Share this page
ya ga giftawar taurari. Sulaiman ne ya fashe da wata dariya da sai da ya komawa kowa madubi abin kallo wato kowa ya tsaya yana kallonsa da mamaki, sai dai yana cikin dariyar sai ya haɗe fuska, ya ɗaga kai yana kallon Ma'aruf da yake dafe da kunci, ya juya ya kalli Mummy sannan ya sauke idanunsa a kan Rahma cike da izza da taƙama irin ta ɗan gidan masu faɗa a ji ya ce "Rahma ki sani daidai da second ɗaya ban taɓa sonki ba" Idanu ta zaro cike da fargaba zuciyarta ta bugu da ƙarfi, Mummy kuma baki ta saki tana kallonsa da tsantsar mamaki, Ma'aruf kuwa da dama ya san kwanan zancen sai hakan bai ɗaɗarashi da ƙasa ba, bai ba kowa damar magana ba ya cigaba da faɗin "Na san saboda ina da kuɗi kike sona, da bani da kuɗi na tabbata ba za ki ƙaunace ni ba, tun da dai kika guji ɗan uwanki saboda bashi da kuɗi, bayan ya fini komai na ɗa namiji nagarta kyau da komai, to kin ga saboda na guje ki kar hakan ya dameki, ni dama don kawai a yi soyayar sharholiya don ki sani ma akwai wacce nake so, dama da a ce soyayyarmu ma ta ɗore sai dai ki ji an ɗaura mini aure, ina miki tuni da waɗanda kika yaudara a baya, kika fasa son su saboda kin sameni kika guje su, to ke ɗin ma yau gashi zan nisance ki, dama an ce duk abin da ka shuka shi kake girba, sannan duk abin da ka yi shi za a yi maka" Yana kaiwa nan ya mayar da kallonsa ga Ma'aruf wanda ba ya mamaku furucin Sulaiman ɗin don shi abu ne da ya gama fahimta tun ba yau ba. Yana kallonsa ya ce "Ɗan jagaliya ga ƙanawarka nan na bar ta zan je na tafi" Rahma ita mutuwar tsaye ta yi don kuwa maganganun Sulaiman sun ɗaure mata kai, ta kasa furta komai tana a hakan ya nuna mata fuskar wayarsa ya ce "Kin ganta wacce nake da burin na aure ƙiris ya rage" Ya ce yana nuna mata hoton wata a wayae, sai ya juya ya nuna wa Mummy kawai sai ya fara taku ya fara tafiya. Ma'aruf ya ce "Ka je da mugun nufinka, Allah raka taki gona" ,Mummy ta ɗaga murya ta ce "Shege mai baƙin hali, mummunan halinka ya bika Allah ya isa, sai ka samu wanda zai maka abin da ka yi" Juyowa ya yi ya ce "Kamar yadda kuka sameni na muku abin da kuka yi wa wasu ba" Rahma juyawa ta yi da gudu ta yi hanyar da za ta sada ta da cikin gida. Mummy ta ɗaga kai ta kalli Ma'aruf tana surfa masa zagi kamar ta ari baki, tana jaddada masa cewar ya ɗauko ruwan dafa kansa, don ta ɗauki aniyar saita gintse masa ɗan karatun bokon da yake taƙamar yana yi don dole sai ungulu ta koma gidanta na tsamiyata. Ko fitar da za ta yi fasawa ta yi, ta koma ta hau lallashin Rahma da take ta kukan maganganun Sulaiman duk da abin da ya furta amma sai da ta koma tana faman kiransa a waya amma yake katsewa daga ƙarshe ma sai wayar ta ji a kashe. Ma'aruf kuwa godiya ya yi wa Allah da ya sa halin Sulaiman ya bayyana ko ba komai ya ceci ƴar uwarsa daga mummunan nufin da Sulaiman ɗin yake yi a kanta, ko bai auri Rahma ba duk da cewa dama ya san abu ne mawuyaci ya aure ta duba da yadda ita da mahaifiyarta suka tsane shi amma dai zai so ta samu namiji mai sonta da aure ba wai ɗan a hole ba. Tun kafin Daddy ya dawo gidan Mummy take doka masa kira a waya, yadda ya tsinci muryarta ne ma ya sa gabansa faɗuwa, saboda a nasa tunanin ko ɓoyayyan sirrin da yake ɓoye mata ne ta sani. Amma bayan ta shiga faɗa masa akwai matsala a gida sai ya ji ya ɗan samu sassauci don shi ba ya fatan Hajiyar ta ji ƙudurin sirrinsa a yanzu, ya san dai za ta sani amma akwai lokaci!. Da dare yana dawowa ko ruwa bai watsa ba bare a yi batun cin abinci, Hajiya da Rahma suka saka shi a gaba da batun abin da ya faru, Rahma sai kuka take abin da ya sa hankalinsa ya tashi saboda ba ya haɗa damuwar Rahma da komai. Ransa ya ɓaci duk da Mummy ta cewa Rahma kar su bayyanawa Daddy furucin Sulaiman na cewa dama ba son ta yake ba da gaskiya kawai soyayyar shan minti yake son su yi, kuma sun ɓoyewa Daddy hakan nr don ya ɗauki maganar da muhimmanci ta yadda zai yanke tsatstsauran ra'ayi a kan Ma'aruf. Ran Daddy ne ya ɓaci ya ɗaga waya ya kira Ma'aruf, sai gashi ya shigo da sallama, Hajiya sai aika masa harara take tamkar idanunta za su faɗo. A ƙasan kafet ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai ya shiga gaishe da Daddy. Rahma sautin kukanta ta ƙara saboda Daddy ya yi hukuncin da ba zai yi wa Ma'aruf daɗi ba. Daddy ko amsa gaisuwar bai yi ba ya ce "Ma'aruf mai ya kai ka shiga sabgar da ba ruwanka? Mai ya sa ka bari haka ta faru a kan mai za ka yi yadda ka yi ka raba Rahma da mijin da za ta aura?" Baki ya buɗe zai masa bayani cikin nutsuwa amma sai Mummy ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce "A cikinmu babu mai maka ƙarya don haka ba bayaninka ake nema, ko kuma kare kanka, hujja kawai ,a ka bayar" Shiru ya ratsa falon saboda ya rasa ma mai zai ce. Daga haka Mummy ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har Daddy yana ce mata wataƙila shi Sulaiman ɗin ya dawo su shirya amma Mummy ta ce ai ba zai taɓa dawowa ba. Tashi ta yi ta fita, jim kaɗan sai gata da akwati niƙi-niƙi tana zuwa ta dangwarar da akwatin a gaban Ma'aruf ta ce. "Alhaji ni dai daga yau na bar zama da wanann mai nufin mutane da sharrin a gidan nan, dole ya koma ƙauye don ba zai zauna yake korewa ƴata samari ba, idan su basu yaudare ta ba shi ai ya yaudare ta da kalamai ya ya gusar mata da abin da kowace ƴa mace take taƙama da shi.... *INNA TA SALLAH* Tun kafin su ƙaraso fadar Mai Gari take hango rawanin Mai Gari take aikawa rawanin harara, ji take gabaɗaya har Mai Garin ma haushinsa take ji, a nata ganin ai shi ma ba zai ce kwana uku ba, tun da ya san a magana ta gaskiya ba lallai Ibra ya dawo ba a kwana kusa ma bare kwana uku ai dama sai ya ce daga wata uku zuwa shekara uku, wannan shi ne magana ta adalci. Zaunawa ta yi ta ce "Lami miƙo min saitin samirar wanann" Lami tana muzurai ta miƙa mata samira. A gabanata ta ajiye tana jiran abin da uban gayya wato Mai Gari zai ce domin ita ko arziƙin gaisuwa bai samu daga gare ta ba saboda tana ganin ai bai kamata tun da ya san ba ita ta ɗauki saniya ba yake mata aike kamar ta ci bashi. Gyaran murya ya yi ya ce "Tasallah ya za ki zo ki mana gurum da tsoffin kwanuka a gabanmu? Duk tunanina ma ko kaji ne kika soyawa fada kika taho da shi don in ke ci ina gabatar da shari'a cikin adalci, amma sai na ga an miƙo miki shafal da su samirun babu wani nauyi sai wata uwar lamba duk sun kwankwatse" Wani kallo ta masa ta ce ",Ai da kana son cin kaji sai ka aika mini zakara da kaza tun jiya da yamma, ka ga zuwa yanzu da na gama soyawa sai in taho maka da su" Ta faɗa tana kawar da kai gefe. Ƙwafa ya yi bai ƙara maganar naman ba don ya gane magana Innar ta faɗa masa. Ya cigaba da cewa "Ko gabatar da kanki baki yi ba kika yi gurum da ke" Idanu ta ɗago ta ce "Wai Mai Gari shari'a za ka yi a kan saniya ko kuma dai cin fuska za ka mini a gaban jama'a sanin kanka ne babu wanda bai san sunana ba Tasallah nake matar Malam kaka a wajen Ibra, mai ake neman sani kuma?" Ta tambaya tana kafe Mai Gari da ido. Taɓe baki ya yi don ya ji hashin yadda ta bashi amsar ya ce "To ina maganar mu ta kwana?" Shiru ta yi sai kuma ta ce "Yo tana inda ta kwana mana, a inda ka tsayar da ita ranar nan ina ganin ai bata motsa ba" Cike da jin haushi ya ce "Tasallah kar fa abin naki ya fara wuce gona da iri, ana batun saniya amma kina mayar da abin wasa kamar ana maganar tsuntsuwa" Ta ce "To mai kake so in ce in ban faɗi haka ba fisabilillahi, yaron nan an bashi saniya ya tafi bai shawarce ni ba ban san ma ua bar garin ba, amma sai tuhuma ta ake kamar tsohuwar ɓarauniya ina dalili" Mai Gari ya ce "Abu ne da ya zama dole, in ba a faɗa miki ba wa za a faɗawa yanzun nan kika gama gabatar da kanki har da inkiyar kakar Ibra, kin ga kenan ba laifi ba ne don mun nemi ki a cikin laifinsa" Kallon Jummai da take muzurai ta yi ta ce "To fa! Allah ya dawo da mu ke dai wannan mata baki da haƙuri a ce a kan saniya ɗaya kina azalzalar mutane" Jummai kamar jira take dama ta ce "Guntun gatarinka ya fi sari ka bani" Ta ce tana mata kallon up and down. Mai Gari ya ce "Ya isa haka Tasallah ku dakata yanzu dai duk magana tana wajen ki Tasallah" Cike da takaici Inna ta ɗauko ledar nan ta fara fito da atamfofin nan ranta yana ƙuna, sai da ta fito da su gabaɗaya tana duddubawa ta ce "Tsakani da Allah na kai zuciyata nesa, kafin in ɗakko wannan atamfofin ka gansu dai a wanke suke karrr, sun sha linki " Mai Gari ne ya ce "In za ka yi alheri ai ba sai a idanun mutane ba, sai ki bari sai kin je wurin wanda za ki ba jacen kayan sai ki fito da su yanzu dai batun saniya ake" ,Galala ta saki bari tana kallonsa hannunta riƙe da rigar atamfar ta mai dogon hannu, Lami ta shiga danne dariyarta don ta ga kamar dai Inna tana son bada kayan ne a maimakon kuɗi. Cike da masifa ta ce "Wane jace wai? Ni ina na ga arziƙin bayar da jacen atamfa sabbil dal ya wannan basu sha jiki ba, ai ni in ka ga na bayar da zani to na ga yana darewa ne ta wajen mazaunai, sai in ba mai so ya ƙarasa, amma waɗannan basu ji jiki ba daga wacce na saka sau goma sai wacce na saka sau sha biyar dama dama ɗayar ce ma na saka sau bakwai ita ce ta ganin aarki" Jummau ta ce "Mu duk wanann bai shafe mu ba... Inna ta katse Jummai da faɗin "To Almunafunfun masu zuwa lahira da ƙoƙon bara" Ta faɗa tana ɗaukan cinikin kayan miya ta miƙawa Mai Gari ta ce "Irga min nan" Da kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya karɓa ganin dubu biyu da ɗari takwas da hamsin sai ya washe baki don ya ɗauka ko ladan rufe baki ne ta bashi saboda ya sassauta mata a wajen shari'a. Yana gama doɓara yawu ya yatsansa ya irga ya faɗa mata yawansu, tana jin babu daɗi a ranta ta tura masa setin kwankwatsatstsun samirun nata kamar za ta yi kuka ta ce "Abu uku dai dole ya famshi abu ɗaya, ga atamfofi, ga samiru, ga kuɗi" Ya ce "Ban gane ba" Ta ce "Duka fa na bayar Jummai ta zauna a matsayin saniyarta" Tsaye Jummai ta tashi tana baloƙoƙo ta ce "In na yarda da wannan tatsuniyar in daskare a wajen nan, duk inda saniya take sai an nemo min" Inna tana kama haɓa ta ce "To tun da haka ne sai ki jira dawowar Ibra ya biya amma ni dai iya arziƙina kenan" Mai Gari ya ce "Tasallah baki da gaskiya, yanzu fa a wajen nan kowa ke yake jira ki ba Jummai kuɗinta don ta warawa Lami haƙƙinta" Inna ta ce "To sai dai a kaini mahauta wajen mahauta masu yankan nama, a yi cinikina su saya su yi tsirena su sayar in Allah ya sa na yi kasuwa shikenan sai a biya su amma dai ni bani da wani kuɗi wannan ma ƙundubala ce na yi zan koma in zauna in rungumi ƙaddara don jarin kayan miyar ne karkaf na kawo" Jummai masifa kawai take surfawa Mai Gari yana taka mata birki amma ta ƙi yin shiru hakan ya sa Inn tashi tana goge ƙwalla ta ce "Ni dai wannan abu bai mini rana ba, a ce baka ji ba baka gani ba ana maka titsiye a kan abin sa baka da laifi a ciki, Mai Gari bani wannan kuɗin" Mai Gari ganin Inna ta fitittike sai ya miƙa mata, ƙullewa ta yi a hannun zaninta, ta kwashe atamfofin ra mayar cikin leda ta ajiye a gefe ta janyo setin samirun ta daga gaban Mai Gari ta ajiye kusa da ledae atamfofin. Komawa ta yi ta zauna ta ce "Haƙiƙa tashin hankali ba a saka masa rana, sannan shi ya sa ba a son yin alƙawari saboda wata rana, da na ɗauki alƙawarin tun da Malam mijina ya bar duniya ba zan sake yin aure ba, amma yanzu ƙaddara ta gifta dole in yi aure, Mai Gari ina so tun da ga mijin Jummai a zaune, kaima gaka kuma ga mutane nan matsayin shedu" Dakatawa ta yi da bayanin tana share hawaye tsakaninta da Allah kuka take kowa ita yake kallo duk da basu gane inda maganar tata ta dosa ba ta ce "Na yarda na amince a ɗaura min aure da mijin Jummai, na yafe masa sadaki aurena da zai yi shi ne biyan bashin saniyar Jummai wallahi na amince zan aure shi" Jummai wacce ta koma ɗazu ta zauna yanzu sai gata a tsaye ba shiri... MAMAN AFRAH 09025576222 [7/13, 7:00 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 12 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture *INNA TASALLAH* Kamar Jummai za ta kai mata duka haka ta hayayyaƙo mata tana kumfar baki, Lami kuwa tsabar mamaki ta rasa bakin magana baki sake take kallon Inna ganin jiki duk yaba amma tana ambaton a aure ta kuma ma wai a fansar saniya, bayan kowacce mace ta tsani kishiya bare ma wai da bashin ta. Cike da masifa ta ce "Tasallah cin fuskar taki har ya kai haka a ce wai ni da kuɗina zan wa kaina da kaina kishiya, wato ga Jumman mahaukata ke ko kunya ma bakya ji" Inna haɓa ta kama ta ce "Mene ne abin kunyar a aure sunnar ma'aiki? Kuma ni a ganina da a zauna ana ɗauki ba daɗi ai gwara na aure shi shiknn" Jummai ta ce "Tsofai tsofai da ke sai ki auri jikan cikin ki?" Inna ta ce "Yo haramun ne kuma da kike wannan maganar sai ki ga ni tsohuwar na fiki kataɓus a gidan auren... Cike da haushi ta katse Inna da cewa "Yo Sale mai zai yi da ke" Inna ta ce "A'a Jummai tsakani da Allah kar ki ari bakinsa ki ci masa albasa ai sai ki bari ya bada amsa da kansa" Jummai tana nuna Inna da yatsa kamar za ta tsone mata ido ta ce "Yo wannan abu ai a bayyyane yake gwara tun muna shaida juna ki biya bashi in ba haka ba birni zan je in ɗakko miki ɗan sanda" Inna ta ce "Kulki za ki ɗakko mini, ke ko ƙarewa ki ɗakko soja" Sale ya ce "Haba Jummai ya ana neman masahala kina ƙin karɓa ko kin gwammace ake abu ɗaya wato faɗa" Juyaw Jummai ta yi bakinta sake tana son tabbatar da manufar mijin nata, saboda a yanayin maganarsa sai ta ji kamar dai yana goyon bayan Innar ne. Ya cigaba da faɗin "Tun da har ta amince ai babu komai in har hakan zai zama masalaha" Inna wani murmushi ta yi saboda ita dai ta san wannan ce mafita babu inda za ta samo kuɗin saniya. Jummai ta ce "Babu wani masalaha munfurci dai irin naka in ba haka ba, ta yaya za ka amince da auren tsohuwa" ,Mai Gari ya dakatar da su ya ce "Haba Jummai wai ni ku mata wani lokacin me ya sa bakwa son gaskiya, duk wani abu in dai aka ce warwarar matsala ne shikenan kuma mutum ba ya fita a wajenku" Zuwa wannan lokacin Jummai ta kai linta a ɓacin rai, ji take tamkar ta yi da dukan Sule, Inna da kuma Mai Gari, tsabar haushi. Lami ta ce "Inna wai da kike maganar aure da mijin Jummai da wasa kike? Idan ba da wasa kike ba ni kuma ya za a yi da nawa kuɗin" Inna ta ce Lami kin san dai ni guda ɗaya ce ba biyu ba, kuma dai jikana kike aure bare ke ɗin ma in ce zan aure mijinki a fanshe kuɗin, sannan tun da ba wani shegen ya aike ki basho sanoysr ba sai ki jira ya dawo ya biya ki" Mai Gari ne ya katse da cewa "Ni kaina na gaji da shari'ar nan kuma shi wanda ya cinye saniya ba a san inda yake ba ma, yanzu tun da Tasallah ta amince da auren Sale za a ɗaura auren... Jummai ce ta koma ta yi zaman ƴan bori ta ce "Yanzu Mai Gari wanann ne adalci? Ya za a yi a dakeni a hanani kuka, a cinye min saniya kuma a aure mini miji" Mai Gari ya ce "Idan har kin amince kin haƙura har ranar da Ibra zai dawo to, amma da sharaɗin kar in ƙara ganin ƙafarki a fadar nan" Jummai ta fitittike ta ce bata yarda da jiran Ibra ba kuma ba za a auri Inna ba. Sale ya ce ai ko an fasa shari'ar nan to fa shi dai aure da Inna babu fashi, a cewarsa ma zai biya Jummai kuɗin saniyar idan ya yi noma da damina" Kafin ya gama rufe baki Jumma ta je tsakiyarsa inda yake zaune tana ruwan bala'i, a ƙarshe dai Inna ta ce "Jummai ki kwantar da hankalinki auren nn na wuce gadi ne, idan na aure shi duk inda Ibra ya dawo to takardar sakina za a bani in bar muku gida, in ba larura ba ma ina ni ina aure a wannan shekarun nawa" Mai Gari bai jira komai ba ya fara gabatar da shawara a wajen jama'ar fada kowa ya ce wannan ce mafita, Sule ya kyallara idanu yana kallon Inna da wani murmushi Inna ta rufe fuska irin na jin kunyar nan. Har za a fara gabatar da ɗaurin auren Inna ta ce ",Mai Gari a ja kunnen Jummai fa kar a zo bayan aure take ce mini ƴar sadaka, ko take kiran aurena da auren biyan bashin saniya" Mai Gari ya ce "Ai sai dai in bana garin nan na Mai Mangwaro" Sule ya ce "Daga na bata kuɗin ta in na yi noma ai kin zama mallakina ma" Wani farrrr da idanu Inna ta yi. Mai Gari ya ce " A yi wa annabi salati" Jama'a suka ce S.A.W" Yaraf Jummai ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. *MA'ARUF* Da sauri Ma'aruf ya ɗago kansa yana kallonta, Rahma kuwa sai ƙwafa take a ranta tana cewa Allah ya ƙara maganin mai shishshigi da shiga abin da babu ruwansa. Daddy jikinsa ne ya yi sanyi jin furucin Hajiya tabbas yana son Rahma amma ba zai kori Ma'aruf daga gidansa ba saboda ya san Mai Gari yayansa shi ne sanadiyyar dawowarsa garin abuja da zama sannan a taƙaice ma shi ne silar arziƙinsa, yanzu yana jin nauyinsa ya kora masa ɗa gida saboda wanann maganar sannan ba zai iya yi wa su Hajiya musu ba hakan ya sa ya ce "To shikenan Ma'aruf ke ɗauki kayanka mu je in sauke ka a tasha sai ka je gida, idan ka je ka haɗani da Mai Gari in masa bayani" Cike da takaici da kuma da na sani Ma'aruf ya ɗago kai ya sauke a kan ɗan uwan mahaifin nasa, amma abin mamaki sai ya ga Daddy ya faki idanun su Hajiya ya ƙifta masa idanu, duk dabya kasa ganewa cewa gizo idanunsa suke masa ko kuwa dai ya ga Daddyn ya masa wata alama. Daddy ya ce "Amma yanzu tun da dare ya yi da safe sai ka tafi" Haka ya buɗe baki zai yi magana Daddy ya dakatar da shi, akwatin ya kinkima Hajiya tana murmushin nasara, na ganin sun jefar da ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda, Rahma har da cewa Allah raka taki gona. Da daddare bayan kowa na gidan ya yi bacci, Hajiya da ta gama ƙwawar Alhaji ya kwana a ɗakinta ya ce shi ba ya jin daɗin katifar ɗakinta saboda bata da laushi ya fi so ya kwana a ɗakinsa, ta rasa mai ya sa yanzu ya fi son kwana a ɗakinsa, ita kuma kawai bata son gadon ɗakinsa saboda irin ƙaramin nan ne bashi da wasaci sosai, wannan dalilin ya sa sai ta yi kwanciyarta. Yau ma kamar kullum hakan ce ta faru, Alhaji da tun da ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa ya hangi wayarsa da take kan bed side drower tana kawo haske wani murmushin gefen baki ya saki yana shafa haɓarsa, wajen wayar ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce ta kasance sunata ya gani kamar yadda ya yi saving my zee bakin gadon ya koma ya zauna ya ɗaga wayar cikin muryarta mai ɗauki da sinadarin shagwaɓa ta ce "Haba baby ka barni sai tsoron nake ji ina dakon jiran dawowarka" Ta faɗa tana sakin kukan kissa. Wata ajiyar zuciya ya sauke tana jin ta har cikin kunnenta cikin ƙasa da murya ya ce "Haba amarya ke kin san sai dai in wani abu ne zai riƙe ni amma ina nan zuwa gare ki, kin san dai daga kasuwa ma a nan na yada zango, to yanzu ma ina so ta yi nisan zango a bacci in lallaɓo in taho" Daɗi ne ya rufe Zee ta ce "Sai ka ƙaraso" Amsa mata ya yi yana lunshe ido tonowa da ya yi da cewa yanzu idan ya je tana nan sanye da kayan baccin nan nata masu taushi da kama jiki. Sai da ya ɗauki kamar minti talatin ya fito ya nufi ɗakin Mummy yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin, tun kafin ya shiga ɗakin kunnuwansa suka yi arba da munsharin da take sakin tamkar an shaƙewa raƙumi wuya, kasancewar tana da nauyin bacci har ya ɗan tsaya amma ko motsi bata yi ba ta yi shame -shame. Ƙofar ya jawo mata a hankali, ya rufo, ɗakinsa ya koma ransa fari ƙal, yana zuwa ya ɗauki wayarsa da kuma mukullin ƙofar baya wacce yake bi ya yi ɓadda kama ya tafi gidan Zee. Zee ƙawar Rahma ce amma ba ƙawa ta jiki sosai ba, sun yi aure da Daddy ba tare da sanin Hajiya ba kasancewar tsananin kishin Hajiya ya saka ta sanya shi ya mata alƙawarin ba zai mata kishiya ba, yanzu kuma da tafiya ta yi tafiya yana son ya yi auren amma babu hali. Don ba za ta bari ba, sun haɗu da Zee ne watarana ta zo wajen Rahma, bayan ta fita shi kuma yana ƙoƙarin shiga get ɗin gidan, hakan ya sa ya ɗauke ta a motarsa ya kaita har gida, daga nan ya karɓi lambar wayarta. Komai a ɓoye ya yi hatta bikin Zee Rahma bata san an yi ba, saboda lokacin ta je hoto Kaduna gidan wata ƙawar Mummy. Ya fito cikin dunu da yake gabaɗaya ƙwayayan gidan an kashe su, sannan shi ma ya kashe na ɗakinsa, yana lallaɓawa zai sauka daga matakalae kasancewar a sama suke, kamar daga sama ya ji an buɗe ƙofar ɗaki, da sauri ya ɗauke sawub takalminsa yana saurin ƙarasa sauka daga matakalar. haske ya hango an kunna fitilar harabar wajen, jin ƙaran tafiya ya yi saurin laɓewa, yana nan a laɓe sai ya ga Rahma ta sakko tana sanye sa doguwar rigar bacci hannunta riƙe da waya ta kunna fitilar. Gabansa ne ya faɗi saboda ya san matsawar ta ganshi sai ta gane shirin fita ne a jikinsa, don bai yi kama da mai bacci ba, kuma ya san idan ta ganshi tamkar a kunnen Hajiya sai ta faɗa mata. Fitilar falon ta kunna ta nufi frige ta buɗe ta ɗakko ruwan roba ta rufe, fitilar ta kashe ta haura sama, sai da ya ga duhu ya rasa saman alamar ta kashe fitilar kuma ya ji ƙaran buɗe ƙofa da rufewa, alamun ta koma ɗakin ta. Ƙofar falon ya buɗe ya fita ta ƙofar bayan gidan ya kulle ta, machine ya samu ya tsare ya hau ya nufi gidan amaryarsa. Yana zuwa ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa ya shiga, yana zuwa part ɗinta ya ta buɗe ƙofar ya shiga ta rufe,

Chapter 10 of 14