Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kamata ko baza'ayi auren ba to a rabu cikin mutunta juna. Su malam Bukar da Yayan Alhajin Wanda suke 'yan maza Alhajin ya Samu da maganar basuyi kasa a Gwiwa ba zuka nufi gurin waliyyan Sahal sai dai maganar haka take Dan sun tsame ma hannunsu daga lamarin tunda iyayensa Basu da lissafi, Wai yaron ne yace musu shi baze iya auren Zahrar ba yanzu ba wadda ya tsana kamarta duk duniya". Lokacin da suka dawowa da Alhajin wannan labarin ransa yayi matukar baci, a ranar aka maida duk wani Abu da yake mallakinsu ne. Sai dare Abban ya Samu kebewa da Ammah in da ya ringa tausarta da kalamai masu Dadi har ta Samu ta Samu nutsuwa Amma fa kasa kwana tayi a dakin nasa. Lokacin data dawo daki Zahra Bata tafi nasu bangaren ba tana dakin Amma a kan gadon tayi rigingine idanuta a rife hawaye na zurarowa daga gefen idon wani Abu yake Mata yukuki a zuciyar ta. Har Ammah ta bude kofa zahra Bata sani ba saida ta zauna a kiss da ita taji shashhshekar kukanta kasa -kasa. "Tashi zaune magana zamuyi". Daga sama taji maganar Sam bata San Ammar ta shigo ba. Ba musu ta tashi zaunen tana koge fuskarta da tayi wajir. "Meye dalilin da Sahal ya fasa Aurenki ko ya sanki 'ya mace ne". Cikin tashin hankali marar misaltuwa Zahra ta dago ta kalli Ammah kafin ta fasa kukan da take dannewa tana na zuci. Kai ta shiga girgizawa tana wani irin numfashi nKamar wadda zata shide. Kafin Allah ya batan ikon bude bakinta ta magantu. "Wallahi Ammah ban taba abinda kike tuhumata ba Koda wasa wallahi zan rantse Miki da Alur'an a bani zanyi Alwala in ratse, idan na taba Zina Ammah Allah ya haramtamin shiga Aljannarsa ranar Alkiyama" Ta fada tana wani irin kuka Mai taba zuciyar Mai sauraro. "Shitttt.....kada na Kara Jin wata magana makaranciyar wannan daga bakin ki. Ba zarginki nakeyi ba na kasa samun nutusawa ne tun lokacin da sabbin halayensa suka Fara fitowa, nake cikin zulumi da taraddadi saboda sanin yanda rayuwa ta Zama abinda ta zama, ba komai kansa yayiwa ke kuma Allah yayi Miki Albarka ya bakin Wanda yafi Sahal". Bata iya amsawa a fill ba sai a zuciyar ta. Tun bayan faruwar lamarin Zahra ke cikin damuwa Dan ma Haneeda tana tausarta da kalamai na kwantar da hankali. Ammah ta Kira su Ummee ta fada musu komai sun so kwarai zahrar taje Amma Alhaji Jafar yayi uwa yayi makarb'iya akan suzuzo idan hankali ya kwanta, da haka suka bar zancen. A Dan tsakanain ne Aunty Hasana tazo, sun Sha jajantawa sosai da Ammah itama sai da ta tsare zahra da tambayoyi kala kala, daga karshe ta Kare da nasiha Mai tsoratarwa sosai. Lokacin da zata koma Jos ta nemi zata tafi da Zahra Abban bai Hana ba Yana ganin idan tayi nisa da garin zatafi Samun kwanciyar hankali. Zamanta a Jos Mai Dadi ne Dan daga baya ma fafutukar nemar Mata admission mijin Aunty Hasanar ya Fara ba'a samu wadda ake so ba, sai diploma ya nemar Mata a wata private school ta Fara computer science. Hankalinta ya kwanta sosai ta cire soyayya daga zuciyar ta Sam taqi ba kowa fuska akan soyayya duk da yanda ake kawo Mata Rida. Ranar wata litinin sun Gama lectures dinsu na safe suna zaune da wata course mate dinta 'yar kabilar Tiv suna wani Assignment jininsu ya hadu da jannifer sosai Dan har gidan Aunty Hasana tana zuwa idan zasuyi wani aikin. Bayan sun Gama ne suka nufe caf'e na cikin makarantar a cire musu hard copy din aikin suka tarar da cinkoson mutane dole tasa suka fito waje ayi musu. Har sun Gama sun fito suna niyyar tsallaka titi ne wata mota Mai azabar kyau ta tsaya dai dai inda suke tsaye. A hankali na ciki ya sauke tinted glass din motar, wani guy ne da gani hutu ya ratsa shi sosai, murmushi yayi musu idonsa na kan zahra Yana fadin "sannunki" Jannifer ce to amsa masa Dan tana Jin hausa Kamar jakar kano. "Yauwa sannunka" ta fada. Kofar ya bude ya fito Yana sanye da kananun Kaya,fari tas dashi kamar irin ruwa biyu din Nan half cast Dan sumarsa a nannade take kamar irin ta buzaye din Nan. Cikin kwarewa da yadda da Kai kalli jannifer Yana fadar "Naga kawarki ne inso da fatan zakiyi min campaign". Dariya tayi tana kallon Zahra wadda tayi kicin kicin da fuska Kamar zatace wayyo Allah. "Gaskiya na tafi tunda Baki da aikin Yi ke saiki zauna". Zahra ta fada tana nufar titi ganin an Sami space din tsallawa. Jannifer da Dan jima dashi kafin ta shigo cikin makarantar, Koda ta shigo Bata yi Mata maganar komai ba har suka Gama lacture dinsu suka tashi. Direban su Aunty Hasana ya dauke su ya ajiye jannifer a hanya kasancewar su zahra sun gaba dasu Amma hanyarsu daya sau da Daman sukan tafi tare ranar da jannifer Bata zuwa shagonsu. Ranar Saturday misalin hudu da rabi haka su zahra da yaran Aunty suna compound din gidan tana Dora Yara kan lilo marry go round suna Wasa kusan duk weekend a Nan suke hutawa da yamma tunda islamiyyar safe suke zuwa a weekend. Mai gadi ne ya nufo gurin da suke Yana fadin Zahara'u ki fadawa yallabai Yana da bako a waje". Auntyn ta fadawa Abban su Faruq Yana da bako inji Mai gadi. Lokacin daya fito yayi mamakin da baiga bakon ba ya nufi gate Yana tambayar Mai gadi, shine yace "ni ne na hana ya shigo tunda yace bakasan da zuwansa ba bilhasal ma yace baka sanshi ba" Kofar Mai gadin ya bude masa ya nufi gurin da motar take yayin da shi kuma na cikin ya fito. Da gaske baisan yaron ba, hannu ya bashi sukayi musahiha sai Kuma sukayi shiru Ya Aliyun ne mijin Aunty Hasanar yace Masa "ko kaine maisallama Dani?". "Eh nine"sai Kuma ya danyi shiru. Ya Aliyun ne yace "my friend pls talk feel free with me". Nan yayi Masa bayanin yaga Zahra ne Yana sonta shine ya biyota gida, ya fada masa sunansa MUNEEB mahaifansa Kuma Alhaji Salman Mai fata. Kallonsa ya Aliyu ya karayi yayi mamakin yanda d'a Kamar na Alhaji Salman Mai fata yake da irin wannan tarbiyya ganin yanda mahaifansa yake da mahaukanta kudi Kuma yasan 'ya'yansa sosai Amma da yawansu gata yasa sun lalace basa ganin kan mutane da gashi. Ya Aliyun yaji dadi sosai ya Kuma bashi damar zuwa gurin Zahrar sannan ya Dan fada Masa wacece Zahrar a gurinsa. Lokacin da ya Aliyun ya koma bayani ya yiwa Aunty Hasana na abinda ya faru itama ta bada goyon baya tasan ko yanzu Zahra tayi gaba Allah ya Bata Wanda yafi Sahal Dan ba karya ba hadi a tafiyar. Da dare Aunty ta Samu zahra da maganar da farko tuburewa tayi akan ita Bata so saida Aunty ta fito Mata ta bayan gida sannan ta fashimci abinda Auntyn take son ta Gane. Washe gari Aunty har da ita aka hadawa MUNEEB abin tarba, Zahra ta Dade tana mamakin yanda akayi yasan gidan su Amma data Zama very curious sai ta gano duk yanda akayi jannifer ce ta bashi address dinta. Yau ma da yamma yazo, falon Ya Aliyu aka bude Masa yayin da Mai aikin Aunty shema'u ta Kai Masa abin tarba. Wata straight gown ta saka ta atamfa glitter Mai ruwan peach colour sai madaidaici gyale kalar lemon green irin touching din jikin atamfar sai takalmi shima lemon green din plat Mai kyau. Bata daura dankwalin kayan ba. Ta fesa turenta Amber oud gold, tun kafin ta karaso kamshin ta ya fada Masa zuwanta, kofar ya zubawa idanu ai lokacin data shigo da sallama Saida ya Dan samu shock na wucin gadi Ashe ranar ba inishin Zahrar ya gani ba yanzu ne yaga zahirinta, a kasa ta zauna kan carpet tana gaishe shi kanta Yana kallon kasa. Nan ya gabatar Mata da kansa da abinda ya kawo na son aurenta, bai matsa Mata na lallai sai yaji ra'ayinta a sannan ba shima bai jima ba ya tafi, bayan ta shigo ne Mai gadi yayi knocking a kofar falon shema'u ta bude manyan ledoji ne ya Mika Mata guda biyu yace a bawa Zahara'u inji bakonta. Tun daga lokacin Koda yaushe Muneeb yana hanyar gurin Zahra,r tun tana dari dari dashi har ta sake, shi mutum ne Mai saurin shiga Rai Yana da wasu Qualities da zasusa asoshi. Kafin su rufe wata biyu sunyi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a family din Mubeen yasan da zaman Zahra haka itama nata sun San Muneeb Dan har Azare yaje ya gaishe su da ashirin bama sha tarabta Arziki ba,har Saida Abban su yayi Masa fada sosai akan kada ya Kara musu haka in dai Yana son su Shirya. Sun daf da Gama diploma dinsu Iyayen Muneeb sukayi maganar aure, ba Bata lokaci aka saka Rana ba'a wani ja lokaci ba Mai tsawo ba, abu kama-kama shima Kamar na baya abun ya shashence ba wani cikakken dalili haka Nan Rana tsaka Muneeb yace ya fasa akayi juyin duniyar Nan yace shifa aure ba dai da Zahra ba komai za'ayi, dole aka hakura Dan shi cewa yayi har kayan ya bar Mata saidai abinda iyayenta Basu amince ba kenan. Fadin halin da zahra da su Ammah suka shiga bazai misaltu ba, Dan hankalinsu yanzu yafi tashi fiye da wancan lokacin. Ammah taso kwarai zahrar ta koma Azare Amman Maman Ya Aliyu ta roki Alfarmar zata Kai zahra gurin masu Islamic chemist a gani ko namijin Aljani ne ya aureta. Ammah ba tayi musu ba sai godiya tayi sosai, sunje harda Aunty Hasana anyiwa Zahra tambayoyi ba alamar Aljani a jikinta sai dai sun fada musu da alamar sihiri a tare da ita Amma ba sosai ba, Nan suka bada magunguna Hajiyar ta biya suka dawo gida. Jannifer ma tayi bakin cikin abinda ya faru taso Zahra ta Bata dama taje garinsu ayi mata wani Abu akan idan ma wani ne yake lalata lamarin auren zega abinda ze same shi. Nunawa tayi Bata so ita haka Allah ya tsara Mata wannan qaddarorin Kuma ba makawa sai sun sameta. A haka har suka Gama diploma dinsu kafin Aunty Hasana ta mayar da Zahra Azare. Haha rayuwa taci gaba da gudana, duk wani buri akan aure Zahra ta cire shi Bata kula kowa duk iya nacin mutum Bai isheta kallo ba, wani lokacin har fada suke da Hameeda akan rashin kula samari sai dai sau da yawa tana Mata uzuri akan irin yanda fasuwar aure take walagigi da ita. Zama ya Mika lokacin har anyi wurin wata Tara da fasa aurenta da Muneeb. Wani yammaci suna zaune a bayan part din Ammah ita da Hameeda da Mujiba data shigo musu yawan yamma suna hira Kiran ya Abdul Hakeem ya shigo wayar Hameeda Yana tambayar suna ina ne ya shigo Bai gansu ba. Inda suke ta fada Masa suna niyyar tashi ya zagayo bayan, a tare suka gaishe dashi ya amsa Yana gaisuwar tasu yana fadin "Congratulations" "For what Yaya?" cewar Zahra. Irin Brown din envelope din Nan babba ya Mika Mata Admissions letters ne guda biyu a ciki na Salma da Hameeda duk sun Sami gurbin karata a federal University Dutse jigawa state (F.U.D). Cikin murna ta rungume Hameeda tana fadin "congratulations sister". Kafin ta sake ta tana Mika Mata takardun, ai tana arba da wannan abin Arziki ta Diba a guje tana fadin"thank you Yaya Allah ya saka maka da Alkhairi". Bayan ta wuce ne zahra ma ta Kara Masa godiya sosai. Kujerar da Hameeda ta tashi ya janyo ya zauna alamun dake nuna magana Mai mahimmanci zeyi da ita. Ganin haka yasa Mujiba tashi tana fadin "Yaya sai anjima". "Dawo ki zauna ba Zama zanyi ba.magana zan fada Mata kawai" A takure ta koma ta zauna. Kan Zahra ya maida kallonsa "kina jina?" Kai ta gyada Masa alamar eh. "Good" ya fada. "Ina ga Nan da one month ko three weeks kema Zaki wuce Zuwa Turkey daga can Kuma idan komai ya daidaita Zaki wuce syprus inda Zaki hada a degree dinki, idan kin tuna Kamar two months da suka wuce ai na karbi komai naki to Mama Hanifa ce ta bukata a tura Mata a she makarantar zata nemar Miki taso a Samu a Nan turkey din to ba'a samu ba, ita kuma Bata son a Kara Bata lokaci, shine ta yiwa danta magana tunda a can yake aiki da ofishin jakadancin turkiyya na kasar Kuma ma Nan ne kawai Mama Hanifar ke ganin yafi kusa da istanbul din". Ba Zahra kawai ba hatta Mujiba tayi murna kwarai da gaske gatan da za'a yiwa Zahra kenan a irin wannan lokacin na a rabata da kasar gaba daya Kota Samu peace of mind. Godiya ta ringa yiwa ya Abdul Hakeem din harda 'yan hawayenta na Dadi. Gashi Ammah Bata Nan taje Jimeta gurin biki, taso tana Nan ta kwanta a jikinta suyi sharing din farin cikin. Har ya Abdul Hakeem din ya kai kwanar da ze fita ya juyo Yana fadin "don't talk to anyone, keep silent pls, nasan Mujiba Bata da problem shi yasa na fada a gabanta". Yasa Kai ya wuce. Kallon junan su sukayi suna son banbance maganar Ya Abdul Hakeem. 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ MAMAN FATIMAH PAGE TWELVE (12) __________A cikin qanqanin lokaci aka Gama yiwa su Hameeda shirye - shiryen tafiya makaranta Dan sau biyu suna Zuwa jigawar akan registration din. Sai wannan ciccira kai salma keyi tana sakin maganganu bare idan suna dakinsu su kadai ta dinga fadin magana kenan, ko ci kanki zahra Bata ce Mata sai ma wani lokacin Hameeda ke kwabawa Nan da Nan Kuma su hau sama da ita. Ranar da zasu tafi harda ZAHRA a 'yan rakiyar, Mama ma taso zuwa Abba ne ya hanata ya Kama fadan me zatayo. Har hostel Zahra ta rakasu Lokacin da zasu taho ne Hameeda ta Fara share hawaye itama zahra ta Kama, Saida ya Hamza yayi musu Jan Ido suka daina kukan, Yayin da Ya Abdul Hakeem yake musu dariya Yana fadar "Banda tsabar shagwaba ta lalacewa har wani kuka kuke Kamar wasu 'yan J's one". Wani kallo ya ai kawa zahra na Baki Fara kuka ba.sai kin ganki a tsakiyar masu jajayen kunne tukunna Dan ma dai kema samman kalne ya gada a zuciyar sa. Sai bayan magariba suka dawo gidan. Ba'a fi sati biyu da tafiyar su Hameeda ba visa din su Zahra ta fito ita da Abdul Hakeem. Sai ana ya gobe zasu tafi Ammah ta fadawa Mama. Ai Kuma tayi korafin abin Dan har Alhajn ta fadawa yace shima jiya yake Jin labarin tunda Saida komai ya kankama sannan suka Kira suka fada Masa Dan kada ya Hana. Da safe Bala dureba ta dauke sai kano inda zasu tashi. Satin Abdul Hakeem hudu a can Dan Bai taho ba Saida ya raka Zahra har syprus din a gabansa komai ya kammala ranar da ze tafi Zahra tayi kuka Kamar idonta ze fita sai a sannan taga ba karamar wauta tayi ba data yarda da wannan karatun, dadin ta daya da uncle Haisam a kasar ko banza tana da gurin zuwa a debe Mata kewar gida. Ta Fara karatu cikin nasara Bata da wata matsala ta zahiri saidai sau da yawa tana shiga dogon tunani akan al'amuranta ta rasa Gane daga Ina ne ake samun irin wannan akasin? matsalar dai iri daya ce, Kuma salon tafiyar iri daya ce sai Dan banbancin da baza'a rasa ba. Suna yawan waya dasu Ammah da mutanen Jordan, lokacin data Kira Hameeda mita ta ringa yi Mata akan tana boye Mata wani Abu tunda gashi Saida ta bar kasar kana ta Kira ta. Da kyar ta fashimtar da ita abun ne yazo da gaggawa itama Bata sani ba Saida komai ya Zama ready, Kuma tayi ta try din ta sameta Bata Samu ba lokacin ana fama da matsalar network a area dinsu. Zahra najin dadin Zama a kasar duk karshen sati a gidan uncle Haisam take yin weekend din ta, sai Monday da safe motar Embassy take dawo da ita. Tsakanin syprus science University din wadda take kyrenia city a arewacin syrups din da capital city din dake Nicosia tafiyar kilometers talatin ne, kawai daga Baya ma da uncle din cewa yayi ta baro cikin makarantar ta dawo gidansa kawai da Zama sai a ringa kaita kullum itace taqi tana ganin Kamar abun da wahala yau da gobe sai Allah daga nesa nesa dai. Yau ma Monday da wuri motar Embassy din ta kawo ta, tayi gaba da wasu daliban zuwa mabanbantan makarantu inda suke karatunsu.Ganin da saura Kamar awa aya da rabi kafin su shiga lectures yasa ta wuce hostel Dan ta aje kayan da tazo dasu. Tana cikin tafiya tazo gota wani hostel Kamar a mafarki sai taji Kamar ana hausa a dakin abin ya Bata mamaki tayi Kamar ta koma ta duba sai dai tayi gaba tunda bin kwakwkwafi haramun ne. Lokacin da suka Gama lectures din Bata koma hostel ba, karatu suka zauna sunayi da wata course mate dinta 'yar kasar Lebanon Asseyeh tasu tazo daya sosai saboda itama akwai nacin karatu ga Kuma kwanyar Allah ya hore itama, uwa uba ga rikon addini tunda su dai kasar sai a hankali kawai culture din ta rinjayi addinin, Dan wasu Ma sai kaga suna sallah zaka Gane musulmi ne. Yamma likis su Zahra suka nufi hostel, haka nan Zahra taji tana son karabi ta wurin inda taji ana magana da Hausar nan, can ta nufa bayan sun rabu da Aseeyeh. Very lockly kuwa tayi Dace da wata daga ciki ta fito tana waya bahaushiya sosai.A shape ce a jikinta ta atamfa sai karamin hijabi a jikinta da alama Kamar fita zatayi.Dan tsayawa zahra tayi har ta karasa wayar, cikin nuna zallar farin ciki zahra ta nufeta tayi Mata sallama. Da sauri ta juyo Jin an Mata magana da Hausa cikakkiya. "Wa'alaiki Salam" yarinyar ta amsa Mata tana kallon zahrar da murmushi itama a fuskarta. "Masha Allah wallahi naji dadin ganinki kema daga Nigeria kike". Zahra ta tambaye ta. "Eh daga Nigeria muke muna da Dan yawa zamu Kai goma". Mamaki ne ya Kama zahra ganin Bata taba ganinsu ba Koda wasa. "Ikon Allah! Amman dai baku Dade ba ko?" Kai ta gyada "Mata gaskiya Kam ai ba school daya muke ba mu a Nan mu hudu ne, sauran suna different Universities ne on transfer mukazo nan daga Sudan tunda can rikici ya d'ai d'aita Qasar. Zo mu shiga ciki ki gaisa da sisters Dina kafin na dawo zan fita na samo Ko fizza ne yau bamuyi girki ba". Ta fada tana juyawa ciki, bayan ta zahra tabi suka nufi ciki. "Khadijah ! Fatima,! Sajida! Kuna Ina ku fito gashi mun Samu qaruwa". Kowacce barin abinda take tayi ta nufo kofar tana fadin "Anisa menene?". Ai kafin tayi magana Zahra tayi Arba da sajida Musa, sajidar ta ta FGGC KAZAURE. Cikin wani irin farin ciki suka rungume juna Zahra sai kuka Dan wani abune da Bata taba zata ba robonta da sajidar tun suna cikin bala'in Sudan kafin wayar sajidar ta salwanta shi kenan suka daina Jin juma Amma kullum zahra da fargaba take kwana har zuwa lokacin da ta Samu labarin dawowar su sajidar a bakin Maryam Suraj wata kawarsu. Kallo saiya koma sama Wai shaho ya dauki giwa ita Mai kawo bakuwa sai duk suka Zama 'yan kallo. Hannun zahra sajidar ta Kama ta nufi bed in ta da ita tana fadin "wannan wace irin ranar farin ciki ce bestie wallahi ranar nan tana daga cikin ranekun da bazan taba mantawa dasu ba cikin tarishin zamana a syprus, pls bestie talk ya akayi haka ta faru Dan Allah kece ko gizo idona yake mini ne Dan Allah kiyi magana". Ita dai zahra ba baka sai kunne, ai ita nata mamakin yafi na sajidar sau dari idan da Wanda Allah ya yiwa gyadar dogo ai ita ce, ba zato ba tsammani Allah yayi Mata irin wannan suturar bama 'yan Nigeria ba A'a aminiyar ta sukutun ya kawo Mata kasar, ba abinda zata cewa mahalicci sai godiya take a Nan tayin sujudushshukur ga Allah. Sai da ta goge hawayenta sannan ta Samu damar magana suka gaisa da sauran yayin da Anisar ta cire hijabin tana fadin "Ai Kuma saidai kowa ya hakura da cin fizzar Dan na fasa fitar kawai ayi abinci tunda Naga bakuwar tamu ce ko sister" ta fada tana kallon sajida. "Kwarai kuwa ai dukkanku kowa ya kwana da sanin Zahra Muhammad sani ko?". Gaba daya suka zubawa Zahra idanu suna fadin sosai ma kuwa, niba har gaisawa munayi ba some times idan Kuna vedio call lokacin muna Sudan" inji Khadijah. "To ai ita ce gata a gabanki zahiri" Khadijah ta Dade tana mamakin abun ita sai taga Kamar canza Zahra akayi tasan dai yesss ba karya zahra Mai kyauce na a bugi kirji a fada, amma sai taga wannan Kamar ma Bata taba hada dangantaka da 9ja tamu ba, komai nata classic ne. Nan suka baje hajar hirar yaushe gamo, har kusan karfe goma na agogon kasar suna tare anan su sajida suka fada Mata gwamnatin tarayya ce ta dawo dasu Nan tunda suna under scholarship ne shine aka rarrabasu kasa kasa su Allah yasa suka shigo cikin daliban da aka kawo Nan din. Har daki suka raka Zahra a Nan ta Basu fizzar tunda Daman tazo da ita daga gidan uncle Nan ma sun jima kafin su koma. Ai tun daga ranar wata nutsuwa da kwanciyar hankali suka Samu kyakykyawan muhalli a zuciyar Zahra, haka itama sajidar duk da Daman ita tana da masu dauke Mata kewar gida, Suma su sajidar sau da yawa suna bin Zahra a wasu weekend din zuwa gidan uncle Haisam din Amma su basa kwana duk da irin nacin da zahrar ke musu. A haka karatunsu ya Mika har sukayi exams, Mama Hanifa taso Zahra taje Mata tayi hutu Amma Haisam yace tayi hakuri sai hutun karshe session. A haka suka Kare hutunsu suka Dora da karatu, ba Sajida ba hatta su Khadijah suna Jin dadin Zama da zahra gashi Sam abin duniya Bai rufe Mata ido ba, Dan ta ko'ina kudi ne ke sauka a Account din ta ba daga 9ja din ba, ba daga Jordan ba, ba daga turkey ba, kowa kokarin farantawa zahra yake zuwa lokacin tayi wani irin mahaukacin kyau na ban mamaki ga wayewa da wayon zaman duniya ta Kara Zama 'yar gayu Kamar me Dan ba karya matar Uncle Haisam Yar gayu ce sosai kamar Auntyn ta Hasana tasan yanda ake tattalin jiki matuka. Har zuwa lokacin ba ruwan Zahra da saurayi bil hasal ko aboki namiji Bata dashi, akwai wani Dan Syria Omer yaso Zahra Kamar kaddara Amma ta shafawa idanunta toka tace ba wannan maganar yace to su Zama friends Nan ma tace lah lah. Dole ya hakura saindai duk inda zasu hadu sai yayi Mata magana idan abu ta saya duk yawan kudin shi ze biya. Lokacin hutun karshen shekara Zahra taso zuwa Nigeria tunda taga su sajida nata Shirin tafiya, ta kwallafa Rai sosai akan zuwan Amman sai Ammah ta hanata zuwan tace taje Jordan idan hutun ya kusa karewa ta dawo Nan gurin Mama Hanifa ta karasa Abdul Hakeem zezo ya ganta. Ba haka taso ba da har tayi niyyar Kiran Abban ta fada Masa sai Kuma tayi tunanin kada Ammah tace ta Kai Kara dole ta hakura tunda Bata San nufin Ammah din ba data hanata zuwan. Taji dadin zuwa Jordan din sosai, dan Ummee na Shirin zuwa Saudi Arabia ne ma zuwan Zahrar ne ya kawo Mata tsaiko, tare suka tafi bayan ta huta, a can suka tarar da Aunty Nawwara wadda taje zuwa na musamman tunda lokacin ana daf da bikin aurenta inda za'a kaita Bagdad (Iraq). Sunyi sati daya zuwa suka nufi makka sukayi Umara, sosai Zahra ta mayar da hankali gurin addu'a akan matsalolinta na yanda rayuwa ke walankekuwa da ita Bata rasa komai ba Amma aure Yana neman yafi karfinta dah kudi ko kyau ke sawa mace ta auru tasan da yanzu ba wannan zancen ake ba, sai dai tasan duk Dan Adam baya wuce tasa kaddarar sai dai neman sauki gurin Allah s.w.a. Madina suka koma da suka Gama umarar,basu Dade ba suka koma Jordan. Lokacin da hutunsu ya taho garewa zahra ta koma syprus. Gidan uncle ta Fara Zama kafin daliban su dawo tunda ana saura one week ayi resuming ta dawo. Karatu suke ka'in da na'in ba Kama

Chapter 9 of 31