Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nake can kauyen mu". Ta fad'a Tana Zama a cikin one seat dake kusa da ita. "Eh wlh Aunty tana da excuse a gurina tunda nasan Bata Nan taje gida sokoto Amma ke kuwa ko waya fa Baki Kira kinji ya ake ciki ba". "Kice dai ban Kira ba. Amma tambayi Sajida kiji na kirata yafi sau ashirin ma ke dince lokacin Kiran baze yuwu ba Sai ki qara narkewa". Dariya suka saka su duka harda Aunty safiyyar. "Wlh Amah saina rama kinci bashi, Wai na narke kamar wani danyan tuwo". "To da mecece? mutuniyar dake somewa Kikayi fa dif kika dauke wuta". Kyale Amatu Zahra tayi ta karasa kusa da Aunty safiyya ta zauna ta Dora Shureem a Kan cinyarta tana Fadin. "Aunty sannu da zuwa Ina yini?" "Lafiya kalau Amarya ya Amarcin Naga ya barbeki kanwata Masha Allah". Dan sinne Kai tayi tana Fadin "Kai Aunty Ina wani Amarci a Nan kawai dai". "Gulmammiya Kinga yanda kikayi wani mahaukacin kyau kuwa? Ai da gani Amarci ya tabbata a gare ki,wa Zaki kife a baibai yarinya Kar nake kallonki fa". "Allah ya shiryeki tunda haka Kika zama, Bari ki gani". Ta Mike da Shureem a hannunta ta nufi kitchen, saida ta Zuba musu kayan garar a plate ta dauko musu ruwa da drinks ta dauko plate ta fito tana Fadin "Amah shiga ki dauko dayan Dan Allah". Sai da suka Gama sannan Zahra tace su shiga suga gidan, ko Ina suka shiga Fadi suke Masha Allah! a gurin fridge din dake cikin Dan Arc din dake tsakanin kitchen da dining area ne Aunty safiyya ta kasa hakuri Saida ta magantu lokacin data Kai hannu ta bude tana fadar. "Yau ne ganina na biyu da fridge din nan naso shi kamar qaddara Amma da aka fad'a Mana kudinsa Saida na Raina kaina" "Kai haba Aunty bakiyi niyyar saye bane". Zahra ta fada. 'yar dariya Auntyn tayi. "Bazaki gane ba Idan ci baizo daya ba ai koshi ma baya zuwa daya". "Haka ne kam Aunty". Amatu ta fada, suka nufi bedrooms dinta ko Ina dai maganar daya ce Masha. Amatu ce ke fadar "Allah ya mayar damu danshinki". "Amin. Amma Banda kalubale irin nawa, ba Dadi Amah har gobe abun Yana damuna bani da nutsuwa ko Kankani wlh duk lamurana sun tsaya cak bani da wani karsashi irin na amarya a gidanta, komai ganinsa nake Wai banbarakwai kamar a mafarki haka". Sai Kuma idanunta ya ciko da hawayen da taketa kokarin kada su zubo. "Ayya haba Zahra kiyi hakuri Mana, ai zuwa yanzu yaci ace kin hakura da koke-koken Nan tunda Mai abkuwa ta abku ai sai hakuri ki rungumi abinda Allah ya Baki ki dangana wata Rana sai labari". Aunty safiyya ta fad'a. Parlour suka dawo sukaci gaba da Hira, rabi duk ban Baki ne Aunty safiyyar kewa Zahra da nuna Mata ribar hakuri a cikin hirar ne Amatu take fadawa Zahra sakon Sajida na tana kiran wayata Amma Koda yaushe switch off. Dan lumshe ido tayi sannan ta bude tana kallon Amatun. "Matsala wayar ta samu shi yasa ba'a samuna Amma in Sha Allah soon zan sayi wata, yanzu bani taki na kirata". Wayar Amah ta Mika Mata tana dialing din number ta. Tana dauka ta Fara mata tsugudidi. "Yau wacce Rana Amatu ta kirani". "Assalamu Alaikum ayi sallama Mana bestie". Ta fad'a tana murmushi. "Kai!!! wa nakeji haka bestie, haba Dan Allah kin kyauta kenan ba waya ba wasika kin barni a tunani kala-kala Sam na kasa samun nutsuwa". Tashi Zahra tayi ta shige ciki tana Fadin "Bari kawai bestie guy din nan ya fa karbe wayar tun ranar da Kika tafi ya dauketa da safe daya shigo, shine fa daya shigo ya tarar duk na hargitse gado ina neman ta yace tana gurinsa, ya kama min wasu zantika akan Kiran da Musbahu yayi ranar ni kuma na kasa hakuri shine yayi min Rashin mutunci Kuma ya hanani wayar". Ta fada kamar zata fashe Mata da kuka, tambayar ta tayi yanda abun ya faru Bata rufe Mata komai ba ta fada Mata. Bata katse Mata hanzari ba har ta gama. "Amma ban taba sanin Baki da wayo ba sai yau, Gaskiya Baki kyauta ba ko alama Ina hankalinki ya tafi kada ki Kara Koda Wasa saboda wani ki ciwa mijin aurenki fuska ai wallahi jarimi ne daya iya hadiye fushinsa bakiji a jikinki ba". Ta fada a kufule, kit ta kashe Kiran. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana kallon wayar a zuciyarta tana fadin ji a jiki na nawa Kuma ba ze fadu bane shi yasa. Lokacin da zahrar ta fito wasu bakin ta tarar sun shigo su biyu har Amatu ta kawo musu ruwa da drinks suna hira dasu Aunty safiyya, sallama tayi musu sannan suka gaisa Nan Amatu tace musu "ga matar gidan nan". "Masha Allah" Suka fada a tare sannan babbar wadda zatayi kamar sa'ar Aunty safiyya tace "mune makotanki da hannun dama sunana Hafsat Amma ana kirana maman junior, wannan Kuma kanwata ce Nuratu da take karatu a Nan Abubakar Tatari Ali polytechnic (ATAP) aiki ne ya kawo Mai gidana mu 'yan Taraba ne". "Masha Allah! Allah ya taimaka ya bada sa'a". Suka fada. Sun Dan jima ana hira dasu sannan suka tafi har gate Amatu ta rakasu da ledar kayan garar biki. Suma mikewa Aunty safiyya tana goya Shureem da yayi barci, Dan langabar da Kai Zahra. "Wai har zaku wuce ne Kuma Aunty?". "Eh mana zan shiga gidan fachalata data haihu bana Nan". "Amman Banda ke dai Amah gaskiya tunda nasan kina garin Nan sai karshen wata keda jama'are". Aunty safiyya ce ta tari numfashin zahra "Ai ita ke driving dinmu ya zan barta a Nan ta dawo Miki special ko weekend ne". Alamar bude kofar da akayi ne yaja hankalinsu, Mahmud ne ya shigo Yana musu sallama da katuwar leda a hannunsa, tunda ya shigo Aunty safiyya ke kallonsa ita dai tasan wannan fuskar amma ta Yaya za'ayi haka ko Kuma kama ce kawai. A cikin takunsa na cikakken namiji ya shigo, da sauri Zahra ta nufo gurinsa tana Fadin. "Sannu da zuwa". Tana Mika hannu zata karbi ledar. "Da nauyi bazaki iya dauka ba". Ya fada Yana kallon ta. Har cikin kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce bedroom. Amatu ce ta zunguri zahra. "Ke! meye hakan Kuma? Kika wani sharesa Kada dai kice min sokoncin da kike bazawa a gidan kenan ko Kuma Dan kin gammu ne kikayi wani biris dashi". "Gaskiya Kam ki dage ki Kama mijinki irinsu tsada suke". Aunty safiyya ta fada tana nunawa Zahra hanyar daya bi. "Kai! Aunty Kuma ......" Bata karasa ba Amatu ta Kama hannunta ta nufi steps din tana Fadin "kije kawai tunda daman tafiya zamuyi saina shigo Saturday in Sha Allah". Dan raurau tayi tana kallon Aunty safiyyar. "Na gode Aunty ku gaida gida saina zo har gida ban gajiya". Dariya Auntyn tayi. 'Haba dai sai dai mun dawo, wannan turaren kada kiyi Wasa dashi tun daga besse na taho Miki dashi kakata ta wurin Babana take haduwa da Kanta Yana da matukar kyau sosai ba sai fada Miki ba da kanki Zaki nema". Dawowa tayi Saida ta rakasu har gurin mota duk da mitar da Amatu ke mata, ta hadasu da kayan garar fal ledoji biyu dasu bokitan roba da mug masu kyau da plates Wanda Aunty Hasana ta bada aka kawo mata saboda Baki masu zuwa. Saida suka fice daga gidan sannan ta dawo ciki. Bata shiga ciki ba a parlourn ta zauna tana mitar. "Idan na shiga me zan Masa wanda yake ganina a wata Mai neman rayuwarsa". *** Saida Amatu ta dai daita a titi sannan da Dan dubi gurin da Aunty safiyyar ke zaune tana rungume da Shureem. "Aunty nifa wani Abu ya bani mamaki da daure Kai" "Kamar me fa?". "Duk gari ya dauka an aurawa zahra Almajiri k'olo saboda ita ba 'yar Alhajin bace, surutu dai gashi nan, ni Kuma yanzu Naga sabanin abinda ake fada, yaushe Zaki kalli wannan kice Yana Qasqantacciyar rayuwa irin wadda ake fada?". "Ni Nama fiki mamaki Dan ni dai Idan ba gizo idona yayi min ba ko Kuma kama ce ta halitta tunda ance kowa Yana da Mai Kama dashi a wani gurin, da sai nace Miki M.M DANGE na gani". "Waye hakan?". Amatu ta tambaya. "Bazaki gane ba Amatu wasu Family ne a sokoto masu mahaukanta kudi Nima fa sau daya na taba ganin M.M DANGEN a bikin wata cussing Dina zainab data auri Dan Family din, Kai gaskiya bashi bane inaga Kama ce kawai, amma Kuma kamar harta baci sai dai ba yanda za'ayi DANGE ya iya rayuwa a nan". "Kamar Yaya Aunty?" "Tab kinsan kuwa waye shi? ai inaga kaf ba Wanda ya mallaki abunda ya mallaka a duk Family din, gashi yaro matashi Kinga gidansa na sokoto ma kuwa? Banda na Abuja da sauran garuruwa, to in kuwa shine me zeyi da Dan wannan gidan ai ji zeyi kamar Yana rayuwa a kurkuku ne, bama shi bane shifa ko bodyguard dinsa abin kallon ne Suma sun Zama done fa" Ido Amatu ta zaro. "Kikace wannan gidan kamar kurkuku? Duk yanda na ganshi Aljannar duniya". "Naki wasane Amatu. Allah ya kawo dalilin da Zaki shiga ko gidan daya daga cikin families din DANGE ne kiyo kallon duniya me Kika gani a Nan kedai Allah ya Kai damo ga garawa kawai, Dan dai a wannan zuwan da nayi sokoto naje yiwa zainab din barka naji wasu a cikin family din sunata hirar MM DANGEN Wai ko ya bar kasar ya koma turai tun bayan samun wata matsala Mai zafi a cikin family din wadda ta tada kura har rayuka suka baci". Da ire-iren hirarrakin suka karasa gidan barkar. ... Tana zaune a Nan parlourn ya fito cikin kananun kaya da karamar leda a hannunsa direct inda take ya nufo ji tayi gabanta ya Fadi. "Ya Ilahiy" ta fada a zuciyarta. Gefenta ya zauna Yana Fadin "Wash!! I am tired wlh samo min ruwa Mai dan sanyi". Yayi maganar yana dan matsowa jikinta. Da sauri ta tashi yabi ta da kallo Yana kissima abubuwa da yawa a kanta kunyar ta tayi yawa yasan sai yasha fama kafin ya rabata da ita yanzu dai most important thing ya samu shakuwa da ita sosai. Ruwan da farm fresh yogurt da snacks ta bawo Masa, idonsa a limshe Kamar me barci Amma Yana kallon ta yanda take tafiya kamar me counting steps sai rausaya take. Table coffee ta janyo ta Dora tare da bude Masa ruwan ta Zuba duk Yana kallonta. Ajewa tayi ta juya zata wuce taji hannuwan mutum duka biyun ya zagaye k'ugunta ya mannata a jikinsa ta baya, yayi Mata bazata Dan ko motsin mikewarsa bataji ba ko alama, a tare suka sauke ajiyar zuciya juyota yayi gabadayan ta suna facing din juna Yana Mata wani duban kasa-kasa. Narke fuska tayi Kamar zatayi kuka tace Masa. "Menene Kuma? gafa ruwan Nan na kawo maka". Fuskarsa ya matso da ita dai-dai tata yace. "Haka ake tarbar miji? Ki bani abincin yunwa nakeji fa, tun safe banci komai ba tunda kika tada min hankali abincin ya fice min daga Rai, waini Kika kalli kwayar idona Kika gasa min maganganu son ranki ko?". "Ni me nace, cewa fa kayi zanyi poison dinka ni banji haushi ba sai kai, kisa fa? To me kayi min, ni na daina abincin ma ba shike nan ba ban dafa ba bare na zuba maka guba". Ta fada tana kokarin zame jikinta, Kara gyara rikon da yayi Mata yayi ya nufi two seat da ita a jikinsa kan cinyarsa yayi Mata masauki, ya Kai hannunsa daya ya zame veil din da tayi rolling gashin ya shiga shafawa yana fadin. "Nifa da Wasa nake Miki dazun bada niyyar na bata Miki rai ba na fada, so I am very sorry Baby in Sha Allah bazan Kara fada ba, na Saba haka nake yiwa kakata Hajiya Inna a irin wannan lokacin na break shine na tunata da ita na fada Miki kema Ashe lefi zanyi, yanzu muje na tayaki ki Samar Mana light Abu muci bana son cin Abu Mai nauyi sosai da dare nasan kafin mu Gama anyi magariba ko" Ita dai tayi tsumu tsumu duk ta takura fatan ta ya saketa ta fece tunda Allah yasa yanzu ba 'yan tabe taben bane a Kansa a iya gashi kawai aka tsaya. Dagota yayi daga jikinsa ya rike hannunta kamar wata 'yar baby suka nufi kitchen, ledar daya shigo da ita ya dauko ya Dora a Kan cabinet din kitchen din Yana Fadin "zo ki cire wadan Nan daga ciki. Kayayyakin amfanin gida ne masu yawa harda su biscuits su chocolate, sai da ta saka komai a muhallinsa sannan ta Fara hada abinda zatayi, kujerar kitchen ya samu ya zauna Yana kallon movement dinta friend spaghetti Mai vegetables tayi sai tayi gasmeat. Lokacin data Gama komai an Fara Kiran sallah. Tare suka fito ya mannata da jikinsa a haka ya nufi bedroom dinsa da ita suna shiga ya zaunar da ita Kan sofa ya wuce toilet. Sai daya rufe kofar sannan ta tashi ta wuce nata dakin wanka take sonyi. Koda ya fito Bai ganta ba beyi mamaki ba yasan za'ayi haka, lokacin daya leka ya fada Mata ya wuce masallaci tana toilet. Saida yayi insha'i sannan ya shigo gidan abincin Mai gadi ya dauko ya futa ya Mika masa, daya dawo be nemeta ba,sport news ya kamo yana kallon labarun wasannin da akayi Bai gani ba. Zahra Kuma da tayi sallah saita zauna tayi Azkar na yamma da Bata samu tayi ba, data Gama tayi shafa ta saka riga da siket English waars combination din milk da maroon tayi rolling da milk veil tayi kyau kamar ka dauke ka boye body mist kawai tayi amfani dasu kusan kala uku cikin Wanda ta gani a cikin locker din mirror dinta sai kamshin ya Bata wani irin Dadi Mai kwantar da zuciyar me shaqarsa. Plat shoes tasaka a kafarta ta nufi falon,jin gidan shiru batayi tunanin Yana Nan ba Saida ta shigo sosai ta ganshi a kishingide da remote a hannunsa Yana kokarin canza tasha. Tashi yayi daga kishingidar ya zauna sosai Yana binta da wani mayen kallon, tunda suka hada ido sau daya Bata Kara yarda ta kalleshi ba. "Zo ga wayar ki Nan tunda Naga itama kinyi zuciya da ita kin bar min". Ya fada yana Mika Mata hannunsa alamar tazo ba musu ta nufo shi cikin takunta na nutsuwa, shi komai yarinyar Nan tayi burgeshi takeyi ga uwa uba Kuma ya fuskanci tana da tarbiyya da biyayya sabanin yanda yake kallonta, Bai zaci zata kwantar da hankalinta haka ba sai yaga ta tattara komai ta aje gefe abinda ya fuskanta kawai dai Bata daukar raini. Tana karasowa saita zauna kusa da kafafunsa a kasa taki zuwa gurin hannunsa da yake Miko Mata. Dan murmushi yayi Shima ya sauku Yana facing dinta da karamar ledar dake hannunsa, Mika mata yayi."Gata Nan ayi hakuri ki hada ta batirin ma yana da full charge da sim a ciki, duk numbers dinki important suna ciki. Wayar ta bude sabuwa ce Kar jujjuyata ta Fara tafi wadda ya Fara Bata tsada nesa ba kusa ba kallon tuhuma ta Farayi Masa tana girgiza Kai tare da Mika masa wayar tana Fadin. "A Ina kake samun irin wadan Nan wayoyin na mahaukatan kudi wlh ba ruwa na ka rike kayanka bana so ka maido min tawa ta asali kawai". ✨✨ ✨✨ ✨💎AUREN HUCE HAUSHI💎✨ Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Aminci su tabbata ga Annabin Rahama Muhammad s.a w.w. Page 25 📖🖋️ ________Dariya ya kama harda hawaye abinda bata taba gani ba. Sororo tayi tana kallonsa, ita bataga wani abin dariya ba a maganarta, hannu ya Mika ya karbi wayar kunnawa yayi ya Mika mata Yana kashe Mata ido tare da d'age gira. "Kina son kisan inda nake samun mahaukanta kudaden Nan ne?". Kai ta gyada Masa. "Good ki Bari sai ranar da Kika Zama ni na zama ke na mallaki kayana, a ranar nayi Miki Alkawarin sanin komai nawa na duniyar Nan, Idan Kuma yanzu you are ready za'a taimaki Dan Malam a lullubeshi da bargon ni'ima to? yanzu kuwa kisha labari har wanda Baki nema bama zan fad'a Miki, tunda ke inda nake samun kudi kawai Kika bukata baki son sanin waye ni?daga Ina nake?meya kawoni garinku? Gasu nan rab'ab'a da yawa, to ki rubuta ki aje har abada ni Mahmud bazan tab'a ciyar dake ko shayar dake ko wani Abu na jindadin rayuwa da haramun ba, duk abinda na Baki ki tabbata da gumin halalina na nema, kinga wannan wayar da kudina na saka na saya Miki,wato kina tsoron kada na Sato kayan mutane na kawo Miki ko?" Kai shiga gigizawa. "Ni ba cewa nayi kayi sata ba, gani nayi kana ta abubuwan da sai Mai wadata ne ze iya yinsu Kai Kuma Naga...." Sai kuma tayi shiru tana kallonsa. "Oya continue Mana,kinyi shiru wato Kinga bana aikin komai ko?". Shirun tayi Bata Kara cewa komai ba. "Tashi ni ki bani abinda zanci idan na biye Miki da wannan yarintar taki sai yunwa tayi min illah kisa a Fara gulmarki ace kina barina da yunwa, ganshi kin sani azumin da Babu lada". "Ba Kaine kayi zuciya ba ka tafi kabar abincin" Ta fada a shagwabe. "Ki tashi ki bani kada lissafin ya canza fa" Ya fada yana matsowa jikinta sosai, da sauri ta Mike ta nufi dining inda ta jera abinci. Table mat ta shimfida a Kan carpet din sannan ta dauko abincin ta aje. Plate biyu ta dauko dayan ya janye. "Ki Zuba Mana a plate daya ya Isa ai Kuma indai Ina gida plate din mu daya tunda Kika yimin horon yunwa yau daga Wasa Dan kawai kewar Hajiya ta ta kamani shine Kika horani duk ranar dana kaiki gabanta saina fada Mata tasan irin zaman da zatayi dake, ni Dan gata ne a gurinta bana laifi zakiga yanda take sona". "Ko?" Ta fada tana zuba abincin a plate, Dan tura Masa plate din tayi kusa dashi "Gashi Nan ni bana Jin yunwa". "Ashe zan Miki dura wlh, sai kinci kuji min yarinya da kinibibi Wai so kike da karfi sai kin koya min surutu ne? Kin iya kalato abin magana da wani bakinki chut". Ya fada yana shafo pink din lips dinta. Taci Amman ba wani na kirki ba da gaske abinci Bai dameta ba barta dai da 'yan ciye-ciye. Bayan sun gama ne ta kwshe kayan ta gyara gurin duk Yana kallonta komai tayi kyau yake mata gata ba wata babba ba sai dai akwai Sama da kasa masha Allah. Lokacin data gama ne ya yafito ta da hannu,a hankali ta nufo shi kamar me counting steps sai rausaya take, wani yawu ya hadiye, Dan risinawa tayi a gabansa duka hannuwanta ya kamo ya zaunar da it kusa dashi. "Zaki rakani unguwa?" Ya fada Yana zame Mata veil din da tayi rolling gashinta ne ya bayyana biki sidik dashi sai walqiya yake yasha gyara ga kamshin hair spray Yana tashi. "Eh zani Bari naje na shirya". ta fada Tana kokarin zare jikinta daga nasa. Duka hannuwansa yasa ya riko kugunta ya hade ta da jikinsa. "Ina zaki?wane irin Shiri zakiyi kinsan inda zamu ne kike sauri?". Lakwas tayi a jikinsa da karfi da yaji so yake ya Saba mata da Zama a jikinsa gashi baya ko Jin jauyin taba Mata jikin sai dai idan Bai soba. "Bazaki tambayi inda zamu ba, kina Neman sake canza Kaya". "Nasan gida zamuje Mana". "Ai kece gidan, kinaji da so nake muje gidan da gaske mu roki alfarmar a bamu aron me aiki daya Wadda zata zauna min dake kafin na dawo". "Kafin ka dawo? Ina zakuje?". "Au Ashe ban fada Miki ba, aikin NGOS din Nan ne ya taso suka gayyace mu zuwa meeting da zasuyi a UK Kinga ai bazan zauna ba da dollars ko stalling founds suke biyan mu, idan Allah yasa na samu da Dan auki Kinga na Kara jarina tunda Naga Nima Ina sha'awar siyar da materials har munyi magana da Abba yace ze bani rumfa daya a Muda lawal market na gwada ko ina da nasibi a cikin sana'ar, sannan Habib ma munyi magana zamu Fara siyar da spare parts na motoci a nan Muda lawal market din dai". "Allah ya bada sa'a, Kuma idan ka tafi sai yaushe zaka dawo? Ko kaima shike Nan abinda yake faruwa Dani ze faru a kanka kaima, kada ka tafi ka barni Dan Allah tunda nasan ba Sona kake ba baka ni akayi sadaka, Dan Allah ka taimaka ka kaini Jordan tunda Ina kudin flight kawai ka taimaka ka fitar Dani daga kasar da sunan Kai zaka tafi dani, bana son Ammah ta qara shiga cikin damuwa a kaina wlh Batasan tashin hankali ba Sai Dana isa aure Kullum idan kaga Ammah a cikin tashin hankali to a kan lamarina ne ni Kuma yanzu bana fatan na qara ganinta cikin bacin rai ta dalilina, kaje ka fada musu zaka tafi Dani ko Kano ne ka Kaini na zauna gidan su bestie kafin na samu visa, nagaji da Kasar nan wlh Ina da gata Amma sai walagigi rayuwa ta takeyi anan Dan Allah kayi min wannan alfarmar Koda ita kadai zakayi min ta karshe a zamana da Kai". Ta kifa kanta a jikin kafad'arsa ta saki wani kuka Mai tsuma zuciya. Bai hanata ba ya dai Kara matseta a jikinsa Yana shafa bayanta yasan abin Yana cin zuciyarta ne bata rasa komai ba amma an dabaibaye Mata Jin dadin rayuwa kamar yanda Baba malam ya fada masa. Sai da tayi Mai isarta ya dago kanta daga jikin kafadar tasa. "Kiyi hakuri kowa da irin tasa jarabawar ke taki a haka tazo, Kuma waya fad'a Miki zan tafi na barki bazan dawo ba? Waye kuma yace Miki bana sonki? Kinsan tun tsawon lokacin da nake dakon soyayyarki kuwa? Tun Baki san meye son bama yarinya share hawayen ki Mahmud naki ne har abada, dole kije Jordan ke me gida sukutum a can.Amma yanzu kiyi hakuri nema zani idan Kuma na zauna bakya son tafiyar saina fasa Sameer yayi komai kawai nace madam ta Hana". "Kaje kawai idan baka dawo ba nasan abinda zanyi". "Keh! kina da hankali kuwa me zakiyi wlh zan turaki gurin Hajiya Inna duk da ban shirya zuwa yanzu ba kawai ki Kira min ruwa, zaman Allah nakeyi zamanki nakeyi badan ke ba Dana Dade da barin garin Nan". " Ni Kuma?" "Off course" Ya fada da karfin gwiwa. "As how?" Share ta yayi kamar bai jita ba. "Tashi ki rakani kada dare yayi, dauko Mana key din motarki na dana kada na tafi ban Sanya albarka ba, ki canza shiga kada a kalle min kayana" fada Yana mikar da ita daga jikinsa. Duk kin haye min cinya kinsa sai ciwo take min". Ya fada Yana Mata wani smile. Bata kula shi ba tayi gaba abinta duk zuciyarta ba Dadi sannan tana jujjuya maganganunsa a zuciyarta, kinsan tun lokacin da nake sonki? Danke nake zaune a garin Nan gasu Nan dai da yawa. Saida ta sakarwa Kanta ruwa sannan ta shirya agurguje ta saka wata Riga da siket na atamfa super dinkin ya zauna das a jikinta ta saka mayafin da yayi matching da atamfar ba tayi amfani da turaren kaya ba body mist kawai tayi amfani dasu a jikinta kusan kala uku, sai ya bada wani sansanyan kanshi Mai dadi. Tana gyara gyalen ya shigo dakin tsayawa tayi tana kallonsa shida yace unguwa zata raka shi sai gashi da Riga armless da wandon ta farare tas na kamfanin Adidas sai taga kwata kwata ya canza Mata ya koma irin 'ya'yan hutu din Nan na gaske wadanda Jin Dadi ya gama ratsa su yayi wani irin fresh da shi. Matsowa yayi kusa da ita Yana Dan watsa hannu irin dai na isassun yaran. Mayafin ya kama ya ida rufa Mata a kanta. "Kallon fa na menene? Kona canza Miki ne?". Kai ta girgiza Masa. "Baba son body language fa ki bude Baki kiyi min magana". Yana janyo ta jikinsa. "A'a kawai dai da naji kace unguwa zan rakaka kuma na ganka da......" Sai tayi shiru. "Karasa Mana sai Kika ganni da shigar nigas ko?" Shirun dai tayi. "Idan Ina tare da iyalin dole na sake, kema da nace ki canza ai na Shan iska nake nufi ba Wai irin wannan ba, zo muje ki canza yawon Shan iska zamu ki min hira ki bani labarin ki tunda ke bakya bukatar nawa ki bani happiness a wannan Daren yanda duk inda nake na rinqa Tino da abubuwan su zamar min kamar kina kusa Dani". "Ni dai Dan Allah ka barni haka muje kawai" "Dauko

Chapter 18 of 31