Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
PAGE EIGHT Lokacin da suka shigo gidan ana ta kokarin daura alwalar sallar magariba. Sai bayan sallar insha'i ne Mama ta shigo dakin Ammah suka hadu da Aunty Hasana suna fadawa Ammah yanda suka gano gidan da Kuma yanda abin ya daure musu kai. Nisawa Ammar tayi tana fadar "Mama ki Sami Abban kiyi Masa bayani yanda ze fahimta kinsan yanda suke da malam bana tunanin wannan abun ze saka ya canza ra'ayinsa duba da yanda ya yanke hukuncinsa Bai nemi shawarar kowa ba". "Aiko dai ya kamata ayi wani Abu gaskiya Nima lamarin ya tsaya mini a cikin zuciya". Aunty Hasana ta fada. Sun jima suna tattaunawar kafin Mama ta koma daki tabar Autty Hasanar da Ammah. Zama Aunty Hasanar ta kyara ta fuskanci Ammar ta Kira sunanta "Anya wannan Mahmud din ba abinda yake boyewa kuwa Ammah Kinga gidan kuwa ga wannan uwar wayar daya canza Mata kinsan kudinta kuwa ? gaskiya I doubt much, ni dai kiyiwa Abban magana da kanki Kamar zefi daukar abun serious akan na Mama". Can Kuma sajida ce tasa Zahra a gaba tana ta faman zuba. "Innalillahi! Kinga gidanki kuwa? Allah ya bamu ya taku wallahi Zahra ki godewa Allah. Wallahi Allah ya Gama miki duk wata ni'ima ta ko Ina kinyi gaban da Nan kurkusa dai kafin a fiki za'a Dade ana lalube. Zahra Naga mijinki har mun gaisa ada Ina adawa da auren Amma tunda na ganshi Naga Yana yinsa nasan yanzu ne kikayi aure da mijin daya Dace ke.Kawai dai matsalar za'ace ba Mai kudi bane,amma a yanda gidan da zaya ajeki yake wallahi ko minister ne sai hakan, akwai abinda na gani a gidanki wallahi ban taba gani a gidanki kowa ba duk yawona sai dai a film amma dai a zahiri A'a ban taba gani ba Allah Bai kaini gurin ba". Tunda ta Fara zuba Zahrar ke bin sajida da idon lokaci daya duk ta wani rude sai zuba take Kamar 'ya 'yan kanya. "Kin Gama?" zahrar ta tambayi sajidar. "Eh na Gama aini an ma yanka ta tashi na fasa tafiyar zanyi waya da Mom taje can Rimin sumailar gurin Baffan kawai, tunda Daman zatazo nan din ba suna kwantagora". "Ke Kika sani dai tunda Naga kina nema ki Zama wata daban ko dai an canza min ke da wata ne ko Kuma wani abun ya fada Miki ya goge Miki hadda ne?". "Eh da alama Kam Dan ya fiki iya lafazi gaskiya inaga na Zama 'yar team dinsa fa tunda Naga ke Baki da wayo". Ta fada tana dariya. Washe gari tun safe Abba yasa aka Kai furniture's din Zahra gidan Daman Aunty Hasana sunyi magana da Wanda zasu hada musu kayan, kayan kitchen da sauran kayayyakin duk suna gidan Aunty Hasana daga can aka ringa daukowa, masu aikin su suka hada komai na gidan hatta kitchen su suka gyara komai, gidan ba karamin kyau yayi ba, ba karya duk Wanda yaga gidan yasan na 'yar gata ne.Dan wasu irin mahaukatan Turkish furniture's ne wanda kakanninta ta gurin uwa sukayi Mata duk wani abun more rayuwa akwai shi a gidan Nan, bangaren electronics ma sai a cikin lockers aka zuba wasu, komai yayi. Lokacin da aka Gama gyaran Aunty Hasana da sajida ne sukazo gani ba karamin burgesu gidan yayi ba Dan sai yanzu ne ya fito a asalinsa na kyau da kayatar da Mai gani, komai na gidan unique ne Masha Allah. A waya sajida ta daukowa Ammah komai. Ita kanta Ammah Kai Kawai take jinjinawa Dan ba karamin burgeta abin yayi ba, sai dai can kasan ranta rudani ne kala-kala domin abin ne duk yazo a hagunce. Tana tsoron lamarin sosai sai da har abada baza iya jayayya da Alhajin ba Dan da gaske ubane tsayayye Wanda baya nuna banbanci tsakanin abinda ya Haifa da Wanda yake bashi ya Haifa ba, amma harga Allah tana zulumin wannan AUREN HUCE HAUSHIN da Alhajin yayiwa 'yar marainiyar Allah, mazan yanzu sunce suna sonka ma ya kukan kare idan Zama yayi Zama ballantana matar cushe ta San komai Daren dadewa ranar da yaga irin matar da yake so Sai dai zahra tayi hakurin zama Kawai, duk da tasan Bata da haufi akan yarinyar Tata Dan macece har mace abin alfaharin kowa ne namiji ace ya mallaki Kamar ta, to Amma shi lamarin so daban yake duk kyan mutum da asalinsa ba lallai ne ace yana burge kowa ba domin shi dai so makaho ne. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk jikinta yayi Mata wani irin Sanya ta kalli Aunty Hasana tace "Hasana Ina jin wani irin rauni a zuciya ta game da lamarin nan Ina tausayin yarinyar nan rayuwa tana ta walagigi da ita sai nake ganin Kamar laifi nane Dana kafe a barmin yarinyar Nan na hana kakanninta ita ni Kuma nayi sakacin da aka maida rayuwar ta Kamar kwallo ana ta dokata daga Nan zuwa nan". Ta karasa maganar hawaye na zubo mata. Abinda tunda Allah ya kawo Aunty Hasana duniya Bata taba gani ba a zahiri gurin Ammah Nan da Nan hankalinta ya tashi sajida ma kukan ta Fara duk da batasas takamaimai man abinda ya saka Ammah kukan ba, tashi tayi ta fice daga dakin jin an Fara Kiran sallar magariba. Aunty Hasana ce tace "Haba Ammah duk yanda Kika jure bakin cikin baya na abubuwan da suka faru Baki taba zubar da hawaye ba sai yanzu da Allah ya nufa akayi ai godiya Zaki yiwa Allah daya kawo karshen wahalar ba kuka ba". Gefen zani tasa tana goge hawayen. "Hasana Ina hango abinda ke bakya hangowa ne,masu iya magana suna cewa matar shige Bata daraja ba irin wannan rayuwar na sowa Zahra ba to sai dai kana naka Allah Yana nasa Kuma nasan ne gaskiya. Ba komai haka Allah ya tsara komai mukaddari ne daga gare shi, naji Alhaji Yana maganar zuwa juma'a za'a kaita". *******Tun bayan kammala karatunsu na bayan insha'i da suke na littafin iziyya yake zaune a kusa da Baba malam har kowa ya watse ya rage saura su biyu tunda malam yaga haka yasan da magana a bakin Mahmud ne. "Ya ya akayi ne Mahmuda?" Malam ya jefo Masa tambayar, Kara dukar da Kai yayi kafin yace "Daman maganar kayan lefe ne dazu Oga Sameer ya kirani yace ya hado tasa gudunmawar kenan, shine nace Bari na fada maka Dan kasan da zuwansu". "Ikon Allah shi wannan yaron baya gajiya ne Kamar baisan ciwon nema ba tunda yazo ya riski maganar Nan yake Yi kan jiki kan karfi. Allah ya saka Masa da Alkhairi yabar muku zumunci". "Ameen" ya amsa. Harya Mike ze tafi sai malam din ya dakatar dashi, dawowa yayi zauna. Gyaran murya malam din yafa kafin ta jefo Masa tambayar. "Sai zuwa yaushe ne kake ganin zamuje ga mahaifan naka kaga dole muje musu tunda wannan lamarin ya faru". Kai ya sadda kasa Yana fadin "zamuje in Sha Allah Amma Dan Allah a Kara min lokaci da kaina zanyi maganar ayi hakuri". "To ba laifi Allah ya iya Mana kaje ka Samu su Habibu kuje acan gidan ku kwana kaga sun zuba dukiyar kasan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba". "To in Sha Allah za'ayi hakan amma ni Ina Nan sai dai su Habib din suje". "To ai hakan ma yayi Allah yayi Albarka". Saida ya dudduba dakunan yaran ya tabbatar da komai lafiya lokacin sha biyu ta wuce, dakinsu ya nufa wanka yayi ya saka kayan barci sannan ya hau gado ya bude laptop dinsa. Email dinsa ya shiga Yana duba sakknnin daya samu sakon daya shigo ne ya dauki hankalinsa. "Ya Salam!". Abinda ya iya ambata kenan sai Kuma sautin daddad'an ringtone dinsa ya karade dakin. "Sameer!" Ya fada a hankali yasan za'ayi haka, ya haga wayar Yana fadin "Ta Yaya hakan ya faru?" Daga can bangaren Sameer din yadan furzar huci Mai zafi Yana fadar "wallahi nayi duk yanda zanyi Amma abun yaki yuwuwa dole ka daura ka kawar da komai muje gaskiya Dan kasan tunda akaje Nan zuwan nake ne Kawai mafita". "Amman ai kasan halin da ake ciki so kake ace na gudu nabar 'yar mutane Eyeh?". "Cool down Mana my man abin Bai Kai nan ba aikin daine ya taso na gaggawa Kuma dole sai da Kai za'ayi Dan haka suyi hakuri su aje maka ita zuwa sanda ka dawo ko Kuma ka dauko abarka ku tafi, kaga ai tafiyar tafi yi maka armashi ko?" Ya fada cikin zolaya. "Dan Allah ka Zama serious mana, kayi duk abinda ya kamata a Nan goben ka hakura da zuwan ka turo wannan friend din naka tunda yasan gurin ya kawo kayan kawai, Kai Kuma ka Kira Baba malam ka fada Masa daga can sun nemi ganin wakilansu na kasa da jahoshi da kananan hukumomi nasan dai kome ake ciki baze wuce kwana buying zuwa uku ba kaga lokacin na tare a gidana nafi son na barta a Nan gidana akan na tafi Bata tare ba". "Ko dai.......?" Sameer ya fada Yana dariya. "Allah ya shiryeka ko dai me? kasan ni salihn ne ba ruwana da wannan sabgar sai ku". Kit ya kashe wayar sannan yayi switch off dinta. Misalin karfe Sha biyun Rana wata tamfatsetsiyar mota Parker a kofar gidan malam. Akwatuna Yara suka dunga saukewa suna shiga falon malam saida suka Gama sannan baki nufi falon malam din bisa jagorancin Habib sun gaisa sosai da malam suka gabatar Masa da kayan daga Sameer. Malam yayi godiya ya saka Albarka ba adadi. Falon malam ya bar musu sukaci abinci suka huta sannan Habib ya rakasu can gidan suka gaisa da Mahmud din. Sai bayan Azahar suka tafi malam yayi musu Sha Tara ta arziki. Kayan malam yace suje su duba su gani saboda da an jima za'a Mika musu can gidan Alhajin. Kaya ne na gani na fada an zubasu Kamar ba gobe, an shigarwa da iya Abu ciki ta gani malam yace ta turawa makotanta na kusa suzo su gani anjima za'a Mika musu. Bayan fitowa daga sallar la'asar ne Malam Bukar ya fadawa Alhaji yanzu su malam Mudi da Alaramma malam Haruna zasu kawo kayan Zahara'u. Fada Alhajin yayi akan kayan da za'a kawo Yana fadar "Haba malam Dan me za'ayi min haka ko wancen da aka fasa auren Kai sheda ne ban karbi lefe ba da suka matsa cewa nayi suje da kayan idan tazo saiya ba matarsa". Kai malam yanjinjina Yana fadin "Anyi hakan Kam amma wannan shima bamu muka hada ba wannan yaron Sameeru ne ya turo dasu dazu yace gudunmawarsa ce aba Amarya" "Ikon Allah shi baya gajiya da dawainya haka daga wannan sai wance Allah ya saka da Alkhairi ya bar.zumunci na jima banga yaro mai karqmcinsa ba abin duniya Bai rufe Masa ido ba". Da yamma su sajida suna zaune suna Shira ita da Zahra da wata kawar Zahra Mujiba Nan take makotansu suna dasawa da Zahra sosai sun Kuma yi sabo sosai da Sajida tun lokacin da sake zuwa hutu da Sajidar lokacin suna makaranta. Ba zato ba tsammani Yara suka shigo da manyan jakunkuna dasu cylinder din gas, ai Zahra na ganin haka ta tashi da sauri ta nufi hanyar shigowa gidan da gudu ta karasa Kamar karamar yarinya suka rungume juna da Hameeda Kamar zasu fadi. Suna rike da hannun suka shigo ciki su Mujiba suna ta faman yi Mata sannu da zuwa, sai daga baya Salma ta shigo tana wani shankanshi Bata kula su Zahra ba Suma ba Wanda ya kula ta, directly dakin Mama ta nufa. Kamar jira ake Salma ta wuce saiga su Magaji da manyan Akwatunan lefe suna shigowa da sauri Zilai Mai aiki ta warto Babbar tabarma ta baza tana rabsa guda tana fadin "Masha Allah! Alherin Allah ya sauka. Fara Mai farar aniya sukari bakai farin banza Fatima Zahara'u 'yar Muhammadu sani, jikar hardon fulanin Mubi, Amarya gidan Mahmud Kuma uwar gidansa Alherin Allah ya Kai Miki, Mama!Ammah ku fito ga abin arziki ya sauka". Har rige-rigen fitowa a key tsakanin Mama da Salma yayin daga dakin Ammah Inna maimuna ta fito. 💋❤️ 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHIN 💋❤️ 💋❤️ WRITTEN BY MAMAN FATIMAH PAGE NINE🔷(9) ____Akwatuna ne na garari masu tsadedden kyau har set biyu aka shigo dasu, sai wasu irin manyan jakunkuna guda uku, guda Zilai ta dinga gud tana fadin "wani kaya sai amale wane jaki. Allah ya Kara daukaki Fatima ya Dora ki akan makiyanki lallai girma sai dan girma kaga wadda ta gaji arziki gaba da baya" Inna maimuna ce ta jimko kudi ta dankawa zilai tana fadin "na fanshi jikata tunda kin koma roko". Dariya tayi tana fadin "wallahi Inna Dana iya kirarin da yafi wannan da nayi Mata. Uwar dakina murucin kan dutse ce Bata fito ba Saida ta shirya, yakuwar akan kabarice bakin cikin 'yan taushe, bikin cikinka sauro yau ga xanzaro a bene" . Ta Kara kwarara wata gudar. Da sauri Mama ma tazo ta dankawa zilai kudi tana fadin yau ai ranar farin ciki ce maza bude Mana muga karamar Arziki" Tunda aka Fara shigo da kayan Zahra tayi dakinsu tabar su Sajidar anan.Hameeda da zilai ne suke fama bude kayan suna santinsu komai na ciki Mai kyau ne ba karya duk wadda ta hado kayan 'yar gayu ce ta gani kasheni komai na ciki classic ne. Saida suka bude kowa ne akwatin duka Sha biyun. Ba abinda Inna maimuna ke maimatawa sai Masha Allah,Allah ya kade fitina yasa gurin zamane Allah ya hada arzikinsau. Duk bidirin da ake Salma na tsaye Bata taba ko tsinke a ciki ba sai cika take tana batsewa Kamar anyi Mata dole sai ta zaune a gurin. Su Sajida da Mujiba da Hameeda ne suka shigar da kayan falon Ammah. Sai da suka jerasu sannan Hameeda ta nufi dakin Mama su Kuma su Mujiba suka nufi gurin Zahra. Wata uwar harara Salma da dokawa Hameeda tafin tayi dogon tsaki tana fadin "Allah wadaran naka ya lalace yanzu ke ko kishin Kai Baki dashi Kika bige gurin jidar kayan kanwar bayanki kina wani washe Baki ke game kirki". Baki Hameedar ta murguda Mata tayi gaba tana cewa "Ina ruwanki Aunty Salma danke bakya ra'ayinta dole Nima sai nabi naki ra'ayi kowa yayi ta kansa kawai ni bana ara na yafa abinda Babu ruwana ba. Mama ce ta fito daga bed room dinta fuskarta a hade da waya a hannunta kallon Hameedar tayi "to rasa kunya b'eran tanka Dan ta fada Miki gaskiya Zaki kare Mata tana din rashin mutunci cewa nake koni Dana tsuguna na haifeki ban Isa kizo inda nake ba Saida Kika dangana da gurin kanwar uwarki". Baki Hameedar ta zumbura tayi gaba tana magana kasa -kasa. "Ai Daman za'a rina tunda Naga kin biyo Mama daki, wallahi mutum ya kiyayi gulma da munafurci in dai yansla son yaga ci gaba a rayuwarsa" Tana Gama fada ta shige uwar daki. A waya Ammqh ta Kira Aunty Hasana ta fada Mata an kawo lefen Zahra. Lokacin da tazo taga kayan ta kadu da gasken gaske, Amma dai Bata furta komai ba kada Ammah taga Kamar Bata son auren ne ko wani Abu. Sai bayan sallar magariba Mujiba tayiwa su Ammah sallama Sajida ta rakata ita Haidar din Aunty Hasana. Tun Zahra na tsammanin ganin Hameeda har ta hakura saboda dare ya fara so sai Dan Sajida har tayi barci, sai tayi Kamar ta kirata a waya saita fasa, da taga zaman yayi yawa sai ta dauko alqur'ani ta Fara karatu har Saida daya ta gota sannan tayi addu'a ta shafa. Kwantawa tayi rigingine tana tariyo rayuwartan ta baya komai ya ringa dawo Mata Kamar lokacin yake faruwa ************_ _ TUSHEN LABARIN AZARE KATAGUM L.G.A BAUCHI STATE UNGUWAR FAMFON SHANU. Yarinya ce 'yar kimanin sheKara goma Sha biyu haka, kyakykyawar gaske fara irin farin Nan Mai hade da Kamar golden yellow , idanunta dara-dara farare tas sai gashin kanta bakirkirin har gadon bayanta hancinta irin dogon Nan ne har baka bakinta Dan karami Mai dauke da 'yan jaja-jaja pink-pink din lebe, bazaka kirata doguwa sosai ba irin tsaka tsakiyar nan, jikin lublub Kamar Mai rayuwa a kasanshen sanyi komai nata Mai kyau ne Wanda idan ka kalleta saika Kara kallonta Dan Allah s.w.a yayi Mata sura Mai kyau na a gani a Kara kalla. Da sallama ta shigo cikin gida tana fadar "wash Allah Ammah wallahi na gaji wadannan littatafan sunyi nauyi da yawa inaga sai dai na kwafo time table kullum na ringa zuwa da Wanda zamuyi amfani dasu kawai". Ta fada tana kokarin Ciro jikar daga bayanta, dariya Ammah tayi tana fadin "ke dai anyi raguwa wallahi zahra ke Sam bakya da juriya jakar da Zaki Goya zuwa mota ma neman gagararki tajeyi". Kwantawa tayi saman kujera tana fadin "Allah da nauyi dauki fa kiji". Sulaiman ne ya shigo shima da tasa jakar a kafada Yana dariya. "Kai Kuma dariyar me kake?" Ammah ta tambaye shi. Zahra ya nuna Yana cigaba da dariya. Baki ta zumbura tana dira kafa tana fadar "Allaha Ammah ki rabani da Ya sulaiman Kinga tundazu yake min dariya Kuma nace ya tayani daukar jikar ya Kiya". "Wai Kai meye haka kazo kana ta dariya Kamar wani sabon kamu". Jakarsa ya jefa kusa data Zahra kafin ya zauna Yana ba Ammah labari. "Wato Ammah muna hanyar dawowa ne man motar ya Kare tunanin Malam Bala harya kawo mu gida man Bai Kare ba saboda yace ya biya gidan man yaga da layi idan yace zebi layin zamu Dade muna jiransa shine kawai ya taho, to muna zuwa wurin gidan sarki kawai man motar Nan ya Kare shine fa muka tako a kafa, ita Kuma gwanar iya son jiki ta wani shagwabe mini Wai na daukar Mata jaka na hada da tawa Kamar wani jaki, shine Dan tsabar rainin hankali Wai to na dauka zata karbi kudin gurin Abba ta biyani Kamar wani Dan dako". Tsaki Ammah tayi tana hararar Sulaiman din "wannan shine abin dariyar Kuma wallahi kayi girman kwabo da meye amfanin hada babba da yaron ba saboda taimakon ba". "A'a Ammah duka da wata biyar fa na girme mata, to Ina wani girma sa'anni muke ba gashi ajinmu daya ba da dai su Ya Sadiq ne su Aunty Janah, kuma fa duk su Hameeda kowa fa ya dauko tasa sai itace tafi kowa son jika za'a daukar Mata wa zata yiwa karatun ba kanta ba". Ya fada Yana cire safarsa. Fita Ammah tayi, ita Kuma Zahra ta shige bedroom din Ammah ba Wanda ya Kara bi takan sulaiman.wanka ta shiga tayi kafin taci abinci saboda Bata son ta makara a islamiyya Sam Bata son abinda ze taba lafiyar jikinta tunda a makarantar bokon suke sallar Azahar. Lokacin data fito tana sanye da uniform din islamiyya da Jakarta tana kokarin shiga dakin Mama ta biya Hameeda ne taga Hameedar da wani Kaya a wata leda babba ta fito tana zumburar Baki. "Ya Naga Baki shirya ba ko bazaki makarantar ba? Kinga fa yau zamu bada hadda". Mama ce ta fito daga dakin tana hararar Zahra "to uwar kinibibi bazatan ba ki Kama hanya ki wuce, ko zata ai bazaku tafi tare ba ana gqninki waye ze kalleta na nuna Miki bana son kina shige Mata amman kin kasa ganewa, Haba yarinya sai kwawa" Duk wanna maganar da Mama takeyi a hankali take fada Banda Zahrar da Hameedar ba Mai jin abinda take fada duk da Ammah na kofar kitchen dinsu Wanda yake kusa da bangaren na Mama. Daki Mama ta nunawa Hameeda ta koma yayin da Zahra ta nufi Ammah tana fadin "Ammah na tafi" "To Allah ya bada sa'a a maida hankali ki biyawa Mujiba ki tafi". "To" ta amsa ta nufi waje da sauri. Saida dama Ammah tana ankare da Mama Sam Bata son Zahra na mu'amala da Hameeda kwata-kwata sai Kuma Allah ya hada wata irin kauna tsakanin yaran salma ce Sam basa jituwa da Zahra da ita wata sakarai ce da zahra ko ruwa Mai dadi Salma bazata Bari Tasha a gidan ba, motsi ba motsi ba sai ta Fara fadin ai dai Nan ba gidanki bane ke 'yar riko ce. Lokacin da Ammah taji maganar a bakin yarinyar tayi mamaki sosai Dan a lokacin wayonta Bai Kai ta iya banbance tsakanin Dan gida na ruko. Da Ammah ta tsareta ta fada Mata wayace Zahra ba 'yar gidan bace sai tace " Mama ce ta fada tace min na duba Mana Naga ko kalar jiki mu ba iri daya bace mu daina tafiya ma da ita, Wai ta fimu kyau idan muna binta idan muka girma baza'a sure mu ba". Kan Salma Ammah ta dafa tana fadin "itama 'yar uwarku ce kuyi zumunci da ita kinji" kai ta gyada alamar to. Abin ya jima Yana baiwa Ammah mamaki Bata zaci haka a gurin mamar ba, tunda a zahiri ba komai a tsakaninsu sai mutunta juna duk da tasan sha'anin kishi ta ciki na ciki ne ta baka na baka. Sai kusan magariba su zahra suka shigo hannunsu na sarkafe da juna ita da Hameedar, daga gurin Aiken ta wuce makarantar Amma Tasha bulalar makara. Bayan sun Gama cin abincin dare ne suna hira a dakin Ammah Hameeda ta shigo ta gaishe da Ammah ta zauna sukaci gaba da hira lokacin Ammar tana dakin Abbansu ta Kai Masa abinci. Lokacin data shigo dakin ya kacame sunata musu akan wani aiki da akayi musu yau a makaranta su matan suna ga yanda za'ayi shi Kuma Sulaiman Yana fadar ga yanda za'ayi, Ammar ce ta zauna tana fadin su kawo ta gani maths ne, Kuma duk hanyar da akabi za'a kaiga samun amsar Dan haka tace kowa yayi nasa yanda ya fashimta. Har ta shiga bedroom dinta ta fito tana fadin "Na manta Abbanku yace na fada muku ranar Saturday zakiyi jarabawar share fagen shiga karamar secondary school ta kwamnatin tarayya, yace kuyi karatu duk Wanda baici ba baze saimasa ba Saida yaci gaba a makarantar da yake". Murna suka farayi da gudu Hameeda ta nufi dakinsu Dan ta fadawa Mama. ******Alhaji Jafar Mai yadi haifaffan garin Azare ne ta jihar Bauch a unguwar fanfon shanu, su hudu ne iyayensu suka Haifa uku maza sai autarsu daya mace amman su biyu suka rayu biyu tun suna Yara suka rasu, sun taso shi da kanwarsa Amina a hannun Babarsu Hajiya Fatima wadda ake kiranta da Nanna, kasancewar Babansu Malam Ibrahim Wanda ake Masa laqabi khalilu Allah yayi masa rasuwa tun Yana aji day na babbar sakandire Amina Kuma tana aji shida na primary. Sun Sha wahala kasancewar mahaifan su ba Mai karfi bane Bai bar musu wani Abu Mai yawa ba daga gidan da suke cikin sai konaki biyu, tunda Jafar ya Gama babbar sakandire yake zaune a gida saidai dinkin hula da aikin hannu na riguna kusan dashi yake rike Nanna da Amina said Kuma 'yan kulle-kullen kayan Miya daaya kafawa Nanna jarinsu. A hankali Jafar yana Tara kudinsa lokacin daya da yaga kudin sun danyi auki ya nemi Shawarar Nanna akan yana son ya Fara sayar da Yadiddika na maza, tayi murna sosai ta dinga saka Masa albarka. Cikin ikon Allah ya Fara kasuwar da kafar dama Nan da Nan abun ya Fara bunkasa da taimakon wani uban gida da Allah ya hada jininsu yake bashi Kaya akan farashi Mai sauki har takai ga Fara tura shi aba Yana sawo Masa Kaya a hankali ya bashi aron kudi masu Dan yawa yace shima ya hada da nasa jarin ya sawo nasa kayan zeyi Masa kokarin shago kafin ya dawo. Nan da Nan al'amura suka kankama ba'a rufe shekara ba arzikinsau ya Fara habaka da taimakon Ubangidansa ya samu Yara masu amana ya zuba a shagon shi Kuma ya shiga cuku- cukun nema admission Nan University ta Bauchi cikin ikon Allah ya samu course din da ya nema Agricultural science. Cikin ikon Allah karatu ya kankama, yayin da a gefe ga kasuwanci Yana ta habaka. Lokacin Yana shiga level 300 lokaci Amina ta kammala secondary dinta manema sukayi Mata chaaaa, Amma an kada an raya ta fitar da gwani ta Kiya Wai duk Bata sonsu. Haha aka tattara aka kyaleta Jafar yaso ya nemar Mata gurbin karatun N.C.E Amma Nanna tayi tsalle ta dire ba za'a wannan aiki da

Chapter 5 of 31