Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem. Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta haifi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma Ammah. WACECE FATIMAH ZAHRA? 'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya har Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can. Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a can yayi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda. A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga iyayensa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah. Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar. Zahra nada wata biyar wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono. Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja. Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi Kuma ya koma Abuja. Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta. Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar da har abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba. Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Zahra ta hakura ta barwa Ammah Zahrar. Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin Kamar nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta. Wannan kenan. Ranar da za'ayi jarabawar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta. Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Zahra ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna". Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside locker ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana". Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu" "To naji maza Allah ya bada sa'a" A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan". Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan. Masha Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako. A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha. Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sannan ya fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru Kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "yanzu Yallabai da kanka zaka rakata ai da Koda Hasana ko Hassan ka hadasu zasu kaita ko Kuma a fadawa cen kakanninta su turo a tafi da ita ai cacar kudin Kamar yayi yawa". Daga Ammah har Alhaji Jafar din kallon Mamar suke ita dai Ammah shiru tayi yayin da Alhajin yace. Saboda ban San darajar 'ya'ya ba zan hada Yara a tafiyar uwa duniya daga Nan har Jordan na kwanta a gida hanakli kwance ko?" Kai ta gaigice tare da fadin "gani makudan kudi za'a kashe". Wani kallo yayi Mata "kada ki kawo b'araka Rabi'a duk yaran dake gabana daya na daukesu yada zan yiwa abinda na Haifa haka zan yiwa marainiyar Allah. Da Kuma kike maganar cacar kudi idan zan jera shekara Ina Kai zahra Jordan kullum ba abinda ze girgaiza a cikin abinda na mallaka". Ku tashi kuje. Lokacin da zasu tafi anyi Mata tsara sosai Dan Nanna ma kilishi tasa aka yi Mai yawa na tsaraba. Har kano su Ammah da yara sukayi musu rakiya. Lokacin da sukaje Jordan din ba karamar murna kakanninta zukayi ba Dan Babu zato suka gansu, sun Kuma Kara yabawa da cika Alkawarin Alhaji Jafar Dan da kansa yayi musu Alkawarin ze kawo musu Zahra Dan ko a waya Bai fada musu zuwansu ba,sai address dai daya taba tambaya can wani lokaci. A ranar Zahra taga zallar soyayya a gurin dangin Najwa Dan gidan cika yayi da 'yan uwa aka dasa sabon kukan rashin Najwar da kyar Abbie da Abbanta suka dinga Basu hakuri Dan ma Alhaji Jafar ba larabcin yakeji sosai ba saidai Wanda suke Jin turanci suka ringa magana dasu. Lokacin da Alhaji Jafar din ze tafi masukin daya Kama a hotel Abbie hanawa yayi duk yanda yaso zillewa kin yarda yayi dole ya amince aka sauke shi a wani part dake kusa da nasa Ummee din, Dan ba karya dukiya dai Kam akwaita Dan shi kanshi Alhajin yayi mamakin yanda ya riskesu Bai taba kawo haka suke ba lallai yasan hadin Allah ne kawai da suka bawa Muhammad sani auren 'yarsu Dan tazarar Mai nisa ce a tsakanin su. Kwanan Alhaji Jafar bakwai ya wuce Umara yayin da Ummee tayi Masa Alkawarin zasu hadu a Saudiyyar tunda zata kawo Zahrar Nan gurin iyayenta da 'yan uwa su ganta a cikin garin Madinatul Munawwara. Satinsa daya da zuwa Suma su Zahrar sukazo Saudiyyar ita da Ummeen da Aunty Nawwara. A Nan ma Saudiyyar Zahra taga gata iya gata Dan kowa Nan Nan yake da ita, Dan kanwar Ummee Hanifa sosai ta kafe sai dai a bar Mata Zahra ta tafi da ita Istanbul inda take aure Wai Bata yarda da zaman Nigeria ba. Ankai ruwa Rana da ita kafin ta hakura Dan da gaske Alhaji Jafar ya bude Mata aiki Dan cewa yayi idan irin haka za'a ringa yi bazai Kara bawo musu ita ba saidai duk Mai son ganinta taje ya ganota Kamar yanda Ummee keyi, hakuri aka ringa bashi. Saida aka Kai Zahra makka suyi kayi umara sannan suka fara Shirin baro kasar.l Sayyaya dai Zahra ta shata Dan wasu kayan sai a awon cargo akayo musu su. Sarkar gwal da warwaro zobe kuwa kirar Saudiyya da Dubai zuwa kirar Bahrain sun Kai kala goma duk dai dai size din ta sai na Ammah biyu na Hasana ma biyu shi kanshi Alhajin anyone mass goma Sha Tara ta Arziki. Ranar da zasu dawo Zahra Tasha kuka haka kakarta Ummee,har jidda sukayo musu rakiya Basu suka tafi ba sai da jirgin su Zahra ya tashi a sararin subahanahu wata'ala. Saukar safe sukayi anan suka samu Bala direban Alhaji Dan Bai fadawa kowa sun taho ba sai Balan kawai, sau da yawa idan ya fada gashi Nan a hanya hankalin Nanna baya kwanciya har sai ya iso. Lokacin da suka shigo harabar gidan suna tsayawa Zahra to garzaya cikin gida tana fadin "Ammah!!! mun dawo". Da gudu Hameeda ta fito daga part dinsu, rungume juna sukayi suna ta tsallen murna Sai jikin zahra Hameedar ke shafawa gani take kamar canza Mata Zahrar akayi. Da sauri Ammah ta fito tana "fadin wa nake gani ne haka Kamar bakin saudiyya zuwa ba notice?" Alhajin ne ya Bata amsa. "Surprised din ki mukayi ko Zahra na?. Kai ta gyada masa. Kayansu ne su Bala da Mai gadi suka Fara shigowa dasu kafin Alhajin ya nufi part dinsa na cikin gidan yayin da Ammah ta rufa Masa baya. Har yayi wanka ya shirya Mama Bata shigo ba, har ya tambayar Ammah yayi Ina Rabi'a ? Tace Masa tana ciki watakila ko barci take. Kusan kwana su Zahra sukayi tana baiwa Hameeda labarin abinda ta gani da inda sukaje a Jordan da saudiyya, wurin karfe biyu Ammah ta tashi zatayi nafila ta jiyo su suna Hira a dayan bed room dinta lokacin wuri biyu da rabi na dare, leko tace su kwanta basu san dare yayi sosai ba. Washe gari an baje tsarabar Zahra an baiwa kowa dai dai gwargwado. Amman tsarabar Hameeda daban take Dan har sarka Saida ta baiwa Hameedar. Basifi sati biyu da dawowa ba jarabarsu ta fito ta Federal inda Zahra ta samu F.G.G.C KAZAURE yayin da Sulaiman ya samu F.G.C DAURA, Hameeda F.G.C AZARE. Salma ce kawai bata samu ba a cikinsu. Sunyi murna Kuma sunyi bakin cikin rashin samun makaranta daya duk an watsa su Abban Kuma da ya Hassan sunce kowa ya tafi inda ya samu, ita Hameeda Bata da damuwa tana gida, su Kuma duka 'ya'yan Ammah duk sun fita waje danma hanyarsu daya sai an aje Zahra a karasa da Sulaiman. Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka dauko hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu. Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one. A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Mata "sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa". Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "ni sunana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?". Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C. Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar gasu Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah. Lokacin da akayi hutu Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman. Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsokana. Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha. Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga FGC AZAREN itama a ss1. A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida. Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai. Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin uba namiji ba itace komai nasa. Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'a, cikin ikon Allah sai komai ya daidaita. Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka dinki ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini. Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito. A kasa suka taka suna Hira har sulaje gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane. Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta fito. Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa. Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar. Gaishe shi sukayi su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa". Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da zafin Kasarmu". Ta fada tana dariya. Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?" Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Allah." Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi. Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu. Har kofar gida ya kawosu suna tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana". Dan murmushi tayi tana fadar. "Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi" Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya takura Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra. Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo ta wuce dakin su. Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu. Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka bijiro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira. Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izininsa duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma nemi Jin wacece daga cikin yaran suka gada Masa zahra ce, nan ya amince musu da addu'ar Allah ya hada kawunan su. Tun daga lokacin Sahal ya Fara zuwa gurin Zahra cikin ikon Allah tayi na'am dashi Basu Dade sosai ba sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a unguwar yasan irin soyayyar da sahal yakewa zahra kusan Kullum da yamma Yana nan makale da ita, a haka har manya suka shiga maganar aka tsaida lokaci wata shida inda zasu tafi Colombia inda yake hada masters dinsa ita kuma zata Fara nata degree din. Anyi lefe na garari Wanda ya dauki Baki fiye da tunanin Mai tunani, an kashe kudi Kamar ba'a San zafinsu ba. Lokacin da bikin ya rage baifi saura wata biyu ba sai lamarin ya Fara canzawa kwata -kwata Sahal ya rage zuwa gurin Zahra haka ma sai a kwana a wuni Bai kirata ba, duk wani zazzari da yake na bikin su events din da yake ta faman damun zahra da maganar duk ya daina Kai tafi-tafi sai ayi kwana uku hudu har sati Bai kirata ba, da farkon abin tana kiransa taji ko lafiya a yanayin yanda yake amsa Mata wayar saita hakura da Kiran nasa, tun Ammah na zuba ido har ta samu Zahra a wani dare ta tsareta da tambayar ko wani Abu ya hadata da Sahal ne? Ta Bata tabbacin ba abinda ya hadasu sai dai ta fada Mata yanda suka ringa yi dashi a kwanaki idan ta Kira shi. Addu'a Ammah ta Bata tace ta ringa yi itama zataci gaba da yi, Mata sannan ta umarceta da kada ta Kara kiransa a wayar ta zuba ido kawai. Duk abinda Ammah take na shirye-shiryen Baki Bata fasa ba, tayi waya mutanan Jordan ma sunce suna Nan tafe Amma a daure a turo Zahra Kamar saura wata data bikin. Ba'afi sati daya da waya da kakanninta na uwa ba sakon kayan dakinta ya sauka Nigeria daga Istanbul kayan da suka gigita Mama Dan ba kayan Wasa bane set din gado har hudu kujeru set uku bayan electronics kuwa wasu har ba'a San amfaninsu ba sai dai idan an duba manual din. Alhaji Jafar yayi fada Kamar ya Ari Baki lokacin daya Kira Abbie akan danme zasuyi Masa haka toshi meye amfaninsa da bazasu Bari yayi Mata kayan dakin ba. Hakuri Abbien ya shiga bashi akan su basuyi Dan su Bata Masa raiba, sunga abinda ya kamata suyiwa diyar Najwa kenan. Ammah da Mama Alhaji Jafar ya Kira ya fada musu tunda an Riga an yiwa zahra kayan dakin da duk abinda ya kamata to ga fifty million Nan ya baiwa Zahra idan komai ya nutsa saita Fara business na abinda take son sayarwa sannan ya Bata shanu biyar. Kuka Ammah ta saka saboda Dadi ta rasa bakin da zatayi Masa godiya, yanda take dawainya da wannan marainiyar Allah Bai taba gajiyawa ba. Mama ce ta Ari bakinta tana ta yiwa Abban godiya da saka Albarka sai faman dariya tace bakinta yaki rufuwa, tun Ammah na ganin dariyar farin ciki ce har ta Fara wani tunani na daban, Nan da Nan ta Kori shaidan akan abinda zuciya ke sawwala Mata. Lokaci na Kara tafiya daukewar ma'amala na Kara yawaita a tsakanin Sahal da zahra, yanzu ta Kai kwata-kwata sun daina waya dashi, ana saura kwana talatin da hudu a Fara biki Wanda yayi daidai da saura kwana uku zahra da Hameeda da Abdul Hakeem su tafi Istanbul. Dan direct gurin kanwar Ummeen Hanifa zasu tafi daga baya su Ummeen sun samesu a can, idan an Gama komai su rankato Nigeria Dan da gaske Ummee ta shiryawa bikin sosai. Washe gari, tunda gari ya waje Mama ke Kai kawo tsakar gida duk da ba aikinta bane ba Kuma halayyarta bane hakan. Yayin da a bangaren Ammah ta rasa me yake Mata Dadi duk kasala ta baibayeta jinta take Kamar ma zazzabi na neman rufata... 💋❤ 💋❤️ ✨AUREN HUCE HAUSHIN ✨️ 💋❤️ 💋❤️ STORY & WRITTEN BY MAMAN FATIMAH. 🔷✨PAGE ELEVEN✨🔷 (11) ________Misalin Sha biyu da rabi na Rana kawar Mama kuma Aminiyar Asabe tazo gidan macece wayayya Mai kisisina Bata fiye zuwa gidan sosai ba sai lokaci lokaci, ta Dan jima a dakin Ammah suna hira har tana tsokanar zahra da Amaryar gobe ana dariya. Part din Mama ta shiga suka kule a master bedroom dinta. Batafi awa daya da zuwa ba, wasu Mata suka shigo gidan lokacin Ammah tana bangaren Abba. Zilai Mai aik cei ta leko tana fadin "uwar dakina anyi baki kuwa ko Ammah zaki yiwa magana Naga bakin nata be" Mayafi karami ta Dora a saman gashinta da tayi parking dinsa har wajen kugunta Yana reto Baki sidik dashi jikin Nan nata Kamar ka taba jini fito. Lekowa tayi tana musu sannu da zuwa tare da gaishe su tana fadar "ku shigo daga ciki Bari na Kira Ammar". Ta fada tana zura silifar a kafarta. Daya daga cikin su ukun ne ta tabe Baki ta kauda Kai tana fadar "kirawo ta tazo ba sai mun shiga ba tunda ba Zama mukazo ba" Ita dai Zahra gaba tayi yayin da su Zilai masu aiki suka zuba musu idanu suna kallon kallo ya junansu Dan daga Jin lafazinsu sun San ba abin Arziki ne ya kawosu ba. Kafin Ammah ta fito daga bangaren Abba sahura Daya Mai aikinta ta leka ta fadawa Mama anyi baki. Da ita da Asaben suka fito Asaben na fadin "lale barhabin kushigo Mana kun tsaya daga wajen" Wata ce daga cikinsu Bata farkon da tayi maganar ba tace "A"a Hajiya ba Zama mukazo ba munzo ne mu karbi kayan lefen da muka kawo na Sahal yace baya yi akai kasuwa". Lafazin da Ya yiwa Ammah sallama kenan lokacin data fito Zahra na biye da ita. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Abinda Ammah ta fada kenan a zuciyar ta Nan da Nan wani jibi ya taso Mata. Salatin Mama da Asabe ne ya fito da Alhajin daga part dinsa yayin da su Zilai sukayi cirko-cirko duk wuta ta dauke musu Dan maganar tasu ba karamin razani tasa a zukatansu ba. A hankali ya karaso kusa da Ammah Yana tambayar meke faruwa ne kafin tayi magana Mama tayi tsagal tana fadin "wane irin cin mutunci ne Alhaji ba laifi tsaye bana zaune zasuzo suce a Basu lefensu Wai auren amfasa". Ta karasa fada tana fashewa da kuka tana maganganu, ita kuwa Ammah ba abinda take sai ambaton Allah yayin da Zahra ta nemi gefen inda aka shuka filawoyi ya zauna Dan ji tayi Nan da Nan jiri Yana nema kayar da ita, itama bakinta ba abinda yake sai ambaton Allah. Kallo Daya Alhaji Jafar yayiwa Baki ya kawar da kansa Dan da alama da rashin mutunci suka shigo gidan. Gyaran murya yayi kafin yace "Masha Allah munji sakonku Amma Dan Allah ku koma kuce musu zuwa anjima inshallah Allahu za'a dawo da duk wani Abu daya kasance nasu ne har sadakin da suka kawo Allah yasa hakan yafi Alkhairi". Yana Gama fadar haka ya juya dakinsa ya barsu a Nan a teaye, Dan dukkansu ba karamin kwarjini yayi musu ba. Ammah part dinta ta nufa duk kwakwar mutum baze taba Gane Yanayin da take ciki ba.Dan Allah yayi Mata wata irin zuciya Mai iya danne bacin Rai da wuya ka Gane fushinta tana da hadiye fushi sosai, dakin suka bita suna Bata magana Mama sai sharbe take tana Dan Allah wannan wane irin cin zarafi ne da tazarce ace saida komai ya kankama sannan za'a bullo da wannan cin zatafin dan a wulakanta yarinya har a ringa yi Mata wani gani -gani aga Kamar wani Abu tayi yasa aka fasa". Sai lokacin Ammah tayi magana tana fadin "ba komai Mama Daman can haka Allah ya nufa ba mijinta bane Kuma maganar mutane su ringa ganin Kamar wani Abu marar kyau ne yasa aka fasa na barsu da Allah yayi Mani maganin komai, ba komai haka Allah ya nufa rubutaccen Al'amarine baya goguwa". Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta sun jima a falon suna tattaunawa kafin su koma dakin mamar su Zilai kuma suka nufi in da Zahra tace zaune suka dinga Bata magana duk da Bata want rude ba a nitsenta take. Duk wannan kwamacalar da akayi su Hameeda da Salma basa Nan sunje Aiken Mama. Tunda Alhaji Jafar ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye Bai taba zaton karamar magana daga gida irin Honorable ba Amma ya hanasu kayan ne Dan ya tabbatar da daga Ina maganar take shin da sanin uban yaron da waliyayansa ko Babu Dan yanda sukayi komai cikin girma da mutunci

Chapter 8 of 31