Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a ranki, Mai Martaba sarki ne, sarkin mutane masu dumbun yawa wanda yake mulkarsu sai dai ba sarki bane a tsakanin matansa, Magajiya bazata taba barinsa yai yanda yakeso ba akan matansa, yaci ace a shekaru goman nan kin fahimci haka." Murmushi tai sannan tace "nasan da haka Abu Turab sai dai ina tsoron karmu lakutowa kanmu abinda gaba bazamu iya magani ba." Dariya yai sai dai mai dan sanyi, wanda rabon dayai dariya haka ya dade yace " ina Umma na ne wacce take tsaidani in nai laifi? Ina Umma nane wacce take hanani kuka? Ina Umma nane wacce ke marina duk sanda na b'ata mata rai?" Harara ta makamai tace " da alama girma ya fara kama wannan Umman taka." _Nikaina sai da na saki wata bazawarar dariya....Lol_ *TEAM ABU TURAB🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *21* Shiru tai tana tunani, kayan da aka aikomai dashi wanda ke kan gado ya d'an kura ma ido alamar tunani kafin ya dawo da kallansa kan mahaifiyarsa yace " Umma zan shirya." Kai ta d'aga sannan ta mike ta dafa kafadarsa d'aya tace " duk hukuncin da ka yanke ina tare da kai dan kuwa na tabbata d'ana bazai bani kunya ba." Bata jira amsarsa ba tai waje. Abu Turab ya shirya tsaf ya fito daga d'akinsa, inda yake zama ya wuce dan bayin sa su nad'amai rawani. Tunda ya shigo suke kallansa dayake sunsan baya gani yasa suka kura mai ido kowa da abinda ke ransa nan fa suka dan fara gulma da ido wanda duk yana ganinsu. Rawanin dayake so ya basu nan suka nad'amai, ya sa takalmi yace su tafi. A kofar gida yaga wani bawa rike da doki yasha ado, bawan na ganin Abu Turab ya taho da gudu ya dan rusuna yace " Ranka ya dade ha doki nan inji magajiya." Murmushi yai sannan yace " ayya? Ya za'ayi? Gashi na riga na aikama Barga akan ya aikomin doki sai dai ma maida wannan gun Bargan gudub kar a maka fada akan rashin isar da sakonka da wuri. Bawan yai saurin sunkuyawa yace "Tuba nake D'an Sarki." Abu Turab yai murmushi sannan yace " ba haushi naji ba ina dai gujema fada ne." Kallan d'aya daga cikin bayinsa yai yace " sanar da Barga ya baka dokina." Cikin mamaki yace " Ranka ya dade ai ba'a mai....." Katseshi yai da cewa " hakan nakesansa." To, abinda ya fada kenan yai saurin fara tafiya. Bai dade ba sai gashi da rike da dokin Abu Turab ya hau. Sai daya bari Sarki zai fita hawa sannan ya shiga cikinsu, bai bari sun ganshi a gida ba. Tunda ya shiga cikinsu kuwa ake kallansa, kowa mamaki wannan wanene haka? Dama tawagar Abdulmajid ya shiga, dan kara gudun dokin yai ya matsa bayan Abdulmajid kadan. Nan fa kowa ya fara kallansa, mutand sai juyowa suke ana nunashi da hannu, ganin yanda ake nunuwashi yasa Abdulmajid ya tsargu ganin saitinsa ne. Kallan na kusa dashi yai yace " menene?" Juyawa yai shima, cikin mamaki ya kalli Abu Turab sannan ya matso inda Abdulmajid yake yace " Yarima ai kaninka ne yake bayanmu." Murmushi yai dan dama yasan da zuwan nashi, sunyi shiri sosai dan kuwa d'inki Magajiya tasa aka mai irin wanda zai saka a wannan ranar, wanda hakan sab'awa ne ga al'adarsu ace anyi anko da Sarki balle kuma bai sani ba. Ya sake murmushi tunawa dayai dokin ma kwalliyar irinta Sarki sukasa akamai. Sai yanzu ya fahimci dalilin dayasa ake nuna Abu Turab. Sai da sukaje inda Sarki zai d'an tsaya kafin ya juyo alokacin ne Abdulmajid yaga yanda ake ta nuna Abu Turab, dariya ya kunshe ya juyo dan ganin yanda ma kayan yamai. Sai dai me???? Idanu ya zaro sosai cikin tsananin mamakin abinda idanunsa suka ganemai, me ke faruwa? Menene hakan? Shi kansa Sarki ya fahimci yanda mutane suke nune nune, hakan yasa ya tambayi Galadima yace " meke faruwa?" Nan Galadima yasa aka bincika. Matsowa yai wajen kunnen Sarki ya rad'amai. Ransa ya b'aci sosai nan ya bada alama akan su juya. Haka sukabi har suka koma gida. Abdulmajid kam sukuku ya karasa wannan hawan zuciyarsa tana ta san taga wani irin hukunci Mai Martaba zai yankema d'an lelen nasa. Suna isa akazo aka sanar ma Abu Turab akan Mai Martaba na nemansa a fada. Yasan za'ai haka shiyasa ya sauka zuciya d'aya ya bada dokinsa ya nufi fadar. Dayaje zai shiga sai ya ajiye sandarsa sannan ya shiga ciki. Zama yai irin zaman gurfana d'in nan, Mai Martaba ya kalli dumbun manyan mutane masu mukamin sarauta dake gun, sai dai wannan karan yazamarmai dole duk san da yakema d'an nasa ya mai tambaya a nan Saboda yau a matsayin Sarki yake ba uba ba. Abu Turab ya kalla fuskarsa a had'e sosai yace " Me zaka fad'a game da wannan shigar ta cin zarafi dakai?" Nan fa aka kara kallansa, Abdulmajid wanda ya shigo yanzu yai murmushin jin dadi tare da zama. Abu Turab yai shiru baice komai ba, kallansa Mai Martaba yai yace " in har bakada amsa akan hakan to lalai ne ka fuskanci hukuncin masarauta." Ya fad'a tare da kauda kai. Abu Turab kansa na kasa yace " Tuba nake in har shigar danai laifice a tsarin masarautarmu." Nan fa kowa ya kara kallansa, rigace ta shadda wacce ta tsufa kana ganinta kasan tsohuwace, sannan na babbar riga a jikinsa ya maka wani tsohon rawani, wannan shigar ko a cikin gida ba yinta yake ba balle a gun hawa cikin jama'a. Hisham ya kalleshi yace " kanasan kace shigarka batada laifi kake nufi ko me?" Abu Turab ya kalleshi fuakarsa a sake yace" kuskure nane sai dai ina fatan amin afuwa." Cikin takaici Mai Martaba yace " Abu Turab! Nasan ba gani kakeyi ba dan haka laifin bayinka ne zasu amshi hukuncin barinka kayi wannan shigar dolene su fuskanci hukunci mai tsauri." Abu Turab ya kara kasa dakai cikin kalar tausayi yace " ko wani hukunci ne amin domin kuwa sun bani kayan da ya kamata insaka sai dai daga laushin kayan da yanayin su yasa nasan ba nine na dace da kayan ba, sai dai hakan baisa na musa ba na saka kayan dan kuwa bansan ya suke ba da idona, ka gafarceni Mai Martaba ina fitowa aka sanar dani kayan irin naka ne sak, sannan dokinma irin kwalliyarka ne dashi, wannan yasa na hanzarta na janyo kayan dabansan ya suke ba na saka sannan na aika Barga ya bani dokina nasa amaida mai waccan." Jin kalamansa lalai sun ba kowa mamaki, Abdulmajid kam cikin tsoron kar asirinsu ya tuno yai saurin cewa " menene shaidarka ta fadar haka? Kana tunanin ko me kace yarda zamuyi?" Abu Turab wanda ana cemai Mai Martaba na kiransa ya tura Salau(mai kula dashi wanda suka fi shiri) akan ya d'aukomai kayan nan,sannan ya aika Barga yazo. Nan yace " Salau!" Daga waje Salau ya amsa da karfi. Nan ya shigo rike da kaya. Abu Turab yaba shi kuna ya ware kayan anan kowa ya gani, to fa! Nan aka fara magana kasa kasa. Abu Turab yace " ka gafarceni Ranka ya dade ba gani nake ba bare nasan da haka." Barga! Nan ya amsa shima daga waje sannan ya shigo. Abu Turab yace " wani irin kwalliya ne da dokin danasa a dawom dashi?" Nan Barga ya musu bayani. Mai Martaba cikin tsananin mamaki yace " wanene ya aikoma da kayan da kuma dokin?" Abu Turab yad'an sadda kai tunowa yai da yanda suka karashe da mahaifiyarsa. Harta fita ta dawo tace " Abu Turab! Me kake san yi dan hankalina bazaj kwanta ba sai naji." Ya kalleta yace " bazansa kayan ba haka kuma bazan hau dokin ba, na tabbata akwai wani makirci akasan wannan kayan da dokin zanje inga wani irin makircine sannan insan abinyi." Muryar Galadima ne ya katseshi da cewa " kayi shiru." Cikin Abdulmajid da Waziri ne ya d'ebi ruwa, tsoro da fargaba ya kamasu, duk suka runtse ido saboda tsoron abinda zai ce. Abu Turab ya d'ago yace " ina wannan wanda baya ganin zai sani? Tuba nake ranka ya dade sai dai nikaina bansani ba andai aiko ne ance ga kayan dazansa." Mai Martaba ransa a b'ace yace "dolene abinciko wanda yai wannan laifi dan kuwa bazan laminci irin haka ba." Abdulmajid ya kurama Abu Turab ido lalai ba shakka yaran nan da saninsa. Suna fitowa ya bi Abu Turab zaimai magana, ya tsaya kusa dashi yace " kai!" Abu Turab ya kalli gefensa sannan yad'an matso kadan yace " karka damu nikaina bansan waye ya kawo kayan ba." Yana fadar haka ya juya suka tafi. Mamaki ya kama Abdulmajid ya bishi da kallo, kallan na kusa dashi yai yace " na fadamai dalilin kiran danamai?" A'a sunansa kawai ka kira. Abdulmajid yai dan murmushi yace " wasa farin girki." *#ABU TURAB🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* _Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya da shekaran kiya, hakan ya faru ne saboda wani dalili nawa, 👏🏼 nagode kwarai_ *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *22* Abdulmajid da sauri ya karasa bangaren Magajiya, ko salama baiyi ba ya fad'a, tana zaune tana duba wasu kaya da tasa aka kawo mata, kayan mata ne aka d'inko kala kala. Jin shigowar mutum yasa ta d'ago dan ganin wanene. Abdulmajid ne ya karaso inda take ya zauna ransa a b'ace. Kallansa tai yace " Yarona lafiya ko sallama babu." Ya kalleta yace " Umma da alama mun sakema yaran can dayawa." Ta kalleshi tace "bangane ba? Ni na dauka zakazo cikin murna kamin bayanin abinda ya faru da yaran can, shiyasa naki yardama kowa ya sanar dani nafisan inji daga bakinka." Abdulmajid yai dan ajiyar xuciya yace " Ai baisa kayan ba, da alama mun sakema yaran nan dan yana makaho shiyasa har yake ganin zai iya takara damu." Magajiya tamai kallan bata gane ba, nan ya kwashe komai ya gaya mata, wani sansanyan murmushi ne yaga ta saki ta kalleshi cikin murmushin tace " shine kake wannan fushin?" Kallanta yai cikin mamaki, ta sake wani murmusawa tace " yaro man kaza, karka badani mana Yarimana." Kallanta yai baice komai ba, tace " yaushe ma aka auri uwarsa, yaushe shima aka haifeshi, yaushe aka daina mai tsarki da wanka? Yaushe ya san kansa?" Ta sake wani murmusawa tace " ko kamanta haryanzu baisan kalar fuskarsa ba bare yasan na uwarsa bare kuma tamu?" Abdulmajid ya fahimceta, dariya yai sannan yace "a maida anin kan uwarsa?" Magajiya tace " in har Mai Martaba ya nemi jin ba'asi to ka tabbatar komai ya koma kan Uwarsa." Dariya ya saki yace "Allah yabarmin ke Umma Magajiya." Murmushi tai tace " yaune isowar Khadija fa." Ya kalli kayan yace " au shiyasa naga kaya kala kala a gabanki? Ashe 'yar d'akinki ce zata dawo." Cikin jin dadi tace " daurewa kawai nake na rashinta, amma kaga yanzu tunda Inna Lami take akwance sannan ga shi ina tunanin turawa takarda had'in aure zuwa masarautar Kano shiyasa nakesan ta dawo." Kallanta yai yace " auren wa?" Tace "auranka mana dolene in nemi masarauta mai karfi in had'a auranka saboda nan gaba ko menene ba wanda ya isa tunanin saukeka daga matsayinka ko kwace ma mulkin ka." Kallanta yai yanasan magana amma ina bazai iya ba, dan bai taba mata musu ba, kayanta tacigaba da dubawa. Jiki a sanyaye ya mike yai waje, shikam bai shirya wani aure yanzu ba amma bai isa cewa komai ba, a tsarinsa yafisan yai auren farinsa auren soyayya tunda dai yasan dama shi dolene yai mata dayawa, yana tunanin ina shi ina soyayya da wani bayan an riga an mai aure? ****** Washegari. Yana fitowa daga d'an nesa ya hangota tana tafiya, tsaki yaja yace " sai na takama yarinyarnan birki." Kallan na bayan sa yai yace " kiramin yarjnyarcan, ina bangarena." Ya juya zuwa bangarensa. Yana shiga yaga an kawo mai abinci ga bayin da suka kawo nan a tsatsaye suna jiran isowarsa. Zama yai baice musu komai ba, umarni ne ya basu dolene in suka kawo mai abinci sai yaci yaji yamai kafin su tafi. Da sallama ta shigo fuskarnan tata a d'aure tamau, shima fuskarsa ya had'e bai amsa mata ba ya d'ago ya kalleta. Kanta na gefe, jitai yace " duk ku fita kubarni da yarinyarnan inasan magana da ita." Nan sukai waje, itakam haryanzu kanta na gefe. Kallanta yai yace " ke baki iya gaisuwa ba?" Bata tanka mai ba. Ya kalleta yace " zo ki zubamin abinci, tunda naga alama uwarki bata isa dake ba, kullum kina hanyar gantali." Wani mugun kallo ta bugamai sannan tace " ko karuwanci nakeyi meye naka a ciki?" Hannu taga ya had'a ya fara tafi sannan ya mike ya tako zuwa kusa da ita, idanunta ta kawar tace " malam lafiya?" Ganin yanda ya matso daf da ita yasa ta fara matsawa, haka ya dinga matsowa har takai jikin bango. Hannu yasa a jikin bangon ya tareta yace " abinda kukeyi kenan da makahon?" Kallansa tai ta had'iyi yawu sannan ta daure tace " yaushe raban ma daka ganni a gidan? Wai ni mena tsolema ne?" Dariya yai yace " na tsani duk wanda yake san makahon can, balle ke harda dadin rashin kunya." Sauri tai ta sulale ta kasa ta juya da sauri zata fita, hannunta ya fizgo da karfi, ya dawo da ita gabansa yace " me? Bakyasan kwalliyar da kikai ta goge ne ba tare da kinje gunsa ba?" D'agowa tai takalleshi cikin takaici. Ya saki murmusawa yace " ahh ya zakiyi? Gashi kuma baya gani bare ya yaba." Hannunta tashiga kwacewa, ganin yaki saketa yasa tace " wlh zansama ihu, kasani sarai kuma zan iya." Kafad'a ya d'aga mata alamar ko a jikinsa yace " Go ahead." Lab'anta tad'an ciza sannan ta kalleshi ta kara hade rai tace " malam sakeni ko?" Kallanta yai ba alamar yana da niyyar hakan. Ta kara cewa Malam sakeni ko?" Yace "Mairo kenan, inhar kinasan in kyaleki dolene ki daina zuwa gun waccan yaran ki dinga zuwa guna duk da nidin bawai sanki nake ba ko burgeni kike ba sai dai inasan yanayin fuskarki da shape na jikinki." Iska ya hura kad'an a bakinta tace " hakan kadai kakeso." Gira ya d'aga mata alamar eh, yamai murmushi sannan tace " sakeni to, indai wannan ne kacal. Nan ya saketa yana kallanta, tace " nagode sai anjima." Zai sake magana yaga tayi waje. Hakoransa yad'an had'e yace " na tsani yarinyar nan, bawanda ya rainani kamarta." ******** Mairo kam tana fita ta gyara mayafinta tafiya kawai take amma gabanta sai fad'uwa yakeyi, haka ta isa b'angaren Basira. Bayan sun gaisa ne, Basira ta kalleta tace "Mairo yanzu sam kin daina zuwa, yauma sai dana aika kizo sannan kika zo." Kanta na kasa batace komai ba, kai kadauka irin salahan nan ce. Basira tace " dama so nake ku fita da Abu Turab gari, na tabbata yau yana bukatar iskar cikin gari bawai ta gidan nan ba." D'agowa tai tanasan tambayarta abinda ya faru, sai dai bazata iyaba. Tace " To." Basira ta kalleta cikin kauna tace " bari a kirashi." Ta kara cewa to. Abu Turab yana d'aki a zaune yana karatun alqur'ani, nan aka sanar dashi sakon Basira. Mikewa yai ya bud'e drawer din da kayansa ke ciki dan canzawa. Kurama d'ankwalim dake ajiye a gaban kayan ido yai, baice komai ba sai dai ya dade a tsaye yana kallan d'ankwalin. Kafin ya jawo wani kaya,har ya rufe kofar ya bud'e ya janyo d'ankwalin yardashi yai a kasa sannan ya sura kayansa, ya kara kallan kasa sannan yai waje. Ya rasa dalilin dayasa yakejin zuciyarsa ba dadi bayan ya yarda dankwalin, sai dai menene dalilinsa na ajiye kayan yarinyar da tunda ta tafi ko sakon gaisuwa bai kara samu ba? Wata zuciyar tacemai wa zata aika? Bayan duk ba sanka suke ba? Shikam ya rasa me yasa yakejin zafinta bayan ya tabbatar ba laifinta bane. Haryakai kofa ya koma d'aki ya d'au d'ankwallin ya maida cikin drawer din sannan yai waje. Yana shiga yaga Mairo a zaune, karasa wa yai ya kara gaida mahaifiyarsa. Mairo ta gaisheshi ya amsa. Basira tace " tunani nake ko zaka fita gari yawo." Kallan gefenta yai yace " gari kuma?" Tace " eh, kullum kana gida a zaune shiyasa nai tunani ko zaka zaga gari dukda ba gani zakai ba amma ina ganin zakaji dadin hakan." Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace " bari na sanar ma....." Da sauri tace " ku fita kai da Garzali da Mairo kawai." Kallanta yai yasan me take nufi, dan dama ya dade da sanin so take wata alaka ta shiga tsakaninsu da Mairo. To. Abinda yace kenan ya mike. Mairo itama ta mike ta musu sallama. Garzali na bayansa ita kuma tana d'an kusa dashi kadan, shikuma yana tafe rike da sanda. Sun shiga gari ta gefen ido yana ta kallan yanda mutane suke haba haba, ba shakka wannan shine burinsa ya zauna cikin mutane kamar yanda kowa yakr yi bawai gidan sarauta ba. Jitai yace " Mairo yanzu anbar rigima dai da alama." Kallansa tai tace " lalai Yaya sai kace wata yarinya?" Yace " ah lalai ashefa kin girma." Baki tad'an turo tace " shekarata fa 1." Yace "16? Amma bakiyi aure ba?" Fuska ta d'an had'e tace " ba mijin ne." Ya d'an juyo kadan yace " wanda rannan ya biyoki fa?" Tsaki tadan yi tace "rashin aikinyi ne yamai yawa." Yace " da alama dai akwai wanda kikeso ne shiyasa." Kallansa tai a ranta tace "sosai ma." Ta d'auka a zuciyarta ta fada sai jitai yace " da gaske?" Kallansa tai tace " wasa nake." Murmushi yadanyi yace " kar ki tsaya ruwan ido ki samu saurayin da yake sanki ki aura, bawai wanda ke kike so ba." Kallansa tai zuciyarta ba dadi tace " kamar yanda haryanzu baka manta da Khadija ba?" Tsayawa yai cak, ba tare da ya juyo ba, matsowa tai inda yake tace " karka damu Ya Turab ba wanda yasan hakan, ko ince ba wanda zan fadawa." Bai san sanda ya kalleta ba, yace " me kike nufi? Ko kin tabaji da bakina na fada miki haka?" Murmushi tamai tace " wani sa'in sai inga kamar kana kallona." Fuska ya had'e ya juya kai yace " amsarki nake jira." Daurewa tai tace" a lokacin da Khadija ta tafi bafa yarinya bace ni yaya, ban manta abinda ya faru a lokacin ba, sannan duk sanda muka zauna dakai zancenka kenan khadija tace kaza, ko khadija tayi kaza, a lokacin bansan me hakan yake nufi ba, sai dai daga baya na fahimci meke faruwa." Abu Turab ya juya yace " banasan wannan maganar, sannan ni khadija banaji ko ganinta ma in nai zan iya ganeta." Yana kaiwa nan ya cigaba da tafiya." ********** Tunda suka taho a hanya take kwance kamar mai bacci sai dai zuciyarta fal take da tunani kala kala, Ya Turab! Abinda zuciyarta take fada kawai kenan, anya zata iya ganeshi? Dan ita kamanninsa ma harsun fara bace mata. Ba shakka tasha wuya sosai bayan komawarta kano, sai datai sati biyu tana zazzabi zancen ta kenan a maida ta gun Ya Turab kai kace shine ya haifeta. Yaran gidan har tsokanarta sukeyi suke cemata Aunty Turab. Duk sanda zatai addu'a kafin ta fara rokon komai sai tamai addu'a, ita har mamaki ma take da haryau bata taba mantawa da addu'ar ba in har tai sallah. Ko zai ganeta? Dan wani zuwa da Abdulmajid yai shekarar data wuce data tambayeshi Abu Turab cemata yai wai soyayya suke da Mairo, sannan gwara ma ta cire wani lamarinsa, dan shi kam ya ma manta da ita. A da bata taba tunanin wai san shi take ba, itadai a matsayin yaya ta d'aukeshi sai dai ganin ta kasa cireshi a ranta yasa Aunty Nana wato babbar yarinyar gidan ta fada mata soyayyace bawai 'yan uwantaka ba." Kanta ta kara kwantarwa jikin motar, ya zatayi in har yama kasa ganeta? Dama gashi iyayenta nema suke su had'ata da wani yaron babban d'an siyasa a garin kano yake. Ajiyar zuciya tai sannan ta kara lumshe idanta. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *23* A hanyarsu ta dawowa ne wani ya biyo Mairo da gudu, yana kwalla mata kira. Abu Turab yanaji ganin taki tsayawa bare amsawa yasa shima bai tanka mata ba, sai dayazo daf dasu yanata haki na gudu yace "Mairo kina jina?" Kallansa tai tace " nibanji ka ba, lafiya?" Ta fad'a tana kallan Abu Turab daya cigaba da tafiyarsa. Leda ya miko mata yace " gashi." Cikin fada tace " nameye shi kuma?" Kai ya sosa yana shirin yi mata magana, yana d'agowa yaga bata gun, kallanta yai yanda take dan sauri. Da sauri itakam ta karasa gun Abu Turab tace " Yaya ba jira?" Yace " har kin gama zancen?" Tace "zance kuma?" "ki koma dan muma gida zamu wuce, sai da safe." Abinda ya fada kenan ya cigaba da tafiyarsa. Turus tai agun idanunta suka d'an ciciko, meyasa Abu Turab baya ganin yanda ta damu dashi? Shikam ko a jikinsa har suka isa gidan. Yana shiga daga bakin gate yaji ankira sunansa. Yasan muryar waye, fuskarsa yad'an saki kadan ya juyo saitin inda yaji kiran. Sabi'u d'an gidan galadima ne ya karaso gunsa, cikin farin ciki yace "Ranka ya dade daga ina haka?" Abu Turab ya d'an murmusa kadan yace " naje ganin gari." Sabi'u ya kalli Garzali yace "dafatan ba abinda ya faru?" Garzali zaiyi magana Abu Turab yai saurin cewa " ba abinda ya faru, sannan inhar ka damu da ni nan gaba inzan fita kazo ka d'aukeni." Dariya Sabi'u yasa yace " Angama Ranka ya dade, nima daga gun Mai Martaba nake akan maganar binciken abinda ya faru yau." Fuska Abu Turab ya had'e yace "kai akaba aikin binciken?" Fuskarsa d'auke da mamakin ganin yanda Abu Turab yai yace " eh, da wani abun ne?" Abu Turab ya girgiza kai alamar a'a sannan yace " ka koma gida ka kwanta kace bakada lafiya, inyaso zuwa gobe sai ka turo fada a sanar da rashin lafiyarka." Sabi'u yace " saboda me? Ni ai ina ganin nine na dace da binciken saboda sanar ma Mai Martaba gaskiya abin." Abu Turab yace " shine dalilin dayasa ai banasan ka amshi wannan aikin." Kallan Mamaki Sabi'u yamai, Abu Turab ya sa hannu alamar yana nemansa, da sauri Sabi'u ya rike hannunsa yace "ganinan" Hannunsa ya rike yace " Sabi'u ka manta wacece Magajiya ne? Ina tsoron karkaje daga bincike ta juyo da rashe kanka, dan na tabbata bazata taba bari a gane itace ba, saboda haka ka barni da ita ni zansan wanda ya kamata yai binciken." Sabi'u ya fahimceshi kwarai hakan yasa bai musa ba yace " shikenan zanyi yadda kace." Nagode. Abinda Abu Turab ya fad'a kenan. ******** Tare suka shiga cikin gidan suna tafe suna 'yar hirarsu. Yazo yin kwana inda zai shiga b'angarensa, wata budurwa ya hango a tsaye a jikin katangarsa, kanta na kasa da alama ba shiga zatai ba kuma da

Chapter 9 of 37