Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ina dalili Ni kadai kamar mayya kufa Nan ku uku ko ihun neman taimako kayi an taimaka maka amman Ni kuwa ko kasheni za'ayi sai dai a dauki gawar da safe". "Tab wallahi ba inda Zaki zauna a Nan ba haka big bro yace ba,a can yace ki zauna Dan haka Babu Mai canza wannan Umarnin". Dan turo Baki tayi "Ni na taba ganin haka mutum ya ringa saka doka a gidan mutane inaga baisan girman gidan ba shi yasa yake bada wannan Umarnin, gaskiya da sake". Time Rukayya ta duba a waya kizo muyi break yanzu zakiga ya Sameer yazo tunda da wuri za'ayi Miki sauran gwajin". Suna cikin break din Sameer yazo Saida ya jira a mota suka Gama sannan suka tafi, a ANC department suka samu doctor Haseenar sun awon ciki. Ba yabo ba fallasa ta tarbesu ba kamar jiya ba ko yanda suka ringa Yi jiya da Rukayya yau ba haka bane daga gaisawa Bata Kara cewa komai ba, itama Zahra saita Kama kanta Rukayyar ma haka. Gwajin jini ta Kara tura Zahrar ta hadasu da wata ma'aikaciyar su ta rakasu main lab aka dauki jinin. Lokacin da suka dawo sun Gama ante-natal din gwajin jira ta dauko da scanning din ta Kira Sameer tana fadin mu hadu a office dina". Ta kashe tana fadin Bismillah Ruky muje office dina tunda mun Gama da Ante-natal sai zuwa anjima zamu Fara gyne". A kofar office din suka samu Sameer din ya rigasu zuwa. Sai da suka zauna sannan suka gaisa da Sameer din, bayani ta farayi Masa na gwaje-gwajen jinin jiya "a cikin jininta ba wata cuta ko kadan kawai scanning ne ya nuna Mana akwai matsala a mahaifarta ta fibroid amman be wani girma sosai ba za'ayi aiki a cire mata tun kafin ya girma Amma zamuyi admitting dinta zuwa one week tana karbar magani kafin ayi surgery din, Dan haka sai ta Kira mijinta ta fada masa yazo da mutane muna son jini leda biyu, zamu jira results din Nan ya fito total blood count za'ayi Mata". Rukayya ce tayi farat ta tambayi doctor Haseenar "yanzu dole sai tiyata baza'a iya Shan magani ba a warke?" Kallon tsab Dr Haseenar tayi Mata kafin tace "hanya mafi saukin rabuwa dashi ta sai dai aikin gaskiya". Tunda doctor Haseena ta Fara bayani gaban Zahra ya yanke ya Fadi idan da abinda taki jini a rayuwar duniyar Nan to tiyata ce. Nisawa Sameer yayi kafin ya samu karfin halin fadin. "Thank you so much doctor kome kenan zakiji idan munyi communicating da mijinta saina kiraki later" "Ok.ba damuwa Allah ya sauwaqe". "Amin". Rukayya ta fada Dan zahra ba bakin magana har suka shiga mota tana cikin tashin hankali, kuka takeyi irin na zuci din Nan sai dai hawaye kamar an bude famfo. Saida suka fita daga Asibitin har sun shiga court road sannan Sameer ya Dan juyo, Madam kiyi hakuri in Sha Allah ba wata matsala idan Allah yasa yin surgery din ne yafi Alkhairi ayi kawai Kinga kema saiki huta da zulumin ciwo duk wata". Rukayya ce juyo tana fadin "gaskiya kada ki yarda a yanka ki haka kawai Ni banma yarda da maganar Haseena ba, kawai ta jawo Miki wahala Ni Daman da anyi shawara Dani da Babu abinda zesa Haseena ta duba matar big bro haka kawai taje ta jawo Mata matsala da gangan bakaga yau sai wani share mutane takeyi ba, wani ya Hana big bro din ya aure ta". Wata uwar harara Sameer ya zubawa Rukayya "Billahillazi Zan saukeki a Nan ke wace irin mutumce da bakinki bashi da controlto me kikayi ke Nan? wannan ai shashanci ne keda Zaki kwantar Mata da hankalinta shine Kika sokawa zancen wuqa". Ita dai Zahra maganganun Rukayya sun daga Mata hankalin kenan da wata jikakkiya a tsakanin wannan likitar da Mahmud. Wallahi ko likitoci sun Kare wannan ba zata Kara dubata ba shi yasa Kennan jiya ta damu da sanin waye mijinta da dangartakar ta da Mahmud. Tunda Sameer ya yiwa Rukayya buyagi Bata kara magana ba har sukazo junction din gidan shatima. "Wai yaushe mommy taje gidan Hajyr makwararin?". "Dazu da safe na kaita Wai zasu karbi lefen mujahida". "Ok Allah ya Sanya Alkhairi. Dan Allah ya Sameer Zan sayi alawar Madara idan ka tsallaka Zan kaiwa Hajiyar makwarari". "Kice dai Zaki saya bawai Zaki sayawa Hajiyar makwararin ba". "Allah tana son shi sosai" A kofar gidan Hajiyar yayi parking Babar mommy ce. Da karadi Rukayya ta shigo gida yayin da Zahra da Sameerke biye da ita a baya, suna runfa ana hira da kunnen Rukayya da 'ya'yan dangi da mommy masu karbar lefen basu Fara zuwa ba gaishe dasu yaran sukayi suka fice, sukabar mommy kawai. Cikin nuna kulawar mommy ta kalli Rukayya dake gaba. "Ba dai har kun gama da asibitin ba?" " Mun Gama kin ganta Nan Wai doctor Haseena tace zata yankata tayi Mata tiyata Dan nace ban yarda da ita ba shine ya Sameer yake ganin bekena". Sallama Zahra tayi tana Dan tsugunnawa tana gaishe da mommy cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa da Kuma alamun tasha kuka. Mommy kallonta tayi tana fadin "Masha Allah tabarakalla sannu ya jikin naki?" Da sauki sosai". To Allah ya Kara lafiya naji Rukayyar na fadin tiyata za'ayi Miki". "Eh haka suka fada" Hajiyar makwararin ce ta fito tana fadin "wa nakeji kamar Rakiya a gidan nan waye ba lafiya naji ana magana tiyata". " Kin ganta Hajiya, matar Mahmud mutumin ki ce". Mommy ta nuna zahra. " Wai Amaryar ce? Sannu kinji menene ya sameki?" Rukayya ce ta fada Mata. Mommy ta kalla "Ni Zan hada Mata maganin wannan lalurar ba sai anyi Mata aiki ba, ki huta Rukayya ki shiga Nan kurmi ki sawo min abin hada maganin a Nan na hada Mata insha Allah sai dai ya narke yabi jinin al'ada. "Amma gaskiya ba wanda ze yanka ta Kamar kabewa ku 'ya'yan zamani komai a yanka ta haka ne daji yake shiga ai ta fama da rai idan yazo da karar kwana kiga an mutu, daina kuka, samiru kiwawo min mijin nata na fada Masa da bakina Babu me yi Mata danyan aiki ko haihuwar fari Bata yi ba a jawo mata tsuguniya mazan yanzu marasa hakuri". Ta fada tana nufar uwar dakanta. Ita dai mommy Shiru tayi Saida Hajiyar ta shige sannan ta dubi Rukayya "Wai Ke Sai yaushe hankali ze Gama Miki jiki? Kinzo kin kwatsa zance gashi Nan kin tubzura Hajiya Mai hanata hada maganin Nan sai Allah, itama Kuma Mai lalurar maimakon ki kwantar mata da hankalinta A'a tashin farko kin sokawa zancen wuka, ai kin kyauta". "Wallahi ba haka bane mommy Kinga dai muna good term da Haseena amma wallahi yau kamar ma Bata taba gani na ba sai cin magani take yiwa mutane da dacin rai want ya Hana Ya Mahmud din ya aureta taga yarinya ta gigice zatayi mata illa haka kawai". Maficin dake kusa da ita Mommy ta jefawa Rukayya tana fadin fita ki bani guri tunda kin Zama babbar kwabo kin tasa yarinya gaba kina fadar abinda be Dace ba". Wata uwar harara Sameer ya saukewa Ruky ji yake kamar yayi Mata duka duk ta cakude lamarin tana kokarin ta saka jinin yarinyar mutane ya hau, tun sassafe Mahmud ya Kira shi Yana fada Masa ya kira Rukayya yace ta fadawa Zahra ta bude wayarta ya manta shaf sai fa yanzu ya tuna. Wayarsa ce ta Fara ringing "shine ya kira" ya fadawa mommy. "Ka dauka kayi Masa bayanin halin da ake ciki". "Nasan Haseena ce ta fada Masa shine ya Kira yaji". Wayar ya saka a speaker yanda zahrar ma zataji. Bai jira komai ba ya Fara fadin "Sameer wace magana naji Haseena tana fada min? kada ka Bari su taba min yarinyar nan Zan kaita inda ya Dace, naji tana fada min wasu nonsense wallahi idan na shigo saina Bata Mata rai, ita harta isa ta fada min son ranta who is she? Yanzu ina ita zahran take? Tun jiya jikina ya bani an samu problem wayar ta fa ta rufe ta Hana nayi magana da ita fa". Tashi Sameer yayi tsam ya fita ya cire wayar daga speaker saboda kada yayi katobara. "Gamu Nan a makwarari gidan Hajiya Zahrar sai kuka takeyi,ita Kuma Ruky sai tinzira ta take kada ta Bari a yankata har Hajiyar makwarari taji tayi tsallen Albarka tace bata san wannan magana ba, ita zata hada Mata maganin hausa Wanda ze narke ciwon, wallahi sun caza min kai har na rasa yanda zanyi da rigimar Hajiyar, yanzu haka kasuwar kurmi zata aiki Rukayya ta sawo Mata mahadin maganin da zata hadawa zahrar". "Yanzu dai bazan Gane kome kake fada ba hadani da Zahrar muyi magana" "Ok Bari na kira ta dakin mujahida Naga ba kowa a ciki ka kwantar Mata da hankali duk ta shiga damuwa sosai sai kuka takeyi" Rukayya dake zaune a tsakar gida ya yiwa nuni data Kira Zahra, lokacin da suka fito Yana tsaye suna ciga da maganar. Wayar ya Miko Mata ya nuna Mata dakin mujahida yayi nufi waje. Tana shiga cikin dakin tana Jinsa Yana faman hello, hello tayi shiru karshe ma ta sakata wayar a flight mood tayi kwanciyarta a katifar mujahadar tana goge hawaye. "Me kake son fada min Kuma? naji komai me Za'ayi bazan zauna a garin Nan ba wallahi, gida Zan tafi kuma idan ma ciwon ne ai Ina da inda za'ayi min maganin ba sai Nan ba, da gata na da komai na zauna sai watangaririya nake yi Dani".AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 41. 📖🖋️ ________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala. Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi". Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" . Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala. Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" . Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya. Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa". Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna". Ta taso tana karbar tabarmin. "Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki". Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi". "Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita". Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar. A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki. Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?. Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah". Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita. "Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi". Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron. "Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa" 'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi". "Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba". Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba. Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata". "Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida". Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata". Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata. "Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi". "Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba" Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne". Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin. Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa. Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan. Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini". "Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa". "Muje Zan baka kudin drop din". Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai" Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi. Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?" Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare". "Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka". Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin". Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa". *********** Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da adudu biyu. Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share hawaye. Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?" "Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba". "Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota". "To mommy". Ta fada sukayi waje su uku. Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi". Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane". "Ungo Nan". Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu. Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa. Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa. A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko. "Gani mommy lafiya na ganku haka?". Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta". Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?" "Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka". "Ok, Bari naje Nan Ina zuwa" Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?. Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema. Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane" Jiki ba kwari ya koma ciki.. ***** ***** ***** Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa". Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki. "Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?" "Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin". "Allah sarki ko kawu Musa?" "Shine Ashe kin sanshi". Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne".. "Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin". Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida. Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa. Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH Page 42. _______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice. Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga". "Yanzu ya za'ayi kenan?" Rukayya ta tambaya. "Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba. Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take. Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?" Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta. Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare. A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala. "Wai menene?" Ta fada cikin damuwa. "Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan". Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce". Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta". Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta. "Ka Kira ka fada masa?" Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba". *** *** *** *** Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?" Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya". "Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya". Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo" Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan". "Eh zamuzo Aunty zahra". Nusaiba ta fada suna Zama kusa

Chapter 29 of 31