Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tambayi dalili ba dan nasan ba kirana kai a matsayi uba ba, ka kira ni ne a matsayin Sarki, zanyi abinda kace sai dai inada tambaya, a makaho xan je mata?" Sarki yace " wannan na bar maka hukuncin domin ni Sarki ne wanda baisan d'ansa yana gani ba." Nagode, kawai abinda yace kenan ya mike. Suna fita daga gun ya tsaya cak, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe. Sabi'u ka dafashi yace "me yasa baka musa mai ba?" Yace " ta ina zan musamai bayan Umarnin Sarki ne bana uba ba?" Sabi'u ya kalleshi cikin tausayi yace " amma nifa hadin auren ya birgeni, Bilkisu itakadai ce gun Sarkin kano aurenka da ita zai karama matsayi da kuma daraja agun mutane." Abu Turab murmusawa kawai yai baice komai ba, Sabi'u ya kalleshi yace "yanzu ya zakai?" Juyowa yai saitinsa yace " Sabi'u nasan bazan samu abinda zuciya ta takeso ba dan haka banga wani damuwa ba akan auren wata, ban dauki auren nan wani abun ba banda biyayya da kuma raba gado da wata ba." Dariya ce ta kama Sabi'u yace " raba gado?lalai Turab bakada kyau, taya zaka dauki auren 'yar sarki akan raba gado?" Tsaki yad'an ja yace " to fadamim, soyayya ce?aminta ce?yan uwan taka ce? Ko kuwa shakuwa ce?" Dariya Sabi'u ya sakeyi baice komai ba. ******** Acan gidan Waziri kuwa Hisham kuwa tunda Khadija ta dawo zazzabi ya rufe ta yau sati d'aya kenan tana fama da zazzabi da ciwon kai. Wannan kenan *ABU TURAB TEAM 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *28* B'angaren Mahaifiyarsa ya nufa, tana zaune gefenta kuma Lantana ce, daga bayanta kuma a tsaye Mairo ce take mata kitso, jiki a sanyaye yai sallama. Dukansu suka amsa nan ya karasa ya zauna a kasa tare da lankwashe kafafunsa. Basira ta kalleshi sai dai batace komai ba, d'agowa yai yace " Umma gobe zani Kano." Gabanta ne ya fadi dan kuwa tasan me zaije yi kanon. Sam ta manta da Mairo dan kuwa hankalinta ya tashi, ta kalleshi tace " ka amince da ganin yarinyar ne ko kuwa har auren?" Idanu Mairo ta zaro cikin tsananin tashin hankali, kallan Abu Turab kawai tayi, shima jin kalaman Basira yasa ya d'ago ya kalli Mairo. Ganin yanda idanunta sukai yasa ya kalli Basira kansa na kasa yace "Mairo bamu guri." Jin haka yasa Basira ta juyo da sauri ta kalleta, ganin yanda kwallq ta ciciko mata yasa tace " Lantana shiga da ita d'aki " Mikewa Lantana tai ta ja ta ciki, suna shiga ta zube a kasa tare da hade kanta da gwiwarta, ba kuka take ba sai dai yanda takeji a ranta tabbas taso ace ma kukan takeyi. Tana iya jiyo muryar Basira sama sama tana cewa " Abu Turab nifa wannan hadin auren bai kwantamin ba, nafisan ka auri Mairo ko dan samun nutsuwarka da kuma kwanciyar hankalinka." Dan murmusawa yai yace " Umma kinaso ne na karya umarnin Sarki ko me? Abba ya kiranine a matsayin Sarki bawai a matsayin Uba ba, sannan maganar Mairo nicewa tai tana sona ko kuwa nice nace ina santa?" Shikam yasan tana sansa sai dai yayi hakan ne dan sa Umma ta saduda, ya cigaba da cewa " itama ta kanon xan dai jene kawai inbi Umarnin da aka bani amma tana 'yar sarki guda d'aya tilo mai zatai dani? Makaho?" Basira cikin bacin rai tace " Da farko amsarka xan ba, na tabbata kai kanka kasan Mairo tana sanka, sannan kaima nasan haka, sannan na biyu shi mai martaba cewa yai kaje a Makaho?" Gaban Mairo ne ya fadi, Lantana jin haka ta taso fa sauri daga inda take a d'akin tace " tashi ki shiga can ciki." Mairo ta kalleta tama kasa magana mikewa tai a hankali ganin yanda ta tsaya kamar me shirin faduwa yasa Lantana ta riketa, ji sukai Abu Turab yace " yace inje a duk yanda naso, nima haryanzu ban tantance a me zanje mata ba." Jitai kanta yayi wani irin sarawa, cikin rawar murya ta kalli Lantana tace " meke faruwa?" Lantana ta kamata suka fara tafiya, sai data kaita canciki sannan ta kalleta tace " ba abinda ya faru nikaina bansan me suke nufi ba." Mairo ta kalleta tace " amma dai ba kina nufin in yarda da kalamanki ba ko?" A makaho xakaje mata? Ta maimaita maganar da Basira tai sannan tacigaba da cewa " me hakan yake nufi? Duk wanda qwaqwalwarsa take aiki na tabbata xai gane magana ce aka yita mai ma'ana biyu, a makaho zakaje mata?ko da ido?" Lantana ta kalleta cikin tsoro, Mairo ta mike ta tsaya gaban Lantana tace " zan gyara tambayar dana miki d'azu, Yaya yana gani?" Idanu Lantana ta runtse batace komai ba, Mairo tace " zan kara gyara tambaya ta, Lantana meyasa yake pretending din baya gani?" Lantana ta girgiza kai tace " nima bansan komai ba, da sauri tabar d'akin tare da janyo kofa." Mairo tai shiru tana tunani, me yasa yaya yana gani yake nuna baya gani? Wani irin abu ne yau takeji haka? Abubuwan da sukai ta faruwa dashi yana yari ta tuna, kai ta girgiza tace bazai yiwu ace pretending yakeyi tun da ba sai dai in warkewa yai." A can bangarensu Basira kuwa, kallansa tai tace " Abu Turab harga Allah zaka cemin baka san Mairo tana sanka ba?" Kallanta yai yace " Umma!" Tace " ni mahaifiyarka ce nasan abinda zai taimakeka gun samun farincikinka, Mairo zata kula dakai, zata taimakeka ni aguna ita kadaice zata dawoma da farincikinka." Idanu ya runste yace " nifa Mairo kanwa tace ban taba tunanin zaman aure da ita ba." Jiyai tace " sai ka fara yanzu." Mamaki ne ya kamashi yace " Umma nawa nake? Shekarata kwatakwata nawa? Taya zakumin zancen auren mata ba d'aya ba har biyu a rana d'aya wanda kuma duk cikinsu ba alakar soyayya dake tsakaninmu?" Basira tace " Ba takura maka zanyi ba sai dai inaso ka duba ra'ayina ka kuma ba shawarata lokaci mai yawa." Sunyi shiru kafin tace " tashi kaje." Mikewa yai ya fita, d'akinsa ya shiga ya kwanta akan gado yana kallan sama. Mairo ce ta fito kana ganinta kasan tana cikin wani yanayi, Basira ta kalleta tace " Mairo jeki gida zansa a karasa min kitson." Kai ta girgiza alamar a'a tace " a'a Umma bari na karasa miki." Basira tace " jike Mairo, ninace kije ai." Jakarta kawai ta d'auka ta mata sallama tai waje. Tafiya kawai takeyi amma zuciyarta fal take da tunani kala kala tama rasa ta inda zata samo amsoshin tambayoyin. Jitai an fizgo hannunta, a tsorace ta juyo, janta kawai taga yayi soron kusa da gun ya sata a ciki. Hannunta ta shiga fizgewa ta hada cewa " Malam meye hakan? Sakarmin hannu ko?" Baisake ta ba ya d'ora da cewa " da dan rashin mutunci kina ganina kika wuce ni?" Kallansa tai cikin takaici tace " Malam sakeni dan Allah, ni ba muharamarka ba zaka wani dinga rikeni? In magana zakamin kamin da baki." Murmushi taga ya saki yace " Karki damu saura kiris ki zama matata dan na kula shi kadai ne yanya mafi sauki da zan daidaita miki sahu." Kallansa tai cikin takaici tace " in zama matarka? To ko nidin baiwa ce banaji kamada damar yanke hukunci akaina bare kuma....." Katseta yai tare da sakin hannunta yace " kin dai san nidin waye kin kuma san matsayina a garin nan, ko Mahaifinki bai isa in yanke hukunci ya canza min ba." Dan karamin tsaki taja sannan ta kalleshi ido cikin ido tace " Abdulmajid kake ko wa?" Idanu ya zaro ya kafeta dasu, tacigaba " Zan maka kashaidi xa gargadi na farko kuma na karshe, in har zamuyi magana dakai ka kiyayi min abubuwa guda biyu, na farko kada ka kuskura ka kara rikeni ko ka taba ni ko da kuwa hijab din jikina ne, na biyu kuma kada ka kuskura ka dinga sako iyayena in muna magana, ni yanzu banda lokacin ka abinda ke gabana yafi karfin na tsaya ina bata lokacina." Matsawa tai da nufin wucewa, fizgota yai da karfi ya bugata jikin bango yace " ke harkin isa ina magana kina magana, har kina da matsayin da zaki kira sunana gatse gatse har kice zakimin gargadi?" Ajiyar zuciya tai tace " in kaji haushi inji sammaci." Tana gama fadar haka ta ture hannunsa tai waje. Kallan bayanta yai cikin kuluwa yace " mu zuba mu gani, ina tausaya miki in kika shigo hannuna, auranki kuma ya zama dole a gareni." Yanajin haushin yanda baya iya yanke mata hukunci duk wulakanci da zatamai. Itakam ranta a bace tai gaba, tana kokarin fita taga wata kamar Khadija ta wuce, binta tai da kallo cikin mamaki da san tabbatar da abinda zuciyarta ke zargi. Khadija kam bata kula da ita ba dan ba lafiya ce ta isheta ba yanzun ma daliline ya shigo da ita. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻*   🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *29* Khadija bangaren Magajiya ta isa, tana shiga ta taddata a zaune, karasawa tai ta gaisheta, Magajiya ta kalleta cikin kulawa tace " Khadija sannu, ina nan hankalina a tashe ina tunanin yanda jikinki yake, Khadija ya akai haka? Duk kin rame." Khadija ta d'ago ta kalleta bata bata amsar tambayarta ba sai jitai tace " Umma an tura wani ya dubo Inna Lami?" Magajiya tad'an tabe baki kadan sannan ta kalleta tace " na tura, sunce jikin da sauki." Hawaye ne ya zuboma Khadija tace " Umma me yasa bakwasa tausayi a ranku?" Hade rai Magajiya tai tace " KHADIJA!" Khadija tana kuka tace " makociyar Inna Lami ba ta aiko a sanar daku jikinta yayi tsanani ba?" Magajiya tace " a yaushe akai hakan?" Khadija tace " amma tace ai ta sanar da Yaya, Umma Allah ya d'auki ran Inna Lami, ita kanta bata sani ba tunda ita tasan ta sanar da Yaya ta dauka anje an dauketa, ita kuma a ranar tai tafiya, sai jiya da ta dawo ta shiga gidan ta ganta duk ta kumbura da alama ma ta dade da rasuwa, nan tasa aka kira mutane aka mata sallah aka kaita, d'azu da naje take sanar dani......" Kukanta ne ya tsananta sanda tazo karshe. Tace "Umma Inna Lami fa kanwar Mahaifiyar ku ce, tayaya zaku..." Ya isa haka! Abinda Magajiya tace kenan, d'agowa Khadija tai ta kalleta, dan tayi maganar ne da kakkausar murya. Magajiya tacigaba " Ya isa haka Khadija, Inna Lami ta rasu Allah ya jikanta, zansa aje gidan, ke kuma jan maganar ya isa, ba kuma na san ki kara tada maganar nan." Kallanta Khadija ta shiga yi cikin tsananin mamaki, Magajiya ta kalleta tace " ki tashi ki koma gida zan aiko miki da magani da abubuwan bukata, banasan ki dinga kwanciya ciwo akan abinda bai kai ya kawo ba." Sam ma ta rasa me zatace sai kallan mamaki kawai datake binta dashi. Ganin batada niyyar kara magana yasa Khadija ta mike ta fito daga d'akin. Ba shakka yau taga abin mamaki ace d'an uwanka na jini? Sannan harda wani wai batasan taga tana kwanciya akan abinda bai kai ya kawo ba? Kenan abinda sukama Turab da wannan rashin kula da Inna Lamin da sukai ba wani abin bane a gunsu? Samun kanta tai kawai da bin hanyar da zata kaita gun Abu Turab. Sai dataje kofar shiga ta tsaya tana tunani me zatace mai? Tabbas ganinsa ne kadai zaisa taji saukin wannan abin. Tura kofar tai a hankali, Mai kula da gun ne ya taso ya gaisheta, a hankali ta furta Ya Turab nanan? Yace " eh yana ciki, a sanar mai da zuwanki?" Tace " bari na shiga ai kasan ni ko?" Kallanta yai yace " na sani amma taya....." Gani yai kawai tayi gaba batama san yanayi ba. Falo ta duba ganin bayanan yasa ta tsaya taba kallan falon, idanunta ne suka kara zubo da wasu kwallar sannan a hankali ta nufi kofar d'akinsa kwankwasa wa tai daga ciki yace " waye?" Shiru tai sai kuma ta kara kwankwasawa. Mikewa yai ya bud'e kofar. Kallanta yai sannan yai saurin kauda kai ya kara cewa " waye?" Kallansa ta shiga yi hawaye na zubo mata, a zuciyarta tace "Yaya ina cikin wani hali, su Umma Magajiya, Yaya, da Abbana sun fara bani tsoro, banaji suna da digon tausayi a zuciyoyinsu, Yaya ya zanyi in canza su? Ya zanyi in nuna musu hanyar gaskiya?" Hawayenta ta shiga sharewa, jiyai zuciyarsa na kuna ya tsani yaganta tana kuka, gashi yaga ta rame sosai da alama rashin lafiya tai, daurewa yai ya juya da nufin komawa ciki, jiyai tace " nice Yaya." Juyowa yai yace " Khadija? Me kike a nan?" Ta daure tace " ganinka kawai nazoyi, ya hannun naka?" Fuska ya had'e yace " me zaisa ki damu da ciwon da baikai ya kawo ba, bayan kece kike bukatar kulawa?" Daurewa tai tace " yaya ya warke?" Labansa yadan ciza yace " Khadija meke damunki? Me yasa bakya fahimtar abinda nake nufi? Kina tunanin in kika nuna damuwarki akan ciwona kika wulakanta naki lafiyar zanji dadi? Me yasa kike san ki dinga sani cikin damuwa?" Kallansa tai fuskarta cike da mamakin kalamansa, tace " Yaya." Idanu ya d'an runtse yace " please in har kinasan ki nuna kulawarki a kaina to ki kula da lafiyarki." Juyawa yai ya koma ciki, ya rufo kofar. Shiru tai sai hawaye da suke zubowa daga idanunta, jingina tai da jikin kofar, shikansa yana shiga ya jingina da jikin kofar. Idanunta a lumshe tace " Yaya." Bai amsa mata ba sai dai yana jinta, tacigaba " Kayi hakuri yaya, kayi hakuri da rashin sanar dakai tafiyata fa banyi ba, kasan ina zaune a gunka lokacin da aka aiko inje, ina zuwa aka sani a mota ko gida ban shiga ba, kayi hakuri da rashin nemanka dabanyi ba, tunda naje garin ba'a kara barina na zo ba sai wannan dawowar." Iska tadan furzar sannan tace " Yya kayi hakuri na abinda su Umma Babba sukama, sannan kayi hakuri na rashin baka hakuri da sukai." Ransane ya bace ya bud'e kofar da karfi, hakan yasa tai saurin gyarawa ganin ta kusa faduwa, a fusace yace " meyasa kike bada hakuri? Me kikai? Me yasa kike bada hakuri a koda yaushe? Bayan wadanda ya kamata su bada hakurin basusan ma sunyi laifi ba? Me yasa Khadija? Meyasa kike neman tadamin hankali?" Kai ta shiga girgizawa har ya gama fadan sannan tace " Yaya na san....." Katseta yai yace " Khadija meyasa bazaki fahimceni ba? Banasan kina yawan bani hakuri hakan na sa inji kamar nine nake miki laifi." Daurewa tai tace " Nadaina yaya." Yace " Khadija please....." Murmushi ta kakaro tace " na daina Yaya, nazo ne dan ina cikin wani hali zuciyata bata kawo min kowa ba sai kai, shiyasa nazo." Kallanta yai yace " me ya sameki?" Murmushi tai tace " hmm inama Yaya kana gani? Da kaganni ina ma murmushi." Shiru yai baice komai ba, tace " Haryanzu addu'ata kenan, Allah ya bud'ema idanunka." Murmushi taga yayi, itama murmushin tai sannan tace " Ahh da alama zuciyata tayi sanyi,duk da hankalina haryanzu bai kwanta ba." Yace " me ya faru kuma?" Tace " Inna Lami ta rasu." Yace " yaushe?" Kallansa yai tace " ba'a san yaushe bane." Kallan mamaki ya mata, ganin zata d'ago yasa ya kauda kai yace " ban gane ba." Zama tai a kasa a jikin bango, ta kama rigarsa tace " Yaya zauna plz." Zama yai dan ya kula tana bukatar mai lalashi." Zayannemai komai tai. Hankalinsa ya tashi, lalai mutanen nan basuda imani, wato abin ma harda jininsu? Khadija ta d'ora da cewa " Yaya in kaine me zakayi?" "Hmmm in nine ba abinda zanyi." Tace " ba abinda zakai?" Kai ya d'aga alamar eh yace " me zanyi to? Abin nan dai ya riga ya faru, sannan mutanen na basu nuna tausayawa ko dana sani ba, ni da nake d'a me kike tunanin zanyi? Sai dai...." Shiru yai hakan yasa tace " sai dai me?" Yai ajiyar zuciya yace "sai dai dole girma da darajarsu zai ragu a idona." Tace " na fahimceka Yaya na kuma gode." Mikewa tai tace " yau naji dadin dana dade banji ba duk da wata zuciyar tana tausayawa Inna Lami, sai dai wata zuciyar tana farin cikin zama tare da kai danai wanda na dade ban samu ba." Baice komai ba, tace " nagode yaya." Ta fada tare da tafiya. Kallo ya bita dashi sannan ya mike a hankali ya koma ciki. Ya zaiyi? Ya zaiyi? Ba shakka yanasan Khadija sai dai yana ganin auransa da ita ba mai yiwuwa bane, tsanar Magajiya da ahalinta ne suka kara shigarsa jin labarin da khadija ta bashi. Kansa ya dan shafa yace " Ya zanyi?" *TEAM ABU TURAB 🤝🏻*   🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *30* Wajen karfe sha biyu na rana ya fito daga bangarensa sanye da shadda mai kyau da tsada da yake kayan mu na da masu kyau ne da quality kai ka dauka sabuwa ce, yayi kyau sosai sannan ya zuba wasu kayan a cikin yar karamar jaka tunda Mai Martaba yace kwana biyu zasuyi a can din. Sabi'u ne ya zo kusa dashi yana dan tafi yace " Yayai Ango ai da alama Bilkisu takace, ta ina zatai wasa wannan saurayin ya wuce ta?" Fuska ya d'aure tamau yace " zaka fara ko?" Sabi'u yazo gefensa yace " Nadaina Ango." Abu Turab yace " matsalarka ce wannan, mikam mu tafi." Su biyu suka fito dan ko Garzali bai dauka ba, dan Mai Martaba yace zuwan nasu kano ya zama sirri. Bangaren Mahaifiyarsa yaje ya mata sallama, duk da ranta baiso sai dai tamai fatan alkairi, ta kudura a ranta in har Bilkisu ta aminta dashi to fa yana aurenta zatasa ya auri Mairo, in kuma bata amince ba to dama ita hakan take so. Ya fito suka shiga motar da Mai Martaba ya umarcesu suje, suna fita daga kofar gidan ya ga Mairo jikin katangar gidan a tsaye, sun hada ido sai dai da sauri ya dauke na sa idan, ya tabbata fitowa tai dan taga tafiyarsa, shikam tausayinta yake, yana kuma mata fatan samun miji na gari. Sunyi da nisa, jefi jefi suna dan taba hira, sun danyi shiru kafin Sabi'u yace " Abokina!" Turab yace " ya akai kuma? Dan nasanka sarai wannan Kiran kira ne na tambaya." Sabi'u yace " tun jiya nakeso nai ma tambayar sai dai na rasa ta inda zan fara, ba kuma nasan mu samu sabani saboda ita." " ina jinka." Sabi'u yai shiru kafin ya dan kalli titi sannan yace " me kake nufi da a makaho zanje mata?" Abu Turab bai ko kalleshi ba bare yaga alamar mamaki a tambayarsa, Sabi'u yana tukinsa yace " ba wai naso naji maganarku bane da mai martaba sai dai jin maganar nai daga inda nake tsaye." " Ina gani." Abinda Abu Turab ya fada kenan, cikin tsananin mamaki Sabi'u ya gangara gefen titi yai parking, Abu Turab ya kalleshi yace "meye abin tsorata? Harda tsayawa?" Sabi'u yace " ban gane kana gani ba?" Murmushi Abu Turab yai yace " Kaya ruwan toka ne a jikinka ka sa hula baka, sannan kaidin fatsi ne, kanaso in cigaba?" Sabi'u idanunsa a waje yace " Yaushe ka warke?" Abu Turab yai murmushi yace " that's not important, ka wuce muje." Jiki a sanyaye Sabi'u ya tada mota, da kyar ya iya furta amma me yasaka pretending? Shiru Abu Turab yamai, jin haka yasa yasan bazai amsa mai ba, sun dade a haka kafin Abu Turab yace " sanar dani halayenta da akace ka binciko." Sabi'u yace " Bilkisu ita kadai ce mace a gun Sarkin Kano, yarinyace mai kyan gaske, dan kowa yana fadan irin kyan datake dashi, mace ce mai tausayi ayanda aka fada tanada saukin kai, ko kadan batasan a tozarta wani." Shiru yai hakan yasa Abu Turabya kalleshi yace " shi kenan?" Kallansa Sabi'u yadanyi yace sai dai tanada matsala d'aya. Abu Turab ya kalleshi yace " na me kenan?" Sabi'u yace " batasan a komenene a hadata da wani, wannan dalilin ne yasa taki aminta da duk mazan da suke kawo mata hari, a yanda naji ita kishi ko na menene batasan tayi dan tanada zafin kishi." Tsaki Abu Turab yai yace " zancen banza takeyi kuma kenan baya yarda da kanta ba, in har tanaji da kanta tana ganin komai nata yayi 💯 banaji ya kamata ta dinga wannan shirman, wannan alamace na akwai abinda take lacking." Sabi'u ya girgiza kai yana dariya yace " lalai Turab bakada kyau, yanzu kishin ma sai ka fassarashi? To ita kishin in hallitarta ce fa?" Baki yadan tabe yace " sai ta danne shi tunda ba ita tai kanta ba." Sosai yaba Sabi'u dariya, haka sukai ta zancen Sabi'u na kara dariya, sun isa kano da la'asar gidan Sarki suka wuce direct, Mai Martaba sarkin Zariya ya riga ya sanar da Sarkin kano akan zuwan nasu, suna zuwa aka wuce dasu ma saukin su, aka kuma turo musu bayi guda uku masu kula dasu. Sunyi wanka sunyi Sallah sannan aka kawo musu abinci. Abu Turab ya kwanta akan gado tare da daure hannunsa kan goshinsa kamar yanda ya saba, Sabi'u ya kalleshi yace " Malam Makaho sauko muci abinci." Murmushi yadan mai yace " fara ci." Sabi'u ya matso kusa dashi yace " kodai ka kosa ka ganta ne? Dan na kula tunaninta kake yi." Abu Turab ya juya mai baya yace " kasan ni din ai ba kai bane." Saida Sabi'u ya kusan gana cin abincin sannan shima ya sauko dan kadan yaci ya mike ya fito wajen harabar gidan. Wata yarinya ya gani wacce batafi shekara 12 ba tana leko shi. Alama ya mata da hannu akan tazo, tsayawa tai tana wasa da yatsun hannunta, Abu Turab ya tako har inda take ya dan rusuno yace " yan mata me kike anan?" Kallansa tai tace " Kaine Yarima Turab?" Cikin mamaki ya kalleta yace " kin san ni ne?" Kai ta girgiza tace " Aunty na ce ta aikon inganka." UmmaBilkisu?kina nufin Gimbiya Bilkisu?" Kai ta daga alamar eh, sannan tace " amma karka fada mata kaji." Murmushi yai yace " naji kedin wacece to?" Tace " babana shine Yarima Nazir magajin sarki." Kai ya jinjina zaiyi magana yaga ta juya da gudu, mamaki ne ya kamashi ya juya bayansa, ganin Sabi'u yasa ya fahimci ganinsa ne yasa ta gudu, murmushi yai sannan ya juyo. Sabi'u ya karaso yace " Kai da waye?" Abu Turab ya juya yace " bakowa." Sabi'u ya matso yace " an turo wai bayan Magrib zamuje." Harararsa yai yace " Zamuje ina?" Sabi'u ya matso wajen kunnensa yace " Zance mana." Abu Turab yace " dakai zanje zancen?" "Eh mana, da kai da wa?" "Sry Malam ni kadai zanje." Sabi'u yace "Mai Martaba cewa fa yai in bika." Kafadarsa ya dafa yace "sry mutumina amma ni kadai zani." *******   A can kuwa Bilkisu ce xaune a d'aki, Munnira tana shigowa ta kalleta tare da mata alama da hannu akan ta matso, sannan ta sallami masu kula da ita, kallan Munira tai tace " Munnira ya?" Munnira tace " Nikam Yamin UmmaBilkisu dama kibarmin shi." Harararta Bilkisu tai tace " abinda na aikeki kiyi kenan?" Munnira ta turo baki tace " Nidai shi zan aura." Bilkisu ta harareta tace " ni tashi kiban gu bansan kayan haushi." Bayan Magrib bayinta suka kara shigowa aka gyarata sosai,wasu kaya ta saka sun mata kyau sosai, karan miski ne an mata doguwar riga, dashi

Chapter 12 of 37