Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wasu daka b'oye a d'akin nan? So kake kaji me zan fada?" Turab yace " me kike san kice?" Tafin hannunfa ta d'aga tace " ka san me yasa muke da zane kala kala a hannun mu?" Yace " kwarai, kissa ta biyo akan mata ne lokacin Annabi Yusuf......"   Ta matso kusa dashi sosai yanda shikadai zai iya jin ke take cewa tace " mata ko? Amma tunda kasan wannan kissar kasan me matar da ta sasu tai ko?" Kallanta kawai Turab yake, tace " mace aka ce, ni kuma a matan ma dabamce. Sharri na da sanin duniya da nai ko rabinta bakai ba, kai baka isa ka shiryamin ramin da zan afka ba." Hannu tasa ta ture hannunsa ta bud'e kofa tai waje.   Turab ya ciji lab'anbansa. Mahaifinsa dake jikin d'ayan d'akin ne ya fito. Bazaka taba cewa sarki bane dan Shadda ya saka ba rawani a kansa sai hula, shida Sabi'u ne. Abdussamad ya matso ya dan daku kafadar Turab yace " ya kafadar jarumin d'ana zata yi kasa?kana tunanin daga bugun farko zakasa magajya tai kasa? Da daddare naje naga jikin nasa, sannan mayi maganar abinda ke faruwa a hankali, yanzu in aka kula na dade bama fada za'ai zargin wani abu." Turab yace " Tuba nake." Sarki yai murmushi yace sannan yai waje.   Turab ya tuno plan dinsa. Sanda Sabi'u zai tafi d'auko Khadija ya sanar dashi akan in har yanasan ganin d'ansa to yaje ya sanar da Sarki akan Magajiya na san ganinsa ganin gaggawa dan da matsala,  saboda shi a ka'ida bai isa yaje fada yasa mahaifinsa tasowa. Idan mahaifinsa yaji haka ya tabbatar ransa zai baci, sai dai bai isa nunawa ba saboda girmama matarsa kuma uwar gida. To in ya fito sai Jakadiya ta sanar dashi shigar burtu. To yasan mahaifinsa inyaji haka yasan Turab ne ya shirya wani abu. Ita Jakadiya zatazo bangaren magajiya ta tabbatar ta sa mutane sun fita gun kida da wayau, shikuma Sabi'u yana dawowa sai ya taho raka sarki yanda ganinsu tare bazai sa mutane susan sarki bane. Turab ya kalli Sabi'u yace " da alama nayi gaggawa akan yin plan dina, bazata taba yarda ta a sake fooling dinta twice ba." Sabi'u ya girgiza kai yace " wacce kake yi da ita ne tafi karfin plan din bawai kayu gaggawa ba." Turab ya shafi kansa yace " ka kai khadijan?" Yace " eh, na kuma maida Mairo gun Umma." Turab yace " nagode." Sabi'u yace " gobe fa Amarya zatazo haka zaka tarbeta jiki a sanyaye?" Turab yai murmushi yai waje. ********* Magajiya na fita tai bangaren Abdulmajid tasa a kira mata Hisham. Gabanta sai faduwa yake ba kakkautawa, inka kula da hannunta ma rawa suke yi. Yana shigowa ta taso a rikice tace " Me ya samu Abdulmajid?" Hisham yace " tun yaushe nake aikawa kizo?" Tace " meya sameshi?" Hisham yace " yana asibiti gun Turab." A rikice tace "wani irin hauka nakeji haka?" Ganin baiyi magana ba cikin tsawa tace " uban waye ya dakarmib d'a? A kuma wani dalili ne zai kasance gun Turab??" *Turab*    🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *73*     Ta gabansa ta wuce a zuciye tai waje. B'angaren Turab ta nufa, ba kowa a bangaren sai mai kula da kofa, gaisheta yai ya sanar da ita ai ba kowa a nan. Juyawa tai hankalinta a tashe, ina ya kaimata d'anta? Itakam mai makon wannan ranar ta zama ranar farin ciki yau kam wannan ranar ta gama zame mata ranar bakin ciki.   Ga magrib ta kawo kai..... ***********   Duk yanda Khadija taso da ya bud'e ido amma inaaa, ya kasa,yana kwance idanunsa a rufe, itakam gani take kamar baya haccinsa, sai dai shikam bayaji zai iya bud'e idanunsa yaga maike faruwa a wannan duniyar, bayasan ya bud'e idanunsa yaji abinda kwakwalwarsa bazata iya d'auka ba. Khadija zama tai a gabansa duk ta rame a 'yan kwanakin nan dan itakam sam yanzu rayuwar bata mata dadi, tace " Yaya ka taimaka ka farka." A can gidan Barde kuwa kwance take a kan gado banda juyi ba abinda takeyi, ta rasa menene ya hanata bacci, ta dade tanata juyi ta gaji ta mike zaune tare dayin dogon tsaki tace " Allah ya isa? Wannan wace irin muguntace? Haka kawai ku samu mutum ku hau dukansa ba gaira ba dalili?" Ahh ashe fa akwai dalili tunda Ya Turab akaje daka shi kuma ya shiga motar? Hannu tasa akan kirjinta tare da turo baki gaba tace " Allah sarki, ashe mutumin nan nada tausayi, sannan zuciyarsa ba wai mara kyau bace duka, me yasa muka kasa gani?" Ajiyar zuciya tai ta tuno sanda take mai rashin mutunci shi kuma yake nuna ba komai, batasan sanda ta sa murmushi ba, tunowa datai yanda ta ganshi a kan gado yasa jikinta yai sanyi. Idanunta ne taji ya ciciko, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe duka har kanta. ***********    Mai Martaba ne ya kalli Turab yace " ya akai Abdulmajid ya kasance cikin wannan halin?"   Turab ya kalli Abdulmajid da ke kwance yana bacci, karfe shida da rabi ne na safe dan ana sallar asuba suka taho shida Mai Martaba. Khadija na kwance akan sallaya rike da karamin kur'ani izu biyu da alama tana karatu bacci yai gaba da ita. Yace " Tuba nake ranka ya dade amma ni akaso halakawa." Sarki ya kalleshi yace "Shi kuma yaji kenan?" Turab ya d'aga mai kyai. Idansa ya runtse kadan sannan ya juya. Turab yace " Abba bazaka shiga ba?" Kai ya girgiza yace " kana tunanin zaiso gani na? Ko kana tunanin zai so ganin kowa? Bayan yaji da kunnensa mahaifiyarsa na neman yin kisan kai? Me kake tunanin yana ayyana wa a kwancen nan da yake?" Turab ya kalli Andulmajid cikin tausayawa. Sarki ya kamo hannun Turab yace " Abu Turab!" Turab ya kalleshi sai dai bai amsa ba. Sarki cikin wata irin murya yace " na girma, sannan ko ban girma ba haka na taso a rayuwar auranmu da barin Magajiya taci galaba akan dukkan lamuranta, saboda bata taba barin evidence dazai nuna tabbas itace ta aikata abu, sannan inba wanda ya san halinta ba ba wanda zai yanda akan abin da zata iya aikatawa, ina rokonka daka taimakama wannan mahaifin naka ya aiwatar da babban harkar shari'a ta gaskiya na karshe akan gadon mulkinsa, ka kawomin hujjojin da zasusa Magajiya ta fuskanci hukunci akan mayyan laifukan da ta aikata, wannan shine babban burina da ya ragemin a duniya in hakan ta faru inaso inyi murabus in baka mulkin nan, in d'auki mahaifiyata da matata mu ziyarci ka'aba dan ziyarar d'akin ma'aiki sannan mu jira sanda in karasa rayuwata cikin al'umma ina kallan yanda kake tafiyar da naka mulkin wanda shine abinda nafisan gani."   Turab yai shiru yanajin kalaman mahaifinsa,can ya d'ago yace " Abba insha Allah wannan d'an naka bazai baka kunya ba, sai dai maganar murabus mayi daga baya in komai ya kamalla."   Sarki yai murmushi sannan ya kara kallan Abdulmajid cikin tausayawa sannan yai waje. Turab ne ya murd'a d'akin jinshi a kulle ya kai hannu zai kwankwasa. Yanda yaga khadija tana bacci ne yasa ya sauke hannu tare da fasawa, ya tabbatar tana bukatar hutu.   Maida kayan mota yai ya zauna a cikin motar tare da kwantar da kansa jikin kujera. Garzali ya saukemai glass, a hankali shima bacci ya zareshi. *********   Magajiya kam wannan rana a zaune digirgir ta mata, babban tashib hankalinta duk inda ta aika a nemomata Turab sai ace baya nan, a wani hali Abdulmajid yake ciki? Dan itakam batasan wani abu ya sameshi, yanzu in matsala ta sameshi ta tabbatar shikenan ba shi ba hawa mulki, in hakan ta faru kuwa to wallahi sai dai kowa ya mutu dan Abu Turab bai isa hawa mulki ba sai dai su mutu tare.   Karfe bakwai tai wanka tai kwalliya tsaf kai kace ba matsalar dake damunta ta kintsa ta fito. Masu kula da ita mutum biyu tace " su biyota." Wajen karfe takwas tasa driver dinta akan ya wuce da ita ABU, manta wa ma tai ta tsaya tunanin ina aka kaishi.   Suna isa asibitin cikin sa'a ta hango motar Turab a waje. Driver dinta ta kalla tace " je ka kiramin Garzali." Nan yai waje, bai dade ba sai gasunan tare, Magajiya ta kalli Garzali tace " me kuke a waje haka?" Yace " Yallabai ne ya samu bacci." Tace " ayya, gashi shi yace inzo asibitin mu shiga tare gun Abdulmajid, kuma ba dadi yana bacci a tasheshi, ga ba wanda yasan gun, da alama sai dai ka taso shi din ko?" Garzali yace "gun Yarima zaku?" Tace " eh, kasan jiya ina cikin taro ban samu nazo ba sai yanzu." Sunkuyawa yai yace " nasan d'akin in ba damuwa sai na kaiku kafin ya tashi." Tace " shikenan." Ta fada tare da fitowa.   Sun isa har d'akin, ta sa aka kwankwasa kofar. Khadija dake kwance ta mike tare da zuwa bakin kofar tace waye?" Magajiya tace " Bud'e." Kallan masu kula da ita tai a Garzali tace "su juya." Gaban Khadija ne ya fadi dan Turab ko Ummansu bai bari tazo ba, a hankali ta bud'e kofar Suna juyawa ta d'aga hannu ta wankama Khadija wani gigitacen mari. Kuncinta ta rike saboda azabar da taji, shikanshi Abdulmajid sai daya farka daga baccin, dukda dai bai bud'e ido ba amma yana jinsu. Magajiya tace " Wato ke kin zama rikakiya ko? D'ana bashida lafiya dan tsabar rashin mutinci baki aikomin ba, bare insa ran zaki sanar dani inda yake."   A yanzu ji take zata iya yin komai dan kare d'anta, duk kuwa da yanda takesan Khadija. Wucewa tai ta kusa da ita ta nufi gadon da Abdulmajid ke kwance. Kallansa ta shiga yi sannan ta sa hannu kan kafarsa tace " wa ya saka? Wayace ka shiga motar da ba taka ba? Da kai nake magana, ka bud'e ido ka bani amsa ko sai ranka ya b'aci?"   Gaban Abdulmajid ne ke ta faduwa. Muryar Khadija taji tace " Haka Uwar kirki ya kamata ta fada ma d'anta dake kwance ba lafiya?" Magajiya ta juyo ta kalleta tace "mene?" Khadija tace " girma ana bawa wanda yasan darajarsa ne sai dai wanda baisan darajar ba banaji ya cancanceshi, bansan me kike nufi ba da cewa Wayace ya shiga mota ba amma banaji haka ya kamata uwar da danta ke kwance ta fadama d'anta."   Magajiya cikin gadara ta fara takowa inda Khadija take, ba shakka yarinyar nan Turab ya gama lalatata. Kusa da ita tazo ta d'aga hannu zata kara wanka mata mari. Har Khadija ta runtse ido jin bataji saukar mari ba yasa ta bud'e idanunta a hankali.   Magajiya ce ta kalleshi tace " me kakeyi hakan?" Turab ya kalli Khadija yace " bamu guri ko?" Khadija tai waje. Turab ya sauke mata hannunta yace " me kike anan?" Tace " kaine kasa d'ana a cikin motar daya kamata ka tafi ko?" Turab yace " mene?" D'anki? Hannu yasa akasan hancinsa yace " a da banso kisan abinda na sani ba sai dai kunnuwana sun gaji dajin muryarki tana cewa d'an da batasan zafinsa ba da sunan d'anta."   Idanu Magajiya ta zaro, a tsorace tad'anyi taku biyu baya. Turab yace " me? Kina mamaki ne? Wato kinaso ki halaka asalin d'an sarki ki saka d'an d'anuwanki akan mulki shiyasa kika sa a kasheni?"   Magajiya bakinta ya fara rawa tace " bansan me kake cewa ba, sannan zance kasheka bansan wannan maganar ba, sai dai ka tambayi Hisham."   Turab ya kalleta yace " banyi mamaki ba, dan dama nasan cewa zakiyi shine ya aikata hakan."   Shiyasa ana sanar dani zuwanki nasa Garzali ya kirashi, bari yazo sai muji wanene yasa a kasheni, daga nan sai mu nufi turakar Sarki."   Magajiya tsoro da fargaba ne suka dinga ratsata, inza'asan komai nata bazai dameta ba amma banda sirrin Abdulmajid, komai zata iya kwatar kanta inhar d'anta nada matsayinsa.   Abdulmajid dake kwance a kan gado a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro mai. Turab ne ya kalli kan gadon, ko tunanin me yai sai ya kalli Magajiya yace "ahhh yau Gimbiya zatazo banaji ya kamata in zauna anan, ina tunanin maganar a gida ya kamata muyi." Ya juya da sauri yai waje. A can gefe ya hango Khadija, gunta ya nufa fuskarnan a d'aure yace " Abdulmajid ya farka bayan na tafi? Tace "a'a." Bai jira mai zata kara cew ba yai gaba.   Dawowa yai inda take, kallansa tai, hannu yasa a aljihunsa ya ciro d'ankwalinta ya mika mata. Ya juya yai gaba, bakinta ta saki tana kallansa. Kallan bayansa tai har sai da ya bace mata, kwallar data zubo mata ta share. Sannan ta kurama d'ankwalin ido, ita kanta dan dai ya bata d'ankwalin ne yasa tasan nata ne, amma ita kanta ta manta dashi. Hawaye ne suka shiga zubo mata, in har Turab zai ajiye abinda ita kanta ta manta dashi to ba shakka yana santa. Amma meye amfanin san da bata tashi sani ba sai lokacin da bazai mata amfani ba, ko da yaks da can ma ko ta sani ma ba zai musu amfani ba.   Jingina tai da bango tanajin zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i na azaba........   ******* Magajiya kuwa Turab na fita ta rufe kofa da makulli ta zauna kusa da Abdulmajid tace " Uban waye ya isa ya ce ba ni na haifeka ba?"   Inhar kana tare dani ba abinda ba zan iya ba, dan haka ka gaggauta mikewa, Mairo kake so ko? Ka farka zan baka ita, mulki? wannan dama dole ne, sai me? Turab? Karka damu ko me zai faru sai naga bayansa, bazan taba bari yafadama wani sirrin nan nawa ba. Ko mai zai faru banaso kasan komai, ni dai kawai ka tashi. Sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin Abdulmajid ko motsi baya yi.   Shi kuwa Abdulmajid samun kansa yai da Addu'a mara amfani, baisan sanda yace " Allah ka d'auki raina......" *******   A can kano kuwa anata shirin zuwa kawo amarya, dan wasu ma yau da wuri suka taho dan kara gyara gidan Amarya da kara duba jeren da akai, Amarya Gimbiya Bilkisu kuwa yau tun safe ake ta gyarata, gyara mai sunan gyara na gargajiya bawai irin na xamani ba...... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *74*    Turab gidan Umma ya wuce inda take, yana isa ya tadda ta shiryamai abinci, nan yaci sannan ya kwanta akan kujerar falo. Fitowa tai daga d'aki ta kalleshi tace " Turab meye hakan? Ta ya zakaci abinci ka kwanta?" Mikewa zaune yai yace "Wlh Umma kaina kemin ciwo." Zama tai gefensa tace " Ba dole kanka yai ciwo ba, tun da ka tafi d'aurin aure har yanzu banaji ka samu isasshen hutu na awa biyu cikake, ni na kasa gane me kake tayi a waje haka, gashi ni kace in zauna anan." Turab ya kalli falon sannan yace "Umma ni dama ki dawo nan da zama." Kallansa tai tace "akwai abinda kake b'oyemin ko?" Turab yai kasa dakai yace " Ni Umma haryanzu Abba bai fad'amiki inda Hajiya dasu Lantana suke ba?" Umma tace " Bai fad'amin ba, sai dai inaji kamar fa har yanzu jikin Hajiya ba sauki." Turab yace "dama nayi tunanin haka, dan da ta warke da ta sanar dashi wani abu." Basira ta kalleshi tace " me kenan?" Kai Turab ya girgiza sannan yace " In kawo miki masu aiki daga can? Naga waccan kamar aikin zai mata yawa." Tace " karka damu, ni ma zaman haka kawai damuna yakeyi, yanzu kai haka zaka zauna har a kawo Amaryar?" Turab yace " name?" Tace " ko ma dai menene, ka samu ka huta sosai kafin suzo, kar suzo suganka a haka." Murmushi yai yace " a haka kamar ya?" Tace " oho dai nidai na fad'ama in ba so kake su juya da ita suce dama Ashe Angon ba shida jini a jika."   Dariya ya saka sosai, yace " lalai Umma, kawai kice kinaso in huta amma wannan sharhin babu shi." Tace " haka kace?" Yace " hmm, ni kam Umma akwai abinda nakesan sanar dake." Tace " name kenan?" Yace " Umma so nake idan komai ya kammala in d'aukeki da Bilkisu muje kauyen da na taso."   Umma ta kalleshi cikin jin dadi, tace " Ni kaina inasan zuwa sai dai ina tunanin me zance ma Sarki." Yace " ki jira in gama abinda nakeyi, sannan ki kara min addu'a akan Allah ya bani ikon gurfanar da masu laifi, ya kuma kareni daga sharrinsu, sannan karya bani ikon cutar da wasu saboda wani buri nawa."   Basira cikin kulawa take kallansa tace " Insha Allahu Allah na tare dakai, sannan muma bazamu daina maka addu'a ba." Haka sukai ta dan hira sama sama kafin daga baya ya kwanta.   Bacci sosai ne ya d'aukeshi wanda shi kansa bai san jikinshi ya gaji haka ba.   Bai tashi ba sai karfe biyu na rana. *********   A can gida kuwa Magajiya ce zaune a kuryar d'aki ita da Hisham ta kalleshi tace " Yaya Yaran can yasan komai." Hisham yace " name kenan?" Magajiya tace " yasan Abdulmajid ba d'ana bane." Hisham yai kasa dakai wato shiyasa ya ce mai haka? Sanda ya koreshi daga asibiti?"   Magajiya ta kalli Hisham tace " yaya duk yanda za'ai inaso ka tabbatar baka bari an san nice na sa a kama Turab ba, inaso ka yarda akan kaine kai komai, ni zan san yanda zanyi karyai magana akan Abdulmajid."   Tsananin mamaki ne ya kama Hisham ya kalleta yace " ban gane ba?" Tace " inaso ka ce kaine kasa a kama Turab in Sarki ya tambayeka, ni zansan yanda zanyi kar a hukuntaka." Tsananin mamaki yama hanashi magana sai kallanta kawaj da yakeyi. Magajiya tace " Sannan inaso a maida Khadija Kano, duk sauran matsalar daga baya ni zan san yanda zanyi, kai dai kai wannan abun guda biyu."   Ta mike ba tare da ta jira amsarsa ba tace " bari naje na kara shiryawa asibiti zan koma, dan bazan iya barin D'ana a can ba." Hisham yabi bayanta kawai da kallo Baki a bud'e. Ya dade a zaune kafin ya mike yai waje cikin tsananin takaici.   Gida ya wuce, ya shiga d'aki ya baza uban tagumi.   ***********    Mairo kuwa tana gama aikin gida da takeyi tai wanka ta shirya ta cema Ummanta zataje gun Umma Basira, nan ta fito, sai dai me? Asibiti ta fara wucewa.    A jikin windown d'akin ta tsaya, ba kowa a d'akin, batai niyyar shiga ba dama, gani tai yana kokarin motsi da hannunsa da alama idanunsa a bud'e yake kuma abu yakesan d'auka.   Da sauri ta shiga ciki, yana jin motsi ya koma ya kwanta tare da rufe ido. Mairo ta karasa gunsa da sauri tace " me kakesan d'auka?" Ta fad'a tana kallan gefe, ruwa ta gani a jarka da alama shi yakesan d'auka. Tace "Ruwa zaka sha?"   Jin shiru yasa ta matsa daf dashi tace " nice bakasan gani?"   Ganin bashida niyyar bud'e ido yasa haushi ya kamata ta juya zata tafi, jitai an riko hannunta. Tsayawa tai ba tare da ta juya ba, Abdulmajid a hankali yace "Karki fad'awa kowa na farfado, na rokeki." Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, gani tai yayi wani mugun fadawa, tace " bakasan asan ka farfado?" Kai ya d'aga mata, tace "ban gane ba? Abinci fa? Ruwa fa? Kashe kanka kake sanyi?"    Maimakon taga ya bata amsa gani tai yana murmushi, tace " murmushi ma kake?" Yace "in kina fada kyau kikeyi." Kallan mamaki tamai, sannan ta d'auko ruwa a cup ta mikamai tace ungo. Sam ya ma manta abinda ke gabansa ganin Mairo, yace " bazan iya tashi ba." Harararsa tai sannan tace " ta ya ya ma zaka sha ruwa? Ai kullema ciki zaiyi." Ta karasa tare da ajiye ruwan. Inda kayayyakinsu yake ta shiga dubawa, kular abinci ta bude ta zubo shinkafa miya wacce taji naman kaji. Abdulmajid yace " so kike inaci wani ya shigo?" Tace " wai me ke faruwa?" Idanunsa nd suka kada yace " ban cancanci cin abinci ba, magana ma bancancanci yimiki ba, Mairo." Mairo ta kalleshi tace " nima ce maka akai ina san yi maka magana?" Yace " haka ne, amma yanzu in wani ya shigo fa? Dan Khadija ma fita tai taje ta dawo." Bata amsa mai ba kawai yaga ta kukule window ta sa sakata a kofa, sannan tazo ta taimaka mai ya zauna ta mikamai abinci. Hannunsa ya nuna mata tace " to me kakeso ai?" Yace " shiyasa nace bazan ci........" Abincin data samai a baki ne ya hanashi karasa abinda zai fada. Haka ta shiga bashi abinci, tana bashi ruwa, daga zaiyi magana zata ballamai harara. ********** Turab na farkawa yaga Sabi'u a kujerar gabansa. Kallansa yai yace " kai kuma fa?" Sabi'u yace "gaskiya ban taba ganin ango irinka ba, ana can ana ta hidima a gidan sarauta amma kai baka nan, Ummanka bata nan, yayanka bayanan, nikam yau an ka wahalar dani." Turab yai murmushi yace " dama ko muna nan ai jama'a ne masu hidimar ba mu ba." Sabi'u yace " ka tashi ka shirya mu tafi, 'yan uwan Amarya sun fara zuwa. Yace" to ni mai kake nufi inje?" Sabi'u yace " au bazaka ku gaisa ba?" Turab yace "amma lalai kafi kowa, a ina aka taba haka?" Sabi'u yace " haba? Ba haka ake ba?" Turab ya girgiza kai yace " kai in anzo naka kayi, yanzu ina Umma?" Ya fada tare da mikewa. Sabi'u yace "ta tafi gun 'yan uwan Amarya, tace in fadama inka tashi, insun watse ta taho." Turab ya d'aga kai alamar gamsuwa. Sabi'u ya kalleshi yace " dazu waziri ya aiko inje." Turab yace " me yace?" "yace zaiyi tunani akan abinda kace mai." Turab yai murmushi a ransa yace " ko kayi tunani dolene ka amince da abinda nace dan nasan halin magajiya maida komai kanka zatai, in har kanasan taimakon d'anka da kuma kanka dolene kabi abinda nace." Sabi'u ne ya kalleshi yace "me kace mai wai?" Turab yace " ba komai." Yai ciki. Wanka yai ya saka kayan da Sarki ya aikomai. Yadi ne mai masifar kyau, kallo d'aya zaka mata kasan tsadarsa. Farin yadi ne, ya saka aikin babbar rigar kayan, yasa hula da takalmi ya fito. Tafi Sabi'u ya saka yana ganinsa yace "kai Ango, yaufa ba dama, da alama Gimbiya yau sai an tausaya mata." Turab ya kalleshi yace " yo ai dole a tausaya mata tunda Amaryar Sabi'u aka kai." Sabi'u yace "anma kafadamin magana." Haka suka taso suka fito. ""******** Zaune take a cikin mota, sai kuka takeyi, kanwar Fulani na gefenta da kishiyar Fulani. Wani had'ad'an leshi na da mai nauyi da tsada, ta sanya, tayi kyau sosai da sosai sai dai kukan da takeyi yasa duk kwalliyar fuskar tata ta tafi. Haka har suka isa garin na zazzagawa. Suna isa gidan aka saki wani busa na sarauta. Su Magajiya dama sun shirya dan tarbar ta, tana isowa suma suka fito suka zo inda suka tsaya. Magajiya ta dafa ta saboda fuskarta a lulube take ruf. Nan suka shiga har bangarenta, ana tafe ana zabga guda. Magajiya na ajiyesu ta tabbatar komai ya kammala ta fito. Tana san ganin fuskar Amarya amma hankalinta na gun Abdulmajid. ******** A asibiti kuwa Mairo tana gama bashi abinci, tana bashi ruwa aka fara kwankwasawa. Nan ta tattare kwanukan ta ajiye a kasa, shikuma ya kwanta. Kofar ta bude tana addu'a Allah yasa ba Magajiya bace. Ajiyar zuciya tai ganin Hisham ne da Khadija. Khadija ta kalleta tace " saukar yaushe?" Mairo tace " d'azu, har abinci ma naci, dan sanda ma taho ban tsaya naci abinci ba." Hisham ta gaida, jiki a sanyaye ya amsa ya shiga ciki ya duba Abdulmajid sannan yai waje. Mairo ta kalli Khadija tace " are u okay?" Khadija tace " name kenan?" Mairo tai murmushi tace " yau ake tariyar ya Turab." Khadija kanta ta sunkuyar sannan ta d'ago tace " ke zan tambaya ai duba da yanayin dake tsakaninku na shakuwa, ni dama mun dade a haka." Mairo ta kamo hannunta cikin tausayawa ganin yanda idanun Khadija suka ciciko, tace " Khadija ya Turab na bala'in sanki, in nace so tofa so d'in gaske nake nufi, tun kina karama yake sanki sai dai da alama har zuwa wannan lokacin bai bayyana miki ba." Kallanta khadija kawai takeyi, idanunta na zubo da kwalla. Mairo tace " Ya Turab a matsayin kanwa ya d'aukeni, kece zabin ransa ban san me yasa soyayyar ku ta koma haka ba." Khadija ta runtse ido tare da share kwallar ta tace " Mairo inaji dama can Allah baiyi akwai wata rayuwar jin dadi ta soyayya ba a tsakaninmu, soyayya ta zamantakewa bazata taba shiga tsakanina da yaya ba, mahaifina da Kanwarsa sun

Chapter 29 of 37