aure?
Fitowa yai waje dakyar yake sa kafarsa.
Khadija ce ta karaso da sauri, itada Mahaifiyarta.
Yana kallanta ta shiga ciki kamar bata ganshi ba.
Kallan waje yai mutane sun cika gun sosai, sai gulmar Basira akeyi, kowa na fadan albarkacin bakinsa, shikansa yana fitowa ya fahimci gulmar hardashi.
Wato Basira dan taga d'anta ya warke shine take kokarin halaka Magajiya, sannan ta halaka Abdulmajid ta d'aura nata akan mulki.
Inka ganta kamar bazatai haka ba.
Gulma dai kala kala...
Basira kam tana zaune a falo cikin tashin hankali, ta tambayi masu aikinta kowa yace baisan meya faru ba.
Mairo duk ta rukice itama ta shiga kitchen sai dube dube takeyi cikin tashin hankali.
Kan kace me? Zance har ya fita daga gidan ya shiga cikin gari......
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*_Wannan shafin naku ne 'yan Zauren BieBie Isa, tnx alot 4 ur support....Much luv_*
*42*
Abu Turab ya shiga bangaren mahaifiyarsa, ba kowa a falon sai Lantana dake zaune jugum.
Tana ganinsa ta mike ta gaisheshi, kallanta yai yace " Umma fa?"
A hankali tace "tana d'aki."
Juyawa yai ya fita, dayake magrib ta duso massalaci ya nufa.
Ana idar da sallar wasu dan gulma tun a cikin massalacin suke yan gulmace gulmacen maganar, mikewa yai ya fito.
Bangaren Mahaifinsa ya nufa.
Jakadiya tana ganinsa ta iso gunsa ta gaidashi.
Kallanta yai yace " Mai Martaba fa?"
Tace " Yana ciki, a ma iso?"
Kai ya d'aga mata alamar eh, har ta fara tafiya sai ta dawo gunsa tace " Hmm nikam Yarima naji abinda ya faru, sai dai kuma hmm tuba nake ranka ya dade amma ni nasan akwai alamar tambaya a al'amarin nan."
Gefe da gefe ta kalla tace " Sai dai neman Allah ya fitar da ku lafiya."
Kauda kansa yai daga kanta dan shi sam bayasan harkar gulma tunda kuwa yaga yanda take wani juye juye yaji ransa ya baci.
Juyawa tai, bata dade ba sai gashi ta dawo tace ya shiga.
Abu Turab ya shiga.
A zaune ya tadda mahaifinsa sanye da tabarau, rike da wata takarda da alama karantawa yakeyi.
Abu Turab ya shiga sannan ya kara gaidashi.
Sarki ya zare tabarau din ya kalleshi yace " Turab ya akai?"
Abu Turab ya kalleshi yace " Abba, na tabbata kasan Umma bazata aikata wannan laifin ba."
Murmushi yai sannan yace " bansan komai ba Turab, bansan ko zata aikata ba ko bazata aikata ba."
Kallan mamaki Abu Turab yamai yace " Abba."
Sarki ya kalleshi kallo wanda bazaka tana fahimtar yanayin da mutun yake ciki ba yace " Abu Turab ba dai so kake kacemin in yarda da Basira ba, bayan a gabana Magajiya ta fadi?"
Abu Turab cikin mamaki ya kalleshi yace " Amma......"
Katseshi yai yace " In har kanaso in yarda da Mahaifiyarka to inga evidence wannan shine kadai abinda zan fadama."
Abu Turab yai shiru" nagode." Kawai abinda yace kenan yai waje.
Mai Martaba ya bi bayansa da kallo cikin tausayawa a fili yace " Abu Turab dolene sai ka yaki weakness dinka, Magajiya ta riga tasan Basira tace lagwanka, tunda nake bantaba ganinka cikin damuwa kamar tayau ba.
Abu Turab yana fita ya nufi bangarensa, sam ya rasa dalili zuciyarsa ta kasa bashi wata mafita, kwakwaran tunani ma ya kasayi, mahaifiyarsa kawai yake hangowa lokacin da ta kalleshi cikin wani yanayi, kallo d'aya yamata ya fahimci tsantsan tashin hankali karara a idanunta.
Wannan rana ta zame musu ranar tashin hankali, Abu Turab da Basira.
Magajiya kuwa ta daina amai sai dai har alokacin bata bude idanunta ba a haka a ka kwana, khadija ce ta zauna a gunta.
Washe gari da safe yana zaune a d'aki Garzali ya kwankwasa mai kofa.
Mikewa yai ya bud'e, kallansa yai yace " Garzali ya akai?"
Garzali yace " Sabi'u ne ya zo Ranka ya dade."
Bai koma ciki ba kawai ya jawo kofar d'akin ya fito falo.
Garzali yabi bayansa.
A zaune yaga Sabi'u.
Kusa dashi ya karasa ya mikamai hannu sukai musabaha.
Sabi'u ya kalleshi cikin kulawa yace " Mutumina are u okay?"
Murmushin yake ya masa yace " ya akai da safen nan?"
Sabi'u ya kalleshi yace " maganar Gimbiya Bilkisu ce."
Kallansa Abu Turab yai yace " ta fasa aurena?" Murmushi yai yace " nasan haka zata faru ai."
Sabi'u yace "no ba haka bane." Ya fada yana girgiza kai.
Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Sabi'u yace " nemanka takeyi."
Cikin mamaki Abu Turab ya kalleshi yace " nema kamar ya?"
Sabi'u yace " bansani ba ni kaina, bansan me ya faru ba d'azu da safe wambai ya kira gida a landline ya ce abani, ina amsa ya sanar dani, kasan Wamban kano shike auren kanwar Mamana."
Abu Turab yace " shikenan a satin nan naje."
Sabi'u da sauri yace " da alama neman na gaggawa ne fa, kasan ana asuba aka kira wayar? Bansan meke faruwa ba amma tabbas yanda aka sanar dani da alama neman gaggawa ne."
Mikewa yai yace " Kana tunanin zan tafi inbar Umma na da take cikin wannan halin?"
Sabi'u yace "haka ne sai dai ina ganin ka nemi shawararta, ita kanta nasan cewa zatai kaje."
Abu Turab yace "zan nemeka duk yanda mukai da ita."
Daga nan ya wuce ciki.
Tun dare yake tunanin mafita, sau biyo yana komawa bangaren mahaifiyarsa amma har a lokacin bata fito ba wannan dalilin shi ya kara d'agamai hankali sosai.
Har ya zauna sai kuma ya mike ya fito bangaren mahaifiyarsa.
Lantana tana ganinsa ta taso ta gaidashi.
Kallanta yai cikin damuwa yace " ta fito?"
Lantana ta girgiza mai kai alamar a'a sannan tai kasa da kanta alamar damuwa.
Kofar d'akin ya nufa, ya kwankwasa, shiru yaji ya kara kwankwasawa.
Jin ba alamar motsi yasa ya murd'a kofar d'akin.
A kan gado ya hangota a kwance lulube da bargo.
Da sauri ya karasa ciki.
Bacci takeyi sai dai kana kallanta da yanda take futar da numfashinta zakasan ba tada lafiya.
A hankali yakai hannunsa kan goshinta.
Zafin dayaji ne yasa hankalinsa ya tashi.
Da karfi ya kwallawa Lantana kira.
Da gudu ta shigo dan yanda ya kirata tasan da matsala, Lantana ta kalleshu cikin tashin hankali ta kalli basira.
Cikin fada yace " Lanata me kike yi jikin Umma yakai haka?"
Lantana ta kalli Basira cikin yanayin na ban tausayi tace " Uban gidana jiya da zata shiga tace kar inbar kowa ya shigo mata ciki kuwa harda ni, sannan ko abinci in na kwankwasa mata sai tace min kar na sake shiyasa ban kara dawowa ba."
Idanu ya runtse cikin tashin hankali yace " kira mai magani."
Hannu Basira tasa ta rike hannun Turab cikin a hankali tace " a'a Turab inba so kake magana ta kara karfafa ba ka bar zancen mai maganin nan
"
Kallanta yai cikin tausayawa idanunsa duk sun rine yace " Umma?"
A hankali tace " Lantana kisa a kira Mairo kice ta tahomin da magani, hakan ya isheni Turab
"
Rasa abin cewa yai, jiyai tace " Ya jikin Magajiyan?"
Kallanta yai cikin wani yanayi, yace " wake zancen wannan? Matar da ita tajama kanta ciwo dan ganin bayana? Meyasa in zatai sharrin bazai tsaya iya kaina ba? Menene dalilinta na had'awa dake?"
Kallansa tai, jiyai zuciyarsa ta kara karaya, mikewa yai da sauri ya fito daga d'akin, bakin ciki ya addabeshi.
Bangaren Magajiya ya nufa rai a bace.
Tana kwance, Khadija ce kawai a gunta tana zaune tana matsa mata kafa.
Kallo d'aya yama khadija ya maida dubansa kan Magajiya, yana kallanta yace " Ta farfado?"
Khadija ta kalleshi ba shakka tafi kowa sanin yana cikin wani hali sai dai ita kam ta rasa inda matsalar take, ta tabbata Umman Turab bazata taba yin haka ba, to meya faru? Daga ina aka samu matsalar?
"A hankali ta amsa mai baya farka ba yaya."
Idanunsa nakan Magajiya yace " d'an bamu guri."
Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje, zuciyarta a karye, ba shakka tasan jiya ya turab ko bacci bai samu ba.
Juyowa tai ta kurama kofar d'akin ido, ya zatai da ya Turab?ya zatai ta taimaki mahaifiyarsa?"
Abu Turab bayan ta fita ya kalli Magajiya yace " Kina kokari, na kuma jinjina miki a salo na makirci da iya tugu, kinfi mahaifiyata girma amma saboda kinasan ganin bayana kika ajiye girmanki."
Gani yai ta bud'e idanunta.
Kallan mamaki ya mata yace " Idanki biyu?"
Murmushi ta saki ma tsantsar mugunta tace " Turab naji da ka fahimci na girmi uwarka, kaga alama ce ta ko ita bata isa taja dani ba, duk sanda ka nemi izinin durkusawa da bani hakuri lokacin zan saurareka."
Tana gama fad'ar haka ta maida idanunta ta rufe, tsananin mamaki ya hanashi magana, kallanta yai cikin takaici yace " zan baki mamaki, wlh wahalar da mahaifiyata da kikai, zagin da kikasa a ka mata......"
Kasa karasawa yai jin an turo kofa.
Abdulmajid ne, yana shigowa ya ce " malam yi waje ko? Tayaya ma Khadija zata barka kai kadai a ciki? In ka karasata fa?"
Abu Turab ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma yai waje.
Khadija tana tsaye taga ya fito, kallansa tai cikin tausayawa, ko kallanta baiyi ba yai gaba.
Kansa ya dafe cikin tsananin takaici.
Sabi'u ne ya nufoshi cikin hanzari.
Yana karasowa gun Abu Turab ya kalleshi, kafin yai magana Sabi'u yace " Yarima ko zuwa zamuyi kuyi magana da Gimbiya? Na d'auko number data kira da ita muje dan Allah ka kirata, yanzun nan ta sa aka sake kirana tace ko magana ne a hadaku kuyi."
Abu Turab yace muje to.
Da yake akwai landline a bangaren Basira nan suka nufa.
Sabi'u ya danna numbobin, bayan sun gaisa da wace ta d'aga yace " Gimbiya suke nema ga Yarima Turab din."
Nan tace to.
Ba'a dade ba Bilkisu ta amshi wayar.
Nan ya mikama Abu Turab bayan ya gaidata.
Abu Turab ya amsa, Sabi'u kuma ya fita.
Shiru ne ya d'an ratsa kafin Abu Turab yace " kuna lafiya?"
A hankali tace " naji abinda ya faru, ya Umman taka?"
Mamaki ne ya kamashi dan baiyi zatan abinda zaiji daga gareta ba kenan.
Bata jira amsarsa ba tace " ance bazaka samu damar zuwa ba."
Yace " Bilkisu kinsan halin da ake ciki sannan Umma batajin dadi."
Kai ta jinjina tace " na fahimta, Abbana yace zai sake tunani akan auranmu."
Yasan hakan zai faru sai dai baiyi tunanin ji daga bakinta ba.
Murmushi yai yace " Nasani dole ne hakan ya faru, duba da yanayin da muka shiga, ko nine mahaifinki dole ne na sake tunani akan auran."
Jiyai tace " abinda yasa na kiraka shine inaso in tunama abu 2, kada ka bari wannan abun ya kwantar dakai, bansan meke faruwa a masarautarku ba sai dai nasan abu d'aya in har ka bari akaci galabarka a kan wannan abun banaji zaka farfado daga kuncin abin, zan duba ingani zan kuma sanar da Abbana akan mujira mugani in zaka iya warware matsalar nan daka shiga, na san zuciyarka dakakiya ce, zuciyace kuma ta 'ya'yan da suka kasance jarumai dan wannan dalilin ne yasa na aminta dakai, sai dai jin muryarka yanzu ya nunamin Mahaifiyarka itace lagwanka, inhar aka biyo ta bangaren Mahaifiyarka alamace ta angama cutar ka, an kuma rufema tunaninka da jarumtarka."
Idanunsa ne suka canza daga kalar tausayawar da suke dazu, Murmushi ya saki yace " Nagode Bilkisu jin kalamanki yasa na fahimci dalilin dayasa aka biyo ta bayan mahaifiyata, dan ansan bazan iya yin komai ba, zuciyata zata raunana ta hanani tunani komai, ta sani cikin rudo da tausayawa."
Zai sake magana yaji ta katse wayar.
Ajiye wayar yai yabita da murmushi lalai Bilkisu jinin sarautace ta asali, har daga jin muryarsa ta fahimci abinda ya kamata ta fadamai? Mikewa yai ya nufi waje.
Mairo wacce ta taho da magani ta ganshi.
Ta d'auka xata ganshi cikin yanayi na tashin hankali.
Kallanta yai yace " Mairo kin iso?"
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
_Tuba nake plz na jina shiru da kukai ✌🏻dayz_
*43*
Mairo ta tsaya kawai tana binsa da kallo, kai yad'an lank'wasar kadan yace " Lafiya?wannan kalan fa?"
Cikin mamaki ta amsa mai " Yaya Umma ta warke ne?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace " baki taho mata da ganin bane? Ko samu ne ba'ai ba?"
Tace " to ko an gano gaskiya ne?"
Kallan rashin fahimta ya mata yace " menene?"
Tace " naganka ne kamar abin ya daina damunka, sannan idanunka suna d'auke da confidence."
Murmushi taga ya sakar mata yace " ni kaina bansan ya akai ba bayan nayi wata 'yar karamar waya na samu kaina cikin wannan yanayin."
Tana kokarin tambayarsa wace irin waya yai jitai yace " shiga ciki, inada abinyi."
Kafin tai kokarin magaa ma yayi gaba.
Komawa yai b'angarensa yai wanka ya d'auko kaya had'ad'u ya saka, shadda ce bugagiya light brown, yayi kyau sosai da sosai.
In har ka ganshi to fa lalai zaka d'auka wani taro na mahimmanci zaije.
Haka ya fito hankalinsa kwance, Garzali na ganinsa ya mike ya biyoshi yana tambayarsa inda zasu.
Turab yace " Bangaren Umma Babba zamu."
Bayan ya shiga ne yaga ragowar matan sarki da kuma matan kannansa a zazzaune suna gulmar abin, da alama dubiya sukazo suka bige da gulma.
Ganinsa yasa kowa ya ja bakinsa ya tsuke, Abu Turab fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi ya gaishesu, haka kowa ya dinga amsa gaisuwar a kunyace dan sun tabbata yaji me sukace.
Kowa sai dayai mamakin ganin yanda ya d'au kwalliya duba da yanayi da suke ciki.
Kwankwasa kofa yai, Khadija ta taso.
Tana tura kofar tai ido hudu da Abu Turab, tana rike da kofar take binsa da kallo, kallanta yai kallo na bege sai dai bayanda zaiyi, da sauri ta katse kallon da takemai tace " Barkanka da Zuwa."
Ta karasa maganar tare da matsamai ta bashi guri.
Magajiya ce a kwance kamar d'azu sai dai Abdulmajid na zaune a kasa yana cin abinci.
Murmushi ya saki sannan ya kalli Khadija yace " nima zanci abincin."
Da sauri Abdulmajid ya kalleshi dan da ya dauke kai dayaji muryarsa.
Khadija ta kalleshi itakanta tayi mamaki sai dai amsa mai tai dato, tai waje.
Abu Turab ya kara tura kofar ya shiga bakinsa d'auke da sallama.
Abdulmajid ko amsa mai baiyi ba sai kallan mamaki da yake binsa dashi, wannam kwalliyar fa?
Abu Turab ya karaso ciki ya zauna gaban Abdulmajid yace " Abdulmajid Barka da war haka."
Bai amsa mai ba sai kallan mamaki da yake mai.
Shima bai nemi amsar tasa ba Kallan Magajiya yai yace " Har yanzu Umman tamu bata farfad'o ba? Inata tsoro kar muje ta wuce ta can kasan matsalar guba akwai illa ta gaske."
Yanda yake maganar kai kace irin Abokinsa ne Abdulmajid d'in.
Abu Turab ya kalleshi yace " kayi shiru ko baka neman mata sauki ne?"
Abdulmajid ya saki wata dariya ta takaici yace " duk duniya inda wanda zai fi damuwa da ciwon ta ai banaji ya kaini ko?"
Jinjina kai ya shiga yi yana cewa " gaskiya ne kuma kayi magana anan, sai dai ni kaina ina mata fatan samun waraka, dan ciwonta duk ya hanani sukuni."
Mamaki da takaici ma sam ya hana Abdulmajid magana.
Abu Turab ya d'an furzar da wata iska yace " ta ina zanso Ummanmu ta gangara bayan ko bikina da Gimbiya Bilkisu bata gani ba? Sannan Bata ga d'anta akan mulki ba?"
Ba shakka wannan kalma ta hawa mulki ta konama Abdulmajid rai, cikin zafin rai ya mike a zuciye ya kaima Turab naushi a kunci, wamda hakan yazo da daidai Khadija ta shigo d'auke da abinci.
Tana ganin Abu Turab ya fadi ta saki abincin tai gunsa da gudu.
Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace " Yaya sannu."
Sannan ta d'ago ta kalli Abdulmajid cikin takaicin abinda ya aikata tace " Yaya kana hauka ne? Ta yaya zaka nausheshi?"
Idanu Abdulmajid ya zaro yace" Khadija? Ni kike fadawa haka?"
Idanunta ya rufe gaba d'aya cikin masifa tace " an fadama, tayaya zaku dinga abu sam ba tunani? Me ya Turab ya maka? Dan yazo duba Umma? Ko dan ana zargin Mahaifiyarsa?"
Wannan kururuwar tasa mata dake zaune a falo leko d'akin dan dama Khadija bata ko rufe kofar ba.
Abu Turab ne ya sauye fuska zuwa yanayin tausayi yace " Khadija ki bari menene hakan kike yi?Laifine in yaya ya hukunta kaninsa?"
Kallansa tai cikin tsananin tausayawa idanunta sun ciciko da kwalla, tace yaya kalli gefen bakinka fa? Ya fashe."
Magajiya dake kwance tana jin duk abinda ke faruwa jitai zuciyarsa kamar zata fashe ba shakka sai taci mutuncin yaran nan.
Abdulmajid ganin yanda Khadija take ma AbuTurab hawaye yasa ma ya kasa magana, tsawa ya buga mata yace " ke dam gidanku fita daga nan."
Kallansa tai fuskarta a turbune cikin tsananin bacin rai, Abu Turab yace " fita mana."
Juyawa tai cikin takaici ta nufi kofa, ta na fita tai gida, tana tafe tana hawaye.
Magajiya data d'auka Khadija ta fita sannan ba kowa a d'akin kenan sai Abu Turab da Abdulmajid ta mike cikin kunar rai zatai magana.
Idanunta ne ya sauka akan matan dake labe jikin kofar d'aki, suma kallanta suke cikin mamaki.
" Laaa Magajiya ta farfado."
Nan suka shigo ciki, Abdulmajid ya runste ido na takaici sannan ya kalli Abu Turab.
Gani yai Abu Turab ya sakar masa murmushin rainin hankali.
Mikewa yai yace " Umma kin farfado? Kin ganeni?"
Wani irin kallan tsana da takaici takaima Abu Turab dan gaba d'aya ya wargaza mata shirinta ita dataso sai an ma Basira hukunci mai tsanani kafin ta nuna musu ta farfado? Sai an d'auka ta kusa mutuwa tukunna?
Kowa murna ne ya bayyana a fuskarsa, Abu Turab ya sosa keya yace " Lalai na yadda Mai maganin nan ya iya bada magani daga bata yanzu har ta warke?"
Kallansa sukai cikin mamaki sukace " Yanzu ka kawo mata?"
Kai ya d'aga alamar eh sannan ya kalli Abdulmajid yace "ko yaya?"
Abdulmajid bakim ciki yasa kawai ya d'aga kai , nan suka fito cikin tsananin farin ciki.
Suna fita Magajiya ta kalli Turab kallan Takaici tace " kai bazaka tafi ba? Uban me kake jira kuma?"
Fuska ya canza yace " Umma ina kikeso inje bayan yanzu kika farfado ke kanki ai bazaki so d'anki ya barnan ba."
Kallansa tai tace " mene?" Yace " abinda kikaji nace, ni ai yanzu tunanin dawowa kusa dake nake yu saboda na kula bakyasan nai nesa dake."
A zuciye Abdulmajid ya fizgoshi yace " kai wai kanka ko ya zare ne?"
Hannu Abu Turab yasa ya tureshi da karfinsa sannan ya nunashi da yatsa yace " Gargadi ne zan maka shi ka tsaya kajini dakyau, yau inaso ya zama rana ta karshe da zaka kara gigin tabani, wlh duk randa ka sake ina sanarma da duk abinda ya biyo baya kai kuka da kanka."
Sannan ya kalli Magajiya yace " Umma ya kike jinki? Kina farin ciki da dawowa duniya da na taimaka miki kikai da wuri?kinga yanzu kafin na fita d'aga nan zance zai kaiwa mutane na maganin dana baki kika warke da kuma wulakantani da Abdulmajid yai dan nazo baki magani."
Ya d'an langwab'e kai yace " ya kika gani Umma? Puzzle din ya shiryo ko?"
Ta cika taf dan kawai wani kallo takemai, Abdulmajid ma ya gama cika, juyawa yai ya fara tafiya har ya kusa isa kofa sai kuma ya juyo yace " ahhhh ina tayaki murna Umma dan Gimbiya Bilkisu bata yadani ba akan wannan al'amarin, na gode da kara bani karfin gwiwa da kikai na auranta."
Yana kai nan yai waje.
Magajiya yana fita ta juyo ta kalli Abdulmajid cikin tsawa tace " fita."
Waje yai yana fita ta ta kama bargon da aka lulubeta dashi ta matse da karfi kai kace juyemai bakin cikin takeyi.
Bangaren Mai Martaba ya nufa.
A hanya yaga Jakadiya tana ganinsa ta iso da sauri tace " ikon Allah ashe yarima kaine ka samu mata magani? "
Bai tanka mata ba saidai yana tsaye.
Tace " hmm gaskiya ne amma nikam yarima banso ka cece ta ba Kana ganin halin datasaka mahaifiyarka a........."
Katseta yai yace " Jakadiya, in zaki fadi abu ki fada amma banasan zancen gulma."
Ya juya yai gaba.
Zance ya yad'o a masarauta akan Abu Turab shine ya nemi mata magani, ba shakka in har mahaifiyarsa ce take neman kasheta bazata taba yarda d'anta ya nemo mata magani ba, wannan labari yasa mutane dayawa sun canza zargin su na cewa Basira ce ta bata gubar nan.
Zaune yake a gaban Mai Martaba, Sarki yace " Ka kawomin shaida ne?"
Abu Turab yace " a'a sai dai na rage zargin da akema Ummana."
Yace " kana tunanin wannan ya isa?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace " sai dai zai rage zagi da gulmar da ake mata, gaskiya kuma zan bayyanata ko ba yanzu, na kula in nace zan nemi gaskiya yanzu bazan taba samun komai ba dan na tabbata Magajiya ta riga ta gyara komai."
Sarki ya jinjina kai yace " na fahimceka."
Abu Turab yace " sannan maganar Gimbiya Bilkisu." Ya karasa fadar sunan yana susa keya.
Sarki yace " inajinka."
" Dama ina ganin zan shiga gunta karshen satin nan."
Murmushi mai Martaba ya saki yace " Naji dadi da fahimtarka da kuma amincewarka Allah ya kaimu karshen satin lafiya."
Abu Turab yace Ameen.
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*44*
Mikewa Magajiya tai daga kan gado cikin tsananin takaicin abinda Turab ya mata, abin haushi jitai baiwarta tana sanar da ita isowar baki dan tayata murnar warkewarta.
Haka ta bada umarni suka shigo, kan gado ta koma ta zauna, kowa yazo tayata murna sai ya jinjinama Turab da kokarinsa wannan abu yafi kular da ita, wasu dan gulma ma so suke suji me ya had'a Abu Turab da Abdulmajid.
In taji haka sai dai kawai tace " zancen mutane ne kawai amma su ba abinda ya had'a su."
Sai wajen Magrib ta samu sauki tai wanka ta sa kaya sannan ta aika a kira mata Hisham.
*******
Mairo kuwa bayan ta ba Umma magani nan ta dafa mata abinci ta bata taci, suna zaune labarin abinda ya faru ya isomusu, wannan labari yasa Umma dan jin dama dama.
Mairo kuwa jitai Abu Turab ya kara birgeta, ba shakka jinin sarauta ma yawo a jikinsa, ba shakka kwakwalwarsa da basirarsa tana aiki.
Sai wajen Magrib ta baro bangaren, Basira nata mata godiya, tana tafe tana murmushi dan ba shakka hankalinta ya kwanta da abinda ya faru.
Sam bata kula da shi ba tadai san ta wuce wasu daga gefenta sai dai bata san su waye ba.
Tana tafiya kawai taji an cafko hannunta ta baya.
A tsorace ta juyo, dan sai da gabanta ya fadi lokacin daya rikota.
Kallan mamaki da takaici ta sakar masa, sannan ta kalli hannunta tace " Malam sakeni ko"
Yace " ina san magana dake."
Tace " To dan kanasan magana dani sai akace ka rike min hannu? Sakeni tun kafin mutane su gamu."
Ga mamakita gani tai ya kara kankame hannunta yace " kina tsoron aganmu ne?"
Kokarin kwace hannunta ta shiga yi tana cewa " meye hakan?"
Abdulmajid ya matso daf da ita kamar zai rungumeta tsoro yasa tai baya, karfi yasa ya rikota, cikin murya mai kama da rad'a yace " zaki biyoni ko sai na rungumeki anan?"
Idanu ta zaro ta cigaba da kokarin kwace hannunta.
Murmushi ya sakar mata yace " Gimbiyata muje ko?"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 37