadin "nida Hajiya mama ne kayan miya ne da Naman rago Dana kaji Abba ya Kara badawa aka kawo shine take magana ko yayi yawa kame?" Dan murmushi Amma tayi "Abban Nan naku baya son a zauna lafiya wallahi magaji kamar zai aurar da Yara uku sai irin wannan shidima yake haka". Kai magajin ya jinjina "Amma kenan kin manta yanda Abba keson Zahra ai kawai kowa ya zuba Ido ana auren uwar masu gida tab ai kowa sai yasan anayi Yasin, ki Bari kawai Ammah Nan zan kawo nama a ajiye min". Ya fad'a Yana dariya ya nufi kofar fita saboda sallamar wasu Mata da yaji a kofar dakin. ___ Daki Mahmud ya koma ya samu Habib a tsaye a tsakar dakin da alama daga wanka ya fito, saida ya Gama wayar sannan ya kalli Mahmud. "Wai ina kaje ne? Naga fitowarka daga gurin Baba Malam kafin na saka caji na nemeka na rasa, Bilya ne ya kirani Wai mu sameshi a hayin Banki shi Yana can yaje da masu aiki su duba yanda za'ayi gyaran" Dan Dafe Kai Mahmud yayi ya Dan fesar da numfashi. "Ikon Allah Wai Daman kamar jira kuke ace za'ayi min auren Nan kowa sai rawar jiki yake yi, daga fad'a shine har ya want kwashi jiki da masu aiki ya tafi tun garin Bai Gama watstsakewa ba". "Naka wasa ne Alaji, aini yanzu haka mun Gama magana dasu Bashir sunce mun gasu Nan zuwa har suna cewa shegen zurfin ciki ne da Kai baka fad'a musu ba jiya ko kunya kakeji irin ta Mata". Ya karasa maganar Yana dariya. Har ya nufi gurin mirror ya tsaya "kaji na manta ba Salis yace na tura Masa cikakken sunan da ze saka a IV da zeyi a waya ya turawa friends na kusa". "Ok ba matsala ka tura Masa kawai da sunan aika Sani ba saina maimaita make ba". Misalin karfe Sha daya na safe wata bakar Hilux sabuwa kar ta dira a kofar gidan Malam Bukar. Lokacin yaran sun firfito suna sugogin su masu wanki nayi masu wasa nayi Amma idan ba fada maka akayi bazaka taba cewa yaran Almajirai bane kowa cikin tsabta Kuma a lokacin anyi hutun makarantar book shi yasa basayi tunda suma tsarin makarantar gwamnati suke bi. Mutane biyu be suka fito daga motar da sauri 'yan samarin dake kusa taso da sauri suna fadin barkan ki da zuwa kasancewar sun saba dasu sosai sune wadanda suke kawo musu tallafi daga organization din. Da sauri suka bude musu falon saukar bakin Malam kafin wani ya shiga ya fadawa Malam din. Ba jimawa Malam din ya fito suka gaisa a mutunce, sannan suka gabarwa da kayan abincin da suka kawo sannan suka gabatar Masa da bukatar daukar Mahmud zuwa wani taron karawa juna Sani na makarantun tsangaya Wanda za'ayi a kano, tunda shine Wanda suka dauka aiki a Nan tsangayar yake wakiltar su kuma gobe juma'a za'ayi taron na Rana daya ne kawai. Dan Jim malam din yayi kafin yace " Ikon Allah malam Sameeru ga koshi ga kwanan yunwa WALLAHI shi Mahmudan dai baze Sami damar halartar taron nan naku ba, domin a goben in Sha Allah za'a daura Masa Aure". Cikin wani irin madaukakin mamaki Sameer dake kusa da Malam din Kuma jagaban tafiyar ya kalli Malam Yana cewa. "Aure! Kuma Malam?". Kai ya jinjina Masa alamar tabbatarwa, "yanzu haka suna can gidan da ze zauna ana dudduba gyaran da za'a Masa duk da gidan Bai jima da kammaluwa ba kasan kullum abin duniya sabuntashi akeyi". Kai ya jinjina ya hadiye wani yawu da kyar shifa duk ya shiga rudu meye hakan Wai Kuma. Fara'ar dole Sameer ya kirkiro Yana kallon Malam yana fadar "Masha Allah Abu yayi Dadi to ai mu wannan lamarin namu ne munzo a dai dai kenan tunda Abu ne na ma'aikacin mu koma kunya zatayi Masa malam kada kuyi komai yanzu zanyi waya za'ayi duk abinda ya kamata tun daga abinda ango ze saka har abinda za'aci duk Yana karkashin kularmu tunda mu yakewa aiki, Kuma zamu zauna sai an daura auren damu in Sha Allah. Maganar taron Kuma sai dai a daga zuwa wani lokacin Dan bamaso wani yayi missing gaskiya". Tunda Sameer ya Fara Kora bayani malam ke jinjina Kai saida yake Aya sannan ya Sami zarafin magana. "To malam sameeru anyi haka abin fa da yawa kids bakuzo da Shirin wannan abun ba kunzo Kuma kuyi ya kuyi makarbiya ai da wahala abun". Dariya Sameer din yayi Yana fadar "malam ba abunda ze gagara kungiyoyin masu karfi ne, yanzu ma ga wannan saboda biyan sadaki". Ya aje Masa cheque na Banki suka Mike Yana fadar "Bari na Nemo shi a waya sai muje muji meye shirye-shiryen nasu, a huta lfy". Suka kad'a suka fita. _____ Kyakykyawan guri ne Aunty Hasana ta kama inda za'ayi mother's day din gurin ya kayatu ba karya kudi dai an kashe su gurin Kama event center din, anyi taron Mata 'yan gayu kamar ba gobe amarya tasha kyau kamar a dauke ba boye. Ga wani slow music da mc din ya saka na wakar Amarya da ango kowa ka gani cikin nishadi yake sabanin Amarya da Yayarta Banda ta Riga ta gayyato mutane harda wadanda sukayo Mata tafiyayya sukazo da ba abinda ze saka tayi wannan taron to Amma mutum Bai Tara Sani ga Allah ba. An raba kayayyaki na alfarma na bikin, sai magariba taron ya tashi, zuwa yanzu 'yan Qananan maganganu sun Fara fita a tsakanin kawayen Zahra tunda har zuwa lokacin ba wani duriyar Ango ko wani nasa, sai Dan kus-kus ake abinda yafi bada mamaki bai wuce ganin anata faman programs ba normal. Su Mahmud Basu samu kansu ban sai bayan sallar insha'i lokacin suka zauna Dan wuni guda suna ta faman sunturi daga can zuwa can abin dai ba sauki dan su sameer suna zuwa gidan suka babbago aikin da sai anyi sati ba'a Gama ba Dan sunce tsarin gidan gaba daya za'a sake, basunda ta cewa tunda oganninsu ne sai godiya suka dunga zubawa harda su Bashir. Gurin karfe goma malam ya Kira Mahmud a waya yace yazo cikin gida ya same shi. Saida ya leka falon iya Abu suka gaisa tana faman jansa tana ita ce ta karfen Dan haka ita zata koma sabon gidan a kawo Amarya nan. Da haka ya karasa turakar malam Yana zaune a falo Yana sauraren wa'azi a TV, yayi sallama Malam din ya bashi izinin shiga, Nan kasa ya zauna Yana gaishe da malam din.Wasu manyan ledoji malam din ya nunawa Mahmd Yana fadin. "Dauko wadan can kayan ka duba daya Wanda nasa a kawo maka ne biyun Kuma wadannan masu kungiyar ne ta taimakon tsangayu suka kawo ga lemuka can da ruwan roba sun kawo yafi catoon dari sunce kada ayi abinci ma duk za'a kawo, har na rasa da wane bakin zan gode musu, sai dai Ina rokon Ubangiji s.w.w yafi mu yabawa, naji su Habibu ma sun ce sun dauko aiki Mai yawa a wancan gidan ko?" "Eh wallahi munyi-munyi su Bari suka Kiya Wai haka aikin Qungiyar yake in dai kana musu aiki idan wani Abu ya sameka Mai Dadi ko marar dadi su zasu tsaya maka". "Alhaji yace min kun shiga dazu bayan sallar magariba har da bakin kunyi Masa godiya, kun kyauta haka ake so". Lokacin Mahmud ya koma dakinsu Habib baya Nan gurin da yake aje makullin lifan dinsa ya duba ya kuwa you sa'a yana nan, lodojin ya zube a kan gado ya dauki makullin ya rufe dakin ya hau mashin din yayi gaba. Bai dawo ba sai kusan Sha biyu da rabi har lokacin kuma Habib baya dakin yasan suna can suna kujuba kujuba. Yauma Zahra taso kwana a dakin Aunty Hasana saboda tana bukatar kadaicewa Amma Sajida ta matsa Mata da mita Saida suka tafi Amma fa zuciyarta Bata da nutsuwa gashi tana ankare da Aunty Hasana tun jiya da dare a taje can gida cikin gari Bata da nutsuwa ko alama Amma tana ta kokarin ta basar sai dai ko Yaya mutum ya shiga damuwa indai kayi Masa farin Sani zaka fahimta, ita Abu mafi Bata mamaki yanda aketa kwaramniyar bikin ba wani canji sai dai abunda baza'a rasa ba duk da Daman ba wata muguwar bidi'a ba ta had'a, walima ce kawai Bata Sami ba saboda tace ita malam Tijjani Ahmad zeyi Mata Kuma bayanan yana Umara. Tunda tayi sallah ta kasa tashi daga gurin tana kallon su Sajida sunata sabgarsu, Amma ita da wata irin faduwar gaba ta tashi ta rasa nutsuwarta kwata kwata da kyar ta tsahi sauko kasa gurin Aunty Hasana a fall ta sameta tana hadawa Abbansu Haidar break fast. Gurin dining din ta karasa tana gaishe shi sannan gaida Auntyn. Dakin Auntyn ta shiga kwanciya tayi tana ta faman sakawa da kwancewa zuwa yanzu dai tasan tabbas da matsala sai dai yanda ba Wanda ya fad'a Mata shi yasa itama ta zubawa sarautar Allah Ido taga iya karshen film din tasan ko menene yau dai za'a yita ta Kare tunda yau ne deadline duk wata kunbiya kunbiya za'a zazzageta. Tun karfe goma Mai yiwa Amarya make up tazo Amma kememe Zahra tace ita bataso a kyaleta aka dunga yiwa kawayenta, ganin guri ze kure ne Sajida take ta fadawa Aunty Hasana Saida tazo sannan akayi Mata light makeup Amma fa duk da hakan tayi karshen kyau, farin material ne ta sakata Mai touching din sky blue sai aka daura Mata head shima sky blue din takalman da pos din duk sky blue din ne. Wani san sanyan kyau tayi na ban mamaki, komai na Zahra Mai kyau lallai zaharar ce Dan duk cikin kawayen Bata da mahad'i. A babban masallacin juma'a za'a daura auren Masha Allah, ango ya fito Shar abokansa sai mamakinsa suke Basu taba sanin kyawunsa da cikar haibarsa ya Kai haka ba sai daya fito sun Sha mamakin kwarai har wasu suka Fara kokonto a kansa, Yana kallon yanda idanun sukayi Masa caa. Dan dakakkiyar getzener ta saka ga takalman da agogo ga hula, Sam bazaka taba cewa Wai alamajirin malam bane ba, ga wani irin kamshin tunda ta tumkaro taron abokanensa kamshin ya hade gurin. Daga gefe sameer ne da abokinsa Naraddeen suna tsaye lokacin da Mahmud ya fito Sameer ya kalli Naraddeen din yace "wallahi wannan guy kwallon Dan duniya ne na rasa Gane kan alkiblar daya kalla Wai aure zai daura shi kadai kamar marara gata, ni so nake Naga karshen wannan wasan kwaikwayon nasa. Daga inda yake tsaye ya kafe Sameer da Ido ko Bai fad'a ba yasan me yake nufi tun jiya yake tuhumarsa aka zuwa da abokinsa da yayi duk da ya nuna Masa wannan ba wata matsala bace Amma har yanzu Yana hukunta shida idanunsa. Masha Allah dubban mutane ne suka shaida daurin Auren FATIMAH ZAHRA AHMAD SANI da Angonta MAHMUD MUHAMMAD DANGE akan sadaki dubu dari uku lakadan ba ajalan ba. Daurin aure daya bawa dubun mutane mamaki bare wadanda sukazo daga bangaren Mushahu sunyi mamaki kwarai sunan Amarya dai shine Amma ba mijin daya gayyato su bane yayin da yan unguwa ya Zama abin kasawa a faifai ana yawo dashi, da yawa na ganin beken Alhaji Jafar na aurawa bakon da ba'asan asalinsa ba yarinya kamar Zahra yayin da wasu ke fadar ai Dan ba 'yarsa bace shi yasa yayin wannan danyan aikin. ....... 💋❤️AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ Page four🔷 ___________''📖🖋️ Wata marokiya ce irin dattawan Nan da suke bin manyan marok'a ta biyo tawagar masu dawowa zuwa gida kasancewar gidan ba nisa daga masallacin juma'ar, itace ta rangad'a guda har sau uku ta Kara da fadin "Alkawarin Allah ya tabbata an daura auren Fatima Zahara'u da zukeken Angonta Mahmud Ubangiji Allah ya bada zaman lafiya da kazantar daki Bata shara ba, munzo much arziki mubar arziki a gurinsa. Kamar saukar aradu haka maganar ta shiga kunnen Hajiya mama, batasan lokacin data tsallake mutanen falonta ta fito ba dankwalinta a hannu, tana fadin "me naji ana fad'a wa aka daurawa aure da Mahmud naji kowa". "Eh haka ne Kam Alkawarin Allah ya ciki Zahara'u ta Zama matar Mahamuda" Ta debo wata gudar ta Kara rabsawa. Dai dai lokacin Hajiya kaltume aminiyar Ammah ta fito ta dukulawa wannan marokiyar kudi sannan ta Mika Mata babbar leda Mai abincin biki har da ruwa da lemo. Cikin rashin nutsuwa Hajiya mama ta nufi dakin Amma ko sallama Babu ta Fara fadar "Hajiya kinji abinda naji ko kunnena ne ya jiyo min ba dai dai ba?". Kallonta duk 'yan dakin suke kafin Ammar tace Mata "nima haka naji kamar yanda kikaji sai dai ko shirme takeyi ita Mai rokon tunda ba sanin su tayi ba". "Eh gaskiya Kam sai dai hakan". Ta juya ta koma daki. Bata zauna a falon ba uwar daki ta wuce, Asabe ce ta rufa Mata baya, a tsaye ta sameta ta Goya hannu a baya tana Dan Kai kawo a tsakanin gado da madubi. Waiwayowa tayi tana kallon Asaben kafin ta zauna a bakin gado, kusa da ita Asaben itama ta zauna. Tana fadar "Haba Hajiya Dan Allah ki nutsu bana son ki bada wata baraka a sabgar Nan keda na fad'a Miki Daman malam na BANDE yace wannan karon aure sai anyi Amma ba da Mushahun ba, Amma abinda yake daure min Kai malam na banden yace Wanda zata aura a nesa yake Kuma yaga haske so sai akan lamarin duk yanda yaso ya Bata lamarin abin Bai yuwu ba shine nace kawai a kyale tunda dai Wanda muke son a fasa da shin din aikin ya yuwu, nasan dai da wuya ta Sami irin Wanda ta rasa a bay". "Haka ne Amma abin dubawar waye wannan din sanan me yasa aka kudundune zance? Wai fa Dan munafurci Hajiya Asma'u cewa tayi Bata Sani ba ke kin yarda Alhaji ze aurar da Zahra Bata da masaniya, ko meye ma dai kyawaun ya kare a auren Hadi tunda nasan ba wani sai Mushahun shi Kuma ya Kara gaba kamar sauran". Ta fad'a tana kwafa, mikewa tayi tana gafar "Bari na fita sai Naga kul uwar daka". "Allah ya taimaki uwar dakina, aikinki Yana kyau". Asabe ta fad'a tana mikewa itama. ********** Daga gurin daurin aure Kai tsaye gidan gonar Alhaji Jafar suka wuce har tawagar angon bisa umarnin Alhajin tun safe ya turo Mai sunasa (magaji) yaje ya fadawa Baba malam. Anci an Sha kamar ba gobe mutane sunyi mamakin irin wannan karamar arzikin dan duk zarin mutum sai dai yaci ya Bari ruwa da lemo kuwa kamar banza. Abokan Mahmud kuwa sai Dan biki suke Masa. A gidan malam ma Masha Allah anci an Sha Yara sun san ana biki a gidansu, Iya Abu ma tayi nata taron komai baja baja makotanta ma sunsan ana hidimar arzki a gidan Kuma Suma sunzo Mata harda masu riko abin arzikinsu su kawo Mata. ******** A guje Faruq ya Fado falon Aunty Hasana,danta ne na uku Yana rungume da babbar rigarsa ta daurin aure daya saka Yana Fadi "Aunty Zahra wallahi Naga mijinki ba wannan Uncle din bane na kano wallahi wanna yafi shi kyau Baki gani ba yanda yake rabawa marok'a kudi ba, Kuma Dan gayu ne sosai Naga Uncle Abdul Hakeem ma ya rugume shi Yana ta dariya, Dana tambayi Auncle Imam yace min sunansa uncle Mahmud". Tunda ya shigo Yana karadin Nan ta zuba masa Ido tana sauraren abinda yake fad'a, kana ganinsa kasan har zuciyarsa abinda yake fad'a din gaskiya ne, wani irin gingirin taji kanta yayi mata, nan ta sulale ta kwanta kan kujerar ta saka hannunta ta rufe fuskarta wasu hawaye na zubo Mata masu zafi. Sajida da Amatu suka nufi gurin Faruq din suna neman Karin bayani. Yayin da wasu da yawa suke ta sabgar ciye ciyensu Dan Suma Kam an kawo koma enough. Kamar yanda ya fad'a haka Suma ya mayar musu Dan su harda Karin bayanin yayi musu kasancewarsa Mai surutun tsiya. A hankali Sajida ta kamo hannun Zahra Dan Bata fatan wani daga cikin bakinsu su fuskanci an samu matsala gaskiya, kamar masu you shawara suka shiga dakin Auntyn saboda Nan ne baza'a shigo ba. Bakin gadon ta zaunar da Zahra ita Kuma ta janyo stool ta zauna har lokacin Bata saki hannunta ba,tana Jin yanda ilahirin jikinta yake rawa. Hannun ta Kara jimkewa cikin nata tana fadar. "Cool down Mana bestie haba take it easy, kada ki tada hankalinki Taya Zaki kama maganar faruq kinsan dai ba wani hankali ya Gama Masa jiki ba". Kai ta shiga girgizawa cikin muryar Kuka tace. "Wallahi Saji akwai matsala kema Kuma kin sani sai dai kik'i fad'a

Chapter 2 of 31