Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da alama dama naso kaina dayawa ne, Umma amma ba Abdulmajid ba, dan Allah Umma ki tai......." Idanu ta runtse dan ji take kamar ta kwalla kara na bakin ciki. Basira ta matso da ita ta rungumeta tana lallashinta, kuka sosai Mairo takeyi tana cewa " Umma ba Abdulmajid dan Allah, naji aban kowanenen amma bandashi." *************** A can garin kano kuwa bayan sun dawo a kofar shiga Mai Martaba ya kalli Turab yace " Inka koma wannan karan kasa a turo domin sa rana dan ba'asan masarauta da jan magana ba." Turab yace " Godiya nake Mai Martaba." Bayan mai tuka motar yai parking, wani bafade ne yazo da gudu ya bud'e sannan ya rad'a mai magana a kunne." Murmushi naga yayi sannan ya kalli Abu Turab yace " Turab muje kaima kwa gaisa da Minister." Abu Turab ya kalleshi sai dai baiyi magana ba yabi bayansa. Wani bangare aka kaisu, bangaren ya tsaru sosai wasu maza ne guda biyu a zaune kana ganinsu kaga uba da d'a duba da yanayin kamar su. Suna ganin Mai Martaba suka mike, uban na ta murmushin jin dadi. Sarki ma cikin fara'a ya kalleshi yace "Malam Haruna yau kaine da kanka?" Wanda ya kira da Haruna ya karaso suka gaisa, yace " Tuba nake Ranka ya dade da alama fishi ake dani." Zama Sarki yai sannan suka kara gaisawa. Yaran nasa ne ya matso ya gaisheshi. Shima Abu Turab ya gaida mutum. Haruna ya kalli Sarki yace " Ga d'ana Saifullahi, kullum ina cewa zan kawoshi ya gaidakai sai yau Allah yai." Saifullahi ya kara gaidashi. Sarki yace " naji dadi, ni kuma wannan sirikina ne." Mamaki ya kama Haruna ya kara kallan Turab. Sarki yace " d'an Sarkin Zazzau ne, Abu Turab." Fara'a ce ta kara bayana a fuskar Haruna, Saifullahi ya kalli Abu Turab." Haruna ya kalli Turab yace " Kace na ganka kai tun yanzu kafin mu had'a zuri'a." Turab yamai kallan mamaki da rashin fahimta. Haruna ya kalli sarki yace " ai Saifullahi shine zai auri yar gidan Waziri sunanta Khadija." Wani mugun fad'uwa gabasa yai da sauri ya d'ago ya kalli Saifullahi, wanda shima kallansa yakeyi. Idanu suka kafema juna. Sarki shikam bai kula dasu ba ya kalli Haruna yace " lalai Minister na tayaka murna Allah ya sanya alkairi." Yanayin kallan da Abu Turab yakema Saif yasa Saifullahi yace " Lafiya?" Turab yai saurin kauda kai yace " ba komai." Kallan mamaki Saif ya bishi dashi, dan ya kasa fahimtar ma'anar kallan da yake mai. 🤝🏻 *TEAM ABU TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *50* Mikewa Turab yai ya kalli Mai Martaba sannan yai kasa da Kansas yace " bari na baku guri." Ya fad'a kansa  na kasa.   Sarki ya jinjina kai yana murmusawa yace " To Turab kaje ka huta."   Gaida  Mahaifin Saif yai sannan ya musu sallama yai waje.   Jiyai ance Ina magana. Tsayawa yai tare da juyowa dan duba mai magana.   Saif ya gani ya ya tsaye daga kan baranda, saukwa yai ya nufoshi. Tunda ya taho Turab yake binsa da kallo ni kaina bansan me yake aiyanawa a ransa na. Saif ya karaso sannan ya saki fuska yace " Naga kamar bai dace mu rabuba ba tare da sanin  junan mu ba, duba da yanayin nan gaba zamu zama dangin juna?" "Dangi?" Abu Turab yai fad'a sannan ya murmusa yace " Yama kace sunan?" Saif. Turab ya jinjina kai yace "Saifullahi, am sai dai kayi mantuwa Abdulmajid zaka fadawa haka bani ba."   Saif ya kalli Turab tabbas yaji haushin maganarsa yace " Amma na d'auka......" Turab ya katseshi yace "Allah ya sanya alkairi." ya juya ya tafi, dangin juna? Ya kara maimaita Kalmar tare da jan tsaki yace " kama rainamin hankali."   Yana shiga masaukinsu Sabi'u ya taso saga zaunen da yake yace " Ka dawu? Sirikin mu." Turab ya bugamai wani kallo yace " wai ni har wani d'an rainin hankali zai kalla yace wai mun kusa zama dangin juna? Ha ha amma ya gama rainamin hankali ya karasa maganar tare da zama. Sabi'u cikin mamaki ya kalleshi yace " Nikam kai da waye?" Turab yaja tsaki yace " wai wani Saif, ko Khadija yakeso ko Khadija zai aura ni ban ma sani ba."   Sabi'u ya tuntsure da dariya yace " Turab? Kaine?" Kallansa Turab yai baice komai ba sai dai takaicin dariyar yakeyi. Sabi'u ya matso kusa dashi yace " Khadijan ka?" "Eh ma......." Sai kuma yai shiru sannan yai saurin mikewa tsaye yace " wace irin banzar tambaya ce wannan, ban gane Khadija ta ba? Wai kai Sabi'u me yasa ka iya abin haushi ne?"   Sabi'u yace "ohhh abin haushi? Sai naga kamar kishi ne ya ciwoka kake bukatar tausa." Turab ya bugamai wani banzan kallo yace " kishi?" Mtsw kai fa sai a hankali wlh. Ya fad'a tare da shigewa d'aki yanaji Sabi'u na cewa " karka manta anjima zakaje gaida Fulani mijin Gimbiya "   Yana shiga d'aki ya zauna a bakin gado yace " me ya sameni? Why am i acting like this?" Sai kuma ya nuna kansa cikin mamaki yace " don't tell me kishi nake?" Kai ya girgiza da sauri yace " inaa tayaya ma zanyi kishi akan wacce take zuri'ar makiyana?"   Yin baya yai ya kwanta akan gado, yana takaicin wannan abu, inama shikam baisan Khadija ba a rayuwarsa?" ********* A can Zariya kuwa Magajiya ta rasa abinda ya kamata tai ta dade tana tunani kafin daga baya ta wuce cikin d'akinta.   A zaune a kasa ta taradda Khadija kana ganinta kasan tana cikin wani hali. Magajiya ta karaso kusa da ita tace "Mamana mike." Ta fad'a tare da miko mata hannu. A hankali Khadija ta tashi sannan ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna a kusa da ita.   Hannayenta ta riko tace " Khadija san Abu Turab kike?"   D'agowa tai da sauri ta zubama Magajiya idanunta wad'anda suka cika fal da hawaye, sai dai bata iya bata amsa ba. Magajiya tai murmushi sannan tace " kin san waye Abu Turab?" Kallan mamaki ta mata dan bata fahimci me take nufi ba. Magajiya ta d'anyi ajiyar zuciya tace " Khadija baki san waye yaran nan ba, wannan maciji ne wanda dafinsa keda tsananin zafi, kinsan yaron nan idanunsa biyu amma yake nuna makaho ne? Kinsan ya tsaneni da mahaifinki amma yake nuna miki so dan kawai yai amfani da ke? Mune jininke, mu kad'ai ne muka san darajarki bazamu taba cutar dake ba."   Ganin Khadija ta zare hannunsa daga cikin nata yasa ta tsaya da maganar tana binta da kallo. Sai kuma ta mike sannan tai murmushi tace " Umma Babba bazan ce nasan Ya Turab ba tunda ba tare mukai rayuwa dashi ba sai dai namanta ban fad'a miki kalma d'aya ba, nice nakesan Ya Turab ba shine yakeso na ba."   Ta juya tana tafe kamar wacce zata fad'i dan ba shakka kalaman Magajiya sun so kawo mata rud'u cikin kwakwalwarta, maciji?yana gani?amfani da ita? Ba shakka ba dan tayi saurin katseta ba da alama da sai ta canza mata ra'ayi a xuciyarta. Kallan kofar data rufo ta Magajiya tai  a ranta tace " Umma Babba please don't disappoint me anymore."   Abdulmajid ta gani a tsaye a waje da alama ma jiranta yakeyi. Yi tai kamar bata ganshi ba ta fara tafiya. Da karfi ya finciko hijab dinta yace " Wato ke Abu Turab ya fi miki ni ko? In taimaka in barma Turab Mairo? Ke meyasa bakida hankali ne?" Khadija ta kalleshi idanunta sunyi raurau tace " Yaya me ka nema ka rasa a duniyan nan?" Kallanta yai baice komai ba. Tace " kanada komai na rayuwa, matsayi,iyaye, lafiya, girmamawa, me ka nema ka rasa?" Ta share hawayenta tacigaba " Ya Turab na san yarinyar nan, kai ko tausayin sa bakayi?"   Kallanta kawai yake yama kasa magana, ta share hawayenta sannan tace " ku kanku kunki kyale bawan Allahn nan, bakin cikin abinda kuke mai shine na tabbata dalilin dayasa ko ganina baisan yi....." Hawaye ne suka nemi fin karfinta, da sauri ta juya ta fara tafiya. Abdulmajid baki kawai ya saki yake kallan mamaki. Shi Khadija takema wannan banzan sharhin? *********   Mairo kuwa baya ta gama fad'an kalamanta Baseera ta jawota jikinta tana lalashi. Tace " Mairo dama kina san Turab? Na dade ina hasashen haka sai dai wani sa'in ina tunanin rad'in kainane yasa nake ganin haka ba wai kece kike sanshi ba, ki kwantar da hankalinki ki koma gida, tunda har nasan abinda ke ranki ni kuma xanyi iya kokarina naga komai ya dawo daidai." Mairo ta d'ago sai dai batace komai ba.   Hisham na fita ya wuce gida ransa a b'ace a tsakar gida yaga mahaifiyar Khadija a zaune. Rufeta kawai yai da fad'a. " Aikin banza ace tarbiya wannan kin kasama 'yarki, inba rashin tsaro ba har yaushe ma kika bari yarinyar nan ta sakankance da wani can sokon yaro, yaron da zuwansa doron kasa shine abu mafi muni da ya taba faruwa a rayuwata, to wlh inma zaki sa Khadija ta cire wannan shirman a ranta kiyi dan wlh in har na sake kamata tana kuka akan yaron can wlh abinda zan miki sai kinsha mamaki." Bai jira ta tofa komai ba yai gaba fuuuu....... 🕊 *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*   *51* Zaune yake a cikin wani had'ad'an gun hutawa, a hankali yana cin inibin dake gabansa sannan yana duba littafin hannunsa, lumshe ido yake yi saboda yanda yakejin dadin rayuwa, cikinsa ne yaji ya murd'a nan fa wani azababben ciwo mai tada hankali ya rutsashi, baisan sanda ya durkuso kasa ba yana murkususu saboda azaba, idannan nasa yayi jaa kamar garwashi, tsananin tashin hankali da rad'adin da ya ke ciki. Jiyai an sakar masa wata irin dariya na keta da sauri ya d'ago dan ganin wani mugun ne wannan ba taimako sai dariya?   Magajiya ce cikin wani had'ad'an shiga tayi kwalliya sosai, dariya take sosai. Abdulmajid ne ya fito daga bayanta shima yana dariya harda kyakya tawa. D'ayan gefen kuma Hisham ne ya fito shima dariya yakeyi sosai, nuna shi suka shiga yi suna dariya. Basira ya gani a kasansu a kwance wanda baisan ko tana raye ba ko ta mutu. Sannan Abdulmajid yana rike da igiya yana jan wata yarinya a kasa, kallan yarinyar yai ga mamakinsa sai yaga Mairo. Kirjinsa ne ya d'au zafi, Khadija ce ta taho da gudu gunsa tana kuka kamar ranta zai fita, da sauri Hisham yasa hannu ya fizgota. Jiyai gaba d'aya ya kasa numfashi da sauri ya bud'e idanunsa. Cikin tashin hankali yake kallan d'akin, ga zufa da yai sharkaf. Zama yai cikin tashin hankali yana addu'oi, ba shakka wannan mafarkin ya tsoratashi, shi yasa baccin yamma bashida kyau. Mikewa yai ya sauko daga kan gadon, sai dai jiyai kafafunsa na rawa. Gado ya dafa tare da runtse idanunsa. Ya dade a haka kafin ya daure ya shiga ban d'aki. Bayan ya fito ne ya zauna a bakin gado, ba shakka mafarkin ya bayyana karara kamar gaske. Ga kansa na mai wani azababben ciwo. Sabi'u ne ya leko yace " Ranka ya dade ka tashi? Wai daga shigowa sai in tadda kai kana bacci?" Turab ya kalleshi kawai baice komai ba. Sabi'u yacigaba " dama aiko wa akai in anyi magrib zakaje ku gaisa da Fulani." "Gobe da sassafe zamu koma gida." Abinda Sabi'u yaji ya fad'a kenan. Mamaki ya kama Sabi'u da sauri ya karaso cikin d'akin yace " Mutumina lafiya?" Turab ya kalleshi, ganin yanda idanunsa sukai ja ya matso da sauri yace " Yarima Lafiya?" Turab ya mike yazo kusa dashi kawai ya dafa kafad'arsa sannan ya wuce. Waje ya fito ya tsaya yana kallan sararin samaniya, me yasa yakejinsa haka? Bayan Magrib jakadiya tazo ta raja Abu Turab gun Fulani, sosai ta karbeshi sannan itama ta rokeshi akan rikon Bilkisu, irin amsar dayaba Mai Martaba ita ya bata. Haka ya taso cikin gamsuwa da yanda sukesan 'yar tasu. Munnira ce ta biyoshi da sauri ta mikamau wata takarda. Amsar takardar yai ya kalleta yace " ta menene?" Munnira tai dariya tace " UmmaBilkisu ce tace in baka." Amsa yai yana cewa " Yau Umman taki rowar ganinta take min?" Munnira tace " zaka ganta gobe ai." Bud'e takardar yai yana cewa "Gobe zan tafi da safe." Kallan mamaki tamai tace " Amma UmmaBilkisu vata sani ba?" Kai ya d'aga yace " nima dazun na yanke shawarar haka, amma zan dawo ko zuwa sati biyu ne." Duba takardar yai, number waya ce ta landline a jiki a kasa tasa, inka samu time ka nemin a layin nan." Murmushi yai ya kalli Munnira yace "kice mata nagode, dama nayi tunanin tambayarta." Ya juya yai gaba *********** Washegari. A zariya Basira tayi shiru tana tunanin mafita, ba shakka ko d'anta bazai auri Mairo ba bazata taba bari Abdulmajid ya aureta ba. Mikewa tai ta kali Lantana tace "Lantana muje in duba Hajiya sannan muje gun Magajiya." Mamaki ne ya kama Lantana sai dai bata ce komai ba. Sunje gun Hajiya jikinta kam kamar kullum ba sauki sam, dan ko maganarta dama ba ganewa akeyi ba. Yau kam jikin ya d'anyi sauki. Mai kula da ita suka tarar tana bata magani, sai dai tana ganinsu ta daina bada maganin ta mike da sauri ta rufe maganin ta d'auka. Basira ta kalleta tace " ta gama shan maganin ne?" Dan yanayin yanda yarinyar tai yasa ta kasa fahimtar hakan. Cikin rawar murya tace " ta gama." Ta karasa magana tare da fita. Basira ta zauna kusa da ita sannan ta gaisheta. Kai ta d'aga mata, Basira tai murmushi tace " yau kam naga jikin da sauki." Basira gani tai ta miko mata hannu alamar ta riketa. Nan ta riketa tace " Hajiya." Kokarin magana takeyi sai dai ta kasa da alama akwai abinda takesan fad'a. Kunnenta ta matso dashi tace " Hajiya menene? Akwai abinda kike so ne?" Ma ma ma ga....... Basira tace " maga me?" Hajiya ta kara daurewa tace " Abbbbb......" Da sauri wannan yarinyar ta shigo tace " Hajiya a kawo miki ruwa?" Yunkuri takeyi da alama akwai abinda takesan ta fad'a. Basira ganin yanda taketa keta zufa tace " Hajiya ki barshi sanda kika ji dama in har abun daya kamata ne sai ki fad'amin." Idanu ta runtse na takaicin kasa magana da take, gashi dama ko zama bata iyayi. Sun dade kafin su fito, Hajiya tai shiru tana tunanin abinda ya faru shekaru hud'u da suka wuce. Taya zatai ta sanar da d'anta abinda ke faruwa? Tundaga ranar da ta mata magana akan abin a ranar ta fara rashin lafiya wanda har yau ciwo sai gaba yake baya raguwa. Kowa ya d'auka tsufa ce ta sata wannan rashin lafiyar sai dai ita tasan ba haka bane. B'angaren Magajiya suka nufa. Bayan ta zauna a kilisarta ne, aka shiga ciki dan sanar da Magajiya zuwan Basira. Ta dade dan takai akalla minti 20 kafin ta fito. Tafiyarta take cikin takama, tazo ta zauna cikin isa sannan ta kalli Basira a wulakance. Basira ta gaisheta sannan tace " Zuwa nai muyi wata magana." Magajiya ta kalleta tace " inajinki, sannan inaso ki hanzarta saboda inada abinyi." Basira tai shiru tana tunani kafin tace " Me kike tunani game da auran Abdulmajid da Mairo?" Magajiya ta zuba mata ido sai dai batace komai ba. Basira tacigaba " Zuwa nai inji ra'ayinki akan auran......." " nikam a iya sanin kwakwalwata ban ji ance kin sake haihuwa ba, ko ince banji ance kina d'auke da cikin wata yarinya Mairo ba, dan haka banaji kina da hakki akan auranta." Basira ta d'ago cikin mamaki tace " ai ba sai ka haifi mutum ba kake da hakki akansa ba Ranki ya dade." Magajiya tai wani banzan murmushi tace " ko? To in haka ne nima bari nai iko da Abu Turab wanda ban haifa ba, inaso kice ya dawo daga garin kano sannan ya janye auren Bilkisu ya auri Mairo wacce kike so." Tsananin mamaki ya hana Basira yin magana, ta kalleta tace " ban gane......" "Kurma ce ke? Ko kuwa fahimtace baki dashi?" Sai kuma tai wani lalausan murmushi tace " ko dayake wacce akai rufa rufa agun auranta saboda rashin matsayinta da abinda ta aikata a baya banaji tanada inda zatai tunani a kwakwalwarta." Gaban Basira ne ya fad'i tama rasa me zatace. " kin kyauta da kika zo, dama ko bakizo ba zan aika kizo, inhar kinaso in rufe sirrin da aka fad'amin ki tabbatar kin sa d'anki ya janye auran Bilkisu dan d'an sarki sai 'yar sarki, Abdulmajid zai auri Bilkisu shikuma d'anki Turab ya auri Mairo kinga in akai hakan komai yazo da sauki kenan, kema kinsamu abinda kikeso kamar ni." Basira tai dauriya tace " me kikaji akaina? Banaji inada wani abu da zan......" "Hmmm kin manta ba'a cikakiya aka aureki ba?" Tashin hankali ne karara ya bayyana a idanun Basira, ta daure tace " ban....." Wata irin dariya Magajiya ta saki ta kalleta tace " Basira sunana Magajiya." Basira tai shiru sai jikinta dake tsuma. Magajiya ta mike ta zo inda take ta tsugunna tare da dafata tace " Me yasa banyi tunanin komai ba da? Sai dai karki damu sirrinki zan tayaki ajiyewa in har kika sa d'anki ya janye maganar auran Gimbiya, dan ko za'a mutu bazan taba bari ya aureta ba." Ta karkad'e mata kafada tai gaba. Magajiya tana shiga d'aki tai wani mugun murmushi tace " lalai da gaske ne." Tunowa tai jiya bayan ta rasa mafita kawai ta kira Hisham tace ya kira abokinsa dake garin Daura, yasa yamai bincike akan Basira, ba shakka sai yanzu ta fara tunanin tabbas haka kawai sarki bazai auri Basira a b'oyeba, duk da batai tunanin wannan matsalar ba tadai san akwai wani abun. Basira kam da kyar ta mike jikinta na rawa ta fito. 🤝🏻 *ABU TURAB TEAM* *KAINUWA*🕊      ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_)    *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _AyI hakuri da Jina shiru da kukai kwana biyu, azumi nakeyi_🙈 *52* Abu Turab dama ya sanar da Fulani zancen tafiyarsa, nan sukai sallama da mai martaba cikin jin dadi dan bai tambayeshi dalilin tafiyarsa ba. Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan ya nemi ganin Bilkisu dan yin sallama. Itakam Bilkisu tunda Munnira ta sanar da ita take tsaye tana zagaye d'akin, meke faruwa? abinda ke mata yawo kenan har mai kula da ita ta sanar da ita neman da Turab yake mata. Cikin sauri ta duba fuskarta a jikin madubi sannan ta nemi fita, harta kai kofa sai kuma ta tsaya, taja wani dogon numfashi sannan ta kara neman nutsuwarta kafin ta fito. Yana zaune yayi shiru ta shigo da sallama, dagowa yai tare da amsawa yana kallanta. Sai data zauna sannan ta gaisheshi tare da cewa " Lafiya dai ko?" kallanta yai yace " nikaina abinda nake san sani kenan." Kallan mamaki tamai sannan ta d'ora da cewa " badai wani abu mara kyau bane ya faru ko?" Hannunsa ya sa yad'an shafi saman goshinsa sannan yace " Ina ji nane ba dadi, inajin kamar da wata babbar matsala datake faruwa a gida." Kallansa tai sannan ta d'anyi murmushi tace " Insha Allah ba abinda ya faru sai alkairi, sannan in har wani abu mara kyau ya faru ko ka fuskanci kana cikin tsaka mai wuya ina rokonka da karka yanke hukuncin da nan gaba zakai dana sani, ka jinkirta yanke hukunci har sai zuciyarka ta aminta da wannan hukuncin." Murmushi ya sakar mata yace " Nagode." Itama murmushi tamai sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Mikewa yai yace " zan wuce." D'agowa tai ta kuramai ido sai dai batace komai ba, a hankali ya tako zuwa inda take sannan ya tsuguna a gabanta tare da zaro abu a aljihu, ya nuna mata takardar databa Munnira na layin waya, yana murmushi yace " na gani na kuma gode." Kallansa tai sannan ta saki wani lalausan murmushi. Mikewa yai yace " kafin in dawo maybe an tsaida rana." Da sauri ta maida kanta kasa, wata yar karamar dariya yai wacce batada sauti yace " wannan d'in kunya ce?" D'agowa tai ta harareshi tace " dama haka ake yi? da kanka ya kamata ka fad'amin zancen?" Dariya ya sakeyi yace "au haka ne? to goge abinda na fad'a a zuciyarki inyaso sai a sake sabon la le." Murmushi tamai tare da juya kanta gefe tace " na goge." cikin zolaya yace " nikam me ma nace?" Hararar sa ta sakeyi sannan ta maida kanta kasa tana murmushi, ashe yanada side na zolaya, farkon ganinsa ta d'auka mutum ne wanda bayasan wasa sam, sai dai yanzu ta fara tunanin tsauri da jinin mulki ne ya sashi haka. Dagowa tai ta kalleshi sai dai batace komai ba. Murmushi ya mata sannan yace " zan kira." kai ta d'agamai, yace " zan wuce" nan ma kai ta d'agamai. Lab'ansa ya d'an hade sannan yace " nagode." Murmushi tamai, nan ya juya yai hanayar fita. Sai dayaje kofa yaji muryarta a hankali tace " Allah ya kiyaye hanya." Juyowa yai yana murmushi yace " Ameen." Nan ya juya ya fita, yana zuwa ya tadda Sabi'u ya sa an fita da komai, nan suka kama hanyar gida. Basira kam abin duniya duk ya gama damunta tama rasa ina zata saka kanta, da farko tayi tunanin fad'ama Sarki sai dai tace me? wad'annan tunanin sun hanata sakat, fatanta kawai d'anta ya dawo, ta sanar dashi hukuncin magajiya. Magajiya kam tana zaune a kilisarta tana kurb'an shayi wanda yaji kayan kamshi, tana sha tana lumshe ido, kana ganinga kaga wacce take cikin nishad'i da jin dadi. ********** Da rana su Abu Turab iso, Sabi'u yana ajiyeshi ya sauka daga motar yace " ni nayi gida mutumina." Turab kai kawai ya d'aga mai, fadawa ne suka taho da sauri suka shiga kwashe kaya. Kallansu yai yace"ku kai kayan b'angaren Umma ni zan shiga fada na gaida Sarki." nan suka amsa da to, shi kuma yai gaba. Bayan ya shiga fada ne ya kwashi gaisuwa, Sarki cikin mamaki yace " me ya dawo dakai yau? bayan sai gobe kace?" Shiru yai na wasu dakiku kafin ya d'an sosa keya yace " zuwa nai na sanar da Sarkin Kano mahaifin Gimbiya yace ya na jiran lokacin sa rana." ya karasa maganar tare da maida kansa kasa. Galadima yace " Alhamdulila abu yayi kyau, nikam Takawa mai zai hana ka had'a auran yarima Abdulmajid da na Yarima Turab kawai ayi a rana d'aya?ko har yanzu ba'a tsaida maganar ba?" D'agowa Turab yai cikin mamaki sannan ya kalli Galadima, cikin neman karin bayani yace " Abdulmajid ya samu mata ne?" Galadima yana murmushi ya kalli Barde wanda yai shiru kamar wanda aka daka haka yake jinsa, sannan ya kalli Wambai yace " au ashe fa bakanan? ai 'yar gidan Barde yakeso yama sunan ta?" Wambai yace " Mairo." Idanu Turab ya zaro cikin tsananin mamaki yace " Mairo? ya fad'a yana kallan Barde, sannan ya kalli Hisham wanda shima yaci magani." Murmushi ya kakaro sannan yace " Bari na shiga ciki Ranka ya dade." Sarki wanda shima ya rasa ta cewa yace " Ya kamata kam, kaje ka huta." Turab ya kara gaidasu sanan yai waje. Cikin hanzari yake tafiya Mairo? lalai ma yaran nan ba karamin mahaukaci bane, an tab'a aure dole? Hangoshi yai a gabansa kamar irin yasan maganarsa d'in nan yakeyi. Tsayawa Turab yai ya kafeshi da ido, shima Abdulmajid wanda ke hanyar Fada dan jin hukuncin da aka yanke ya tsaya tare da kafe Turab shima da ido. Cikin kasaita kowannen su ya fara takowa, idanunsu na kallan juna har zukazo daf da juna. Abdulmajid ya kalleshi yace " Sirikin sarkin kano ka iso?" Wani murmushi na gefe Turab ya saki

Chapter 20 of 37