Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kalleshi yace " menene?" Magajiya ta kalli Turab cikin takaici da san jin me yake shirin yi." Turab ya d'ago yace " godiya nake, magana ce game da Hajiya." Da sauri Magajiya ta kalleshi. Yai murmushi sannan ya cigaba " Bayan mun kai Hajiya asibiti likita yayi bincike gun warkar da ita, a lokacin ne ya gano cewar guba ce aka bata wacce ta nakasar mata da duk gab'obin jiki." Inalilahi wa ina ilaihi raji'un, abinda yake fitowa daga bakin jama'ar gun kenan, Abdulmajid da sauri ya kalli Magajiya. Turab ya mika ma dogarin dake tsaye akan Sarki takardar yace " ga abinda likitan ya rubuta." Duk da sarki yayi mamakin jin wannan zancen wai likita? Bayan har Hajiya ta warke Turab baisan inda take ba, sai dai bai bari mamakin ya bayana ba a fuskarsa. Amsar takardar yai ya gani sannan ya mika aka bi kowa aka nuna mai. Sarki nuna bacin ransa yai kamar irin baisan komai din nan ba, yace " Guba kenan aka shayar da Hajiya?" Turab yace " sosai, sannan inada shaidar da zata sanar damu hakan." Nan yace shigo. Yarinyar dake waje aka ce waye xai shigo? Nan tace nice, tare da shiga. A tsorace ta shiga, tana shiga ta zube a kasa tare da gaisuwa. Sarki yace " kece shaida akan abinda ke faruwa?" A rikice tace " Tuba nake ranka ya dade na cancanci hukunci mai tsanani." Galadima yace " tashin hankali." Turab yace " sanar damu abinda ke faruwa." Yarinyar ta d'ago tana kallan Turab a tsorace. Turab yace " sanar damu abinda kika sani." Magajiya ta kalleta duk ta rasa me zatace. Hisham kam idanunsa kawai ya runtse dan yasan yau kam sai dai Allah. Yarinyar ta kwashe komai ta sanar dasu. Mai Shari'a yace " yarinyar data baki maganin tana nan?" Kai ta girgiza alamar a'a, dan mai baiwa ce." Sarki yace " wannan alama ce ta kenan wanda ya bada umarnin mutum ne mai mukami." Turab yace " a wani bangaren take aiki?" Magajiya ta kalla sannan ta sunkuyar da kai. Magajiya tace " kanaso kace guba aka ba Hajiya? Wani mara imanin ne zai in aikata hakan?" Turab yace " ina muka sani, ko mara imanin na cikin d'akin nan?" Bai bi takan me zatace ba ya kalli Yarinyar yace " a wani bangare take aiki yarinyar?" Yarinyar ta nuna da yatsa, yatsar kowa yabi sukaga ta tsaya akan Magajiya. Magajiya tai murmushi tace " ba dai ni kike nunawa ba ko?" Kallan Magajiya kowa yai. Yarinyar ta sunkuya sannan tace "a bangareki take aiki sannan tace inhar ban sa maganin ba......." A zuciye ta mike tace " ke dan gudanku sharri zakimin?" Sarkin yace " Magajiya me kikeyi hakan?" Tace " ban gane me nakeyi ba, bayan ina zaune ana neman ace nine nake neman halaka Hajiya, meye dalilin da xai sani halaka mahaifiyarka?" Turab yace " shine yanzu zan sanar." Tace " mene?" Turab ya kalleta sannan ya kalli ragowar matan sarki yace " ko zaku iya tuna shayin da Magajiya ke baku a shekarun baya?" Kallan juna sukai dukansu harda Basira, sannan sukace eh. Turab ya kalli Magajiya sannan yace " Magajiya tana saka magani a ciki wanda zai hanaku d'aukar ciki a wannan shayin, bansan dalili ba wanda yasa daga baya ta canza tunani ta koma shayar da Sarki wannan shayin." Mikewa tai sannan tai wani murmushi tace " mene?" Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham yace " Waziri me zakace game da sharhi na?" Hisham ya kalli Magajiya sannan ya tuna ziyartarsa da Turab yai jiya, ya sanar dashi abinda ke faruwa da Hajiya da abinda ta sani har Magajiya ta mata hakan, Hisham yace tabbas shine ya amso maganin dan akan matan sarki aka fara. Magajiya ta kalli Hisham tace " Yaya me kenan?kana nufin kaine ka sanar dashi wannam kagagen labarin?" Hisham ya kalleta yace "Magajiya sai yaushe ne zaki daina san kanki?" Kallan sarki tai tace " bansan wannan labarin ba, sai dai in shi Hisham din shine ya aikata hakan." Gaba d'aya d'akin kowa kallanta yakeyi. Khadija kuwa gaba d'aya jitai kanta na wani juyawa, Abdulmajid kam idanunsa kawai ya rufe, ita kanta mahaifiyar Khadija ta girgixa da jin wannan muguntar. Bilkisu kam kallan Magajiya tai cikin tsananin mamakin wannan muguwar zuciyar tata. Sarki ya daka mata tsawa yace " ashe bakida imani?" Kallansa tai itama tace " dama abinda kake fata kenan ya faru, ko kana tunanin bansan so kake kaga bayana ba?" Sarki yace " mene?" Tace " da kai da danka kun hada kai kuna neman mun sharri, shine yanzu zakace wai banida imani?" Hisham yace " Magajiya!" Kallansa tai tace " yimun shiru tsohon munafuki, ni zakaci amana?" Khadija tace inada magana. Kallo ne ya dawo kanta, Turab ya zuba mata idanu. Khadija tace "tuba nake ranka ya dade amma Umma Magajiya da Abba sun aikata laifin dayafi wannan." Magajiya ta kalleta sannan tai dariya tace " khadija ke kam wa kike tunanin zai yarda da maganar ki? Bayan kowa yasan yanda kike bala'in san Abu Turab? Banaji akwai abinda zai saki da bazaki aikata ba." Da sauri Bilkisu ta kalli Khadija sannan ta kalli Turab wanda hakan yayi daidai da kallanta dayai. Murmushi ya sakar mata sannan ya d'auke idanunsa da sauri ya kalli Magajiya yace " Umma bakya tsoron incigaba da magana? Ko zaki fad'i sauran laifin da kanki?" Tace " laifi?ni ba laifin dana aikata." Turab yai murmushi yace " idan har zan sanar da laifufukan da kika aikata banaji wannan rana xata ishemu." Magajiya tace " good kun kyauta, sai kuce yau ba ranar bincike bace akan abinda akama d'ana, ranar yimun sharri ne." Turab ya kalli Sarki yanasan tona d'ayan sirrin sai dai inya kalli Abdulmajid ya kuma kalli Sarki sai ya kasa. Kansa ya sunkuyar yana tunanin abinyi. Muryar Andulmajid ce ya katseshi dayace " Umma ya isa haka nan, sao yaushe ne zakiyi nadamar abinda kika aikata?" Tace " mene?" Cikin murya mai sauti yace " Umma please ki tsaya haka nan, a da ina tunanin san da kike mun ne yasa kike aikata abinda kike aikatawa sai dai yanzu jin abinda kikema matan sarki da kuma shi kansa yasa nasan san kaine kawai naki, sai yaushene zuciyarki zata gamsu da abinda take so? Sai na zama sarki? Ko sai kin ganki akan gangarar mutuwa?" Tace " Abdulmajid." Abdulmajid yace " kin rabani da Mahaifana, tunda nake ban taba kiran matar data reni cikina da sunan uwa ba, ban taba kyautata mata ba a matsayin wacce ta d'au cikina na wata tara ba......." Da karfi tace " YA ISA HAKA!" Turab ya runtse ido tare da cewa thanks Abdulmajid. Inalilahi wa ina ilaihi raji'un....... Ba shakka wannan kalaman sunfi tadawa kowa hankali, Hisham kam hawaye ne ya zubo masa, Turab Sarki ya kalla wanda gaba d'aya zuciyarsa tayi wani nauyi, kallan Abdulmajid kawai yake yana nanata kalamansa. Bilkisu ce ta daure ta kalli Abdulmajid cikin mamaki tace " kana nufin ba Umma Magajiya bace Mahaifiyarka? Ba kuma Sarki ne ya haifeka ba?" Gaba d'aya zubama Abdulmajid ido akai cikin mamaki. Khadija kam hawaye ne ke zubo mata, itakam Umman Khadija jitai hawayen ma sun kafe kaf sun kasa ma zubowa........ *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* Gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyan littafin nan gabaki d'aya, ina godiya kwarai da kaunar da kuke ma littafin nan, nagode da hakuri dani na rashin posting akai akai da kuke, ni kaina ba hakan naso ba. Always love u....... *86* Wani irin ihu Magajiya ta saka da karfi tace " ABDULMAJID....." Mikewa tai a zuciye ta isa inda yake, ta d'aga hannu zata zabgamai mari, da sauri Turab ya tsaya a gabanta. Kallansa tai idanunta duk sun kada sunyi jaa, kallan juna suka shigayi, tana mai wani irin kallo wanda ba komai a ciki sai tsantsar kiyayya. Mai Martaba idanunsa a rufe kawai suke saboda jin abin yake kawai yana mai yawo akai. D'akin yayi tsit kowa da abinda yake sakawa a ransa, wani dogari ne ya shigo da gudu ya tsugunna, Barde ya kalleshi yace " lafiya kai kuma?" Cikin in in na yace " mai kula da kofar gidan mai martaba ne na cikin gari." Galadima yace " to ya akai?" Bakinsa ya shiga motsawa ya kasa magana, Basira tace " ya akai Hadi?" Da sauri ya ya maida kansa kasa ya sa kuka, Turab ya kalleshi ganin yanda yake kuka yasa Turab ya matsa daga gun magajiya ya taho inda yake yace " Hajiya......" Wani kuka dogarin ya saka, da sauri Sarki ya bud'e idanunsa wanda gaba d'aya sun yi jaa, mikewa yai yana kokarin takawa baya yai da sauri dogarawan dake bayansa suka tareshi, kallansu yai sannan ya kwace jikinsa ya koma ya zauna saboda jirin da yakeji, Dogarin yace " Allah yama Hajiya cikawa yanzun nan......" Inalilahi wa ina ilaihi raji'un......Abinda kowa dake d'akin ya shiga fada kenan, Banda Magajiya wacce take tsaye, sai Sarki wanda gaba d'aya yaji kansa ya kulle ya kasa tunanin komai. Turab ya karasa inda yake da sauri yace " Abba!" Idanunsa ya sauke akan Turab cikin tsananin tausayawa, ba shakka lalai bai cancanci mulkin nan ba, lalai laifinsa ne na kyale Magajiya tun farko ta dinga yin abinda taga dama. A hankali ya fara karanto inalilahi a ransa, kallan Turab yai sannan yace " jeka zauna." Turab ya mike ya koma gun xamansa. Gaba d'aya d'akin yayi tsit kowa ya koma gun zamansa, Sarki ya mike tsaye tare da zare rawanin kansa ya ajiye akan teburin dake gabansa, sannan ya tako a hankali har zuwa inda Magajiya take gaba d'aya kana kallanta kasan a tsorace take, kallan ta Sarki yai ya dade idanunsa na kanta sannan ya kalli Hisham, sannan ya maida dubansa kan Abdulmajid, haka yabi kowa da kallo d'aya bayan d'aya. Akan Barde ya tsaya yace " Barde jeka taho da gawar Hajiya." Nan barde ya mike. Sarki ya kalli Magajiya sannan yace " kafin in sallaci gawar Hajiya inkaita makwancinta inaso in sanar da abu d'aya kafin in yankema Matarnan hukunci, daga wannan lokacin na ajiye mukamin mulkin Masarautar Zazzau, sannan na d'aura d'ana Abu Turab a wannan matsayi, wannan matar a d'aureta da kaca itada d'an uwanta Waziri a rufaffen d'aki, sannan bazan yanke mata hukunci ba d'an da take neman ganin baya, wanda ta makantar dashi bayan neman ajalinsa, wanda ta ke neman halaka masa rayuwa a koda yaushe shine zai yanke mata hukunci da kansa, sannan na umarceshi da yanke mata hukunci mai tsaurin gaske." Ya juya ya fara takawa kallo d'aya zakamai kasan lalai yana cikin tashin hankali. Matan sarki ne suka mike suka bi bayansa. Sunje zasu fita daga kofar Magajiya cikin karaji tace " KAI ABDUSSALAMAD!" Gaba d'aya d'akin kowa juyowa yai ya kalleta tace " mene? Kaba Abu Turab mulki? Inji uban wa? Inji uban wa? Kana tunanin ni Magajiya zan yarda wannan dan tsinaniyar yahau mulki? Mafarki kukeyi daga kai har yan d'akin nan, indai har ni inada.........." Kasa karasawa tai jin muryarta ta sarke, duk yanda tai gun yin magana ta kasa, tsugunnawa tai da sauri tare da rike wuyanta, a hankali kowa na d'akin ya fita wannan abu yafi komau yi mata ciwo, balle tana kallan Abdulmajid Khadija ta turashi a kekensa sunyi gaba, ga magana ta tsaya cak. Masu tsaro ne sukazo inda take rike da kaca, Hisham aka fara sawa kaca, kallan Magajiya yai yace " Allah ya isa tsakanina dake, shawararki itace tasa zuciyata ta rikid'e gaba d'aya, sannan maganarki bazata taba d'aowa ba wannan rana itace rana ta karshe da kikai magana da bakinki, domin kuwa inbaki mantaba da gubar da kikasha danyima Basira sharri, a lokacin dana amshi wannan gubar dama ansanar da sharad'inta, bata fita duka a jiki sannan kar babba wanda ya wuce shekara 45 yasha wannan gubar sannan duk sanda ran wanda yasha gubar nan ya baci sosai to xata cigaba da mai illa ta cikin jikinsa, sannan idan tai nisa xata jawo kurmancewa, sannan zata nakasa gab'obin jiki." Kakari ta shiga yi idanunta kamar zasu fito, kirjinta ta shiga bugawa da karfin gaske, Hisham yace " kina tunanin duk abinda kikemin a banza?" Ya juya yai gaba. Durkushewa tai cikin tashin hankali tana rike da wuya, tana wani irin gurnanin gaske. Bayan sun fita ne daga d'akin Turab ya kalli Bilkisu yace " bari muje mu d'auko Hajiya." Kallansa tai cikin tsananin tausayawa sannan ta daure ta kakaro murmushi tace " to, bari inje gun Umma." Gun Abdulmajid taga ya nufa, ya kalli Khadija yace " kawoshi zamu gun jana'iza tunda anan za'ai." Khadija ta saki hannun kujerar data rike tana kallan Turab, bai ko kara kallanta ba ya tura Abdulmajid. Suna d'an matsawa kadan Abdulmajid dake hawaye yace " Turab ta yaya xan iya zuwa gun jana'izar Hajiya?" Turab yace " me kake nufi? Kai ba d'an Abba bane ko me?" Abdulmajid ya juyo ya kalli Turab idanunsa na kara zubar da hawaye, Turab ya kalleshi yace " meye hakan kuma?" Abdulmajid ya maida kansa kasa. Bilkisu ta kara kallan Khadija wacce ke tsaye kusa da Mahaifiyarta. Karasowa tai kusa dasu tace " ciki zaku shiga gun zaman makoki?" Umma ta kalleta da idanunta da suka kod'e tace " ta yaya zamu iya shiga ciki? Da wani idon zamu kallesu?" Khadija tace " mun gode da kulawa amma....." Bilkisu ta katseta tace " in kuna ganin hakan ne yadace ba matsala." Ta juya ta fara tafiya. Sai datai nisa sannan ta juyo ta kara kallen inda suke, can ta hangosu sunyi nisa. Juyawa tai ta nufi bangaren Umma. An d'auko Hajiya an mata wanka an mata sallah sannan an kaita gidanta. (Allah ya mana kyakyawan karshe Ameen suma Ameen) Ana gama jana'iza Abdulmajid ya kallu bawansa yace " mu fita." Turashi yai sukai waje. Motarsa ya sakashi sukai waje. Sai a sukai nisa akan titi sannan Ya juyo yace "ina zamu?" Idanunsa a rufe yace " ina zani? Ni kaina bansan inda zani ba, banida gun zuwa......" Hawayene suka kara zubomai. Yace kaini can bayan gari iska nake san sha, nan ya kara jan motar sukai gaba. Sunyi tafiya mai nisa kafin su fita can wajen gari. Sai daya gangara gefen titi wajen wata bishiyar darbejiya katuwa yace " nan yayi?" Abdulmajid ya kalli gun yace yayi. Nan ya fito dashi ya d'aurashi kan kekensa. Abdulmajid ya kalleshi yace " barni anan kai tafiyarka." Yace " Yarima....." Abdulmajid yace " ina san kasancewa ni kadai, sannan karka kara kirana da Yarima." Jiki a sanyaye ya kalli Abdulmajid sannan ya hau mota ya koma. Yana komawa gidan sarki gun Abu Turab ya nufa ya sanar dashi abinda ya faru. Turab wanda dama nemab Abdulmajid yake yace " kasan gidan Barde?" Yace "eh" Turab yace " kaje gidan kace Umma na naiman Mairo in ta fito ka kaita gun Abdulmajid a hanya ka ce mata injini nace Abdulmajid na cikin wani yanayi tai kokari ta taimaka ta dawo dashi nan." Yace to, Turab yace " ni ban isa fita ba cikin wannan yanayin." nan ya amsa da to yai waje. Gidan Barde ya nufa yai yanda Turab yace mai, a mota tana shiga ya sanar da ita sakon Turab. Gaba d'aya ta kagu su isa inda yake dan jitai gaba d'aya jikinta yayi sanyi, dan ta tabbata tunda taji Turab ya ce a sanar da ita haka to tabbas babban abu ya faru. Suna isa ta fito da sauri ko motar bata rufe ba ta taho inda yake da sauri. Daga dan nesa kadan ta tsaya tare da kuramai ido, kallanta shima yakeyi idanunsa na zubar da hawaye. Jitai idanunta sun ciciko, a hankali take takawa zuwa inda yake idanunsu nakan juna. Kusa dashi ta tsaya sannan a hankali tace " me kakeyi a nan?" Idanunsa ya rufe tare da kokarin shanye kukansa, tace " me kakeyi anan?" Kallanta yai sannan yace " Maryam ni ba d'an Abba na bane." Tace " mene?" Hawaye na zubomai yana dariyar takaici yace " iyayen da kike tunanin iyaye nane ba sune suka haifeni ba." Yanzu kam ta fahimceshi sai dai ta tabbatar inta nuna karayar ta to lalai batasan wani hali zai shiga ba, ta daure tace " to sai ka canza daga Abdulmajid dan ba sune iyayenka ba?" Ya kara cewa " yariman da nake tunanin ni yarima ne mai jiran gado ashe ni ba kowan kowa bane." Tace " dan kai ba yarima bane sai aka canza ka daga Abdulmajid?" Hawaye suka sake zubomai yace " wacce ta d'auki ciki na ta haifen ko sau d'aya ban taba girmamata ba da sunan uwar data haifeni." Yanzu kam sai da hawaye suka gangaro mata tace " Yanzu lokaci bai kure ba ai..." Yace " Maryam duk wata rayuwa da kika sani nawa ta karyace." Tace " hakan na nufin a karyar harda san da kake min?" Hannu yasa ya share hawayen yana girgiza kai, kara takowa tai wanda takun ya zama ta karasa daf dashi ta tsuguna inda yake sannan tace " then it's okay." Kallanta yai sam ya kasa magana, murmushi ta mai sannan tace " me yasa bakazo guna ba?" Yace " ta yaya zanzo bayan ina tsoron kiji abinda ke faruwa, da wani ido kike tunanin zan kalleki? Ga takurar da namiki a da, wanda nije sanadin hanaki auran wanda kike......" Hararsa tai tace " ka taba ganin wanda ya auri mijin wani? Duk aurab da kaga anyi a duniya to dama wannan auran Allah yayi sai anyishi, duk kuwa kiyayar dake tsakanin masoyan biyu, duk kuma inda kaga aure bai yiwu ba to lalai dama Allah baiyi za'ai wannan auran ba, duk kuwa da irin san da suke ma junansu." Yace " amma ai nasan kinasan Turab, inaji kamar nine sanadi..." Tace " ina sanshi kam, sai dai yanzu a wannan lokacin na tabbatar san da nakemai yana neman zama past tense." Kallanta yai, murmushi tai tace " Turab yace ka koma ai jana'iza dakai." Ta mike dan taji kunyar kalamanta ta rike keken zata tura. Kansa ya juyo saitinta yace " Maryam me kike nufi????" Harararsa tai tace " abinda nake nufi bansan ragon namiji." Kara kallanta yai yace " Maryam kina nufin......" Tace " tambayarka nai? Inka fahimci me nace sai ka had'iye a ranka." Bai san sanda wani lalausan murmushi ya bayyana a fuskarsa ba..... Magajiya kam an rufeta ruf a wani d'aki wanda yake dulum duhu gareshi sosai, an d'aureta cikin kaca, abinci sai dai a turo mata ta karasa ta d'auka taci. Gashi bata saba cin irin wannan abincin ba, ga ta da gardamar tsiya, gani take tafi karfin haka, kin cin abincin tai har dare. Wani irin ciwon ciki ne ya shiga murd'a mata, ga bata isa yin magana ba......... *TURAB* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *Nayi mistake wancan page din zan saka 87 na kara sa 86* *88*   Gidan ya cika taf ana ta fama zuwa gaisuwa, Turab jefi jefi yake kallan Mahaifinsa wanda yake ta amsar gaisuwa daga manya manyan mutane, bayan anyi sallar la'asar ne Sarki Ya shiga d'akinsa tare da bada umarnin a kira masa Turab.   Ya dade sosai baiyi magana ba kafin yace " wanene mahaifin Abdulmajid?" Turab ya kalleshi a sanyaye yace " Abba!" Sarki yai saurin cewa " su waye iyayensa?" Turab yace " d'an gidan Waziri ne." Kallansa Sarki yai yace " waziri?" Turab yai kasa da kansa. Idanu ya dan runtse kafin yace " Tun yaushe kasan maganar nan?" Turab ya d'ago yace " sanda na fahimci abinda sukama Hajiya, daga nan ne abubuwa dayawa suka fara bayyana."   Shiru ne ya ratsa kafin Sarki yace " Allah kana ganin abinda ya sameni, kaine ka bani mulkin nan ba ni na ba kaina ba, saboda mulki an bani d'an da ba nawa ba a Matsayin nawa, sannan an halakamin matan da zasu haifar min, an kuma halakamun nawa jikin dan kar na haifa, sai dai duk da haka bazanyi fishi ba saboda ka bani wannan d'an da ke gabana, Allah ina rokanka daka karemin wannan yaran daga sharrin duk mai sharri ka kuma bashi ikon rike mulki da taimakon talakawa, ka bashi ikon yin hukunci na gaskiya ba san rai ba, ka karemin shi daga had'uwa da wanda zai nufeshi da sharri, Allah ina rokonka wannan yaran............."   Kasa karasawa yai saboda muryarsa da yaji ta fara rawa. Duk dauriyar zuciya irin ta Turab sai da hawaye suka zubo masa,kallan Mahaifinsa yake cikin tsananin tausayawa, lalai yau Allah ne kadai yasan yanda bawan Allahn nan yake ji a ransa. Sarki ya kalleshi yace " Abu Turab." Nutsuwa Turab yai tare da tattara hankalinsa kan mahaifinsa dan ya fahimci magana mai mahimmanci yake san yi. Sarki ya cigaba " zan d'auki ragowar mata na uku zamu koma can wajen gari inda nai katan gidana, inaso daga anyi sadakar uku inyi murabus in baka mulkina sannan in tattara inbar gidan nan." Turab yace " Abba akan me zakayi murabus?" Sarki ya girgiza kai yace " kana tunanin bayan faruwar wannan al'amarin zan iya cigaba da zama akan mulkin nan?" " to me kayi? Duk ai laifin ba naka bane na Umma Magajiya ne." Sarki ya girgiza kai yace " Me kakeso ince? A matsayin na sarkin garin zazzau wanda ya kasa kula da matarsa? Ko a matsayina na sarkin garin wanda matarsa tafi karfinsa?"   Turab ya motsa baki yana sanyin magana, sarki yace " na gama yanke hukuncina sannan umarnine daga Sarki bawai mahaifinka ba." Turab yai kasa dakai. Sarki yace " sannan Magajiya, Hisham da Matarsa, inaso kowa kamai hukunci dai dai da laifinsa, sannan kada ka kuskura ka sassautama d'aya daga cikinsu, wannan ma umarni ne." Turab ya kalleshi yace " Matar Waziri?" Sarki yace " kwarai, a matsayinta na uwa, akan me zata amince da abinda mijinta da kanwarsa suka tsara?banda itama tana san jininta yahau mulki?" Turab ya had'iyi wani abu tunowa dayai mahaifiyar Khadija ce. Sarki ya cigaba " sannan duk wanda suke da hannu akan al'amarin nan, da al'amarin Hajiya inaso ka hukunta kowa, shima umarni ne." Turab yace " to Ranka ya dade." Sarki yace " Abdulmajid......." Sai kuma yai shiru dan baisan me zai ce ba, Turab ya kalleshi yace " Abba, me zai hana mu bar maganar matsayin Abdulmajid a junan mu?" Kallansa Sarki yai yace " mene?"   Turab yace " Abba wace rayuwa Abdulmajid zaiyi in har akasan asalin abinda ya faru dashi?" Sarki yai shiru. Turab yace " Abba idan muka duba wannan lamari wanda akafi cuta ba kowa bane sai Abdulmajid, gaba d'aya shine aka ruguzawa rayuwa, sannan shine wanda za'afi tausayama." Sarki yace " Abdulmajid ni kaina bazanso akan laifin da banasa ba ya shiga garari na rayuwa ba, amma kana tunanin hakan zai yiwu?" Turab yace " a lokacin da akai maganar nan akwai mutane dayawa, sannan shi sirri duk yanda akaso da b'oyeshi in har akwai mutanen da suka sani to fa ba wani abu da za'a iya yi, ina tunanin mai zai hana tunda yanada ilimi sannan yanada babbayar hanya na matsayinsa na d'an Sarki a nemar masa aiki babba na gomnati yabar garin nan, yanda baya kusa ma balle gulma a dameshi, sannan yanada matsayin da ko asiri ya tuno ba abinda zai sameshi."   Sarki kallansa kawai yake cikin jin dadi, yace " lalai Kai Kainuwa ne, dashe ne wanda Allah yai, ba shakka kasata xataji dadin mulkin ka." Turab ya sunkuyar da kai cikin jin kunya. Sarki yace " ni kuma zan kwabi duk wanda ke d'akin sannan ni zan sa a bashi aikin ba sai ka wahala ba." Turab yace " Godiya nake, amma Abba mai zai hana ka cigaba da zama anan ko dan shawara da nunamin hanya?" Sarki ya girgiza kai yace " Turab kasan me yasa ake kishi, gaba, tsana, sharri da mugunta akan mulki?" Turab ya gurgiza kai cikin rashin fahimta, Sarki yace "

Chapter 35 of 37